NA RANTSE DA SAMA MA'ABUCIYAR MAIDOWA

NA RANTSE DA SAMA MA'ABUCIYAR MAIDOWA

 

Allah(s.w) na cewa" na rantse da sama ma'abuciyar maidowa"(al- tariq 11)

Allah(s.w) na cewa" na rantse da sama ma'abuciyar maidowa"(al- tariq 11)
 
Haqiqar ilimi:

sararin samaniya na maida tururin ruwa da ya tashi zuwa gareta da siffar Ruwar sama.

Sararin samaniya na maido da abuwuwa da dama zuwa qasa bayan sun tashi daga qasan.

Sararin samaniya na maida wasu tartsatsin haske masu kashe rayayyu nesa da qasa.

Sararin samaniya  na akasta sauti da amo na kusa da na nesa zuwa qasa, wato yana xaukan sauti daga qasa sannan ya maida shi qasa kaman amsa amo da sautin talfo da sauransu.

Sararin samaniya yayi kama da madubi da take xaukan zafi, sai ta riqa kare mutum daga zafin rana, kuma kamar yadda yake kariya da dare, da za a sami tangarxa awannan tsari da komai yaya lalace da kuma rayuwa tayi wahala, ko dai saboda tsananin zafin rana ko sanyin dare.
 
Fuskacin mu'ujizar:

Ayar Alqur'ani tayi nuni  " da sama ma'abuciyar maidawa" ga muhimmin sifar sama wacce take kewaye da doron qasa, wato da cewa ma'abuciyar maidawa, malamai magabata sun fassara wannan abu da ruwan sama ne kawai,sai ilimi yazo daga baya don ya zurfafa wannan ma'ana ta hanyar yadda sararin samaniya ke yin wasu ayyuka da dama na maidawa xin, ba ma kawai ruwa ba, kamar amon sauti, abin nufi da sama anan shine makarin saman da yadda ya ke tare komai don kada ya cutar da halittu, bai cin wannan aiki da yake yi da rayuwa tayi wahara a doron qasa baki xaya, saboda haka Alqur'ani ya taqaita abin da kalmar " ma'abuciyar maidawa