Haramta naman Alade ilimi ya bayyan haka

Haramta naman Alade ilimi ya bayyan haka

 

Allah(s.w):" kace ba sami wani abu daga cikin abinda aka yi min wahayi da shi ba haramtacce, na abinci sai dai in ya kasance mushe ne ko jini n yanka ko naman alade, to shi najasa ne ko fasikanci aka yanka ba don wanin Allah. .wanda ya ya matsu ba mai  qetare iyaka ba ko shisshigi  to lalle Ubangijinka mai gafara ne mai rahama" Al-an'am 145).
Haqiqar ilimi:
ilimi ya zo ya riski waxansu fuskokin da ya sa Shari'a ta hana wasu abubuwa a Musulumci, abin da ya kare mabiya qarnoni da dama tun kafin a gano madubin likita kuma ajere : Mushe dai akwai wasu kwayoyin cuta da suke tasowa daga cikinsa,sannan jini shima kwayoyin cuta suna saurin yaxuwa aciki  Aqarshe Alade wanda ya ke  qumshe da tili wasu cutuka acikinsa wanda ba sa wankuwa,domin wari yana tattare da kwayoyin cuta da suke kaiwa ga mutane da dabbobi. Akwai wasu da suke Aladu kawai ke xauke dasu kamar cutar (Trchinella) da cutukan( Balantidium Dysentery) da tsutsotsin ciki (Taenia Solium) da macijin ciki(Spiralis) wasu cutukan kuma mutane ma na  xauke dasu kamarsu:( Cysticercosis da mura (Influenza) da kuma murar (Zoonoses. Kuma an gano cewa akwai wasu cutuka da masu yawan mu'amala da Aladu suke yawan kamuwa da su. Kamar yadda ya faru a wani tsibiri tekun indiya, lokacin da aka sami ambaliyar ruwa ta kwaso turoson Aladu cuta ta yaxu ayankin kamar annoba. Kuma irin wannan cutuka suna yaxuwa a wuraren da ake kiwon aladu hatta a irin  qasashe kamar Jamus,Faransa, filipin da Benuzuwela.
Kuma cin naman damatsar Aladu tana kawo cutar(Trichinellosis) kuma waxannan cuta sukan bi jini su shiga mahaifar macen Alade sannan cin naman da ya kamu da irin wannan cuta yana haifar da macijin ciki da sauranran dangin cutuka,ta yadda kuma suke zuba wasu kwayoyin cuta dubanni su kuma shanye jinin mutum, musamman ma irin macijin cikin nan mai kawuna da dama (Taenia Saginata).
Fuskacin mu'ujizar:
al'adu suna da munanan xabi'u kuma ana kyamarsu hatta ma ga masu bautan gumaka, inda suke sifatasu da cewa suna kashe Allolin alheri, tatsuniyoyi na cewa Alade ne ya kashen Horus  na misirawan da, da Adwan na Kan'anawa . da Odonis na Girkawa, da Itis na mutanen Asiya . kuma misarawan da suna kallon masu kiwon Aladu mutanene mara qima da kamala,hakan nan kuma masu kiwon Aladu ba sa auren  kowa sai yasu-yasu, kuma dukkan wanda ya shafi Alade yayi wanka.
Haka ma an harantawa Ahlul kitabi cin Alade duk da cewa sun savawa addinin. Amma addinin musulumci ya bayyana dalilin haranta naman Aladeda cewa (qazanta ne)ko cuta ko najasa duk ta kumshi wannan ma'ana ayoyi har uku suka bayyana haramcin naman Alade: Allah (s.w) na cewa"lalle an haramta maku mushe da jini da naman Alade , da abin da aka yanka don wanin Allah, wanda ya ya matsu ba mai qetare iyaka ba ko shisshigi  to lalle Ubangijinka mai gafara ne mai jin qai" (An-nahal :115) .
Allah (s.w) na cewa "an haramta maku mushe da jini da naman Alade da abinda aka yanka don wanin Allah…"(Al-maida 3).
Kuma haramcin ya kunshi kitsensa da aka haramtawa yahudawa kawai ya nuna mana cewa ya shafi namansa kamar yadda Allah (s.w) yake cewa: " ga yahudawa mun haramta duk wani abu mai akaifa,daga shanu kuma da awaki mun haramta masu kitsensu ko abin baynasu ke xauke dashi ko kayan ciki ko abinda ya cakuxu da qashi, wannan mun sakanya masu da shisshinsu lalle mu masu gaskiya ne" (Al-an'am 146).
Haranta kitse ya qumshi haranta nama koda ko kamar raugar dabbobi ne da mutum zai ci . alokacin da Al'qur'ani ya sauka mutane ba su san haxarin da Alade ke xauke dashi ba, ta yaya zamu sami wannan garkuwa in dai ba ta hanyar ilimin da Allah maxaukakin sarki ya saukar mana da shi ba.:" Al'ummanka suka qaryata dashi kuma shi gaskiya ne.ka ce ni ba madogaranku bane, kuma ko wane labari na da matabbaci da sannan ya ku sani" ( Al-an'am 66).