Game da rubutattun maudu'ai

mawallafi :

www.eajaz.org

kwanan wata :

Thu, Jan 15 2015

Bangarori :

Buwayar Ilimi

YANKIN DA YAFI KO KWARI A DORON QASA

YANKIN DA YAFI KO KWARI A DORON QASA

 

Allah (s.w) yana cewa: An rinjayi Rum* a mafi kusan qasa, kuma su bayan rinjayar ta su za suyi galaga* a cikin tsukin shekaru al'amura na Allah gabanin haka da bayan haka, a wannan rana musulmai za su yi farin ciki*(al—rum  1-4).
Haqiqar ilimi:
Littafan tarihi sun bayyana aukuwar yaqi tsakanin daular Farisa da Rumawa- wato yankin gabashin daular Rumawa – a wani yanki dake tsakanin Azri'at da Basara kusa da tekun mayit a lokacin da farisa ta ci nasara a kan Rumawa a shekara ta 619. Hakika Rumawa sun yi babbabr hasara a wannan yaqin har waxanda suka halarci yakin su tabbatar da mutuwar daular Rumawa.. amma abin da ba ayi zato ba shi ya auku a watan satumba ta shekara 627 a ka sake yin yaqi tsakanin Farisa da Rumawa a garin Nineveh. Rumawa suka ci nasara a kan Farisawa, bayan watanni Farisawa suka nemi sulhu da Rumawa don a maida masu wuraren da suka qwace daga garesu.
To masu ilimi sanin qasa qawo jogurafi sun tabbatar da cewa yankin da yafi ko ina kwari a doron qasa shi ne garin da yake kusa da tekun Mayit a falasxinu inda aka tabbatar da cewa ta yi qasa ta zurfin ruwa kimanin mita 395. kuma hotunan da ka xauka ta tauraron xan Adam sun tabbatar da haka.
  Fuskacin mu;ujiza:
Akwai fuskoki biyu na mu'ujiza a nan a wannan ayoyi masu tsarki da farko: qur'ani ya ba da labarin nasara da Rumawa za su yi a kan Farisawa bayan sun yi nasara a kansu a tsukin shekaru |"kalmar Bidh'i " a cikin larabci yana nufin daga shekaru uku zuwa tara . kuma abin da Qur'ani ya ba da labarinsa ya auku a cikin shekaru bakwai  a lokacin da yaqi ya sake aukuwa a shekara ta 627 kuma Rumawa suka yi nasara a kan Farisawa kuma abin ya zo dai dai  lokacin da musulmai suka yi nasara  ayiqin Badar.
Da mushirikan larabawa suna ganin wannan nasara ba zai tava aukuwa ba har suna yi wa musulmi izgili da maganan Alqur'ani suna cewa magana yadda wannan abin zai yi ya auku, sai suka kunyata lokacin da abin da Qur'ani ya ba da labarinsa ya auku wato nasarar Rumawa a kan Farisawa.
Na biyu: haqiqa ta jogurafi ya tabbatar da cewa wannna wuri shi ne yafi ko ina kwari a doron Qasa kamar yadda Qur'ani ya ba da labarin cewa nasara zata auku ne a mafi kwarin wuri. " kalmar Adna" a larabci tana nufi kusa ko kwari, a vangaren kusa wannan ruri ya fi ko ina kusa ga jazirar larabawa.a vangaren kwari kuma wato wurin yana qasa da zurfin ruwa kusan mita 400, kuma  shi ne mafi kwarin wuri da tauraron Dan Adam ya dauki hotonsa  kamar yadda Insakwafidiya ta Birtaniya ta tabbatar. Kuma tarihi ya tabbatar da cewa wannan abu ya auku ne a wuri da yafi ko ina kwari  wanda bai cin cigaban ilimin zamani ba wanda yasan haka lamarin yake.. shin wannan ba zai tabbatar mana da cewa Qur;ani daga wurin Allah yake ba. Hakika Allah yayi gaskiya da yake cewa " ka ce godiya ya tabbata ga Allah  zamu nuna maku ayoyinsa za kuma kusansu"