HAUHAWA ZUWA SANA

HAUHAWA ZUWA SANA

 

 

Allah (s.w) na cewa" wanda Allah ke son ya shiryar dashi sai buxe zuciyarsa da musulumci, wanda kuma yake so ya vatar dashi zai sanya qunci a qirjinsa kamar mai hauhawa zuwa sama, haka Allah ke sanya datti akan waxanda ba sa yin imani" (al-an'am 125)

Allah (s.w) na cewa" wanda Allah ke son ya shiryar dashi sai buxe zuciyarsa da musulumci, wanda kuma yake so ya vatar dashi zai sanya qunci a qirjinsa kamar mai hauhawa zuwa sama, haka Allah ke sanya datti akan waxanda ba sa yin imani" (al-an'am 125)
 
Haqiqar Ilimi:

Da can ba asan yadda tsarin yana yi yake ba sai da wani malami wai shi Pascal ya gano ashekara ta  164 8 cewa qarfin iska na raguwa aduk lokacin da aka yi sama  bisan teku, sanna kuma daga baya aka gano cew a iska ya fi tattaruwa a qqarqashin rufin iska na qasa da kusan 50% na deukkan iskan da yake cikin yaanayi ,hakanan kuma ya kan ragu da kusan wannan adadin tsakanin doron qasa da bisan da yakai  qafa dubu ashirin (20,000 ) , da kuma yawan(90%) daga bisan qafa dubu hamsin daga doron qasa(50,000) , ataqaice ana samun raguwar qarfin iska duk lokacin da akayi sama, har lokacin da zaa kai inda babu samuwar iskan, samuwar mutum a bisan da ya gaza qafa dubu goma(10,000)ba zai kawo mashi babban haxari ba, don zai iya yin nunfashi a yanayin da yayi bisa kamar qafa +dubu goma zuwa dubu ashirin da biyar(10,000-25,000), saboda duk lokacin da mutum yayi sama qarfin iska na raguwa da kuma raguwar Okosajin abinda zai haifar masa da wahalar nunfashi a qirji duk lokacin da buqatuwar Oksajin yayi yawa wahalar mutum kan karu wurin nunfashi , in yayi yasa yai kai shi mummunar kamuwa da ciwon nunfashi da ake kira (Oxygen Starvation) abin da zai kai mutum ka kamuwa da (Respiratory System). Har yakai ka hallaka.
 
Fuskacin mu'ujizar:

Kamar yadda aka sani cewa mututane a irin lokuta da suka gabata alokacin wahayi ba su san abin da yake faruwa wa na yanayi samaniya da iskar gaz da ya ke yaxuwa, balle har su san cewa idan aka yi bisa yana raguwa, ko qasa yana qaruwa ba. Balle har su san cewa okusijin na da mahimmanci ga rayuwa ba duk lokacin da aka yi bisa buqatuwa gare shi yana qara qaruwa.har idan aka ce mutum ya rasa shi zai kai shi ga rasa iya nunfashi abinda zai kai shi ga hallaka.

Kai mutane ma sun kasance suna zaton cewa duk lokacin da mutum yayi bisa ya fi kusa da iska, kuma qirjinsa zai fi walwala.

Ayar Alqur'ani kai tsaye na mana nuni ga wasu haqiqa biyu, waxanda

Ilimin zamani ya tabbatar dasu:

Na farko: quncin qirji da wahalar nunfashi,a duk lokacin da mutum yayi sama a sararin samaniya, daga baya aka gano  cewa saboda raguwar okosajin ne.

Na biyu:irin turnuqewa dake rigayar mutuwa lokacin  da mutum ya sami kansa a bisan samaniya na nisa qafa dubu talatin, saboda matsanancin buqatuwar okosojin masu shiga huhu, daga nan mutum zai kai ga hallaka.

Gami da qari kalmar da Allah yayi amfani da ita wato"hauhawa" abin da ke qarawa abin qarfi da tsanani, don ya bayyana yadda yanayin wahalar da mai hawa sama yake fuskanta . shin wannan haqiqa in banda Allah (s.w) wa zai iya sanar damu ita. Lalle wahayi ne daga Allah