CUXEXENIYAR TEKUNA DA BANBANCIN RUWA

CUXEXENIYAR TEKUNA DA BANBANCIN RUWA

 

Allah yana cewa:"ya garwaya teku biyu(ruwan daxi da na zartsi) suna haxuwa.* A tsakaninsu akwai shamaki, ba za su  qetare haddi ba.* To, saboda wane daga ni'imomin Ubangijinku , kuke  qaryatawa.lu ulu u da murjani na fita daga gare su."(19-22 Al Rahman ).
Haqiqanin Ilimi:
ba asan cewa tekuna nan gishiri dangi dangi ne ba. awurin garwayarsu, kuma tekuna ba iri xaya ba ne, sai a shekara ta 1830 a ka gano haka lokacin da wani mai binciken tekuna (Chalenger)  ya kewaye tekuna na tsawon shekaru uku, a shekara ta 1942 akaran farkoya sami sakamakon binciken bayan da aka kafa tashoshi a cikin ruwa.sai suka gano cewa tekun Atalantika ba teku  xaya ba ne. a'a akwai koguna da yawa a ciki, duk da cewa teku guda ne , ko wane yanki,na ruwa ya yi daban a darajar zafi da sanyi da zartsi da daxida kuma irin halittun da suke rayuwa ciki, da kuma karvar oksajin da narkewarsa, duka wannan a cikin teku  xaya ke nan.Ina kuma  ga koguna biyu mabambanta. Kamar ruwan Bahar Maliy,da kogin Bahar Rum, da kuma tekun Atalantika da kogin gulf  ta Adan. Ance dukansu suna haxuwa ta wasu mahaxai.
A shekara ta 1942 aka gano cewa akwai wasu koguna da ruwansu yake gaurayuwa amma ko wannaensu ya yi daban wurin xanxanonsa da kamanni. Ruwan teku a ayaune yake ba yana cikin motsi ne ko da yaushe,, abin da ya sa ko wane vangare na cakuxuwa da wani vangare , amma duk da da haka akwai shamaki a tsakaninsu ba sa haxuwa.
Fuskacin mu'ujiza:
Ayoyin suna magana ne game da tekuna biyu ko koguna biyu, masu maqwabtaka da juna, suna kuma gaurayuwa ,amma ko wane vangare na da nasa siffofi da kamannu akwai shamaki tsakaninsu ba sa tsakuxuwa. Kuma ambaton lu'ulu'u  da murjani da akayi a cikin ayoyin sun tabbatar da cewa tekunan duka na gishiri ne, domin ba a samunsu sai a cikin kogunan zartsi. Abin da ke kara tabbatar da cewa tsakuduwar tekuna biyu masu zartsi baya nufin dukansu suna gauraya.
Kamar yadda duk mai kallo da ido zai gansu kamar a haxe suke amma kowanensu na da nasa siffa,amma duka ba a gano wannan bayanai ba sai da aka sami takanolojiya mai qarfi sanna aka gano haka,amma Alqur'ani mai girma ya yi mana wannan bayani a cikin ayoyi bayyanannu, shin wannan ba dalili bane da yake tabbatar da Alqur'ani maganar Allah bane?