Game da rubutattun maudu'ai

mawallafi :

www.eajaz.org

kwanan wata :

Wed, Jan 14 2015

Bangarori :

Buwayar Ilimi

YIZGAR FARKO NA HALITTA

YIZGAR FARKO NA HALITTA

 

An ruwaito daga Abu huraira cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: dukkan xan Adam turvaya na cinsa sai dai kawai yizgar farko daga shi ne aka halicce shi a cikinsa ake harhaxa shi"

An ruwaito daga Abu huraira cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: dukkan xan Adam turvaya na cinsa sai dai kawai yizgar farko daga shi ne aka halicce shi a cikinsa ake harhaxa shi"
 
Haqiqar Ilimi:

Yizga a cikin ilimin halittu ( shi ne faifan  farko):

Ilimi halittu ya tattabar da cewa  yizga shi ne faifan farko acikinsa ne ake haxa jariri lokacin da zai zama tayi sannan har a sami qashin bayansa bayan da shi wannan faifan ya vace .

Haxa faifan farko: A rana ta goma sha huxu igiyoyin ciki da na waje na tayi za su fara haxewa su zama kaman yana yi gwaiba a dunqule sai qasan ya yi faxi kasan kuma ya tsuke sai qasan ya zama ya yi wutsiya kaman na gwadari ta nan wannan faifan farkon yake haxuwa a rana ta goma sha biyar.

Daga nan kuma sai ya fara rarrabewa ya fara toho jijiyoyi su yi yawa dama da hauni bayan haka ya faru ne sai asami qashin baya kuma a fara samun tsiran gavovin jariri. Amma idan ba a sami haxuwar wannan faifan  ba za a sami tuhuwar gavovin jariri ba, balle har a sami wani qashin baya.

Saboda mahimmancin wannan faifan kwamitin ilimin halittan tayi na Ingila suka sanya lokacin da likitoci zasu iya samin lokacin da zasu iya bincike da gwaje gwaje game da jariran da ake rainonso a kwalba. A lokacin da wannan faifai ya fito saboda kai komo da motsin da zai riqa yi za aga bayyanar abubuwa kamar haka:

A lokacin da za a rufe wannan kwalba za a ga bullan faifan kunne da alamun ido.

Kwakwalwa kuma na haxuwa asaman wannan bututun jijiyar  sai ya  samar da vargo a yankin qasa sai afara samun ginuwar qashi kwakwalwa.

Wato dai ataiqaice wannan faifan farko xin shi ne babbabr alamar fara halittan jariri kuma daga baya zai fara dishewa har ya zamana ba a ganinsa da ido sai dai da madubi likita a lokacin da aka sami ginuwar kashin baya kenan .
 
Fuskacin mu'ujizar:

Wannan hadisin na yizgar farko ko kuma faifan farko xin yana xaya daga cikin mu'ujizarsa (s.a.w) kuma ilimin halittun tayi ya tabbatar da cewa ta nan ne ake haliitar mutum har ma suna kiransa da faifan farko. Kuma tanan ne za a sake tada mutum ranar ta shin Kiyama kamar yadda Ma'aiki mai tsira da aminci ya bayyana a cikin wannan hadisin.