KOMAWA ZUWA GA ASALI

KOMAWA ZUWA GA ASALI​

KOMAWA ZUWA GA ASALI
العودة إلى الأصل بلغة الهوسا

 

Mawallafi
Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha
د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة


Fassara
European Islamic Research Center (EIRC)
المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية
& Hashim Muhammad Sani
Wanda ya bibiyi fassara
Muhammad Khamis
 

www.islamland.com

 

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga annabin mu Muhammad da iyalan sa da sahabban sa baki daya.
Gabatarwa:
A cikin wannan littafi zamuyi magana akan wani abu wanda ya shagaltar da jinsin mutum daga mahangar alkur'ani (watan zamuyi bayanin ra'ayin alkur'ani akan wannan abu) bawai sabuwar zance bace wanda ta faro asali cikin wannan zamani namu bane kawai ta kare a'a zataci gaba ne matukar dan adam na raye a doron kasa, watan magana akan asalin abubuwa da magana akan farkon halitta mutum da tashi bayan mutuwa da tashin da hisabai bayan mutuwa wacce wasu sukayi imani da ita wasu kuma suka kafurce mata, alkur'ani ya labarta banbancin mutune wurin inkarin haka game da tashi bayan mutuwa da hisabi, daga cikin su akwai wanda yace wannan ai abubuwa wanda aka gada tsofaffi da kuma tatsuniya ta mutanen farko wanda annabawa suka gado ta daga iyayen su da kakannin su, Allah,madaukaki yace yana me bayyana haka: " sun ce yanzu ace idan mun mutu mun koma kasa da kasusuwa ace wai za'a tayar damu kuma (82) hakika munyi alkawari mu da iyayen mu na baya cewa lallai wannan fa tatsuniya ce irinta mutanen farko (83)" suratul muminun. Daga cikin su kuma akwai wanda suka nemi a dawo da iyayensu wanda suka riga su mutuwa da kakannin su idan anason suyi imani saboda girman kai kawai nasu da karyatawa, Allah madaukaki yace: " lallai wancan suna cewa (34) ai ba komai bace face mutuwan da zamuyi na farko amma dai baza'a tashemu ba (35) idan kuma kunce haka to ku zo mana da iyayen ku mana idan kun kasance masu gaskiya (36)" suratul al-dukkhan.
Daga cikin su kuma akwai wanda suka dauki rayuwan a matsayin juyi juyi ce da matakai wasu al'umma su zo bayan wasu idan wannan al'umman suka mutu sai wasu suzo bayan su haka za'ata zagayawa babu zance tashi bayan mutuwa da hisabi, Allah madaukaki yace: " sunce ba komai bace face rayuwan mu nanan duniya muna mutuwa kuma mu tashi babu abunda yake kashe mu face zamani, basu da wani ilimi akan haka kawai zato sukeyi (24)" suratul jasiya.
Zamuyi magana cikin wannan dan karamin littafi ta hanyar alkur'ani akan wannan zance daga mahangan hankali da magana saboda duk wanda ya karyata tashin alkiyama da hisabi yafi ace basuyi imani da cewa akwai me halitta ba kuma duk wanda beyi imani ba da cewa akwai me halitta baza'ayi muhawara dashu ba sai ta hanyar hankali da magana, dayawa daga cikin wannan mutane hankalin su da maganar su da fidiyar su suna kalubanlantar sun a ganin cewa sun gane hakikanin gaskiya da imani da wannan tashin alkiyama da hisabi wasu kuma daga cikin su hankalin su da maganar su baya baya kara masu komai face musu da dagawa da karyatawa, kamar yadda mutanen fir'auna suka aikata lokacin da Musa yazo masu da hujjoji bayyanannu wanda sukayi yakini akan gaskiyanta cikin zukatan su amma sai dai girman kai da mulki da kuma gabatar da maslahar duniya ta sanya su karyatata, Allah madaukaki yace: " sun karyatata saboda zalumci da dagawa bayan zukatan su ta sakankance da ita, ka kalla kagani yaya karshen masu barna ta kaya (14)" suratun namli.
Zai kasance ta hanyar magana na mandiki cike da hujjoji daga alkur'ani me girma dangane da mahalicci da halittu da kuma dalilin samar dasu da kuma tashin alkiyama da yiwar aukuwan hakan da kuma makoma bayan hakan ina me fatan ganin cewa na gabatar da abubuwa na ilimi masu amfani ga dukkanin makarancin wannan littafi.
Addu'ar da nakeyi ga dukkanin wanda wannan littafi ya fada hannun sa daya ji dadin karantashi idan yayi imani da gamsuwa da abunda ke cikin sa Alhamdulillah wannan ake fata daman, idan kuma ba haka ba to wannan sabbin abubuwa ne na ilimi wanda zai karu cikin runbun tunanin sa kuma zai san gaskiya wanda ya boye masa ko kuma ya riske sa amma ta hanyar kuskure ko kuma hanyar da aka lallatata da gangan.
Kayi addu'a da zuciya daya yakai makarancin wannan littafi da cewa " ya wanda ya halicci wannan duniya ka shiryar dani kuma ka nunamun hanya ta kwarai ka kuma kama hannuna zuwa ga gaskiya bani da wani mataimaki koma bayanka", kuma kayi kokarin yakar zuciyar ka zuwa ga sanin gaskiya da isa gareta koda kuwa ka kasance mara addini ne domin kuwa lallai a hakan kana addinin bautan zuciyar ka ne da son ranka kuma ita halitta ce kamar ka kenan ka zama bawan bayan baka sani ba, Allah madaukaki yana cewa: " wanda sukayi kokari cikin al'amuran mu da sannu zamu shiryar dasu hanyoyin mu kuma lallai Allah yana tare da masu kyautatawa (69)" suratul ankabut.
Yazu cikin littafin "mutum, wannan dinnan da ba'a sani ba " littafin malami me fidan mutum da kuma sanin ilimin halittan mutum dan faransa me suna Alexis Caryl wanda ya samu kyautan duniya ta noble: lallai neman sanin Allah abune wajibi ga ko wane mutum, kamar yadda mutum ke wayan gari nacimma nasara da kokarin kansa cikin wasannin motsa jini, to akwai yiwuwar wani mutum ya idan yayi amfani da abubuwan jin dadin sa da kuma ibadar sa zai iya kaiwa zuwa ga sanin ruhaniya, itace wacce tana haifar da natsuwa ta hanyar da mutum ya fuskanta. Lallai karfin cikin zuciyar mutum da haske na ruhani da son allah da natsuwa marar iyaka da kuma samun addini wannan duka alama ce ta hakikanin zuciya wacce muke daukan ta a matsayin tanaji a dunkule na hakika. Lallai abubuwan da suke sanar da Allah da alamomin sa suna kai wa zuwa ga hakikar ta karshe ta hanyar sawwara me kyau a saman mutum, mutum da kashin kansa yana kokarin kaiwa ga hakika ba tare da yagani ba kasancewar fidira ta hakika. Karkashin wannan manufa ne mutum yake kai kansa zuwa ga jarabawa masu hatsari wanda babu wanda zai iya kare masa hakan, wanda hakan zai iya kai zuciyar mutum zuwa ga haduwa da ruhi ta hakika ko kuma akasin haka..!!
Hakika mutane sun shagaitu da ilimi daga barin addini kuma sunyi murna da abunda ke hannun su na ilimi suka ganu wasu abubuwan da suke boye sukayi zaton cewa basu da wata bukatar addini, wannan zaton nasu ya ginu ne akan wasu addinai wanda aka caccanza su karkashin karnin tsakiya wacce ya haramta ilimi da neman sani sai ta hanya wanda yake tafiya tare da siyasar cuci da kuma fadakarwan ta da tarihinta wanda ake ganin abunda suka aikata na nesantar da zamantakewa cikin hakkin mutum da malamai daga gare sun a musamman, wannan shine abunda yasa mutane suke zanga zanga ga coci da kuma karantarwanta wanda ya sabawa fidira da hankali, Koran mutane daga addini wanda basu damu da hakan ba sai maguzanci ya yadu ta dalilin haka, amma shi musulunci ya warware hakan ta yadda yabude kofa ga malamai ya kuma kwadaitar akan neman ilimi da kuma zaburar akan sa ya sanya shi cikin manyan ayyukan bauta wanda ake samun kusancin Allah dasu, Allah madaukaki yace: " kace shin wanda ya sani zayyi daidai da wanda be sani ba, hakika yana tunatar da masu tunani ne kawai (9)" suratul zumar.
Hasalima farkon surar da aka fara saukarwa ga manzon Allah s.a.w tana kira ne zuwa ga karatu da neman ilimi da sani, allah madaukaki yace: " kayi karatu da sunan ubangijinka wanda yayi halitta (1) ya halicci mutum daga gudan jini (2) kayi karatu da ubangijin ka me karamci (3) wanda ya sanar da alkalami (4) ya sanar da mutum abunda be sani ba (5)" suratul alaq.
Kuma be umurci annabin sa ba da neman Karin wani abu cikin al'amuran duniya face ilimi saboda matsayin sa da daukakar sa da darajar sa a musulunci, Allah madaukaki yace: " kuma kace ya ubangiji na ka karamun ilimi (114)" suratu daha.
Kuma musani cewa duk inda mutane suka kai ga ilimi da sani ilimin su da sanin su kadan ne kayyadajje, sun san wani abu wasu abubuwa dayawa sun bace masu wannan shine abunda Allah ya karfafa da fadin sa cewa: " ba'a baku komai ba cikin ilimi face dan kadan (85)" suratul isra'i. lallai ci gaba ta bangaren ilimi daga wannan al'umma zuwa wancan dalili ne akan samuwan Allah na gaskiya wanda ilimi zai koma gare shi a karshe, saboda ko wani malami akwai malami sama dashi wanda yafi shi sani har akai ga mahalicci madaukaki, kuma Allah yayi gaskiya cikin fadin sa cewa: " kuma sama ga ko wani malami akwai malamin daya fi shi ilimi (76)" suratu yusuf.
Likita dan faransa Alexis Caryl yana cewa cikin littafin sa me sunan "mutum, wannan dinnan wanda ba'a sani ba": " hakika ya bayyana cewa dukkanin ilimin da yake da alaka da mutum baya isan bukatar mu game dashi kuma kasawa me tsanani shine ilimin mu game da kan mu har yanzu sabon abu yake wanda Kaman yanzu aka fara shi, ya kuma kara cewa: " lallai bazamu iya kaiwa zuwa ga sirrukan mutum ba ta wannan hanyar wanda muke amfani da ita wurin sanin asalin abubuwa, shi kuma kasawar mu babba kuma mai muhimmanci itace dukknin karatun mu na dabi'a na karantar gawar mamaci, bazamuji dadi ba bayan mutum ya gama rayuwan sa.
Haka dai ilimin da dan adam suke gazawa game da shiryar da halittu da kuma warware matsalolin su, wasun su ma suna amfani da ita ne ta hanyar kuskure domin inkarin wahayi da karyata annabawa da kore addini da yada maguzanci.
Lallai yada barna cikin rayuwan yamma da kuma lallacewar halaye na kwarai da makamai kare dangi wanda suke halaka gonaki da dangantaka da yaduwar cutuka na zamantakewa masu hatsari wanda suke kawo cikas ga al'umma da yaduwan riba da gurbata yanayi duka bazasu fitar da rayuwan yamma ba cikin halin da suke ciki sai dai idan sun koma zuwa ga abunda annabawan Allah amincin Allah ya tabbata agaresu suka zo dashi kuma musamman ma sakon Muhammad s.a.w,shi ne sako na karshe kuma cikamako, ya share sakonnin da suka gabata, Allah madaukaki yace: " bamu aikeka ba face rahama ga talikai baki daya (107)" suratul anbiya'i.

Karin bayani:
•    Bangarorin da wannan littafi ya tabo bangarori ne wanda takaitattu sosai, wannan littafi kamar soman tabi ne da ishara saboda gudun kada a tsawaita ma makaranci me daraja duk wanda yake son neman Karin sani dalla dalla game da wasu bangarorin wanda yake da himma akan haka to Alhamdulillah al'amarin a saukake yake kuma me sauki ne nayin bincike cikin shafin addinin musulunci wanda suke da tabbaci da inganci ko kuma ta hanyar kiran cibiyoyi na musulunci wanda suke da yawa cikin kasashen duniya.
•    Muslunci addini ne da manhaji saboda haka shi baya canzawa amma kuma musulmai sune wanda suke aiwatar da shari'o'insa da manhajin sa saboda haka suna canzawa, zakaga wasu daga cikin musulmai wanda suke karya da yaudara da algushi… zuwa dai karshe da aiwata abunda da manhaji ya hana kuma shari'a ya tsawatar akan sa wanda hakan ana samun sa cikin dukkanin addinai wanda hakan shi zai bayyana mana cewa matsalar da gazawar yana cikin aiwatarwa ne na wasu daga cikin musulmai ga wannan shari'a matsalar da gazawar bawai daga shari'ar bace, baya halatta hadawa tsakanin shari'a da aiwatar da ita baza'a yima musulunci hukunci ba ta hanyar hukunci ga ayyukan wasu daga cikin musulmai wanda suke kuskure wurin dabbaka manhajin sa da karantarwan shari'a.
•    Shari'u na sama sashin su yana cike sashi ne, asalin su daya ne wanda shine (tauhidi) ammam kuma shari'un su sun banbanta, suhufi Ibrahim da zabura da attaura da injila dana karshen su alkur'ani wanda shine shari'ar Allah wanda yake cika makon shari'u kuma yana cika su ne, baya dacewa a fahimta daga hakan tawayan sauran addinin na sama, saboda duk wanda ya rage wani shari'a cikin shari'un Allah na sama ya kafurta kuma ya fita daga cikin musulkunci, Allah madaukaki yace: " kuce munyi imani da Allah da abunda ya saukar mana da abunda ya saukar ma Ibrahim da Ismai'l da Ishaq da Yakub da Asbada da abunda akaba Musa da Isa da abunda akaba annabawa daga ubangijin su, bama banbanta wani daga cikin su kuma lallai mu musulmai ne a gare shi (136)" suratu al'imran.
Ko wace shari'a cikin zamaninta tanada kamala tazo daidai da bukatun mutanen da aka aiko masu ita, manzon Allah s.a.w yace yana bayyana hakikanin hakan: " lallai misali na da auran annabwan da suka gabace ni kamar misalign mutum ne da ya gina gina ya kyautata ginin ka kawantashi, sai dai yabar wurin bulo daya a lungu, sai mutane suka rika kewaye gidan yana burge su suna cewa: shin kasanwa wannan bulo din? Sai yace nine bulo din kuma nine cika makon annabawa" buhari da muslim da ahmad da ibn hibban da tirmizi ne suka rawaito shi.
Addinai na sama Kaman gida ne wanda annanbawa sukayi tarayya gabaki dayan su wurin gina shi, ko wani annabin da aka aiko sai ya daura bulo wanda wannan gini ya kammalu da aiko manzon Allah Muhammad s.a.w, addinin sa da shari; ar sa sun kasance bulo na cika wannan gini.
•    A fadin duniya ba tare da kebe wani wuri ba zamuga cewa musulunci shine addinin da ake yakan sa sabanin sauran addinai da mazhabobi na daban kaba kanka lokaci domin tunani da binciken dalilin wannan kiyayya haka domin sanin dalilin haka kuwa shine kasancewar sa yana sanya mutum ya bautawa ubangijin sa, amma sauran addinan kuma suna sanya mutum ne bautan wani mutum wannan itace amsa ta wani bangare ta wani bangare kuma na daban shine kasancewar sa addini ne wanda be yarda da zalumci ba da ta'addanci da dagawa da mugunta, Allah madaukaki yace cikin hadisin kudusi: " yaku bayina lallai na haramta zulumci akai na sannan kuma na haramta maku shi a tsakanin ku saboda haka kada kuyi zalumci" sahihu muslim.
Kuma be yarda da girman kai da jiji da kai ba, Allah madaukaki yace: {“ kuma kada ka juya kuncin ka ga mutane kuma kada kada kayi tafiya a ban kasa kana mai taqama lallai Allah baya san dukkan mai taqama mai alfahari (18) kuma ka takaita a cikin tafiyar ka kuma ka rage sautin ka lallai mafi munin sautuka shi ne sautin jaki (19) “} suratul luqman.
Kuma be yarda da cin kudiyar mutane ba da barna, Allah madaukaki yace: " kada kuci dukiyoyin ku a tsakanin ku da barna kuma ku kai su zuwa ga mahukunta domin su baku hanyar cin dukiyan mutane da zanubu alhani kuna sane (188)" suratul bakara.
Kuma be yarda ya wulakantar da hakkokin mutane ba, Allah madaukaki yace: " kada ku rika toye ma mutane abubuwan su" [suratul hud ayata 85, da suratul shu'ara'I ayata 183].
Kuma be yarda me karfi ya danne mara karfi ba, Allah madaukaki yace: " shi maraya kada a danne sa (9) shi kuma matambayi kada a tsawata masa (10)" suratul duha.
Kuma be yarda me kudi yaci hakkin talaka ba, Allah madaukaki yace: " kada masu rowa da abunda Allah ya basu daga cikin falalar sa suyi tsammanin hakan alheri ne a wurin su a'a hakan sharri ne a garesu kuma da sannu za'a rataya masu abunda suke rowa dashi ranan alkiyama kuma Allah ne zai gaje dukkanin abunda suke sammai da kasa, kuma Allah me bada labari game da abunda kuke aikatawa (180)" suratu al'imran.
Kuma be yarda mutum da bautar da mutane ba domin bukatuwar su, Allah madaukaki yace: " ku kyautata lallai Allah yana son masu kyautatawa (195)" suratul bakara.
Kuma be yarda da barna ba da yadata a tsakanin daidaikun mutane ko kuma al'umma, Allah madaukaki yace: " kada kuyi barna a doron kasa bayan gyaruwan ta lallai hakan shine yafi zama alheri agareku idan kun kasance muminai (85)" suratul a'araf.
Wannan wurin gabar tambaya ce ga dukkanin me hankali cewa: addinin da wannan shine asalin sa shin ya kamata ace ana yakar sa da adawa dashi?
Wannan shine musulunci me amfani ga mutum kamar yadda manzon Allah s.a.w ya bayyana cikin fadin sa: " mutumin da yafi soyuwa cikin mutane agun Allah shine wanda yafi amfanar da mutane, kuma mafi soyuwan ayyuka agun Allah shine ka sanyawa musulmi fara'a a fuskar sa ko kuma ka yaye masa wata damuwar sa ko kuma ka biya masa bashin sa ko kuma ka Koran masa yanwu" daru khudniy ne ya rawaito shi, da ibn asakir kuma albani ya inganta shi cikin littafin sahihul jami'u 3289, alsahiha 426.
Da kuma soyayya ga mutum, manzon Allah s.a.w yace: " imanin dayan ku bazai cika ba har sai ya soma dan uwansa abunda yake soma kansa" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Da aminci ga wanda ya zauna dashi cikin aminci da kuma yaki ga wanda ya yake shi, Allah madaukaki yace: " Allah baya hanaku ga wanda basu yake ku ba cikin addinin ku sannan kuma basu fitar daku ba daga cikin gidajen ku da kuyi masu biyayya kuma ku masu adakci lallai Allah yanason masu adalci (8) kawai dai Allah ya hanaku biyayya ne ga wanda suka yake ku a cikin addinin ku kuma suka fitar daku daga cikin gidajen ku kuma suka taimaka ma wasu wurin fitar daku daku daga gidajen ku, duk wanda yayi masu biyayya to wannan sune azzalumai (9)" suratul mumtahana.
•    Lallai canzawa daga addini zuwa wani addini na daban, abune bayyananne matuka cikin duniya, daga cikin yahudawa wanda suakafi mutane tsananin riko ga addinin su munga cewa sun canza daga addinin su zuwa wani addinin, kuma dayawa cikin kiristoci sun wayi gari basu da gamsuwa da addinin su sai suka fara bincike acan da nan domin samun abunda zai kosar masu da kishin su na zuciya kuma su samu natsuwa na zuciya, haka suma yan addinin hindusawa da buzawa da saik wanda suka gina addinin su akan karairayi da tatsuniyoyi sun kama abun da kiristoci suka bari saboda rashin gamsuwar su dashi, sabanin addinin musulunci wanda duk wand ya shige shi zayyi wahala kaga ya fita daga cikin sa hasalima kididdga ya nuna cewa shine addini wanda ya yadu cikin sauri a wannan duniya, addini ne wanda aka yakesa da dukiya da mazaje domin su kange mutane daga gareshi kuma su hanashi yaduwa amma dukda haka burin su be cika ba sai suka wayi gari Kaman wanda yake sama wuta karmami ba abunda yake kara mata sai ruruwa, saboda kasancewar sa addini ne wanda Allah yayi alkawarin kiyaye shi da taimakon sa, Allah madaukaki yace: " suna son kashe hasken Allah da bakunan su Allah kuma yaki hakan sai ya cika hasken sa koda kuwa kafirai basa son haka (32)" suratul tauba.
    Wancan wanda suka fara canzawa daga addinan su saboda rashin gamsuwa dashi, ina mika masu kirana zuwa ga zaben abunda yafi da addini wanda yake da cika da kamala, addinin musulunci, addinin gaskiya wanda baya sabawa hankali kuma bayacin karo da fidira.
Wanene Allah?
        Ya kamata gabanin muyi bayanin wanene Allah ubangijin talikai muyi bayani akan maganar hankalin mutum ta fuskar ikonsa wanda yake da iyaka wanda Allah ya halicce sa da shi ya kuma kebance mutum da shi akan sauran halittu domin yayi amfani da shi domin isa ta hanyar tunani game da halittun sa da amfani da misali cikin abunda zai dawo masu da amfani cikin addinin su da duniyar su, misali rai wacce take motsi da wannan jiki wanda idan babu wannan ran zata zama gawa mara motsi, dukda cewa bazamu iya amfani ba da gabban mu dani da tabawa domin kuwa bata gani sannan kuma bata jin kamshi bata tabawa ko jin magana kuma ta hankulan mu sun gaza wurin sanin hakikanin ta, sai dai munyi imanin cewa akwaita fa, kuma halitta ce cikin halittun Allah, to ya kake tsammani ga wanda ya halicce ta ya kuma samar da ita? Saboda haka ne lokacin da aka tambayi manzon Allah s.a.w akan rai, sai amsar yazo daga wurin Allah madaukaki cewa: " suna tambayan ka game da rai kace masu rai yana cikin ikon ubangijina kuma ba'a baku ilimi ba face dan kadan (85)" suratul isra'i.
Sayyid kudub Allah yayi masa rahama yana cewa: " manhajin da alkur'ani ya tafi akansa shine manhaji me karfi na bawa mutane amsa akan abunda suke bukata zuwa gareshi, da abunda suke iya riskan sa ta hanyar sani da isahankalin su da Allah ya basu bashi da ikon cikin abunda baya samarwa da kerawa, ko kuma sauran wurin da bai mallaki hanyar sa ba, hakan baya nufin an hana hankalin mutum bane yin aiki, sai dai ana fadakar da wannan hankalin ne cewa fa yayi aiki a daidai iyakan sa, da kuma wurin sa da zai iya riska, babu alama na sahu ga mutum daya bace hanya cikin dimuwa. Da kuma tafiyar da iko cikin abunda hankali bazai iya riskan sa ba, saboda be mallaki hanyar riskan hakan ba.
Idan hakan ya kasance ga wasu halittu cikin halittun Allah to menene tunanin ka game da mahalicci da kuma kokarin sanin asalin sa, wannan abu ne wanda bazai taba yiwuwa ba kuma hankalin mutum bashi da ikon kewaye hakan ko kuma sanin sa sannan kuma ko kari da bata lokaci wurin sanin haka zai zama wasa da hankali, hankali halitta ce wacce take da iyaka bazai iya wuce wannan iyaka ba, tunani akan asalin Allah kuma ya wuce wannan iyaka sannan kuma daurama hankali ne abunda bazai iya ba saboda al'amarin Allah ya kareta cikin fadin sa cewa: " kuma bazasu taba iya karade shi ba da sanin sa (110)" [suratu daha] da kuma fadin sa " idanu baza iya ganin sa amma shi yana ganin idanu kuma shi me tausayi ne kuma me bada kabari (103)" suratul an'am.
        Misalin wanda yake shagaltar da hankalin sa da wannan al'amari kamar misalin wanda ya sanya kaya ne me nauyin tan biyar a cikin mota wanda bata daukan sama da tan daya wannan babu shakka cewa ya daura mata abunda bazata iya ba motsawa ba da kuma sanadin lallacewar ta, haka hankalin mutum yake a wurin tunanin asalin Allah ko kuma tunanin abubuwan gaibu wanda ba'a sanin su sai ta hanyar abunda aka ba annabawa labarin sa Amincin Allah ya tabbata a agare su.
        Hakika mutanen yeman sun tambayi manzon Allah s.a.w cewa: mun zo ne domin tambayan ka akan wannan al'amari, sai manzon Allah s.a.w yace: " Allah ya kasance kuma babu wani abunda ya kasance bayan shi" [yanki ne na hadisin sahihul buhari]


A ina Allah yake?
Lallai Allah madaukaki yana sama, akan al'arshin sa akan sammmai ta bakwai sai dai wasu maguzawa zasu iya tambaya cewa a ina Allah yake suna nufin asalin wurin da yake cikin wannan duniya, sai muce masu lallai Allah madaukaki shine wanda ya halicci zamani da wuri, wuri da zamani halittu ne cikin halittan sa saboda haka bazasu iya karade shi ba kuma zamani baya mas hukunci, hakika ya kasance kuma babu abunda ya kasance gabanin sa ko kuma bayan sa ko saman sa da zatin sa ya daidaita akan al'arshin sa kuma ilimin mutum bai kai kusa gareshi ba, Allah madaukaki yace: " shine na farko da karshe da zahiri da badini kuma shi masani ne ga dukkan komai (3)" suratul hadid.
 Siffofin Allah baza'a iya karade su ba cikin wannan littafi dan karami sai dai zamu ambaci wasu daga cikin siffofin Allah wanda ya halicci wannan duniya ya kuma samar dashi kamar haka:
•    Shine Allah daya bashi da abokin tarayya kuma bashi da kishiya ko makamanci cikin Allantakar sa da renon sa da siffofin sa, Allah madaukaki yace: " kace shine Allah shi kadai (1) Allah wanda ake nufi da bukata (2) be Haifa ba kuma ba'a haife shi ba (3) kuma babu wani tamkar a gareshi (4)" suratul ikhlas.
•    Shine Allah rayayye rayuwa ta har abada wanda baya mutuwa, Allah madaukaki yace: " shine rayayye babu wani abun bautawa da gaskiya bisa cancanta sais hi saboda haka ku bauta masa shi kadai gareshi addini yake, godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai (65)" suratul gafir.
Sauran mahalukai kuma da ba shi ba dukanin su zasu kare kuma zasu gushe, Allah madaukaki yace: " dukkanin abunda ke kanta me karewa ne (26) fuskan ubangijinka ne kadai zai wanzu ya cancanci a girmama da karamci (27)" suratul rahman.
•    Ya tsayu da zatin sa ya wadatu daga bayin sa baya bukatar wanda zai karfafa shi ta ko wane fuska sannan kuma shine wanda ya tsayama wanin sa, babu wanda ya iya ya tsayu babu shi, Allah madaukaki yace: " Allah wanda babu wani abun bauta da gaskiya bisa cancanta sai shi, rayayye tsayayye, gyangyadi baya daukan sa ko kuma bacci, dukkanin abunda suke cikin sammai da kassai nashi ne" suratul bakara.
•    Shi me hikima ne cikin ayyukan sa da maganganun sa da ikon sa, yana sanya komai a wurin sa cikin hikimar sa da adalcin sa, me hikima ne cikin halittun sa da kuma tafiyar dasu, kuma masani ne da maslahar su, Allah madaukaki yace: " shine mabuwayi akan bayin sa kuma shi me hikima ne kuma masani (18)" suratul an'am.
•    Shi ne me iko babu abunda ya gagare shi cikin sammai da kassai, Allah madaukaki yace: " duk inda kuke sai Allah yazo daku baki dayan ku, lallai Allah me iko ne akan dukkan komai (148)" suratul bakara.
•    Kuma shi masani ga komai ya kuma karade komai da karadewan sa cikakke, jahilci be taba riga ilimin sa kuma mantuwa bai taba samun sa ba, yasan abunda yake boye, yasan abunda ya kasance da abunda zai kasance da dukkanin wani mahaluki da abunda be kasance ba da zai kasance kuma ya zai kasance din, Allah madaukaki yace: " babu wani abu da yake boyewa ga ubangijin ka na kwayan zarra cikin sama ko kasa ko kuma wanda yafi hakan kankanta ko kuma wanda ya fishi girma face yana cikin littafi bayyananne (61)" suratu Yunus.
•    Shine mahaliccin komai da samar dashi daga rashin sa, Allah madaukaki yace: " shine Allah mahalicci me aiwatar da abunda yayi niyya na halitta me sawwara halitta yadda yakeson su, gareshi sunaye masu kyawu suke, abubuwan da suke sammai da kasa suna masa tasbihi kuma shi mabuwayi ne me hikima (24)" suratul hashri.
•    Shine me azurta dukkanin bayin sa, yana basu abaunda suke bukata na rayuwan su, Allah madaukaki yace: " babu wata dabba a doron kasa face ga Allah arzikin ta yake kuma yasan iyakan zamanta anan duniya da makomarta bayan mutuwar ta komai yana cikin littafi a bayyane (6)" suratu hud.
•    Lallai shie me iko ne akan rayawa da kashewa da kuma tayar da mutane bayan mutuwar su da hisabi, Allah madaukaki yace: " kace Allah shine yake rayaku sa'annan ya kashe ku sa'annan ya taraku zuwa ranan alkiyama wanda babu kokwanto akan sa sai dai dayawa daga cikin mutane basu sani ba (26)" suratul jasiya.


Wannan shine Allah:
-    Me rahama yanason bayi masu rahama, manzon Allah s.a.w yana cewa: " kuji tausayin wanda suke kasa sai wanda yake sama yaji tausayin ku" hadisi ne ingantacce, tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
-    Me gafara ne kuma yana son bayin sa masu yafiya, Allah madaukaki yace: " ka riki yafiya sannan kuma kayi umurni da kyakkyawan aiki kuma ka kawar dakai daga jahilai (199)" suratul a'araf.
-    Me karamci ne kuma yanason bayin sa masu karamci, manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah me karamci ne kuma yana son masu karamci, kuma yanason kyawawan dabi'u kuma bayason munanan halaye" baihaki ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi cikin sahihul jami'u 1744, da kuma alsahiha 1378.
-    Me sauki ne da rangwame kuma yanason bayin sa masu saukakawa, manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah me saukakawa ne kuma yana son saukakawa sannan kuma yana tabbatar da bayin sa masu kiran mutane da saukaka irin tabbatarwan bayayi ma masu tsanantawa ko kuma abunda yake ba wanin su" muslim ne ya rawaito shi da ibn hibban.
-    Me rufa asiri ne kuma yana son bayin sa masu rufa asiri, manzon Allah s.a.w yace: " wani mutum bazai rufama wani asiri ba a nan duniya face Allah ya rufa masa asiri a lahira" muslim ne ya rawaito shi da Ahmad.
-    Me kyau ne kuma yana son kyau, kuma yanason bayin sa masu tsabta da tsarki, manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah me kyau ne kuma yanason kyau" sahihu muslim.
-    Me kunya ne kuma yanason bayin sa masu kunya, manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah madaukaki me hakuri ne kuma me kunya ne da kuma rufa asiri sannan kuma yana son kunya da rufa asiri, idan dayan ku zayyi wanka ya suturta kansa" hadisi ne ingantacce Ahmad ne ya rawaito shi da abu dawud da nasa'i kuma lafazin nashi ne, sannan albani ya inganta shi cikin irawa'i 2335.


Dalilai na hankali akan cewa akwai Allah yana nan
Wani bamaguje ya tambaya sheikh Ahmad Deedat Allah yayi masa rahama cewa: ya zakaji da za'ace ka mutu kaga cewa lahira karya ne?
Sai yace masa hakan befi muni ba da yadda zakaji a lokacin da zaka mutu zakasan cewa lallai gaskiya ce!
        Wata kila wannan amsar ta wadatar ga dukkanin wani mai hankali domin riske kansa da kuma daukan izina da himma game da abunda ke gaban sa, me wayau shine wanda yayi addini da aiki domin bayan mutuwar sa, kila daga cikin muhimman dalilai akan kasancewar Allah shine dalili na ji wanda babu wanda ya isa yayi inkarin haka, lallai duk wanda ya kirkiro wannan duniya me dadi da tsari na samar da kasa da sama da halitta dukkanin abubuwan dake cikin su na mutum da dabbobi da kwari da duwatsu da bishiyoyi da wata da rana da taurari da rafi da kogi da makamantan su wacce take tafiya akan tsari wanda aka hukunta mata hakan wanda da ace wani abu a cikin sa zai lallace da ba'a samu rayuwa ba, sai kuma ace wanene ya samar da wannan ya kuma tsaya akan sa da hukunta halittan sa da wannan tsari na ban mamaki? Dayan abubuwa uku ne babu na hudun su na hasashe:
Na farko: kodai ace wannan duniya da abunda ke cikinta na tsari da sauran duniyoyi ma sun samar da kansu ne da kansu haka kawai wanda wannan hasashen bazayyiwu ba lalatacce ne tun asalin sa saboda dukkanin wani abu da ya samu lallai dole akwai wanda yayi shi, sannan dukkanin wata halitta dole ne akwai wanda ya halicce ta sannan dukkanin ko wani sabani akwai wanda ya sabbaba haka.
Na biyu: ko dai ya kasance cewa wannan duniya wani abune ya samar dashi wanda a cikin sa abun yake wanda shima wannan hasashen be dace da hankali ba kuma hankali bazai karbe shi ba saboda abu baya halittan irin sa.
Na uku: ko dai ya kasance cewa wannan duniya da abunda ke cikin ta akwai wanda ya halicce ta wanda baya cikin ta wanda wannan hasashen shine wanda hankali zai karba kuma yanayi yana gasgata shi wanda wannan mahaliccin shine Allah ubangijin talikai wannan shine abunda dukkanin masu kadaita Allah muminai sukayi imani dashi na cewa akwai Allah na wannan duniya amma wanda basu ba maguzawa suna cikin shakka game da hakan, Allah yayi gaskiya cikin fadin sa cewa: " ko dai shin an halicce su ne ba daga komai ba ko dai sune masu halittan (35) ko dai sune suka halicci sammai da kasa, hakika basa sakankance wa (36)" suratul dur.
        Me yiwu daga cikin dalilan canzawan dayawa cikin mutane da zaman su maguzawa shine hukuncin hankalin su cikin abubuwan da be dace yayi hukunci ba aciki, saboda hukuncin hankali yana kasancewa ne akan abunda yake halitta irin sa amma kuma mahalicci babu shakka hankali zai gaza wurin riskan sa, saboda haka ne musulunci ya bayyana maganin na tsira daga hakan sai manzon Allah s.a.w yace: "(shedan yana zuwa ma dayan ku sai yace masa wanene ya halicci kaza kuma wanene ya halicci kaza har sai yakai g ace masa wanene ya halicci ubangijin ka? Idan dayan ku yaji haka ya nemi tsarin Allah kuma ya daina wannan tunani.)" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.


Dalilai na hankali akan kadaitar Allah:
        Hakika alkur'ani ya bayyana cewa abune wanda bazeyiwu ba ya kasance Allah yana da abokin tarayya ko kuma kishiya saboda samun abokin tararra nakasa ne wanda yake kore kamala cikin hakkin Allah saboda haka ne mafiya yawan ayoyin alkur'ani suke tsrakake Allah daga dukkanin wani abokin tarayya da nakasu da aibu da kuma dukkanin abokin tarayya, Allah madaukaki yace: " shine Allah wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, almalik, alkuddus, assalam, almumin, almuhaimin, al azizu, aljabbaru, al mutakabiru tsraki ya tabbata ga Allah daga abunda suke masa shirka dashi (23)" suratul hashri.
Ya tabbatar da dalilai na hankali da mandiki wanda hankali me hankali zai isa dasu zuwa ga kore tarayya ga Allah sannan kuma da rashin yiwuwar hakan cikin hakkin sa daga cikin su akwai:
•    samuwar wasu alloli tare da Allah ya kunshi cewa akwai iko cikakke ga ko wanne daga cikin su – saboda hakan yana cikin siffofin allantaka – ya zama cewa kenan samuwar wani abokin tarayya ga Allah kowa zai so wani abu sabanin abun da dayan yake so daganan sai fada ya kaure da husuma wanda zai jawo lallacewar duniya saboda haka, Allah madaukaki ya tsarkaka daga samun abokin tarayya, sai yace: " da ace akwai wasu allolin bayan Allah da duniyar ta lallace, tsarki ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffatawa (22)" suratul anbiya'i.
•    kasancewar wani alla tare da Allah hakan ya kunshi ko wanne daga cikin su cewa yana da karfi da iko wanda zai bashi damar samun nasara da yaki a tsakanin su domin neman mulki da hukunci da wannan duniya daganan sai fada da jayayya da husuma ya faru a tsakanin su wanda hakan ya kunshi lallacewar duniya saboda haka, Allah madaukaki ya tsarkaka daga shirka, Allah madaukaki yace: " kace da ace akwai wani alla atare dashi kamar yadda suke fadi lallai kuwa da sun nemi hanyar dagawa ga me al'arshi (42) tsarki ya tabbatan masa kuma ya daukaka daga abunda suke fadi daukaka babba (43)" suratul isra'i.
•    kasancewar wasu alloli tare da Allah ya kunshi raba duniya kenan a tsakanin su kowa ya tafi da abunda ya halitta, cikin haka akwai barna me girma wanda bazai boyu ba ga ko wani me hankali, hakan bazai taba yiwuwa ba ta bangaren Allah, Allah madaukaki yana cewa: " Allah be riki da ba kuma babu wani alla a tare dashi, dan kuwa da ko wani allah ya tafi da abunda ya halitta kuma da wani ya nemi daukaka akan sashin sa,tsarki ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffanta shi dashi (91)" suratul muminun.
        Shine Allah shi kadai yake wanda ake nufi da bukata bashi da bukatar wani tarayya ko kuma mata ko yaro ko mataimaki, Allah madaukaki yace: " kace godiya ta tabbata ga Allah wanda bashi da yaro kuma bashi da abokin tarayya cikin mulki kuma bashi da majibincin al'amura daga kaskanci kuma ka girmamashi hakikanin girmamawa (111)" suratul isra'i.
        Ya kuma kara cewa: " shine wanda ya kirkiri sammai da kasa taya zai samu yaro bayan bashi da mata kuma ya halicci komai kuma shi ne masani ga dukkanin komai (101)" suratul an'am.


Shin Allah yanada bukata daga halittun sa?
        Sanannen abu ne ga hankali cewa duk wanda ya mallaki wani abu to yana da iyanci na yin amfani da abunda ya mallaka ganin daman sa – Allah shine me misali na kololuwa – Allah madaukaki shine wanda ya halicci duniya da abunda ke cikinta shine mamallakin ta kuma ya juyata yadda yake so a duk lokacin daya so yadda kuma yaso, mutum halittace cikin halittun sa, Allah madaukaki yace: " lallai ubangijin ku shine Allah wanda ya halicci sammai da kasa cikin kwanaki shida sa'annan ya daidaita akan al'arshi, dare yana lullube rana yana neman sa da gaggawa da rana da wata da taurari horarru ne da umurnin sa, ku saurara halitta da umurni nashi ne, tsarki ya tabbata ga Allah ubangijn talikai (54)" suratul a'araf.
        Shine me raba arziki da kuma jujjuya al'amura na ruwa da fari da girgizan kasa da talauci da arziki da rayuwa da mutuwa da lafiya da rashin lafiya da tsira da tabewa duka hakan cikin hukimar da Allah yake son su ne kuma yayi umurni yana kaddara su kuma babu wani mahaluki da ya isa ya hana hakan ko kuma ya kalubalance shi akan aikin sa ko kuma ya fita karkashin mulkin sa da da yadda yake so" ba'a tambayan sa akan abunda ya aikata amma su ana tambayan su (23)" suratul anbiya'i, Allah madaukaki kuma yace: “ Ubangijin ka yana halittan abunda yaso kuma yana zaban wanda ya so, basu suke da zabi ba, tsarki ya tabbatan masa kuma ya daukaka daga abunda suke masa tayarra dashi (68)" suratul kasas.
        Hikimar sa a bayyane take ana sanin ta ba karam ba tana a boye bane yadda baza'a santa ba, abunda ya kaddara wanda zahirin sa yake zama sharri badinin sa zai iya zama alheri amma mu bamu sani ba ko kuma akasin haka, Allah madaukaki yace: " kuma kila ku ki abu amma alheri ne a gareku kuma kila ku so abu amma sharri ne a gare ku, Allah shine masani amma ku baku sani ba (216)" suratul bakara.
        Wanda ya samar da wannan duniya yanada ikon samar da wanin ta cikin abunda ya sani wanda mu bamu sansa ba, bashi da bukata zuwa ga halittun sa hasali ma sune mabukata zuwa gareshi cikin dukkanin ayyukan su, Allah madaukaki yace: " yaku mutane kune mabukata zuwa ga Allah shi kuma Allah me wadata ne kuma me godiya (15) idan yaga dama zai tafiyar daku sai yazo da wasu halittu na daban (16) kuma hakan ba gagararre bane agun Allah (17)" suratul fadir.
        Kamar yadda jikin su yake da bukata zuwa ga ababen rayuwa na dole domin rayuwa kamar su abinci da abinsha haka zukatan su ke da bukata zuwa ga mahaliccin wanda zasu rika bauta mawa suna kum akai masa bukatun su suna kuma kankantar dakai a gare sa suna jin natsuwa da aminci na kusancin sa, kamar yadda jariri yakejin aminci a tsakanin cinyar mahaifin sa haka mutum yake da bukata zuwa ga mahalicci wanda zai baje a tsakanin sa ya kuma rika mika masa koken sa zuwa gareshi, karkashin kaskantar dakai da jayuwa da bauta ga wannan mahalicci zuciya take samun abinci da natsuwa da tsira, kuma bazata iya samun wannan abinci ba sai ta hanyar manzanni wanda suke zuwa masu da wahayi daga wurin mahalicci wanda ya halicci zuciyar ka ya kuma sanya masa abinci ta hanyar abunda suke zuwa dashi na sharia, Allah madaukaki yace: " shin wanda yayi halitta be sani ba kuma shi me rangwame ne kuma me bada labari (14)" suratul mulk.
        Abunda ke karfafa rayuwan mutum da jujjaya dukkanin al'amuran su dukkanin haka yana komawa ne zuwa ga ganin daman sa da kuma iradan sa, be halicce su domin samun karfi daga gare su kuma be halicce su ba domin wasa kuma be halicce su domin su amfanar dashi ko cutar dashi ba, shi mawadaci ne daga garesu su kuma bukata zuwa gareshi kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari cikin hadisin kudusi: " yaku bayina lallai bazaku iya kaiwa ga cutar dani ba bare ku cutar dani kuma bazaku iya kaiwa ga amfanar dani ba bare ku amfanar dani, yaku bayi na da ace farkon ku da karshen ku mutanen ku da lajannun ku zasu kasance akan zuciyar mutum daya daga cikin ku wanda yafi ku tsoron Allah hakan zabai karamun komai ba cikin mulki na, yaku bayina da ace farkon da karshen ku mutanen ku da aljannun ku zasu kasance akan zuciyar wani mutum wanda yafiku fajirci hakan bazai ragemun komai ba cikin mulki na, yaku bayi na da ace farkon ku da karshen ku mutanen ku da aljannun ku zasu kasance a wuri daya sais u tambayeni sai naba kowa abunda ya tambaye ni hakan bazai ragemjun komai ba cikin abunda nake dashi sai kamar abunda allura zai rage idan an tsoma shi cikin kogi an fito dashi, yaku bayi na wannan ayyukan ku ne nake kididdigewa sa'annan ya sakanya maku dasu duk wanda ya tarar da alheri to ya godema Allah wanda kuma ya tarar da akasin haka to kada ya zargi kowa sai kansa" sahihu muslim.
        Ayyukan bayi zai dawo masu koda alheri ko kuma da sharri, za'a masu hisabi akan su idan alheri mutum ya aikata zaiga alheri idan kuma sharri ya aikata zaiga sharri, daga cikin rahamar Allah da adalcin sa ya sanya hisabi da sakamako da lada da ukuba saboda kada me datti yayi daidai da me kyau, Allah madaukaki yace: " idan kun kyautata to kanku kuka kyautata mawa idan kuma kun munana shi ma haka" [suratul isra'I ayata 7].


Dalilan halittan mutum:
        Baya yiwuwa game hankali face ya sallama cewa ba'a halicci abubuwa ba sai dan hikimomi, mutum me hankali yana barrantar da kansa daga aikata wani abun cikin rayuwa ba tare da wani hakima ba wanda yake sonsa da hakan, to taya hakan bazai zama ga Allah wanda shine mafi hikiman masu hikama?! Allah madaukaki yace: " ko wanne acikin ku mun sanya musu shari'ar su da manhajin su, da Allah yaga dama da yasanya ku al'aumma daya sai dai don ya so jarabaku ne cikin abunda ya baku, saboda haka kuyi gaggawa cikin ayyukan alheri ga Allah makomar ku take sa'annan ya baku labari akan abunda kuka samu sabani akai (48)" suratul ma'idah.
        Lallai dukkanin abunda Allah ya halitta cikin wannan duniyan an halicce sa ne domin wata hikima kuma ba'a samar dashi ba face dan wata maslaha shin mun san hakan ko kuma bamu sani ba, Allah madaukaki yace: " bamu halicci sama da kasa ba da abunda ke tsakanin su haka kawai dan barna, wannan shine zaton wanda suka kafurta, boni na wuta ya tabbata ga wanda suka kafurta (27)" suratu saad.
        A hankalce be kamata ace ana tambaya ba don me Allah ya halicci mutum sai dai ya kamata a rika tambaya menene hikimar halittan mutum? Sannan kuma me ake nema daga garesu subi a lokacin rayuwar su?
        Lallai hikimar halitta babu wanda yasani sai Allah madaukaki bamusan komai ba cikin hikimar haka sai abinda Allah ya bayyana mana me tsarki da daukaka, kuma hakika ya bada labarin cewa hikimar halittan sammai da kasa da abunda ya yada a tsakanin su na halittu wanda babu wanda ya sani sai shi shine domin jarabtan mutane kamar yadda ya fadi me tsarki da daukaka: " shine wanda ya halicci sammai da kasa cikin kwanaki shida kuma al'arshin say a kasance akan ruwa domin ya jaraba ku ya gani wanene zai fi kyautata aikin sa" suratu hud ayata 7.
        Kuma Allah be halicci rayuwa da mutuwa ba face dan wannan hikimar, ajali a kaddare yake kuma a kayyade shi kuma an rubuta shi, lokacin dake tsakanin rayuwa da mutuwa kuma shine wurin yin jarabawa domin asan me kyautatawa dame munanawa a tsakanin sa da mumini da kafiri, Allah madaukaki yace: " wanda ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya jarabaku ya gani wanene zai fi kyautata ayyuka, kuma shi mabuwayi ne me gafara (2)" suratul mulku.
        Jarabawa Allah ya kaddara ta akan baban mutum Adam amincin Allah ya tabbata a gareshi yana cikin aljanna bayan yayi masa umurni da kada yaci wata itaciya shi da matar sa sai shedan yayi masu wasiwasi suka masa biyayya suka sabama ubangijin su kuma sun amsa laifin su suka tuba sai Allah ya amshi tubar su ya saukar dasu zuwa kasa domin ta zama wurin jarabawa a gareshi da zuriyan sa bayan sa, Allah madaukaki yace: " kuma munce ya adam ka zauna kai da matarka cikin aljanna kuma kuci dukkanin abunda kuke so a cikinta amma lkada ku kusanci wannan bishiya sai ku zama cikin azzalumai (35) sai shedan ya batar dashi akanta sai aka fitar dasu daga inda suke ciki, muka ce masu ku sauka zuwa doron kasa sashin ku suna gaba da sashi, kuma kuna da matabbata a doron kasa da jin dadi zuwa wani lokaci sananne (36) sai adamu ya amso wasu kalmomi daga ubangijin say a tuba sai ya amshi tubar sa lallai ya ksance me yawan amsan tuba kuma me jin kai (37) sai mukace ku sauka zuwa daga cikinta dukan ku, kuma idan shiriyata tazo maku duk wanda yabi shiriyata to babu wani tsoro a garesu kuma babu bakin ciki a tare dasu (38) wanda kuma suka kafirta suka karyata ayoyin mu wannan sune yan wuta suna masu dawwama acikinta (39)" suratul bakara.
        Saboda wata hikima wanda yake sonta ne ya sanya mutum suka zama khalifa bayan baban su Adam wasu musanya wasu domin ayi masu jarabawa wanda ya kaddara masu, Allah madaukaki yace: " shine wanda yasanyaku khalifofi a doron kasa ya kuma daukaka sashin ku akan sashin ku a daraja domin ya jarabaku cikin abunda ya baku, lallai ubangijin ka me saurin yin ukuba ne kuma lallai shi me yawan gafara ne ma jin kai (165)" suratul an'am.
Saboda haka ne sabani tsakanin mutane ya zama sunna cikin sunnonin Allah cikin wannan duniya, Allah madaukaki yace: " da ubangijin ka yaso daya sanya mutane sun zama al'umma daya sai dai bazasu gushe ba suna masu sabani (118) sai dai wanda ubangijin ka yaji kansa kuma saboda haka aka halicce su" suratu hud.
        Domin a samu mumini a cikin su da kafiri da me kyautatawa da me munanawa kuma su kasance tsakanin alheri da sharri har zuwa tashin alkiyama, kuma domin hakan ya zama jarabawa Allah ya tace gaskiya daga barna, sai adalcin sa ya bayyana acikin su sai ya bada lada ga wanda yayi masa biyayya ya kuma azabtar da wnada ya saba masa, Allah madaukaki yace: " amma wanda sukayi imani suka kuma aikata ayyuka na kwarai to zai cika masu ladan su kuma zai kara masu daga falalar sa wanda kuma suka kawar dakai sukayi girman kai zai azabtar dasu azaba me radadi kuma bazasu samu waliyyi ba koma bayan sa ko kuma me taimako (173)" suratun nisa'i.
        Jarabawa da biyayya da sabo sababi ne cikin sabubban halittan mutum domin me gaskiya ya bayyana daga me karya, da mumini daga kafiri, cikin abunda ya kasance sananne ga Allah madaukaki tun gabanin halittan su, Allah madaukaki yace: " Allah be kasance ba zai bar muminai akan abunda kuke kai har sai ya tantance me datti daga me kyau, kuma Allah be hakance ze barku akan gaibu ba sai dai yana zaba daga manzannin sa wanda yaso, kuyi imani da Allah da manzannin sa, idan kuma kunyi imani kuka ji tsoron Allah to kunada lada me girma (179)" suratu al'imran.
        Daga cikin manyan jarabawan sa wanda ya halicci mutum domin sa shine kadaitashi da bautansa shi kadai babu abokin tarayya kamar yadda ya bada labari cikin fadin sa madaukaki: " ban halicci mutum da aljan ba face don su bauta mini (56) bana bukatar arziki daga gare su kuma bana bukatar su ciyar dashi (57) lallai Allah shine me azurtawa ma'a bocin karfi bayyananne (58)" suratul zariyat.
        Bawai za'a fahimta daga haka bane cewa Allah ya halicci halittu bane domin bukatar su bauta masa, ya wadatu daga gare su da kuma ayyukan su sune masu bukata daga gareshi wanda bazasu wadatu daga falalar sa ba da tausayin sa da rahamar sa, biyayyar su bazata amfane shi ba kuma sabawar su bazata cutar dashi ba, saboda shi mawadaci ne da zatin sa daga dukkanin abunda bashi ba sai dai yana son bayin sa su bauta mishi kuma suyi masa biyayya, Allah madaukaki yace: " yaku mutane kune mabukata zuwa ga Allah lallai Allah mawadaci ne kuma me godiya (15)" suratu fadir.
        Kuma yanason su gode masa ya basu ko be basu ba, Allah madaukaki yace: " in kun kafurta to lallai Allah mawadaci ne daga gare ku kuma baya yarda da kafurci ga bayin sa, kuma idan kun gode masa zai yarda daku, wata rai bata daukan nauyin wata rai, sa'annan wuirn ubangijin ku zaku koma sai ya baku labarin akan abunda kuke aikatawa lallai shi masani ne ga abunda yake cikin zukata (7)" suratul zumar.
        Daga wanann zai bayyana cewa lallai Allah fa be halicci mutum ba domin suci da sha da haihuwa bane kawai su zama Kaman dabbobi da hakan bayan Allah ya karrama su daga hakan da hankali ya kuma daukaka su akan halittun sa dayawa, sai dai dayawa daga cikin mutane sunki sai sun kafurta dole sai suka jahilci ko kuma inkarin hikimar halittan su, suka zama Kaman dabbobi wanda suke jin dadi na sha'awowi cikin duniya na gamsar da farjin su da cikin su, rayuwan wannan shine kamar yadda Allah ya wasifta su kamar dabbobi kai sunfi su ma bacewa saboda rashin amfanin su da hankulan su wanda Allah ya masu ni'ima da ita ya kuma banbance su da ita akan sauran halittun sa domin suyi tunanin cikin halittan su da kuma dalilin samar dasu, Allah madaukaki yace: " wanda suka kafurta suna jin dadi da cin abinci kamar yadda dabbobi ke ci kumas wuta itace makomar su (12)" suratu Muhammad.
        Baza'a fahimci cewa jarabawa ta taqaitu ne kawai cikin sharri da abunda babu dadi ba kawai, babu wani abu dake faruwa cikin wannan duniya na ni'ima da fitina har wayau na jarabawa sai dan hikima na jarabawa, Allah madaukaki yace yana me hakaitu labari akan annabi sulaiman na ni'imar da yayi masa na mulki wanda ya bashi abunda bai taba ba wani ba cikin talikai na mulki lokacin daya nema daga cikin mutanen sa da su kawo masa gadon bilkisu, : " sai wanda yake da ilimi cikin littafi yace ni zanzo maka da shi gabanin kyaftawar idonka a lokacin daya ga wannan gado a gaban sa sai yace wannan daga cikin falalar ubangiji nane domin ya jarabani ya gani shin zan gode ko kuma zan kafurta, duk wanda ya gode to hakika ya gode ne domin kansa wanda kuma ya kafurta to lallai ubangijina mawadaci ne me karamci (40)" suratun namli.
        kuma dukkanin abunda ke faruwa cikin wannan duniya na musiba da ciwo da makamantan su duk suna cikin jarabawa da fitina shima har wayau duk domin hikimar jarabawa ne, Allah madaukaki yace: " kuma hakika zamu jarabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawayan arziki da rayuwa da yayan itace, kuma kayi bishara ga masu hakuri (155) sune wanda idan fitina ta same su sai suce innan lillahi wa inna ilaihi rahiji'un (156) wannan sune ambato ke kansu daga ubangijin su da rahama kuma sune shiryayyu (157)" suratul bakara.


Dalilai na hankali akan tashi bayan mutuwa cikin alkur'ani:
        Mutum yana mamakin yiwuwan tashi bayan mutuwa da kuma dawowan rai na biyu bayan mutuwa, Allah madaukaki yana cewa: " mutum yana cewa wai ace idan mun mutu za'a kara tayar damu kuma darai (66) shin mutum bazai tuna ba cewa lallai mu muka halicce sa gabanin be kasance komai ba (67)" suratu Maryam.
        Allah madaukaki ya bayyana cewa lallai abunda suke kudurcewa na inkarin tashi bayan mutuwa wanda suke sawwara shi da abu wanda bazai yiwu ba, abu ne me sauki a wurin wanda yake cema abu kasance sai ya kasance, Allah madaukaki yace yana me hakaitowa daga garesu: " wanda suka kafurta sunyi tsammanin cewa baza'a tashe su ba, kace masu tabbas ina rantsuwa da ubangijina za'a tayar daku kuma za'a baku labarin abunda kuka aikata hakan abune me sauki a wurin Allah (7)" suratul tagabun.
        Kasancewar me inkarin tashi bayan mutuwa bashi da wani dalili wanda yake dogaro dashi sai dai dalilan hankali wanda ake gani ko ji sai kur'ani ya fara gabatar da dalilai wanda yayi daidai da halin su na rashin imani da tashi bayan mutuwa da kuma fitowa daga kabari wanda daga cikin su akwai:
•    lallai duk wanda ya samar da halitta daga rashi, to lallai maganar tashi bayan mutuwa fa a wurin sa abune me sauki saboda maimaita abunda ya kaance akwai shi tun asali shi yafi sauki akan samar dashi a farko, Allah madaukaki yace: " shine wanda ya fara kirkiran halitta sa'annan kuma zai maimaitata kuma hakan shi yafi zama sauki a gareshi, yana da misali mafi kololuwa cikin sammai da kasa kuma shi mabuwayi ne me hikima (27)" suratul rum.
        Wannan ubayyu dan khalaf ne yazo wurin manzon Allah s.a.w da wani kashi tsho sai yace: ya Muhammad, shin kana ganin cewa lallai Allah zai tayar da wannan bayan ya dadaddage? Sai yace masa: " eh tabbas kuwa, zai tayar dakai kuma ya shigar dakai wuta" sai Allah ya saukar da fadin sa cewa: " suna buga mana misali sun manta da halittan kansu cewa wanene zai tayar da kasha bayan ya dadaddage (78) kace wanda ya kirkirota tun farfo shine wanda zai tayar da ita kuma shi maani game da dukkanin wani halitta (79) shine wanda ya sanya maku wuta daga koren bishiya sai gashi kuna kunna wuta daga gareta (80) shin bashi bane kuma wanda ya halicci sammai da kasa kuma yana da ikon halittan wasu irin su, hakika shine me halitta kuma masani (81) al'amarin sa shine idan yaso abu kawai ce masa yake kasance sai ya kasance (82) tsarki ya tabbata ga Allah wanda a hannu sa ne mulkin komai yake kuma gareshi zamu koma (83)" [suratu yasin]
Tafsirin Abdulrazzak (3/87, h2498), da baihaki da hakim kuma sun rawaito shi kuma yana cikin sahihul sira shafi na 201.

        Saboda haka ne Allah madaukaki ya umurci manzon Allah s.a.w da yace ma kafirai wanda suka tambaye shi " sunce yanzu wai idan mun kasance kashi da kasa wai za'a tayar damu a halitta sabo (49)" suratul isra'i.
        Da cewa ya amsa musu da irin wannan tunani nasu " kace masu ku zama dutse ko kuma karfe (50) ko kuma wani halitta babba a cikin zukatan ku da sannu zasuce wanene zai dawo damu to, kace masu wanda ya halicce tun farko, da sannu zasu sunkuyar da kansu suce maka yaushe ne to, kace masu yana nan kusa tafe (51) a ranan da za'a kira ku sai ku amsa da godiya a gareshi kuma kuyi tsammanin baku zauna ba a cikin ta sai lokaci kankani (53)" suratul isra'i.
Lallai kirkiran abu a karo na biyu a hankalce yafi sauki akan halittan sa a karo na farko, wanda ya halicce ka a farkon al'amari lallai yana da ikon halittan ka a karo na biyu, Allah madaukaki yana cewa: " shin mutum yana tsammanin za'a kyale shih aka kawai (36) ashe be kasance gudan ba daga ruwan maniyyiwanda ake fitarwa (37) sa'annan ya zama gudan jini sai aka halicce sa daga hakan aka daidaita shi (38) ya sanya su suka zama ma'aurata biyu mace dana miji (39) shin me wannan bashi da ikon tayar da matattu (40)" suratul kiyama.
•    Wanda ya halicci abu me wahala yana da ikon halittan me sauki kumadukkanin su a wurin Allah masu sauki ne, misali duk wanda yake da daman daukan kilo hamsin na kaya bazai gaza daukan kilo day aba na kaya, Allah madaukaki yace: " shin bashi bane wanda ya halicci sammai da kasa kuma yanada ikon halittan wani irin su, tabbas shine me halitta kuma masani 981) lallai al'amarin sa fa kawai shine idan yana son abu ce masa yake kasance sai ya kasance (82)" suratu yasin.
•    Wanda ya samar da kai ba tare da sonka ba ko kuma ilimin ka a karon farko a hankalce yana da iko akan samar dakai a karo na biyu ba tare da sanin ka ba kuma dason ka, Allah madaukaki yace: " mutum yana cewa yanzu ace idan na mutum wai zan fito a raye kuma (66) shin mutum bazai tuna ba cewa lallai mufa muka halicce sa gabanin be kasance ba wani abu (67)" suratu Maryam.
A gun Allah halittan mutum daya daidai yake da halittan mutane baki daya, Allah madaukaki yace: " halittan ku da tayar da ku bayan mtuwan ku ba komai bane sai kamar halitta da tayar da mutum daya, lallai Allah me ji ne kuma me gani (28)" suratu Lukman.
•    Lallai duk wanda ya canza halitta daga wanann yanayi zuwa wani yanayi kuma daga irin wannan sinadari zuwa wani sinadari na daban ya fitar da rayayye daga matacce ya kuma fitar da matacce daga rayayye lallai yanada ikon a hankalce na tayar da mutune bayan mutuwan su kasancewa Allah ya fitar da zangarniya daga kwaya matacce, kuma ya fitar da iri matacce daga jikin bishiya me rai, da kwai matacce daga kaza me rai, da dan tsako daga cikin kwai matacce, Allah madaukaki yace: " lallai Allah shine yanda yake rarrabe iri da kwaya, yana fitar da rayayye daga matacce kuma ya fitar da matacce daga rayayye wannan shine Allah ubangijin ku to dan me yasa kuka kaucewa (95) mahaliccin haske ya kuma sanya dare ya zama lokacin hutu da rana da wata suna tafiya da lissafi me yakini wanda baya canzawa lallai wanda shine dakkarawa na mamuwayi me hikima (96)" suratul an'am.
•    Duk wanda ya fitar da tsirrai da itatuwa daga cikin kasa matacce bayan saukar da ruwa akanta bayan ta kasance bushashiya babu wani tsiro akanta lallai yana da ikon tayar da mutane bayan mutuwar su da kuma fitar dasu, Allah madaukaki yace: " Allah shine wanda ya aiko da iska sai ta kora girgije sai mu saukar dashi a matsayin ruwa zuwa ga wani gari sai mu raya kasa dashi bayan kakashewar ta, Kaman haka ne tayar bayan mutuwa zai kasance (9)" suratu fadir.
•    Wanda ya halicci mutum daga rashin sa bayan yabi matakai har yakai ga mutuwa lallai yana da ikin tayar dashi karo na biyu, mutuwa ba ita bace matakin karshi na rayuwa ga mutum akwai lahira a bayanta wanda za'ayi masa hisabi a cikinta na abunda ya aikata baya halatta inkarin tayar wa bayan mutuwa da ban komai ba sai dan be ga hakan ba, duk wanda yayi halitta tun farko wacce tabi matakai bayan matakai yanada ikon maimaitata kamar yadda ya farata ya kuma kaita zuwa ga mataki na karshe kodai aljanna ko wuta, Allah madaukaki yace: " yaku mutane idan kun kasance cikin shakka dan gane da tashi bayan mutuwa to lallai fa mu muka halicce ku daga kasa sa'annan ta koma gudan maniyyi sa'annan ta koma gudan jini sa'annan ta koma tsoka wacce ake halitta da wanda ba'a halitta domin mu bayyana maku, kuma muna tabbatarwa cikin mahaifa abunda mukeso zuwa wani lokaci tsananne sa'annan mu fito daku a jarirai sa'annan ku kai tsufan ku, daga cikin ku akwai wanda suke mutuwa kuma daga cikin ku akwai wanda suke tsufa tukuf kamar basusan wani abu ba abaya, zakaga kasa bushashiya amma idan muka saukar mata da ruwa sai ta kunbura ta fashe fitar da tsirrai daga dukkanin nau'oka biyu biyu me ban sha'awa (5) haka ya faru ne saboda lallai Allah shine gaskiya kuma lallai zai tayar da matattu kuma lallai shi me iko ne akan komai (6)” Suratul hajj.
Ibn kayyim Allah yayi masa rahama yace: Allah madaukaki yana cewa idan kun kusance kuna shakka akan tashi bayan mutuwa me yasa bakwa shakka akan cewa ku halitta ne, kuma baka shakka akan farkon halittan ku daga wani yanayi zuwa wani yanayi hark u mutu, tashi bayan mutuwar da ake maku alkawari ai iri daya ne da halittan ku tun farko wanda bakwa shakka akan sa, to dan me yasa kuke inkarin daya daga cikin kirkiran halitta bayan kunga irin sa.
Sayyid kudub Allah ya masa rahama yana cewa: lallai canji da ci gaban da jariri yake bi sannan yaro yabi shima bayan yaga haske, domin ta nuna cewa lallai wannan ikon wanda yake jujjuya wannan canji da matakai zai ka mutum zuwa ga kamalar sa zuwa matuka, daganan kuma sai ya fara komawa baya: " har yakai matakin tsufan da kamar be taba sanin komai ba a rayuwa a baya" lallai babu makawa cewa akwai wani gida bayan wannan wanda mutum zai karasa cikan sa acikinta.
Dalilan wannan matakan da suke nuni akan tashi bayan mutuwa dalilai ne na cukude, wacce take nuni akan tashi bayan mutuwa ta wani bangaren cewa wanda yake da ikon akan kirkiran mutum lallai yanada ikon maimaita shi, kuma tana nuni akan tashi bayan mutuwa saboda ikon jujjuya mutum har zuwa ga cikin kamalar sa a gidan lahira, wannan zai dace da kimiya na hakitta da maimaitata da kimiyan rayuwa da tashi bayan mutuwar ta, da kimiyar hisabi da sakamako, kuma dukkanin su suna bada shedar samuwar Amahalicci wanda yake jujjuya al'amura me iko wanda babu jayayya akan samuwar sa.
•    Rashin wasa cikin halitta ka kalli mota ka gani misali mutum be kirkiri wani bangare ba a cikinta ya kuma jerasu hakanan ba tare da wani buri nasa ba saboda ahankalce bazai wahalar da kansa ba domin wasa yayi asarar dukin sa wurin aikin da bazai amfana dashi ba kuma bazai amfanar ba, to shin hanakali zai dauka cewa wannan halitta me girma an halicce ta ne domin wasa, kalli ko wani gaba kagani cikin gabban jikinka yadda suke da kuma yadda sukeyin motsi da yin ayyuka wanda aka halicce ta domin shi, lallai yana daga cikin wasa a halicci irin wannan halitta haka kawai ba tare da tayi aikin ibada ba wacce aka halicce ta domin shi kuma a tashe ta bayan mutuwa domin ayi mata hisabi akan abunda ta aikata, Allah madaukaki yace: " shin kuna tsammanin mun halicce ku ne kawai domin wasa kuma bazaku dawo zuwa gare mu ba (115) tsarki da daukaka ya tabbata ga Allah sarki na gaskiya babu abun bautawa da gaskiya bisa cancanta sa shi ubangijin al'arshi me girma (116)" suratul muminun.
•    Zahirin bacci da tashi ga wanda ya ke lura, mutuwa ce da rayuwa bacci fitar rai ne daga gangan jiki sa'annan ta dawo bayan ta fita kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari: " Allah shine wanda yake kashe rayuwaka a lokacin mutuwar su da kuma wanda bazata mutuba a lokacin baccin ta, sai ya rika ran da ya rubuta mata mutuwa ya dawo da sauran zuwa wani lokaci sananne, lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (42)" suratul zumar.
Kurdhubi Allah yayi masa rahama yace a cikin wannan al'amari: bacci da mutuwa suna haduwa ne cikin cewa dukkanin su akwai yankewan rai daga jiki kuma hakan zai iya kasancewa zahirin bacci, saboda haka ne akace bacci kanin mutuwa ne, kuma zai iya zama a badini mutuwa ne, kenan kiran bacca da sunan mutuwa ya halatta saboda kasancewar su sunyi yarayya cikin yankewan rai daga jiki.
Wanda ya tayar dakai daga bacci ya dawo maka da ran ka yana da ikon dawo maka da ran ka bayan ka mutu ya kuma tayar dakai, manzon Allah s.a.w yayi gaskiya a lokacin day ace: " bacci dan uwan mutuwa ne, kuma mutanen aljanna basa bacci" hadisi ne ingantacce, dabari ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi cikin alsahiha 1086.


Asalin mutum cikin alkur'ani me girma:
Asalain mutum yana komawa ne zuwa ga Adam amincin Allah ya tabbata a gareshi wanda Allah madaukaki ya halicce sa da hannun sa ya kuma daidaita shi ya hura masa rai daga ran sa kuma mala'iku suka masa sujjada domin girmama shi, Allah madaukaki yace: " lokacin da ubangijin ka yacema mala'iku lallai zan halicci mutum daga kasa (71) idan na daidaita shi na hura masa rai daga raina to kuyi masa sujjada (72)" suratu saad.
Sa'annan kuma aka halitta masa matan sa hauwa'u daga gareshi domin ya samu natsuwa zuwa gareta, Allah, madaukaki yace: " ya halicce ku daga rai daya sa'annan ya sanya masa mata daga gareshi ya kuma saukar maku da dabbobin ni'ima aure guda takwas, yan halittan ku daga cikin mahaifiyar ku halitta bayan halitta cikin duhu guda uku, wancan shine shine Allah ubangijin ku gareshi mulki yake babu abun bautawa da gaskiya basa cancanta sais hi to me yasa kuke kaucewa (6)" suratul zumar
Kuma domin ya kasance daga tsatson su mutune zasu fito domin aikin khalifanci a kasa wanda wasu suke maye wasu a cikin kasa da rayata kamar yadda Allah yake so ya kuma tabbatar, Allah madaukaki yace: " shine wanda ya kyautata halittan komai, kuma ya fara halittan mutum ne daga tabo (7) sa'annan ya sanya dangantakan sa ya zama daga ruwa wulakantacce 98) sa'annan kuma ya daidaita shi ya hura masa rai daga ran sa ya kuma sanya maku ji da gani da hankali kadan ne masu godiya (9)" suratul sajada.
Mutane baki dayan su ba tare da dubi ba ga banbancin fatar su da dangantakan su na asali suna komawa ne zuwa ga Adam amincin Allah ya tabbata a gareshi wanda shine a salin su kuma daga shine mafarin su, Allah madaukaki yace: " yaku mutane kuji tsoron ubangijin ku wanda ya halicce ku daga mutum guda ya kuma halitta masa mata daga gareshi ya kuma yada mutane maza da mata daga tsakanin su biyu kuji tsoron Allah wanda kuke rokon sa da kuma sada zumunta domin sa, lallai Allah ya kasance me bibiyan ku a duk inda kuke (1)" suratun nisa'i.
Wannan yana cikin abunda yake nuna rashin daukakan wasun su akan wasu a wurin Allah sai dai akan gwargwadon biyayyan su da kuma sabon su, wurin zaman sa a farko ya kasance aljanna, alkur'ani me girma ya hakaito man agirmamawan da Allah madaukaki yayi masa yayima mala'iku umurni da suyi masa sujjada da kuma kissar kiyyayr shedan akan sa yadda yayi girman kai da dagawa da hassada akan darajar sa wanda Allah ya ajiye sa sai yaki yi masa sujjada bayan fushin Allah me tsanani da tsinuwar say a bayyana akan sa sai yayi rantsuwa sai ya bayyanar da kiyayyar sa akan zuriyan sa bayan sa kuma zeyi dukkanin kokarin na batar dasu domin suma fushin Allah ya same su da zaban sa, Allah madaukaki yace: " hakika mun halicce ku sannan kuma muka hura maku rai sannan muka cema mala'iku suyi sujjad ga Adam sai sukayi sujjad sai iblis kadai yaki zama cikin masu sujjada (11) sai yace me ya hanaka sujjada lokacin danayi maka umurni sai yace ni nafi shi alheri ka halicce ni daga wuta shi kuma ka halicce sa daga tabo (12) sai yace masa to ka fita daga cikin ta saboda be dace agareka ba kayi girman kai acikinta ka fita lallai kana cikin kaskantattu (13) sai yace ya Allah kadan sauraramun to zuwa ranan alkiyama kada ka kashe ni (14) sai yace jeka kana cikin wanda aka saurara mawa (15) sai yace ina rantsuwa kamar yadda ka batar dani sai na zauna masu akan hanyar ka mikakkiya (16) sa'anna zan zo masu daga gaban su da kuma bayan su ta daman su da hagun su kuma baza ka samu dayawan su ba suna godiya (17) sai yace ka fita daga cikinta kana makaskanci abun zargi kuma duk wanda ya bika daga cikin su sai na cika jahannama daku baki daya (18) ya Adam ka kazauna kai da matarka a cikin aljanna kuma kuci dukkakin abunda kuke so a cikinta amma kada ku kusanci wannan itaciya sai ku zama cikin azzalumai (19) sai shedan yayi masu wasiwasi domin ya bayyanar masu da abunda aka biye masu na tsiraicin su yace masu ubangijin ku ba bai hanaku cin wannan itaciya ba sai domin kada ku zama masu mulki ko kuma ku dawwama acikin aljanna (20) ya kuma masu rantsuwar cewa lallai fa ni ina cikin masu maku nasiha ne (21) sai ya nuna masu wannan itaciya da rudu irin nasa bayan sun dandana wannan itaciya sai al'auran su ya bayyana sai suka rika tsintan ganye cikin aljanna suna rufe al'auran su dashi, sai ubangijin su ya kirasu yace masu ashe ban haneku ba daga cikin wannan itaciya kuma nace maku shedan makiyi ne a gare ku bayyananne (22) sai suka ce ya ubangijin mu lallai mun zalumci kawunan mu kuma idan baka gafarta man aba lallai zamu kasance cikin masu hasara (23) sai yace ku fida daga cikin ta ku sauka kasa sashin ku yana gaba da sashi kuma kuma kuna da rayuwa a doron kasa da jin dadi zuwa wani lokaci (24) sai yace acikinta zakuyi rayuwa kuma acikinta zaku mutu kuma daga cikinta za'a fito daku (25)" suratul a'araf.
Saboda haka muyi taka tsantsan a matsayin mu na mutane daga zurriyyan Adam kada shedan ya batar damu ya fitar damu daga biyayyan Allah zuwa saba masa, daga imani zuwa kafurci, muyi riko da abunda Adam yake kai na tauhidi da bautan Allah shi kadai kuma ku tsarkake zuciyar mu daga kyashi da mugunta da hassada, zuciyar mu ya kasance me kyau akan junan mu kuma muyi imani da abunda manzannin Allah suka zo dashi na shari'a kuma shar'ar Muhammad ta kasance mana kashen shari'a wanda zamuyi imani dashi domin mu toshe ma shedan damar sa na cika alkawarin dayayi na batar damu sai abunda Allah yayi masa alkawari dashi ya same me ga wanda yayi masa biyayya, da cewan sa " sai yace ka fita daga cikinta kana makaskanci abun zargi kuma duk wanda ya bika daga cikin su sai na cika jahannama daku baki daya (18)" suratul a'araf.


Wanene mutum?
Mutum shine Adam da matar sa hauwa'u Amincin Allah ya tabbata agaresu da dukkanin abunda suka fito daga jinin su na mutane jinsi daban da ban da kala daban daban, Allah madaukaki yace: " yaku mutane kuji tsoron Allah wanda ya halicce ku daga mutum daya ya kuma halitta masa matan sa daga gareshi ya yada a tsakanin su mutane maza da mata, kuji tsoron ubangijin ku wanda kuke rokon sa da sada zumunta domin sa, lallai Allah ya kasance me bibiyan ku duk inda kuke (1)" suratun nisa'i.
Allah ya zabeshi cikin halittun sa sai ya kyautata halittan sa ya sanya shi da sura me kyau da yanayi cikakke, Allah madaukaki yace: " hakika mun halicci mutum cikin mafi kawun sura (4)" suratul teen
Ya kuma bashi gabbai na ji da gani da dabi'a ta rai da hankali wanda yake iya banabce alheri da sharri dasu da amfani da cuta, idan mukayi tunana akan wannan zamu san hikimar sanya masa hankali da kuma halitta me kyau wanda akayi masa domin ya zama zai iya fahimtar abunda Allah zai saukar masa na sakonni da sauke abunda ke kansa na wajibobin addini da zamanta kewa, kuma ya iya rayuwa da dukkanin abun da suke kewaye dashi cikin wannan duniya me fadi da kuma hore masa su domin amfanin sa na duniya.
Allah ya halicci mutum da gangan jiki da rai da hankali, Allah madaukaki yace: " Allah shi ne wanda ya sanya maku kasa tabbatacciya ya kuma sanya sama ginanniya ya halitta ku ya kuma kyautata halittan ku ya azurta ku daga abubuwa masu dadi, wancan shine Allah ubangijin ku, tsarki da daukaka ya tabbata ga Allah ubangijin talikai (64)" suratu gafir.
Allah madaukaki ya kara cewa: " ya halicci sammai da kasa da gaskiya ya kuma halicce ku ya kyautata halittan ku kuma gareshi zaku koma (3)" suratul tagabun.
Ko wanni daga cikin wannan sinadarai na halittan mutum yana da abincin sa domin ya ginu dashi ya kara masa karfi:

•    Sinadarin (gangan jiki):
Abunda yake karfafashi da lafiyar sa shine tsabtace shi da tsarkake shi da kuma kosar dashi sha'awar sa na dabi'a na abinci da ruwa da aure, Allah madaukaki yace: " yak u yayan Adam ku dinga rike kawar ku lokacin zuwa ko wani masallaci da salla kuma kuci ku sha kada kuyi almubazaranci, lallai Allah baya son almubazzari (31) kace wanene ya haramta maku adon Allah wanda ya fitar dashi domin bayin sa da dadaden abubuwa na arziki kace anyi su ne domin wanda sukayi imani a rayuwan duniya kuma a lahira nasu ne su kadai kawai banda wanin su, kamar haka ne muke bayyana ayoyin mu ga utane masu sani (32)" suratul a'araf.
An umurce sa da yin magani ga jikin idan bashi da lafiya ta hanyar ko wani irin magani wanda yake halal, manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah ya saukar da cuta da kuma magani, ya sanya magani ga ko wace cuta saboda haka kuyi magani, amma kada kuyi magani da haramun" (hadisi ne ingantacce) dabarani ne ya yarawaito shi daga Ummi darda'i Allah ya kara mata yarda, kuma albani ya ingantashi cikin sahihul jami'u lamba ta 1762.
Kosar da sha'awa ta halittan dan Adam yanada dokoki da ka'ida wanda Allah ya shar'anta masa domin ya daukaka shi daga nau'in dabbobi kada ya zama irin su, Allah madaukaki yace: " kuma daga cikin ayoyin say a halitta maku mata domin ku samu na tsuwa zuwa garesu kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakanin ku lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (21)" suratul rum.

•    Rai (ruhi):
Abunda yake karfafata da abincinta shine imani da mahaliccinta da dangantaka da kuma bautan sa da jayuwa zuwa gareshi da masa biyayya hakan ya samuwa ne ta hanyar aikata ayyukan da ya wajabta da kuma barin aikata ayyukan daya hana aikatawa kasancewa tana bukatar zuwa ga wanda ya halicce ta, dashi ne take samun natsuwa da kwanciyan hankali da aiki da murna da rabauta da ni'ima kuma daga shi take tsarkaka daga tsoro da kunci wanda yake tasiri ga jiki sai ya halaka ta, Allah madaukaki yace: " wanda sukayi imani kuma zukatansu yana samun natsuwa da ambaton Allah, ku sauarara kuji da ambaton Allah ne zukata suke samun natsuwa (28)" suratul ra'ad.

•    Hankali:
Musulunci ya daga kimar hankali ya kuma ba mutum yanci cikakke na tunani cikin dukkanin abunda aka masa umurni dashi, kada yayi imani da wata akida wacce aka kira shi zuwa gareta har sai ya gamsu kuma ya yarda, kuma kada ya riki wani shari'a da manhaji cikin rayuwan sa har sai yayi tunani yasan ingancinta.
Wannan shine abunda Allah ya banabanta mutum dashi akan sauran halittu, da hankali ne al'umma take samun canji da ci gaba har mutum ya wayi gari yana da ikon amfani da dukkanin abunda suke ke waye dashi na sama da kasa da rafi ya kuma hore masa su domin kyautata hada hada na rayuwa, da hankali ne ake tace halaye na gari da kuma tsara yanayin rayuwa da nuna fahimta da tsara al'ummomi, da kuma hankali ne ake sanin gaskiya da barna da alheri da sharri da amfani da cuta, itace dalili na ratayan nauyin ayyukan bauta musulunci, daga cikin adalcin Allah madaukaki shine baya yima mutane hisabi sai ta hanyar sa, duk wanda bashi da hankali kuma baya gane shari'ar musulunci baza'a masa hisabi ba, saboda haka ne musulunci yayi umurni da kiyaye hankali ya kuma shar'anta iyakoki anan duniya da ukuba a lahira ga wanda ya lallata hankali da gangan da sonsa ta hanyar shan kayayyakin maye da kwayoyi masu bugarwa, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani lallai giya da caca da dara da rantsuwa da gumaka datti ne daga cikin ayyukan shedan, saboda haka ku nesance su koda zaku tsira da rabauta (90)" suratul ma'ida.
Ya kuma wasafta wanda ya lallata hankali da kansa da zabin sa ya haramta masa tunani da karatu cikin martaban dabbobi wanda basu da wani burin daya wuce ci da sha da jima'i, Allah madaukaki yace: " lallai mafi sharrin dabbobi a wurin Allah sune wanda suke kurame da bebaye wanda basu da hankalta (22)" suratul anfal.
Wannan hankalin yanada abinci wanda yake ginashi da nunar dashi kuma dashi ne yake kirkira ya da samu wanda wannan abinci yake samuwa tsakanin:

Na farko: imili:
Allah maduakaki ya tanadar wa wannan hankali hanyoyi na ji da gani da shaka da tabawa wanda ta hanyar su ne abincin sa da kuma girman sa ta hanyar dukkanin nau'uka na sani domin ya iya raya wannan duniya da kuma hore masa dukkanin abunda ke cikinta ta hanyar abunda yake kirkira da gyara shi zuwa ga matakin rayuwan sa, Allah madaukaki yace: " Allah shi ne wanda ya fitar daku daga cikin mahaifiyan ku baku san komai ba ya kuma sanya maku ji da gani da hankali koda zaku gode masa (78)" suratun nahli.
Sabod ahaka ne musulunci ya daga sha'anin ilimi da malamai ya kuma banbanta tsakanin malami da jahili da banbanci me yawa kamar yadda Allah ya bayyana cikin fadin sa cewa: " kace shin wanda suka sani zasuyi daidai da wanda basu sani ba, lallai baya tunatar da kowa sai masu hankali (9)" suratul zumar.
Yadda musulunci ya sanya neman ilimi cikin ayyukan kusanci zuwa ga Allah musamman ma ilimi wanda amfaninsa yake komawa ga mutum saboda haka ne malaman musulmai wanda suka gabata suke rigegeniya wurin neman ilimi wanda sakamakon hakan ne suka fitar mana da ilimi ya yadu cikin dukkanin fadin duniya kuma ci gaban zamani ya ginu akan sa, Allah madaukaki yace: " zai daga darajar ku da kuma wanda suke da ilimin acikin ku da darajoji, Allah me bada labari ne game da abunda kuke aikatawa (11)" suratul mujadala.

Na biyu: tunani:
Wuraren sa yana da fadi shine aikin hankali da kuma raya rai sai ya tsayu da kansa ya kai mataki kololuwa da hankalinta wurin tunani cikin wannan duniya me fadi yana nazari cikin abunda Allah ya samar na halittu, kuma har wayau zababben hankali zai san hakikanin wannan duniya wanda ba ita ta halicci kanta ba kuma ba wani abu bane daga jinsin say a halicce sa kuma bata samu hakanan ba kawai kuma yana nuni zuwa ga mahaliccin sa wanda babu shakka da wanda ya kirkire sa, Allah madaukaki yace: " shin bazasuyi dubi zuwa ga mallakoki na sammai da kasa da abunda Allah ya halitta na komai kuma ijalin su ya kusa ya gabato, da wani labari ne bayan wannan zasuyi imani dashi (185)" suratul a'araf.
Tunani da nazari suna cikin ayyaka madaukaka cikin musulunci ta yadda ayoyi da yawa na alkur'ani suka karfafa hakan da kwadaitar wa akan sa, Allah madaukaki yana nema daga wurin bayan sa su rika dubawa " shin bazasu rika dubawa ba" da tunani " shin bazasu rika yin tunani ba" da tunawa " shin bazasu rika tunawa ba" da kuma hukunci da hankali " shin bazasu rika hankalta ba" da nazari cikin abunda suke gani " shin bazasu rika nazari ba" dukkanin haka domin tabbatar da hadafi na koluluwa da ake so ne wanda shine amfani dasu domin tabbatar da Allah da girman sa, daga cikin wannan ayoyi akwai:
•    Kira da yin tuna cikin abunda muke rayuwa acikinsa da jin dadi dashi na ni'imomi wanda Allah ya halitta mana su domin jin dadin mu, Allah madaukaki yace: " kuma daga cikin ayoyin sa ya halicce ku daga tabo sa'annan sai gashi kawai kun zama mutum kuna ta yaduwa (20) kuma daga cikin ayoyin sa ya yalitta maku matayen ku daga jikin ku domin ku samu natsuwa zuwa garesu ya kuma sanya soyyay da tausayi a tsakanin ku, lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (21) kuma daga cikin ayoyin halittan sammai da kasa da kuma sabanin harsunan ku da kalan fatar ku, lallai a cikin haka akwai ayoyi ga masana (22) kuma daga cikin ayoyin sa baccin ku da daddare da neman daga cikin falalar sa da rana lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu ji (23) kuma daga cikin ayoyin sa yana nuna maku walkiya domin tsoratarwa da kuma kwadayi kuma yana saukan da ruwa daga sama sai ya rana kasa da shi bayan mutuwar ta lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutune masu hankalta (24) kuma daga cikin ayoyin sa zama da kasa suna kafu da umurnin sa sa'annan idan ya kira ku da wani kira sai gashi kawai kuna fitowa daga cikin kasa (25)" suratul rum.
•    Kira ga yin tunani cikin kawunan ku da kuma yadda aka shiryata da hadata da abunda ta kunsa na gabbai wanda sukeyin aiki wanda ya gagari mutum baki dayan su game da kera irin sa, Allah madaukaki yace: " a cikin kasa akwai ayoyi ga masu sakankancewa (20) da kuma cikin kawunan ku shin bazaku gani bane (21) kuma cikin sama akwai arzikun ku da abunda aka maku alkawari (22)" suratul zariyat.
•    Kira zuwa ga tunani game da wannan kwarin da suke rayuwa tare damu cikin wannan duniya da kuma amfanin da mutum ke samu da wasun su, Allah madaukaki yace: " kuma ubangijin ka yayi wahayi zuwa ga tururuwa da cewa ki rika gida daga cikin duwatsu da bishiya da kuma abunda suke rayuwa dashi (68) sa'annan kuci daga dukkainin kayan bishiya kuma kibi hanyar ubangiji ki a saukake, abun sha yana fitowa daga cikinta mabanbanta launuka wanda akwai waraka ga mutane a cikinsa, lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (69)" suratun nahli.
•    Kira zuwa ga tunani game da dabbobi wanda suke rayuwa tare damu kuma aka hore mana su domin muci da sha da hawan su, Allah madaukaki yace: " kuma lallai kuna da abun lura a cikin dabbobin ni'ima muna shayar daku daga abun cikin su na mada wanda yake daga tsakanin bayan gida da jini tatacce da dandano ga masu shansa (66) kuma daga cikin yayan dabino da inabi kuna yin kayan maye daga cikin su da kuma arziki me kyau, lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu hankalta (67)" suratun nahli.
Kira zuwa ga kira game da abunda yake tashi a sama na tsuntsaye yadda Allah madaukaki ya hore masu sararin samaniya domin yayi daidai dasu wurin tashi ya kuma halicce ta da fuka fuki wanda yake iya daga ta zuwa sama dukda cewa mutum bazai iya gwada hakan ba koda kuwa an sanya masa fuka fukai shima nunkin nata, Allah madaukaki yace: " shin basu gani zuwa ga tsuntsu wanda aka hore su cikin sararin samaniya babu me rike su sai Allah, lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu imani (79)" suratun nahli.
Sayyid kudub yana cewa Allah yayi masa rahama: mu rika nazari da lura game da wannan tsuntsayen, wanda yake shinfida fuka fukan sa ya kuma dunkule su a halin da yana zaune a kasa yana rika yawo cikin iska, yana tashi a cikin sa cikin sauki da tsanake; kuma yana zuwa da wasu halaye wani lokaci wanda me kallon sa zai rika tunanin da kayun haka, kayi nazari ka gani cikin haka, da kuma bibiya dukkanin nau'I na tsuntsu na harkokin sa na daban, wanda ido baya koshi da ganin sa ko kuma zuciya ta gaji dashi. Dukkan dadi ne cikin motso tunani da nazari cikin halittun Allah, wanda kyawu da kamala ya hadu a cikin sa, alkur'ani kuma yana nuni zuwa ga wannan abu me tasiri kuma Allah me rahama yana rike so da tsari wand aka tsara da wannan mamaki, abun lura a cikin haka ga ko wani babba da karami da kuma hisabi acikin san a zarra, rike tsuntsu cikin sararin samaniya kamar yadda ake rike dabba akan kasa da kuma jirgin sama da abunda ke cikinta na nauyi cikin sararin samaniya kamar rike sauran kayayyaki masu nauyi wanda babu me rike su a wurin su sai Allah.
•    Kira zuwa ga tunani game da duniya baki dayanta sama da kasa da abunda aka halitta a tsakanin su da cikin sun a dabbobi da kuma yadda akayi halitta da tsari na rayuwan su, Allah madaukaki yace: " Allah ya halicci dukkanin dabbobi daga ruwa, daga cikin su akwai wanda yake tafiya akan cikin sa, daga cikin su akwai me tafiya akan kafafuwa biyu kuma daga cikin su akwai me tafiya akan kafafuwa hudu, Allah yana halittan abunda yaso lallai Allah me iko ne akan komai (45)" suratul nur.
•    Da kuma yadda Allah ya raba arziki a tsakanin su wanda abunda ya dace da wannan jinsi baya dace wa da wani jinsin kuma gidan daya dace da wannan baya dacewa da wani jinsin, Allah madaukaki yace: " [babu wata dabba cikin kasa face arzikinta na gun Allah yasan tsawon rayuwanta kuma yasan makomarta duka hakan suna cikin littafi bayyananne (6)]" suratul an'am.
•    Kira zuwa ga tunani game da asalin halittan mutum da kuma yadda yake rayuwa da abincin sa da abun shan sa, Allah madaukaki yace: " shin bakwa ganin abunda kuke zubar wa na maniyyi cikin mahaifan mata (58) shin ku ne kuke halittan sa ko kuma mune muke halittan sa (59) mune muka kaddar mutuwa a tsakanin ku kuma ba'a gagare mu ba (60) akan cewa mu kashe ku mu halitto wasu irin ku wanda baku ba cikin irin halittan da muke so (61) kuma hakika kun san yanayin halittan ku na farko to dan me yasa baza kuyi tunani ba (62) shin bakwa ganin abunda kuke shukawa ne (63) shin kune kuke raya shi da fito dashi ko kuma mune (64) da mun ga dama da mun sanya shi ya zama ciyawa bushashe wanda bazaku amfana dashi ba da komai mu barku cikin mamakin haka (65) kuna cewa lallai an azabtar damu (66) an haramta mana abunda muka nema na iska kayan shuka (67) shin baku ga ruwan da kuke sha bane (68) shin kune kuka saukar dashi daga girgije ko kuma mune muka saukar dashi (69) da mun ga dama da mun sanya shi ya zama me dandanon gishiri dayawa wanda bazaku iya shaba to dan me yasa bazaku gode ba (70) shin baku ga wutan da kuke izawa bane (71) shin kune kuka samar dashi daga bishiya ko kuma mune muka samar dashi (72) lallai mu ne muka sanya ta domin ta zama tunatar wa da kuma amfani ga matafiya da masu amfani da ita (73)" suratul waqi'at.
Saboda haka ne alkur'ani ya zargi wanda basa gani da tunani kuma basa hankalta da daukan izina daga abunda suke gani cikin wannan duniya me fadi yadda ya wasafta su a msatsayin wanda suka rasa gabbai saboda rashin riskan suzuwa ga sanin mahalicci da kuma abunda aka halicce su domin sa sai ya kwatantasu da dabbobi wanda basu da hankali, Allah madaukaki yace: "kuma hakika mun halitta ma wutan jahannama mutane da aljanu da yawa suna da zuciya amma basa fahimta da ita kuma suna da idanu amma basa gani da su kuma suna da kunnuwa amma basa ji da su, wannan Kaman dabbobi suke koma kai sunfi su bacewa kuma wannan sune gafalallu (179)" suratul a'araf.

Sai dai musulunci ya iyakance wannan tunani da iyaka wanda zai kai mutum da sanin Allah ta hanyar halittun sa sai ya tsaya a wannan gaba kada ya wuce hakan cikin tunanin abunda bashi da ikon ganewa sabda hankali halitta ne yana da iyaka na riskan abubuwa kada ya wuce haka wanda kuma ya wuce iyakan hankalin sa to hakika ya zalumce sa kuma yayi masa ta'adi kuma misalin sa shine kamar misalin mutumin daya sanya fitila ne wanda karfin jan wutan sa 110 ne acikin lantarki me karfin 220 wanda kowa yasan sakamakon haka.

Zaben Allah ga dan Adam:
A cikin wannan halittu wanda suke cikin wannan duniya ubangijin mu ya zabi mutum ya kuma daukaka shi akan sauran halittu, Allah madaukaki yace: " hakika mun karrama dan adam kuma mun sanya shi a doron kasa da saman rafi mun kuma azurta shi daga dadadan abubuwa kuma mun daukaka shi akan dayawa daga cikin halittun mu daukakawa (70)" suratul isra'i.
Daga cikin zahirin karramawan Allah ga dan Adam:

•    Ya hore masa duniya:
Allah madaukaki ya horema mutum wannan duniya kasansa da saman sa da kuma abunda ya halitta a cikin sa da abubuwa ya kuma tanadar masa su domin yayi daidai ga rayuwan sa na abunda ya sanya aciki wanda suke karfafa rayuwa na iska da ruwa da abinci da dabbobi da bishiyoyi da tsirrai ya kuma hore mashi su yana amfani dasu da abunda Allah ya bashi na ilimi ya kuma daukakashi akan su da hankali, kamar yadda Allah madaukaki ya bada kabarin haka da cewa: " kuma ya hore maku abunda ke cikin sammai da kasa baki daya lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (13)" suratul jasiya.
Ya kuma umurce su da kiyaye shi da kuma gyara shi da rayashi kamar yadda yake cikin siffan san a kasa da sama da ruwa domin yanayin ya zama yayi daidai ga rayuwan su aciki da kuma wanda zaizo a bayan su cikin mutane ta yadda ya hana barnatashi da abunda ke cikin sa, Allah madaukaki yace: " kada kuyi barna a cikin kasa bayan gyaruwan ta kuma ki kirashi kuna masu tsoro da kwadayi lallai rahamar Allah tana kusa ga masu kyautatawa (56)" suratul a'araf.

•    Khalifanci a cikin kasa:
Allah ya karrama mutum ya sanyashi ya zama khalifa a cikin kasa wasu suna maye wasu zamani bayan zamani basa karewa suna gadan ilimi da addini kuma domin sunnar Allah ta dore wanda yake so cikin wannan duniya, Allah madaukakai yace: " shine wanda yasanya ku khalifofi abayan kasa yana kuma daga wasu akan wasun ku a daraja domin ya jarabaku ya gani cikin abunda ya baku, lallai ubangijin ka me saurin ukuba ne kuma lallai me yawan gafara ne rahama (165)" suratul an'am.
Sai ya sanya wannan duniya zata iya dauke dukkanin halittun sa yadda ta dauki nauyin arzikin su da abincin su har zuwa lokacin da za'ayi umurni da karewan ta yadda yace: " kace yanzu kuna kafurcewa da wanda ya halicci kasa cikin kwanaki biyu kuma kuna sanya masa kishiyoyi, wancan shine ubangijin talikai (9) ya kuma sanya masa makarfafata da danneta da duwatsu a samanta ya kuma mata albarka ya kuma kaddara abinci da abubuwan maslaha na rayuwan mutanen cikinta cikin kwanaki hudu dai dai ga duk wani mabukaci (10)" suratul fussilat.

•    Haduwa da zama wuri daya da kuma hakkin kai:
Allah ya halicci mutane mabanbanta cikin fadin duniya domin wata hikima wanda yake sonta ya kuma sanya suka zama jama'a da kabilu kowa daga cikin su da irin dabi'ar sa da al'adar sa da harshen sa da yanayin sa domin su samu sanayya a tsakanin su kuma suyi masayan maslaha ta duniyar su da lahira, be halicce su ba domin ta'adi ga junan su da satan kayayyakin su a tsakanin su ba ko kuma wasu su mallake wasu da bautar dasu, kamar yadda Allah madaukaki ya bada labar da hakan cikin fadin sa cewa: " yaku mutane lallai mun halicce ku daga namiji da mace muka sanya ku kuka zama jama'a da kabilu domin ku samu sanayya a tsakanin ku, lallai wanda yafi wani a cikin ku a wurin Allah dajara shine wanda yafi tsoron Allah lallai Allah masani ne kuma me bada labari (13)" suratul hujurat.

Sai ya halicce kasa da banbanci wurin fitar da alheranta kamar yadda Allah ya halicci mutane mabanbanta cikin ikon su da hankulan su da yanayin su abunda zaka samu a wurin wasu jama'ar na alheri bazaka same shi ba a wurin wasu to kamar haka ne hakan be kasance ba sai domin tabbatar da wannan sanayya da kuma hakin kai da zamanta kewa akan abunda zai tabbatar da maslahar kowa sai fasaha su rika yawo da kuma musanyan sani sai a samu taimakekeniya me amfani a tsakanin su, Allah madaukaki yace: " shin ko sune suke raba rahamar ubangijin ka, mune muke rarraba abubuwan rayuwan su a tsakanin su cikin duniya kuma muna daga wasu akan wasu a daraja domin wasun su suyi aiki ga wasu su biya su, rahamar ubangijin ka tafi alheri sama da abunda suke Tarawa (32)" suratul zukhruf.

Be halicce su domin junan su su rika wulakanta juna ba ko kuma wasu su ruka kaskantar da wasu domin samun girma ko kuma amfani da wasu ta hanyar bautar dasu na neman abun rayuwa dasu, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani kada wasu su rika yima wasu isgilanci wata kila sun fisu alheri, kada kuma mata su rika yima mata yan uwansu isgilanci suma kila sunfi su alheri kada ku rika bata junan ku da magana kuma kada ku rika jiran junan ku da sunayen banza, tir da sunan fasikanci bayan imani kuma duk wanda be tuba to wannan sune azzalumai (11)" suratul hujurat.
Sabod ahaka ne musulunci ya tsawatar sosai akan dukkanin abubuwan da zasu kawo rarrabuwa da kin juna da kuma yada kiyayya da riko a tsakanin mutane wanda zai gadar da gaba a tsakanin mutane, Allah madaukaki yace: " boni ya tabbata ga me nune da me rada (1)" kuma ya tsawatar akan dukkanin abunda zai lalata al'umma na game da hassada wanda hakan dabi'ar shedan ne wanda ake samun shi cikin zukatan wasu muyagun mutane wanda basason alheri ga wanin su sai hakan ya haifar da fitina da yaduwar gaba da kiyayya a tsakanin mutane wasu su kace wasu kuma babu tausayi atsakanin su, saboda haka ne manzon Allah s.a.w yace: " kada kuyi hassada, kuma kada wani ya kuranta abunda yasan ba siya zayyi ba domin ya burge wani ya siya da tsada ko kuma makamancin haka, kuma kada kuyi gaba, kuma kada ku juyama juna baya, kuma kada wani yayi ciniki akan cinikin dan uwan sa, ku kasance bayan Allah yan uwan juna" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.

Ya kuma yi umurni da dukkanin abunda zai kawo hadin kan jama'a da yada soyayya da aminci a tsakanin mutane, Allah madaukaki yace: " babu alheri a cikin mafiya yawan tarin su sai taron da akayi shi domin umurni da sadaka ko kuma wani kyakyawan aiki ko kuma sulhu a tsakanin mutane, duk wanda ya aikata wannan abubuwa domin neman yardan Allah to da sannu za'a bashi lada me tarin yawa (114)" suratun nisa'i.

 

Asalin addini
Kamar yadda asalin mutum ya kasance daga mutum daya haka shima asalin addini ya kasance abu daya wanda Allah ya yardan musu dashi har zuwa tashin alkiyama, wannan addini shine musulunci, ma'anar musulunci shine mika wuya ga Allah da kuma jayuuwa gareshi da masa biyayya da tsarkaka daga dukkanin wani shirka, musulunci shine addinin annabin mu Adam amincin Allah ya tabbata agareshi, Allah madaukaki yace: " lallai addini a wurin Allahshine musulunci" suratu al'imran.
Addini wanda dukkanin ayyuka da hutawanka zai zama ga Allah ubangijin talikai babu wani mutum da yake da hakki ko kadan acikin su kamar yadda Allah madaukaki ya fadi: " kace lallai sallata da yanka na da rayuwa ta da mutuwa ta ga Allah suke ubangijin talikai (162) bashi da abokin tarayya da haka aka umurce ni kuma nine farkon musulmai (163)" suratul an'am.
Dukkanin manzanni Amincin Allah ya tabbata agaresu tun daga bayan Adam addinin su shine musulunci, kuma an aiko su domin kira gareshi dan su fitar da mutane daga bautan mutane yan uwansu zuwa ga bautan ubangijin mutane tun daga kan Nuhu amincin Allah ya tabbata a gareshi har zuwa na karshen su kuma cikamakon su Muhammad s.a.w, Allah madaukaki yace: " kuma bamu aike wani manzo ba gabanin ka face mun masa wahayi cewa babu wani abun bauta da gaskiya bisa cancanta sai ni saboda haka ku bauta mun (25)" suratul anbiya'i.

Shine addinin annabawa baki dayan su be kasance addini ba ga wani annabi shi kadai, shine addinin wanda Allah ya shar'anta kuma ya yarda dashi ga dukkanin bayin sa, Allah madaukaki yace: " ya shar'anta maku cikin addini irin abunda yayima Nuhu wasiyya dashi da kuma abunda akayima Ibrahim da Musa da Isa wasiyya dashi cewa su tsayar da addini kuma kada su rarrabu a cikin sa, abunda kake kiran mushirikai zuwa gareshi yayi masu girma, Allah shine wanda yake zaban wanda yasu zuwa gareshi kuma yana shiryar da wanda ya mika wuya zuwa gareshi (13)" suratul shura.

Kuma shine da’awar annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata agareshi baban Annabawa zuwa ga mutanen sa, Allah madaukaki yace: " Ibrahim be kasance bayahude ba ko kuma kirista sai dai ya kasance me mika wuya musulmi kuma bai kasance cikin mushrikai ba (67)" suratu al'imran.

Kuma shine wasiyya Ibrahim ga yaransa bayan sa kuma wasiyyayn yaran sa ga yaran su bayan su, Allah madaukaki yace: " kuma Ibrahim yayiwa yaran sa wasiyya dashi da Yakubu cewa yaku yayana lallai Allah ya zaban maku addini saboda haka kada ku mutu face kuna musulmai (132)" suratul bakara.

Kuma shine da’awar annabi Musa amincin Allah ya tabbata agareshi zuwa ga mutanen sa, Allah madaukaki yace: " kuma musa yace yaku mutane na idan kun kasance kunyi imani da Allah to ku dogara a gareshi idan kun kasance musulmai (84)" sutratu yunus.

Kuma shine addinin da Isa amincin Allah ya tabbata agareshi yake kai shida mabiyan sa kuma ya kira mutanen sa zuwa gareshi, Allah madaukaki yace: " a lokacin da Isa yaga rinjayan kafurci a wurin sai yace wanene zai zama mataimaki na zuwa ga Allah, sai hawariyyawa sukace mune mataimakan Allah, munyi imani da Allah kuma ka shaida cewa lallai mu musulmai ne (52)" suratu al'imran.

Kuma wannan shinea abunda annabi Muhammad s.a.w cika makon Annabawa ya karfafa shi kenan na kasancewar musulunci kira ne zuwa ga tauhidi (kadaita Allah) wanda shine asalin addinin dukkanin Annabawa da amnzanni kuma abunda aiko shi ya share acikin sa kawai shine hukunce hukunce na shari'ar annabawa da manzanni wanda suka gabata, yadda shari'ar sa cikakkiya kuma wacce ta kunshi komai kuma tayi daidai ga ko wani zamani da wuri ta canje su, amma akidar bata canza ba, sai manzon Allah s.a.w yace: " ni ne nafi kusa zuwa ga Isa akan mutane anan duniya da lahira, kuma annabawa yan uba ne, iyayen su mata ne suka banbanta, kuma addinin su daya ne". buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
[kasancewar annabawa yan uba ne kawai iyayen su mata ne suka banbanta kuma addinin su daya ne wanda shine kadaita Allah hakan yana nuna mana cewa dangantaka na hakika itace dangantakan akida da imani kuma da shine ake samun banbanci na falala bada iyaye ba].

Musulunci ba sabon addini bane kamar yadda wasu suke zato, shine addini na asali wanda ya wajaba dukkanin mutane suyi shi kasancewar sa asalin addinin su kuma Alah baya amsan wani bautan da aka masa in ba dashi ba, Allah madaukaki yace: " duk wanda ya riki wani addini wand aba musulunci ba to Allah bazai taba amsa mashi ba kuma a lahira yana cikin masu asara (85)" suratu al'imran.

Idan al'amarin ya kasance haka, to kayi gaggawa ya kai dan uwa makaranci me daraja na komawa zuwa asalin addinin ka wanda iyayen ka da kakannin ka suka kasance akai masu kadaita Allah stofaffi, ka bar dukkanin abunda aka shigar dashi cikin san wanda zai fitar dashi daga tauhidi zuwa ga shirka kuma daga sunna zuwa ga bidi'a a hannun iyayen ka da kakannin ka na baya bayan nan, idan ka kasance me koyi da bi to kayi koyi da bin iyayen ka na farko masu tauhidi wanda suka kasance akan bautan Allah shi kadai kada kayi koyi da bin iyayen ka wanda suka canza sababbi, Allah madaukaki yace: " idan akace masu kubi abunda Allah ya saukar sai suce a'a mu abunda muka samu iyayen mu akai zamu bi, yanzu koda shedan ya kasance yana kiran su zuwa ga azaba ne na wutan sa'ir (21)" suratu lukman.

Lallai komawa zuwa ga gaskiya yafi alheri akan mutum ya doge akan barna koda kuwa acikin aljihun me gidan ka da sarkinka da kuma wanda yake sonka ne, ni'ima me dawwama tafi alheri akan ni'ima wacce take gushewa, kuma lallai inada tabbacin cewa da ace kowa a cikin mu zai bibiyi dangantakan sa na iyaye da kakanni tabbat zai samu daya daga cikin su cewa musulmi ne, wannan gaskiya ce nake fadi domin abita saboda haka kayi gaggawa kada ka tsaya shakka.


Farkon shirka a cikin mutane:
Zamanin dake tsakanin annabi Adam da Nuhu karni goma ne mutane sun kasance cikin su akan addini daya wanda shine (musulunci) kadaita Allah shi kadai da kuma rashin yi masa shirka da wani cikin bayin sa kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari cikin fadin sa cewa: " mutane sun kasance al'umma daya sai Allah ya aiko masu da annabawa masu bishara da gargadi ya kuma saukar da littafi tare dasu da gaskiya domin suyi hukunci a tsakanin mutane cikin abunda suka samu sabani akan sa, kuma basu samu sabani ba acikin sa sai ga abunda aka basu bayan hujjoji bayyanannu domin zalumci a tsakin su, sai Allah ya shiryar da wanda sukayi imani cikin abunda suka samu sabani akan san a gaskiya da izinin sa, Allah yana shiryar da wanda yaso zuwa ga hanya madaidaiciya (213)" suratul bakara.

Hakan ya kasance sakamakon dabi'a na yawan zurriyan Adam zamani bayan zamani wanda suka yadu cikin doron kasa suna neman arziki da kuma neman wurin da zai dauke su, sai ya kasance sakamakon wannan yaduwar ya sanya suka yi nisa ga asalin su na kwarai na bautan Allah sai sabani da miyagun ayyuka ya fara yaduwa a tsakanin su da kuma shigar da abunda yana cikin addina cikin addini har suka juya akidar su, suka bace gada hanya madaidaiciya wanda hakan shin abunda shedan yake so wanda ya fitar da baban mu Adam da hauwa'u daga cikin aljanna kuma kiyayyar sa da hassada yaci gaba akan yaran sa bayan sshi domin ya jefa musu shirka acikin su da sabon Allah wanda zai kais u zuwa ga wuta kamar yadda Allah yabada labari da hakan yace: " ka tuna a lokacin da muka cema mala'iku kuyi sujjada ga Adam sai duk sukayi sai shedan kadai yakiyi yace ya za'ayi nayi sujjada ga abunda halitta daga tabo (61) sai yace kaga wannan dinnan daka karrama shi akaina idan hark a jinkirta mun har zuwa ranan alkiyama to sai na batar da zuriyar shi baki dayan su sai yan kadan daga cikin su (62) sai Allah yace masa tafi kuma duk wanda yabika daga cikin su lallai wutan jahannama itace sakamakon ku isashe (63)" suratul isra'i.

Ya kasance farkon bayyanar shirka a doron kasa itace cikin mutanen Nuhu amincin Allah ya tabbata a gareshi yadda shedan ya kawata masu bautan gumaka a hankali a hankali ba lokaci da yaba farko dai ya fara kawata masu cewa su girmama mutanen wannan kabar-buran da kuma zama a wurin su har suka fada cikin shirka, hakan ya farune domin ka'ida ta fiqhu cikin musulunci ta haramta dukkanin zai zama hanya zuwa shirka, Allah madaukaki yace yana me hakaito labari akan su: " Nuhu yace ya ubangijina lallai sun sabamun kuma sunbi abunda baya kara masu dukiya da yara sai asara kawai (21) kuma sunyi makirki makirci na girman kai (22) kuma sunce kada ku bar allolin ku kuma kada kubar wadda da suwa'a da yagusa da nasra (23)" suratu nuhu.

Ibn Abbas yace: wannan sunayen bayin Allah ne na mutanen nuhu, bayan Allah ya kasheshu sai shedan yayi masu wahayi da cewa su sassaka gumaka na dutse ko na wani abun su ajiye su a wuraren zaman su domin su rika tuna wa dasu, sai suka aikata hakan suka kirasu da sunayen wancan bayin Allah amma basu bauta masu ba, har sai bayan wannan sun mutu sun tafi bayan an manta ilimi sai aka bautama wannan gumaka" [sahihul buhari].

Ya zauna a cikin su tsawon shekaru dubu daya babu hamsin yana kiran su dare da rana har yayi amfani da dukkanin salo na da'awa a boye da bayyane amma sukayi girman kai kuma suka sabama Nuhu sai ya roki ubangijinsa ya hallaka su da ruwan dufana, Allah madaukaki yace: " yace ya ubangijina lallai ya kira mutane na dare da rana (5) amma kirana baya kara masu komai sai kaura ce mun (6) kuma duk lokacin dana kira su domin ka gafarta masu sais u sanya hannayen su cikin kunnuwan su karama rigunan su iska kuma suka ci gaba akan abunda suke kai da kuma yin girman kai babba (7) sa'annan na kirasu a bayyane (8) sa'annan kuma na kirasu a biye da asirce (9)" har zuwa fadin sa cewa " sai Nuhu yace ya ubangijina kada kabar wani cikin kafirai a doron kasan nan (26) domin kuwa idan ka barsu zasu batar da bayin ka kuma bazasu Haifa ba sai yara fajirai kafirai (27)" suratu Nuhu.

Bayan Allah ya halaka mutanen Nuhu ya kuma tsiratar dashi da wanda sukayi imani dashi cikin muminai da abunda suka kwaso cikin halittu cikin jirgin ruwa kamar yadda Allah madaukaki ya bayyana cikin fadin sa: " har lokacin da al'amarin mu yazo idanuwan ruwa suka cika kasa ko ina suna fitar da ruwa sai muk ce musu ku dauki aure cikin ko wani halitta tare daku cikin wannan jirgin ruwa da iyalan ka sai wanda alkawari ya rigaya akan su da wanda sukayi imani, basuyi imani dashi sai yan kadan (40)" suratu Hud
Raya kasa ya fara daga farko da mutanen da sukayi imani da Nuhu cikin muminai bayan zamani yayi tsayi sun mutu sai wasu mutane da suka zo abayan su shedan ya kawata masu aikin sassaka iyayen su wanda Allah ya tsiratar dasu daga ruwan dufana domin su rika tunawa dasu har al'amarin yaci gaba zuwa ga mutanen da ke bayansu suka fara bauta masu, sai Allah ya aiko masu da annabi Hudu amincin Allah ya tabbata a gareshi domin ya dawo dasu zuwa ga addini na gaskiya suka saba masa sai Allah ya halaka su da iska makauniya kurma, Allah madaukaki yace: " ku tuna dan uwan Adawa lokacin daya gargadi mutanen sa daga dutse da guguwa kuma masu gargadi sun gabata agaban su da bayan su da cewa kada ku bautawa kowa sai Allah, lallai ina maku tsoron wata azaba a kanku me girma (21) sai sukayi yanzu shin kazoo mana ne domin ka hufantar damu daga allolin mu to kazoo mana da abunda kake mana alkawari din idan ka kasance cikin masu gaskiya (22) sai yace lallai ilimi yana wurin Allah kuma na isar maku da abunda aka aiko ni dashi sai dai ni ina kallon ku a matsayin mutane masu jahilta (23) a lokaci da suka ganshi a matsayin hadari yana fuskantan gidajen su sai sukace kai wannan hadari ne wanda za'a mana ruwa, ina ai abunda da kuka kasance kuna gaggawa ne akan zuwan s, iska ne wanda acikin sa akwai azaba me radadi (24) tana darkake komai da umurnin ubangijinta sai aka wayi gari ba'a ganin komai sai gidajen su kawai, da Kaman haka ne muke sakawa mutane mujirimai (25)" suratul ahkaf.
Sa'annan mutanen samudawa sukazo bayan su suka bautawa gumaka sai Allah ya aiko masu da annabi Salihu amincin Allah ya tabbata agareshi domin ya dawo dasu zuwa ga bautan Allah sai suka karyata shi sai Allah ya halaka su, Allah madaukaki yace: " su kuma samudawa mun halaka su ne dalilin taguwa (5)" suratul hakkah.

Su kuma mutanen annabi Ibrahim baban Annabawa amincin Allah ya tabbata agareshi sun bautawa taurari da gumaka sai ya tsawatar masu ya kuma hanasu bautan su amma basu amsa kiran sa ba sai Allah ya halaka su, Allah madaukaki yace: " hakika mun ba Ibrahim shiriyan sa tun gabani kuma mun kasance masani game dashi (51) lokacin da yace ma mahaifin sa da mutanen sa menene wannan sassakin da kuke bautamawa (52) sai sukace muma dai haka muka samu iyayen mu suna bauta musu (53) sai yace hakika kun kasance ku da iayayen naku cikin bata bayyananne (54)" suratul anbiya'i.

Daganan sai bani isra'ila suka zo Allah ya aika masu annabi Musa amincin Allah ya tabbata agareshi sai suka riki dan maraki suna bauta masa koma bayan Allah wanda hakan shine farkon shirka acikin su, Allah madaukaki yace: " sai mutanen Musa suka riki dan maraki a bayan idon sa wanda yake fitar da sauti, shin basu gani bane cewa baya masu magana kuma baya shiryar dasu zuwa ga wani alheri, sun rikeshi ne kawai kuma sun kasance azzalumai (148) alokacin da ya fadi daga hannayen su kuma sukaga cewa hakika fa sun bace sai sukace idan dai ubangijin mu be mana rahama ba ya kuma gafarta mana to tabbas zamu kasance cikin masu asara (149)" suratul a'araf.

Sannan kuma a karshen zamanin su suka bautawa Uzairu sai Allah ya aiko masu da annabi Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi domin ya mayar sasu zuwa ga tauhidi da bautan Allah shi kadai, Allah madaukakik yace: " a lokacin da Isa dan Maryam yace yaku bani isra'ila lallai ni manzon Allah ne zuwa gareku me gasgata abunda yake gaba a gareni na attaura kuma ina bishara da zuwan wani manzo abayana me suna Ahmad, a yayin da yazo masu da hujjoji sai sukace kai wannan sihiri ne a bayyane (6)" suratul saf.

Al'amarin yaci gaba har yakai ga sun bautawa annabi Isa amincin Allah ya tabbata agareshi koma bayan Allah sukace wannan dan Allah ne kuma sukace shine dayan ukun Allah- Allah ya daukaka daga abunda suke fadi daukaki me girma-, Allah madaukaki yace: " yaku ma'abota littafi kada ku wuce gona da iri cikin addinin ku kuma kada ku rika fadin komai akan Allah sai gaskiya, lallai masihu Isa dan Maryam manzon Allah ne da kuma Kalmar sa wanda aka wurga zuwa ga Maryam da kuma ruhi daga gareshi, kuyi imani da Allah da manzannin sa kuma kada ku rika cewa Allah dayan uku ne idan kun bari zaifi maku alheri, lallai Allah shi kadai yake tsarki ya tabbatan masa ace yana da yaro, abunda suke cikin sammai da kasa nashi ne kuma Allah ya isa ya zama wakili (171)" suratun nisa'i.

Shekaru dari shida ya kasance zamani tsakanin annabi Isa da aiko annabi Muhammada s.a.w wanda duhu ya karade duniya baki dayan ta saboda tsaban shirka har ya kusa da kaiwa babu wani mai bautan Allah akan addinin gaskiya- sai dai wasu yan tsiraru cikin ma'abota littafi wanda suke bautawa Allah akan addinin annabi Ibrahim masoyin Allah amincin Allah ya tabbata a gareshi, wanda sune mabiya Ariyus- yadda shedan ya kawata masu cikin wannan lokaci ababen bauta dayawa, wasu ya kawata masu bautan wuta da ruwa da dutse da bishiya da sanuwa kai har ma da bautan shedan kansa da dukkanin abunda hankalin su ya karkata zuwa gareshi da tunanin su wanda yasanya su bin wanin Allah suka bautawa halittu irin su wanda suka gaza wurin amfanar dakansu da komai bare amfanar da wasun su, kuma Allah yayi gaskiya inda yace: " ….. abunda kuke kira koma bayan Allah basu mallaki koda misalin zaren cikin kwallon dabino ba (13) idan kuka kiraye su basa jin kiran ku koda sunji ma bazasu iya amsa maku ba sannan kuma ranan alkiyama zusu kafurce ma shirkan da kukeyi masu kuma babu wanda zai baka labari kaman na masani (14)" suratu fadir.

malam kirawani ya sawwara wannan zamani na duhu Allah yayi masa rahama yace: lallai yadda al'amarin yake- watan annabi Muhammad s.a.w ya bayyana ne a lokacin da mutane suka kasance suna da bukatan wanda zai shiryar dasu zuwa ga hanya mikakkiya, zai kirasu zuwa ga addini mikakke, saboda larabawa sun kasance suna bautan gumaka da kuma kashe yara mata, su kuma kasar farisa sun kasance akan ikidar alloli biyu [watan allan alheri da sharri ko kuma allan haske da duhu] da kuma zina da yan mata da iyayen su, shi kuma tatar yanakan lallata garuruwa da azabtar da mutane, su kuma Hindu sun kasance akan bautan sanuwa da sujjada ga bishiya da duste, su kuma yahudawa sun kasance akan maguzanci da kuma kamanta halitta da mahaliccin su da yada karya da maganganu marasa hujja, su kuma kiristoci suna kan akidar cewa allah dayan uku ne da bautan gumaka da hutunan manyan malamai masu tsarki da mata masu tsarki, haka dai sauran kungiyoyi na addini suka kasance cikin bata da canzawa daga gaskiya da shagaltuwa da abunda bazzayyiwu ba, kuma baya dacewa da hikiman Allah me mulki da cewa kada ya aiko da wani manzo cikin wannan lokaci wanda zai zama rahama ga duniya baki daya, kuma babu wani wanda ya bayyana wanda ya dace da wannan abu me girma kuma ya gina wannan gini me kwari sai annabi Muhammad dan Abdullahi s.a.w, sai Allah ya kawar da alamomi na bata da maganganu gurbatattu ya kuma kunna hasken tauhidi, da jirgin tsarkakewa, ya kuma kawar da hudun shirka maguzanci, da alla dayan uku, da kamanta halittu da mahaliccin su, tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi.

A daidai wannan yanayi ne Allah ya aiko Annabi Muhammad s.a.w bayan yakai shekaru arba'in da haihuwa bayan Allah ya zabe shi kamar yadda ya zabi annabawan da suka gabace shi kamar Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa ya kuma saukar masa da shari'a wacce ta dace da kowani zamani da wuri wacce ta kunshi shari'a wanda ya lamuncewa rayuwan kowa cikin mutane cikin aminci da zaman lafiya da yalwa na zama da kuma jin dadi da rayuwa me kyau da karamci ga kowa, daga cikin abunda yake nuni akan wannan cewa shari'a daya ce cikin abunda na fadi, manzon Allah s.a.w yace: " lallai jinin ku da dukiyoyin ku da mutuncin ku haramun ne a tsakanin ku kamar haramcin wannan rana taku" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.

Da’awar sa ta kasance kamar da’awar sauran yan uwan sa annabawa wanda suka gabace shi kira zuwa ga imani da Allah shi kadai da kuma barin shirka dashi, kra zuwa ga alheri ga dukkanin nau'ukan alheri, da kuma tsawatar wa akan shirka da dukkanin nau'in ta, aiko shi ya kasance rahama ga duniya da kuma ni'ima ga halittu baki daya domin fitar dasu daga abunda suka kasance a ciki na bata da jahilci, Allah madaukaki yace: " hakika Allah yayima muminai ni'ima daya aiko masu manzo daga cikin su wanda yake karanta masu ayoyin sa yan akuma tsarkake su da kuma karantar dasu littafin sa da hikima bayan sun kasance gabanin sa cikin bata bayyananne (164)" suratu al'imran.
Da aiko sa aka cikama mutum addinin sa kuma aka cika masa ni'imar Allah a gareshi, Allah madaukaki yace: " a yau ne zan cika maku addinin ku kuma zan cika maku ni'imata agareku kuma na yardan maku da musulunci ya zama addini agareku" suratul ma'ida.

Anan wurin tambaya zai zo kwakwalwan mutum cewa shin tsari da dokoki wanda mutum ke kirkiya da shari'a da kundun tsarin mulkin mutum wanda aketa yayata shi da tallata shi ayau dare da rana a cikin fadin duniya me ya kaddamar ga mutum shin ya tsiratar dasu? Shin ya kosar dasu daga yunwan su? Shin ya saukake hanyoyin rayuwa me inganci a garesu? Shin ya daraja mutum? Shin ya basu yancin sun a hakika wanda zai kiyaye masu karamar su? Ko kuma yanci ne mayaudariya wacce ta kunshi barna da lalata duniya da kuma dadashe dukkanin wani hali na gari da ko wani shari'a da addini?!!!

Ka tambayi kanka wannan tambaya sannan ka dubi duniya wanda kake ciki zakaga cewa lallai wannan tsarukan amfanin su ga wasu kasashe ne banda wasu kuma ga wasu mutane kawai yan kadan banda wasu wanda suke son baitar da wanin su cikin mutane, sanadiyyan shi yunwa ta yadu cikin kasashe dayawa! Da kuma mulkan kasashe da mayar dasu bayi duka wannan ya samu ne saboda wannan tsarin na duniya! Yaki da tsoro duk abunda yake kawo ta shine dai wannan tsari na duniya! Wannan shine abunda da dokoki da tsari na mutum ya kaddamar ma mutane a duniyan nan, saboda haka ku koma zuwa ga asalin ku zaku tsira da rabauta duniya da lahira.

Bukatan mutum game da aiko annabawa
Lallai mutum ba tare da addini ba da shari'a zai wayi gari Kaman dabba ne wanda bashi da wani hadafi face maslahar kansa da kuma abunda zai samu na dukiya cikin wannan duniya babu ruwan shi da cewa ta wani hanya ya samu, ita kamar birki ne wanda yake tsara harkokin mutum da kuma toshe sharrin dake cikin zuciyar sa, idan babu addini dokan daji ne zai jagoranci mutum wanda me karfi yake cin mara karfi kuma a cire rahama a cikin zuciya, addini da shari'a rahama ne ga mutane baki daya wanda ya wajaba ayi kira zuwa ga aiwatar da ita saboda ta lamuntar maka hakkokin ka da kuma rayuwan ka me daraja ta halin arzikin ka da talaucin ka da duma halin lafiyar ka da rashin lafiyar ka da halin karfin ka dana raunin ka domin sanin haka saura kaji bangare cikin bangarorin shari'a wanda aka saukar ma Muhammad manzon Allah s.a.w wacce kuma ya karade dukkanin lamuni ga hakkokin mutum wanda zai zo mas aba tare da ya nema ba ko kuma wahala domin samun ta ba a duk lokacin daya aiwatar da ita, yana cewa: " dukkanin ku makiwata ne kuma dukkanin ku za'a tambaye ku akan abun kiwon ku, shugaba me kiwo ne kuma za'a tambaye shi akan abun kiwon sa, namiji me kiwo ne akan iyalan gidan sa kuma za'a tambaye shi akan kiwon sa, mace me kiwo ce akan gidan mijin ta kuma za'a tambaye ta akan kiwon ta, me aiki me kiwo ne akan dukiyar me gidan sa kuma za'a tambaye shi akan kiwon sa,- sai yace kamar ina tsammanin yace: mutum me kiwo ne akan dukiyar mahaifin sa kuma za'a tambaye shi akan kiwon sa- dukkakinin ku makiwata ne kuma za'a tambayeku akan kiwon ku" buhari da muslim ne suka rawaito shi.
 
saboda haka ne Allah yake daukan aiko manzanni a matsayin ni'ima cikin ni'imomin da Allah yayi ma mutum da kuma rahama cikin rahamar sa wanda ya daukaka dashi da ita yadda be barsu hakan ba kara zube suta amfani da zaton su dason zuciyar su ko kuma hankulan su wanda yake da iyaka da rauni wacce ta gagara warin shiryar dasu ba tare da shari'a ba da kuma addini, daga cikin abunda Allah yaba mutum na hanyoyin sani da ilimi daji da gani da hankali basu da iko akan shiryar dashi da masu jagora zuwa ga hanya wacce taka kaiwa zuwa ga manufa wacce saboda itace aka halicce mutum kuma bazata ita sanya masu shari'a ba da dokoki wacce zata tsara rayuwan su ta kuma tabbatar da adalci a tsakanin su da daidaito kuma ta lura da darajar su ta mutane a cikinta ba'a banbanta wani akan wani acikinta sai da tsoron Allah da aiki na kwarai, shari'a ce wacce bata bin son rai kuma bata tasirantuwa da abunda ke kewaye da ita wanda yake da tasiri na waje wacce take da tasiri wurin gyaruwanta da karade wanta da kuma kasance warta na duniya baki daya wacce tayi daidai da ko wani wuri da zamani, Allah madaukaki yace: " yaku yan adam idan manzannin mu suka zo maku suna karanto maku ayoyin mu duk wanda yaji tsoron Allah ya kuma gyara to babu tsoro a garesu kuma baza suyi bakin ciki ba (35) wanda kuma suka karyata ayoyin mu sukayi girman kai daga garesu wannan sune yan wuta suna masu dawwama a cikin ta (36)" suratul a'araf.
    
Dabi'ar mutum da kuma yanayin sa wanda Allah ya halicce sa akai bazata iya yin wannan aiki ba me girma kuma wannan ba aibi bane hasali ma al'amari ne na dabi'a wanda yake nuna buqatarr sa zuwa ga mahaliccin sa wanda zai tafiyar dashi akan tafarki da shari'a wacce zata gyara halin sa, hankula sunada rauni bazasu iya tsara halin me ita ba to tayaya zata zata iya tsara halin mutune baki daya saboda gazawarta da kuma karancin dabararta da kuma sabanin su da kuma banbancin su wurin iyaka abunda yake daidai a wurin wasu zai iya zama akasin haka a wurin sauran haka kuma saboda kasancewar sa be san komai ba sabanin abunda yake gani ko kuma tabawa da kuma rashin saninta da abunda zai faru nan gaba, abunda aka amshe shi ayau gobe za'a iya kin amsan shi, Allah madaukaki yace: " Allah yana son ya sawwaka maku kuma ya halicci mutum da rauni (28)" suratun nisa'i.
    
Kuma haka dabi'ar hankali wanda Allah ya halicce ta akai na gaggawan isa zuwa ga abu da kuma kokwanto da rashin tabbatan ta a hali daya kanaso kuma tana ki, tana bayarwa kuma ta hana, tana karfafawa da kuma yin inkari… zuwa dai karshe dukkan haka bazai bata cancanta ba na zama me yin doka da tsarin rayuwan mutum ba, Allah madaukaki yace: " kuma mutum yana yima kansa addu'a na sharri kamar yadda yakeyin addu'ar akheri akan sa, mutum ya kasance me gaggawa (11)" suratul isra'i

Kokwanton wannan hankula da kuma kai komanta da rashin tsayawan ta akan hali daya sai aka yita akan amsan kyauta dayawa da kuma son kai dayawa sama da kowa ya samu da kuma rikewa sama da bayarwa, Allah madaukaki yace: " kace da ace kune kuke rike da taskar rahamar ubangiji na to da kun rike saboda tsoron bayar wa, mutum ya kasance me tsaban rowa (100)" suratul isra'i.

Kari kuma akan yadda aka halicce sa akai na dabi'a wannan hankulan na mantuwa da kuma rashin sanin sinadarin da suke kewaye da su abunda ya kasance ayau daidai zai iya kasancewa a gobe kuskure, kuma abunda ya kasance gaskiya a yau abunda zai faru gobe zai iya karyata shi haka dai ka kiyasta akan haka akwai wasu daga cikin bincike na hukuncin mutum wanda suke daidai a jiya amma hankali ya karyata su ayau, kamar yadda bata zama wacce bata sabo ba tana bayar da hukunci ne sakamakon halin yanzu da kuma bukatan mutane wanda take rayuwa a cikinta, ka dub aka gani zagaka dayawa daga cikin wannan dokoki da tsari na kasashe wanda zababbun mutanen su suka rubuta ya fara cancanzawa saboda wani abu da ya fura shi kadai a wannan kasa wanda hakan ya tilasta mata canza wannan tsari nasu da dokoki da abunda zai dace da yanayin su wanda suke ciki abunda wannan hankali take sanya shi ya zama doka da kuma shar'anta shi bashi da tabbas sannan kuma bai zama me dacewa ba da dukkanin zamani da wurare sabanin shari'ar ubangiji, Allah madaukaki yace: " lallai an halicci mutum me butulci (19) idan sharri ya same shi baya hakuri (20) kuma idan alheri ya same shi baya godiya (21)" suratul ma'arij.

Muduba mugani misali abunda hankula suka gabatar akan wasu mutane cikin al'umma na kayan yaki masu kisa da lallatawa cikin ababen da suka kirkiro na mulkan mutane wanda suke lallata kasashe da mutane da sunan mulkin mallaka kuma suna alfari da ikon su na kirkiro ilimi- sunce- shin wannan baya cikin sakamako na rashin shari'a cikin rayyuwan su da kuma rashin imanin su da gaibu na cewa akwai fa tashi bayan mutuwa da kuma hisabi akan ayyuka idan alheri mutum ya aikata to zai ga alheri idan kuma sharri ya aikata to zai ga sharri, da ace sun kaance sunyi imani da gaibu da basu aikata komai ba sai abunda yake alheri ne ga kawunan su da mutane kuma sun nisanci dukkanin abunda yake da sharri acikinsa gare su da mutane baki daya, Allah madaukaki yace: " duk wanda ya aikata kwatankwacin kwayan zarra na alheri zai ganshii (7) wanda kuma ya aikata kwatankwacin kwayan zarra na sharri shima zai ganin shi (8)" suratul zilzilat.

Haka kuma lokacin da wannan hankula suka gabata a karkashin rashin imani da gaibu na abun bauta sai abun bautan da suke gina masu gidajen su kamar su duwatsu da bishiya ko kuma abun bautan da suke dafa abinci da bun sha a kan su kamar wuta ko kuma abun bautan da mutum yake cin su kamar shanu ko kuma abun bautan da suke kashewa Kaman bera ko kuma abun bautan da suke tabbatarwa cewa sune mafarin sharri kamar shedanu… da dai sauran su.

Saboda haka ne aiko da manzanni yana cikin abun da suke bukata na halittan su domin su bayyana masu shari'a wacce zata kare su baki daya daga kura kurai ya kuma masu bayanin hukunce hukunce na daidai, kamar kuma yadda muka ce ne lallai mutum da abunda aka bashi na hankali da ilimi suna tsayawa ne akan riskan abubuwan da suke iya gani ko kuma tabawa cikin wannan duniya amma duk abunda yake na gaibu ne bazasu iya sanin sa ba ko kuma riskan sa sai ta hanyar manzanni, misali tsohon tarihi na mutanen da suka gabata gabanin mu bazamu iya sanin sub a face ta hanyar abunda masani tarihi suka rubuta mana badan rubutun su ba da ace hankulan duniya baki dayan su zasuyi aiki domin sanin wannan tarihi bazasu taba iya sani ba, haka manzanni wanda hakan yana cikin karramawan Allah a garesu na aiko masu da manzanni lokaci bayan lokaci duk lokacin da mutane sukayi nisa akan hanyar gaskiya sai Allah ya aiko masu da manzo wanda zai mayar dasu zuwa kan hanyar gaskiya da kuma yi masu bayanin shari'a wanda zasu tsara harkokin su nasu dana mutane baki daya da kuma manhajin da zasuyi tafiya akai domin isa zuwa gareshi, kuma domin ya zama hujja akan su cikin aiko su kamar yadda Allah madaukaki ya bayyana haka cikin fadin sa: " manzanni masu bishara da gargadi saboda kada mutane su zama sunada hanzari akan Allah bayan aiko da manzanni, Allah ya kasance mabuwayi kuma me hikima (165)" suratun nisa'i.
Sai wahayi wanda aka saukar akan manzanni ya zama rayuwa ga mutane da kuma haske wanda zasu rika ganin gaban su dashi da kuma haskaka duhun jahilci dashi, da kuma hanya ta tsira a garsu na abunda suke ciki na bata, da kuma nasara ko kuma rashin rasara wanda ya ratayu akan rikon su dashi ko kuma saba masa babu hanya wanda yake kai halittu zuwa ga mahaliccin su sai ta shi duk kuma wata hanya wanda bashi ba to me halakarwa ce da batarwa kamar yadda Allah ya bada labari cikin fadin sa: " kace yanzu zamu rika kiran wani abu koma bayan Allah wanda bazai amfanar damu ba ko kuma cutar damu kuma mu koma zuwa ga kafurcin mu bayan Allah ya shiryar damu kamar wanda shedanu suka batar dashi yana cikin dimuwa yanda mutane wanda suke kiransa zuwa ga shiriya sun ace masa zo muje ga hanyar gaskiya nan, kace shiriyar Allah ita ce shiriya kuma an umurce mu da mika wuya ga ubangijin talikai (71)" suratul an 'am.

Sa'annan bayan haka sai zabi ya rage ga mutum wurin amsan abunda Allah ya saukar akan manzon sa ko kuma yaki amsa domin ya tsira ta sanadiyyar sa ko kuma halaka idan yaki amsa kamar yadda Allah madaukaki ya fadi: " da ubangijin ka yaso da mutanen duniya sunyi imani baki dayan su, yanzu shin zaka rika tilastama mutane ne har sai sun zama muminai (99)" suratu yunus.

Mahalicci yayi gaskiya me tsarki da daukaka cikin bayyanawar sa cewa lallai wahayin da ya saukar akan manzanni kamar misalin ruhi ne ga jiki, kamar yadda rayuwan gangan jiki bazata kasance ba sai da ruhi haka rayuwan zuciyar mutum da tabbatawanta da kuma natsuwan sa baya kasance wa sai ta hanyar sa, Allah madaukaki yace: " haka kuma mukayi wahayin ruhi cikin al'amarin mu zuwa gareka baka kasance kasan menene littafi ba ko kuma imani ba gabanin sa sai dai mun sanya shi haske muna shiryarwa dashi ga wanda muke so cikin bayin mu, kuma lallai kai kana shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya (52)" suratu shura.

Kasancewar annabawa da manzanni mutane ne amincin Allah ya tabbata a garesu:
Dukkanin manzanni da annabawan da Allah ya aiko sun kasance cikin mutane kuma hakan shine sunnar Allah cikin halittan sa yana aiko da manzanni daga cikin su mutum irin su kalar fatar su kuma ba wanda yake da banbanci dasu ba sai da abunda Allah ya daukaka su dashi na wahayi da sako, kuma hakika kafirai sun riki cewa- manzanni fa mutane ne- a mastayin dalili na inkarin annabtar su, kamar yadda Allah madaukaki ya bada labarin haka akan mutanen Nuhu da adawa da samudawa dacewa sun ki yarda da kiran manzannin su ne badan komai ba sai dan kasancewar su mutane cikin fadin sa cewa: " sai amnzannin su suka ce masu yanzu kuna shakka ne game da Allah wanda ya kirkiri halitan sammai da kasa yana kiranku domin ya gafarta maku zunuban ku kuma ya jinkirta maku zuwa wani lokaci sananne, sai sukace ku din nan bakomai bane face mutane irin mu kuna son ku kange mu daga abunda iyayen mu suka bautamawa to ku zo mana da hujja bayyananne (10) sai manzannin su sukace masu mu bakomai bane face mutane irin ku sai da Allah yana bayar da ni'ima ga wanda yake so cikin bayin sa kuma bazamu iya zuwa maku ba da wani hujja sai da izinin Allah kuma ga Allah ne muminai suke dogaro (11)" suratu Ibrahim.
    
Sannan kuma daga fir'auna da yan fadan sa sarakuna bayan sun karyata annabi Musa amincin Allah ya tabbata agareshi sun bayyan adalilin da yasa sukayi inkarin sakon sa da kuma kare mutane da suke tayi daga gareta, Allah madaukaki yace: " sa'annan muka aiki annabi Musa da dan uwansa Haruna da ayoyin mu da hujjoji bayyanannu (45) zuwa ga fir'auna da sarakunan sa sai sukayi girman kai kuma sun kasance mutane musu girman da zalumtar wanda basu ba (46) sai sukace yanzu zamuyi imani da mutane irin mu bayan mutanensu mu suke bautamawa (47)" suratul muminun.
    
Wannan iatce dabi'ar masu karyatawa da jayayya ga kiran manzanni wanda suke son bata da kuma batar da mutane zuwa bata, haka cikamakon annabawa da manzanni shima be tsira ba daga cirin wannan magana hakika kafiran kuraishawa suma sunbi irin wannan hanyar wanda suka gabace su wurin karyata manzanni, Allah madaukaki yace yana bayyana haka: " sai wanda sukayi zalumci na shirka suka kulla zama a tsakanin su da cewa shin wannan fa da yake kiran ku mutum ne irin ku, shin yanzu zakuje ma sirihi bayan kuna gani da hankalin ku (3)" suratul anbiya'i.

Dukkanin manzanni baki dayan su babu cire daya daga cikin su, ba alloli bane kuma babu wanda yake da siffar allantaka ko daya a cikin su, wannan annabi Isa ne amincin Allah ya tabbata agareshi yana nisanta kanshi daga abunda aka jingina masa wanda sukace na ikirarin allantakan sa, Allah madaukaki yace: " a lokacin da Allah yace ma Isa dan Maryma kai ne kace ma mutane su rike ka da mahaifiyar ka a matsayin abun bauta koma bayan Allah, sai yace tsarki ya tabbata a gareka baya halatta a gareni na fadi abunda bani da hakki akan sa idan ni nafadi haka hakika kasani kasan abunda ke cikin raina amma ni bansan abunda ke cikin rank aba lallai kaine masanin gaibu (116) bance masu komai ba sai abunda ka umurce ni dashi cewa ko bautawa Allah ubangijina da ubangijin ku, kuma na kasance me sheda a garesu tsawon zaman danayi acikin su, amma a lokacin da ka kashe ni kai ne me kula da su kuma kai me sheda ne akan komai (117)" suratul ma'ida.
    
Haka shima annabin Muhammad s.a.w ya kore ma kansa cewa yanada wata siffa ta allantaka, Allah madaukaki yace: " kace masu bana iya mallaka wa kaina wani amfani ko kuma kawar mata da wani cutarwa ba sai abunda Allah ya so, da ace nasan gaibu kuma da ban yawaita aikin alheri ba kuma da babu wani mummunan abunda zai same ni, ni ban kasance ba face me gargadi da bishara ga mutane muminai (188)" suratul a'araf.
    
Ya isa hujja akan kasancewar su mutane cewa abunda ke samun mutum na mutuwa suma yana samun su basu kasance suna dawwama ba, kamar yadda mahalicci me tsarki da daukaki yaba da labari cikin fadin sa cewa: " dukkanin wata rai sai ta dandani mutuwa, kuma za'a sakanya maku ladan ayyukan ku ranan alkiyama, duk wanda aka ketarar dashi daga wuta aka shigar dashi aljanna to hakika ya rabauta rayuwan duniya ba komai bace face jin dadi na rudu (185)" suratu al'imran.

    Kuma bala'i yana shafan su kamar yadda yake shafan sauran mutane suna rashin lafiya da cuta, kamar yadda cuta ta shafi annabi Ayyub amincin Allah ya tabbata a gareshi na bala'i a jikin sa da karewan dukiya da tafiyan yaron sa da matan sa sai yayi hakuri akan haka, Allah madaukaki yace: "kuma Ayyuba lokacin daya kira Ubangijin sa cewa cuta ta same ni kuma kaine mafi tausayin masu tausayi (83) sai muka amsa masa muka yaye masa abunda ke damunsa na cuta muka kuma bashi iyalan sa da kuma irin su tare dasu rahama daga garemu da kuma tuna ga masu bauta (84)" suratul anbiya'i.

    Kuma ana kulle su da Koran su daga gidajen su, kamar yadda Allah ya bada labarin haka cikin fadin sa: " sai wanda suka kafurta sukace ga manzannin su zamu fitar daku daga kasar mu ko kuma ku dawo cikin addinin mu, sai ubangijin su yayi wahayi agaresu cewa wallahi sai mun halaka azzalumai (13) kuma wallahi sai mun gadar maku da kasa bayan su wannan ga duk wanda yaji tsoron tsayawa a gabana ranan alkiyama kuma yaji tsoron azabata 914)" suratu Ibrahim.

    Kuma ana kashesu kamar yadda Allah ya bada labarin haka game da wasu daga cikin annabawa cikin bani isra'ila wanda kafirai cikin bani isra'ila suka kashe su, Allah madaukaki yace: " yanzu duk lokacin da manzo yazo maku da abunda zuciyar ku bataso sai kuyi girman kai wasu ku karyata su wasu kuma ku kashe su (87)" suratul bakara.

    Kuma kasancewar dabi'ar su ta mutane ce sun kasance suna bukatar abunda mutane ke bukata, suna ci kuma suna sha kuma suna cudanya da mutane kuma suna dariya da kuka da farin ciki da bakin ciki, Allah madaukaki yace: " kuma bamu aiki wani ba cikin manzanni gabanin ka face suna cin abunci kuma suna tafiya cikin kasuwan ni, kuma mun sanya sashin ku su zama fitina ga wasu sashi mugani koda zakuyi hakuri, ubangijin ka ya kasance me gani (20)" suratul furkan.

    A lokacin da kafiran bani isra'ila sukayi guluwwi akan anninbi Isa suka ce allah ne, sai Allah ya bayyana masu cewa mutum ne fa kuma yana bukatan dukan abunda mutane ke bukata na ci da sha sai sakamakon haka ya same shi na bukatar fitar da bahaya ko kuma bawali da majina da zufa, Allah madaukaki yace: " masihi dan Maryam ba kasance ba face manzo wanda manzanni suka gabata gabanin sa da kuma mahaifiyar sa me gaskiya sun kasance suna cin abinci ka dub aka gani yadda muka masu bayanin ayoyin mu sa'annan ka ga yadda aka kawar dasu (75)" suratul ma'ida.

Kuma suna aure domin su samu zuriya na yara da jikoki, Allah madaukaki yace: " kuma hakika mun aiki manzanni gabaninka kuma mun sanya masu mata da zuriya kuma be kasance ga wani annabi ba daya zo da wata aya face da izinin Allah kowani littafi yana da iyaka nashi (38)" suratul ra'ad.
    Suna banbanta ne da cewa da'awar su domin Allah kadai sukeyin ta baya cudanya da wani maslaha ta duniya, basu kasance ba suna neman wani lada daga wurin mutanen su ba akan haka ko kuma kudi amadadin da'awar su sun kasance ne suna neman lada da sakamako daga wurin Allah kuma sun kasance baki dayan su suna yima mutanen su magana da abunda da Allah madaukaki ya bayyana cikin fadin sa: " kace ban tambaye ku wani lada ba akan haka na nasihar da nake maku da umurni da bautan Allah, lada na yana ga Allah kuma shi me sheda ne akan komai (47)" suratu saba'i.
Idan ya kasance manzanni amincin Allah ya tabbata a garesu sun kore ma kansu kasancewar sun banbanta da mutane ko kuma cewa a hannun su amfanarwa da cutarwa take to lallai zakayi mamakin mutanen da suke bautan mutum ko gunki kamar yadda suke bautan Allah kuma suna kudurce cewa amfanarwa da cutarwa a hannun su yake alhalin sun mutu sun gaza wurin amfanar da kawunan su, Allah me girma yayi gaskiya: " dan me yasa wanda suka rika koma bayan Allah a matsayin makusanta da abun bauta basu taimake su ba ina hakika sun bace musu wannan shine karyan su da kuma abunda suka kasance suka kirkira (28)" suratul ahkaf.


Annabawa baki dayan su suna kira ne zuwa ga bautan Allah shi kadai:
kira ga tauhidi da kuma tsarkkae Allah da bauta da tsawatarwa daga shirka shi ne kiran annabawa da manzanni baki dayan su ga mutanen su, Allah madaukaki yace: " bamu aiki wani manzo ba gabanin ka face munyi masa wahayi cewa babu abun bautawa da gaskiya sai ni saboda haka ku bautamani (25)" suratul anbiya'i.
    
basu kasance suna kiran mutane zuwa ga su bauta masu ba ko kuma bautan wanin su ba sun kasance suna tsawatarwa akan haka matuka hakamar yadda Allah madaukaki ya bayyana haka cikin fadin sa cewa: " be kasane ga wani mutum ba Allah ya bashi littafi da hikima da annabta ba sa'annan yace ma mutane ku zama bayina ba koma bayan Allah sai dai ku kasance bayin Allah da abunda kuke karantawa cikin littafi da kuma abunda ake karantar daku (79) kuma be umurtan ku da ku riki mala'iku da annabawa a matsayin abun bauta shin zasu umurce ku ne da kafurce bayan kun kasance musulmai (80)" suratu al'imran.
    
Nuhu amincin Allah ya tabbata a gareshi farkon manzanni ya zauna cikin mutanen sa tsawon shekaru dubu daya babu hamsin yana kiramn su zuwa ga bautan Allah da barin abunda suke kai na shirka, Allah madaukaki yace: " hakika mun aiki Nuhu zuwa ga mutanen sa sai yace yaku mutane na ku bautawa Allah baku da wani Allah sai shi lallai ina tsoron muku azaba wani rana me girma (59)" suratul a'araf.
    
Haka shima annabi Ibrahim baban annbawa amincin Allah ya tabbata a gareshi ya nemi mutanen sa da su bautawa Allah shi kadai babu abokin tarayya, Allah madaukaki yace: " da Ibrahim a lokacin daya cema mutanen sa ku bautawa Allah kum akuji tsoran sa hakan shi yafi zama maku alheri idan da kun kasance kun sani (16) lallai abunda kuke bautamawa koma bayan Allah gumaka ne kawai wanda kuke kirkira da hannun ku, lallai abunda kuke kira koma bayan Allah baya mllaka maku arziki saboda haka ku nemi arziki agun Allah kuma ku bauta mashi da gode masa gareshi zaku koma (17)" suratul ankabut.
    
Da annabi Hudu amincin Allah ya tabbata a agreshi kiransa ya kasance ga mutanen sa akan kadaita Allah da kuma barin shirka a gareshi, Allah madaukaki yace: " mun aika zuwa ga adawa dan uwan su Hudu yace masu yaku mutane na ku bautawa Allah baku da abun bauta sai shi ku baku kasance ba sai masu kirkire kirkiren karya (50)" suratu hudu.
    
Haka annabi Salihu shima amincin Allah su tabbata agareshi kiransa ya kasance ga mutanen sa akan kadaita Allah shi kadai da kuma barin masa shirka da komai, Allah madaukaki yace: " mun aika zuwa ga samudawa dan uwansu Salihu yace masu yaku mutane na ku bautawa Allah baku da wani abun bauta bayan shi" suratu hudu ayata 61.
    
Haka shima annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gareshi bayan Allah ya tsiratar dashi da mutanen sa daga fir'auna da sarakuna sa sun nemi daya sanya masu abun bauta wanda zasu rika bautamawa sai ya bayyana masu mummunan sakamako game da aikata haka, Allah amdaukaki yace: " kuma muka ketarar da bani isra'ila rafi sai suka zo wurin wasu mutane wanda suke bautan gumaka sai sukace ya Musa muma kasanya mana abun bauta kamar yadda wannan muatnen suke da abaun bauta sai yace masu lallai ku mutane ne masu jahilci (138) wa'innan da kuke gani halakakku ne akan abunda suke kai kuma barna ne abunda suke aikatawa (139) sai yace yanzu zaku nemi abun bauta koma bayan Allah bayan ya daukaka ku akan mutane baki daya (140)" suratul a'araf.
    Haka shima annabi Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi a lokacin da aka aikeshi zuwa ga kafiran bani isra'ila domin ya kirasu zuwa ga gaskiya da kadaita Allah sai ubangijin say a tambaye sa bayan yana sane da abunda ke zuciyar sa, Allah madaukaki yace: " a lokacin da Allah yace ya Isa shin kai kace ma mutanen ka su rike ka da mahaifiyar ka a matsayin abun bauta koma bayan Allah sia yace tsarki ya tabbata a gareka baya halatta a gareni na fadi abunda bani da hakki akan sa idan ni nafada masu haka to ai kasani kasan abunda ke cikin zucya na amma bansan abunda cikin zuciyar ka ba lallai kai ne masanin gaibu (116) bance masu fa sai abunda ka umurce ni dashi cewa su bautawa Allah ubangiji na da ubangijin ku kuma na kasance me sheda akan tsawan lokacin danayi acikin su amma bayan ka kashe ni kai ne me ganin su da bibiyan su kuma ka kasance me sheda akan komai (117)" suratul ma'ida.
    
Shima annabi Muhammad amincin Allah ya tabbata a gareshi cikamakon annbawa kiran sa ya kasance akan kadaita Allah da barin duk wani abu koma bayan sa na gumaka da sassake, Allah madaukaki yace: " yaku mutane ku bautawa ubangijin ku wanda ya halicce ku da wanda suka gabace ku tabbas zaku samu tsoron Allah (21)" suratul bakara.


Shari'o'i da mazahibu na wannan zamani
Allah madukaki yayi gaskiya da yake cewa: " lallai idan kabi dayawa daga cikin mutanen duniya zasu batar dakai daga hanyar Allah ba komai suke bi ba face zato kuma ba komai suke kai ba face kaddarawa (116)" suratul an'am.
    
Bari mu dauki wasu daga cikin addini da mazhabobi a gurguje wanda suka fi yaduwa da mabiya cikin duniya domin mu gani yadda mafiya yawan su basa dacewa da hankali lafiyayye da kwakwalwa shiryayya saboda abunda ke cikin su na shirka da sanya halittu su zama abun bauta da girmama su, bazamuyi masu karya ba lallai cikin wasun su akwai kira zuwa ga dabi'u kyawawa da kuma hani ga munanan dabi'u, ko wnai makaranci zai iya gano haka karkashin baiwan da Allah yayi masa na hankali wanda yake rarrabewa tsakanin daidai da kuskure, da abunda yake na hankali da wanda bana hankali ba da wanda ya kamata da wanda be kamata ba:
•    Littafin Attaura: addinin da yahudawa sukeyi ayau sun cancanza shi da kuma bautan wanin Allah ta bangaren akida da cewa Uzaiu dan Allah ne, kuma abun bauta a wurin su yakanyi zunubi da kuma farin ciki kuma yana fadawa cikin nadama, kuma yana umurni da sata kuma mugu ne me tsananin riko, kuma shine abun bautan bani isra'ila kawai banda sauran mutane, kamar yadda suke kudurtawa cewa sune yaran Allah zababbu sauran mutane kuma basu kai su dajraja ba kuma duk wanda mahaifiyar sa ba bayahudiya bace bazai taba zama bayahude ba, suna daukan sa addini ne nasu su kadai kawai banda sauran mutane wanda hakan baya dacewa ya zama addini na duniya wanda ko wani mutane zasuyi shi, kamar yanda suke ganin cewa rayukan yahudawa wani bangare ne na Allah -Allah ya tsarkaki da daukaka daga abunda suke fadi daukaka me girma- idan mutumin da ba bayahude bay a duki bayahude to kamar ya duki buwayan abun bauta ne, addini ne wanda aka gina shi akan kiyayya da rook akan wasu mutane wanda ya hakatta cikin addinin su amfani dasu da kuma mamaye su da satan masu dukiya da masu ha'inci da karya da kuma basu bashi da riba me yawa da shedar karya akan wand aba bayahude ba saboda duk wanda ba bayahude ba a cikin akidar su kamar dabba yake, kuma hakika alkur'ani tuni ya gabatar da hujja me karfi da yake karyata wannan akida na yahudawa yadda Allah madaukaki yace: " yahudawa da kiristoci sunce mune yaran Allah da kuma masoyan sa, kace to dan me yasa yake azabtar daku da zunuban ku baku kasance ba face halittu cikin halittun sa yana gafartawa wanda yaso ya kuma azabtar da wanda yaso, mulkin sammai da kasa da abunda ke tsakanin su ga Allah suke kuma gareshi makoma take (18)" suratul ma'ida.
kuma mu sani cewa mafiya yawan yahudawan wannan zamani basu da asali zuwa ga Ibraniyyin na bani isra'ila tsofaffi wanda suka samo asali daga Ibrahim amincin Allah ya tabbata agareshi daga yaraon sa Isra'ila wanda shine Yakubu amincin Allah ya tabbata a gareshi, kasancewar sun cudanya da mutanen duniya wanda suka shiga addinin yahudanci domin mulkin mallaka na addini, amma yahudawa na asali sune wanda suke da asali daga tsatson Isra'ila (Yakubu amincin Allah ya tabbata agareshi) amma sauran yahudawan da basu ba suna daukan su a matsayin makaskantu a daraja.
•    Littafin injila (bible): wanda kiristoci suke addini dashi ayau ya bi ta matakai da yawa da cancanzawa na zamani cikin tarihi maban banta wanda yasha banban da sakon da aka saukar masu daga wurin Allah sun cancanza shi da shigar da bautan wasun Allah wanda yan siyasan su da bokaye suke da hannu dayawa cikin wannan aiki na canza shi yadda akidar su itace imani da dayan uku watan Uba da Da da Ruhi me tsarki, suna kiransa da suna abun bautan dayan uku da kuma kasancewar abun bauta dayan ukun ne kamar yadda suke fadi, kuma sun samu sabani akan sa dayawa saboda ba'a iya fahimtar sa kuma ko wace bangare a cikin su tana kafurta dayan bangaren saboda haka, kuma Allah madaukaki yayi hukunce da kafurtan su baki dayan su indai basu daina fadin abunda suke fadi ban a shirka, Allah madaukaki yace: " hakika wanda sukace Allah dayan uku ne sun kafurta, babu wani abun bauta sai Allah shi kadai kuma idan basu hanu ba daga abunda suke fadi ba to lallai azaba me radadi zata shafi wanda suka kafurta daga cikin su (73)" suratul ma'ida.

Kuma kamar yadda take shari'a wacce aka aiko Isa da ita amincin Allah ya tabbata a gareshi ga wanda ya bace cikin bani isra'ila daga bayan musuamincin Allah ya tabbata a gareshi bawai na dukkanin mutane bane kamar yadda masihi ya bayyana cikin bible na matta, lamba na (10:5,6) da fadin sa: " zuwa ga hanyar mutane kada kubi, da garurrukan samurawa kada ku shiga, kawai ku tafi da yanci zuwa ga batattu cikin bani isra'ila".
Daga cikin haka zai bayyana cewa halinta na yanzu shari'a ce ta bautan wanin Allah saboda abunda ke cikinta na shirka da Allah yadda suka sanya Isa da mahaifiyar sa suka zama abun bauta wanda suke bautamawa koma bayan Allah tare da sanin cewa Isa amincin Allah ya tabbata agareshi kiransa ya kasance akan kadaita Allah ne da barin yi masa shirka kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari akan haka da cewa: " a lokacin da Allah yace ma Isa dan Maryma kai ne kace ma mutane su rike ka da mahaifiyar ka a matsayin abun bauta koma bayan Allah, sai yace tsarki ya tabbata a gareka baya halatta a gareni na fadi abunda bani da hakki akan sa idan ni nafadi haka hakika kasani kasan abunda ke cikin raina amma ni bansan abunda ke cikin rank aba lallai kaine masanin gaibu (116) bance masu komai ba sai abunda ka umurce ni dashi cewa ko bautawa Allah ubangijina da ubangijin ku, kuma na kasance ne sheda a garesu tsawon zaman danayi acikin su, amma a lokacin da ka kashe ni kai ne me ganin su kuma kai me sheda ne akan komai (117)" suratul ma'ida.

Kuma hakika kiristoci sun dauko dayawa daga cikin manyan addinai da akidoji na wanda suka gabace su, sai suka tasirantu da addinai na kariya wanda ya kasance a kasar farisa gabanin haihuwar annabi Isa da karni shida wacce ta kunshi kissa iri daya da kissar raba fikira da jin ubanjiki, haka kuma sun dauko cewa alla dayan uku ne daga addinin hindu yadda abun bauta a wurin su guda uku ne masu suna " fashanu" watan me kiyayewa da " sifa" watan me halakarwa da kuma " burahma" watan me samarwa, kamar yadda suka dauko akidar rataya domin kankare zunubi, da tsantseni da sufanci da kuma tsarkaka daga kudi domin shiga cikin mulkin sammai, kamar yadda wasu akidu da tunani na buzanci wanda ya gaaci kiristan ci da karni biyar ya dawo cikin ta, yadda ilimin kwatanta addinai ya nuna Kaman ceceniya me girma tsakanin mutumin buzanci da mutumin almasihi amincin Allah tabbata a gareshi sannan kuma kasancewar yanayi na haihuwar masihi da rayuwan sa da kuma yanayin da buzanci yabi yana cikin abunda yake tabbatar da wannan tasirin na kiristanci dashi cikin dayawa na akidun su, kamar yadda ya cudanya da addinin babalawa na da can kasancewar hukuncin " ba'al" allan rana yayi kama da hukuncin masihi amincin Allah ya tabbata agareshi, daga haka canzawan injila da kuma shigan abunda baya cikin san a akidun bautan wanin Allah yana daga cikin abunda yasa ya rasa yanayin san a asali wanda isa amincin Allah ya tabbata a gareshi yazo dashi daga wurin ubangijin talikai.

•    Addinin hindu: an gama hadata ne cikin matakai me tsayi na lokaci yadda ba'a san wanda ya kirkiro ta ba kuma ba'asan manyan mawallafanta ba wanda suka rubutata an hadata ne daga falsafar hindanci da kuma attaura (addinin yahudanci) da injila (addinin kirstanci) wanda aka cancanza su, ta kunshi akidu na bautan wanin Allah wanda hankali baya dauka kuma yafi karfin hankalin mutum na bautan bishiyoyi da duwatsu da birrai da kuma girmama shanu wanda yake matukan jin dadi a wurin sun a darajar da yake dashi me girma yadda suna ginata ne tanada butun butumi dayawa a wuraren bauta da kuma gidaje da wuraren taruwa da murna na jama'a baki daya kuma tanada hakkoki wanda irin wanda mutum yake neman samun sa dayawaa cikin su yadda take da yanci na yawo kuma baya halatta a yanka ta ko kuma cutar da ita da ko wani cutarwa idan kuma ta mutu sai a birneta da filawa na addini, addinin hindu bayan kari zuwa ga bautan wasu ababe wanda ba Allah sunada darajoji na mutane cikin al'umma wanda suka rabata zuwa daraja wanda wasu zasu rika yima wasu bauta wanda hakan yake cin karo da hakkokin dan adam da kuma asali na adalci a tsakanin al'umma, cikin abunda yake nuna cewa lallai fa tayi nisa matuka daga zama wahayi ce ta Allah.
 
•     Addinin buzanci: falsafa ce wanda aka kirkiro wacce take kama da addini wanda ake dauka a matsayin tsari na dabi'u da mazahaba na hankali wanda aka ginata akan maganganu na falsafa, da kuma karantarwa wanda bana wahayi ba kawai ra'ayoyi ne da aikdu cikin wasu addinai, ta kuma bayyana ne a kasar indiya bayan addinin hindu cikin karni na biyar gabanin haihuwan annabi Isa. Bayan mutuwar wanda ya kirkire ta me suna Sadahartaa Jutama wanda ya canza daga addinin buzanci shekara 480-560 na karni gabanin haihuwan annabi Isa. Ta canza zuwa ga akida batacciya wacce ta kunshi bautan wanin Allah, yadda suke kudurcewa cewa Buza shine Allah, kuma shine me tsarkake mutane wanda yake daukan dukkanin zunuban su, daga cikin abunda yake nuni akan kasancewar ta addini ce ta bautan wanin Allah fadin su cewa: a lokacin da Buza ya shiga cikin tsari nasu sai gumaka suka masa bauta, saboda haka ne buzawa suke salla ga buza yadda yasu sawwara masa gumaka suka sanya su cikin wuraren bautan su da wuraren su na game gari suna masu dukurcewa cewa zai shigar dasu aljanna.
Cikin wasu kantarwan buzanci akwai dabi'u masu kyau kamar kiran su da sukeyi na son juna da yafiya da mu'amalantar mutane da abubuwa masu kyau da kumayin sadaka ga talakawa, kuma sunada ruhbananci da kuma nisantar wakoki da caca da daurama kai abunda bazata iya ba da tsoro da tsawatarwa daga mata da dukiya da kuma kwadaitarwa game da aure da kuma fatali da dukkanin abunda ya sabawa dabi'a mutum wanda aka halicce sa akai na son dukkanin abunda ya dace su karanta, kuma suna dauka cewa littattafan su sunada matsayi kuma magana ne wanda ya jingunu zuwa ga buza ko kuma labari ne game da ayyukan sa wanda wasu daga cikin mabiyan sa suka suruta.
    
kenan zai bayyana mana cewa ita akida ce ta shirka wanda bana ubangiji bane magana ce akan falsafa da kuma ra'ayoyi na wanda ya kirkireta da kuma mabiyan su wanda suka zo a bayansa wanda suke kira nanata su tsawon zamani har yazu zuwa abunda suke ciki a yanzu.

•    Sekanci (gamayyan addinu): bawai addni bace ko kuma mazahabanci a'a ana daukan ta ne a matsayin tafiya na gyaran addini wanda suka tasirantu da musulunci kuma sunyi kokari wurin hadawa tsakanin akidu da addinai wanda suka yadu da kuma hada kansu su zama akida guda daya, yadda wasu mutanen addini suka kirkirota daga cikin hindu wanda suka bayyana a karshen karni na goma sha biyar cikin farkon karni na goma sha shida bayan haihuwar isa suna masu kira zuwa ga saban addini wanda ya hada tsakanin musulunci da hindu karkashin tuka me suna " ba hindu bane kuma ba musulunci bane". Sai dai basu samu nasara ba akan haka yadda jahilcin su da musulunci da kuma akidar su da ilimin su ya kaisu zuwa ga bata daga hanyar ta daidai da ace sun san musulunci da suncan cewa lallai addini fa baya kasancewa sai idan wahayi ne daga Allah babu halin yin kokarin mutum a cikin sa kokarin sun a hada addinai kuma da mazahaboi mabanbanta domin kusanci a tsakanin su da fitar da akida daya wanda kowa zai taru akai, sa'annan suka wayi gari bayan haka makami a hannun turawa suna amfani dasu wurin ayyuka wanda yake kira zuwa ga fitowar su daga hindu, mulkin mallakan turawa ya kasance yanada tasiri babba wurin taimakawa wannan tafiya tasu da kuma samun nasarar su yadda wannan kira na wayi gari cikin turawa yanada wasu siffofi wanda yake banbance shi dayawa daga sauran mutane cikin jihohi wanda suke kai yawan kasha ashirin 20% na rundunonin hindu na garin burtaniya.

Daga wannan zai bayyana cewa wannan tafiya wanda suka nufi gyara da ita sai dai basu samu nasara ba yadda ta samu mataimaka da rayata gabanin fara mulkin mallaka cikin kasashe da kuma amfani dashi na samun bayi da kuma rusa musulunci na kwarai kasancewar gaskiya fa bazata taba haduwa ba da karya kuma kadaita Allah bazai taba haduwa ba da shirka.

•    Addinin musulunci: shine karshen shari'a na sama wanda aka saukar kuma manzon ta shine cikamakon annabawa da manzanni babu wani manzo a bayan sa ko kuma wani annabi a bayan sa, kuma addinin sa shine karshen addinai babu wani addini ko kuma shari'a a bayan sa har zuwa tashin alkiyama yadda aka cike addini dashi kuma ni'imomi ya cika dashi, yazo ne domin tace dabi'u ya kuma samu daukaka cikin zutaka, Allah madaukaki yace: " ayau ne na cika maku addinin ku da kuma ni'imata a gareku kuma na yardan maku da musulunci ya zama addini agareku" suratul ma'ida.

Shine addini wanda Allah ya yardan ma mutum dashi, Allah baya amsan wani bauta da aka masa inba dashi ba kuma a lahira ma bazai amsa ba sais hi kadai, shine kira zuwa ga kadaita Allah da kuma barin shirka da Allah, Allah madaukaki yace: " lallai yadda abun yake shine duk wanda yayi shirka da Allah to lallai Allah ya haramta masa aljanna kuma makoman sa wuta kuma azzalumai basu da wani mataimaki (72)" suratul ma'ida.
•    Musulunci kira ne ga halaye kyawawa da ayyuka masu falala, Allah madaukaki yace: " kace masu lallai ubangija ya haramta alfasha abunda yake bayyane a cikin sa ko kuma na boye da sabo da dagawa akan gaskiya ko kuma ba'a kan gaskiya ba da kuma shirka da Allah cikin abunda be saukar da hujja ba akai da kuma fadin abunda baku sani ba game da Allah (33)" suratul a'araf.
•    Musulunci kira ne zuwa ga aikata alheri da kyautatawa mutane, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani kuyi ruku'I da sujjada kuma ku bautawa ubangijin ku da kuma aikata alheri tabbas zaku rabauta (77)" suratul hajji.
•    Musulunci kira ne zuwa ga barin munanan halaye da ayyaka kaskantattu, allah madaukaki yace: " ku bar sabo na bayyane dana boye, lallai wanda suke aikata zunubi za'a saka masu da abunda suke aikatawa (120)”. Suratul an'am
•    Musulunci addini ne ga mutane baki daya, Allah madaukaki yace: " kace ya ku mutane lallai ni manzon Allah ne zuwa gareku baki wanda yake da mulkin sammai da kasa babu abun bautawa da gaskiya sai shi yana rayawa da kashewa, kuyi imani da Allah da manzon sa wanda be iya rubutu ba ko karatu ga duk wanda yayi imani da Allah da kalmomin sa kuma ku bishi tabbas zaku shiryu (158)" suratul a'araf.
•    Musulunci rahama ce ga mutane dashi ne mutane ke fita daga cikin duhu zuwa haske kuma dashi ne suke tsira daga azaba da wutan jahim, Allah madaukaki yace: " kuma bamu aikeka ba face rahama ga talikai baki daki (107)" suratul anbiya'i.
•    Musulunci addini ne na yanci me tsari, Allah madaukaki yace: " ka fadi gaskiya daga ubangijinka duk wanda yaso yayi imani wanda kuma yaso ya kafurce, lallai mun tanaji wuta ga azzalumai wanda zata shanye gabban su kuma idan sun nemi agaji na ruwa za'a kawo masu wani irin ruwa na dalama wanda yake kwashe fatan fuska, tir da wannan abun sha kuma wurin zama ya munana (29)" suratul kahafi.

Musulunci addini ne na aiki da inganta aiki, manzaon Allah s.a.w yace: " lallai Allah madaukaki yanson idan mutum zayyi aiki ya inganta aikin sa" (baihaki ne ya rawaito shi cikin babin rabin Imani, da Abu Ya'ala cikin musnadin sa, kuma Albani ya ingantashi cikin littafin sahihul jami'u: 1880, da kuma alsahihah: 1113).

Musulunci addini ne na ilimi, manzon Allah s.a.w yace: " neman ilimi wajibi ne akan ko wani mutum musulmi" (ibn majjah ne ya rawaito shi) 224, da kuma (Abu Ya'ala) 2903, kuma albani ya inganta shi cikin sahihul jami'u: 3913, da sahihul targib da tarhib: 72.
•    Musulunci addini ne na tsarki da tsabta, Allah madaukaki yace: " yaku yayan adam ku riki kawarku a lokacin ko wani masallaci da salla kuma kuci kusha kada kuyi almubazaranci lallai Allah bayason masu yin almubazaranci (31)" suratul a'araf.
•    Musulunci addini ne na jinkai da tausayi, manzon Allah s.a.w yace: " masu jin kai Allah yana jin kan su, kuji kan mutanen cikin kasa sai wanda yake sama yaji kanku" (tirmizi ne ya rawaito shi) 1924, da (abu dawud) 4941, da (ahmad) 6494),, kuma albani ya ingantashi cikin sahihul jami'u: 3522, da alsahihah: 925.
•    Musulunci addini ne na adalci a tsakanin mutane baki dayan su, Allah madaukaki yace: " lallai Allah yana umurtan ku dayin adalci da kyautatawa da bayar da sadaka ga yan uwa makusanta kuma yana hani game da aikata alfasha da mummunan aiki da dagawa da haka yake yana maku wa'azi ko zaku yi tunani (90)" suratun nahali.
•    Musulunci addini ne na sauki da rangwame, Allah madaukaki yace: " Allah yanason sauki a gareku kuma bayason tsananta maku" suratul bakara.
•    Musulunci addini ne na kare rai da kuma rashin jefata zuwa ga halaka, Allah madaukaki yace: " kada ku kashe kawunan ku lallai Allah ya kasan me rahama ne a gareku (29)" suratun nisa'i.
•    Musulunci addini ne na kiyaye jiki zahirin sa da tsabta da kuma tsarki, Allah madaukaki yace: " lallai Allah yanason masu yawan tuba da masu tsarki (222)" suratul bakara.
•    Musulunci addini ne na kare jikin na badinin sa wajen cikin sa ta hanyar hana barna cikin abinci da abunsha da kuma hana wuce iyakan da zai cucar dashi, Allah madaukaki yace: " kuci kusha amma kada kuyi almubazaranci, lallai Allah bayason masu yin almubazaranci (31)" suratul a'araf.
•    Musulunci addini ne na kiyaye wurin zama da yanayi, Allah madaukaki yace: " kuma kada kuyi barna a cikin kasa bayan gyaruwanta kuma bauta masa kuna masu tsoro da kwadayi, lallai rahamar ubangijin ka tana kusa ga masu kyautatawa (56)" suratul a'araf.
•    Musulunci addini ne na tausayin dabbobi da kuma kiyaye su, manzon Allah s.a.w yana cewa: " a lokacin da wani mutum tsananin kishi ya dame shi sai ya shiga cikin wata rijiya yasha ruwa acikinta, sa'annan ya fito sai ga wani kare yana kuka yanacin kasa saboda tsananin kishin ruwa sai yace: Allah sarki irin kishin daya kamani shine ya kama wannan Karen, sai ya cire takalmin sa rike shi da bakin say a shiga rijiya ya diboma wannan kare ruwa ya bashi yasha! Sai Allah ya gode masa, ya kuma gafarta masa sai sukace" ya manzon Allah yanzu muna da lada acikin dabbobin mu? Sai yace: " cikin ko wani hanta me rai kunada lada acikinta" buhari da muslim ne suka rawaito shi.
•    Musulunci addinin adalci ne da kyautatawa: Allah madaukaki yace: " lallai Allah yana umurtan ku dayin adalci da kyautatawa da bayar da sadaka ga yan uwa makusanta kuma yana hani game da aikata alfasha da mummunan aiki da dagawa da haka yake yana maku wa'azi ko zaku yi tunani (90)" suratun nahali.
•    Muslunci addini ne na daidaito tsakanin mutane baki daya. Manzon Allah s.a.w yace: " yaku mutane lallai ubangijin ku daya, kuma babanku dadaya ne, babu falala ga balarabe akan wanda ba balarabe ba, kuma babu falala ga wand aba balarabe ba akan balarabe, ko kuma baki akan fari, ko fari akan baki sai da tsoron Allah" (ahmad ne ya rawaito shi) 23536, da (aldyalisi) 4749, duba cikin alsahiha: 2700, da sahihul targib da tarhib: 2963.

Amma yanayin mutum a duniya Allah yakan banbanta su cikin arziki da kayan rayuwa yasanya wasu masu kudi wasu kuma talakawa, kamar yadda Allah madaukaki ya fadi cewa: " Allah shine wanda ya daukaka wasu akan wasu a cikin ku cikin arziki, wanda aka daukaka da arziki kada ya mayar ya zaki dukiyar sa ga bawan sa su zama daya cikin mulkin wannan dukiya, shin da ni'imar Allah suke jayayya (71)" suratun nahli.
Ya kuma sanya marasa lafiya a cikin su da masu lafiya da dogo da gajere…zuwa dai karshe, Allah madaukaki yace: " mune muke raba masu abubuwan rayuwan su a tsakanin su kuma mun daukaka wasu akan wasu cikin daraja domin wasu su rika yima wasu aiki suna biyan su, kuma rahamar ubangijin ka tafi alheri daga abunda suke Tarawa (32)" suratul zukhruf.

Ya kuma sanya wasu daga cikin su basa haihuwa wasu kuma suna haihuwa ya kuma raba masu jinsin raya maza da mata a tsakanin su ko kuma wani a hada mashi mazan da matan duka Allah yana halittan abunda yaso kuma yana aikata abunda yaso domin wata hikima wanda babu wanda yasanta sai Allah, Allah madaukaki yace: " mulkin sammai da kasa duk na Allah ne yana halittan abunda yaso yana ba wanda yara mata kuma yana ba wanda yaso yara maza (49) ko kuma ya hada mashi maza da mata kuma ya sanya wanda yaso ya zama baya haihuwa lallai shi masani ne kuma me iko (50)" suratul shura.

Kuma musani cewa dukkanin mazahabobi da addinai na daban sabanin muslunci wanda shine kiran cikamakon Annabawa Muhammad s.a.w tana aiki ne kai tsaye ko kuma ta bayan fage wurin mallakewa mara iyaka wanda musulunce ingantacce ke kallaon haka a matsayin hatsari ga duniya na yin hukunci akan amfani da mutum da laheran wannan duniya wurin gamawa da ra'ayin mutane, kamar yadda take aiki tukuru na samar da mazahabobi da kungiyoyi sababbi biyayya da biyan kudin haraji da kuma janyewa daga dayawa cikin asaloli wanda mutum me yanci da wayewa kuma dan birni bazai yarda da hakan ba, dukkanin wannan abunda takeyi tanayi ne domin tsoron kada mutane su hadu karkashin addinin gaskiya wanda da bayyanan sa ne gaskiya yake bayyana kuma yake gamawa da barna kuma mumini ya kwato daukakan sa akan wanda suka kasakantar dashi kuma suka kwace masa alheran san a kasar sa kuma suka karkatar dashi daga bautan ubangijin mutane zuwa bautan mutane.

Komawa zuwa ga asali:
Har yanzu dai dama tanan ga dukkanin mu na komawa zuwa ga asalin addinin mu wanda Allah madaukaki ya yardan mana da bauta masa dashi wanda shine musulunci kuma wannan damar idan ta kasance yalwatacciya yanzu zata iya kasancewa bata a wani lokaci na daban kuma idan harkoki yanzu suna a shirye zasu iya kasancewa akasin haka nan gaba koda kuwa ianson hakan, kkamar yadda Allah madaukaki ya bada labari akan haka da cewa: " kuma babu tuba ga wanda suke aikata laifi har sai mutuwa ya zoma dayan sa sa'annan yace ni na tuba yanzu ko kuma wanda suke mutuwa suna kafirai, wa'innan mun tanadar masu da azaba me radadi (18)" suratul nisa’i
Kuma kamar yadda Allah madaukaki ya bayyana haka cikin halin kafiri a lokacin mutuwar sa lokacin da yake jin mutuwa kuma yaga hakika wanka ya bayyana a gabansa zai san gaskiyan manzanni da kuma karyan abunda yake kai na addini kuma zayyi nadama akan sakacin da yayi a lokacin da nadama bazatayi amfani ba a wannan yanayi za'a rufe ma mutum kofar tuba a gaban sa da kuma kuma dawowa kuma hasara zai yawaita yana fatan dawowa ga rayuwa domin yayi imani da abunda ya kafurce masa sai dai kash hakan zayyiwu ba, Allah madaukaki yace: " har sai mutuwa ta zoma dayan su sai yace ya ubangijina ka mayar dani (99) domin na aikata ayyuka na kwarai a cikin duniya, sai dai ina hakan bazayyiwu ba kawai kalmace wanda ya fada kuma a bayan sa akwai rayuwan barzahu har zuwa ranan da za'ayi tashin alkiyama (100)" suratul muminun.
Alkur'ani me girma ya hakaito labarin fir'auna wanda yayi dagawa da barna yace nine ubangijin ku mafi girma cewa alokacin da yaga hakika yaganta da idonsa sai yayi imani sai dai imanin sa a lokacin be amfanar dashi ba sai Allah ya nitsar dashi da rundunar sa, Allah madaukaki yace: " sai muka ketarar da bani isra'ila rafi sai fir'auna da rundunar sa suka biyu so domin dagawa da kiyayya har lokacin da doriyan ruwa ta hadiye shi sai yace nayi imani cewa babu abun bautawa da gaskiya sai wanda bani isra'ila sukayi imani dashi kadai kuma nima ina cikin musulmai (90) a yanzu ne zakayi imani bayan ka kasance cikin masu barna (91) a yau ne zamu tsiratar da gangan jikin ka domin kazama aya ga mutane wanda suke bayan ka kuma dayawa daga cikin mutane suna gafala daga ayoyin mu (92)" suratu Yunus.
Al'amarin me girma ne da kuma hatsari idan akayi tunani, al'amarin murna da tsira na har Abadan wanda babu wani wahala a bayanta cikin aljanna wacce fadin ta kamar sama da kasa ko kuma wahala na har Abadan wanda babu murna da tsira a bayanta cikin wutan jahannama tir da wannan makoma: " sunada gado cikin wutan jahannama wanda samansa wutane wanda take lullube su, da Kaman haka ne muke sakanya wa azzalumai (41)" suratul a'araf.
Lallai fa wanda ya halicce ka yana farin ciki da tuban ka da kuma komawan ka gareshi, menene yafi wannan girma na cewa mahalicci yanason mu da alheri kamar yadda manzon Allah s.a.w ya bada labari cikin fadin sa: " lallai Allah yafi murna akan tuban bawan sa a lokacin daya ke tuba sama da dayan ku wanda ya kasance akan dabbar sa cikin tsakiyan sahara sai wannan dabbar nasa ta bace masa kuma kayan abincin sa da ruwansa duk yna kanta ya cire rai da rayuwa sai yaje karkashin wata bishiya ya kwanta- ya cire da ganin wannan dabba tashi- yana cikin wannan hali sai kawai yaga wannan dabbar tashi a gaban shi sai ya rike linzamin ta yace saboda tsananin farin ciki ya Allah kaine bawana nine ubangijin ka- watan yayi kuskure saboda tsananin farin ciki-" sahihu muslim.

Me yafi irin wannan girman rahama ta mahalicci wanda yake son ya rahamshe mu kuma yana son farin cikin mu kamar yadda manzon Allah Muhammad s.a.w ya bada labari akan haka da cewa: " lallai Allah yana da rahama dari ya saukar da guda daya daga cikinta a tsakanin mutane da aljanu da dabbobi da kwari, da itace suke tausayin juna, kuma da itace suke jin kan juna, kuma da itace miyagun dabbobi suke tausayin yaran su, sauran tasa'in din da tara na rahamar zai ji kan bayanin sa dashi ne ranan alkiyama" sahihu muslim.
Karanta wannan ayoyi na alkur'ani domin sanin lada me girma wanda zaka samu idan ka dawo zuwa ga mahaliccin ka zuwa ga addinin ka na asali wanda shine musulunci da kuma imani da shari'ar sa wacce take ta karshe wurin sauka da kuma ladan da zaka samu na dawowar ka zuwa gareshi za'a gafarta maka zunuban ka baki dayan su kuma za'a canza maka zunuban ka su koma lada, shin ka tabajin irin wannan karamcin? Wanda ya gaza samun wannan falalar me girma shine kadai wanda yayi sakaci:
•    Allah madaukaki yana cewa: " wanda basa kiran Allah tare da wani abun bauta na daban kuma baza kashe rayukan da Allah ya haramta sai da gaskiya kuma basayin zina, duk wanda ya aikata hakan zai tarar da zunubin sa daya aikata (68) za'a nunka masa azaba ranar alkiyama kuma zai dawwama cikinta wulakantaccce (69) sai wanda ya tuba ya kuma yi imani ya aikata ayyuka na kwarai to wannan za'a canza masu zunubansu su koma lada, kuma Allah ya kasance me gafara da rahama (70) duk wanda ya tuba ya kuma aikata ayyuka na kwarai zai samu tuba zuwa ga Allah da tuban sa (71)" suratul furkan.
•    Allah madaukaki yanacewa: " kace ma wanda suka kafurta idan suka hanu za'a gafarta masu abunda suka aikata a baya idan kuma sun dawo sunci gaba to hakika sunnar mutanen farko ta gabata (38)" suratul anfal.
•    Allah madaukaki yana cewa: " su ne wanda idan sun aikata alfasha sais u tuna Allah sais u nemi gafarar zunuban su wanene yake gafarta zunubi inba Allah ba kuma bazasu sake komawa ba zuwa ga abunda suka aikata suna sane (135)" suratu al'imran.
•    Allah madaukaki yana cewa: " lallai tuba a wurin Allah yana yi ne ga mutanen da suke aikata laifi cikin rashin sani sa'annan su tuba bada dadewa ba to wannan sune Allah zai amshi tuban su, kuma Allah ya kasance masani me hikima (17)" suratun nisa'i.
•    Allah madaukaki yana cewa: " Allah yana son ya amshi tuban ku ya yafe maku kuma wanda suke bin son zuciyarsu suna ku bace daga gaskiya bata me girma (27)" suratun nisa'i.
•    Allah madaukaki yana cewa: " kuma lallai ubangijinka ma'abocin gafara ne ga mutane akan zalumcin su, kuma lallai ubangijin ka me tsananin ukuba ne (6)" suratul ra'ad.
•    Allah madaukaki yana cewa: " kuma lallai ni me yawan garafa ne ga wanda ya tuba ya kuma yi imani da aikata aikin kwarai sa'annan kuma ya shiryu (82)" suratu daha.
•    Allah madaukaki yana cewa: " kuma babu komai akanku cikin abunda kukayi kuskure sai dai akan abunda kuka aikata da gangan, kuma Allah ya kasance me gafara kuma me jin kai (5)" suratul ahazab.
•    Allah madaukak yana cewa: " idan kuka bayyana alheri ko kuma kuka boye shi ko kuma kukayi lafiya akan laifi to lallai Allah ya kasance me yawan yafiya kuma me iko (149)" sjuratun nisa'i.
•    Allah madaukaki yana cewa cikin hadisin kudusi: " ya kai dan Adam lallai kai baka kira nib a kuma ka nemi gafara ta hakanan na yafe maka abunda ka aikata kuma ban damu ba, ya kai dan adam da ace zunuban ka zasu cika fadin sama sa'annan ka roke ni gafara zan gafarta maka kuma bazan damuwa, ya kai dan adam da ace zaka zo mun da kwatan kwacin fadin duniyacike da laifi sa'annan ta riske nib aka mun shirka da wani abu dana zo maka da kwatankwacin san a gafara " Ahmad ne ya rawaito shi, da tirmizi kuma albani ya ingantashi cikin alsahihah 127.
•    Manzon Allah s.a.w yana cewa: " lallai nasan mutum karshe wanda zai shiga aljanna, da kuma dan wuta na karshe wanda zai fito daga cikinta: za'azo da mutum ranan alkiyama sai ace masa: ya bijo masa da kananan zunuban sa, kuma ka dauke masa manayan akan sa, sai abijiro masa da kananan sai ace masa: ka aikata kaza a rana ta kasa da kaza, kuma ka aikata kaza arana ta ta kaza da kaza? Sai yace: eh na aikata, bazai iya inkari ba, yana tsoron a bijiro masa da manyan zunuban sa, sai ace masa: kana da lada a wurin ko wani zunubi, sai yace ya ubangiji na: hakika ya akata ayyuka dayawa wanda bangan sub a anan", hakika naga manzon Allah s.a.w yana dariya har hakorin sa na gaba ya bayyana. Muslim ne ya rawaito shi.


Tsayuwa domin nazari:
Dukkanin addinan da suke doron kasa addinai nae batattu a mahangan muslunci saboda kasancewar shirka ta shige su da kuma bautan wanin Allah tare dashi ku kuma cewa addinai ne wand aba daga sama aka saukar dasu ba mutane ne kawai suka kirkire su saboda bukatar sun a fidira na kasancewar wani addini wanda zasu rika bi sai dai basu dace ba da gaskiya da hanyar daidai babu wani addini bayan musulunci, kuma mu sani cewa shari'un da suka zo daga sama guda uku ne attaura da injila(bible) da kuma alkur'ani shari'ar annabi Muhammad s.a.w, amma abun takaici shine attaura da injila(bible) duk an canza su wannan dinnan da suke yawo a hannun mutane basu bane na asali, sannan kuma yana nuni ga cinkaro a fili da shirkoki da toye matsayin ubangiji madaukaki a cikin sa dukkanin haka sunanan dayawa cikin littattafan da suke magana akan haka domin bayani hakan dalla dalla ga wanda yake son neman Karin bayani sai ya nemo su ya karanta, abunda akeso ga duk wanda ya karanta wannan littafi shine ya bijiro da addinin sag a hankali shin ya kamata ace a hankalce mun bautamawa abunda bazai iya amfanar damu ba ko kuma cutar damu ba da komai? Shin ya kamata ace a hankalce mun girmama halitta irin mu wanda basu mallaki mutuwa ba ko kuma rayuwa ko tayar da mutane bayan mutuwa? Shin ya kamata ace a hankalce mun wadatu daga mahalicci mu koma ga wani halitta wanda bazai iya yaye mana komai ban a damuwa ko kuma canza mana damuwar mu? Yanzu shin ya kamata ace a hankalce zamu bautamawa mutum irin mu wanda basu halicci komai bas u din ne aka halitta ma?
•    Bauta a musulunci hakki ne na mahalicci shi kadai babu wani me rabo a cikinta cikin halittu, Allah madaukaki yace: " kuma ubangijin ku yace ku roqe ni zan amsa maku lallai masu girman kai game da bautana da sannu zasu shiga jahannama suna kaskantattu (60)" suratu gafir.
•    Bauta a musulunci kai tsaye ne tsakanin Allah da bawan sa babu wani tsaka tsaki ko kuma me ceto, Allah madaukaki yace: " ku saurara kuji ga Allah kadai addini ya tsarkakke, wanda suke rikan waliyyai koma bayan Allah suna cewa ba komai yasa muke bauta masu ba face su kusantar damu kusa ga Allah, lallai Allah zai masu hukunci a tsakanin su cikin abunda suke sabani acikin sa, lallai Allah baya shiryar da wanda ya kasance makaryaci me yawan kafurci (3)" suratul zumar.

Ayoyi na nazari ga wanda yayi shirka ga Allah:

•    fadin Allah madaukaki cikin bayanin nakasun dukkanin abunda ake bauta mawa koma bayan Allah ta dukkanin bangarori: " kuma sun riki abubuwan bauta koma bayan Allah wanda basa halittan komai sai dai sune akama halitta kuma basa mallakama kansu amfani ko kuma cutarwa kuma basa mallakan mutuwa ko rayuwa ko kuma tayar da mutane bayan mutuwa (3)" suratul furkan.

•    fadin Allah madaukaki cikin gazawan dukkanin abunda ake bauta mawa koma bayan Allah: " kace yanzu shin kuna ganin abunda kuke kira koma bayan Allah idan Allah ya nufe ni da wata cuta shin zasu iya yayemun ita ko kuma idan ya nufe ni da wata rahamar sa shin zasu iya rike wannan rahamar tashi, kace Allah ya isar mani kuma gareshi ne masu dogaro suke dogaro (38)" suratul zumar.

•    Fadin Allah madaukaki cikin adawar da dukkanin wanda ake bauta mawa koma bayan Allah zasuyi da masu bauta masu ranan alkiyama: " kuma wanene yafi bata sama da mutumin da yake kiran wani abu koma bayan Allah wanda bazai taba amsa mashi ba har zuwa ranan alkiyama kuma gafalallu ne game da kiran da suke masa (5) kuma idan aka tayar da mutane zasu kasance makiya a garesu kuma zasu kafurce game da bautan da suka masu (6)" suratul ahkaf.

Ya kai wanda ya bautawa wuta ko bishiya ko shanuwa ko dutse… da sauran sucikin abubuwan da ake bauta mawa, kayi nazarin fadin Allah madaukaki: " lallai abunda kuke kira koma bayan Allah bayi ne kamar ku to ku kira su mugani sais u amsa maku idan kun kasance masu gaskiya (194) shin suna da kafafuwa ne wanda suke tafiya da ita ko kuma sunada hannu ne wanda suka taba abu dashi ko suna da idanu ne wanda suke kallo dashi ko suna da kunnuwa ne wanda suke jin magana dashi, kace masu ku kira abokan tarayyan ku sa'annan kuyimun makirci mugani kada ku saurara mun ko kadan (195) lallai majibincin al'amura na shine Allah wanda ya saukar da littafi kuma shine yake jibintan al'amuran salihai (196)" suratul a'araf.

Yakai wanda yayi dawafi ya kuma yi roko da bautan ma'abota kabari da wuraren bauta kayi nazarin fadin Allah madaukaki: " kada ka kira wani abu koma bayan Allah wanda bazai amfanar dakai komai ba kuma bazai cutar dakai ba da komai, idan kuma ka aikata hakan to lallai kana cikin azzalumai (106)" suratu Yunus.

Yakai wanda yabi son zuciyar sa da sha'awar ran sa, ya mara da halal shine duk abunda yayi sha'awa haramun kuma shine duk abun daya kikayi nazarin fadin Allah madaukaki: “in har basu amsa maka ba to ka sani cewa babu abin da suke bi face san ransu, kuma babu wanda fafi bacewa irin wanda ke bin san ran sa ba tare da wata shiriya ba daga Allah lallai Allah bay a shiryadda mutane azzalumai (50)” suratul kasas.
Ka sani lallai dukkan wanda aka bautama zai barranta daga wadan da suka bauta masa kuma suka rike shi masoyi koma bayan Allah, Allah madaukaki yace:" daga cikin mutane akwai wanda suke rikan wani abu koma bayan Allah a matsayin kishiyoyi suna son su kamar son da sukeyi ma Allah, wanda sukayi imani sunfi tsananin so ga Allah da ace zagani lokacin da azzalumai zasu ga azaba lallai farki ga Allah yake baki dayan sa kuma lallai Allah me tsananin azaba ne (165) a lokacin da wanda aka bauata masu zasu barranta daga wanda suka bauta masu kuma zasuga azaba kuma anyake masu dukkanin wani hanya (166)" suratul bakara.
Kuma hakika ubangijin mu ya labarta mana cikin alkur'ani labarin annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da sarki namarudu dagutu wand ayayi ikirarin wasu siffofi na allantaka yayi ikirarin cewa yana da ikon tayar da mamata, annabin Allah be kyaleshu ba har saida yayi mujadala dashi da muhawara na hankali domin ya bayyana karyan sa da karyan abunda yake ikirari; sai ya nemi ya aikata wani aiki na daban wanda aiki ne na ubangiji wanda ba raya mamata ba na jujjaya wasu daga cikin halittun wanan duniya na cewa ya sanya rana tafito daga yamma maimakon daga gabas, Allah madaukaki yace: " shin bakagani ba zuwa ga wanda yayi jayayya da Ibrahim cikin sha'anin ubangijin sa dan ganin cewa Allah ya bashi mulki a lokacin da Ibrahim yace ubangijina shine wanda yake rayawa kuma uya kashe sai shima yace nima ina ranawa kuma ina kashewa sai Ibrahim yace masa lallai Allah zai fito da rana daga gabas kai kuma ka fito da ita daga yamma mugani sai wanda ya kafurta ya dimauce, Allah kuma baya shiryar da mutane azzalumai (258)" suratul bakara.

Da annabi Musa amincin Allah ya tabbata agareshi shi da fir'auna shima alokacin da yayi ikirarin allantaka sai musu yayi muhawara dashi na hankali domin ya bayyanakaryan sa da kuma gazawan sa agaban wanda ya yaudare su yadda Musu ya nema daga gareshi daya fito da taurarin da suke fitowa a gabas ya fito dasu a yamma, Allah madaukaki yace: " fir'auna yace wanene kuma ubangijin talikai (23) sai yace ubangijin sammai da kasa da abunda ke tsakanin sui dan kun kasance masu sakankancewa (24) sai yace ma na gefen sa kunajin kuwa abunda yake fadi (25) sai yace ubangijin ku kuma ubangijin iyayen kun a farko (26) sai yace lalai wannan manzon naku da aka aiko maku mahaukaci ne (27) sai yace ubangijin gabas da yamma da abunda ke tsakanin sui dan kun kasance masu hankalta (28)" sutratul shu'ara'i.

Wannan domin kasan cewa fa lallai wanda ya cancanci bauta da kuma a tsarkake shi daga shirka shine Allah shi kadai ka harraka fidirar ka kuma ka ta tattauna da hankalin ka wanda aka halicce ta akan yantuwa daga kaskantar dakai ga halittu babu shakka cewa zai kai ga zuwa ga lallacewar bautan wanin Allah da kuma rikan waliyya koma bayan Allah.


Kafin kurewar lokaci:
Muyi nazari da hankulan mu masu lafiya da fidiyar mu me ingancicikin abunda muke akan sa, domin lallai rayuwa bata da tsayin da mutum zai batata ga abunda ba zai amfanar dashi ba, Allah madaukaki yace: " ku sani cewa fa lallai rayuwar duniya was ace ta yara da manya da kuma kawa da alfahari a tsakanin ku da kuma gasan tara yara da kudiya Kaman misalin ruwan sama ne wanda ya shayar da gonaki sai kayan wannan gona ya burge masu shi bayan wani lokaci sai kaganshi ya koma yallo sa'annan kuma ya bushe, kuma a lahira akwai azaba me girma da gafara daga Allah da yarda, rayuwan duniya kuma ba komai bace face jin dadi na rudu (20)" suratul hadid.
Hakan bayana nufin mutum ya guji duniya bane baki dayan ta da yanke dukkanin alaka da ita hakika musulunci ya hana hakan, Allah madaukaki yace: " ka nemi gidan lahira cikin abunda Allah ya baka kuma kada ka manta da rabonka na duniya, kuma ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata maka, kada kayi barna a doron kasa lallai Allah bayason masu barna (77)" suratul kasas.
Allah madaukaki ya mana ni'imar hankali domin muyi amfani dashi cikin abunda zai jawo mana alheri duniyar mu da lahiran mu sai dai abun takaici dayawa daga cikin mutune suna amfani dashi ne cikin abunda zai jawo masu amfani ne kawai anan duniya koda kuwa a aljihun wasu ne kuma zai cutar dasu irin wannan nau'i na mutane kuwa Allah madaukaki yayi bayanin su cikin fadin sa cewa: " sun san zahirin komai na rayuwan duniyar su amma gafalallu ne game da lahira (7)" suratul rum.
Me wayau da dabara da hankali shine wanda yayi amfani da hankalin shi domin maslahar sa ta duniya da lahira ya cimma aiwatar da abunda zai sashi farin ciki dashi duniya wurin cin gajiyan dukkanin abunda Allah ya halitta a wannan duniya na maslahar sa da kuma gyara rayuwan sa da kuma sanin abunda zai kusanci ubangijin sa dashi domin ya kasance cikin shirin abunda yake jiran sa bayan mutuwar sa.

Mutum yana bukatar tsaya da nazari cikin ransa cikin abunda yake nashi da kuma abunda yake kansa na addini kasancewar al'amarin tafiyar baya dacewa agun mutum me hankali ya kai kansa zuwa ga bin addini ko kuma akida na karya wanda aka canza kuma bata dace da hankali ba me lafiya, da abunda Allah ya bashi na hankali zai iya banbancewa tsakanin gaskiya da karya da kuma daidai da kuskure, Allah yayi maka ni'ima na hankali domin kayi tunani bawai ka rika bi hakan b aba tare da tambaya ko kuma tunani gabanin haka, abun takaici shine hakan shine ke faruwa a wurin mutane dayawa ya samu iyayen sa da kakannin sa akan akida da addini shikenan kawai sai ya bisu da gado, kamar addinin indiya misali akwai dayawa daga cikin akidun cikinsa wanda yake aka kirkiro sabo wanda yake kashe shaukin gabanin fidira na bautan wasu halittu kamar bera da farji da shanu da dutse da sauran su har takai ga wani daya daga cikin malamai yace " a indiya ana bautan komai sai Allah kadai!" yana nufin addinai wand aba musulunci ba a kasar indiya, kuma hakan ya faru ne saboda bi da takalidanci (shine bin abu ko kuma mutum akan wani aiki daya keyi ba tare da tambayar sa ba menene dalilin sa akan haka) ba tare da lura ba da kuma taka tsantsan, wannan jinsin na mutum sune wanda Allah madaukaki ya zarge su ya kuma bayyana rashin amfanuwar su da fadin sa cewa: " idan kace masu kuzo zuwa ga abunda Allah ya saukar sai suce a'a mudai abunda muka samu iyayen mu akai ya wadatar damu, koda kuwa iyayen nasu basu san komai ba kuma ba shiryayyu bane (104)" suratul ma'ida.

Kada amun tsammani cewa ina zagin akidun wasu ko kuma isgilanci dasu, ba ha ka bane domin kuwa hakika alkur'ani ya hana mu hakan, Allah madaukaki yace: " kada ku zagi abunda suke bautamawa koma bayan Allah sais u zagi Allah saboda kiyayya da rashin ilimi kamar haka ne muka kawatawa ko wani al'umma ayyukan su sa'annan kuma zuwa ga ubangijin su zasu dawo sai ya basu labari game da abunda suka aikata (108)" suratul an'am.

Sai dai kawai kwadayi ne nakeyi na cewa asan wannan addini na gaskiya kuma abunda nakeso shine alheri ya samu kowa da aminci, tausayina irin ta mutum da tsorona akan su a karshen al'amari me ciwo shine mutum yam utu yana bautan wanin Allah da wani shari'a wanda ba shari'ar da aka saukar ma Muhammad s.a.w ba da ita wanda aka yardan masu da ita shine abunda yasani yin haka.

Domin ka kai zuwa ga gaskiya kayi amfani da hankalinka da tunanin ka cikin abunda kake ciki ka natsu sannan ka fara tunani cikin mallakin sararin samaniya da kasa da abunda Allah ya halitta a cikin su kuma kazama daga cikin wanda Allah ya fadi akan su cewa: " wanda suke ambaton Allah a tsaye da zaune da kuma kwance suna tunani cikin halittun sammai da kasa, ya ubangijin mu baka halicci wannan bah aka kawai domin barna tsarki ya tabbata a gareka ka tsire mu daga azabar wuta (191)" suratu al'imran.

Domin ka gane asalin hakika, Allah madaukaki yayi maka bayani da kasancewar be halicci wannan duniya ba domin wasu da yara da many aba cikin fadin sa cewa: " kuma bamu halicci sammai da kasa ba da abunda ke tsakanin su a matsayin was aba (38) bamu halicce sub a sai dagaskiya sai dai dayawa daga cikin mutane basu sani ba (39)" suratul dukkan.

Gaskiya itace ba'a halicci mutum ba domin wasa ba'ayi masa umurnin aikiata komai ba sannan ba'a hanashi aikita wasu abubuwan ba, kuma baza'a bashi lad aba ko kuma masa ukuba, Allah madaukaki yace: " shin kuna tsammani ne cewa mun halicce ku ne domin wasa kuma bazaku dawo ba zuwa gare mu (115) daukaka ya tabbata ga Allah me mulki na gaskiya babu abun bautawa da gaskiya sais hi ubangijin al'arshi me girma (116)" suratul muminun.
A dabi'ance ko wani mutum cikin al'amuran duniyan shi yana neman abunda yafi falala da kuma kamala da kuma abunda zai tabbatar da murnan sa shin cikin abinci ne ko kuma abunsha ko tufafi da sauran ababen more rayuwa, to haka ya dace daga gareshi ya rika aiwatar da haka akan akidar sa da addinin say a rika neman addinin da yafi falala da kamala wanda babu cin karo a cikin sa kuma be sabama fidirar mutum ba ingantacce, kuma hankali me lafiya wanda ake samun murnan zuciya da ita da natsuwa da kwanciyar rai. Ina mika kira na cikin wannan littafi ga makaranci me daraja da ya karanci musulunci addinin karshe zai same shi addini ne na kadaita Allah (tauhidi) wanda beci karo ba da fidirar mutum ko kuma hankali, addinin da Allah ya yardan ma halittun sa dashi hakan bazai zo maka sai ka tsarkake zuciyar ka daga son rai da sha'awar duniya da tsaban bangaranci na addini bayan gan da katar din Allah saboda haka ka tashi tsaye domin karantar sa daga asalin sa ingantattu kum ka amsheshi daga wurin amalaman addini bayin Allah wanda basa neman komai na burin duniya wurin karantar dashi kawai fatan su da babban burin su shine samun yardan Allah da kuma ceton yan uwan sa mutane daga wuta, ka nesanci duk wanda ya mayar da addini da shai'a a matsayin hanyar neman dukiya, Allah madaukaki yace: " lallai wanda suke boye abunda Allah ya saukar cikin littafi kuma suna neman wani lada dan kadan dashi to wannan ba komai suke cima cukunan sub a face wuta kuma Allah bazayyi magana dasu ba ranan alkiyama kuma bazai tsarkake sub a kuma sunada azaba me radadi (174)" suratul bakara.

Ka yaki kanka wurin neman Allah da gaskiyar da ta bace maka da sannu Allah zai kasance tare dakai zai shiryar dakai ya kuma maka jagora, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " duk wanda yayi kokari cikin al'amarin mu to da sannu zamu shiryar dashi hanyoyin mu kuma lallai Allah yana tare da masu kyautatawa (69)" suratul ankabut.


Zabin me wahala:
lallai canza addini yana cikin ababe masu wahala wanda mutum zai dauka cikin rayuwan sa yadda zuciyar sa zai hadu da alheri da sharri da kuma haduwa da rashin sa sai dai wannan hukunci ne wanda ya cancanci mutum ya jefa kansa cikin hanyar sa da komai nashi, Allah madaukaki yace: " a ranar da za'a bijoro da wanda suka kafurce sai ace masu shin wannan ba gaskiya bane sai suce kwarai tabbas muna rantsuwa da ubangijin mu, sai ace masu ku dandani azaba da abunda kuka kasance kuna kafurce masa (34)" suratul ahakaf.

Kasani akwai hanyoyi biyu wanda babu na ukun su, hanya wacce take kaiwa zuwa ga aljanna wannan kuma baya kasancewa sai ta hanyar manzon Allah s.a.w, da kuma hanya wacce take kaiwa zuwa ga wuta ta hanyar bin son rai da abunda take kwadayi, misalin mu kamar mutum ne wanda yake kan hanya mabanbanci bai san wani hanya bace zata kai shi inda yake son zuwa sai ga wani mutum yazo masa wanda yasan hanya ingantacciya sai ya nuna masa ita to kamar haka ne manzannin Allah suke.
Menene yafi wahala na hali da yaynayi a lokacin da mutum mara addini ko kuma wanda ya bautawa Allah bada addinin da manzanni suka zo dashi ba kuma Allah ya yardan ma bayin sa dashi ba sai ya samu wanda zai yaye masa gaskiya da hakikani ya kuma masa bayani halin da yaro yake zama tsoho acikin ta kuma a haifi abun da suke cikin ciki nan take, Allah madaukaki yace: " shin akwai abunda suke jira ne face fassarar sa a rana da fassarar sa zai zo wanda suka mantashi a baya zasu ce hakika fa manzannin ubangijin mu sun zo mana da gaskiya to ko muna da mataimaka wanda zasu taimake mu ko kuma a mayar damu duniya muyi aiki ba irin wanda mukayi ba a baya hakika sunyi asara kuma abunda suke kirkira sun bace masu (53)" suratul a'araf.

Zayyi burin inama da zai iya fansan kansa da abubuwa mafiya daraja wanda ya mallaka a duniya, Allah madaukaki yace: " mujirimi zayyi fatan cewa inama da zai fanshi kansa daga azaban wannan ranan da dansa (11) da masoyiyar sa matanshi da dan uwan sa (12) da mahifiyar sa wacce ta reni shi da kiyaye shi (13) da dukkanin wani wanda yake duniya baki daya indai zai tsiratar dashi (14) ina! Ai wutan jahannama ce (15) wacce take raba tsoka daga kashinta (16) tana kiran duk wani wanda ya juya baya da barin imani (17) ya kuma tara dukiya ya boye (18)" suratul ma'arij.
    
Kowa a cikin mu da fidirar sa yasan akwai alheri da kuma sharri kuma zai iya banbance hakan da abunda Allah ya bashi na hankali, shari'u na sama dukkanin su basu zo ba sai domin suyi umurni da alheri kuma suyi hani da sharri, mutane dukkanin su yan uwa na ksancewar su yan adam wanda uba daya yake hadasu da uwa daya saboda haka ne muke son addini daya ya hadamu wanda shine musulunci wanda dukkanin annabawa sukazo dashi da amnzanni kuma mubi shari'ar karshe wanda Allah ya saukar mubar wannan ababen bautan wanda aka kirkiro na gumaka da dukkanin abunda aka bautamawa wand aba Allah ba wanda Allah be saukar da wani hujja ba akansu kuma mu nisanci girmama wasu mutane da bauta musu, mu koma zuwa ga bautan Allah shi kadai bashi da abokin tarayya.


Karshen littafi:
Nayi imani da tabbacin cewa akwai yiwuwar mutum ya rayu cikin aminci a cikin wannan duniyar kuma suyi rayuwa baki dayan da abunda suke so na rayuwa da kuma natsuwan zuciya da kuma wankakkiyan zuciya da soyayya hakan zai faru ne idan suka hadu akan addinin gaskiya wanda zasu zama bayin Allah, ya lamunci daidaito a tsakanin mutane baki day aba tare da duba zuwa ga kalar fatar sub a ko kuma yarin su da asalinsu kuma ya lamunci yancin su yadda babu wanda zai bautar da wani,karamin cikin su zai girmama babba kuma za'a girmama malami a cikin su, kuma babu zalumci a tsakanin su, me raunin cikin su me karfi ne wanda za'a kwatan masa hakkin sa, kuma me karfin cikin su me rauni ne wanda za'a kwata hakkin wani daga wurin shi, za'a rike amana cikinta abayar da ita zuwa ga masu ita, kuma miyagun ayyuka zasuyi karanci a cikin su, kuma za'a rika bayar da hakkoki acikin su, zata kiyaye rayuwa da dukiyoyi da mutunci a cikin su, sannan kuma zasu so aikin alheri zasu rika umurtan juna da kyakyawan aiki da hanin juna daga aikata sharri domin jin dadin rayuwan su da amincin mutane, wannan wani abubuwa ne kadan cikin ayyukan addini na gaskiya, kamar yadda nace kungiyar fafutukan ganin dawowa da addinin hahudan ci na duniya tana son nisantar da mutane game da wannan addinin ta hanyar kafar yada labaranta wanda suke yakan hankula duniya dashi ta na abunda take sawwarawa na gaje da da kwatowa da kuma keta hakkokin dan adam kasancewa sun sani cewa wanzuwar say a jinginu ne da rashin yaduwar sa sannan kuma karewan say a jinginu ne da rashin yadashi da kuma shigan mutane cikin sa, sai sukayi sauri ta ko wani hanya da zasu iya da ikon da suke dashi domin lallata surarsa ga duniya, kuma basu sani ba cewa sufa Kaman wanda ya rufe rana ne da tafin hannun sa, gaskiya a bayyane take ita kuma karya bata tabbata kamar yadda Allah ya bada labari da hakan cikin fadin sa: " sunason kashe hasken Allah da bakunan su amma Allah yaki sai ya cika hasken sa koda kuwa kafirai basa so (32)" suratul tauba.

Kayi tunani da hankalinka kada ka bari wani ya maka tunani ka kasance me yanci na yanke hukunci kada ka zama mabiyi, a zamanin daya wuce gabanin bayyanar ilimi da ci gaban duniya anayima mutum uziri da jahilci amma yanzu babu wannan uziri, kasancewar hanyoyi masu sauki wurin samun ilimi yadda duniya ta zama kamar alkarya ce guda daya saboda hanyoyi na sadarwa mabanbanta, ka sani cewa hukunce ne me wahala sai dai ya cancanci tunani akai, addinin Allah gaskiya ne wanda yake wanzajje har zuwa tashin duniya, saboda haka ka zama cikin wanda idan ya gamsu da gaskiya sai ya dare kanta, kuma idan yayi imani sai yayi kira zuwa gareshi wannan shine siffar mutum dan birni wayayye yana neman alheri sannan kuma yana gudun sharri, Allah me girma yayi gaskiya: " shine wanda ya aiko da manzon sa da shiriya da kumaaddinin gaskiya domin ya daukaka shi akan addinai baki dayan su koda kuwa mushirikai basa so (33)" [suratul tauba, da suratul saffi ayata (9)].
Ina rokon Allah daya shiryar da zuciyar ka ya kuma haskaka hanyar ka ya kuma rike hannun ka zuwa gaskiya, godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad da iyalan sa da sahabban sa da Karin tsira.
 
www.islamland.com