Kariyan mumini

Kariyan mumini

Kariyan mumini

حصن المؤمن بلغة الهوسا

 

 

 

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha

د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة

 

 

Fassara

European Islamic Research Center (EIRC)

المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية

& Hashim Muhammad Sani

Wanda ya bibiyi fassara

Muhammad Khamis

 

www.islamland.com

 

 

 

Kariyan mumini

da sunan allah mai rahama mai jin kai

Gabtarawa

Lallai godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman gafarar sa da shiriyan sa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunan mu da munanan ayyukan mu, duk wanda allah ya shirya babu me batar dashi wanda kuma ya batar dashi babu me shiryar dashi, na shaida babu abun bautawa da gaskiya bisa cancanta sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, kuma na shaida cewa lallai Muhammad bawan sa ne kuma manzon sa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalan sa da sahabban sa da aminci me yawa har zuwa ranan sakamako, bayan haka:

Lallai daga cikin falalar Allah akan mu a matsayin musulmai shine ya sanya mana daga cikin ayyuka mu da ibadu wanda zasu kasance tsani da kuma alaka dashi me girma da daukaka cikin dukkanain yanayi da lokuta, ya kuma sanya zikiri – Ambato – daga cikin su da addu'a wanda yake cikin mafifita ayyukan ibadu da kuma ayyukan kusanta masu girma kuma suna cikin mafifita ayyukan kwarai masu sauki wanda suke kusantar da musulmi zuwa ga ubangijin sa da kuma daukaka Ambaton sa.

Hakika yazo cikin falalar zikiri da addu'a da kuma kwadaitarwa akan shi ayoyi masu yawa, da hadisai ingantattu daga manzon Allah s.a.w, daga cikin su akwai:

Fadin Allah madaukaki: " kuma kuyi masa tasbihi - tsarkake shi- safiya da maraice"[1].

Allah madaukaki yakara cewa: " ku ambace ni zan ambace ku kuma ku godemun kada ku kafruce mun"[2].

Allah madaukaki yakara cewa: " yaku wanda sukayi imani ku ambaci Allah Ambato me yawa".

Allah madaukaki yakara cewa: " da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambaton Allah dayawa mata; Allah ya tanadar masu wata irin gafara da lada me girma"[3].

Allah madaukaki yakara cewa: " kuma ka ambaci ubangijin ka dayawa kuma kayi tasbihi da maraice da safiya"[4].

Allah madaukaki yakara cewa: " wanda suke ambaton Allah a tsaye da zaune da kuma kishingide akan barin jikin su kuma suna tunani cikin halittan sammai da kasa; ubangijin mu baka halicce wannan ba domin barna; tsarki ya tabbata a gareka ka tsiratar damu daga azabar wuta".[5]

Allah madaukaki yakara cewa: " idan kuka gama aikin hajjin ku to ku ambaci Allah kamar yadda kuke ambaton iyayen ku ko kuma sama da haka"[6].

Allah madaukaki yakara cewa: " yaku wanda sukayi imani kada dukiyoyin ku da yayan ku su shagaltar daku daga ambaton Allah; duk kuma wanda ya aikata haka to hakika wannan sune hasararru"[7].

Allah madaukaki yakara cewa: " Kuma ka ambaci Ubgijinka, a cikin ranka da kankan dakai, da tsoro, kuma koma bayan bayyanawa na magana, dasafe da maraice, kuma kada ka kasance daga gafalallu"[8].

Kuma hakika manzon Allah s.a.w yace: " misalin wanda yake ambaton ubangijin sa da wanda baya ambaton sa kamar misalin me raine da matacce"[9].

Manzon Allah s.a.w ya kara cewa: " duk wanda ya zauna a wurin zama be ambaci Allah ba acikin sa; yana da hasara da nadama agun Allah – wanda za'a tambaye shi akan sa ranan alkiyama -, wanda kuma ya kwanta be ambaci Allah ba a cikin sa; ya kasance yana hasara da nadama agun Allah. Wani bazayyi tafiya be amabci Allah ba a cikin s face ya kasance masa hasara da nadama agun Allah"[10].

Manzon Allah s.a.w ya kara cewa: " mutane bazasu zauna ba a wani majalisi wanda basu ambaci Allah acikin sa kuma basuyi salati bag a manzon su face ya kasance harasa da nadama a gare su agun Allah; idan yaso ya yafe masu idan kuma yaso ya azabtar dasu"[11].

Zikiri da addu'a sune kariyar mumini:

Kasancewar duniya gida ce ta bakinciki da wahala ba gida bace ta dawwama, kamar yadda Allah madaukaki da buwaya ya bada labari da cewa: " hakika mun halicci dan adam cikin wahala"[12].

Kasancewar mutum a cikinta halitta ne me rauni da gazawa akan amfanintan kansa ko kuma wanin sa ko kuma tunkude cutarwa akansa ko wanin say a kasance yana da bukatu wanda basa yanke wa kuma basa karewa har sai idan ijalinsa yakare, ya kasance babu makawa a gareshi na saman madogari wanda zai dogara a mika masa bukatun sa, sai aka shar'anta masa zikiri wanda kariya ne wanda yake kare mumini ransa da iyalan sa da dukiyan sa idan ya kiyaye su ya kuma dawwama akan haka, kamar yadda aka shar'anta masa addu'a wanda silace tsakanin sa da ubangijin sa kuma ta hanyar sa ne bawa ke mika bukatun sa zuwa ga mahaliccin sa domin neman agajin sa warin tabbatar da bukatun sa da burin sa, kuma hakika uabngijin mu ya bayyana mana cikin wurare dayawa cikin alkur'ani falalar addu'a, sai Allah madaukaki yace: " kuma ubangijin mu yace ku roke ni zan amsa maku; lallai masu yin girman kai game da roko na zasu shiga jahannama suna kaskantattu (60)"[13].

Ya kuma kara fadi har wayau cewa: " kuma idan bayina suka tambaye ka game dani to kace kasu ina kusa – dasu-; ina amsa rokon wanda ya roke ni; to su amsa kirana kuma suyi imani dani koda zasu shiryu (186)"[14].

A cikin wannan dan karamin littafi zamuyi magana a takaice akan ibtila'i – bala'i da nau'ukan sa da dalilan fadawa cikin musifu da sharruka da hanyoyin kare hakan gabanin faruwan su, da hanyoyin magance ta bayan faruwan ta ko kuma rage radadinta, ina me rokon Allah madaukaki shiriya da dacewa.

 

 

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha

../../../../../../../Documents/MY%20SITES%20&%20PROJECTS/PROJECTS%20&%20SITES/ISLAML

www.islamland.com

[email protected]

 

 

Ibtila'i a mahangar shari'a

Abunda yake zuwa kwakwalwa shine ibtila'i baya kasancewa sai cikin sharri ta hanyar faruwan abubuwan da ba'aso kamar musifu na rashin lafiya da annoba da makamantan su gaskiya itace kamar yadda yake kasancewa cikin sharri haka ibtila'i yake kasancewa cikin alheri shima kamar yadda ubangijin mu madaukaki ya bada labari yana cewa: " ko wace rai sai ta dandani mutuwa' kuma muna jarabtan ku da fitina na sharri da alheri; kuma agaremu zaku dawo (35)"[15].

Ibtila'i kala biyu ne:

  1. Ibtila'i na hakuri wanda shine ibtila'i na sharri:

Shine wanda Allah yake jaraban bawan sa dashi ya gani shin zayyi hakuri ko kuma a'a, Allah madaukaki yana cewa: " kuma lallai zamu jarabeku da wani abu cikin tsoro da yunwa da tawayan arziki da rayuwaka da yayan itace; kayima masu hakuri bishara (155) wanda idan wata musiba ta shafe su sai suce lallai mu ga Allah muke kuma lallai garishe zamu koma (156) wannan sune ambaton Allah yake kansu da rahama; kuma wannan sune shiryayyu (157)"[16].

  1. Ibtila'i na godiya wanda shine ibtila'i na alheri:

Shine wanda Allah yake jaraban bawansa dashi ya gani zai gode masa ko kuma a'a, Allah madaukaki yana fadi yana me bada labari akan Annabi Sulaiman amincin Allah ya tabbata a gareshi: " sai wanda ilimin littafai ke wurin shi yace ni zanzo maka dashi gabanin kyaftawar idonka; a lokacin daya ganshi tabbace a wurin sa sai yace wannan daga cikin falalar ubangijina ne domin ya jarabani ya gani shin zan gode masa ko kuma zan kafurce ne; duk wanda ya gode to hakika yana godema kansa ne; wanda kuma ya kafurta lallai ubangiji na wadatacce ne me karamci (40)"[17].

Me karatu ya sani cewa akwai ibtila'i da alheri wanda shine Allah ya yalwata ma bawan sa da ni'ima na kudi o lafiya ko yara hakan fa ba dalili bane akan son Allah da yardan sa, Allah madaukaki yana cewa yana me bada labari akan Karuna: " " lallai karuna ya kasance cikin mutanen Musa sai ya fita daga cikin su, kuma mun bashi taska na dukiya wanda makullansu suna gajiyar da masu karfi gun daukan su, a lokacin da mutanen sa sukace masa kada kayi farin ciki, lallai Allah bayason masu farin ciki (76) kuma ka nema gidan lahira cikin abunda Allah ya baka, kuma daka ka manta da rabonka na duniya, kuma ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata maka, lallai Allah baya son masu barna (77) yace: lallai anbani shi ne abisa wani ilimi dake wuri na, shin be sani bane cewa lallai Lallai Allah ya halaka cikin al'ummomi wanda suka fishi karfi da tarin dukiya?, kuma ba'a tambaya tambaya game da zunuban su mujirimai (78) sai ya fita ga al'umman sa cikin kawa, sai wanda suke son rayuwar duniya sukace: kaima dai dama ace muna da irin wannan abunda akaba karuna, lallai shi me rabo ne babba (79) sai wanda akaba ilimi sukace tir dinku, ladar Allah tafi alheri ga wanda yayi imani ya kuma aikata aiki na kwarai kuma babu wanda yake samun sa face masu hakuri (80) sai muka kifar da kasa dashi da dukkanin abunda ya mallaka, kuma bashi da wasu mutane wanda zasu taimake shi koma bayan Allah kuma me kasance cikin masu yin taimako ba (81) sai wanda suke fatan kasancewa a matsayin shi suka wayi gari suna cewa wai kamar Allah yana shinfida arziki ga wanda yaso cikin bayin say a kuma hana ga wanda yaso, badan Allah ya mana ni'ima ba da ya kisfe (kasa) damu, wai kamar kamar shi baya rabautar da kafirai (82) wancan gidan lahira ce wacce muka sanyata ga wanda basason daukaka a duniya ko kuma barna, kuma karshe (me kyau) na masu takawa ne (83)"[18].

Duniya Allah yana bayar da ita ga wanda yakeso da kuma wanda bayaso, sabanin lahira wacce baya bayar da ita sai ga wanda yakeso kawai, an karbo daga Sahal dan Sa'ad Allah ya kara masa yarda yace: " mun kasance tare da manzon Allah s.a.w a zul-khulaifa sai ga wata akuya matacciya kafanta a dage, sai yace: shin kuna ganin wannan bata da wani kima agun me ita?! Na ranste da wanda raina ke hannun sa, duniya tafi zama wulakantacciya agun Allah sama da wannan akuya agun me ita, da ace duniya takai darajar fiffiken sauro da kafiri be sha ruwanta ba koda dugo daya ne har Abadan"[19].

Kuma ibtila'i da sharri bawai dalili bane akan kin LAlah da fushin sa ga bawa na abunda yake kaddara masa na nakasan dukiya da rayuka da yayan itace, ubangijin mu madaukaki yana cewa yana me bada labari akan annabi Ayyuba amincin Allah ya tabbata a gareshi: " da Ayyuba a lokacin daya kira ubangijin sa cewa cuta ta shafe ni kuma kaine mafi rahaman masu rahama (83) sai muka amsa amsa muka yaye masa cutan sa; kuma muka bashi iyakan sa da makamancin su tare dasu rahama daga garemu da kuma ambato ga masu bauta (84) da Isma'il da Idrisa da Zil-kiflu; dukkanin su suna cikin masu hakuri (85) kuma muka shigar dashu cikin rahamar mu; lallai sun kasance cikin salihai (86)"[20].

An karbo daga Sa'ad dan Malik daga babanshi yace: " nace ya manzon Allah: wanene yafi mutane tsananin bala'i? sai yace: Annabawa sai wanda kuke biye dasu cikin bayi salihai, ana jarabtan bawa ne gwargwadon addinin sa, idan yana da addini nada kwari sai bala'in sa yayi tsanani idan kuma addinin sa akwai sakwa sakwa a garabeshi gwargwadon addinin sa, bawa bazai rabu da bala'i ba har sai ya koma yana yawo a doron kasa bashi da zunubi ko daya"[21].

An karbo daga Abdu Allahi dan Mugaffal yace: " wani mutum ya hadu da wata mata wacce ta kasance karuwa ce a zamanin jahiliyya sai ya fara wasa da ita har yakai hannun sa zuwa gareta sai tace: ka daina domin kuwa Allah yayi maganin shirka da musulunci. Sai ya barta ya tafi sai ya rika juyawa yana kallonta har ya hadu da bango sa'annan yazo gun manzon Allah s.a.w jini na zuba a fuskar sa sai yabashi labarin abunda ya faru, sai manzon Allah s.a.w yace: lallai kai bawa ne wanda Allah ke son ka da alheri. Sa'annan yace: lallai Allah madaukaki idan yanason bawa da alheri yana gaggauta masa ukubar zunubin sa daya aikata idan kuma yanason bawan sa da sharri sai ya rike zunubin sa har zuwa ranan alkiyama ya sakanya masa akan haka kamar me bashi ne"[22].

Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " bala'i bazai gushe ba tare da mumini na miji ko mumina mace cikin jikin sa da dukiyan sa da yaran sa har sai ya hadu da Allah bashi da zunubi ko daya"[23].

me yafi karamci sama da haka, ubangiji wanda ya sanya daga cikin wannan jarabawa da bala'i lada wanda zai daga darajara da kuma girmama lada shi da kuma yafe zunubai sa da laifuka ga wanda yayi hakuri da neman lad aba wanda ya kasa hakuri ba akan abunda ya shafe shi, Ibn Kayyim Allah yayi mashi rahama yana cewa: " idan wani abun ya sami bawa cikin abunda aka kaddara masa wanda yake kyaman sa yana da abubuwa lura guda shida acikin sa:

na farko: lura na tauhidi, cewa lallai Allah shine wanda ya kaddara masa ya kuma so ya kuma halicce sa, abunda yaso kuma shi yake kasancewa abunda beso ba kuma baya kasancewa.

Na biyu: lura na adalci, shine me zartar da hukuncin sa akan bawa, lallai abunda Allah ya hukuntama bawa adalci ne babu zalumci a cikin sa.

Na uku: luna na rahama, cewa lallai rahamar Allah cikin wannan abu da aka kaddara masa ya rinjaye fushin sa da kamun sa.

Na hudu: lura na hikima, lallai hikimar sa madaukaki ta kunshi haka be kaddara hakan bah aka kawai kuma be hukunta hakan ba batare da wani hadafi ba.

Na biyar: lura na godiya, cewa lallai shi madaukaki gareshi godiya cikakka take akan haka na dukkanin fuskan godiya.

Na shida: lura na bauta, cewa lallai shi bawa ne ta dukkanin bangarori wanda hukunce hukunce na ubangida yake gudana akansa da abunda ya zartar domin kasancewar sa ubangidan sai ya jujjuya shi karkashin abunda yake so ya hukunce hukuncen sa na kaddara kamar yadda yake jujjaya shi karkashin hukunce hukunce na duniya lallai shi wuri ne na gudanar da wannan hukunce hukuncen akan sa."[24]

Dalilai na musifu da ibtila'i wanda suke samun asali daga fushin Allah:

  1. Aikata zunubi da sabo:

Allah madaukaki yana cewa: " kuma abunda ya same ku na musifa to sakamo ne na abunda kuka aikata da hannuwan ku kuma yana yafewa –laifuka- dawaya (30)"[25].

An karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace: manzon Allah s.a.w yace: " zai kasance a karshen wannan al'umma girgizan kasa da canza halitta da rikitowan duwatsu akan mutane" sai tace: sai nace ya manzon Allah: shin za'a halaka mu alhali a cikin mu akwai salihai? Sai yace: eh idan fasikanci da sabo ya bayyana, da kuma yawaitan masu barna akan mutanen kwarai".[26]

An karbo daga Abu Musa Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah yana yima azzulmi jinkira, har idan ya kama shi bazai kubuta ba. sai yace: sa'annan ya karanta fadin Allah: {kuma Kaman haka ne kamun ubangijin ka yake idan ya kama gari azzaluma; lallai kamun sa me radadi da tsanani ne}[27]."[28]

Wannan zunuban da sabo wanda bawa yake aikatawa dalili ne cikin dalilan da zai zama ya bata zuciya da "datti" sai ya sanya ta yin nisa da ubangijinta madaukaki bazata rika jin wa'azi ba kuma zikiri bazai mata tasiri ba, Allah madaukaki yana cewa: " A’aha! Hakika, lallai ne su, daga Ubangijinsu, a ranar nan, wadanda ake shamakacewa ne (14)"[29].

Kuma hakika manzon Allah s.a.w yace: " lallai bawa idan ya aikata zunubi, zai yi masa bakin dugu daya a zuciyan sa, idan ya nemi gafara ya tuba sai ya wanke zuciyan sa, idan ya koma ya kara yin wani zububin kuma sai aka wani dugun akan zuciyar har sai ya mamaye zuciyar sakamakon yawan zunubin sa, itace lullubi wacce take rufe zuciya wanda Allah ya fadi cewa: {A’aha! Hakika, lallai ne su, daga Ubangijinsu, a ranar nan, wadanda ake shamakacewa ne}."[30]

Kuma me yafi kyawu ga fadin mawaki:

            Naga zunubi yana kashe zuciya kuma dawwamar ta yana gadar da kaskanci

            Barin zunubi rayuwa ne ga zuciya kuma yafi zama alheri agareka da yin sabo

  1. Son duniya da sha'awowi da kuma manta lahira:

Manzon Allah s.a.w yana cewa: " duk wanda lahira ta kasance burin sa a rayuwan duniya Allah zai sanya masa wadata cikin zuciyar sa zai kuma hada mashi al'amauran cikin ta da sawwake masa al'amuran, kuma duniya zata zo masa tana kaskantacciya, wanda kuma burin say a kasance rayuwan duniya Allah zai sanya masa talauci a gaban idon say a kuma daidaita masa al'amuran duniya, duniya bazata zo masa ba sai kwatankwacin abinda aka kaddara masa."[31]

  1. Cin dukiyoyin mutane da barna:

Allah madaukaki yana cewa: " kuma kada kuci dukiyoyin ku a tsakanin ku da barna"[32].

Daga cikin abunda yafi tsanani cikin cin dukiyan mutane da barana shine Riba da taimako wurin yada shi, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani kuji tsoron Allah kuma kubar abunda ya ragu daga riba idan kun kasance muminai (278) idan kuma baku aikata ba to kuyi shelan yaki daga Allah da manzon sa; idan kuma kun tuba to kunada jarin asalin kudin ku kada kuyi cuta kuma kada a cutar daku (279)"[33].

Yana debe albarka, manzon Allah s.a.w yana cewa: " babu wanda zai tara dukiya ta rifa face karshenta ya kasance ta ragu"[34].

Ma'abocin sa kuma an nisantar dashi daga rahamar Allah idan be tuba ba daga yi mu'amala da riba, an karbo daga Jabor Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya tsine ma me cin riba, da me bayar da ita da me rubuta ta da me shedarta, yace: daidai suke cikin zunubi"[35].

  1. Bayya sabo da son yada ta da kuma kawatata ga mutane:

Allah madaukaki yace: " lallai wanda suke son yada alfasha cikin wanda sukayi imani suna da azaba me radadi a duniya da lahira; Allah ya sani amma ku baku sani ba (19)"[36].

Manzon Allah s.a.w yana cewa: " dukkanin al'umma ta ana yafe mata zunuban su sai wanda yake bayyana fasikancin sa, kuma lallai daga cikin masu bayyana sabo zai wayi gari Allah ya rufa masa asiri, sai ya kai wane: na aikata kaza jiya da daddare, bayan ya kwana cikin rufin asirin ubangijin sa, sai ya wayi gari yana tuna asirin da Allah ya rufa amsa"[37].

An karbo daga Abdu Allahi dan umar Allah ya kara masu yarda yace manzon Allah s.a.w yace: " yaku taron masu hijira! Abubuwa guda iyar idan aka jarabe ku dasu, ina neman tsarin Allah kada ya riske su: alfasha (zina) bazai bayyana ba cikin al'umma har su rika shelarta face annoba ya da cuta wanda ba'a taba samun mutanen da suka gabace su ba, kuma ba'a toye awo ba face fari a tsananin talauci da mugun shugaba ya same su, kuma bazasu hana zakkar dukiyar su ba face an hana masu ruwan sama, badan dabbobin su ba da ruwan sama be saukan masu ba, kuma bazasu warware alkawarin Allah ba da alkawarin manzon sa face Allah ya daura masu makiya daga waje, sai su kwace wasu abunda ke hannun su, kuma shuwagabannin su bazasu bar yin hukunci ba da littafin Allah madaukaki ba kuma su rika neman alheri cikin abunda Allah ya saukar ba face Allah ya sanya ki azaba da kiyayya a tsakanin su."[38]

  1. Barin yin umurni da kyakyawan aiki da hani da mummunan aiki:

Shine rigakafin aminci wanda ta hanyar sa ne al'umma zasu samu tsaro da kariya, manzon Allah s.a.w yana cewa: " misalin wanda ya doge akan iyakokin Allah, me yin umurni da kyakyawan aiki da hani daga mummunan aiki da wanda yake fadawa cikinta -watan wanda baya aikata hakan- kamar misalin mutane ne wanda suka shiga cikin jirgin ruwa me hawa hawa sai wasunsu suka ciki hawan sama wasun su kuma suka cinki hawan kasa, sai wanda suek kasa idan suna son debo ruwa sai sunbi ta yan saman su, sai suke: da ace zamu fasa cikinb rabon nan namu rami dan karami wanda basai mu haura saman bam un cutar dasu ba, idan suka kyale su suka aikata abunda suke su zasu halaka baki dayan su amma idan suka hanasu kuma zasu tsira baki dayan su"[39].

An karbo daga Abubakar Assiddiq Allah ya kara masa yarda yace: " yaku mutane,lallai kuna karanta wannan ayar, kuna sanyata a inda ba wurinta ba – watan kuna fahimtar ta ba daidai ba- {yaku wanda sukayi imani kuji da kanku, kada ya bace ya cutar daku idan kun shiryu}[40] lallai naji manzon Allah s.a.w yan acewa: lallai mutane idan sunga zalumci basu hana ba gab azabar Allah yake daya same su, kuma lallai naji manzon Allah s.a.w yana cewa: babu wasu mutane wanda ake aiki da sabo a cikin kuma suna da ikon hanawa amma basu hana ba face azabar Allah ya kusa daya mamaye su saboda haka."[41]

  1. Son masu sabo da azzalumai da kuma yi masu biyayya da aiki domin taimakon su na tabbatar masu da shugabanci da iko:

An karbo daga Abdu Allahi dan Mas'ud Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " lallai farkon shigan tawaya cikin bani isra'ila cikin addinin su shine ya kasance mutum zai hada da mutum sai yace: ya kai wane kaji tsoron Allah kuma kabar abunda kake aikatawa na wannan mummunan aiki, domin be halatta ba a gare ka. Sai kuma ya hadu dashi gobe amma hakan bazai hana shi zama abokin cin abincin sa ba da shan ruwan sa da abokin zaman sa, a lokacin da suka aikata haka sai Allah ya rabbata zukatan su ya jefa masu kiyayya a tsakani su. Sa'annan yace: {an tsine ma wanda suka kafurta cikin bani isra'ila a bisa harshen Dawuda da Isa dan Mryam; hakan ya faru ne saboda abunda suka saba kuma sun kasance masu wuce gona da iri (78) sun kasance basa hani ga mummunan aikin da aka aikata; tur da abunda suka kasance suna aikatawa (79) zakaga dayawan su suna son wanda suka kafurta; hakika tur da abunda suka aikata wanda fushin Allah ya fada akan su kuma cikin azaba zasu dawwama (80) ka ace sun kasance sunayin imani da Allah da manzon sa da abunda aka saukar gareshi da basu rike su majibinta al'amura ba sai dai dayawa daga cikin su fasikai ne (81)}. sa'annan yace: tabbas wallahi ku rika yin umurni da kyakyawan aiki da yin hani daga mummunan aiki da kuma hana azzulumi zalumci da kuma wajabta masa yin gaskiya da sanya shi takaita akan gaskiya kada ya ketare ta."[42]

  1. Isgilanci ga muminai da kiyayya dasu:

Allah madaukaki yana cewa: " lallai Allah yana kariya ga wanda sukayi imani; lallai Allah bayason me ha'inci da kafurcewa (38)"[43]

Manzon Allah s.a.w yana cewa: " lallai Allah madaukaki yace: duk wanda yayi adawa da waliyyina to hakika yayi shelar yaki dashi…"[44].

Mu sani cewa isgilanci ga muminai yakan kai ga isgilanci da addini wanda hakan yake fitar da mutum daga musulunci – Allah yayi mana tsari da hakan – Allah madaukaki yace: " kuma idan ka tambaye su zasu ce maka mun kasance muna wasa da raha; kace – masu – da Allah da manzon sa da ayoyin sa ne kuke isgilanci (65) kada ku bada wani hanzari hakika kun kafurta bayan imanin ku; idan mun yafema wasu mutanen a cikin ku tofa zamu azabtar da wasu saboda sun kasance mujirimai (66)"[45].

  1. Bayyana farin ciki ga musifar da ta samu mutane da wulakanta su da kuma isgilanci dasu:

Allah madaukaki yace: " wanda suka aibanta masu yin sadaka cikin muminai da wanda basu samu komai ba face gumin zu sais u rika masu isgilanci; Allah yanayin isgili gare su. Kuma suna da azaba mai radadi (79)"[46].

  1. Yin makirci ga bayin Allah ta hanyar yi masu wayo da dabara:

Wannan shine makirci mummuna, Allah madaukaki yace: " kuma makirci mummuna baya fadawa face akan masu shi"[47].

  1. Murema ni'imar Allah ta bayyane da ta boye da kuma rashin gode masa akan haka ko kuma jingina shi ga wanin Allah:

Allah madaukaki yace yana bada labari akan Karuna: " lallai karuna ya kasance cikin mutanen Musa sai ya fita daga cikin su, kuma mun bashi taska na dukiya wanda makullansu suna gajiyar da masu karfi gun daukan su, a lokacin da mutanen sa sukace masa kada kayi farin ciki, lallai Allah bayason masu farin ciki (76) kuma ka nema gidan lahira cikin abunda Allah ya baka, kuma daka ka manta da rabonka na duniya, kuma ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata maka, lallai Allah baya son masu barna (77) yace: lallai anbani shi ne abisa wani ilimi dake wuri na, shin be sani bane cewa lallai Lallai Allah ya halaka cikin al'ummomi wanda suka fishi karfi da tarin dukiya?, kuma ba'a tambaya tambaya game da zunuban su mujirimai (78) sai ya fita ga al'umman sa cikin kawa, sai wanda suke son rayuwar duniya sukace: kaima dai dama ace muna da irin wannan abunda akaba karuna, lallai shi me rabo ne babba (79) sai wanda akaba ilimi sukace tir dinku, ladar Allah tafi alheri ga wanda yayi imani ya kuma aikata aiki na kwarai kuma babu wanda yake samun sa face masu hakuri (80) sai muka kifar da kasa dashi da dukkanin abunda ya mallaka, kuma bashi da wasu mutane wanda zasu taimake shi koma bayan Allah kuma me kasance cikin masu yin taimako ba (81) "[48].

Kuma Allah madaukaki yana cewa: cikin suratul rahman: " To saboda wane daga ni’imomin Ubangjinku kuke karyatawa (13)"[49].

Watan da wani irin ni'imar Allah ne na duniya da lahira kuke karya tawa? Kuma me yafi kyawun da dacewa a gun bada amsa irin wanda manzon Allah s.a.w ya amsa da ita a lokacin da aka karanta mashi surar a duk inda fadin Allah haka yazo: " To saboda wane daga ni’imomin Ubangjinku kuke karyatawa " Sai sukace babu wata ni'ima cikin ni'imomin ubangijin mu da muke karyatawa, godiya ta tabbata ga Allah.[50]

 

 

 

Hanyoyin kiyaye ni'imar Allah

Ka sani ya kai dan uwa me daraja cewa fa wanda ya karrama ka da wannan ni'imar yana da ikon kwace su daga gareka, bakafi sauran bayin sa falala ba ko kuma daukaka ba a gunsa sai da tsoron sa da kuma ayyuka na kwarai, Allah madaukaki yace: " yaku mutane lallai mun halicce ku daga namiji da mace kuma muka sanya ku kuka zama al'umma da kabilu domin kuyi sanayya; lallai wanda yafi wani falala a cikinku agun Allah shine wanda yafi tsoron sa; lallai Allah masani ne kuma me bada labari (13)"[51].

Kuma hakika Allah madaukaki ya bayyana cewa godiya da yabo a gareshi akan ni'ima cikin ni'imomin sa hanya ne wanda yakekaiwa ga kiyaye ni'ima da kuma rashin gushewar tasai yace: " a lokacin da ubangijin ku yayi yakuwa cewa idan kun godemun to tabbas zan kara maku; kuma idan kun kafurce mun to lallai azabata me tsanani ce (7)"[52].

Manzon Allah s.a.w yana cewa: " Allah beyima bawa wata ni'ima sai yace godiya ta tabbata ga Allah face wanda zai kasance ya bashi yafi falala akan abunda ya bashi"[53].

  1. Daga cikin godema Allah akan ni'ima cikin al'amuran dukiya shine bayar da abunda Allah ya wajabta acikinta na hakkoki wacce take dole ga talakawa da miskinai da mabukata, Allah madaukaki yace: " kuma acikin dukiyar su akwai hakki ga me tambaya da wanda baya iya tambaya (19)"[54]

Ya kuma sani cewa acikin dukiya akwai hakki wand aba zakka ba, ya, ya ciyar da masu junwa ya tufatar da masu bukatar sutura yayi magani ga marasa lafiya yay aye masu damuwar su ya kuma biya masu basukan su, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " mafi soyuwan mutane agun Allah shine wanda yafi amfanar dasu, kuma mafi soyuwan aiki agun Allah madaukaki shine sanya gfarin ciki ga musulmi, ko kuma yaye masa damuwar sa, ko kuma biya masa bashin sa, ko kuma ka kore masa yunwa, kuma nayi tafiya domin yin hidima ga wata bukata ta dan uwana musulmi yafi soyuwa a gareni sama da nayi ittikafi cikin wannan masallacin nawa na wata daya, duk wanda ya kame fushin sa, Allah zai suturta masa al'aurar sa, wanda ya hadiye fushin sa wanda yake da ikon daukan fansa, Allah zai cika masa zuciya da yarda ranan alkiyama, duk wanda ya fita domin yin hidima ga bukatar dan uwan sa musulmi domin ya tabbatar da ita, Allah zai tabbatar da digadigan sa ranar alkiyama, kuma lallai mummunan dabi'u yana bata aiki kamar yadda ruwan kal ke bata zuma".[55]

Kuma Allah madaukaki ya bayyana ladar da yake tare da share bukatu na talakawa da miskinai da bima biya masu ita domin neman yardan sa, sai yace: " Kuma suna ciyarwa da abinci, a kan suna bukatar sa ga matalauci da maraya da fursinan yaki (8) suna cewa muna ciyar daku ne domin neman yardan Allah kawai, bamu nufin samun wani sakamako daga gareku, kuma bamu nufin godiya (9) lallai ne mu, muna tsoro daga Ubangijin mu wani yini mai gintsewa, mai murtukewa (10) saboda haka Allah ya tsare masu sharrin wannan yini, kuma ya hada su da annurin fuska da farin ciki (11) kuma ya saka musu saboda hakurin da sukayi da aljanna da tufafin alhariri (12)"[56].

  1. Daga cikin godiya ga Allah madaukaki akan ni'imar halitta me kyau madaidaiciya da ni'imar lafiya da gabban jiki, shine kada mutum yayi amfani da wannan lafiya sai cikin da'a ga Allah, ya kiyaye idon sa daga kallon haram, ya kiyaye jinsa daga sauraran haram, ya kiyaye harshen sa daga yin gulma da annamimanci da karya da alfasha na magana, kada yayi tafiya da kafafun sa zuwa wurin da Allah ya haramta kuma kada ya takaita su wurin aikin alheri, kada yayi aiki da hannayen sa cikin sabon Allah kuma kada ya tadaita su cikin aikin alheri, Allah madaukaki yace: " lallai ji da gani da zuciya dukkanin su ababen tambaya akan su (36)"[57].

Kada ya taimaki azzalumi akan zalumcin sa ko kuma sabon sa, ya wajaba ya zama kamar yadda manzon Allah s.a.w yace: " ka taimaki dan uwanka azzalumi ko kuma wanda aka zalumta. Sai wani mutum yace: ya manzon Allah, zan taimake shi idan shi aka zalumta to yaya kake gani idan shine yayi zalumcin yay azan taimake shi? Sai yace: ka hanashi yin wannan zalumci ka taimake shi."[58]

Kuma kada yayi amfani da abunda Allah yayi masa ni'ima dashi na hikima, da baiwa da kwakwalwa cikin taimakon barna ko kuma yaki da gaskiya, ya wajaba a gareshi yin amfani da wannan iko nashi cikin abunda zai jawo ma al'umma amfani duniya da lahira, manzon Allah s.a.w yana cewa: " kafafuwan bawa bazasu gushe ba ranan alkiyama face an tambaye shi akan shekarun sa yaya yayi amfani dasu, da ilimin sa me ya aikata dashi, da dukiyar sa a ina ya samo kuma a ina ya kashe, da jikinsa aina yayi amfani da karfin shi da lafiyar sa."[59]

Kuma ya kiyaye farjin sa da kareshi daga abunda da Allah ya haramta kada ya biya bukatar sa na sha'awa sai ta hanyar da Allah ya halasta mashi na matar sa, Allah madaukaki yace: " wa'inda basa kiran tare da Allah wani abun bauta na daban kuma basa kashe rai wanda Allah ya haramta face da gaskiya kuma basa zina; duk wanda ya aikata haka zai hadu da wani rami cikin jahannama (68)"[60]

Ya kuma yin yabo ga wanda yayi masa ni'ima Allah madaukaki na abunda yayi masa na ni'ima kada ya jingina shi ga wanin LAlah, domin sakamakon jingina shi ga wanin Allah boni ce da halaka da asara a duniya da lahira, Allah madaukaki yana cewa: " sai ya shiga gonar sa yana me zalumtar kansa sai yace bana tsammanin wannan gona zata lallace har Abadan (35) kuma bana tsammanin za'ayi tashin alkiyama kuma idan na koma zuwaga ubangijina tabbas zan tarar da makoma wacce tafita alheri (36) sai abokin sa yace masa yana me masa wa'azi yanzu shin zaka kafurta da wanda ya halicce ka daga tabo sa'annan daga gudan maniyyi sa'annan ya daidaitaka ka zama mutum (37) [nikam bazan fadi irin maganarka ba ina me tabbatar da kadaitar sa] dacewa shine ubangiji na kuma bana tarayya da wani mutum tare da ubangijina (38) inama ace da kashiga gonar taka cewa kayi masha Allah babu wani iko sai ga Allah; dan kaga cewa bankai ka dukiya ba da yara (39) ina fatan ubangijina yana bani mafiyin gonar ka alheri ya kuma aiko ma gonar ka azaba daga sama sai ta wayi gari turbaya me mai santsi (40) ko kuma ruwanta ya wayi gari fakakke, saboda haka bazaka iya nemo shi ba dominta (41) kuma aka halaka dukkan yayan itacensa sai ya wayi gari yana juyar da tafukan sa biyu saboda abinda ya kashe a cikinta, alhali kuwa ita tana kwance akan rassanta kuma yana cewa kaitona, dadai ban tara wani da ubangijina ba! (42)"[61]

Godiyar bawa da yabon Allah akan ni'imar da yayi masa sakamakon sa yana koma ne zuwa ga bawa kansa, Allah madaukaki yace: " yace wannan daga cikin falalar ubangiji na ne domin ya jarabani ya gani shin zan gode ko kuma zan kafurce ne; duk wanda ya gode to lallai kansa yake gode mawa; wanda kuma ya kafurta lallai ubangiji na mawadaci ne me karamci (40)"[62]

  1. Daga cikin godiyar Allah akan ni'imar musulunci wacce itace mafificiyar ni'ima da daukaka, mutum ya biya hakkokin wannan ni'imar ta hanyar:
  1. Jin tsoron Allah da kuma jin yana tare da mutum da ganin sa cikin sirri da bayyane da farin ciki da damuwa, wannan martaba ce ta kyautatawa wacce manzon Allah s.a.w ya bamu labari akanta cikin fadin sa: " ka bautama Allah kamar kana ganin sa, idan baka ganin sa to shi yana ganin ka."[63]

Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda yana cewa: " na kasance bayan manzon Allah s.a.w akan abun hawa sai yace: yakai yaro bazan sanar dakai wasu kalmomi ba wanda Allah zai amfanar dakai dasu? Sai nace: sanar dani ya manzon Allah. Sai yace: ka kiyaye Allah zai kiyaye ka, ka kiyaye Allah zaka tarar dashi a gaba gareka, ka kusanci Allah da masa biyayya cikin yalwa zai kusance ka ciki tsanani, idan zaka roka to ka roki Allah, kuma idan zaka nemi agaji ka nemi agajin Allah, hakika bakin alkalami ya bushe da abunda zai faru, da ace halittu baki dayan su zasu so amfanar dakai da wani abu wanda Allah be rubuta maka shi ba to bazasu iyaba kuma da zasu so cutar dakai da wani abu wanda Allah be rubuta maka shi ba bazasu iyaba, ka sani lallai cikin hakuri akan abunda bakaso akwai alheri dayawa kuma lallai cin nasara yana tare da hakuri kuma damuwa yana tare da yayewa kuma tsanani yana tare da sauki."[64]

  1. Barin abubuwan da aka haramta da nisantar abubuwan da aka hana:

manzon Allah s.a.w yana cewa: " duk abunda ya haneku akai to ku nuisance shi. Kuma abunda ya umurce ku akai ku aikata shi gwargwadon iyawar ku. Lallai daga cikin abunda ya halakar da wanda suke gabanin ku shine yawan tambayan su da kuma sabawar su ga annabawan su."[65]

  1. dawwama akan aikata dukkanin ayyukan wajibai wanda Allah yayi umurni dasu da wajabta su:

manzon Allah s.a.w yana cewa cikin hadisul kudusi Allah madaukaki yana cewa: " … kuma bawa baya kusanta zuwa gareni da wani abu wanda yafi soyuwa a gareni sama da abunda na wajabta mashi…."[66]

Musamman sallah wacce itace ginshikin addini cikin jama'a a masallaci – sai idan akwai wani uziri wanda shari'a ya yarda dashi- domin itace firkin abunda za'a tambaya bawa akai ranar alkiyama idan tayi kyau to sauran ayyukan sa zasuyi kyau, manzon Allah s.a.w yana cewa: " lallai farkon abunda za'a fara yima bawa hisabi akai shine sallar sa, idan tayi kyau to hakika ya tsira ya rabauta, idan batayi kyau ba to hakika ta tabe da hasara"[67]

  1. yawaita ambaton Allah madaukaki:

an karbo daga Abdu Allahi dan Busri Allah ya kara masa yarda yace: " wani balarabe dan kauye yace ma manzon Allah s.a.w: lallai ayyukan shari'u na musulunci sun mun yaw aka fadamun abunda zan tabbata dashi. Sai yace: kada harshen ka ya gushe cikin ambaton Allah a koda yaushe."[68]

  1. Kiyaye nafiloli na ibada (watan ibadun da ba farillai ba):

Musamman ma sallolin nafila na bayan salloli farillai, wanda sune: " raka'a biyu fabanin sallar asuba, raka'a hudu gabanin sallar azahar da raka'a biyu bayan ta, da raka'a biyu bayan sallar magriba, da raka'a biyu bayan sallar isha'i", saboda tabbatar falala da lada me yawa akan kiyaye wannan sallah ta farilla wacce ake cema (Sunan al rawatib), an karbo daga ummu Habiba Allah ya kara mata yarda cewa manzon Allah s.a.w yace: " wanda ya kiyaye raka'o'i goma sha biyu na sunna Allah zai gina masa gida cikin aljanna: raka'a hudu gabanin sallar azahar da raka'a biyu bayanta, da raka'a biyu bayan magriba, da raka'a biyu bayan Isha'i, da raka'a biyu gabanin sallar asuba."[69]

  • Haka kuma sallah walaha, hakika yazo cikin falalar kiyaye ta fadin manzon Allah s.a.w: " ko wace gaba na jikin bawa yana wajaba yin sadaka da ita (watan yayi aiki da ita na lada domin godema ni'imar Allah na lafiyar da ya bashi). Ko wani tasbihi sadaka ne (cewa Subhana Allah- tsarki ya tabbata ga Allah-). Ko wani tahmidi sadaka ne (cewa Alhamdulillah- godiya ta tabbata ga Allah-). Kuma ko wani tahlili sadaka ne (cewa la'ilaha Illallah – babu abun bautawa da gaskiya sai Allah-). Kuma ko wani takbiri sadaka ne (cewa Allahu akbar – Allah me girma-). Umurni da kyakyawan aiki sadaka ne. hani ga mummunan aiki sadaka ne. ya wadatar dakai akan haka, yin raka'a biyu na walaha (watan yin raka'a biyu na walaha ta wadatar dakai daga yin dukkanin abunda aka amabata abaya)"[70].
  • Haka kuma sallar witiri, manzon Allah s.a.w ya kasance yana kiyaye ta kuma baya barinta hatta idan yana cikin tafiya wacce galiba tafiya akwai wahala a cikinta da gajiya kuma mafi karancin ta shine raka'a daya kacal, manzon Allah s.a.w yana cewa: " witiri gaskiya ce duk wanda yaso yayi wutiri da raka'a biyar wanda kuma yaso yayi witiri da raka'a uku wanda kuma yaso yayi witiri da raka'a daya."[71]
  • Azumin nafila kamar azumin ranakun tsakiyar ko wace wata wanda ya fara daga sha uku da sha hudu da sha biyar cikin watan musulunci, da kuma azumin ranan litinin da alhamis, da zamumin ranan arfa, da ranar Ashura da rana daga gabanin sa da rana daya bayan sa, manzon Allah s.a.w yana cewa: " babu wani bawa da zayyi azumi rana daya domin Allah, face Allah ya nisantar da fuskar sa daga wuta na tsawon tafiyan shekara saba'in da wannan rana."[72]

Kuma mafi falalafr azumi shine azumin annabi Dawud amincin Allah ya tabbata a gareshi, an karbo daga Abdu Allahi dan Umar yace: " labari yaje gun manzon Allah s.a.w ina cewa: na rantse da Allah kullum azumi zan rikayi kuma kullum sallar dare zan rikayi baki dayan sa har tsawon rayuwa ta. Sai nace masa hakika anyi haka nafadi hakan, sai yace: " hakika bazaka iya hakan ba, kayi azumi na wasu kwanaki sai ka huta na wasu kwanaki, kuma kayi salla na wasu awanni cikin dare kayi bacci na wasu a wanni acikin sa, kuma kayi azumin guda uku cikin ko wani wata domin kuwa ko wani aikin lada daya daidai yake da guda goma hakan kenan kamar kayi azumin shekara ne baki dayan sa" sai nace: zan iya sama da haka, sai yace: " to kayi azumi yau ka huta kwana biyu" sai nace: zan iya sama da haka. Sai yae: " to kayi azumi yau ka huta gobe wannan shine irin azumin annabi Dawud amncin Allah ya tabbata a gareshi kuma shine mafi falalar azumi" sai nace: zan iya sama da haka. Sai manzon Allah s.a.w yace: " babu falala sama da haka"."[73]

Lallai bawa mumini wanda yake neman soyayyar Allah ta hanyar kiyaye nafiloli da sunnoni zai samu hakan da yardan Allah, an karbo daga abi huraira Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah yace: duk wanda yayi kiyayya da waliyyi na to hakika nayi shelar yaki dashi, kuma bawa be taba kusanta a gare ba da abunda nakso sama da abunda ya wajabta masa, kuma bawa bazai gushe ba yana neman kusanci a gareni da nafiloli face naso shi, idan kuma naso shi: zan kasance masa jinsa da yake sauraro dashi, da ganin sa da yake kallo dashi, da hannun sa da yake taba abu dashi, da kafafuwan sa da yake tafiya dasu, kuma idan ya tambaye ni wallahi bashi abunda ya roka, kuma idan ya nemi tsarina tabbas zan tsare shi, ban taba yin kokwanto[74] ba akan wani abunda zan aikata sama da ran mumini wanda yake kin mutuwa kuma ni inakin munana masa."[75]

  1. Kokarin yada addinin Allah da kiran mutane zuwa gareshi:

Gwargwadon ikon mutum da iyawar sa na magana da aiki ko kuma bayar da dukiya domin Allah, sai ya shiryar da batacce ya karantar da jahili ya gyarama me kuskure kuskuren sa, manzon Allah s.a.w yana fadama Aliyu Allah ya kara masa yarda yana cewa: " in arantsuwa da Allah, Allah ya shiryar da wani mutum ta sanadiyyar ka yafi maka alheri sama abaka tarin jajayen rakuma."[76]

 

 

 

Azkar wanda aka shar'anta yi bayan sallah:

Kasani yakai dan uwa me daraja cewa ya wajaba dagewa da kwadayin yin azkar wanda aka shar'anta bayan sallah, wanda manzon Allah s.a.w ya bayyana hakan kamar haka:

  1. "Astagfiru Allah, Astagfiru Allah, Astagfiru Allah (ina neman gafarar Allah, ina neman gafarar Allah, ina neman gafara Allah), ya Allah kaine aminci kuma aminci daga gareka yake ka daukaka ya me girma da karamci, babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, mulki nashi ne kuma godiya nashi ne kuma shine me iko akan komai, babu iko da dabara sai ga Allah, babu abun bauta sai Allah, kuma bama bautan komai sai shi, ni'ima nashi ne kuma falala nashi ne kuma yabo kyawawa nashi ne, babu abun bautawa da gaskiya sai Allah muna masu tsarkake shi da bauta koda kafirai sunki, ya Allah babu wanda ya isa ya hana abunda ka bayar, kuma babu wanda ya isa ya bayar da abunda ka hana, kuma rabo da kokarin mutum bazai amfane shi ba agunka, ya Allah ka taimake ni akan ambaton ka da gode maka da kyautata bautar ka".
  2. sa'annan yace "subhana Allah" (tsarki ya tabbata ga Allah) sau talatin da uku, "walhamdu Lillah" (kuma godiya ta tabbata ga Allah) sau talatin da uku, da "Allahu Akbar" (Allah me girma) sau talatin da uku, sa'annan ya cika dari da cewa " babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, mulki nashi ne kuma godiya nashi ne kuma shine me iko akan komai",
  3. sa'annan ya karanta ayatul kursiyyu ayata 255 cikin suratul bakara,
  4. sa'annan ya karanta suratul ikhlas surata 112 da falaki da nasi surata 113 da 114, kuma anason ya maimata karanta suratul ikhlas da falaki da nasi sau uku bayan ko wace sallar asuba da magriba.

Saboda tabbatar haka daga manzon Allah s.a.w cikin hadisai ingantattu, an karbo daga Sauban Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya kasance, idan ya idar da sallar sa, yana fadin Astagfiru Allah sau uku. Sai yace" ya Allah kai ne aminci kuma aminci daga gareka yake, tsarki ya tabbatar maka ya ma'abocin girma da karamci"."[77]

Abdu Allah dan zubair Allah ya kara masa yarda ya kasance yana fadi bayan ko wace sallah bayan yayi salla: " babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, mulki nashi ne kuma godiya nashi ne kuma shine me iko akan komai, babu iko da dabara sai ga Allah, babu abun bauta sai Allah, kuma bama bautan komai sais hi, ni'ima nashi ne kuma falala nashi ne kuma yabo kyawawa nashi ne, babu abun bautawa da gaskiya sai Allah muna masu tsarkake shi da bauta koda kafirai sunki" sai yace: manzon Allah s.a.w ya kasance yana fadin su cikin daga sauti bayan ko wani salla."[78]

An karbo daga mugira dan shu'uba Allah ya kara masa yarda yace: " lallai manzon Allah s.a.w ya kasance yana cewa a bayan ko wace salla idan yayi sallama: babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, mulki nashi ne kuma godiya nashi ne kuma shine me iko akan komai, ya Allah babu wanda ya isa ya hana abunda ka bayar, kuma babu wanda ya isa ya bayar da abunda ka hana, kuma rabo da kokarin mutum bazai amfane shi ba agunka"."[79]

An karbo daga abu huraira Allah ya kara masa yarda manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda yace stsarki ya tabbata ga Allah (subhana Allah) bayan ko wace salla sau talatin da uku da kuma Alhamdulillah sau talatin da uku da Allah akbar sau talatin da uku, taca'in da tara kenan, sai ya cika ta darin da cewa: " la 'ilaha illa Allahu Wahadahu la sharika Lahu, Lahu al-mulku walahu al-hamdu wa Huwa ala kulli shai'in Kadir" za'a gafarta masa zunuban sa koda kuwa sun kai yawan kunfan teku ne."[80]

An karbo daga Abi Umamata Allah ya kara masa yarda yace, manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda ya karanta ayatul kursiyyu a bayan ko wace salla; to babu abunda zai hanashi shiga aljanna face kawai ya mutu."[81]

An karbo daga Ukubata dan Amir Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w yace mun: " ku karanta mu'awwizatani a bayan ko wace salla"."[82] (mu'awwizatani shine: suratul ikhlas, da falaki, da nasi)

An karbo daga Mu'azu dan Jabal Allah ya kara masa yarda, manzon Allah s.a.w ya kama hannu na wata rana sai yacemun: " ya Mu'azu lallai inason ka. Sai Mu'azu yace: fansar mahaifina da mahaifiyata a gareka wallahi nima inason ka. Sai yace: ya Mu'azu zan maka wasiyya da cewa kada kabar fadin cewa bayan ko wace salla: ya Allah ka taimake ni akan ambatonka da gode maka da kuma kyautata bautan ka"[83].

 

 

 

Hanyoyin magance musifu da bala'i, da hanyar saukake faruwan sa:

Daga cikin hanyoyi wanda sukafi nasara wurin magance bala'i da masifu:

  1. imani na gaskiya da kaddara da hukuncin Allah:

shine babban ma'aikaci wanda yake rage faruwan bala'i da musifa akan mumuni kuma dashi ne mumini ke kiyaye kansa daga yawan cututtuka na gabbai wanda suke faruwa sakamokon damuwa saboda damuwar dake damun mutum, domin musulmi idan yayi imani da cewa dukkan abunda ya samu bazai taba kubce masa ba kuma abunda ya rasa daman can bazai same shi ba, zai yarda da abunda Allah ya raba masa da kaddara masa akan sa, Allah madaukaki yace: " abunda yake faruwa na musifa acikin kasa da acikin rayukanku face tana a cikin littafi a gabanin Mu halitta ta. Lallai wannan ga Allah mai sauki ne (22) [84]

kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " mumini me karfi (wanda yake da ikon yawaita aikin da'a) yafi alheri da soyuwa agun Allah sama da mumini me rauni, kuma cikin ko wannen su akwai alheri, kayi kokari kan abunda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah kada kayi gaza, idan wani abu ya same ka kada kace: da ace ya aikata kaza da kaza, kace: haka Allah ya kaddara, kuma duk abunda yaso yake aikatawa, domin cewa da'ace yana bude kofar sheda."[85]

Wajibi akan mumini shin eyarda da abunda Allah ya kaddara masa na alheri ko na sharri, cikin halin wadata da talauci da halin lafiya da rashin lafiya da halin tsanani da sauki, kada ya zama cikin masu yarda cikin halin wadata da lafiya da sauki da kuma kin yarda cikin halin talauci da tsanani da rashin lafiya, sai ya zama kamar wanda Allah ya bada labari akan su cikin fadin sa cewa: " kuma daga cikin mutane akwaiwanda yake bautama Allah akan gaba; idan alheri ya same shi sai ya yarda dashi; amma kuma idan fitina ta same shi sai ya juya baya yayi asara duniya da lahira; wancan shine mafi girman asara bayyananne (11)"[86]

Idan bawan ya san cewa al'amura dukkanin su a hannun Allah suke kuma shine me iko cikin halittun sa da mulkin sa kuma baya hukunta komai face acikin sa akwai maslaha da alheri, kuma shine me amfani da me daukewa dame bayarwa zai samu natsuwa cikin zuciyar sa da kwanciyar hankali, Allah madaukaki yace: " kuma idan Allah ya shafeka da wani cuta babu me yayewa face shi; kuma idan yaso ka da alheri babu me mayar da falalar sa; yana samu dashi wanda yaso cikin bayin sa; kuma shi me gafara ne me rahama(107)"[87]

Idan bawa yasan haka ya kuma samu yaki dashi zai alakantu da Allah alakantuwa me kwari kuma zai dogara a gareshi hakikanin dogara, ya kuma koma gareshi shi kadai domin tsoron ukubar sa da kuma fatar samun ladar sa yana me kwadayin samun kyautan sa da falalar sa tare da aikata sabubba wanda suke halal, Allah madaukaki yace: " … duk wanda yaji tsoron Allah zai sanya masa mafita (2) kuma zai azurtashi ta inda baya tsammani; kuma duk wanda ya dogara ga Allah to ya isar masa; lallai Allah zai isar da al'amarin sa; hakika Allah ya sanya komai kaddara (3)"[88]

Bawa me rauni be san inda alheri yake ba zai iya kasancewa a cikin cuta akwai alheri kuma cikin yalwa akwai sharri, Allah madaukaki yace: " kuma sau dayawa kuna kin abu kuma alheri ne a gareku; kuma sau dayawa kuna son abu kuma sharri ne a gare ku; Allah shine masani ku baku sani ba (216)"[89]

A cikin haka babin neman lada da sakamako daga Allah zai zo akan hakuri akan abunda Allah ya hukunta da kaddarawa ga bawa na bala'i da musifu akan sa ne ko kuma iyalan sa ko kudiyar sa, Allah madaukaki yace: " kuma hakika zamu jabaku da wani abu na faga tsoro da yunwa da tawayan arziki da rayuka da kayan itace; kayima masu hakuri bishara (155) sune wanda idan musifa ta same su sai suce lallai mu ga Allah muke kuma gareshi zamu koma (156) wa'innan akwai anbaton Allah akan su da rahama; kuma wa'innan sune shiryayyu (157)"[90]

Manzon Allah s.a.w yana cewa: " babu wani bawa wanda musifa zata same shi sai yace: lallai mu ga Allah muke kuma gareshi zamu koma. Ya Allah ka bani lada akan wannan musifa tawa kuma ka canzamun da mifiyinta alheri. Face Allah ya bashi lada akan musifar sa ya kuma canza masa da mafiyin ta alheri"[91].

Ibn kayyim Allah yayi mashi rahama yana cewa karkashin Karin bayani akan addu'ar da ta gabata cikin wannan hadisi na sama[92]: " wannan Kalmar tana cikin kololuwa wurin magance musifa kuma mafi amfani duniyar sa da lahiran sa, domin kuwa ta kunshi asaloli biyu masu girma wanda idan bawa ya tabbatar da sanin su, al'amarin musifa zai zo masa da sauki:

Nafarkon: lallai bawa da iyalan sa da dukiyar sa mulki mallaka ne ga Allah mabuwayi na hakika kuma ya sanya su agun bawa a matsayin aro ne, idan ya amsa daga cikin su, to kamar wanda ya bada aro ne ya amsa kayan shi daya bada aronsa.

Na biyu: lallai makomar bawa ranan alkiyama zuwa ga Allah ne majibinsa na gaskiya, babu makawa sai ya bara duniya kuma yazo ga ubangijin sa shi kadai kamar yadda aka halicce sa da fari ba tare da iyalai ba ko dukiya ko dangi sai da kyawawan ayyuka da munana, idan hakan ya kasance farkon bawa da karshen sa, to ta yaya zayyi murna da abunda zai kare? Firiyar sa akan farkon sa da makomar sa yana daga cikin manyan maganin wannan bala'i.

  1. Gaggawa zuwa ga sallah:

Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani ku nemi taimakon Allah da hakuri da kuma salla; lallai Allah yana yare da masu hakuri"[93]

Kuma manzon Allah s.a.w ya kasance idan wani abu ya dame shi yana komawa zuwa ga salla, ya kasance yana cewa: " ya Bilal, yi mana ikama, ka hutar damu da ita."[94]

  1. Rashin kin yarda da kuma kyautata zato ga Allah:

An karbo daga abu huraira Allah ya kara masa yara daga manzon Allah s.a.w yace: " Allah madaukaki yace: ni ina inda bawana yayi zato na, idan yayi zaton alheri to zai samu alheri idan kuma yayi zaton sharri to zai samu sharri."[95]

Kuma mawaki yace: " kuma lallai ina rokon Allah kamar cewa** ina ganin kyakyawan zaton abunda Allah zai aikata"

  1. Yawaita ambaton Allah:

Acikin sa akwai sauki ga musifa da karfafa zuciya, Allah madaukaki yace: " wanda sukayi imani kuma zukatun su ya samu natsuwa da ambaton Allah; ku saurara kuji da ambaton Allah ne zukata ke samun natsuwa (28)"[96]

  1. Yawaita rokon Allah:

Allah madaukaki yace: " ko kuma wanda yake amsa kiran mabukaci idan ya kirashi kuma yana yaye damuwa"[97]

 kuma Allah madaukaki ya kara cewa: " kuma ubangijin ku yace ku rokeni zan amsa maku; lallai masu girman kai game da roko bautamun zasu shiga aljanna suna masu kaskanci (60)"[98]

  1. Sanin cewa lallai kunci yana tare da gushewa kuma tsanani yana tare da sauki:

Allah madaukaki yace: " lallai tsanani yana tare da sauki (5) kuma lallai tsanani yana tare da sauki (6)"[99]

  1. Sanin kaskancin duniya:

Cewa lallai ita kaskaci ce wacce ba komai ba gida ce wacce take gushewa bawai gida bace wacce take dawwama dukkanin abunda ke cikinta me karewa ne kawai fuskar Ubangijin ka ne zai saura acikin ta mabuwayi me karamci, Allah madaukaki yace: " Ku sani cewa rayuwar duniya wasa ce da shagala da kawa da alfahari a tsakanin ku da gasar wadata ta dukiya da yara, kamar misalin shuka wadda yabanyarta ta bayar da sha’awa ga manoma, sa’annan ta kekashe har kaganta ta koma rauno. Kuma a lahira akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da yarda. Kuma rayuwar duniya bata zama ba face dan jin dadin rudi kawai (20) "[100]

An karbo daga Sahal dan sa'ad Allah ya kara masa yarda yace: " mun kasance tare da manzon Allah s.a.w a zulkulaifa sai ga wata akuyanan ta mutu kafafuwan ta a sama, sai yace: kuna ganin wannan wulakantacciya ce agun me ita?! Ina rantsuwa da wanda raina ke hannun sa, duniya tafi zama wulakantacciya agun Allah sama da wannan akuyar agun me ita, da ace duniya takai darajar fuffuken sauro agun Allah da kafiri be sha digun wura a cikinta ba har abada."[101]

  1. Sanin cewa mutum bazai bar duniyan nan ba face ya kamala cinye abunda Allah ya kaddara masa:

Manzon Allah s.a.w yana cewa: " lallai ruhul kudusi (Jibril amincin Allah ya tabbata a gareshi) ya jifamun wahayi a cikin zuciya ta ba tare da naji shi ba ko ganin sa, cewa lallai rai bazata mutu ba har sai ta kamala ajalinta, kuji tsoron Allah, kuma ku kyautata nemar kun a arziki, kada wani daga cikin ku ya nemi arziki ta hanyar haram sakamakon jin kirin arzikin sa, domin lallai Allah madaukkai ba'a samun abunda ke wurin sa face dayi masa biyayya"[102]

Ibn kayyim Allah yayi masa rahama ya fado wasu daga cikin magunguna:[103]

  1. Ya samu kwarin gwewa ga wanda musifa ya same su da kuma sanin yakinin cewa kowa yana da nashi musifar bawai shi kadai bane wanda aka rajjaba ko kuma musifa ta sameshi, da ace zai bincika duniya kuwa da yaga masu musifu daban daban, kuma ya sani cewa duniya gida ne na rajabawa idan yayi dariya kadan zayyi kuka dayawa, idan yayi murna yau zayyi bakin ciki na shekara, idan yaji dadi kadan bazai samu ban a tsawon lokaci, Allah madaukaki yana cewa: " idan rauni ya same ku to fa hakika rauni ya sami mutane irin sa; kuma wancan ranaku ne muke jujjuyawa atsakanin mutane"[104]
  2. Yayi tunani cikin abunda ya sameshi na bala'i da musifa, ya kuma godema Allah akan cewa bata zama me girma ba, kuma bata kasance ba cikin addinin sa, komai cikin jin dadin duniya babu bakin ciki akan gushewar sa face gushewar addini, kuma ya godema Allah akan abunda ya sauran masa na ni'imomi na daban. Hakika kafar Urwata dan Zubair ta yanke kuma yaron say a mutu a rana daya, sai yace: " ya Allah godeya ya tabbata a gareka idan ka amsa hakika ka bani, kuma idan ka jarabeni hakika ka bani lafiya, ka bani gabbai guda hudu ka amshi daya kacal, kuma ka bani yara hudu ka amshi daya kacal."
  3.  Ya sani cewa butulci da rashin yarda akan abunda Allah ya kaddara da hukuntawa yana fusatar da ubangijin sa, yana kuma sanya shedan farin ciki, yana gaishe da makiyan sa, da kuma bakantawa abokan sa, ya lalata ladar sa, da raunata zuciyar sa, idan kuma yayi hakuri da neman yardan ubangijin sa, sai shedan yayi bakin cikin ya koma yana tababbe, yasa abokan sa farin ciki, ya bakantawa makiyin sa.
  4. Ya dauka abunda ya same shi na bala'i da musifa babi ne cikin babin samun lada wanda zai samu lada dashi idan yayi hakuri da neman haka, kuma yayi tunani samun ladan lahira abunda Allah yayi alkawari ga me hakuri da neman lada agunsa baya kubce masa. An karbo daga Abi Musa al-ash'ari Allah ya kara masa yarda cewa manzon Allah s.a.w yace: " idan yaron mutum mumini ya mutu, sai Allah yacema mala'iku: ku amshi yaron bawa ne? sai suce: eh. Sai yace: kun amshi riban zuciyar sa? sai suce: eh. Sai yace: to me yace? Sai suce: yace ne lallai mu ga Allah muke muka gareshi zamu koma ya kuma gode maka. Sai yace: to ku gina masa gida cikin aljanna kuma ku kirashi da suna gidan godiya."[105]

An karbo daga abi Sa'ed al-khudri Allah ya kara masa yarda daga amanzon Allah s.a.w yace: " wnai abu baya samun musulmi na gajiya ko rashin lafiya ko bakin ciki ko damuwa ko cuta hatta kayar da zai taka face Allah ya kankare masa zunubin sa dashi."[106]

  1. Ya sani cewa hakuri da juriya akan abunda ya sameshi na musifa da bala'i yana daga cikin siffar mumini kuma sababi ne cikin sababin shiga aljanna, Allah madaukaki yace: " kuma hakika zamu jarabe ku har sai mun san mujahidai a cikin ku da masu hakuri kuma zamu jaraba labaran ku (31)"[107]

An karbo daga Suhaib Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " akwai abun mamaki cikin al'amarin mumini. Lallai al'amuran sa baki dayan su alheri ne. kuma babu me samun haka sai mumini. Idan farin cikin ya same shi sai yayi godiya sai hakan ya kasance alheri a gareshi. Idan kuma wata damuwa da cuta da same shi sai yayi hakuri sai hakn ya kasance alheri a gareshi.[108]

  1. Ya sani cewa duk fa yadda abun ya damesgi to fa karshen sa dole sai yayi hakuri na tilas, kuma wannan hakuri babu yabo akan sa kuma babu lada ga me shi, an karbo daga Mahmud dan Labid cewa manzon Allah s.a.w yace: " idan Allah yana son mutane sai ya jarabe su, wanda yayi hakuri yana da hakuri, wanda kuma ya dimauce yanada dimuwar sa."[109]
  2. Ya sani cewa wanda ya jarabeshi shine mafi tausayin masu tausayi, kuma be aiko masa da bala'i ba domin ya halakar dashi ba ko kuma ya azabtar dashi, ya aiko aiko masa ne domin ya jaraba hakurin sa da yardan sa da imanin sa kuma yaji damuwar sa da bala'in sa da kuma ganin sa a matsayin mabukaci a gaban sa yana me daga hannu domin kai masa kukan sa. a lokacin da manzon Allah s.a.w yaga wata mata tana shayar da danta, sai yace ma sahabban sa: " shin kuna ganin wannan mata zata iya jefa danta cikin wuta? Sai suka ce: a'a ya manzon Allah. Sai yace: Allah yafi tausayin bayin sa sama da wannan mata ga yaronta."[110]
  3. Ya sani cewa lallai dacin duniya itace dadin lahira haka Allah madaukaki ke canzata kuma dadin duniya itace dacin lahira kuma ace ya tashi daha dacin me yankewa zuwa dadi mara yankewa yafi mashi alheri sama da akasin sa, manzon Allah s.a.w yana cewa: " an kewaye aljanna da abubuwan da ake kin su, kuma an kewaye wuta da sha'awowi."[111] Maganar sa ta kare Allah yayi mashi rahama.

Kuma hakan bawai yana nufin cewa mutum dutse bane baya jin wasu abubuwa na dabi'a abun da aka hana shine rashin yarda da dimaucewa da kuma kin yarda da kaddarar Allah da hukuncin sa, an karbo daga Anas dan Malik Allah ya kara masa yarda yace: " mun shiga tare da manzon Allah s.a.w wurin Abu Saif alkin wanda miji ne ga matar da ta shayar da Ibrahim – dan Manzon Allah – amincin Allah ya tabbata a gareshi, sai manzon Allah s.a.w ya dauki Ibrahim ya sunbace shi ya shinshina shi, yace, sai muka shiga wurin sa bayan haka ran Ibrahim yana fita, sai idonun manzon Allah s.a.w suka fara hawaye, sai Abdurrahman dan Auf Allah ya kara masa yarda yace: harda kaima ya manzon Allah? Sai yace: ya dan Auf lallai rahama ce, sa'annan hawaye ya biyo ta, sai manzon Allah s.a.w yace: lallai idonu zasuyi hawaye, kuma zuciya zatayi bakin ciki, amma dai bazamu fadi ba sai abunda Ubangijn mu ya yarda dashi, kuma lallai rabuwa dakai akwai bakin ciki ya Ibrahim."[112]

An karbo daga usama dan zaid Allah ya kara masa yarda yace: " mun kasance agun manzon Allah s.a.w, sai daya daga cikin yarinyar shi tayi mashi aiki tana kiran sa da sheda masa yaron ta yam utu. Sai manzon Allah s.a.w yace ma dan sakon: " ka koma kace mata: lallai abunda Allah ya amsa nashi ne kuma abunda ya bayar nashi ne, kuma komai a wurin sa zuwa wani lokaci ne sananne, kace mata tayi hakuri ta nemi ladan haka daga Allah" sai san sakon ya dawo yace: " lallai ta rantse sai kaje". Sai yace sai manzon Allah s.a.w ya tashi, sai Sa'ad dan Ubadata da Mu'azu dan Jabal suma suka tashi suka bishi. Sai aka dago masa yaron ransa yana motsi kamar mostin ruwa. Sai idanun sa sukayi hawaye. Sai Sa'ad yace masa menene haka ya manzon Allah? Sai yace: " wannan rahama ce. Wanda Allah ya sanya ta cikin zuciyar bayin sa"[113].

 

 

 

Hanyoyin kare kai:

Daga cikin hanyoyin da mutum zai kare kansa:

  1. Yawaita karatun alkur'ani da dawwama akan sa musamman ma suratul bakara, domin shedanu suna gudu daga gidan da ake rayashi da ambaton Allah da karatun alkur'ani. An karbo daga abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " kada ku mayar da gidajen ku ya koma kaburbura, lallai shedan yana gudu daga gidan da ake karanta suratul bakara a cikin sa"[114]
  2. Kiyayewa da kuma dawwama akan fadin (Bismi Ellah) da kuma rashin mantata wurin dukkanin farkon abunda mutum zayyi na ayyukan sa zata kasance da yardan Allah kariya da Katanga daga shedanun aljannu. Manzon Allah s.a.w yace: " kariyar dake tsakanin aljannu da al'aurar dan adam idan dayan su ya shiga bayi yace Bismillah"[115]
  3. Ya rika addu'a na albarka a lokacin daya ga wani abun burgewa a jikin sa da dukiyar sa da iyalan sa da abun farin ciki, kamar yace: "masha Allah la kuwwata Illa Billah – masha Allah babau karfi sai ga Allah -, ko kuma: " masha Allah tabaraka Allah – masha Allah, tibarkalla -", domin hadisin Amir dan Rabi'ata Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " idan dayan ku yaga wani abu daga jikin sa ko dukiyar sa ko kuma agun dan uwan sa abunda ya burgeshi to yayi mashi addu'a da albarka, domin lallai kanbun baka gaskiya – maita –"[116]
  4. Mutum ya rika neman ma kansa tsari da yaran sa kuma ya dawwama akan haka, an karbo daga dan Abbas Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya kasance yana neman ma hasan da husaini tsari yana cewa: lallai ubanku (watan annabi Ibrahim) ya kasance yana neman ma Isma'il da Ishak tsari: " ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkanin shedan da guban sa da kuma dukkanin ido wanda yake me cutarwa".[117]

Daga cikin shi akwai fadin: " da sunan Allah wanda babu abunda ke cutarwa tare da sunan sa cikin kasa ko sama kuma shi me ji ne kuma masani" sau uku safiya da maraice. Haka kuma fadin: " ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku dukkanin su daga sharrin abunda ya halitta" sau uku safiya da maraice.

  1. Dawwamar ambaton Allah na nacewa akan haka, Allah madaukaki yace: " ku ambace zan ambace ku kuma ku gode mani kada ku kafurce mun".[118]

Manzon Allah s.a.w yana cewa cikin hadisul kudusi: Allah mnadaukaki yana cewa: " ni ina inda bawana yayi zato na[119], kuma ina tare dashi idan ya ambace ni, idan ya ambace ni cikin zuciyar s azan ambace shi cikin zuciya ta, idan kuma ya ambace ni cikin tarin jama'a zan ambace shi cikin taron daya nashi alheri, idan ya kusance ni da kamun hannu day azan kusance shi da zira'I daya, idan kuma ya kusance ni da zira'i zan kusance shi da kwatankwacin fadin mutum idan ya bude hannun sa guda biyu, idan yazomun yana tafiya zanzo masa ina sassarfa"[120]

 

 

 

 

Daga cikin fa'idojin ambaton Allah:

  1. Allah madaukaki yayi bayani cikin littafin sa me girma cewa dawwama akan ambaton sa sababi ne cikin sabubba na kawar da bala'i bayan saukan ta, sai madaukaki yace yana me hakaito labari akan annabi Yunus Amincin Allah ya tabbata a gareshi: " Kuma lallai Yunusa hakika yana daga cikin manzanni (139) a lokacin daya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yiwa lodi (140) sa’annan yayi kuri’a sai ha kasance a cikin wadanda aka rinjaya (141) sai kifi yayi loma dashi, alhali kuwa yana wanda ake zargi (142) to, ba domin lallai shi ya kasance daga masu tasbihi ba (143) lallai daya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa ranar da za’a tayar dasu (144) "[121]
  2. Lizimtar ambaton Allah sababi ne cikin sabubban amsar addu'a da kum akariya me taimakon bawa, manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah yayi wahayi zywa ga Yahaya dan Zakariyya da kalmomi guda biyar dayayi aiki dasu, kuma ya umurci bani isra'ila da suyi aiki dasu. Kamar yayi jinkiri dasu, sai Isa yazo masa yace: lallai Allah ya umurce ka da kalmomi guda biyar kayi aiki dasu, kuma ka umurci bani isra'ila da suyi aiki dasu, kodai ka fada masu ko kuma na fada masu. Sai yace: ya dan uwa! Kada ka aikata, domin nina tsoron ka rigani za'a shafe kasa dani ko kuma a azabtani. Sai yace: sai ya hada bani isra'ila a dakin makdis har sai da masallaci ya cika, suka zauna sa'annan ya masu magana yace: lallai Allah yayi wahayi a gareni da wasu kalmoi biyar danayi aiki dasu, sannan na umurce ku da kuyi aiki dasu: nafarkon su ku bautawa Allah kada kuyi shirka dashi da komai, domin lallai misalin wanda yayi shirka da Allah da wani abu kamar misalin mutum ne ya siya bawa daga dukiyar sa na kashin kansa na zinari ko azurfa sa'annan ya zaunar dashi a cikin gida sai yace: kayi aiki kuma rika kawomun kudin sai ya fara aiki yan akaima wani kudin! Wanene zai yarda da haka a cikin ku; to lallai Allah ya halicce ku kuma ya azurta ku, saboda haka kada kuyi masa shirka da komai. Kuma idan kun tashi yin salla kada ku rika juyawa, domin Allah yana fuskantar fuskar sa zuwa ga fuskar bawar sa matukar be juya ba. kuma ya umurce ku dayin azumi, kuma misalin haka kamar misalin mutum ne yana cikin runduna atare dashi akwai fakeji na miski, dukkanin su suna son jin kamshin shi, to lallai azumi yafi kamshi a wurin Allah sama da kamshin almiski. Kuma ya umurce ku dayin sadaka, kuma misalin sa kamar misalin mutum ne wanda makiyi yamai kawanya, sai suka daure masa hannu akan wuyan sa, suka kusanto zasu kashe shi, sai yana cewa: shin zan iya fansar kaina a wurin ku, sai ya rika basu kadan da kuma dayawa har saida ya fansa kansa. Kuma ya umurce ku da ambaton sa dayawa, kuma misalin haka kamar misalin mutum ne wanda makiya suka neme shi dayin fada har sai da yzao ga kariya, sai ya boye kansa a ciki, to kamar haka ne bawa baya tsira daga shedan sai da ambaton Allah."[122]
  3. Lamintar ambaton Allah yana wadatarwa akan karatun alkur'ani ga wanda bazai iya karanta komai ba cikin alkur'ani, an karbo daga Abdu Allah dan Abi Aufa Allah ya kara masa yarda yace: " wani mutum yazo gun manzon Allah sai yace: ya manzon Allah bana iya koyan alkur'ani, ka sanar dani abunda zai wadatar dani daga alkur'ani sai yace: " kace: subhana Allah walhamdu Lillah wala 'ilaha illa Allah wa Allahu Akbar wala haula wala kuwwata illa Billah". Sai yace wannan na Allah ne, ni kuma ina nawa? Sai yace: " kace: ya Allah ka gafartamun kamun rahama ka shiryar dani kuma ka bani lafiya kuma ka azurtani" sai manzon Allah s.a.w yace: " hakika ya cika hannun sa da alheri"."[123]
  4. Lamintar ambaton Allah yana daga cikin sabubba na koran shedan da wasiwasin sa, an karbo daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " shedan yanayin kulli a keyar dayan ku idan yana bacci, yana dukan ko wani kulli: yana ce maka dare yana da tsayi kayi bacci, idan ya tashi ya ambaci Allah sai wannan kulli ya warware, idan yayi alwalla sai dayan kullin ya warware, idan yayi salla sai kullin na uku ya warware, sai ya tashi cikin nishadi da natsuwa, idan kuma bah aka ba zzai tashi cikin damuwa da kasala."[124]

 

 

 

Daga cikin zakiri wanda sukafi falala:

  1. Manzon Allah s.a.w yana cewa: " kalmomi guda biyu masu sauki akan harshe, masu nauyi a cikin ma'auni, abun soyuwa agun me Rahama: Subhana Allah wabi hamdihi, subhana Allahil Azim".[125]"
  2. Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " wanda yace: " subhana Allahi wabi hamdihi", a cikin yini sau dari, za'a kankare masa zunuban sa koda kuwa sun kasance kamar yawan kunfar kogi ne."[126]
  3. Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " duk wanda ya tashi cikin dare sai yace: " babu abunbautawa da gaskiya sai Allah, mulki da godiya nashi ne, kuma shine me iko akan komai, godiya ta tabbata ga Allah, tsariki ya tabbata ga Allah, kuma babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, Allah me girma, kuma babu tsimi da dabara da karfi sai ga Allah", sa'annan yace: " ya Allah ka gafarta mun", ko kuma yayi addu'a, to za'a amsa masa, idan yayi alwalla yayi salla za'a a, shi sallar sa."[127]
  4. Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " na fadi: " tsarki ya tabbata ga Allah kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma babu abun bauta da gaskiya sai Allah, kuma Allah me girma", yafi soyuwa a gareni sama da abunda rana ke fitowa akansa- watan duniya da abunda ke cikin ta na arziki -."[128]
  5. Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " shin dayan ku zai kasa samun lada dubu a kullum? " sai wani ya tambashi cikin majalin sa: ya za'ayi dayan mu ya samu lada dubu a rana? Sai yace: " yayi tasbihi- yace tsarki ya tabbata ga Allah- sau dari, za'a rubuta mashi lada dubu, kuma a kankare masa zunuban sa guda dubu"."[129]
  6. Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " duk wanda yamun salati daya; Allah zayyi masa salati goma da ita, kuma zai kankare masa zunuban sa goma."[130]
  7. Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " tsarki (alwalla) rashin imani ne, walhamdu Lillahi tan acika ma'auni, subhana Allah walhamdu Lillah suna cika takanin sama da kasa, kuma salla harke ce, sadaka hujja ce, hakuri haske ce, kuma alkur'ani hujja ne a gareka ko kuma akanka, dukkanin mutane suna wayen gari, daga cikin su akwai me siyar da kansa, kodai ya yantar da ita ko kuma halakar da ita"[131]
  8. Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa ga daya daga cikin sahabban sa: " shin na numa maka kalma wacce task ace cikin taskokin aljanna? " la haula wala kuwwata illa billah – babu tsima da dabara da karfi sai ga Allah-."[132]
  9. Zikiri dayawa, an karbo daga Juwairiyya Allah ya kara mata yarda tace: " lallai manzon Allah s.a.w ya fita daga wurinta da hantsi bayan yayi sallar asuba, ita kuma tana gun sallarta. Sa'annan yay a dawo bayan walaha ya sameta a zaune a wurin tana tasbihi. Sai yace " har yanzu kina zaune kana abunda nabarki kinayi? " sai tace: eh. Sai manzon Allah s.a.w yace: hakika ya fadi wasu kalmomi guda hudu, sau uku abayanki, da ace za'a auna su da abunda kika fadi tun dazu da sunyi goganya dasu: tsarki ya tabbata ga Allah da godiyan sa, kwatankwacin yawan halittun sa da yardan kansa da nauyin al'arshin sa, da yawan kalmomin sa."[133]

 

 

 

Hanyoyin da suke jawo yardan Allah wanda suke kare sharri da masifu:

  1. Ya kasance ya lazimci istigfari saboda kasancewar mafi yawan amsifu wanda suke shafan mutum sakamakon zunuban sa ne da sabon sa, kamar yadda Allah ya bayyana haka cikin fadin sa: " kuma duk abunda ya shafeku na musifa to sakamako ne ya abunda hannayen ku suka aikata kuma yana yafewa dayawa (30)"[134]

Lazimtar istigfari da dawwama akai yana daga cikin sabubba na yawo arziki da yalwa, kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari akai yace: " sai nace (masu) ku nemi gafarar ubangijin ku lallai shi ya kasance me gafara (10) zai aiko maku da ruwa daga sama me tarin yawa (11) kuma zai kara maku yawan dukiya da yara kuma zai sanya maku gonaki kuma zai sanya maku koramu (12)"[135]

Lazimtar istigfari da dawwama akai sababi ne na yaye damuwa da wande kunci kamar yadda manzon Allah s.a.w ya fadi cikin fadin sa: " duk wanda ya yawaita istigfari Allah zai sanya masa waraka cikin ko wani damuwar sa da kuma mafita cikin ko wani tsanani kuma zai azurtashi ta inda baya zato" [136]

Kuma kasancewa ko wani mutum yana zunubi da yin sabo, yarda dashi da ikirari da kuma tuba daga gareshi sababi ne nay aye musiba da kuma gushewar ta, kuma ya isa yarda dashi da harshe kawai kuma ya wajaba yarda dashi da ikirari na zuciya wanda ya kunshi rabuwa da wannann zunubi da nadama akan aikatashi da kuma yin azama na gaskiya akan bazai kara aikatawa ba, Allah madaukaki yace: " da Zannuni a lokacin da ya tafi cikin fushi sai yayi zaton bazamu samu iko ba akan sa; sai yayi kira cikin duhu cewa babu abun bautawa dagaskiya sai kai; tsarki ya tabbatar maka lallai na kasance cikin azzalumai (89) sai muka amsa masa muka kuma tsiratar dashi daga damuwar sa, kamar haka ne muke tsiratar da muminai (88)"[137]

  1. Sanin Allah cikin halin yalwa ta hanyar riko da umurnin sa da niantar abubuwan da yayi hani, an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " wanene yakeson Allah ya tsiratar dashi a lokacin tsanani da damuwa, to ya yawaita addu'a a lokacin yalwa"[138]

Kuma yana cewa cikin hadisin da dan Abbas ya rawaito: "….. ka san Allah cikin yalwa zai sanka cikin tsanani….."[139]

  1. Yayema musulmai damuwar su da kuma sauki a garesu, manzon Allah s.a.w yana cewa: " duk wanda ya yayewa wani mumini wata damuwar sa cikin damuwar duniya Allah zai yaye masa damuwar sa cikin damuwar ranar lahira, wanda kuma ya saukakema wanda yake cikin kunci, Allah zai saukake masa duniya da lahira, duk wanda ya suturta musulmi, Allah zai suturta shi duniya da lahira, kuma Allah yana cikin taimakon bawa matukar bawa yana cikin taimakon dan uwan sa, duk wanda ya kama hanya yana me neman ilimi a cikinta, Allah zai saukake masa da ita hanya zuwa aljanna, kuma mutane bazasu taru ba cikin wani daki daga cikin dakin Allah suna karanta littafin Allah, da nazarin sa a tsakanin su, face an saukar masu da natsuwa, kuma rahama ta lullube su, kuma mala'iku su lullube su, kuma Allah ya ambace su cikin mutanen dake wurin sa, duk wanda aikin sa yayi baya dashi to dangantakar sa bazai yi gaba dashi ba."[140]
  2. Yawaita yin sadaka da ayyukan da'a domin kuma lallai da izinin Allah zasu kawar da musifu da tafiyar da bala'i, an karbo daga Anas dan Malik Allah ya kara masa yarda yace: lallai manzon Allah s.a.w yace: " lallai sakada tana kashe fushin Ubangiji"[141]

Kuma Umma salma Allah ya kara mata ta rawaito manzon Allah s.a.w yace: " aikata ayyuka na kwarai kariya ne ga abubuwan sharri, kuma sadaka ta boye tana kashe fushin Ubangiji, sadar da zumunci yana kara tsawon shekaru, kuma dukkanin aiki na kwarai sadaka ne, kuma ma'abota ayyuka na kwarai a duniya sune ma'abota ayyukan kwarai a lahira, kuma ma'abota munanan ayyuka a duniya sune ma'abota munanan ayyuka a lahira…"[142]

An karbo daga Mu'azu dan Jabal Allah ya kara masa yarda yace: " ya kasance tare da manzon Allah s.a.w a tafiya, sai na wayi gari wata rana kusa dashi muna cikin tafiya, sai nace: ya manzon Allah ka fadamun aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta. Sai yace: hakika ka tambayeni akan babban abu, amma abu ne mai sauki agun wanda Allah ya saukake masa: ka bautawa Allah kada ka hadashi da wani wabu cikin bauta, ka tsayar da salla, ka bada zakka, kayi azumin Ramadan, kayi hajjin daki me alfarma. Sa'annan yace: shin bazan nuna maka kofofin alheri ba: azumi situra ce da kariya, kuma sadaka kana kashe zunubai kamar yadda ruwa take kashe wuta, da kuma sallan mutum a tsakiyar dare. Sai yace: sa'annan ya karanta ayar nan {jikin su yana nisantar wuraren baccci suna masu kiran Ubangijin su….}, har yakai {suna aikatawa}[143], sa'annan yace: shin bazan fada maka tushen al'amari ba baki dayan sa da ginshikin sa, da mafi kololuwan sa? sai nace: ka fadamun ya manzon Allah, sai yace: tushen abu shine musulunci, ginshikan sa kuma shine salla, mafi kololuwan sa kuma shine jihadi, sa'annan yace: shi bazan fada maka abunda ke kamala ba da cika wannan abu baki dayan sa? sai nace: fadamun ya manzon Allah. Sai yace: sai ya rike harshen say ace: ka kame wannan abu. Sai nace: hya manzon Allah ashe za'a kamamu da abunda muke magana dashi? Sai yace: kaicon ka, shin akwai abunda yake kiba mutane a cikin wuta akan fuskokon su ne ko kuma akan karan hancin su ne face tsinin harshen su."[144]

  1. Sada zumunci ta hanyar ziyartan su da jin bukatun su, Allah madaukaki yace: " To, shin kuna fatan idan kun juya zakuyi barna a cikin kasa, kuma ku yanke zumuntar ku? (22) wadannan sune wadanda Allah ya la’ance su sa’annan ya kurumtar dasu kuma ya makantar da ganin su (23) shin to, baza su kula da alkur’ani ba ko kuwa akan zukatansu akwai makullan su ne? (24)"[145]

Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " babu wani abu wanda akeyi ma Allah biyayya dashi wanda yafi gaggawan bada lada akan sa sama da sada zumunci, kuma babu wani abu wanda yafi saurin jawo ukuba akai sama da zalumci da yanke zumunci, da rantsuwa ta fajirji (wanda zai rantse akan abu alhali yana sane da cewa karya yakeyi) tana busar da gidan ya zama babu komai na arziki acikinta."[146]

  1. Nesantar zalumtar mutane da cucar dasu, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " addu'ar wanda aka zalumta tana hawa sama kuma ana bude mata kofukan sammai, sai Ubangiji madaukaki yace: ina rantsuwa da buwayata sai na taimake ka, koda kuwa bayan wani lokaci ne."[147]

Kuma duk yadda ukubar Azzalumi tayi jinkiri dole dai sai ya same shi, an karbo daga Abu Musa Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah yana talala ga azzalumi har idan ya rike shi to baya kyale shi. Sai yace: sa'annan ya karanta: {kuma kamar haka rikon Ubangijin ka yake idan ya kama alkarya azzaluma, lallai rikon sa me radadi ne kuma me tsanani}[148]."[149]

  1. Magiya zuwa ga Allah ta hanyar luzumtar rokon sa da kuma kaskantar dakai a gaban sa, Allah madaukaki yace: " kuma Ubangiji ku yace ku kirani zani amsa maku, lallai masu yin girman kai game da kirana da sannu zasu shiga jahannama suna kaskantattu (60)"[150]

Manzon Allah s.a.w yana cewa: " babu wani abu da yakai addu'a falala a gun Allah"[151]

An karbo daga saubana Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " lallai mutum ana haramta masa arziki sakamakon zunubin sa, kuma ba'a canza kaddara sai da addu'a kuma baya karama rayuwa komai face aikin kwarai."[152]

Gazali yana cewa:

Idan ance: menene amfanin addu'a to tare da hukuncin Allah wanda babu makawa a gareshi? Kasani cewa daga cikin jumlar hukuncin Allah akwai tunkude bala'i da addu'a, addu'a sababi ce na tunkude bala'i da kuma samar da rahama, kamar yadda yadda salke yake sababi na kare makami, ruwa kuma sababi ne na fitan tsirrai daga kasa, kamar yadda salke yake kare makami, haka addu'a take da bala'i, bawai sharadin rashin yarda da hukuncin Allah bane cewa mutum kada ya dauki makami, kuma hakika Allah madaukaki yace: " kuma su riki shirin su da makaman su"[153] Allah ya kaddara al'amari kuma ya kaddara sababin sa.

Kuma Ibn Kayyim yana cewa[154]:

Da za'a tabbatar da mazhabar su da hakan ya wajabta kore dukkanin sabubba, sai ace ma dayan su: idan an kaddara maka koshi da shayarwa dole ne ka koshi din kaci ko baka ci ba, kuma idan ba'a kaddara maka ba ko kaci kasha din bazaka koshi ba, idan an kaddara maka samun yaro koda ka sadu da matar ka ko baka sadu da ita ba zaka samu yaro, idan kuma ba'a kaddara maka ba bazaka samu ba babu amfanin yin aure, da sauran su dai.

 

 

 

Ladubba na addu'a:

Sarkin mumunai Umar dan Khaddab Allah ya kara masa yarda yana cewa:

" ni bana daurama kaina nauyin amsa addu'a ni nawa kawai itace yin addu'a, idan kayi himma dayin addu'a to lallai amsawa tana tare da ita".

Addu'a tana da ladubba wanda musulmi ya sanya su a gaba gareshi gabanin yin addu'a, domin amsar addu'ar sa a wurin maulana madaukaki, daga cikin wannan ladubba akwai:

  1. Yin kokari wurin neman halal cikin dukkanin al'amuran mutum ya ksance cinsa da shansa da tufafin sa da abun hawar sa dukkanin su halal ne, an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " yaku mutane, lallai Allah me tsarki ne kuma baya amsan ayyuka sai masu tsarki, kuma Allah ya umurci muminai da abunda ya umurci manzanni dashi sai yace: {yaku manzanni kuci daga tsarkakan kuma ku aikata ayyuka na kwarai, lallai ni masani game da abunda kuke aikatawa}[155]. Sai yace: {yaku wanda sukayi imani kuci daga tsarkakan abunda muka azurta ku}[156]. Sa'annan ya ambaci wani mutum wanda yake yawaita tafiya, me datti da kura, yana meka hannuwan sa zuwa sama yana cewa: ya Ubangiji ya Ubangiji! Alhali abincin sa haramun ne, kuma abun shan sa haramun ne, kuma tufafin sa haramun ne, kai da haramun aka ciyar dashi tun yana yaro, to tayaya zamu amsa masa addu'ar sa?"[157]
  2. Kokarin kasancewa cikin tsarki (watan alwalla) yana me fuskantar alkibla da daga hannuwan sa sama a lokacin addu'a da kuma magiya ga Ubangijin sa, saboda abunda aka rawaito daga Salman Allah ya kara masa yarda cewa manzon Allah s.a.w yace: " lallai Ubangijin ku me kunya ne – yanajin kunyar bawa ya daga hannu ya roke shi ya sauke hakanan babu komai."[158]

An karbo daga Muhajir dan Ibn Kinfiz Allah ya kara masa yarda yace: " nazo gun manzon Allah s.a.w yana kama ruwa, sai nayi mashi sallama, sai be amsani ba har sai bayan yayi alwalla, sa'annan ya bani hakuri yacemun: lallai niji kyamar na ambaci Allah ne bani da tsarki. – ko kuma ba'a cikin tsarki ba.-"[159]

  1. Ya kasance sautin sa a cikin addu'ar sa tsakanin babban sauti da kuma karamin sauti, saboda fadin Allah madaukaki: " kuma kada ka bayyana sautin ka kuma kada ka boye ta ka tsaya a tsaka-tsakin haka (110)"[160]

An karbo daga Abu musa al ash'ary Allah ya kara masa yarda yace: " mun kasance tare da manzon Allah s.a.w, sai ya kasance idan munga wani korama sai muyi tahlili (fadin la'ilaha illah) da yin kabarbari sai mu daga sautin mu dasu, sai manzon Allah s.a.w yace: " yaku mutane ku saukake ma kawunan ku, domin lallai wanda kuke kira ba kurma bane ko kuma wanda bayanan, lallai yana tare daku yanaji kuma makusanci ne, sunana ya daukaka kuma ya girmama"."[161]

  1. Ya fara addu'ar sa da godiya ga LAlah da kuma yi masa yabo sa'annan yin salati ga manzon Allah, sai kuma ya fara gabatar da tuba da istigfari da kasakancin sa da kuma bukatar sa sai ya cika da haka, Allah madaukaki yace: " kuma karshen addu'ar su shine godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai (10)"[162]

An karbo daga Fudalata dan Ubaid al Ansari Allah ya kara masa yarda yace: " lallai manzon Allah s.a.w yaga wani mutum yana addu'a a cikin sallar sa be fara da godiya ba da salati ga manzon Allah s.a.w fabanin haka, sai yace wanann mutumi yayi gaggawa fara tambayar bukatun sa yabar abunda ya kamata ya fara dashi na ladubban addu'a, sa'annan ya kira wannan mutum yace masa da wanin sa: idan dayan ku zayyi addu'a to ya fara da godiya ga Allah da kuma yabon sa sa'annan yayi salati ga manzon Allah s.a.w sa'annan ya roki abunda yake so bayan haka."[163]

  1. Ya roki Allah da sunayen sa kyawawa da siffofin san a kololuwa, Allah madaukaki yace: " kuma Allah yana da sunaye kyawawa ku kirashi dasu"[164].

An karbo daga Abdullhi dan Buraida daga babansa: " lallai manzon Allah s.a.w yaji wani mutum yana cewa: ya Allah ina rokon ka da cewa lallai na shaida babu abun bautawa da gaskiya sai kai ka dai wanda ake nufi da bukata wanda be haifaba kuma ba'a haifeshi ba kuma bashi da wani tamkar a gareshi. Sai manzon Allah s.a.w yace: " hakika ya roki Allah da sunan da idan aka tambaye shi dashi yana bayarwa kuma idan aka kirashi dashi yana amsawa".[165]"

An karbo kuma daga Anas dan Malik Allah ya kara masa yarda yace: " na kasance tare da manzon Allah s.a.w muna zaune sai ga wani mutum tsaye yana salla, bayan yayi ruku'u sa sujjad da tahiya sai yayi addu'a, sai yace cikin addu'ar nasa: ya Allah ina rokonka da cewa lallai godiya yana gareka, babu abun bautawa da gaskiya sai me me bayarwa wanda ya kirkiri sammai da kasa, ya ma'abocin girma da karamci, ya me rai ya tsayayye, ina rokon ka (sai ya fadi bukatar sa), sai manzon Allah s.a.w yacema sahabban sa: kunsan dame yayi addu'a? sai sukace Allah da manzon sa ne kadai suka sani, sai yace: na rantse da wanda raina ke hannun sa, hakika ya roki Allah da sunan sa me girma, wanda idan aka roki shi dashi yana amsawa, kuma idan aka tambaye shi dashi yana bayarwa"."[166]

  1. Ya ksance yanayin sa alokacin addu'ar yana me Kankan dakai da tsoro, Allah madaukaki yace: " da Zakariyya a lokacin da ya kira Ubangijin sa cewa ya Ubangiji kada ka barni ni kadai kuma kaine mafi alherin masu gado (89) sai muka amsa masa kuma muka bashi Yahaya sannan kuma muka gyara masa matar sa, lallai sun kasance suna rigegeniya wurin alheri kuma suna kiran mu suna masu kwadayi da tsoro; kuma sun kasance masu tsoro ne a game damu (90)"[167]
  2. Rashin debe tsammani dajin cewa addu'ar ta dade ba'a amsa ba, an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " ana amsama dayan ku addu'ar sa matukar beyi gaggawa ba, yana cewa: nayi addu'a amma ba'a amsa mani ba."[168]
  3. Ya daina wuce gona da iri cikin addu'ar sa, an karbo daga Ibn Sa'ad dan Abi Wakkas Allah ya kara masa yarda yace: " babana yajini ina cewa: ya Allah ina rokon ka aljanna da ni'imar ta da kayan dadinta kada da kaza, kuma ina neman tsarin ka daga wuta da sarkokin ta da kacocin ta kaza da kaza. Sai yace: ya kai dana lallai naji manzon Allah s.a.w yana cewa za'a samu wasu mutane suna wuce gona da iri cikin addu'a, kashedinka ka zama cikin su, lallai idan an baka aljanna za'a baka ita ne da abunda ke cikinta na alheri, kuma idan an kiyaye ka daga wuta an kiyaye ka ne daga gareta da abunda ke cikinta na sharri."[169]
  4. Kada ya kasance a cikin addu'ar sa akwai sabo ko kuma yanke zumunci, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " babu wani mutum da zai roki Allah da wata bukata wacce babu sabo a cikinta ko kuma yanke zumunci face anbashi daya daga cikin abu uku: kodai a gaggauta bashi abunda ya roka, ko kuma ayi mashi tanadin alheri irinta, ko kuma a kawar masa da wani sharri irinta, sai sukace: ya manzon Allah, kenan zamu yawaita, sai yayi: Allah yafi yafi haka yawa."[170]
  5. Daidaitan lokuta da yanayi masu dajara kamar ranar arfa, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " mafi alherin addu'a itace addu'ar ranan arfa, kuma mafi alherin abunda na fadi nida annabawan da suka gabace ni shine: babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, mulki da godiya nashi ne kuma shi me iko ne kan komai"[171]
  • Da ranar jumma'a saboda hadisin Abu Huraira Allah ya kara masa yarda: " lallai manzon Allah s.a.w ya ambaci ranar jumma'a, sai yace: a cikinta akwai wani sa'a, musulmi bazai dace ba da ita, yana salla yana rokon Allah madaukaki wani abu ba face yabashi. Sai yayi nuni da hannun sa yana takaitata."[172]
  • Da watan Ramadan, sabod afadin manzon Allah s.a.w: " idan watan Ramadan ya shiga ana bude kofofin sama, kuma a rufe kofofin jahannama, kuma a daure aljanu."[173]

Addu'ar sa ta kasance a tsakiyan azumin sa, saboda hadisin Abu huraira Allah ya kara masa yarda manzon Allah s.a.w yace: " mutum uku ba'a mayar da addu'ar su, shugaba me adalci, da me azumi a yayin bude bakin sa da addu'ar wanda aka zalumta ana sanya ta akan gazigizai sannan a bude mat kofofin sammai sai ubangiji yace: da buwata sai na taimake ka koda kuwa bayan wani lokaci ne."[174]

  • Da ukun karshe na dare, da bayan salloli na farilla, saboda hadisin Abi Umamata: " ance ya manzon Allah wace addu'a ce akafi amsa? Sai yace: wacce akayita a tsakiyan daren karshe, da bayan salloli na farilla."[175]

An karbo daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w yace: " Allah yana saukowa cikin ko wace dare zuwa saman duniya, a lokacin da ya rage saura ukun karshe na dare, yana cewa: wanene zai kirani na amsa mashi, wanene zai tambaye ni nabashi, wanene zai nemi gafarata na gafarta mashi."[176]

  • Da kuma lokacin sujjada, an karbo daga dan Abbas Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya daga labulen kofar dakin sa a lokacin mutane sunyi sahu a bayan Abubakar sai yace: yaku mutane hakika ba abunda yarage cikin bisharori na annabta face mafarki na gaskiya, musulmi zai ganta cikin mafarkin sa ko kuma ko kuma wani yaganin mai, lallai an hanani karanta alkur'ani a cikin ruku'u da sujjada. A cikin ruku'u ka girmama Ubangijin ka, sannan acikin sujjada kayi kokarin yin addu'a domin wuri ne na amsa maku addu'ar ku."[177]
  • Da lokacin saukar ruwan sama, saboda abunda aka rawaito daga Sahal dan Sa'ad As sa'idi cewa manzon Allah s.a.w yace: " addu'a guda byu ba'a mayar dasu: addu'a a yayin kirin sallah ko kuma bayan kiran sallah, da lokacin saukan ruwan sama."[178]
  1. Ya maimaita addu'a sau uku, saboda hadisin Abdu Allahi dan Mas'ud Allah ya kara masa yarda: " manzon Allah s.a.w ya kasance yana burge shi yin addu'a sau uku sannan yana istigfari sau uku."[179]
  2. Yayi tawassuli ga Allah cikin addu'ar sa da ayyukan sa na kwarai, an karbo daga Abdu Allahi dan umar Allah ya kara masu yarda yace: naji manzon Allah s.a.w yana cewa: " wasu mutum uku cikin mutanen da suka gabace ku sun fita tafiya har sai da suka sauka a wurin bacci a cikin wani kogo sai suka shiga, sai wani dutse ya rufe bakin kogon, sai sukace ma junan su: lallai babu abunda zai tsiratar damu cikin wannan kogo face mu roki Allah da ayyukan mu na kwarai, sai dayan su yace: ya Allah na ksance inada iyaye guda biyu tsofaffi, na kasance bana gabatar da wani cikin iyalai na ko dukiya ta a kansu wurin shayarwa dasu, sia na fita neman wani abu wata rana, ban dawo gida ba har sai da sukayi bacci, sai ta tatsar masu nonon dabbobin da nake shayar dasu dashi naje masu dashi sai na tarar dasu sunyi bacci, sai na kyamaci ya gabatar da iyalai na da dukiya akan su, sai na zauna da wannan koko a hannu na ina jiran su har sai da suka farka da sauba, sai suka tashi sukasha wannan nono, ya Allah idan nayi wannan aiki ne saboda neman yardan k aka yaye mana abunda muke ciki na wannan kogo, sai wannan dutse ya bude kadan ta yadda babu wanda zai iya fita. Sai manzon Allah s.a.w yace: sai dayan su shi kuma yace: ya Allah ya kasance inada wata yarinyar baffata wacce nafi son ta cikin mutane baki daya, sai na nemi yin lalata da ita sai taki bani goyon baya, har zuwa lokacin da annoba na fari ya saukan masu sai gashi tazo wuri na tana neman taimako sai nabata dinari dari da ashirin akan ta bani dama nayi lalata da ita sai ta yarda har sai da nazo yin amfani da ita sai tacemun: kada ka halatta zuben da banaka ba sai da hakkin sa nanda nan sai na shiga taitayi nan a kyaleta alhali ina matukar kaunan ta sannan na bar mata zinarin dana bata, ya Allah idan nayi wannan aiki ne domin neman yardan k aka yayey mana halin da muke cikin sa awannan kogo, sai wannan dutse ya bude amma babu wanda zai iya fita a cikin sa. sai manzon Allah s.a.w yace: sai na ukun su shima yace: ya Allah nayi hayan wasu ma'aikata sai nabiya su hakkin su sai mutum daya a acikin su ya barmun kudin ya tafi, sai ya jujjuyata na habaka ta nayi kasuwanci da ita hat tayi yawa, sai gashi yazo mun wata rana yacemun: ya bawan Allah bani hakki nan a aikin danayi maka na barshi agunka. Sai nace mashi dukkanin abunda kake gani anan kudin ka, na tarin rakuma da shanu da tumakai da bayi. Sai yace: ya bawan Allah kada kamun isgilanci mana. Sai nace: ba isgilanci nake maka ba, ka kwashe su duka naka ne sai ya kwashe su be bar masa komai ba, ya Allah idan na aikata hakan ne dan neman yardan ka ka yaye mana halin da muke cikinsa a wannan kogo. Sai wannan dutse ya bude baki dayan sa suka fita suka tafi."[180]
  3. Yayi himma cikin addu'ar sa ya kuma yima Allah magiya cikin abunda yake bukata da kuma jin dadin kasancewar sa a gaban Allah, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " idan zaku roki Allah ko kuyi azama cikin addu'ar ku, kada dayan ku yace: ya Allah idan kaso ka bani, domin Allah ba'ayi masa tilas."[181]
  4. Ya kasance zuciyar sa tananan kuma yana sakankancewa da amsa masa addu'ar sa, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " zuciyoyi kafofi ne na gudanan jini wasun su sunfi wasu kafa, idan zaku roki Allah madaukaki yaku mutane, ku roke shi kuna masu sakankancewa da amsa maku, domin Allah baya amsama bawa addu'ar sa yana da zuciya rafkananniya."[182]
  5. Kwadayi akan addu'ar ya kasanc ecikin abunda alkur'ani yazo dashi ko kuma a bunda ya inganta daga manzon Allah s.a.w, an karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace: " manzon Allah s.a.w ya kasance yanason kalmomi gajeru wanda suka kunshi komai na addu'a sannan kuma yana barin wanda basu ba."[183]

Kuma be dace ba wani lafi da sabo da bawa yayi ya hanashi yin addu'a, domin kuwa shedan – tsinuwar Allah ya tabbata a gareshi – wanda shine mafi sharrin halittu, ya roki Ubangijin sa, Allah madaukaki yace yana bada labari akan Iblis: " yace ya Ubangijina ka dakatamun zuwa ranann alkiyama (36) sai yace kana cikin wanda aka dakata mawa (37) har zuwa ni wuni na lokaci sananne (38)"[184]

An karbo daga abu Huraira Allah ya kara masa yarda daga manzon Allah s.a.w, cikin abunda yake labartowa daga Ubangijin sa madaukaki yace: " bawa yayi zunubi sai yace: ya Allah! Ka gafartamun zunubi na. sai madaukaki yace: " bawana yayi zunubi kuma yasan yana da Ubanguji me gafarta zunubi kuma yanayin ukuba kana zunubi". Sa'annan ya kara dawowa ya aikata zunubi, sai yace: ya Ubangiji! Ka gafartamun zunubi na, sai madaukaki yace: " bawana yayi zunubi kuma yasan yana da Ubanguji me gafarta zunubi kuma yanayin ukuba kana zunubi". Sa'annan ya kara dawowa ya aikata zunubi, sai yace: ya Ubangiji! Ka gafartamun zunubi na, sai madaukaki yace: " bawana yayi zunubi kuma yasan yana da Ubanguji me gafarta zunubi kuma yanayin ukuba kana zunubi, ka aikata abunda kaso hakika na gafarta maka"."[185]

 

 

 

Bangarori na addu'o'in alkur'ani:

  1. " رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلْنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِ ۖ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا ۚ أَنتَ مَوْلَانَا فَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ (286) "[186]

" Rabbana la tu'akhizna innasina au a'akha'ana, Rabbana wala tahmil alaina isran kama hamaltahu ala allazina min kabalina, Rabbana wala tuhammilna mala taqata lana bihi, wa'afu anna wagfir lana warhamna Anta maulana fansurna ala alkaumi ilkafirin (286)"

" ya Allah kada ka kamamu da abunda muka aikata a halin mantuwa ko kuma bisa kuskure, ya Ubangijin mu kada ka daura mana nauyi kamar yadda ka daurama wanda suka gabace mu, ya Ubangijin mu kada ka daura mana abunda ya wuce ikon mu, ka yafe mana kuma ka gafarta mana kayi mana rahama, kaine majibincin al'amuran mu kuma ka taimake mu akan mutane kafirai (286)". suratul bakara ayata 286.

 

٢- " رَبَّنَا لَا تُزِغْ قُلُوبَنَا بَعْدَ إِذْ هَدَيْتَنَا وَهَبْ لَنَا مِن لَّدُنكَ رَحْمَةً ۚ إِنَّكَ أَنتَ الْوَهَّابُ (8) "[187]

" Rabbana la tuzig kulubana ba'ada iz hadaitana wa hab lana min Ladunka rahmatan Innaka Anta Al-Wahab (8)"

" ya Ubangijin mu kada ka fatar da zukatan mu bayan ka shiryar damu kuma ka bamu rahama daga wurin ka, lallai kai me yawan kyauta ne (8)". suratu al Imran ayata 187.

٣- " رَبَّنَا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرْ عَنَّا سَيِّئَاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ الْأَبْرَارِ (193) "[188]

" Rabbana fagfir lana zunubana wa kaffir anna sayyi'atina watawaffana ma'al abrar (193)"

" ya Ubangijin mu ka gafarta mana zunuban mu kuma ka kankare mana laifukan mu ka kuma kashe mu tare da masu biyayya (193)" suratu al Imran ayata 193.

٤- " رَبَّنَا لَا تَجْعَلْنَا فِتْنَةً لِّلْقَوْمِ الظَّالِمِينَ (85) وَنَجِّنَا بِرَحْمَتِكَ مِنَ الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ (86) "[189]

" Rabbana la taja'alna fitnatan lilkaumi iz-zalimin (85) wa najjina birahamatika mina alkaumi ilkafirin (86)"

" ya Ubangijin mu kada ka sanya mu fitina ga mutane azzalumai (85) kuma ka tsiratar damu daga mutane kafirai (86)". suratu Yunus ayata 85-86.

٥- " رَبَّنَا لَا تَجْعَلْنَا مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ (47) "[190]

" Rabbana la taja'alna ma'a alkaumi iz-zalimin (47)"

" ya Ubangijin mu kada ka sanya mu tare da mutane azzalumai (47)". suratul a'araf ayata 47

٦- " وَقُل رَّبِّ أَدْخِلْنِي مُدْخَلَ صِدْقٍ وَأَخْرِجْنِي مُخْرَجَ صِدْقٍ وَاجْعَل لِّي مِن لَّدُنكَ سُلْطَانًا نَّصِيرًا (80) "[191]

" wa kul Rabbi adkhilni mudkhala sidkin wa akhrijni mukhraja sidkin waj'al li min Ladunka sultanan nasiraa (80)"

" kuma kace ya Ubangijina ka shigar dani mashiga na gaskiya kuma ka fitar dani mafita ta gaskiya kuma ka karfi da iko me taimako (80)". suratul isra'i ayata 80.

٧- " رَبَّنَا أَفْرِغْ عَلَيْنَا صَبْرًا وَتَوَفَّنَا مُسْلِمِينَ (126) "[192]

" Rabbana afrig alaina sabaran watawaffana muslimin (126)"

" ya Ubangijin mu ka koro mana hakuri kuma ka kashe mu muna musulmai (126)". suratul a'araf ayata 126

٨- " رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي (25) وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي (26) "[193]

" Rabbi ishrah li sadri (25) wa yassir li amri (26)"

" ya Ubangiji ka budemun kirjina (25) kuma ka saukake mun al'amurana (26)". suratu daha

٩- " رَبِّ اجْعَلْنِي مُقِيمَ الصَّلَاةِ وَمِن ذُرِّيَّتِي ۚ رَبَّنَا وَتَقَبَّلْ دُعَاءِ (40) رَبَّنَا اغْفِرْ لِي وَلِوَالِدَيَّ وَلِلْمُؤْمِنِينَ يَوْمَ يَقُومُ الْحِسَابُ (41) " [194]

" Rabbi ij‘alni mukima as-salati wamin zurriyyati, Rabbana watakabbal du'a’ (40) Rabbana igfir li wa liwalidayya wa lilmu'minina yauma yakumu alhisaab (40)"

" ya Ubangiji ka sanya na zama me tsayar da salla da zuriyata, ya Ubangijin mu ka amsa (mana) addu'a (40) ya Ubangijin mu ka gafarta mun da iyayena da muminai ranar da hisabi zai tsaya (41)". Suratu Ibrahim

١٠- " رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ (97) وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن يَحْضُرُونِ (98) "[195]

" Rabbi a'uzu Bika min hamazati ish-shayadin (97) wa a'uzu Bika Rabbi an yahdurun"

" ya Ubangiji ina neman tsarin ka daga fisgar shedanu (97) kuma ina neman tsarin ka ubangiji da su zo mun (98)". Suratul muminun

١١- " رَّبِّ اغْفِرْ وَارْحَمْ وَأَنتَ خَيْرُ الرَّاحِمِينَ (118) "[196]

" Rabbi igfir warham wa Anta Khairu Ar-Rahimin (118)"

" ya Ubangiji kayi gafara kuma kayi rahama kaine mafi alherin masu rahama (118)". Suratul muminun

١٢- " رَبَّنَا اغْفِرْ لِي وَلِوَالِدَيَّ وَلِلْمُؤْمِنِينَ يَوْمَ يَقُومُ الْحِسَابُ (41) "[197]

" Rabbana igfir li waliwalidayya walilmu’minina yauma ya kumu alhisaab"

" ya Ubangijin mu ka gafartamun da iyaye na da muminai ranar da hisabi zai tsaya (41)". Suratu Ibrahim

١٣- " رَبَّنَا آتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحْمَةً وَهَيِّئْ لَنَا مِنْ أَمْرِنَا رَشَدًا (10) "[198]

" Rabbana aatina min Ladunka rahmatan wa hayyi' lana min amrina rashadaa (10)"

" ya Ubangijin mu ka bamu rahama daga gareka kuma ka tanadar mana shiriya cikin al'amarin mu (10)". Suratul kahfi

١٤- " رَبَّنَا اصْرِفْ عَنَّا عَذَابَ جَهَنَّمَ ۖ إِنَّ عَذَابَهَا كَانَ غَرَامًا (65) إِنَّهَا سَاءَتْ مُسْتَقَرًّا وَمُقَامًا (66) "[199]

" Rabbana isrif anna azaba Jahannam, inna azabaha kana garama (65) innaha sa’at mustakarra wa mukama (66)"

" ya Ubangijin mu ka kawar da azabar jahannama akammu, lallai azabarta ya kasance lizimtacciya a koda yaushe (65) lallai ta kasance matabbata da wurin tsayawa wacce ta munana (66)". Suratul furkan

١٥- " رَبَّنَا هَبْ لَنَا مِنْ أَزْوَاجِنَا وَذُرِّيَّاتِنَا قُرَّةَ أَعْيُنٍ وَاجْعَلْنَا لِلْمُتَّقِينَ إِمَامًا (74) "[200]

" Rabbana hab lana min azwajina wa zurriyyatina kurrata a‘yunin waj‘alna lilmuttakina imamaa (74)"

" ya Ubangijin mu ka bamu daga cikin matammu da zuriyarmu masu sanyaya ido kuma kasanya mu jagorori ga masu takawa (74)". Suratul furkan

 

١٦- " رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِّلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ (10) "[201]

" Rabbana igfir lana wali-ikhwanina allazina sabakuna bilimani wala taj'al fi kulubina gillan lillazina amanu Rabbana Innaka Ra'uufun Raheem (10)"

" ya Ubangijin mu ka gafarta mana da yan uwan mu wanda suka rigamu da imani kuma kada kasanya wani kyama da kiyayya a zuciyar mu ga wanda sukayi imani ya Ubangijin mu lallai kai me tausayi ne me rahama (10)". Suratul hashri

١٧- " رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الْآخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ (201) "[202]

" Rabbana atina fiddunya hasanatan wa fi al-akhirati hasanatan wakina azaba an-naar (201)"

" ya Ubangijin mu ka bamu me kyau a duniya da me kyau a lahira kuma ki tsiratar damu azabar wuta (201)". Suratul bakara

 

 

 

Bangarori na addu'o'in Annabi:

  1. " Ya Allah ina rokonka shiriya da jin tsoronkam da kamewa da wadata."[203]
  2. " Ya Allah ina neman tsarinka daga azabar kabari, kuma in anemna tsarin ka daga fitinar dujal, kuma ina neman tsarinka daga fitinar rayuwa da fitinar mutuwa, ya Allah ina neman tsarinka daga ababen laifuka da bakin cikin addini."[204]
  3. " Ya Allah ina neman tsarinka daga kasawa da kasala, da tsoro da tsananin tsufa, kuma ina neman tsarin ka daga azabar kabari, kuma ina neman tsarin ka daga fitinar rayuwa da mutuwa."[205]
  4. " Ya Allah! Ka gafartamun kura kurai na da jahilci na, da almubazaranci cikin al'amurana, da abunda kafini sani akan sa daga gareni. Ya Allah! Ka gafartamun abunda na aikata da kokari na da kuma wasa, da kuskure na da gangan dina. Dukkanin su daga gare ni ne. Ya Allah! Ka gafartamun abunda ya aikata da wand azan aikata, da abunda kana aikata a asurce da abunda na aikata a bayyane, da abunda ka fini sani game dani, kaine na farko kuma kaine na karshe, kuma kai me iko ne akan dukkan komai."[206]
  5. " Ya Allah ina neman tsarinka daga gushewar ni'imar ka, da canzawar lafiyar ka, da bala'in ka da take zuwa a mamayem da dukkanin fushin ka."[207]
  6. " Ya Allah ina neman tsarinka daga gazawa da kasala, da tsoro da rowa, da tsananin tsufa da azabar kabari. Ya Allah! Kaba rain a tsoron ka. Kuma ka tsarkake ta kaine mafi alherin masu tsarkake rai, kaine majibincin ta da iko da ita. Ya Allah! Ina neman tsarin ka daga ilimin da baya amfanarwa, da zuciya bushashiya, da kuma rai da bata koshi, da addu'ar da ba'a amsawa"[208]
  7. " Ya Allah ka gyaramun addini na wanda shine kariya na. kuma ka gyaramun duniya na wanda aciki rayuwa ta take. Kuma ka gyaramun lahirata wacce acan makoma ta take. Kuma kasanya rayuwa kari ce a gareni cikin dukkanin alheri. Kuma kasanya mutuwa hutu ce a gareni daga dukkanin sharri."[209]
  8. " Ya Allah ina neman tsarinka daga kasala da tsananin tsufa daukan asara da dukkanin aikin saba maka, ya Allah ina neman tsarin ka daga azabar wuta da fitinar wuta da fitinar kabari (tambayar mala'ikun kabari) da azabar kabari, da sharrin fitinar arziki da sharrin fitinar talauci da sharrin fitinar masihul dajjal, ya Allah ka wanke mun zunubai na da ruwan kankara da sanyi, kuma ka wanke zuciya ta daga zunubai na kamar yadda ake wanke tufafi fari daga datti, kuma ka nisantar dani daga zunubai na kamar yadda ka nisantar da tsakanin gabas da yamma."[210]
  9. " Ya Allah ina neman tsarin da yardan ka wacce fushin zai hau kaina da ita, da kuma ina neman kariyan ka daga kamuwar ka na cikin ukubar ka, kuma ina neman tsarin ka daga kaina, bazan iya cika maka godiya da yabonka ba akan hakikanin ni'imomin ka da falalar ka akaina, kai kamar yadda kayi godiya da yabon kanka ne kawai."[211]
  10. " Ya Allah ka gafartamun abunda na aikata da wand azan aikata da wanda nayi a asirce da wanda nayi a bayyane, da abunda kafi sani akaina sama dani, ya Allah ka azurtani da yi maka biyayya wanda zayyi shinge tsakanina da saba maka, kuma ka azurtani da tsoron ka wanda take son rahamar ka dashi, kuma ka azurta ni da yakini wanda kake wulakanta musifu da bala'i dashi, kuma kamun albarka cikin jina da gani na, kuma kasanya su zama gado a gareni, ya Allah ka sakamun daga duk wanda ya zalumce ni, ka taimake ni akan wanda yayi adawa dani, kuma kada ka sanya duniya ta zama babban damuwa ta, ko kuma makura da hadafin aiki na, ya Allah kada ka daura mun wanda bazai mun rahama ba."[212]
  11. " Ya Allah ka kiyaye ni da musulunci a yanayin tsayuwa ta, kuma ka kiyaye ni da musulunci a yanayin zama ta, kuma ka kiyaye ni da musulunci a yanayin kwanciya ta, kuma kada kasanya makiyi ko me hassada yin murna akai na, ya Allah ina rokon ka daga dukkanin alherin wanda taskar sa ke hannun ka, kuma ina neman tsarin ka daga dukkanin sharri wanda taskar ta ke hannun ka."[213]
  12. " Ya Allah ina neman tsarinka daga munanan dabi'u da ayyuka da son zuciya."[214]
  13. " Ya Allah da ilimin ka na gaibu da ikonka akan halittu, ka rayani matukar rayuwa alheri ce a gareni, kuma ka dauki raina matukar mutuwa itace alheri a gareni, ya Allah ina rokon k tsoron ka cikin gaibu da shahada, da Kalmar adalci da gaskiya a lokacin fushi da lokacin yarda, kuma ina rokon ka daidaito cikin talauci da wadata, kuma ina rokon ka ni'imar da baya karewa, da masu dauke kewan ido wanda basa yankewa, kuma ina rokon ka yarda bayan hukuncin ka, kuma ina rokon ka rayuwa me tsanyi bayan mutuwa, kuma ina rokon ka dadin kallo zuwa ga Fuskarka, kuma ina rokon ka shauki na haduwa dakai ba tare da wata cutarwa ba me tsanani ko fitina me halakarwa, ya Allah ka kawatani da kawar imani, kuma ka sanyani cikin shiryayyu masu shiryarwa."[215]
  14. " Ya Allah ina neman tsarinka daga gazawa da kasala da rowa da tsananin tsufa, da bushewar zuciya da gafala da kaskanci da nakasa kuma ina neman tsarin ka daga talauci da kafurci da shirka da yabo da riya kuma ina neman tsarin ka daga kurmancewa da bebancewa da hauka da kora da lalacewar fata da mummunan rashin lafiya."[216]
  15. " Ya Allah ina neman tsarinka daga yunwa, domin kuwa tsananin me sanya bin gado, kuma ina neman tsarin ka daga ha'inci domin ita mayafi ce abun tur."[217]
  16. " Ya me jujjuya zukata, ka tabbatar da zuciyata akan tafarkin addinin ka."[218]
  17. " Ya Ubangiji ka taimake ni, kada kayi taimako akaina, ka bani nasara, kada ka bada nasara akaina, ka saukar da bala'inka akan duk wanda ya nufeni da sharri ta hanyar da baya zato kuma kada k aka bayar da hanya akaina, ka shiryar dani kuma ka saukakemun shiriya, ka taimakeni akan wanda ya zalumce ni, ya uabngiji ka sanyani na zama me godiya a gareka, da me ambatonka, da yawan bukata zuwa gareka da addu'a da kuka, me yawan maka biyayya, da yawan tsoron ka da Kankan dakai a gareka, me yawan komawa gareka da rokonka cikin kuka, me yawan komawa gareka daga zunubai da kura kurai, ya Ubangiji ka amshi tuba na, ka wanke zunubi da sabo na, kuma ka amsa addu'ata, kuma ka tabbatar da hujjata, kuma ka shiryar da zuciyata, ka datar da harshe na, ka raba zuciya na da hassada da kyashi da ha'inci."[219]
  18. " Ya Allah ka gafarta mani, kamun rahama, ka shiryar dani, ka bani lafiya, ka bani arziki."[220]
  19. " Ya Allah ina rokon ka alheri dukkannin san a kusa dana nesa abunda nasani da wanda bansani ba, kuma ina neman tsarin ka daga shirka baki dayan sa na kusa dana nesa wanda na sani da wanda bansani ba, kuma ina rokon ka aljanna da dukkanin abunda yake kusantarwa gareta na magana ko aiki, kuma ina neman tsarin ka daga wuta da abunda yake kusantarwa gareta na magana ko aiki, kuma ina rokon ka daga abunda Muhammad s.a.w ya tambaye ka, kuma ina neman tsarin ka daga abunda Muhammad s.a.w ya nemi tsarin ka dashi, kuma abunda ka hukuntamun na hukunci ka sanya karshe na akan sa shiriya."[221]
  20. " Ya Allah lallai kai me afuwa ne kanason afuwa kamun afuwa."[222]
  21. " Ya Allah ka taimake ni akan ambaton ka da gode maka da kuma kyautata maka bauta."[223]
  22. " Ya Allah ina rokon ka aikata alherai, da barin mummunan ayyuka, dason miskinai, kuma ka gafartamun damun rahama, kuma idan ka nufi fitina ga mutane ka dauki rain aba tare da na fitunu ba, kuma ina rokon ka sonka dason me sonka, dason aikin da yake kusantarwa zuwa ga sonka."[224]
  23. " Ya Allah ina neman tsarin ka daga mummunan kaddara da kuma tabewa da gajiya ya sameni a duniya da lahira da kuma murnan makiya akaina da kuma bala'i me tsanani."[225]
  24. " Ya Allah lallai na zalumci kaina dayawa, kuma babu wani me gafarta zunubi face kai, ka gafartamun gafara daga gareka, kuma kamun rahama, lallai kai me yawan gafara ne kuma me rahama."[226]
  25. " Ya Allah ina neman tsarinka daga sharrin jina, da sharrin gani na, da sharrin harshen a, da sharrin zuciya na, da sharrin maniyyi na."[227]
  26. " Ya Allah ina neman tsarinka daga talauci, ya karanci cikin kofofin alherai da hakuri da mataimaka da dukiya, da kaskanci, kuma ina neman tsrain ka da kada nayi zalumci ko kuma a zalumce ni."[228]
  27. " Ya Allah ina rokon ka da rahamar ka wacce ta mamaye komai da ka gafartamun zunubai na."[229]
  28. " … Ya Allah! Kaine me mulki babu abun bauta sai kai, kaine Ubangiji na kuma ni bawa ne a gareka, na zalumci kaina kuma na yardan ma kaina da aikata zunubai na, ka gafartamun zunubaina baki dayan su, domin babu me gafarta zunubai sai kai, kuma ka shiryar dani zuwa ga mafi kyawun dabi'u, wanda babu me shiryarwa zuwa ga mafiya kyawun sai kai, kuma ka kawar mun da munanan su, babu me kawarmun da munanan su sai kai…"[230]
  29. " Ya Allah ya isar dani da halal dinka game da haram dinka, kuma ka wadatar dani da falalarka daga wani wanda bakai ba."[231]
  30. " Ya Allah ka raba mana daga cikin tsoron ka wanda zai shamakance mu tsakanin mu da sabo, da kuma biyayyar ka wanda zai kaimu zuwa ga aljannarka, da kuma yakini wanda zai kankantar mana da musifun duniya, kuma ka jiyar damu dadi da jin mu da ganin mu da karfin mu matukar muna raye, kuma kasanya mana masu gadar mu, kuma ka dau mana fansa akan wanda ya zalumce mu, ka taimake mu akan wanda yake gaba damu, kuma kada ka sanya musibarmu cikin duniya, kuma kada kasanya duniya ta zama babbar burin mu ko kuma matuka na ilimin mu, kuma kada ka daura mana wanda bazai ji tausayin mu ba da rahama."[232]
  31. " Ya Allah ka shiryar dani (zuwa hanyar mikakkiya) kuma tabbatar dani (akan tsayawa akan hanya mikakkiyaa)[233]
  32. " Ya Allah ka shiryar dani cikin wand aka shiryar dasu, kuma ka bani waraka cikin wand aka warkar dasu, kuma ka jibinci al'amurana cikin wand aka jibinci al'amuran su, kuma kamun albarka cikin abunda ka bayar, kuma ki tsare ni daga sharrin abunda ka kaddara da hukuntawa (hakan ba yana nufin anjigina sharri bane zuwa ga Allah madaukaki, a'a hakan yana daga cikin babin jingina sharri ne zuwa ga abunda suka kunsa na talauci da rashin lafiya da makamantan su, abunda Allah ya kaddara baki dayan su alheri ne, kuma dukkanin al'amura ta bangaren jingina su zuwa ga Allah alheri ne, ba'a jin gina sharri zuwa gareshi; domin cikar hikimar sa da kuma girman rahamar sa), lallai kaine kake hukuntawa kuma babu me hukunci akanka, kuma ba duk wand aka jibinci al'amuran sa baya kaskanta, albarkunka ya mamaye halittunka baki daya ya Ubangijin mu kuma ka tsarkaka daga dukkanin abunda bai dace da kamalarka ba da girman ka."[234]
  33. " Ya Allah gareka godiya take cikin fadin sama da kasa, da cikin abunda kaso na wani abu bayan haka, Ya Allah ka tsarkake ni da kankara da sanyi da ruwa me sanyi, Ya Allah ka tsarkake ni daga zunubai na da kura kuraina kamar yadda ake wanke farara tufafi daga datti."[235]
  34. " Ya Allah ka gafartamun zunubai na baki dayan sa, kananan sa da manyan sa, na farkon sa dana karshen san a bayyane dana boye."[236]
  35. " Ya Allah ina rokon ka tabbata cikin al'amari, da azama da himma akan shiriya, kuma ina rokon ka godema ni'imar ka da kyautata bautar ka, kuma ina rokon ka daga alherin da kasani (ya kunshi dukkanin alheri wanda mutum ya sani da wanda be sani ba), kuma ina neman gafarar ka daga dukkanin zunubai na wanda ka sansu, lallai kai masani ne na gaibu."[237]

 

 

 

Addu'o'i na safe da maraice

Daga cikin abubuwan da suke jawo yardan Allah madaukaki wanda suke tunkude sharri da musifu shine kiyaye abunda yazo ya kuma tabbata cikin addu'o'in safe da maraice, saboda falalar wannan lokuta guda biyu ambaton su yazo cikin alkur'ani me girma cikin ayoyi mabanbanta da salo masu yawa domin su zama zaburarwa ga masu himma kololuwa dan fa'idanta da abunda ke cikin su na alheri da albarka, Allah madaukaki yace: " kuma kayi tasbihi na godiya ga Ubangijin ka safiya da maraice da safiya (55)"[238]

Allah madaukaki ya kara cewa: " kuma kayi tasbihi na godiya ga Ubangijin ka gabanin fitowar rana da gabanin faduwar ta (39)"[239]

Kuma Allah madaukaki ya kara cewa: " yaku wanda sukayi imani ku ambaci Allah Ambato me yawa (41) kuma kuyi masa tasbihi safiya da maraice (42)"[240]

An kebance wannan lokuta ne da addu'a ga kuma wanda ya kiyaye su dayin imani da yakini dashi zai kasance da izinin Allah kariya agareshi kuma zai kasance masa amatsanin guziji wanda zai rka neman agaji dashi a cikin ranar sa da kuma samun karfi dashi cikin rayuwan sa, kuma hanya ne wacce take kaiwa zuwa ga yardan Allah, ya wajaba ga ko wani musulmi ya kiyaye shi kuma ya sanya shi cikin ayyukan sa masu muhimmanci na farko farko, kuma lokacin fara wannan addu'o'in na safe shine daga fitowar alfijir har zuwa fitowar rana, lokacin addu'ar yamma kuma shine daga bayan sallar la'asar har zuwa faduwar rana.

 

Wasu daga cikin addu'o'i na safiya da maraice:

  1. Manzon Allah s.a.w yace: " idan dayan ku ya wayi gari to yace: " mun wayi gari kuma mulki ya wayi gari ga Allah Ubangijin talikai, Ya Allah ina rokon ka alherin wannan rana, fatahin sa da taimakon sa da hasken sa da albarkan sa da shiriyar sa, kuma ina neman tsarin ka daga sharrin dake cikin sa da sharrin dake bayan sa" sa'annna idan ya yammaci gari to ya fadi irin haka."[241]
  2. An karbo daga Abdu Allahi dan Mas'ud yace: " Annabin Allah s.a.w ya kasance idan ya yammaci gari yana cewa: " mun yammaci gari kuma mulki ya yammaci gari ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abun bautawa sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya". Sai yace: naganci yana cewa a cikin su " mulki nashi ne kuma godiya nashi ne kuma shine me iko akan komai. Ya Ubangiji! Ina rokon ka alherin cikin wannan dare da alherin dake bayan sa. kuma ina neman tsarin ka daga sharrin wannan dare da sharrin dake bayan sa. ya Ubangiji! Ina neman tsarin ka daga kasala da mummunan tsufa. Ya Ubangiji! Ina neman tsarin ka daga azaba a cikin wuta da azaba a cikin kabari". Idan ya wayi gari sai ya fadi haka shima " mun wayi gari kuma mulki ya wayi gari ga Allah…."."[242]
  3. An karbo daga Usman dan Affan Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda yace a lokacin daya wayi gari: " da sunan Allah wanda babu abunda yake cutarwa tare da sunan sa cikin kasa ko sama kuma shi me ji ne kuma masani" sau uku, mamaya na bala'i bazata mamaye shi ba har sai ya yammaci gari idan kuma ya fadeta a lokacin daya yammaci gari mamayan bala'I bazata mamaye shi ba har sai ya wayi gari."[243]
  4. An karbo daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: " wani mutum yazo gun manzon Allah s.a.w sai yace: ya manzon Allah! Na hadu da tsanani na zafin harbin kunama wanda ya harbe ni jiya da daddare. Sai yace: da ace kace a lokacin daka yammaci gari: " ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abunda ya halitta", da bata cutar dakai ba."[244]
  5. An karbo daga Anas Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " wanda yace a lokacin daya wayi gari ko kuma yammaci gari: " ya Allah na wayi gari ina shedaka kuma ina sheda masu daukan al'arshin ka da mala'ikunka, da dukkanin halittun ka cewa kaine Allah wanda babu abun bautawa sai kai kuma lallai Muhammad bawan ka ne kuma manzon ka" Allah zai yanta daya bisa hudu na jikin sa daga wuta, wanda ya fadeta sau biyu Allah zai yanta rabin shi, wanda ya fadeta sau uku Allah zai yanta uku bisa hudun jikinsa, wanda ya fadeta sau hudu Allah zai yantashi daga wuta baki dayan jikin sa."[245]
  6. An karbo daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: manzon s.a.w yace: " duk wanda yace: " babu abun bauta sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, mulki da godiya nashi ne, kuma shine me iko kan komai", a cikin rana sau dari, zata kasance mai kamar yanta bayi goma, kuma a rubuta masa ayyukan lada dari, kuma a kankare masa zunubai dari, kuma zata kasance masa kariya daga shedan har sai ya yammaci gari, kuma babu wanda zaizo da aiki wanda yafi nashi sai mutumin da ya fadeta sama da nashi."[246]
  7. An karbo daga shaddad dan Aus Allah ya kara masa yarda manzon Allah s.a.w yace: " shugaban istigfari shine mutum yace: Ya Allah kaina Ubangiji na, ka halicce ni kuma ni bawan ka ne, kuma ina tsaye akan dokokin ka da alkawarin kamatukar iyawa na, ina neman tsarin ka daga sharrin abunda na aikata, ina ikirari agareka ga ni'imarka a gareni, kuma ina ikirari maka da zunubai n aka gafartamun, domin babu me gafarta zunubi sai kai", sai yace: duk wanda ya fade ta da safe yana me sakankancewa da ita, sai ya mutu gabanin ya yammaci gari, to yana cikin yan aljanna, kuma wanda ya fadeta da daddare yana me sakankancewa da ita, sai yam utu gabanin ya wayi gari, to yana cikin yan aljanna."[247]
  8. An karbo daga abu Huraira daga manzon Allah s.a.w ya kasance yana cewa idan ya wayi gari: " ya Allah gareka muka wayi gari, kuma gareka muka yammaci gari, muka gareka muka rayuwa, kuma gareka zamu mutu, kuma gareka zamu koma". Kuma idan ya yammaci gari sai yace: " ya Allah gareka muka yammaci gari, kuma gareka muka rayu, kuma gareka zamu mutu kuma gareka zamu koma"."[248]
  9. An karbo daga Mu'azu dan Abdu Allahi dan Khabib daga baban sa cewa yace: " mun fita cikin dare da duhu me tsanani muna neman manzon Allah s.a.w domin yayi mana salla, sai muka riske shi, sai yace: kunyi salla? Sai bance komai ba, sai yace: kayi karanta. Sai nayi shiru, sa'annan yace: ka karanta. Sai nayi shiru, sa'annan yace: ka karanta, sai nace: ya manzon Allah me zan karanta? Sai yace: ka karanta Kulhuwallahu da falaki da nasi a lokacin da ka yammaci gari da lokacin daka wayi gari sau uku sun isar maka akan dukkanin komai (watan zasu kare ka daga dukkanin sharri da mummunan abu)."[249]
  10. An karbo daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: " Abubakar yace: ya Manzon Allah! Ka fadamun wani abu wand azan rika fadi idan ya wayi gari da idan ya yammaci gari? Sai yace: kace: " ya Allah! Masanin gaibu da shahada! Wanda ya kirkiri sammai da kasa! Ubangijin komai da mamallakin sa! na shaida babu abun bautawa sai kai, ina neman tsarin ka daga sharrin kaina, da sharrin shedan da shirkan da yake kira zuwa gareshi", ka fadi idan ka wayi gari, da yammaci gari, da idan kaje kwanciya."[250]
  11. An karbo daga dan Umar Allah ya kara masu yarda yace: " manzon Allah s.a.w be kasance yana barin wannan addu'o'in ba lokacin daya yammaci gari da lokacin daya wayi gari: " ya Allah ina rokon ka afuwa a duniya da lahira, ya Allah ina rokonka gafara da yafiya da afuwa a a cikin addini na da duniya na da iyalai na da dukiya ta, ya Allah ka suturtamun al'aurata, kuma ka amintar daga dukkanin wani firgici da tsoro, ya Allah ka kiyaye ni ta gabana da bayana ta damana da haguna da samana, kuma ina neman tsari da girman ka da a kisfeni daga kasana"."[251]
  12. An karbo daga Abdurrahman dan Abi Bakarata yacema babanshi: " ya babana! Ina jinka a duk lokacin da ka wayi gari kana cewa: " ya Allah ya bana lafiya cikin jikina, ya Allah ka bani lafiya cikin jina, ya Allah ka bani lafiya cikin gani na, babu abun bautawa sai kai". Kana maimaitashi sau uku a lokacin da ka wayi gari, haka kuma sau uku a lokacin da ka yammaci gari! Sai yace: lallai naji manzon Allah s.a.w yana addu'a ne dasu, kuma inason koyi da sunnanr sa."[252]
  13. An karbo daga Anas dan malik yana cewa: " manzon Allah s.a.w yace ma Fadima: me zai hanaki jin abunda nayi maki wasiyya dashi? Kice idan kin wayi gari da lokacin da kika yammaci gari: " ya Rayayye ya Tsayayye da rahamar ka nake neman agaji, ka gyaramun al'amurana baki daya, kuma kada ka karbi da zuciyana koda na kwabtawan ido ne"."[253]
  14. An karbo daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda ya fadi a lokacin daya wayi gari da lokacin daya yammaci gari: " tsarki ya tabbata ga Allah da gode masa" sau dari, babu wanda zaizo ranan alkiyama da aikin daya fi nashi, sai dai wanda ya fadi irin abunda ya fadi ko kuma ya kara akan nashi."[254]
  15. An karbo daga Abi zarri Allah ya kara masa yarda manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda ya fadi abayan idar da sallar asuba, gabanin yayi magana: babu abun bauta sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, mulki da godiya nashi ne, yana rayawa yana kashewa kuma shine me iko akan komai sau goma, za'a rubuta mashi ladan aikin kwarai goma, kuma a kankare masa zunubai goma, kuma a daga darjar sa goma, kuma wannan ranar tashi zata kasance dukanta cikin kariya daga dukkanin wani mummunan abu, kuma za'a tsare shi daga shedan, kuma be dace ba da wani zunubi ya same shi cikin wannan rana sai dai shirka da Allah."[255]
  16. An karbo daga Abdu Allahi dan Gannam albayadi Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda ya fadi a lokacin daya wayi gari: " ya Allah abunda na wayi gari dashi na ni'ima ko kuma daya daga cikin halittanka daga gare ka ne kai kadai baka da abokin tarayya, godiya na kai tsaye naka ne haka kuma godiya akan wani abun alheri naka ne " to hakika yai godiyar san a wannan rana, wanda kuma yafadi irinta a lokacin daya yammaci gari ti hakika yayi godiyar sa na wannan dare."[256]

 

 

 

Addu'o'i na wasu halaye wanda mumini yake kare kansa da su

  1. Abunda ake fadi a yayin kwanciya bacci:
  • An karbo daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya wakiltani gadin zakkar Ramadan, sai wani yazo mun yana deban abinci da hannun sa, sai na kamashi nace: wallahi zai na kaika gun manzon Allah s.a.w, sai yacemun: ni mabukaci ne kuma inada iyalai kuma ina cikin tsananin bukata, sai yace: sai na sakeshi, sai na wayi gari sai manzon Allah s.a.w yace : " ya Abu huraira ya kayi da bakon ka na jiya?" sai nace: ya manzon Allah yamun kukan yana cikin tsananin bukata ne, ga iyalai sai naji tausayin san a sake shi, sai yace: " karya yake yi, kuma zai dawo" sai nasan cewa zai dawo, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " cewa lallai zai dawo". Sai nayi dakon jiran sa, sai gashi yazo yana deban abinci da hannun sa sai na kamashi nace: sai na kaika gun manzon Allah s.a.w, sai yacemun: ni mabukaci ne kuma inada iyalai kuma ina cikin tsananin bukata, sai yace: sai na sakeshi, sai na wayi gari sai manzon Allah s.a.w yace: " ya Abu huraira ya kayi da bakon ka na jiya?" sai nace: ya manzon Allah yamun kukan yana cikin tsananin bukata ne, ga iyalai sai naji tausayin san a sake shi, sai yace: " karya yake yi, kuma zai dawo". Sai nayi dakon jiran sa karo na uku, sai yazo yana deban abinci na kama shin ace sai nakaika gun manzon Allah s.a.w, wannan shine karo na uku na karshe kana cewa bazaka dawo ba, sai kuma ka dawo, sai yace: sakeni zan sanar dakai wasu kalmomi wanda Allah zai amfane ka da ita, sai nace menene ita? Sai yace: idan kaje yin kwaniya a wurin baccin ka, ka karanta Ayatul kursiyyu: {Allah babu abun bautawa sais hi rayayye kuma tsayayye}. Har sai ka karasa ayar, lallai bazaka gushe ba cikin kariyar Allah, kuma shedan bazai kusance k aba har sai ka wayi gari, sai na sake shi bayan na wayi gari, sai manzon Allah s.a.w yacemun: " ya abu huraira ya kayi da bakon ka na jiya?" sai ance ya manzon Allah, yace zai karantar dani wasu kalmomi wanda Allah zai amfanar dani da ita sai na sake shi, sai yace: "menene ita?". Sai nace: yacemun idan nace kwanciya, na karanta Ayatul kursiyyu daga farkonta zuwa karshen ta: {Allah babu abun bautawa sais hi rayayye kuma tsayayye}. Sai yacemun: bazan gushe ba cikin kariyar Allah kuma shedan bazai kusance nib a har sai ya wayi gari – sun kasance masu matukar son alheri- sai manzon Allah s.a.w yace" lallai yayi maka gaskiya amma dai makaryaci ne, kasan wanene kake magana dashi tsawon dare ukun ya abu huraira?". Sai nace: a'a, sai yace: " to shedan ne"."[257]
  • An karbo daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda manzon Allah s.a.w yace: " idan kayan ku yaje kwanciya ya kakkabe shinfidan sa da zanin sa, domin besan abunda yah au kai ba a bayan sa[258], sa'annan yace: da sunan ka ya Ubangiji na sanya jikina kuma da sunan ka zan daga shi, idan ka rike raina[259] ka mata rahama, idan kuma ka dawo da it aka kareta da abunda kake kare bayin ka salihai."[260]
  • An karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan yaje kwanciya a ko wani dare yana hada tafukan hannayen sa sa'anna yayi tufi a cikin su, sai ya karanta: {kulhuwallahu}, da {da falaki}, da {nasi} (watan yana karnta suratul ikhlas da falaki da nasi a cikin su), sa'annan ya shafe jikin sa dasu yana faraway da kansa da fuskan sa, da barin gaban san a jikin sa, yana aikata hakan sau uku."[261]
  • An karbo daga Huzaifa Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan yake kwanciya da daddare, yana daura hannun sa gishin sa sa'annan yace: " ya Allah da sunan nake mutuwa da rayuwa". Idan ya farka sai yace: " godiya ya tabbata ga Allah wanda ya rayani bayan ya kashe ni kuma gareshi makoma yake"."[262]
  • An karbo daga Abdu Allahi dan mas'ud Allah ya kara msa yarda yace manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda ya karanta ayoyin karshe na suratul bakara cikin dare sun isar masa (zai zasu kare shi daga sharri da mummunan abu)."[263]

 

  1. Abunda ake fadi a lokacin da mutum yaga abunda bayaso ko kuma abunda yakeso acikin baccin sa:
  • An karbo daga abu kadata Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " mafarki na gaskiya (arru'uyatus sadiq- mafarkin annabawa-) daga Allah ne, shi kuma mafarki daga shedan ne, duk wanda yaga abun da bayaso to yayi tofi a hagun sa sau uku sai ya nemi tsari daga shedan, lallai bazata cutar dashi ba, domin shedan baya shiga irinta surata."[264]
  • An karbo daga abi sa'id alkudry Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " idan dayan ku daga abunda yake so cikin mafarki, to daga Allah ne, ya gode maakan haka sannan kuma ya bada labarin abunda ya gani, idan kuma yaga abunda bayaso, to daga shedan ne, ya nemi tsari daga sharrin sa, kuma kada ya fadama wani, to lallai bazata cutar dashi ba."[265]
  1. Abunda ake fadi a yayin firgici a cikin bacci:
  • Dan karbo daga kakan Amru dan Shu'aib manzon Allah s.a.w yace: " idan dayan ku ya firgita a cikin bacci to yace: " ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushin sa da ukubar sa da sharrin bayin sa, da kuma wasiwasin shedan da kuma yazomun (cikin ibaduna)" to lallai bazat cucar dashi ba."[266]
  1. Abunda ake fadi a lokacin tashi daga bacci:
  • An karbo daga Huzaifa Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan yake kwanciya da daddare, yana daura hannun sa gishin sa sa'annan yace: " ya Allah da sunan nake mutuwa da rayuwa". Idan ya farka sai yace: " godiya ya tabbata ga Allah wanda ya rayani bayan ya kashe ni kuma gareshi makoma yake"."[267]
  1. Abunda ake fadi a yayin shiga bayi:
  • An karbo daga Anas Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan ya shiga bayi yana cewa: " ya allah ina neman tsarin ka daga mazajen shedanu da matan shedanu"."[268] Sai kuma ya shiga da kafar hagun sa.
  1. Abunda ake fadi a lokacin fita daga bayi:
  • An karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan ya fito daga bayi yana cewa: " ina neman gafarar ka"."[269]
  1. Abunda ake fadi a yayin fita daga Gida:
  • An karbo daga ummu salma Allah ya kara mata yarda tace: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan zai fita daga gidansa yana cewa: " da sunan Allah ya Ubangiji ina neman tsari dakai daga yin zunubi ba tare da niyya ba ko na bace ko nayi zalumci ko a zalumce ni, ko jahilta (na aikata aiki na jahilai na cutarwa ko me cutarwa) ko kuma jahilce ni (a aikatamun aiki na jahilai na cutarwa me cutarwa)"."[270]
  • An karbo daga Anas dan malik manzon Allah s.a.w yace: " idan mutum zai fita daga gidan say ace: " dasunan Allah, na dogara ga Allah, babu tsimi da dabara ko karfi sai ga Allah", sai ace masa: ya isar maka, an shiryar dakai, kuma an wadatar maka daga abunda ya dame ka kuma an kiyaye ka daga makiyanka. Sai shedan ya nuisance hanyar sa, sai wani shedanin yace ma wannan shedani: ya zakayi da mutumin da aka isar masa aka wadatar masa aka kuma kareshi!"[271]
  1. Abunda ake fadi a yayin shiga da fita masallaci:

An karbo daga abu Humaid manzon Allah s.a.w yace: " idan dayan ku zai shiga masallaci to yace: " ya Allah! K budemun kofofin rahamar ka". Idan zai fita kuma, yace: " ya Allah! Ina rokon ka daga falalarka".[272]

Kuma zai gabatar da kafar san a dama a yayin shigan sa masallaci idan kuma zai fita sai ya gabatar da kafarsa ta hagu.

  1. Abunda ake fadi a yayin shiga gida:

An karbo daga Abu malik al ash'ari Allah ya kara masa yarda manzon Allah s.a.w yace: " idan mutum zai shiga gidan sa to yace: " ya Allah ina rokon ka alherin mashiga da alherin mafita, da sunan Allah zan shiga kuma da sunan Allah na fita, kuma ga Allah Ubangijin mu na dogara" sa'annan yayi sallama ga iyalan sa."[273]

  1. Addu'ar majalisi da ambaton kaffarar sa:

An karbo daga Abu huraira Allah yakara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda ya zauna a wani majalisi wanda ya yawaita magana a cikin sa mara fa'ida da amfani to yace gabanin ta tashi: " tsarki ya tabbatar maka Ubangijin mu da gode maka, babu abun bauta sa kai ina neman gafarka kuma ina tuba zuwa gareka", face an gafarta masa abunda ya aikata cikin wannan majalisi."[274]

  1. Addu'ar tafiya:

An karbo daga Abdu Allahi dan Umar Allah ya kara masu yarda: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan ya daidaita akan abun hawan sa bayan ya fita zayyi tafiya, sai yayi kabbara sau uku (watan yace Allah Akbar, sau uku), sa'annan yace: " tsarki ya tabbata ga wanda ya hure mana wannan kuma bamu kasance masu iya masa dole ba (tilasta mas aba da sanya shi irin wannan aiki badan Allah ya hure mana shi ba), kuma mu ga Ubangijin mu zamu koma, ya Allah! Ina rokon ka cikin wannan tafiya biyayya da takawa, da kuma ayyuka irin wand aka yarda dashi. Ya Allah! Ka saukake mana wannan tafiya, kuma ka nade mana nisan sa. ya Allah! Kaine aboki cikin tafiya, kuma kalifa a cikin iyalai. Ya Allah! Ina neman tsarin ka daga wahalar tafiya, da mummunan gani, da makoma mummuna cikin dukiya da iyalai". Idan ya dawo sai ya fadesu. Ya kuma kara akan su cewa: " mun dawo daga tafiya lafiya, masu tuba daga zunubi, masu tsarkake ibada ga Ubangijin mu kan ni'imar da yayi mana."[275]

  1. Abunda matafiyi zai fadi ga wanda ya bar masa iyalan sa da abokan sa:

An karbo daga abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya bar masa amanar gidan sa sai yace: " ya sanya ka amana da ajiya agun Allah wanda ajiyar sa baya bata"."[276]

Dan Umar Allah ya kara masu yarda ya kasance yana cema mutum idan yanason tafiya: " saurara na baka ajiya kamar yadda manzon LAlah s.a.w yake bamu ajiya: " nasanya ka ajiya ga Allah na addinin ka da amanarka da karshen ayyukan ka"."[277]

  1. Abunda ake fadi a yayin shiga kauye ko birni:

An karbo daga Suhaib Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w bayaganin wani karkara wanda yakeson shigan ta face yace a lokacin daya ganta: " ya Allah Ubangijin sammai bakwai da abunda dake cikinta, ubangijin kassai da abunda ta kunsa, Ubangijin shedanu da abunda suke batarwa[278], Ubangijin iska da abunda takedaukowa, ina rokonka alherin wannan karkara, da alherin mutanen cikinta, kuma ina neman tsarin ka da ita da sharrin ta da kuma sharrin mutanen ta da sharrin dake cikinta."[279]

  1. Abunda ake fadi a yayin ganin abunda mutum keso:

An karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan wani abu yazo masa na farin ciki sai yace: " godiya ta tabbata ga Allah wanda da ni'imar sa ne ayyukan kwarai suke yiwuwa", idan kuma yaga abunda baya so sai yace: godiya ta tabbata ga Allah cikin dukkan yanayi"."[280]

  1. Abunda ake fadi a yayin sauka a masauki – gida-:

An karbo daga Khaulatu diyar Hakim Allah ya kara mata yarda tace: naji manzon Allah s.a.w yana cewa: " wanda ya sauka a wani masauki sa'annan yace: " ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abunda ya halitta", babu abunda zai cutar dashi, har sai ya tashi daga wannan masauki."[281]

  1. Abunda ake fadi a yayin jima'i:

An karbo daga dan Abbas Allah ya kara masu yarda, manzon Allah s.a.w yace: " da ace dayan ku idan yanason saduwa da iyalin sa zai ce: " da sunan Allah ya Allah ka nisantar damu shedan kuma ka nisantar da shedan daga abunda zaka azurtamu", idan aka kaddara masu yaro a wannan saduwa shedan bazai cutar dashi ba har Abadan."[282]

  1. Abunda ake fadi a lokacin cin abinci:

An karbo daga Jabir Allah ya kara masa yarda yace: naji manzon Allah s.a.w yana cewa: " idan mutum ya shiga gidan sa, sai ya ambaci Allah a lokacin shigan sa da lokacin cin abincin sa, shedan zai ce: babu da wurin kwana da abincin dare cikin (cikin wannan gida)". Idan ya shiga be ambaci Allah ba a lokacin shigan sa, shedan zaice: kun samu wurin kwana. Idan be ambaci Lalah ba a lokacin cin abincin sa, sai yace: kun samu wurin kawana da abincin dare."[283]

An karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace: manzon Allah s.a.w yace: " idan dayan ku zaici abinci to ya ambaci Allah madaukaki,]'' idan ya manta ya ambaci Allah a farko fara cin abincin sa, to yace: " da sunan Allah farkon sa da karshen sa."[284]

  1. Abunda ake fadi a lokacin gama cin abinci ko shan ruwa:

An karbo daga Mu'azu dan Anas aljuhani manzon Allah s.a.w yace: " wanda yaci abinci sai yace: " godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar dani wannan abinci ya kuma azurta ni shi ba tare da dabara ba ko karfi daga gareni", za'a gafarta masa abunda ya gabata na zunuban sa."[285]

  1.  Abunda ake fadi a yayin tsoron makiyi ko kuma makamancin haka:

An karbo daga Abdu Allahi dan Kais babanhi Allah ya kara masa yarda ya fada masa: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan yana tsoron wasu mutane sai yace: " ya Allah mun sanya ka Katanga agaban mu kuma muna neman tsrain ka daga sharrukan su"."[286]

  1. Abunda ake fadi a yayin tsanani ko damuwa:

An karbo daga dan Abbas Allah ya kara masu yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya kasance yana kira da wannan kalmomi a yayin tsanani ko damuwa: " babu abun bautawa sai LAlah me girma da hakuri, babu abun bautawa sai Allah Ubangijin al'arshi me girma, babu abun bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai, da Ubangijin al'arshi me daraja".[287]

An karbo daga Abdurrahman dan Abi bakarata daga babanshi daga manzon Allah s.a.w yace: "addu'o'in wanda damuwa da bakin ciki ya same shi: " Ya Allah rahamar ka nake nema, kada ka barni da raina koda daidai da kyabtawar ido ne, ka kyaramun al'amurana baki dayan su, babu abun bautawa sai kai."[288]

  1. Abunda ake fadi ga wanda aka jarabce sa da damuwa ko bakin ciki:

An karbo daga dan mas'ud yace: manzon Allah s.a.w yace: " bawa bazai taba fadi ba idan abun bakin ciki ya same shi ko damuwa: " ya Allah ni bawanka ne dan bawanka dan baiwarka, goshina a hannun ka yake, zartarwa a cikin hukuncin ka, adalcin ka cikin abunda ka kaddara, ina rokon ka da dukkanin sunan ka wanda naka ne, wand aka kira kanka dashi, ko kuma ka saukar dashi cikin littafin ka, ko kuma ka sanar dawni shi cikin halittan ka, ko kuma ka barma kanka sani cikin ilimin gaibun dake gunka, ka sanya alkur'ani ya zama farin cikin zuciya ta, da hasken gani na, da magance bakin ciki na da tafiyar da damuwa na", face Allah ya tafiyar masa da damuwar say a kuma canza masa hakan da farin ciki. Sai sukace ya manzon Allah: ya kamata mu koyi wanann kalmomi? Sai yace: kwarai kuwa, ya kamata ga duk wanda yaji su daya koye su."[289]

Baya halatta ga wanda aka jarrabe shi da wani abu na musifa da bakin ciki ya yima kansa addu'a mara kyau, ya wajaba a gareshi yayu koyi da manhajin da manzon Allah s.a.w yayi bayani akai, an karbo daga Anas Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " kada dayan ku yayima kan sa fatan mutuwa domin wani cuta da ta same shi, idan ya kasance babu makawa sai yayi fatar mutuwar to yace: " ya Allah ka rayani idan rayuwa itace mafi alheri a gareni, ka kuma kashe ni idan mutuwa itace alheri a gareni"."[290]

  1. Abunda ake fadi a yayin sanya tufafi sabo ko kuma ma'anar haka:

An karbo daga Abi sa'id alkudri Allah ya kara masa yarda manzon Allah s.a.w ya kasance idan ya sanya tufafi sabo sai yace: " " ya Allah godiya ta tabbata a gareka, kai ne ka horemun wannan tufafi, ina rokon ka alhrin sa da alherin da aka za'a aikata dashi, kuma ina neman tsarin ka daga sharrin sa da sharrin abunda za'a aikata dashi". Abu Nadrata yace[291]: sahabban manzon Allah s.a.w sun kasance idan dayan sa yasanya sabom kaya sai suce masa: " Allah ya baka rayuwar cin moriyar kayan kuma Allah ya canza maka wani tufafin bayan lalacewar su"."[292]

  1. Abunda aka fadi a lokacin fushi: an karbo daga sulaiman dan Sardi Allah ya kara masa yarda yace: " na kasance tare da manzon Allah s.a.w \, sai ga wani mutum yana zagin wani, dayan su fuskar sa ta baci jijiyoyin wuyan sa sun tashi, sai manzon Allah s.a.w yace: lallai nasan Kalmar da zai fadeta da fushin ya rabu dashi, da zai ce: " ina neman tsarin Allah daga shedan"m fushin zai barshi. Sai sukace mashi: lallai manzon Allah s.a.w yace: ka nemi tsarin Allah daga shedan. Sai yace: shin ni mahaukaci ne? (a nashi karancin fahimtar neman tsari daga shedan na mahaukata ne besan cewa ba fushi daga cikin fusgan shedan yake)."[293]

 

 

 

Sallar istikhara:

(neman zabin Allah akan abunda mutum keson aikatawa a rayuwan sa):

An shar'anta sallar istikhara ga musulmai domin neman taimakon daga Ubangiji madaukaki, ya kuma daura shi akan alheri cikin al'amuran da yake ko kwanto a cikin zuciyar sa besan wanne yafi dacewa dashi, domin katse hanya a gabar sa na wasiwasin shedan sai ya kiyaye kansa daga nadama akan abunda ya kubce masa na alheri, mutum nashi shine aikata sababi amma sakamakon yana wurin Allah madaukaki, abunda Allah ya kaddara shine mafi dacewa, kuma duk wanda yayi istikhara bazai taba tabewa ba kuma wanda ya nemi shawara bazayyi nadama ba.

 

 Yadda akeyin sallar istikhara:

Mutum zayyi salla raka'a biyu na nafila, zai karanta fatiha da " kulya ayyuhal kafirun" a raka'ar farko sai raka'a ta biyu ya karanta fatiha da " kulhuwallahu Ahad", sai ya bude addu'ar sa dayin godiya da yabo ga Allah sai salati ga manzon Allah s.a.w, sa'annan yayi addu'ar istikhara wanda yazo cikin hadisin da Jabir dan Abdu Allah Allah ya kara masu yarda ya rawaito cewa: " manzon Allah s.a.w ya kasance yana karantar damu addu'ar istikhara cikin al'amura kamar yadda yake karantar damu surorin alkur'ani, yana cewa: idan dayan ku yayi himman yin wani abu, to yayi salla raka biyu na nafila, sai yace: " ya Allah ina neman zabin ka da ilimin ka, kuma ina neman iko da ikon ka, kuma ina rokon ka daga falalar ka me girma, domin kuwa kana da iyawa ni kuma na gaza, ka sani ni kuma ban sani ba, kai ne masanin gaibuka. Ya Allah idan kasan cewa[294] wannan al'amari alheri ne a gareni cikin addini na da rayuwa na da karshen al'amari na, ko kuma yace: " al'amurana na duniya dana lahira" to kani iko akan sa kuma ka saukakemun shi, sa'annan kamun albarka a cikin sa, idan kuma kasan cewa wannan al'amari sharri ne a gareni, cikin addini na da rayuwa na da karshen al'amari na, ko kuma yace: " al'amurana na duniya dana lahira" to ka canzamun shi kuma ka bani iko akan alheri duk inda yake, sa'annan ka yardan mun dashi". Sai ya fadi bukatar sa."[295]

 

 

 

Magani na cutuka na gabban jiki dana zuciya daga sunnar manzon Allah:

Lallai lizimtar musulmi da karantarwan musulunci da aiwatar dashi da ladubban sa da dabi'un sa, kafili ne bayan dacewar Allah madaukaki na samun murna da natsuwa na hankali wanda hakan zai haihar da kariya daga cututtuka masu yawa na gabbai wanda suke faruwa dalilin rashin lafiyar hankali, me yuwa zikiri da addu'a suna cikin manyan hanyoyi wanda Allah yayi baiwa a gareni dasu, domin kariya daga bala'I da sauran musifu gabanin su faru, haka kuma ka tunkude su bayan sun faru, Allah madaukaki yana cewa: " kuma muna saukarwa daga cikin alkur'ani abunda yake waraka ne da rahama ga muminai; amma kuma baya karawa azzalumai komai face hasara (82)"[296]

Kuma Allah madaukaki yana cewa: " kace shi shiriya ne da waraka ga wanda sukayi imani"[297]

Asani cewa magani da alkur'ani da kuma shiryarwan manzon Allah dole ne ya zama akwai imani na gaskiya gabanin me karantawa da wanda ake karanta mawa, bawai ana nufin a bar yin amfani da magunguna bane da aikata dalilai na halal, hakika manzon Allah s.a.w yace: " kuyi magani yaku bayin Allah domin kuwa Allah be bar wani cut aba face tana da maganin ta"[298]

Tare da lura matuka na yin magani wanda yake Allah ya haramta, an karbo daga abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: " manzon Allah s.a.w ya hana yin magani datti (ko haramun, kamar ya kasance cikin sa akwai giya ko kuma naman alade ko kuma makamancin haka)."[299]

Ibn Kayyim Allah yayi mashi rahama yana cewa[300]:

Sai dai akwai wani al'amari daya dace a lura dashi, shine cewa azkar da ayyoyi da addu'o'i wanda Allah yake warkarwa dasu dayin magani dasu, a karon kanta dukda cewa me amfani ce kuma magani, yana bukatan karba daga wurin wanda ake karanta mawa da kuma karfin himma na wanda yakeyin karatun da tasirin sa, duk lokacin da ba'a samu waraka ba to ya kasance ne sakamakon rauni na tasirin me karatun ko kuma saboda rashinkarba na wanda akayima karatun ko kuma domin wani dalili wanda zai hana yin magani, kamar yadda hakan ya kasance cikin magunguna wanda aka sha ko shafawa, lallai rashin tasirin su zai iya zama saboda rashin karban dabi'ar jiki na wannan magani.

Ibn kayyim yana cewa a fagen maganar sa akan shiryarwar manzon Allah cikin magani na cutuwa[301]:

Maganin wannan nau'i da abu guda biyu ne: al'amari na farko ta bangaren mara lafiya da kuma al'amari ta bangaren me yin maganin, wanda yake daga bangaren mara lafiya yana kasancewa ne da karfin ransa da kuma gaskiya fuskantar sa zuwa ga wanda ya kirkiri wannan rayuka da me renon ta, neman tsari na daidai wanda zuciya da harshe suka hadu akai, to lallai wannan nau'i ne na yaki, shi kuma me yaki baya samun nasara daga makiya da makami sai da abu biyu, ya ksance me cikakken lafiya na zuciya me kyau, kuma ya kasance yana da karfi a jiki, duk lokacin da aka rasa daya daga cikin biyun nan makami bazai amfanar ba dayawa, to yaya idan an rasa abun biyu baki daya: zuciya ka sance gurbatacciya daga tauhidi da tawakkali da fadakarwa, kuma bashi da makami, al'amari na biyu: daga bangaren meyin maganin ya kasance akwai wannan al'amari biyu a tare dashi shima.

 

 

 

Magani ta hanyar rukiyyya ta shari’a:

Wannan wasu daga cikin ayoyi da hadisai ne wanda suka inganta daga manzon Allah s.a.w wanda ake yaye bala'i dasu bayan faruwan ta kuma ake warkarwa dasu da izinin Allah madaukaki:

  1. An karbo daga abi sa'id alkudri Allah ya kara masa yarda yace: " wasu mutane cikin sahabban manzon Allah s.a.w sun fita tafiya, har suka sauka a wani gari dun wasu kabila na larabawa, sai suka nemi su basu masauki sukaki basu, sai kunama ta harbi shugaban wannan gari, sukayi masa magani da duk wani abu baki yin amfani, sai wasunsu sukace: ko zamuje gun wannan baki ne wanda suka sauka, ko za'a samu magani agun wasu daga cikin su. Sai suka zo masu suka ce: yaku mutane lallai kunama ya harbi sarkin mu, mun masa duk abunda muka iya amma ba sauki, ko akwai wani acikin ku da yake da wani abu? Sai wasun su sukace: eh, wallahi inayin magani, sai dai da ace kun bamu masauki ne to kuma kunki yin hakan saboda haka bazan masa magani ba har sai kun sanyamun ladan akan haka, sai suka shirya akan zasu bashi akuya, sai ya bisu suka tafi yana masa tufi tare da karanta masa {fatiha- Alhamdu Lillahi Rabbi il‘alamin-}. Sai ya warke, sai ya fito ya dawo cikin nasara. Sai yace: sai suka bashi ladar sa wanda suka shirya akai, sai wasun su sukace: ku raba mana muci, sai wanda yayi maganin yace: kada ku raba ku bari har sai munje gun manzon Allah s.a.w mu fada masa abunda ya faru sai muji hukuncin sa, sai suka zo gun manzon Allah s.a.w suka fada masa sai yace: hakika kun dace, ku raba mana, nima ku ajemun kaso na a ciki. Sai manzon Allah s.a.w yayi dariya."[302]
  2. An karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda: " manzon Allah s.a.w ya kasance idan mara lafiya yazo masa ko kuma aka kawo mashi shi, sai yace: " ka tafiyar masa da rashin lafiya da tsanani ya Ubangijin mutane, ka bashi lafiya kaine me bada lafiya, babu waraka sai warakanka, waraka wanda na kai tsaye wanda baya barin tabon ciwo ko kuma ko wani ciwo"."[303]
  3. Rukyan Jibril amincin Allah ya tabbata a gareshi, an karbo daga Abi sa'id alkhudri Allah ya kara masa yarda: " lallai Jibril yazo gun manzon Allah s.a.w, sai yace: ya Muhammad! Shin kanajin wani rashin lafiya ko ciwo a gabar ka? Sai yace: eh. Sai yace: " da sunan Allah zan maka ina nema maka tsari, daga dukkanin abunda zai cutar dakai, da sharrin dukkanin rai me datti ko kuma ido me hassada Allah ha baka lafiya, da sunan Allah ina maka neman tsari"."[304]
  4. An karbo daga Usman dan Abul Aas al sakhafi: " cewa ya kai kuka gun manzon Allah s.a.w na wani ciwo nashi, wanda yake damun shi a jikin sat un lokacin daya musulunta. Sai manzon Allah s.a.w yace mashi: ka sanya hannun ka akan inda yake maka ciwo ajikin ka, sai kace: " da sunan Allah", sau uku. Sai kace sau bakwai: " ina neman tsarin Allah da ikon sa daga sharrin abunda nakejin sa da kuma jin tsoron sa"."[305]

 

www.islamland.com

 

 

 

[1] Suratul ahzab ayata 42.

[2] Suratul bakara ayata 152.

[3] Suratul ahzab ayata 35.

[4] Suratu al Imran ayata 41.

[5] Suratul ali Imran ayata 191

[6] suratul bakara ayata 200.

[7] Suratul munafikun ayata 9.

[8] Suratul a'araf ayata 205.

[9] Sahihul buhari.

[10] Sahihul targib.

[11] Sahihul tirmizi.

[12] Suratul balad ayata 4.

[13] Suratul gafir ayata 60.

[14] Suratul bakara ayata 186.

[15] Suratul anbiya'I ayata 35.

[16] Suratul bakara ayata 155-156.

[17] Suratun namli ayata 40.

[18] Suratul kasas ayata 76-83.

[19] Sahihu ibn majjah – albani ya inganta shi.

[20] Suratul anbiya'I ayata 83-86.

[21] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 7, shafi na 161, lambar hadisi na 2901.

[22] Sahihu ibn hibban.

[23] Sahihu ibn hibban, ujalladi na 7, shafi na 187, lambar hadisi na 2924.

[24] Alkawa'id shafi na 32.

[25] Suratul shura ayata 30.

[26][26] Sunan al tirmizi, mujalladi na 4, shafi na 479, lambar hadisi na 2185.

[27] Suratu hud ayata 102.

[28] Sahihul buhari, mujalladi na 4, shafi na 1726, lambar hadisi na 4409.

[29] Suratul mudaffifin ayata 14

[30] Sahihul jami'u – kuma albani ya hassana shi

[31] Sahihul tirmizi – kuma albani ya ingantashi

[32] Suratul bakara ayata 188.

[33] Suratul bakara ayata 278-279.

[34] Sunan Ibn Majjah, mujalladi na 2, shafi na 765, lambar hadisi na 2279.

[35] Sahihu Muslim, mujalladi na 3, shafi an 1219, lambar hadisi na 1598.

[36] Suratun nur ayata 19.

[37] Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 2254, lambar hadisi na 5721.

[38] Mustadrak ala sahihain, mujalladi na 4, shafi na 583, lambar hadisi na 8623.

[39] Sahihul buhari, mujalladi na 2, shafi na 882, lambar hadisi na 2361.

[40] Ayar ta sauka ne akan wasu mutane sun kasance suna umurni da kyakyawan aiki da hani daga mummunan aiki sai dai sunki yi masu biyayya da amsan nasihohin su, sai rayukan su ya kusa tafiya akan su domin bakin ciki; sai Allah madaukaki ya saukar da wannan aya domin yarda a garesu.

[41] Sahihu Abi Dawud.

[42] Sunan Abi Dawud, mujalladi na 4, shafi na 121, lambar hadisi na 4336.

[43] Suratul hajji ayata 38

[44] Sahihul bukhari, mujalladi na 5, shafi na 2384 lambar hadisi na 6137.

[45] Suratul taubah ayata 65-66.

[46] Suratul taubah ayata 79.

[47] Suratul fadir ayata 43.

[48] Suratul kasas ayata 76-81.

[49] Suratul rahman ayata 13.

[50] Taisirul kur'anil karim fi kalami minan na sheika Abdulrahman assa'adi Allah yayi masa rahama.

[51] Suratul hujirat ayata 13.

[52] Suratu Ibrahim ayata 7.

[53] Sunan Ibn Majjah, mujalladi na 2, shafi na 1250 lambar hadisi na 3805.

[54]Suratul zariyat ayata 19.

[55] Dabarani ne ya rawaito shi da Abu addunya kuma albani ya ingantashi cikin sahihul jami'u.

[56] Suratul insan ayata 8-12.

[57] Suratul isra'I ayata 36

[58] Sahihul bukhari mujalladi na 6 shafi na 2550 hadisi na 6552

[59] Sunan al tirmizi mujalladi na 4 shafi na 612 hadisi na 2417

[60] Suratul furkan ayata 68

[61] Suratul kahfi ayata 32-42

[62] Suratun namli ayata 40

[63] Sahihul bukhari mujalladi na 1 shafi na 27 hadisi na 50

[64] Musnad Ahmad

[65] Sahihu muslim mujalladi na 4 shafi na 1830 hadisi na 1337

[66] Sahihul bukhari mujalladi na 5 shafi na 2384 hadisi na 6137

[67] Sunan nisa'I mujalladi na 1 shafi na 132 hadisi na 465

[68] Mustadraka ala sahihain mujalladi na 1 shafi na 672 hadisi na 1822

[69] Sahihu ibn majjah da sahihul tirmizi

[70] Sahihu muslim mujalladi na 1 shafi na 498 hadisi na 720

[71] Sahihu ibn hibban mujalladi na 6 shafi na 170 hadisi na 2410

[72] Sahihu muslim mujalladi na 2 shafi na 808 hadisi na 1153

[73] Sahihul bukhari mujalladi na 2 shafi na 697 hadisi na 1875

[75] Sahihul bukhari mujalladi na 5 shafi na 2384 hadisi na 6137

[76] Sahihul bukhari

[77] Sahihu muslim mujalladi na 1 shafi na 414 hadisi na 591

[78] Sahihu muslim mujalladi na 1 shafi na 415 hadisi na 594

[79] Sahihul bukhari mujalladi na 1 shafi na 289 hadisi na 808

[80] Sahihu muslim mujalladi na 1 shafi na 418 hadisi na 597

[81] Sunan al kubra mujalladi na 6 shafi na 30 hadisi na 9928

[82] Sahihu ibn khuzaima mujalladi na 1 shafi na 372 hadisi na 755

[83] Sahihu ibn Hibban mujalladi na 5 shafi na 364 hadisi na 2020

[84] Suratul hadid ayata 22

[85] Sahihu muslim mujalladi na 4 shafi na 2052 hadidi na 2664

[86] Suratul hajj ayata 11

[87] Suratu Yunus ayata 17

[88] Suratul dalak ayata 2

[89] Suratul bakara ayata 216

[90] Suratul bakara ayata 155

[91] Sahihu muslim mujalladi na 2 shafi na 632 hadisi na 918

[92] Zadul ma'ad fi hadyi khairul ibad mujalladi na 4 shafi na 188-195, an takaita da kari da kuma canza wani abu cikin asalin sannin littifin

[93] Suratul bakara ayata 153

[94] Sunan abi dawu mujalladi na 4 shafi na 296 hadisi na 4985

[95]Sahihu ibn hibban mujalladi na 2, shafi na 405, hadisi na 639

[96] Suratul ra'ad ayata 28

[97] Suratun namli ayata 62

[98] Suratu gafir ayata 60

[99] Suratul inshirah ayata 5-6

[100] Suratul hadid ayata 20

[101] Sahihu ibn majjah – kuma albani ya ingantashi

[102] Sahihul jami'u

[103] Zadul ma'ad fi hadiyi khairul ma'ad, mujalladi na 4, shafi na 188-195, an takaita maganar da kuma kari da kuma canza wani abu acikin asalin nassin littafin

[104] Suratu al Imran ayata 140

[105] Sahihul ibn hibban, mujalladi na 7, shafi na 210, hadisi na 2948

[106] Sahihul bukhari, mujalladi na 5, shafi na 2137, hadisi na 5318

[107] Suratul Muhammad ayata 31

[108] Sahihu muslim mujalladi na 4 shafi na 2295 hadisi na 2999

[109] Musnad imamu ahmad mujalladi na 5 shafi na 427 hadisi na 23672

[110] Majmu'ul fatawa

[111] Sahihu muslim mujalladi na 4 shafi na 2174 hadisi na 2822

[112] Sahihul bukhari, mujalladi na 1, shafi na 439, hadisi na 1241

[113] Sahihul bukhari, mujalladi na 1, shafi na 431, hadisi na 1224

[114] Sahihu muslim, mujalladi na 1, shafi na 539, hadisi na 780

[115] Sunan al tirmizi, mujalladi na 2, shafi na 503, hadisi na 606

[116] Sahihul jami'u

[117] Sahihul bukhari, mujalladi na 3, shafi na 1233, hadisi na 3191

[118] Suratul bakara ayata 152

[120] Sahihul bukhari, mujalladi na 6, shafi na 2694, hadisi na 6970

[121] Suratul saffat ayata 139-144

[122] Sahihu ibn Khuzaima, mujalladi na 3, shafi na 195, hadisi na 1895

[123] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 5, shafi na 116, hadisi na 1810

[124] Sahihul bukhari, mujalladi na 1, shafi na 383, hadisi na 1091 da muslim

[125] Sahihul bukhari, mujalladi na 5, shafu na 2352, hadisi na 6043

[126] Sahihul bukhari, mujalladi na 5, shafu na 2352, hadisi na 6042

[127] Sahihul bukhari, mujalladi na 1, shafu na 387, hadisi na 1103

[128] Sahihu muslim, mujalladi na 4, shafi na 2072, hadisi na 2695

[129] Sahihu Muslim

[130] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 3, shafi na 185, hadisi na 904

[131] Sahihu muslim, mujalladi na 1, shafi na 203, hadisi na 223

[132] Sahihul bukhari, mujalladi na 5, shafu na 2346, hadisi na 6021

[133] Sahihu muslimm mujalladi na 4, shafi na 2090, hadisi na 2726

[134] Suratun shura ayata 30

[135] Suratun nur ayata 10-12

[136] Al mustadrak ala sahihain, mujalladi na 4, shafi na 291, hadisi na 7677

[137] Suratul anbiya'I ayata 78-88

[138] Al mustadrak ala sahihain, mujalladi na 1, shafi na 729, hadisi na 1997

[139] Al mustadrak ala sahihain, mujalladi na 3, shafi na 623, hadisi na 6303

[140] Sahihi muslim, mujalladi na 4, shafi na 2074, hadisi na 2699

[141] Sahihu Ibn Hibban, mujalladi na 8. Shafi na 103, hadisi lamba 3309

[142] Sahihul jami'u

[143] Suratul sajada ayata 16019

[144] Sunan altirmizi, mujalladi na 5, shafi na 11, lambar hadisi na 2616

[145] Suratul Muhammad ayata: 22-24

[146] Sunan albaihaqi alkubra, mujalladi na 10, shafi na 35, lambar hadisi na 19655

[147] Sahihu ibn Hibban, mujalladi na 3, shafi na 158, lambar hadisi na 874

[148] Suratu Hud ayata 102

[149] Sahihul buhari, mujalladi na 4, shafi na 1726, hadisi na 4409

[150] Suratul gafir ayata 60

[151] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 3, shafi na 151, hadisi na 870

[152] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 3, shafi na 151, hadisi na 872

[153] Suratun nisa'I ayata 102

[154] Aljawabul kafi, shafi na 37

[155] Suratul muminun ayata 51

[156] Suratul bakara ayata 172

[157] Sahihu muslim, mujalladi na 2, shafi na 703, hadisi na 1015

[158] Sahihu ibn Hibban, mujalladi na 3, shafi na 160, hadisi na 870

[159] Sahihu ibn khuzaima, mujalladi na 1, shafi na 103, hadisi na 206

[160] Suratul isra'I ayata 110

[161] Sahihul buhari, mujalladi na 3, shafi na 1091, hadisi na 2830

[162] Suratu yunus ayata 10

[163] Sahihu ibn khuzaima, mujalladi na 1, shafi na 351, hadisi na 710

[164] Suratul a'araf ayata 180

[165] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 3, shafi na 173, hadisi na 891.

[166] Sahihun nasa'i

[167] Suratul anbiya'I ayata 89-90

[168] Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 2335, hadisi na 5981

[169] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 15, shafi na 166, hadisi na 6763

[170] Al mustadraka ala sahihain, mujalladi na 1, shafi na 670, hadisi na 1816

[171] Sahihul tirmizi

[172] Sahihul buhari, mujalladi na 1, shafi na 316, hadisi na 893

[173] Sahihul bukhari, mujalladi na 2, shafi na 672, lambar hadisi na 1800

[174] Sahihu ibn hibban

[175] Sunanul tirmizi hadisi na 3499

[176] Sahihu bukhari hadisi na 5962

[177] Sunan ibn khuzaima hadisi na 602

[178] سahihul jami'u

[179] Sunan Ahmad da sunan Abu dawud hadisi na 1524

[180] Sahihu bukhari hadisi na 2152

[181] Sahihu bukhari hadisi na 7026

[182] Musnad imamu Ahmad hadisi na 6655

[183] Sunan abu dawud hadisi na 1482

[184] Suratul hujurat ayata 36-37

 [185] Sahihu bukhari hadisi na 2758

[186] Suratul bakara ayata 286

 

[187] Suratu al Imran ayata 8

[188] Suratu al imaran ayata 193

[189] Suratu Yunus ayata 85-86

[190] suratul a'araf ayata 47

[191]suratul isra'i ayata 80

[192]suratul a'araf ayata 126

[193]suratu daha ayata 25-26

[194]Suratu Ibrahim ayata 40-41

[195] Suratul muminun ayata 97-98

[196] Suratul muminun ayata 118

[197] Suratu Ibrahim ayata 41

[198] Suratul kahfi ayata 10

[199] Suratul furkan ayata 65-66

[200] Suratul furkan ayata 74

[201] Suratul hashri ayata 10

[202] Suratul bakara ayata 201

[203] Sahihu muslim hadisi na 2721

[204] Sahihul bukhari hadisi na 798

[205] Sahihul bukhari hadisi na 6006

[206] Sahihu muslim hadisi na2719

[207] Sahihu muslim hadisi na 2739

[208] Sahihu muslim hadisi na 2722

[209] Sahihu muslim hadisi na 2720

[210] Sahihul bukhari hadisi na 6014

[211] Sahihu muslim hadisi na 486

[212] Mustadraka ala sahihain hadisi na 1934

[213] Mustadraka ala sahihain hadisi na 1924

[214] Sahihul tirmizi

[215] Sahihu ibn hibban hadisi na 1971

[216] Sahihu ibn hibban hadisi na 1023

 [217] Sahihu ibn hibban hadisi na 1029

[218] Sahihu ibn hibban hadisi na 943

[219] Sahihu ibn hibban hadisi na 947

[220] Sahihu muslim

[221] Sahihul jami'u

[222] Mustadraka ala sahihain hadisi na 1942

[223] Mustadraka ala sahihain hadisi na 1838

[224] Sahihul tirmizi

[225] Sahihu muslim hadisi na 2707

[226] Sahihul bukhari hadisi na 799

[227] Mustadraka ala sahihain hadisi na 1953

[228] Sunan abu dawu hadisi na 1544

[229] Mustadraka ala sahihain hadisi na 1535

[230] Sahihu muslim hadisi na 771

[231] Mustadraka ala sahihain hadisi na 1973

[232] sunanul tirmizi hadisi na 3502

[233] Sahihi muslim hadisi na 2725

[234] Sahihu ibn khuzaima hadisi na 1095

[235] Sahihu muslim hadisi na 476

[236] Sahihu muslim hadisi na 483

[237] Sahuhu ibn hibban hadisi na 935

[238] Suratu gafir ayata 55

[239] Suratu Khaaf ayata 39

[240] Suratul ahzab ayata 41-42

[241] Sunan abu dawud hadisi na 5084

[242] Sahihu muslim hadisi na 2723

[243] Sahihu ibn hibban hadisi na 852

[244] Sahihu muslim hadisi na 2709

[245] Sunan abu dawud hadisi na 5069

[246] Sahihul buhari hadisi na 6040

[247] Sahihul buhari hadisi na 5947

[248] Sunan abu dawud hadisi na 5068

[249] Sahihu abu dawud hadisi na 5082

[250] Sunanul tirmizi hadisi na 3392

[251] Sahihu ibn hibban

[252] Sunan abu dawu hadisi na 5090

[253] Mustadrak ala sahihain hadisi na 2000

[254] Sahihu muslim hadisi na 2692

[255] Sunanl tirmizi hadisi na 3474

[256] Zadul ma'ad

[257] Sahihul buhari hadisi na 2187

[258] An gano cikin ilimin zamani sabo cewa akwai wani kwaro nag ado wanda ake kira da suna a turance (Cimex Lectularius – Bed Bugs).

[259] Allah madaukaki yace: {Allah shine wanda yake kare rayuwa a lokacin mutuwar su da wanda bata mutu ba a cikin baccin ta, sai ya rike wacce ya rubuta mata mutuwa sai ya saki ssauran zuwa wani lokaci sananne, lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani} suratul zumar ayata 42. Ya kara cewa kuma: {shine kuma wanda yake kashe ku da daddare kuma yana sanin abubuwan da aikatawa da rana}

[260] Sahihul buhari hadisi na 5961

[261] Sahihul buhari hadisi na 4729

[262] Sahihul buhari hadisi na 5955

[263] Sahihul buhari hadisi na 4722

[264] Sahihul buhari hadisi na 6594

[265] Sahihul buhari hadisi na 6638

[266] Sahihul tirmizi

[267] Sahihul buhari hadisi na 5955

[268] Sahihul buhari hadisi na 142

[269] Sahihu ibn hibban hadisi na 1444

[270] Mustadraka ala sahihain hadisi na 1907

[271] Sahihu ibn hibban hadisi na 822

[272] Sahihu muslim hadisi na 713

[273] Sunan abu dawud hadisi na 5096

[274][274] Sahihu ibn hibban hadisi na 9594

[275] Sahihu muslim hadisi na 1342

[276] Sunan ibn majjah hadisi na 2825

[277] Sahihu ibn khuzaima hadisi na 2531

[278] Idan bawa yasan cewa Allah madaukaki Ubangijin komai da mulkin sa, kuma shi ya karade komai, kuma ikon say a shafi komai kuma mashi'ar sa wanzaziya ce, babu abunda ya gagare shi a kasa ko kuma sama, zai koma gare shi shi kadai ya kuma nemi tsari dashi shi kadai kuma bzaiji tsoron wani ba bayan shi.

[279] Sahihu ibn khuzaima hadisi na 2565

[280] Sahihul jami'u, da mustadrak ala sahihain hadisi na 1840

[281] Sahihu muslim hadisi na 2708

[282] Sahihul bukhari, hadisi na 6025

[283] Sahihu muslim haidisi na 2018

[284] Sunan abi dawud hadisi na 3767

[285] Sunan al tirmizi haidis na 3458

[286] Mustadraka ala sahihain hadisi na 2629

[287] Sahihul bukhari, hadisi na 6994

[288] Sahihu ibn hibban hadisi na 970

[289] Sahihu ibn hibban, hadisi na 972

[290] Sahihul bukhari, hadisi na 5990

[291] Shine Almunzir dan Malik, daya daga cikin tabi'ai

[292] Sahihu abu dawud da mustadrak ala sahihain hadisi na 7408

[293] Sahihul bukhari, hadisi na 3108

[294] Yayi magana kamar da shakka ma'anar say a mika masa komai, da yarda da ilimin sa a ciki, zai kuma iya zama shakkan a cikin cewa ilimin wanda yake alaka da alheri ko kuma sharri, bawai asalin ilimin ba.

[295] Sahihul bukhari, hadisi na 1109

[296] Suratul isra'I ayata 82

[297] Suratul fussilat ayata 44

[298] Sahihu ibn hibban, hadisi na 6061

[299] Mustadrak ala sahihain, hadisi na 8260

[300] Aljawabul khafi liman sa'ala anid dawa'ish-shafi, shafi na 21

[301] Zadul ma'ad juzu'I na 4, shafi na 67-68

[302] Sahihul bukhari, hadisi na 2156

[303] Sahihul bukhari, hadisi na 5351

[304] Sahihu Muslim, hadisi na 2186

[305] Sahihu Muslim, mujalladi na 4, shafi na 1728, nadisi na