NA FITALA CE WATA KUMA HASKE

NA FITALA CE WATA KUMA HASKE

Allah (s.w) yana cewa: ‘Tsarki ya tabbata ga Allah da ya sanya burujjai a cikin sama. Kuma  ya sanya kuma fitila da wata mai haskakewa  a cikinta.* (al- Furqan 61)

Allah (s.w) yana cewa: ‘Tsarki ya tabbata ga Allah da ya sanya burujjai a cikin sama. Kuma  ya sanya kuma fitila da wata mai haskakewa  a cikinta.* (al- Furqan 61)
 
Haqiqar ilimi:

Qarfin rana( makamashin nokiliyar duniya):ana samun hasken rana ne ta hanyar konewar haydrojin shi ne babban makamashinta yadda take sarrafa shi zuwa hiliyom a cikinta ta yadda za a sami zafi da xumama da zai kai darajar miliyan 15,  abin da zai haifar da aikin makamashin nokiya da zarrar haydrojin huxu sai su samar da hiliyon guda, ta yadda ciki da wajen ranar za su riqa fitar da hasken maganaxisu ta yadda hasken zai riqa fita ta qarqashin wani jan da wani mai ruwan rawaya, abin da yake nuni da cewa rana na samun haskensa ne ta hanyar zafin da yake faruwa ta hanyan haxuwar makamashin da yake cakuxuwa ta makamashin nokiliyar duniya. Domin rana tauraro ne  wato jiki ne mai haske da kansa, amma wata tararuwa ce da take tabbatacciya wacce take karvar haske daga daga sauran taurari da rana.
 
Fuskacin mu'ujizar:

Nassoshin qur'ani sun tabbatar tun shekaru dubu da xari huxu da cewa akwai bambanci tsakanin tauraro da kaukabi  kamar rana da wata, kuma shi ne abin malaman falaki suka tabbatar a wannan zamani namu bayan da aka samu wasu abubuwa na gwaje gwaje da hange hange da abubuwan xaukan hoto na haske a cikin qarnoni kadan da suka gabata. Tauraro dai jiki ne mai haske a sama wanda yake fidda haskensa daga cikinsa, amma kaukabi  shi fidda hasken da yake amsa daga rana da taurari ya ke yi,kuma wannan abin haka ma sauran kaukabai suke yi.

Rana kamar wani babban makamashin nokiliya wanda yake yawa a sararin samaniya cikin saurin gaske tana da haske da zafi mabambanta a yawanu da yanayinsu, ba wani jiki ne mai matabbacin haske ba . a a shi jiki ne mai haske mai yawan juyawa( mun sanya fitila mai juyawa)  Al- Nabai 13.

Amma wata jiki ne wai fitar da hasken rana sai ya haskaka duhun duniya. Wannan shi ne abin da Alqurani ya tabbatar a cikin waxannan ayoyin biyu. To wanene ya sanar da Muhammad (S.A.W) waxannan bayanan na ilimi? Haqiqa sai dai Allah sarki mabuwayi.