Game da rubutattun maudu'ai

mawallafi :

www.eajaz.org

kwanan wata :

Thu, Jan 15 2015

Bangarori :

Buwayar Ilimi

Rigirigen jiki

Rigirigen jiki

 

Manzo (s.a.w) ya ce : misalin muminai wurin san hunansu da tauyinsu da qaunan junansu, misali jiki ne idan gava xaya daga ciki ta sami rauni sai sauran gavovin jiki suyi rige rige wurin jin zafin da rashin barci." Buhari da Musulum suka ruwaito da wasunsu.

Manzo (s.a.w) ya ce : misalin muminai wurin san hunansu da tauyinsu da qaunan junansu, misali jiki ne idan gava xaya daga ciki ta sami rauni sai sauran gavovin jiki suyi rige rige wurin jin zafin da rashin barci." Buhari da Musulum suka ruwaito da wasunsu.
 
Haqiqar ilimi:

Binciken ilimi da aka yi da dama sun tabbatar da cewa:  a lokacin da wani abu ya sami jiki na haxari ko jin ciwo akwai wasu hanyoyi da sauran gavuvva suke ba da gudumuwar kariya ga wannan gavar da ta kamu.

Kuma wannan kariya da gudunmawa ya danganta ne gwargwadon girman ko qanqancin ciwon, duk lokacin da jin ciwon yayi qarfi a lokacin bada gudunmawar ke qara karfi  haka kuma idan abin ya zamanto qarami ne haka lamarin yakan kasance.

Misalin lokacin da aka sami wani rauni agava sai kwakwalwa ta kira wasu vargo dake ciki su su zuba wasu abubuwa waxanda za su kare wannan wurin rauni daga shigan wani irin kwayar cuta, da kuma wasu abubuwa mai danqo da zai riqa zuba don ya sanya wurin yayi saurin warkewa ataqaice ko yane vangaren jiki zai riqa bada nasa gudunmuwa na abin da yake dashi don wannan gavan da yake da rauni ya sami sauqin warkewa ta hanyar gudunmawa da taimakekeniyar sauran gavovin nasa. Wannan shi ne abin da haqiqanin ilimi ya tabbatar da shi a likitance.
 
Fuskacin mu'ujizar:

Abin da hadisin ya faxa shi ne abin da yake faruwa a likitance, wato duk gavovin jiki suna kiran junansu da rige rige, kamar yadda Manzo (s.a.w) ya ba mu labari na yadda halin musulmai ya kamata ya kasance wurin soyayya da qaunar juna da tausayi, sai ya buga misali da jiki a lokacin da wani rauni ya sami gava daga gavovinsa, kuma babu wani abu da yafi wannan kalma da ya yi amfani da ita wato "rige rige" don ita tafi dacewa da wannan wuri kuma wannan haqiqan haka yake a likitance tun da har likitoci suna amfani da garkuwar jiki da wannan suna don shi yake bada gudunmuwa na gaggawa da kiran sauran gavovi wurin taimako,kuma wannan shi ne abin da Manzo yake nufi  da soyayya da qaunar juna acikin wannan hadisin.