Taurari masu tafiya masu gudu suna vuya

Taurari masu tafiya masu gudu suna vuya

 

Allah(s.w) na cewa : ba sai na rantse da taurari masu tafiya ba* masu gudu suna vuya"(at-takwir 15-16).

Allah(s.w) na cewa : ba sai na rantse da taurari masu tafiya ba* masu gudu suna vuya"(at-takwir 15-16).
 
Haqiqar ilimi:

Taurari idan suka riqa suna kai wani munzali da suke tsufa ana kiransu da (Black Holes) sukan sami huji baqi wanda yake da girman gaske wanda yafi girman rana da ninki biyar,kuma tana da qarfin maganaxisu awannan lokaci ta inda take janye duk wani abu da yayi kusa da ita da kusan kilomita(dubu 300 acikin daqiqa) shi yasa ake kiranta da ramuka masu janye dukkan wani abu da yayi kusa dasu, na kananan taurari(Giant vacum-Cleaners) wato suna share duk wani abu da yayi kusa dasu kamar yadda(Karl Schwars ) a shekara1916 da kuma(Child) ashekara ta 1934, a kuma shekata ta 1971(Oppenheimer Robert) ilimi ya tabbatar da cewa idan tauararuwa ta soma tsufa takan yi huji baqi inda take haxiye duk abinda da yayi kusa da ita.
 
Fuskacin mu'ujiza:

Salon Alqur'ani mai girma na  kore rantsuwa, kamar yana cewa ne ba sai na rantse da abinda kowa yake ganini qiriqiri ba, wannan salo kuma ya qara tabbatar da cewa Alqur'ani wahayi ne na Allah  da yake cewa" ba sai na rantse da taurari masu tafiya ba* masu gudu suna vuya* da dare yayin da yayi duhu da safiya yayinda tayi haske* lalle shi maganan manzo ne mai girma"(at-takwir 15-19) kuma duk abinda Allah ya rantse dashi to lalle abin nada mahimmanci wurin kafa hujja dashi, annan wurin abin da aka faxa ya dace da hujin taurari ko tsufarsu kamar yadda ake faxi,shi yasa sifata su da aka yi da (masu gudu) ya dace da gudun da suke yi,amma kalmar(masu vuya) ita ma ta dace da abin da yake faruwa mata na vuya da vacewa da tsufa ko mutuwa bayan ta girma ta zama abar sha'awa.kuma haka abin yake kasancewa lokacinda tauraruwa ta shufa sai ta sami wani hujji ta kuma vace baki xaya ta zamo bata da haske, saboda tana janye dukkan wani haske da yabi kusa da ita. Shi yasa aka kira su da sunan "masu gudu suna vuya" anan zamu ga Alqur'ani ya sifatasu da siffofi da suka dace abinda ilimin taurari na zaamani ya gano, abinda yake tabbatar da cewa wannan magana ne na Allah (s.w).