JIN ZAFI KO RAXAXI

JIN ZAFI KO RAXAXI

 

Allah (s.w) na cewa "lalle waxanda suka kafirce da ayoyinmu da sannu zamu qona su da wuta, a duk lokacin da fatar su ta nuna sai mu sauya masu fata sabuwa , don su xanxani azaba, lalle Allah ya kasance mabuwayi ne mai hikima" (an- nisa'I 56)

Allah (s.w) na cewa "lalle waxanda suka kafirce da ayoyinmu da sannu zamu qona su da wuta, a duk lokacin da fatar su ta nuna sai mu sauya masu fata sabuwa , don su xanxani azaba, lalle Allah ya kasance mabuwayi ne mai hikima" (an- nisa'I 56)

Allah (s.w) na cewa:a shayar dasu ruwa mai zafi sai ya yanke masu hanjinsu"(Muhammad:15)


Haqiqar ilimi:

Da can kafin bayyanar ilimin zamani ana zaton dukkan jiki ne ke jin zafi mutane ba su gano cewa akwai wani yanki na fata shi yake xaukar zafi  da raxaxi ba. Har sai lokacin da ilimi ya gano haka , inda docta Head  ya kasa jin fata zuwa kishi biyu: ji mai tsanani (Epicritic) shine ya shafi jin shafa xan kaxan ta rarrabewa tsakanin zafi. Da kuma ji na farko( Protopathic) shi ya shafi  jin zafi, da kuma darajar zafi mai tsanani,ko wanne acikin yana aikin sa daban ne kamar yadda kuma akwai wani yanki na musamman da yake banbance yanayi( Receptors) shi kansa ya kasu kishi hudu: halittun da suke  tasiri da yanayin waje(Exterocetors), wato na vangaren shafa, da sauran jiki (Meissners Corpuscles) da kuma( Merkes  Corpuscles) wato na hallitun gashi, da qarshen Erause  End Bulbes) wato mai jin sanyi, da kuma (Rffini,scylinders) mai jin zafi ke nan wato qarshen mai xaukan zafi  da raxaxi.wato fata shi yafi komai dauran xaukan zafi da raxaxi.

Kamar yadda malam likata suka tabbatar da cewa wanda ya fatarsa ta kone baki xaya baya jin zafi da yawa saboda ya rasa wannan yanki za yake xaukan zafin ko raxaxi. Ba irin konewa xan kaxan ba inda zai fin kan qaru sosai saboda an isa wurin xaukan zafin  kai tsaye.kamar yadda likitoci suka tabbar da cewa irin kananan hanji na kusa da uwar hanji ba shi da abin daxkan zafi ,a mma uwar hanji da sauran hanji suna da wannan abin da yake xaukan zafin, abin da aka tabbatar da cewa yana dauke da kwayoyin halittu da suka kai 20400 sanimita  kuma yawan sa ya kai yawan halittun da suke cikin fatar da take daukan zafi awaje.
 
Fuskacin mu'ujiza:

Allah ya bayyan a cewa Fta shine wurin xaukan azaba sai mai girma da xaukaka ya haxa azabar da fata da zafin a cikin ayan farko ya bayyan cewa idan fatan ta nuna sai asauya masu wata fatar mai xauke da irin wannan halittun da suke xaukan zafi  don asanya wannan kafirin yai ta shan azaba da qunar wuta.

Kuma ilimin zamani ya gano cewa cewa fatar baya baya  ita ce ke daukan zafi  da raxaxi  da quna, abin da babu wani mahaluqi da zai iya fahimtar haka bayan ci gaban ilimin likitanci wanda ya gano wannan haqiqar da Alqu'ani mai girma ya bamu labari, aqarni goma sha huxu da suka gabata. Haqiqa wannan na qara bayyan ayoyin Allah maxaukakin sarki

Alqur'ani ya tsoratar da kafirai da azaba da ruwan zafi mai yanke uwar hanji a cikin aya ta biyu, daga baya aka gano cewa uwar hanji bata jin zafi sai idan an yanke ta sai ruwan zafin ya shiga ya isa zuwa kwakwalwa ta hanyar wasu halittun fata masu xaukan zafi daga nan sai mutium yaji zafin da quna da raxaxi.

anan zamu ga haqiqani mu'ujizar ta bayyana bayan da haqiqar ilimi ya tabbara abin da Alqur'ani mai girma ya riga ya faxa.