SAKON MUSULUNCI

SAKON MUSULUNCI

SAKON MUSULUNCI
رسالة الإسلام بلغة الهوسا

 

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha
د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة


Fassara
European Islamic Research Center (EIRC)
المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية
& Muhammad Khamis
Wanda ya bibiyi fassara
& Hashim Muhammad Sani
 

www.islamland.com

 

 

Da sunan Allah me rahama me jin kai
Dukkan godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad (SAW), da iyalan sa das sahabban sa baki daya.
GABATARWA
Allah madaukaki yace: “kace yaku ma’abota litttafi ku taho zuwa ga wata kalma wacce take daidaita tsakanin mu wato kada mu bauta ma kowa sai Allah kuma kada muyi taraiya da shi da komai kuma kada sashin mu su rike wani sashi ababen bauta koma bayan Allah kuma idan suka juya baya to kuce musu ku shaida lallai mu musulmai ne (64)”
Lallai addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, saboda shi ne ya dace da fitira ingantacciya, kuma addini ne baiyananne babu rudani a cikin sa kuma babu jurwaye, saboda masu yin sa sun yi bincike ta hanyar tambayan dukkan abun da ya shige musu duhu, ko kuma abun da ke kwakwalen su sai sai dai bai bar amsar wadannan tambayoyi wadan da suka shafi addini a hannun kowa da kowa ba, Allah madaukaki yace: “kace lallai ubangiji na ya hana alfasha a baiyyane da boye, kuma ya hana zunubi da zalunci da da hakki ba, kuma ya hana ku hada wani abu da Allah a wurin bauta wanda bai saukar da hujja akan sa ba, kuma ya hana ku fadi wani abu game da Allah wanda baku sani ba (33)”
Sai dai hakkin amsa tambayoyin da suka shfi addini ya takaita ne ga ma’abota ilimi da kuma wadan da suka san al’amuran shari’a, Allah madaukaki yace: “ku tambayi ma’abota sani in ku baku sani ba (43)”
Hakika Annabi (SAW) ya baiyana irin barnar da ke faruwa in aka tambayi wanda bai da ilimin addini game da al’a muran addini, Annabi (SAW) yace: “lallai Allah baya karbe ilimi daga bayin sa ta hanyar fisge shi, sai dai yana karbe ilimi ne ta hanyar karban ran malamai, har idan ya zama ba malamin da ya rage sai mutane su riki wasu mutane jahilai sai a a dinga tambayan su su kuma suna bada fatawa ba da ilimi ba sai su bace kuma su batar “
Babu wasu mas’aloli a musulunci masu tsauri wadanda munyi imani da su kuma amma ace baza muyi tambaya game da su ba, sai dai abun da hankalin dan adam bazai iya riskan sa ba na al’amuran da suka shafi gaibu wanda ubangijin mu bai baiyana mana su ba, saboda babu wata maslaha da dan adam zai samu a in ya san su, amma abun da akwai maslaha a cikin su in dan adam ya san su na al’amuran gaibu to hakika ubangijin mu ya baiyan shi akan harshen manzan sa (SAW), kuma mu iyan adam akwai wasu tambayoyi wadan da ke kwakwalen kowa a cikin mu wanda suke bukatar amsa, amma sai mu samu musulunci ya amsa su ta hanya mai sauki kuma mai jan hankali, misali: da mutum zai yi tambaya game da asalin sa da ya samu amsa acikin fadar Allah madaukaki: “hakika mun halicci mutum daga asali na tabo (12) sai muka sanya shi maniyi a wuri matabbaci (13) sai muka halicci gudan jini daga maniyyi kuma muka halicci tsoka daga gudan jinin kuma muka halicci kasusuwa ga tsokar sai muka rufe kasusuwan da nama sa’annan muka tada shi a wata halitta ta daban Allah yayi albarka mafi kyautatawar masu halitta (14)” .
Kuma da mutum zai yi tambaya akan matsayin sa wannan duniyar da kuma darajar sa a tsakanin sauran halittun Allah masu yawa, zai samu amsa acikin fadar Allah madaukaki: “hakika mun karrama dan adam kuma mun rike su a kan tudu da kuma cikin teku kuma mun azurta su da abubuwa masu dadi kuma mun fifita su akan babe da yawa wadan da muka halitta fifitawa (70)” .
Kuma da mutum zai yi tambaya akan me ya kamata yayi game da sauran halittun da Allah ya halitta a wannan duniyar, zai samu amsa a cikin fadar Allah madaukaki: “Allah ne ya halitta muku teku dan jiragen ruwa suyi tafiya a cikin su da umurnin sa kuma dan ku nema daga falalar sa ko zakuyi godiya (12) kuma ya hore muku abun da ke cikin sammai da kasa dukkan su daga gareshi lallai akwai ayoyi a cikin wannan ga mutane masu tynani (13)” .
Kuma da mutum zai yi tambaya akan dalilin halittar sa da samuwar sa, zai samu amsa a cikin fadar Allah madaukaki: “kuma ban halicci aljani da mutum ba sai dan su bauta mini (56) bana bukatar wani arziki daga wurin su kuma bana bukatar su ciyar da ni (57) lallai Allah shi ne me azurtawa ma’abocin karfi mai tsanani (58)” .
Kuma da mutum zai yi tambaya akan mahaliccin da ya samar da wannan duniyar, kuma yake wajaba a bauta masa shi kadai banda wanin sa, zai samu amsa a cikin fadar Allah madaukaki: “kace shi ne Allah makadai ci (1) Allah wanda ake nufin sa da bukatu (2) be haifa ba kuma ba’a haife shi ba (3) kuma babu wanda ya kasance irin sa (4)”  kuma da fadar sa madaukaki: “shi ne na farko dakarshe kuma na baiyyane da boye kuma shi masani ne ga dukkan komai (3)” , da kuma fadar Allah madaukaki: “shi ne Allah wanda babu abin bauta koma bayan sa almalik alquddus as salam almuminu al muhaiminu al’azizu aljabbaru almutakabbiru, tsarki ya tabbata ga Allah daga abinda suke masa shirka (24) shi ne Allah mahalicci gwani mai suranta halitta yana da sunaye kyawawa abunda ke cikin sammai da kasa suna masa tasbihi kuma shi ne mabuwayi mai hikima (24)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da hanyar samun natsuwa da kuma kwanciyar hankali da kuma samun tabbatuwa, zai samu amsa a cikin fadar Allah madaukaki: “wadanda sukayi imani kuma zukatan su na natsuwa da ambatan Allah ku saurara lallai da ambatan Allah ne zukata ke samun natsuwa (28)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da hanyar dacewa da nasara da kuma ingantacciyar rayuwa, zai samu amsa a cikin fadar Allah madaukaki: “duk wanda yayi aiki na kwarai a cikin maza ko mata kuma yana mai imani to lallai zamu raya shi kyakkyawar rayuwa kuma zamu saka musu da mafi kyawon abun da suka kasance suna aikiatawa (97)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da halin wadanda basuyi imani da Allah ba, kuma basuyi imani da abun da aka saukar ba, zai samu amsa acikin fadan Allah madaukaki: “kuma duk wanda ya kauda kai daga ambato na to laali yana da rayuwa mai kunci kuma zamu tashe shi a ranar alkiyama yana makaho (124) zai ce ya ubangiji ya ka tada ni makaho alhalin da na kasance ina gani (125) sai Allah yace hakanan ayoyin mu suka zo maka sai ka manta da su to kai ma haka yau za’a manta da kai (126)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da cikakken addini wanda ya tattaro dukkan shari’O’I wanda ke gyara gari da mutun a cikin addinin sa da duniyar sa, zai samu amsa acikin fadan Allah madaukaki: “a yau na cikia muku addinin ku kuma na cika ni’ima ta a gare ku kuma na yadda da musulunci ne addinin ku (3)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da addinin gaskiya wanda ya cancanta ya rike shi da kuma hanyar da zata kai shi zuwa ga Allah da aljannnah, zai samu amsa a cikin fadar Allah madaukaki: “duk wanda ya riki wani addini wanda ba musulunci ba to baza a amsa masa ba kuma shi a lahira yana cikin masu hasara (85)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da alakar shi da sauran mutane, zai samu amsa a cikin fadan Allah madaukaki: “yaku mutane lallai mun halicce ku daga namiji da mace kuma muka sanya ku alummu da qabilu dan kusan juna lallai wanda yafi karamci a cikin ku a wurin Allah shi ne wanda yafi ku tsoran Allah (13)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da matsayar sa da ililmi, zai samu ama a cikin fadr Allah madaukaki: “Allah zai daga wadanda sukayi imani daga cikin ku kuma masu ililmi za’a qara musu darajoji (11)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da karshen sa a cikin wannan rayuwar, zai samu amsa a cikin fadar Allah madaukaki: “dukkan rai mai dandana mutuwa ce kuma lallai ku za’a cika muku ladan ku ranar alkiyama duk wanda aka nisanta shi daga wuta kuma aka shigar da shi aljannah to hakika ya rabauta kuma rayuwar duniya ba komai bace face wani dan jin dadi mai rudarwa (185)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da yiwuwar tada shi bayan mutuwar sa da kuma samar da shi sabo, zai samu amsa a cikin fadar Allah madaukaki: “kuma ya buga mana misali sai ya manta da halittar sa sai yace waye zai tayar da kasusuwa bayan sun rube (78) kace wanda ya kirkire su da farko shi ne zai tashe su kuma shi masani ne ga dukkan halitta (79) shi ne wanda ya sanya muku wuta daga bishiya koriya sai gashi daga gare ta kuke kunna wa (80) shin wanda ya halicci sammai da kasa bai da ikon yin halitta irin su, lalli zai iya dan shi ne mai halitta masani (81) lalli yadda al’amarin sa yake shi ne in ya so faruwar wani abu sai ya ce masa kasance sai ya kasance (82)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da karbabben aiki a wurin Allah bayan an tashe shi daga qabari, zai samu amsa a cikin fadar Allah madaukaki: “lalli wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiyuka na kwarai to aljannar firdausi ce zata zamo makomar su (107)”
Kuma da mutum zai yi tambaya game da makoma bayan tashi daga qabari, zai samu amsa mai baiyana cewa lallai al’amarin makoma abu ne na har abada dindindin, hanyoyi ne guda biyu babu na ukun su, ko dai zuwa aljannah ne ko kuma zuwa wuta, Allah madaukaki yace: “lallai wadan da suka kafirta daga ma’abota littafi da mushirikai suna cikin wutar jahannama zasu dawwama acikin ta wadannan su ne mafi sharrin halitta (6) lallai wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiyuka na kwarai wadannan su ne mafi al kairin halitta (7) sakamakon su a wurin ubangijin su shi ne aljannah wacce koramu ke gudana a karkashin ta suna masu dawwama a cikin ta Allah ya yadda da su kuma suma sun yadda da shi wannan sakamako ne ga wanda yaji tsoron ubangijin sa (8)”

Ya kai me karatu me daraja
Lallai ni ina da tabbacin cewa a musulunci akwai maganinin dukkan matsalolin da muka fama da su a duniyar mu ta yau, kuma ruko da musulunci da kuma aiki da shi zai warware dukkan su, laali dunuya ta gwada dukkan mazahabobi wanda a karshe zamani ya tabbatar da ceawa baza su iya warware matsalolin ba – duk da cewa za’a iya samun wata mazhabar wacce zata magance kadan daga cikin matsalolin – to me yasa duniya bazata yi ruko da musulunci ba kuma ta dabbaka shi?! (F Filweas)  yana cewa: jaridu s karshe sun watsa bayanai cewa lallai masu falsafa da marubuta a yammaci suna raya cewa lallai addainai na zamani sun tsufa sosai......kuma dole ne a rabu da su, wannan yana baiyana irin matsalar da da yawa daga cikin marubutan ke fama da ita saboda abun da suke cin karo da shi na rudu da kuma duhu a cikin addinin kiristanci, sai dai wadancan sunyi kuskure, dan musulunci shi ne kawai addinin da zai warware musu dukkan matsalolin su kuma yana nan shirye dan a zama canji ga wadancan addinai na rudu kuma shi a shirye yake dan kai,

Ya kai me karatu me daraja:
Bazan yi kuskure ba in nace da yawa daga cikin musulmai a wannan zamanin sun nisanci karantarwar musulunci da koyarwar sa ingantattu, dan abun da musulmai da yawa suke aikatawa a yau kawai wasu alamu ne na addini wanda ake aikatasu a wasu lokuta na musamman kawai, duk da cewa musulunci aqida ne da shari’a da manhaji da ibada da mu’amala, shi addini ne da kuma daula da dukkanin ma’anar da wannan kalmar zata iya dauka, kuma ana cewa: “wannan wane irin addini ne mai girma da yana da mazaje masu aiki da shi da karantarwar sa kuma suna bin umarnin sa kuma suna hanuwa daga abin da ya hana kuma suna isar da shi ga wanin su daidai da koyarwar Allah inda yace: “kayi kira zuwa tafarkin ubangijin ka da hikima da wa’azi mai kyau kuma kayi jayaiya da su da abun da yafi kyau”.
(Jack S Restler)  yana cewa a cikin farkon littafin sa mai suna, al hadaratul arabiyyah....... lallai sunan musulunci za’a iya ciro shi daga ma’anoni uku daban daban: ma’ana ta farko addini, ma’ana ta biyu daula, ma’ana ta uku wayewa, a takaice wayewa ta musamman.
Lallai musulunci da aqidar sa da ibadar sa da mu’amalar sa da koyarwar sa da kuma shari’ar sa tun lokacin da ya sauka ga annabi muhammad (SAW) har zuwa yau bai canza ba kuma bai jurwaya ba sai dai musulmai su ne suka canza, idan wani musulmi yayi kuskure to ba wai koyarwar musulunci ne hakan ba kuma musulunci bai yadda da hakan ba, bari mu buga wani misali akan hakan wanda zai baiyana mas’alar: da zamu ba wani mutum wata na’ura a warwatse amma akwai wani dan littafi daga masana’anta wanda zai nuna masa yadda zai hada wannan na’urar, to in yayi kuskure wurin hada ta ko kuma ya hada ta ba ta hanyar da aka nuna masa a cikin littafin ba, to shin za’ace bayanan da ke cikin littafinnan kuskure ne ko kuma ya za’a ce?! Akwai dai yiwuwar faruwar ababe uku:
1 - ko dai mutumin bai bi hanyoyin da aka baiyana a littafin ba ta hanya mai kyau.
2 - ko kuma mutumin bai dabbaka hanyoyin da aka baiyana a littafin ba dukkan su’
3 - ko kuma mutumin bai fahimci bayanan da ke cikin littafin ba, to a wannan yanayin dole ya koma kamfanin da sukayi wannan na’urar dan suyi mai bayanin yadda zai hada wannan na’urar da kuma tada ita, wannan misalin haka yake game da musulunci, ya kamata duk me san ya fahimce shi to ya koma tushen sa ingantattu wadan da aka yadda da su, domin ilimi na addini dole ne a koyo shi daga masanan sa, misali in mutum bashi da lafiya ai wurin likita zai je, in kuma gida zai gina ai wurin inginiya zai je, to haka nan kowa yana da inda ya kware.
Ni ina fata ga dukkan wanda ya karanta wannan littafi ya bar dukkan sanran sa ko kuma tunanin sa na molan ka, ya karanta irin karatun mai neman gaskiya dan ya santa kuma ya bita, ba wai irin karatun mai bibiyan kurarai ba da kuma neman aibi da kuma bin zamiya, irin karatun me tunani da hankalin sa ba wai mai gabatar da san ran saba, dan kar ya zama irin wanda Allah ya zarge su a cikin fadar sa: “kuma idan aka ce musu kubi abun da Allah ya saukar sai suce mu zamu bi abun da muka samu iyayen mu ne a kansakoda iyayen su basa gane komai kuma basa kan shiriya (170)”
Domin shi wayayyen mutum dan birni mai lafiyayyen tunani shi ne wanda baya dora molon kan sa ga wanin sa kuma ba ya aminta da abu sai bayan ya karan ta shi kuma ya san shi kuma ya tantan ce, to idan ya gane gaskiya kuma yaji ya natsu sai yayi saurin ruko da abun da ya natsu da shi, kuma bazai takaita abun nan da ya sani a kan sa shi kadai ba, zai ta kokarin yada abun da ya sani a cikin mutane sai ya sanar da wanda bai sani ba kuma yayi gyara ga wanda ke kuskure, kuma lallai ni ina mai tabbatar da cewa ban ba wannan maudu’in haqqin sa ba, kuma ban bashi abun da ya dace da shi ba na bincike a cikin wannan dan karamin littafin, domin kamar yadda muka fada musulunci tsari ne na bai daya yana tsara dukkan al’amuran duniya da lahira, to wannan yana bukatar a tattauna shi ne a cikin babban littafi ba dan karami ba, saboda haka ne na takaitu da yin nuni da shagube ga wasu daga cikin asulla da halaye na musulunci, dan ya zamu makulli ga wanda ke san yin bincike kuma ya zurfafa dan sanin hakikanin addinin musulunci.
Me magana zai iya cewa, ni ina cikin tsare tsare da dokokin mutanen zamani wanda suke kama da tsare tsaren da musulunci yazo da su! To amsa ita ce, waye ya riga musulunci ko tsare-tsaren zami? Lallai shari’ar musulunci ta riga wadannan tsare-tsare da dokoki, dan ana aiki da musulunci tun sama da karni goma sha hudu, duk abun da yazo yana kama da wasu tsare-tsare na musulunci da shari’ar sa to kada ayi mamaki cewa ya ciro ne daga musulunci, musamman ma idan muka san cewa a kwai wasu bincike da suka shafi musulunci – tun farkon zuwan sa – daga wadan da ba musulmai ba iyan gabaci wadanda hadafin su da niyyar su ta sha bam-ban daga mai neman gaskiya, da kuma makaranta dan tufka da warwara da kuma batanci.

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha
 
www.islamland.com
[email protected]

ABABE WADAN DA SUKE GIMSHIKAI A ADDININ MUSULUNCI
Manzan musulunci (SAW) yace a mina a hajjin ban kwana: “shin kun san wace rana ce wannan?” sai sukace Allah da manzan sa ne suka sani, sai yace: wannan rana ce mai alfarma, to ko kun san wane gari ne wannan?” sai suka ce Allah da manzan sa ne suka sani, sai yace: “gari ne mai alfarma, to ko kunsan wane wata ne wannan?” sai suka ce, Allah da manzan sa ne suka sani, sai yace”wata me alfarma” sai yace: “lallai Allah ya haramta muku jinin ku da da dukiyoyin ku da mutuncin ku kamar alfarmar wannan ranar a cikin wannan watan a cikin wannan garin naku””
Daga cikin gimshaikai na musulunci akawi kiyaye rai da mutunci da dukiya da hankali da dangantaka da kuma haqqin me rauni ko kuma gajiyayye, Allah madaukaki yace game da haramcin yin ta’addanci a kan rai: “kada ku kashe ran da Allah ya haramta sai da hakki”
Kuma Allah madaukaki yace game da haramcin ta’addanci ga mutunci: “kuma kada ku kusanci zinz domin laali al’amari ne na alfasha kuma mummunar hanya ce (32)”
Kuma Allah madaukaki yace game da haramcin ta’addanci game da dukiya: “kuma kada ku dunga cin dukiyoyin ku a tsakanin ku ta hanyar barna”
Kuma Allah ya fada game da haramcin ta’addanci ga hankali: “ya ku wadanda sukayi imani lallai giya da caca da gumaka da kibau datti ne daga aikin shedan to ku nisance su in kunyi haka tabbas zaku rabauta (90)”
Kuma Allah madaukaki ya fada game da haramcin yin ta’addanci akan dangantaka: ”kuma idan ya juya baya sai ya yi tafiya a ban kasa dan yayi barna a cikin ta kuma ya halaka shuka da dange kuma Allah baya san barna (205)”
Game da hakkin masu rauni kuma a cikin mutane Allah yana cewa:
1- game da hakkin iyaye: “kuma ubangijinka ya hukunta cewa kada a bauta ma kowa sai Allah kuma iyaye a kyautata musu idan dayan su ko kuma su biyun suka kai matakin tsufa a tare da kai to kada ka ce musu tur kuma kada kayi musu tsawa kuma ka fada musu zance na karamci (23) kuma ka saukar musu da fukafukanka na rahama kuma ka ya ubangiji ka jikan su kamar yadda suka ji kai na ina karami (24)”
2- game da hakkin maraya: “amma maraya kada kayi masa fin karfi (9)”
Kuma yana cewa game da kiyaye dukiyar sa: “kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai da abun da yafi ta kyau”
3- kuma game da hakkin yara: “kada ku kashe yaranku saboda talauci mune muke azurta ku da su”
4- Kuma game da hakkin marasa lafiya, Annabi (SAW) yana cewa: “kuyi belin wanda ke tsre kuma ku ciyar da mai jin yunwa kuma ku ziyarci mara lafiya “
5- Kuma game da hakkin gajiyayyu, Annabi (SAW) yana cewa: “baya cikin al umma ta duk wanda baya girmama babban mu kuma yaji tausayin karamin mu”
6- Kuma da hakkin mabukata, Allah madaukaki yana cewa: “kuma mai tambaya kada kayi masa tsawa (10)”
Kuma Annabi(SAW) yana cewa: “duk wanda ya tsaya dan bukatar dan uwan sa shima Allah zai biya masa bukatun sa”


BANGAREN RUHI A MUSULUNCI
Lallai addinin musulunci kamar wanin sa ne daga cikin addinai na sama wadanda suka gabace shi yazo da asulla da aqidu wanda suke wajaba mabiyan sa suyi imani da su kuma su kudurce su kuma suyi kokarin yada su da kuma kira zuwa gare su ba tare da tilastawa ba ko lazimtawa, dan yin aiki da fadar Allah madaukaki “babu tilastawa a cikin addini hakika gaskiya ta baiyana daga bata duk wanda ya kafirce wa dagutu kuma yayi imani da Allah to hakika yayi ruko da igiya mai kwari wacce bata tsinkewa kuma Allah mai ji ne masani (265)”
Kuma ya umarci mabiyansa da cewa da’awar su zuwa ga wannan addinin ta kasanci ta hanya me kyau dan yin aiki da fadar Allah madaukaki: “kayi kira zuwa hanyar ubangijin ka da hikima da wa’azi mai kyau kuma kayi jayayya da su da abin da yafi kyau “
Gamsuwa al’amari ne na asali a musulunci domin duk abin da aka gina shi akan tilasci to zai sa mutum ya fadi abun da ba shi bane a zuciyar sa to kuma wannan shi ne munafunci wanda musulunci ya tsawatar game da shi kuma ya nuna cewa yafi kafirci ma girma, Allah madaukaki yace: “lallai munafukai suna can cikin kasan wuta kuma baza ka samu me taimakon su ba (145)”

BANGAREN IBADA A MUSULUNCI
Musulunci ya zo da wasu tarin ibadu na kudircewa da magana da kuma aiki.
Na farko: ibadu na kudurcewa wanda ake kiransu a musulunci rukunnan imani, su ne:
1- Imani da Allah:
Yana hukunta kadaita Allah a cikin ababe uku:
A) Kadaita shi a cikin rububiyyar sa (aiyukan sa): shi ne tabbatar da samuwar sa kuma shi kadai ne mahaliccin wannan duniyar da abun da ke cikin ta kuma shi ne mamallakin ta mai juya al’amuranta, shi ke aikata komai shi kadai a wannan duniyar, babu abun da ke faruwa sai abun da ya so kuma babu abun da ke aukuwa sai da nufin sa, Allah madaukaki yace: “ku saurara lallai halitta da umuarni nashi ne Allah yayi albarka ubangijin talikai (45)”
Kuma hakika Allah ya baiyana abun da ke nuni akan kadaituwar sa da halitta, da kuma kore wane abun bauta tare da shi, Allah madaukaki yace: “Allah bai riki da ba kuma babu wani abun bauta tare da shi, in da akwai da kowane allah ya tafi da abun da halitta kuma da wanin su yafi karfin dayan tsarki ya tabbata ga Allah daga abun da suke siffata shi (91)”
B) kadaita shi a wurin bauta: shi ne kudurcewa ta gaskiya cewa lallai Allah shi ne abun bauta na gaskiya babu wani abun bauta koma bayan sa wanda ya cancanta a mai bauta, ba’a dogaro sai da shi, kuma ba’a roko sai shi, kuma ba’a neman warware wata matsala ko tabbatar wani abu sai a wurin shi, kuma ba’a alwashi sai gare shi, kuma ba’a yin wata ibada sai gare shi shi kadai banda wanin sa, Allah madaukaki yace: “bamu aiko wani manzo ba kafin ka face sai mun mai wahayi cewa babu abun bauta da gaskiya sai ni kadai to ku bauta mini (25)”
c) kadaita shi a cikin sunayen sa siffofin sa: shi ne kudurce cewa Allah yana da sunaye kyawawa da siffofi madaukaka, kuma shi ya tsarkak daga dukkan tawaya da aibi, Allah madaukaki yace: “kuma Allah yana da sunaye kyawawa to ku roke shi da su kuma ku rabu da masu ilhadi a cikin sunayen sa da sannu za’a saka musu da abun da suke aikatawa wa (180)
sai mu tabbatar masa abun da ya tabbatar wa kansa a cikin littafin sa ko kuma abun da manzan sa annnabi muhammadu (SAW) ya tabbatar masa da shi, wanda babu wata halitta dake kama da shi a cikin su, ba tare da yayantawa ba ko kuma kore su ko kuma kamantawa ko siffantawa ba, Allah madaukaki yace: “babu wani abu misalin sa kuma shi me ji ne me gani (11)”

2- Imani da mala’iku:
Shi ne imani da cewa lallai Allah yana da mala’iku masu yawa babu wanda yasa iyakar su sai Allah,suna kawo sakon Allah game da tsaro da kuma kulawa da wannan duniyar da abun da ke cikin ta na halittu gwargwadon zartarwar sa  , su ne aka wakilta da kula da sama da kasa da kuma dukkan motsi a duniya yana cikin kebantaccen aikin su kamar yadda mahaliccin su ya so, Allah madaukaki yace: “ina rantsuwa da mala’iku masu kula da al’amura (5) , da kuma fadar sa: “ina rantsuwa da mal’iku masu raba al’amura (4)”
An halicce su ne daga haske, Annabi (SAW) yana cewa: “an halicci mala’iku daga haske kuma an halicci aljanu daga wuta kuma an halicci Adam daga abun da aka siffanta muku”
Kuma su halitta ne na gaibu, duk da cewa mutane basa iya ganin su da ido, sai dai Allah ya basu ikun canzawa zuwa halittu iri- iri dan su iya ganin su duk lokacin da Allah yaso, kamar yadda ubangijin mu mabuwayi da saukaka ya bada labari game da mala’ika jibril amincin Allah ya tabbata a gare shi, cewa shi lallai ya zo wurin Maryam da siffan mutum: “sai ta riki wurin buya daga gare su sai muka aika mata da mala’ikan mu sai ya zo mata a matsayin madaidaicin mutum (17) sai tace lallai ni ina neman kariyar me rahama daga gare ka in kai me tsoran Allah ne to ka tafi ka barni (18) sai yace lallai ni dan aike ne kawai na ubangijinm ki dan in yi miki kyautar yaro me tsarki (19)
Kuma hakika Annabi (SAW) yaga mala’ika Jibrilu a yanayin halittar shi wacce Allah ya halicce shi akanta yana da fukafukai dari shida . Kuma su mala’iku suna da fukafukai, daka cikin su akwai me fufuke biyu kuma akwai me uku kuma akwai wanda nashi yafi haka yawa, Allah madaukaki yace: “godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa kuma ya sanya mala’iku iyan sako masu fukafukai wasu biyu wasu uku wasu hudu yana karawa a cikin halitta abun da yaso lallai Allah me iko ne akan dukkan komai (1) , amma sauran halaye da yanayin su abu ne wanda Allah ne kadai ya sani.
Suna raya lokutan su baki daya da ambaton Allah da yimasa tasbihi da kuma yabon sa, Allah madaukaki yace: “suna tasbihi dare da rana kuma su basa gajiya su dena (20)
Allah ya halicce su ne dan bautar sa, kamar yadda ya bada labari: “masihu bazi ki ya zama bawan Allah ba kuma mala’iku makusanta ma haka kuma duk wanda yaki bauta mini yayi girman kai to da sannu za’a tada su a gare shi baki daya (172)
Kuma su iyan sako ne tsakanin su da Allah da kuma mazannin sa cikin mutane, Allah madaukaki yace: “Ruhi amintacce ne ya saukar da shi (193) akan zuciyar ka dan ka zamo cikin masu gargadi (194) da haeshe na larabci mabaiyani (194)
Kuma Allah ya halicce su ne dan tsayuwa da ayyukan da ya umurce su, da kuma yin ibadar da ya dora musu, kamar yadda Allah madaukaki ya fada: “suna jin tsoran ubangijin su daga saman su kuma suna aikata aban da ake umaurtar su (50)  
Kuma su mala’iku ba iyaiyan Allah bane, yana wajaba a girmama su kuma a so su, Allah madaukaki yace: “kuma suka ce Allah ya riki yara tsarki ya tabbata a gare shi, a’a su ba yaran Allah bane sai dai su bayin Allah ne masu daraja (26) basa rugashi wurin zance kuma su suna aiki ne da umurnin sa (27)
Kuma su ba kishiyoyin Allah bane ko kuma abokan taraiya a gare shi, Allah madaukaki yace: “kuma baya umurtar ku da ku riki mala’iku da annnabawa ababen bauta shin zai umurce ku ne da kafirci bayan kun kasance musulmai (80)
Daga cikin wadannan mala’iku akawai wanda Allah ya fada mana sunayensu da aiyukan su, misali:
- Mala’ika Jibrilu amincin Allah ya tabbata a gare shi, shi ne wakili wurin wahayi, Allah madaukaki yace: “mala’ika jibrilu ne ya saukar da shi (193) akan zuciyar ka dan ka kasance cikin masu gargadi (194)”
 - mala’ika mika’il amincin Allah ya tabbata a gare shi, shi aka wakilta wurin ruwan sama da tsirrai, Allah madaukaki yace: “duk wanda ya kasance makiye ga Allah da mala’ikun sa da manzannin sajibrilu da mika’ilu to lallai Allah makiyi ne ga kafirai (98)   
- malakul mauti, Allah madaukaki yace: “kace mala’ikan mutuwa ne ke dankan ranku wanda aka wakilta muku sannan lalli zuwa ga ubangijin ku zaku koma (11)
- mala’ika israfilu amincin Allah tabbata a gare shi, shi aka wakilta wurin busa kaho dan tashi domin hisabi, Allah madaukaki yace: “idan akayi busa a cikin kaho to babu dangantaka a tsakaninsu a wannan ranar kuma basa tambaya (101)
- mala’ika malik amincin Allah ya tabbata a gare shi, shi ne me tsaron wuta, Allah madaukaki yace: “kuma iyan wuta zasuyi kira cewa ya maliku ka roka mana ubangijinka ya kashe mu sai yace ku kuna masu dawwama ne anan wuta (77)  
- zabaniyawa, su ne mala’ikun da aka wakilta dan yiwa iyan wuta azaba, Allah madaukaki yace: “to ya kira wanda zai kira (17) mu kuma zamu kira zabaniyawa (18)
- kuma kowane mutum yana tare da mala’iku guda biyu, dayan su yana rubuta aikin lada, shi kuma dayan yana rubuta aikin zunubai, Allah madaukaki yace: “lokacin da masu haduwa guda biyu suka hadu hagu da dama suna zaune (17) babu wani abu da zai fada faci akwai raqibu da atidu a wurin sa (18)
- mala’ika Ridwan, shi ne me tsaron aljannah, akwai kuma mala’ikun da aka wakilta dan tsare dan adam...... har dai zuwa karshe, cikin wanda sunayen su suka zo a cikin alkur’ani da hadisi, kuma acikin su akwai wanda ba’a bamu labarin su ba, to duka dai ya wajaba ayi imani da su baki daya.
Fa’idojin imani da mala’iku:
1- sanin girman Allah me tsarki da daukaka, da kuma ikon sa da kewayewar sa ga dukkan komai, domin girman halitta tana nuna girman mahalicci.
2- kwadayi wurin aikin alkairi da kuma nisantar munkarai a baiyane da boye, lokacin da musulmi ya tuna cewa akwai mala’ikun da suke kula da zantuttukan sa da aiyukan sa, kuma ya tuna cewa dukkan aiyukan sa ana lissafa su ko dai lada a gare shi ko kuma zunubi akan sa.
3- nisantar fadawa cikin rububi da rudani rin wanda basuyi imani da gaibi ba suka fada.
4- rahamar Allah ga bayin sa da kulawar sa a garesu, da kuwa ya wikilta musu mala’ikun da suke gadin su kuma suke jujjuya al’amuran su.

3 – imani da littattafai:
Shi ne imani da cewa lallai Allah ya saukar da littattafai daga wurin sa ga manzannin sa dan su isar da su ga mutane, sun kunshi gaskiya da kadaita Allah madaukaki a cikin ayyukan sa da bautar sa da sunayen sa da siffofin sa, Allah madaukaki yace: “hakika mun aiko manzannin mu da hujjoji kuma mun saukar da littafi da ma’auni a tare da su dan muta ne su tsayu da adalci”
Kuma musulmi ana so yayi imani da dukkan littattafan sama baki dayan su wadanda suka sauka kafin zuwan alkur’ani, kuma lalli su daga Allah suke, amma dai ba’ace yayi aiki da su ba ko kuma ya bisu, domin su an saukar da su ne dan wani kebantaccen zamani zuwa ga wasu tsurarun mutane, daga cikin wadannan littattafai wanda Allah ya fad mana sunansu a cikin littafin sa akwai:
1- suhufu Ibrahim da Musa amincin Allah ya tabbata a gare su: hakika alkur’ani yazo yana baiyana wasu asulla na addini wanda suka zo cikin wannan suhuf din, Allah madaukaki yace: “shin ko ba’a bashi labari game da abin da ke cikin suhufu Musa bane (36) da Ibrahim wanda ya cika alkawari (37) cewa wata rai bata daukar laifin wata (38) kuma mutam bai da komai sai abun da ya aikata (39) kuma lallai aikin sa da sannu za’a gani (40) sannan a saka mai sakamako cikakke (41)
2- attaurah: shi ne littafi me tsarki wanda aka saukar wa annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gareshi,Allah madaukaki yace: “lallai mu mun saukar da attaura a cikin ta akwai shiriya da haske annabawan da suka mika wuga ga Allah suna hukunci da ita ga wadanda suka zama yahudawa da malaman kiristoci da masu bautan su saboda abun da yaka basu tsaro na littafin Allah kuma su masu shaida ne akan sa kada kuji tsoron su sai dai kuji tsoro na kuma kada ku dinga saida ayoyin Allah da saboda kudade iyan kadan kuma duk wanda baiyu hukunci da abun da Allah ya saukar ba to wadannan su ne kafirai (44)
Kuma hakika alku’ani ya baiyana wasu ababe dake cikin attaura, daga cikin haka akwai ambatan wasu daga cikin siffofin Annabi Muhammad (SAW), Allah madaukaki yace: “Muhammadu manzan Allah ne kuma wadan da suke tare da shi masu tsanani ne ga kafiri amma masu tausayi ne a tsakanin su zaka gansu sunayin ruku’i da sujada suna neman falala daga ubangijin su da kuma yardar sa akwai alamun sujada a fuskokin su wannan shi ne misalin su a cikin attaura”
Kamar yadda alkur’ani ya baiyana wasu daga cikin hukunce-hukunce na shari’ahwanda aka ambata a cikin attaura, Allah madaukaki yace: “kuma mun wajabta musu a cikinta cewa lallai rai a matsayin rai ido da ido kuma hanci da hanci kunne da kunne hakori da hakori su kuma ciwuka sai ayi kisasi duk wanda ya yafe to kaffara ne a gare shi kuma duk wanda baiyi hukunci da abun da Allah ya saukar ba to wadannan su ne azzalumai (45)
3- zabura: shi ne littafin da aka saukar wa annabi Daud amincin Allah ya tabbata a gare shi, Allah madaukaki yace: “kuma mun ba wa annabi Dauda zabura (163)”
4- injila: shi ne littafi me tsarki wanda Allah ya saukar wa annabi Isa amincin Allah ya tabbata a gare shi, Allah madaukaki yace: “kuma mun taho da Isa dan Maryam a bayan su yana me gaegata abun da ya gabace shi na attaura kuma mun bashi injila a cikin ta akwai shiriya da haske kuma kuma shi littatafin attauran yana gasgata abunda ya gabace shi na attaura kuma shi shiriya ne da kuma wa’azi ga masu tsoron Allah (46)
Kuma hakika alkur’ani yayi bayanin wasu daga cikin ababen da suka zo a cikin attaura da injila, daga cikin haka akwai bushara da zuwan annabi Muhammad (SAW), Allah madaukaki yace: “kuma lokacin da Isa dan maryam yace ya ku bani isra’ila lallai ni manzan Allah ne zuwa gare ku ina me gasgata abun da ya gaba ce ni na attaura kuma ina muku albishir da zuwan wani manzo da zai zo a bayana sunan sa Ahmad”
5- alkur’ani mai girma: yana wajaba ayi imani da cewa lallai shi maganar Allah ne wanda mala’ika Jibrilu ya saukar da shi ga annabi Muhammad(SAW), da harshen larabci mabaiyani, Allah madaukaki yace: “mala’ika Jbrilu amintacce ne ya sauko da shi (193) akan zuciyarka dan ka zama cikin masu gargadi (194) da harshen larabci mabaiyani (195)”
Kuma shi Alkur’ani ya sha bam-bam da sauran littattafan da suka gabata da abubuwa masu zuwa:
- shi ne karshen littattafan sama, yana me gasgata abun da ya zo na sauran littattafan da suka gabace shi, kuma shi ba’a canza shi ko juyashi ba daga bayanin kadaita Allah da kuma wajabcin yimasa biyaiya da kuma bauta masa, Allah madaukaki yace: “kuma mun saukar ma da Alkur’ani da gaskiya yana me gasgata abun da ya gabace shi na littattafai kuma yana me shafe su”
- Allah ya shafe littattafan da suka gabace shi da zuwan sa, domin ya kunshi dukkan karantar wa na ubangiji na karshe masu tabbata masu dacewa da kowane zamani da lokaci, Allah madaukaki yace: “a yau na cika muku addinin ku kuma na cika ni’ima ta a gare ku kuma na yarda musulunci ne addinin ku”
- an saukar da shi ne saboda dukkan mutane, kuma shi ba na wasu mutane bane banda wasu kamar yadda lamarin yake game da littattafan, Allah madaukaki yace: “alif laam ra wannan littafi ne da muka saukar a gareka dan ka fitar da mutane daga duhu zuwa haske da izinin ubangijin su zuwa ga hanyar mabuwayi wanda ake godemawa (1)
- amma sauran littattafan duk da cewa sunyi taraiya da shi a cikin asalin addini sai dai an fuskantar da magana ne a cikin su zuwa ga wasu kebantattun mutane, saboda haka ne shari’u da hukunce hukuncen da ke cikin su kebantattu ne ga wadancan mutanen a zamanin su, banda wanin su, annabi Isa amincin Allah ya tabbata a gare shi yana cewa: ba’a aikoni ba face zuwa ga wasu batattun jama’a na bani isra’ila” (injilan matta 15:24)
- lallai shi alkur’ani ana bautar Allah da karanta shi da kuma haddace shi, manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace: “duk wanda ya karanta harafi daya daga littafin Allahi to yana da lada daya, kuma kowane lada za’a ninka shi sau goma, ba wai ina nufin cewa alif laam miim harafi daya bane, a’a alif harafi ne kuma miimun harafi ne kuma lamun harafi ne”
- lallai shi ya kunshi dukkan shari’o’in da suke samar da jama’a masu mutunci, (J.S. Restler)  yana cewa a cikin littafin sa, wayewar larabci: lalli alkur’ani yanada maganin dukkan matsaloli, kuma yana hada tsakanin dokoki na addini da kuma halaye,kuma yana kokarin samar da tsari na kasancewa jama’a daya, kuma yana kokarin sassauta tsanani da kwashe-kwashe, lalli shi yana kokarin kula da masu rauni, kuma yana wasiya da yin da’a, kuma yana umarni da ji tausay..... kuma game da yanayin tsari shari’a ya sanya ka’idoji na masu zurfi dan aikace aikacen yau da kullum, da tsare-tsaren yarjejeniya da kuma gado, kuma game da iyali ya iyakance kowane mutum da irin mu’amalar da zaiyi wa yara da bayi da dabbobi da kuma tufafi...... har dai zuwa karshe,
- lallai shi musulunci ya hikaaito ababen da suka faru a tarihi wanda suke baiyana yadda addini ya sauka a jere ga annabwa ds manzanni, da kuma abun da ya faru tsakanin su da mutanen su tun daga annabi Adam har zuwa karshen su Annabi Muhammadu (SAW).
- lallai Allah ya kiyaye shi daga kari ko kuma ragi, da kuma canzawa ko juya shi dan yazama jagoran mutane har zuwa lokacin da Allah zai gaje kasa da abun da ke kanta, Allah madaukaki yace: “lallai mu muka saukar da alkur’ani kuma lallai mu zamu kare shi (9)
Amma sauran littattafan Allah baiyi alkawarin kare su ba, saboda su sun sauka ne ga wasu mutane kebantattu a wani lokaci kebantacce, saboda haka ne ma aka caccanza su da jujjuya su, Allah ya fada game da caccanzawar da yahudawa sukayi wa attaura: “shin zaku yi tsammanin suyi imani da ku kuma daga cikin su akwai masu saurarar maganar Allah sai daga baya su canza ta bayan sun san ma’anar ta alhali suna sane (75) ,
 kuma game da canzawar da kiristoci sukayi wa Injila Allah madaukaki yace: “kuma daga cikin wadanda sukace mu nasara ne mun riki alkawarin su sai suka manta da wani kaso na abun da aka tunatar da su sai muka shigar da kiyayya da gaba a tsakanin su har zuwa ranar alkiyama kuma da sannu Allah zai basu labarin abun da suka kasance suna aikatawa (14) ya ku ma’abota littafi hakika manzan mu ya zo muku yana baiyana muku da dayawa daga cikin abun da kuke boyewa na littafi kuma yana kauda kai daga abubuwa da yawa hakika haske yazo muku daga Allah da kuma littafi mabaiyani (15)
kuma game da canje-canjen da yahudawa da kiristoci suka shigar a cikin addinin su, akwai rayawar da hahudawa sukayi cewa Uzairu dan Allah ne, su kuma kiristoci suka raya cewa Isa dan Allah ne, Allah madaukaki yace,: “kuma yahudawa sukace Uzairu dan Allah ne su kuma kiristoci suka ce Isa dan Allah ne wannan zance ne da sukeyi da bakunan su suna kama da zancen wadanda suka kafurta kafin su Allah ya tsine musu yaya ake juya su daga barin gaskiya (30)  sai alkur’ani ya mayar musu da martani dan gyara akan akan abun da suka kudurce na kuskura, Allah madaukaki yana cewa: “kace shi ne Allah makadaici (1) Allah wanda ake nufinsa dan biyan bukatu (2) be haifa ba kuma ba’a haife shi ba (3) kuma babu wani wanda yayi kama da shi (4).
Da Wannan ne zamu gane cewa Injilun (bible) da suke nan yanzu wanda suka hannnun mutane ba maganar Allah bane, kuma ba maganar annabi Isa bane, maganganun mabiyan sa ne da daliban sa, sun hada tarihin sa da wa’azozin sa da wasiyyoyin sa a cikin su, kuma hakika canje canje da sauye-sauye sun shiga cikin su,saboda wasu abubuwa na musamman, rabran T.J takur  yana cewa: kuma haka aka fitar da bible dan su samar da aikin yi ga jama’a wanda aka rubuta domin su, hakika anyi amfani da wasu nassoshi aciki wanda babu shakka a cikin su sai dai babu kokwanto akan cewa an canza su ko juya su da kuma kari a cikin su ko kuma cire abun da baiyi wa marubucin dadi ba.
Fa’idojin imani da littatttafai:
1 sanin rahamar Allah ga bayin sa da kuma sanda yake musu ta yadda ya saukar musu da littattafai wanda ke nuna musu hanyar da zata kaisu ga yaddar sa, kuma bai barsu a cikin rudu ba dan kar shedanu da sanrai su fisge su.
2 sanin hikimar Allah ta yadda ya shar’anta ma kowane mutane abun da ya dace da su na shari’a.
3- tace mumini na gaske daga wanda ba shi ba, dan duk wanda yayi imani da da littafin sa to ya lazimi ne yayi imani da sauran littattafan da Allah ya saukar wanda akyi albishir da su da kuma manzannin su.
4- rubanya lada daga Allah ga bayin sa, dan wanda yayi imani da littafin da aka saukar musu da kuma littattafan da suka sauka a bayan nasu to zai samu lada har sau biyu.

4 – imani da manzanni:
Shi ne imani da cewa lalli Allah ya zabi wasu mutane a matsayin manzanni da annabawa, ya aiko su zuwa ga halittun sa da shari’o’i dan tabbatar da bautar Allah da kuma tsaida addinin sa da kuma kadaita shi a cikin aiyukan sa da bautar sa da sunayen sa da siffofin sa, Allah madaukaki yace: “bamu aiko wani manzo ba kafin ka face sai mun mai wahayi cewa babu abun bauta da gaskiya sai ni to ku bauta mini ni kadai (25)
Kuma ya umarce su da isar da shari’ar sa ga mutane, dan kada mutane ya zama suna da hujja akan Allah bayan manzanni, su masu bushara ne da samun yaddar Allah da kuma aljannarsa ga wanda yayi imani da su da kuma abun da suka zo da shi, kuma suna gargadi daga fushin Allah da azabar sa ga wanda ya kafurce musu da abun da suka zo da shi, Allah madaukaki yace: “bamu aiko manzanni ba face su kasance masu bushara da gargadi duk wanda yayi imani kuma ya gyara to babu tsoro a kan su kuma su basa bakin ciki (48) kuma wanda suka karya a’yoyin mu to azaba zata shafe su saboda abun da suke yi na fasikanci (49)
Kuma annabawan Allah da manzannin sa suna da yawa babu wanda yasan adadin su sai Allah, Allah madaukaki yace: “hakika mun aiko da manzanni kafin ka daga cikin su akwai wanda muka baka labarin su kuma akwai wanda bamu baka labarin su ba a cikin su”
Yana wajaba ayi imani da su baki daya, kuma lallai su mutane ne, basu da wasu dabi’u na daban wanda ba na mutane ba, Allah madaukaki yace: “kuma bamu aiku ba kafin ka face wasu mazaje wanda muke musu wahayi to ku tambayi masana in baku sani ba (7) kuma bamu sanya su wani jiki na daban ba wanda basa cin abinci kuma su baza su dawwama ba (8) , Allah madaukaki ya fada game da annabi Muhammad (SAW): “kace lallai ni mutum ne irinku sai dai ni ana mini wahayi cewa lallai abun bautarku abun bauta ne guda daya duk wanda yake fatar haduwa da ubangijin sa to yayi aiki na kwarai kuma kada yayi shirka a wurin bautar ubangijin sa da kowa (110)
kuma Allah ya fada game da annabi Isa: “masihu dan Maryam ba kowa bane face manzo wanda manzannin sun zo kafin sakuma mahaifiyar sa me gaskiya ce sun kasance suna cin abinci ka duba yadda muke baiyana musu a’yoyi sannan ka duba kaga yadda ake kirkira musu karya (75)
kuma lallai su basu mallaki komai ba na siffofin da zasu sa a bauta musu, basa cutarwa ko amfanarwa kuma basa juya duniya da makamancin haka, Allah kadaukaki yace: “kace musu ban mallaki amfanarwa ko cutarwa ga kaina ba sai dai abun da Allah ya so da ace nasan gaibu da na yawaita aikin alheri kuma da wata cuta bata same ni ba “
kuma lalli su sun sauke amanar da aka dora musu kuma sun isar da sako, kuma su sun fi kowa ilimi cikin mutane da aiki, kuma lallai Allah yakare su daga karya da yaudara da yin dungu wurin isar da sako, Allah madaukaki yace: “babu wani manzo da zai zo da wata aya face da izinin Allah “
kuma wajibi ne muyi imani da su baki dayan su, duk wanda yayi imani da wasu daga cikin su kuma ya kafurce wa sauran to wannan ya kafurta kuma ya fita daga musulunci, Allah madaukaki yace: “lallai wadan da ke kafurce wa Allah da manzannin sa kuma suke son su bambamta tsakanin Allah da manzannin sa kuma suke cewa zamuyi imani da wasu kuma mu kafurce ma wasu kuma suna son su riki wata hanya tsakanin haka (150) to wadannan su ne kafurai na gaskiya kuma mun tanada azaba ta wulakanci ga kafurai (151)
kuma hakika alkur’ani ya ambata mana sunayen annabawa da manzanni guda ashirin da biyar, Allah madaukaki yace: “kuma waccan ita ce hujjar mu da muka baiwa Ibrahim akan mutanen sa muna daga darajar wanda muka so lallai ubangijin ka me hikima ne masani (83) kuma mun bashi kyautar Ishaq da Ya’aqub dukkann su munshiryar da su kuma mun shiryar da Nuhu kafin su kuma daga cikin zurriyar sa akwai Dau’d da sSulaimana da Ayyuba da Yusufa da Musa da Haruna kuma haka nan muke saka wa masu kyautatawa (84) da Zakariyya da Yahaya da Isa da Ilyas dukkan su suna cikin salihai (85) da Isma’il da alyasa’u da Lud dukkan su mun fifita su akan talikai (86) , kuma Allah ya fada game da Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi: “lallai Allah ya zabe Adam da Nuhu da iyalan Ibrahim da Iyalan Imrana akan talikai (33)  kuma Allah ya fada game da Hudu amincin Allah ya tabbata a gareshi: “kuma mun aika Hudu zuwa ga iyann uwan sa a’dawa sai yace yaku mutane na ku bauta wa Allah shi kadi baku da wani abun bauta koma bayan sa”  kuma Allah ya fada game da Salihu amincin Allah ya tabbta a gare shi: “kuma mun aiki Salihu zuwa ga iyan uwan sa samudawa sai yace yaku mutane na ku bauta wa Allah baku da wani abun bauta koma bayan sa”  
kuma Allah ya fada game da annabi Shu’aibu amincin Allah ya tabbata a gare shi: “kuma mun aika zuwa madyana dan uwansu Shu’aibu sai yace ya ku mutane na ku bauta wa Allah baku da wani abun bauta koma bayan sa “  kuma Allah ya fada game da annabi Idris amincin Allah ya tabbata a gare shi: “da Isma’ila da Idrisa da Zulkifl dukkan su suna cikin masu hakuri (85)”
kuma Allah ya fada game da annabi Muhammad (SAW), yana me bada labari cewa shi ne na karshen su kuma cikamakon su, babu wani annabi ko manzo da zai zo a bayan sa har zuwa ranar alkiyama” annabi Muhammad bai zamo daya daga cikin ubannin ku ba sai dai shi manzan Allah ne kjma cikamakon Annabawa” , addinin annabi muhammad shi ne cikon sauran addinan da suka gabace shi, dan haka shi ne addini cikakke na gaskiya wanda yake wajaba a bi shi kuma shi ne dauwamamme har zuwa tashin kiyama.
Daga cikin wadannan manzannin akwai wanda sukafi daraja, su ne mafi karfi wurin dakko sako da isar da shi ga mutane da kuma hakuri akan haka, su ne, nuhu, ibrahim,musa, isa, da kuma annabi Muhammad (SAW) Allah ya kara musu aminci baki dayan su, Allah madaukaki ya ce: “ka tuna lokacin da muka riki alkawari daga annabawa da kai da Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa kuma muka riki alkawari mai karfi daga gare su (7)”
Fa’idojin imani da manzanni:
1 sanin rahamar Allah ga bayin sa da kuma kaunar su dan ya aiko musu da manzanni daga cikin su domin su isar musu da shari’ar sa kuma dan ayi koyi da su.
2 tantance muminai na gaske daga wanda ba su ba dan duk wanda yayi imani da manzan sa to dole ne yayi imani da sauran manzannin wanda busharar zuwan su ta zo a cikin littafin sa da aka aiko musu.
3 rubanya lada daga wurin Allah ga bayin sa dan duk wanda yayi imani da manzan da aka aiko musu da kuma manzannin da suka zo a baya to za’a bashi lada har kaso biyu.

5- Imani da rana ta karshe:
Shi ne kudurce cewa lallai wannan rayuwar ta duniya zata kare wata rana, Allah madaukaki yace: “dukkan wanda ke kanta zasu kare (26) kuma fuskar ubangijin ka ce zata wanzu ma’abocin girma da daukaka (27)
idan Allah yaso duniya ta kare sai ya unarci mala’ika Israfilu ya busa kaho, sai sai dukkan halittu su mutu, se kuma ya kara umarni a busa kaho karo na biyu, sai mutane gabadayan su su fito daga kaburburan su a raye, kuma dukkan bangarorin jikin su zasu tattaro su hade tun daga zamanin annabi Adam, Allah madaukaki yace: “kuma za’ayi busa a cikin kaho sai dukkan wanda ke cikin sammai da kasa su mutu sai dai wanda Allah ya so sai a kara busa karo na biyu sai su tashi tsaye suna kallo (68)
kuma imani da rana ta karshe ya kunshi yin imani da dukkan abun da Allah ya bada labarin sa a cikin littafin sa da kuma dukkan abun da manzan sa ya bada labari na abun da zai kasance bayan mutuwa na:
1 - imani da rayuwar barzahu, ita ce abun da ke farawa tun daga mutuwar mutum har zuwa tashin alkiyama, kuma muminai ana musu ni’ima a cikin ta, su kuma kafirai ana azabtar da su a cikin ta, Allah madaukaki yace: “kuma mummunar azaba ta samu mutanen fir’auna (45) wuta ce za’a dinga bijiro da su a gare ta safiya da yammaci kuma ranar tashin alkiyama za’a ce wa mala’iku ku tura mutanen fir’auna zuwa azaba mafi tsanani (46)
2- imani da tashi daga kabari, ita ce ranar da Allah zai tada halittu baki dayan su ba takalma a tsirara ba kaciya, Allah madaukaki yace: “wadanda suka kafurta sun raya cewa baza’a tashe su ba kace na rantse da ubangiji na lallai za’a tashe ku sannan a baku labarin abun da kuka aikata kuma wannan mai sauki ne a wurin Allah (7)
Lura da cewa tashin mutane daga kabarin su abu ne wanda da yawa daga cikin mutane suna inkarin sa, sai alkur’ani yazo da misalai masu yawa wanda Allah yayi bayanin yiwuwar tada mutane kuma yana kore shubuhar masu musun hakan, daga cikin wadannan misalai:
a) yin tunan akan yadda kasa ke rauwa bayan ta mutu ta hanyar fitar da tsirrai a cikinta, Allah madaukaki yace: “kuma zaka ga kasa a bushe idan muka saukar da ruwa akan ta sai tayi girgiza kuma ta bude sai ta fitar da ko wane irin tsiro mai bada sha’awar kallo (5) wannan kuwa dan kusan cewa lallai Allah shi ne gaskiya kuma lallai shi ne me tada matattu kuma shi me iko ne akan dukkan komai (6) kuma lallai tashi alkiyama zata zo babu shakka a cikin ta kuma lallai Allah zai tada wadanda suke cikin kabari(7)
b) tunani a cikin halittar sammai da kasa wanda yafi girman halittar mutum, Allah madaukaki yace: “shin basa gane cewa lallai Allah wanda ya halicci sammai da kasa baida iko akan taba matattu lallai zai iya hakan kuma shi me iko ne akan dukkan komai (33)
c) tunani game da baccin mutum da kuma farkawar sa shi kamar rayuwa ne bayan mutuwa, shi yasa ake kiran shi karamar mutuwa-kanin mutuwa-, Allah madaukaki yace: “Allah shine wanda yake kashe rayuwaka a lokacin mutuwar su da kuma wanda bazata mutuba a lokacin baccin ta, sai ya rika ran da ya rubuta mata mutuwa ya dawo da sauran zuwa wani lokaci sananne, lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (42)
d) tunani akan halittar mutum tun farko, Allah madaukaki yace: “kuma ya buga mana misali sai ya manta halittar sa sai yace waye zai tada kasusuwa bayan sun zama rududdugaggu (78) kace wanda ya halicce su tun farko shi ne zai tada su kuma shi masani ne ga dukkan halttu (79)
3- imani da tashi daga kabari da kuma bijiro da aiyuka, Allah zai tada halittu dukkan su dan yin hisabi za kuma a bijiro musu da aiyukan su, Allah madaukaki yace: “kuma a ranar zamu tafiyar da duwatsu kuma zaka ga kasa a shimfide kumsai mu tado su daga kabari bazamu bar ko daya ba daga cikin su (47) za’a bijiro da su ga ubangijin ka sahu-sahu hakika kun zo mana kamar yadda muka halicce ku tun farko”
4- imani da cewa gabobi zasu yi shaida, Allah madaukaki yace: “kuma suka ce wa gabban su dan me zakuyi shaida akan mu sai suce Allah ne yasa mukayi magana wanda shi ne ke sawa komai yayi magana kuma shi ne ya halicce ku tun farko kuma zuwa gare shi zaku koma (21) ku baku kasance kuna boyewa dan kada jinku ko ganin ku ko fatunku suyi shaida akan ku ba sai dai ku kuna zaton cewa Allah be san dayawa daga abun da kuke aikatawa ba (22)
5- imani da yin tambaya, Allah madaukaki yace: “ku tsaida su lallai su abun tambaya ne (24) dan me baza ku taimaki juna ba (25) a’a su a yau sun mika wuya (26)
6- imani da siradi da kuma wucewa da za’ayi akan sa,Allah madaukaki yace: “kuma babu wani acikin ku face sai ya biyo ta kansa wannan ga ubangijinka alkawari ne tabbatacce sai ya faru (71) sai mu tsiratar da masu tsoron Allah su kuma azzalumai sai mu bassu su fada cikin wuta (72)
7- imani da auna aiyuka, sai a saka ma wanda suka kyautata saboda kyautatawar su da imanin su da kuma biyayyar su ga annabawa, kuma za’a yiwa wanda suka munana aiyukan su ukuba, sakamakon abun da suka aikata na munantawa da kuma kafirci ko kuma sabawa annabawansu, Allah madaukaki yace: “kuma zamu ajiye ma’aunai na adalci a ranar alkiyama baza’a zalunci wata rai da komai ba koda kwayar zarra ce ta kwallan dabino ta zamu zo da ita kuma mun isa mu zamu masu hisabi (47)  
8- imani da raba takaddu da kuma littattafai, Allah madaukaki yace: “duk wanda aka bashi littafin sa da hannun daman sa (7) to za’ayi masa hisabi mai sauki (8) amma duk wanda aka bashi littafin sa ta bayan sa (10) ta da sannu zai dinga kiran halaka (11) kuma zai shiga wutar sa’ira (12)
9- imani da sakamako kodai aljanna ko wuta, za’ayi rayuwa ta har abada, Allah madaukaki yace: “lallai wadanda suka kafurta daga ma’abota littafi da mushirikai zasu shiga wutar jahannama suna masu dawwama a cikin ta wadannan su ne mafi sharrin halitta (6) lallai wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiyuka na kwarai to wadannan su ne mafi alkairin halitta (7) sakamakon su a wurin ubangijin su ita ce aljanna wacce koramu ke gudana a karkashin ta suna masu dawwama a cikin ta har abada Allah ya yadda dasu kuma suma sun yadda da shi wannan sakamako ne ga wanda yaji tsoron ubangijin sa (8)
10- imani da haudi da kuma ceto...., har dai zuwa karshe cikin abun da manzan Allah (SAW) ya bada labarin sa.
Fa’idojin imanimda rana ta karshe:
1- yin tattali dan zuwan wannan ranar, ta hanyar dawwama akan aikin alkairi da kuma rige-rige a wurin su dan neman lada da sakamako me kyau, da kuma guje wa sabo dan tsoran azabar a wannan ranar.
2- lallashin muminai daga abun da ya kubuce musu na jin dadin duniya saboda sakamakon da suke kauna a wurin Allah a ranar lahira na lada da kuma ni’ma.
3- tantance muminai na kwarai da kuma wanda basu ba.

6- imani da da abun da Allah ya hukun ta da kuma kaddara:
Shi ne imani da cewa lallai Allah ya san dukkan komai tun fil azal tun kafin su faru kuma yasan yadda zasu kasance, sai ya samar da su yadda ilimin shi yake da kuma yadda ya kaddara, Allah madaukaki ya ce: “lallai mu mun halicci dukkan komai da kaddara (49) , dukkan abun da ya faru da kuma wanda zai faru a wnnan duniyar duk sananne ne a wurin Allah tun kafun aukuwar sa, sai daga baya Allah ya samar da shi daidai da yadda yaso kuma ya kaddara, Annabi (SAW) yace: bawa bazai yi imani ba har sai yayi imani da kaddara alkairinta da kuma sharrinta, kuma har sai ya san cewa duk abun da ya same shi to dama bazi kubuce masa ba kuma duk abun da ya kubuce masa to dama bazai same shi ba”
Kuma wannan bai kore ruko da sababi da kuma aiki da su, misali:duk wanda ke san zurriyya to dole yayi riko da sababin da zai cika masa wannan burin shi ne aure, sai da wannan sababin zai iya samar da abun da ake kauna naga gareshi- wato samun yara- kuma zai iya rashin samunsa’a, gwargwadon abun da Allah ya so, dan sabubba basu ne ke zartarwa ba, abun da ke zartarwa shi ne abun da Allah yaso, kuma su wadannan sabubban da muke rukon su kuma muke aiki da su, suna daga cikin abun da Allah ya kaddara, saboda haka ne manzan Allah (SAW) yake cewa yana yiwa sahabban sa bayani lokacin da suka tambaye shi, sai suka ce: ya manzan Allah, me kake gani game da rukiyya da muke yi da kuma magani da muke yi da kuma neman kariya da muke yi shin zasu iya tunkude wani abu daga cikin Abunda Allah ya kaddar, sai annabi yace: ai su din ma suna cikin abun da Allah ya kaddara”
Yinwa da kishirwa da sanyi duk suna cikin abunda aka kaddara, mutane suna kokarin tunkude yinwa ta hanyar cin abinci, kuma suna ture kishi ta hanyar shan ruwa, kuma suna tunkude sanyi ta hanyar abu mai dumi, sai su tunkude abun da aka kaddara musu na yinwa da kishi da sanyi da wani abunda aka kaddara musu wanda shi ne ci da sha neman abu mai dumi, sai su tunkude wata kaddara da wata kaddarar.
Fa’idojin imani da abun da aka hukunta da kuma kaddara:
1 yadda da abun da ya auku wanda aka kaddara ya haifar da natsuwa acikin zuciya da kuma kwanciyar hankali, zai zama ba wurin zaman damuwa da bacin rai a zuciya na abunda kubuce, kuma bazai boyu ba ga dukkan kowa cewa rashin natsuwar zuciya da kwanciyar hankali yana haifar da cututtuka masu yawa na zuciya na daga damuwa da bakinciki wanda suke da cutarwa a jiki, imani da kaddara kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari yana gusar da wannan dukkan sa, Allah madaukaki yace: “babu wata musiba da zata faru a cikin kasa ko kuma a kawunan kuface mun rubuta ta a cikin littafi tun kafin mu halicce ta lallai wannan a wurin Allah me sauki ne (22) dan kada kuyi bakin ciki akan abun da ya kubuce muku kuma kada ku dinga farinciki da abun da ya baku kuma Allah baya kaunar dukkan me takama me yawan alfahari (23)
2- kira zuwa ga ilimi da kuma binciken abunda Allah ya ya halitta a wannan duniyar, dan kuwa abunda aka kaddara wa mutum na rashin lafiya kaddara ne amma zai iya neman tunkude shi ta hanyar magani sai ya tunkude abun da aka kaddara masa a farko ta hanyar neman tushen magani cikin abun da Allah ya halitta a wannan duniyar
3- sassauci ga abun da ke samun mutum na masibu, da wata hasara zata fada wa wani mutum a cikin kasuwancin sa, to aukuwar hasarar musibace da zai bita da bakin ciki da damuwa zai zama musiba biyu kenan, musibar hasara da kuma musibar bakin ciki da damuwa, duk wanda yayi imani da kaddara zai yadda da hasarar farko, dan yasan cewa haka aka kaddara a kan sa kuma babu makawa sai ta auku, Annabi (SAW) yana cewa: “mumini me karfi yafi alkairi kuma yafi soyuwa a wurin Allah daga mumini me rauni, kuma dukkan su akwai alkairi a cikin su kayi kwadayi akan abun da zai amfanar da kai kuma ka nemi taimakon Allah kuma kada ka gajiya, kuma idan wani abu ya same ka to kada kace da na aikata kaza da kaza da kaza sun faru, sai dai kace haka Allah ya kaddara kuma yana aikata abun da yaso, domin cewa dama-dama tana bude kofar shaidan
Kuma shi imani da kaddara ba kamar yadda wasu ke tunani bane na cewa kirane na zaman kashe wando da kin yin aiki da kuma kin riko da sabubba, annabi (SAW) yace wa wani mutum da ya tambaye shi< yace ya manzan Allah in daure dabbata inyi tawakkali koko in sake ta inyi tawakkali, sai annabi yace: ka daure ta sai ka dogara ga Allah (tawakkali)”


Na biyu: ibadu na magana da aiki su ne ake kira rukunnan musulunci:
Su ne gimshikai wanda musulunci ya kafu a kansu, kuma da su ne ake yiwa mutum hukunci da musulunci ko rashin sa, daga cikin wadannan rukunnan akwai wanda na magana ne, shi ne “kalmar shahada”, kuma akwai wanda da jiki ake yi, shi ne “salla”, akwai wanda da dukiya akeyi, shi ne “zakka”, akwai wanda da jiki da dukiya ake yi, shi ne “hajji”, musulunci ba wai yana nufin da wadannan abubuwan na ibada zahirin su kawai bane, sai dai shi yana kokarin tsarkake zukatansu ne da kuma dogewarsu da tsabtacesu ta hanyar yin wadannan ibadun, musulunci yan bukata dabbaka wadannan rukunnani da su zama hanya na gyara ga mutum da kuma daidaituwar sa, Allah madaukaki yace: “lallai salla tana hani daga alfasha da abun ki” , kuma Allah ya fada game da zakka: “ka karbi zakka da dukiyoyin su ka tsarkake su kuma ka tsabtace su da ita” , kuma Allah yace game da azumi: “ya ku wadanda sukayi imani an wajabta azumi akan ku kamar yadda aka wajabta shi akan wadan da suke gabanin ku domin ku samu tsoran Allah (183)” , shi azumi tarbiyya ne da koyan kamewa daga san rai da abun da take sha’awa, wannan shi ne abun da fadar manzan Allah (SAW) ke baiyanawa game da azumi: “duk wanda be bar maganar karya ba da kuma aiki da kuma aiki da ita ba da jahilci to Allah be bukatar ya bar abincin sa da abin shan sa” , kuma Allah ya fada game da hajji: “hajji watanni ne sanannu duk wanda ya je sauke farali a cikin su to babu zagi kuma babu fasikanci kuma babu jayayya a hajji”
Ibadu a musulunci suna da matsayi me girma wurin gina kyawawan dabi’u da kuma habakasu,kuma rukunnan musulunci su ne kamar haka:
1- rukuni na farko: kalmar shahada biyu:
Su ne “shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, da kuma shaidawa Muhammadu bawan Allah ne kuma manzan sa ne”. Wannan rukuni yana cikin rukunnani na zance kuma shine mabudin shiga musulunci wanda akan shi ne ake gina saura rukunnan.
Ma’anar “lai’laha’illallahu”
Ita ce kalmar tauhidi, saboda itane Allah ya halicci dukkan halittu,da aljannah da wuta, Allah madaukaki yace: “ban halicci aljani da mutum ba sai dan su bauta mini ni kadai (56)”
Kuma ita ce da’awar annabwa da manzanni dukkan su tun daga Nuhu har zuwa na karshen su annabi Muhammad (SAW), Allah madaukaki yace: “bamu aiko wani manzo ba kafin ka face sai mun mai wahayi cewa babu wani abun bauta da gaskiya sai ni to ku bauta mini ni kadai (25)
Kuma ma’anar ta shi ne babu wani abu da ya cancanta da bauta sai dai Allah shi kadai.
Ababen da la’ilaha’illallahu ta hukuntawa:
1 -sanin cewa duk wani abun bauta wanda ba Allah ba to bata ne, babu abun bauta da gaskiya sai Allah, shi kadai ne wanda ya cancanci a yiwa bauta baki daya na salla da addu’a da fata da yanka da alwashi.... duk wanda yayi wani nau’i na bauta ga wanin Allah yana me bauta masa da girmama shi to ya kafurta koda kuwa ya furta kalmar shahada.
2- samun yaqini wanda ke kore shakka, baya shakka akan haka kuma baya kokwanto, Allah madaukaki yace: “lallai muminai su ne wanda sukayi imanida Allah da manzan sa sannan basuyi shakka ba akan haka kuma suka yi jihadi da dukiyoyin su da rayukan susaboda Allah to wadannan su ne masu gaskiya (15)
3- karbar ta da kumarashin kore ta, Allalh madukaki yace: “lallai su sun kasance in aka ce musu babu abun bauta da gaskiya sai Allah sai su dunga giman kai (35)
4- aiki da abun da ta kunsa, yana me jayuwa zuwa gare ta, sai yayi abun da Allah yayi umarni kuma ya hanu daga abun da ya hana, Allah madaukaki yace: “duk wanda ya mika wuyan sa zuwa ga Allah kuma yana me kyautatawa to hakika yayi ruko da igiya me kwari kuma ga Allah ne karshen al’amari yake (22)
5- ya kasance me gaskiya a cikin hakan, Allah madaukaki yace: “munafukai suna furtawa da harshen su abun da ba shi ne a zuciyar su ba”
6- ya kasance me iklasi a cikin bautar sa ga Allah shi kadai, Allah madaukaki yace: “kuma ba’a umarce su da komai ba sai dai su bautawa Allah suna masu tsarkake addini a gareshi masu karkata zuwa ga addinin gaskiya”
7- kaunar Allah da manzan sa da masoyan sa da bayin Allah na kwarai, da kin makiya Allah da manzan sa, da gabatar da son Allah da manzan sa koda ya sabawa san ransa, Allah madaukaki yace: “kace in iyayen ku da iyaiyan ku da iyan uwan ku da matan ku da dangin ku da dukiyoyin ku da kuke tara wa da kuma kasuwancin da kuke fata ya habaka da kuma gidaje da kuke kauna su suka fi soyuwa a gare ku fiye da Allah da manzan sa da kuma jihadi dan daukaka addinin sa to ku jira har lokacin da Allah zai zo da al’amarin sa kuma Allah baya shiryar da mutane fasikai (24)
8- daga cikin abun da ta kunsa shi ne lallai hakkin shar’antawa a wurin bauta da tsara mu’amala ga gama’a da kuma daidaikun mutane, da kuma halattawa da haramtawa hakkin Allah ne shi kadai wanda yayi bayanin sa ta harshen manzan sa (SAW), Allah madaukaki yace: “duk abun da manzo yazo muku da shi to ku rike shi kuma duk abun da ya hane ku daga gare shi to ku hanu”
Ma’anar shaidawa lallai “annabi muhammadu manzan Allah ne”:
Yi masa da’a a cikin abun da yayi umarni, da gasgata shi cikin abun da ya bada labari, da nisantar abun da ya hana kuma ya tsawatar, Allah madaukaki yace: “duk abun da manzo yazo muku da shi to ku rike shi kuma duk abun da ya hane ku daga gare shi to ku hanu “
Kuma wanna yana hukun ta:
1 kudurce gaskiyar sakon sa, kuma shi ne manzanni kuma cikamakon su kuma mafificin su, babu wani annabi ko manzo a bayan sa. Allah madaukaki yace: “muhammadu be zama mahaifin daya daga cikin mazajen ku ba sai dai shi manzan Alah ne kuma cikamakin annabawa”
2- kudurce cewa ma’asumi ne shi (SAW) cikin sakon da yake isarwa daga Allah, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma shi baya magana ta sanran sa (3) duk abun da zai fada wahayi ne aka mai (4)”
Amma al’amuransa na duniya to shi mutun ne, abubuwan sa na yau da kullum na rayuwar duniya yana ijtihadi ne a cikin su, annabi (SAW) yana cewa: “lallai ni mutum ne irin kukuma lalliai ku kuna husuma a wuri na ba mamaki wani yafi wani iya baiyana hujjarsa sai in mashi rin jaye gwargwadan abun da naji na hujjoji, to duk wanda na bashi hakkin dan’uwan sa to kar ya amsa in kuma ya amsa to ya amsa wuta”
3- kudurce cewa sakon sa ya shafi dukkan aljanu da mutane har zuwa tashin alkiyama, Allah madaukaki yace: “bamu aiko ba face manzo ga dukkan mutane kana me bushara da kuma gargadi”
4- bin sunnar sa (SAW) da yin ruko da ita, da kuma rashin kari a cikin ta, saboda fadar Allah madaukaki: “kace musu in kun kasance kuna san Allah to ku bi ni sai Allah ya so ku kuma ya gafarta muku zunuban ku kuma Allah me gafara ne me jin kai (31)”

2- rukini na biyu: tsaida salla:
Ita ce gimshikin addini wanda be tsayuwa sai da shi, duk wanda ya barta to ya kafurta, Annabi (SAW) yace: “kololuwar al’amari shi ne musulunci, kuma gimshikin sa shi ne sallah”
Kuma ita zantuka ne da aiyuka wanda ake fara su da kabbara kuma ake karewa da sallama, musulmi na tsaida ita dan yin biyayya ga Allah da kuma girmamawa a gareshi, yana kebewa da ubangijin sa a cikin ta., yana ganawa da shi kuma yana kaskantar da kai a gare shi, ita ce tsani tsakanin bawa da ubangijin sa, a duk lokacin da musulmi ya nutse a cikin jin dadin rayuwar duniya, kuma hasken imani ya fara dashewa a zuciyar sa, sai me kiran sallah ya kira salla sai wannan hasken ya fara karfi, sai ya zama yana da alaka da ubangijin sa a cikin dukkan lokutan sa, kuma su salloli ne guda biyar a cikin yini da dare, musulmi na yin su a cikin jam’i a masallaci sai dai in da wani uzuri, sai hakan ya sanya sanayya a tsakanin su kuma kauna ta yi karfi a cikinsu, kuma sai su dinga biciken sashe in basu gan shi ba, duk wanda bai da lafiya a cikin su sai su ziyar ce shi, kuma duk wanda ya kasance mabukaci a cikin su sai su taimake shi, kuma duk wanda ke cikin bakin cii sai su lallashe shi, kuma duk wanda ya kasance me rauni wurin zuwa masallaci sai suyi mai nasiha, kuma a ciki ta akwai debe dukkan bambance-bambance a mutane, musulmai suna tsayuwa dukkan su cikin sahu a gefen juna yaro da babba, talaka da me kudi, me daraja da wanda beda ita, dukkan su daya suke wurin kaskantar da kai ga Allah da kuma tsayuwa a gaban sa, suna masu fuskantar alkibila daya, suna yin motsi iri daya da kuma karatu iri daya kuma cikin lokaci daya.

3- rukuni na uku: bada zakka:
Ita wani kaso ne na dukiya wanda musulmi mawadaci ke fitarwa daga dukiyar sa, yana me dadin rai, dan yin da’a ga Allah da kuma bin umarnin sa, zai bada ita ga iyan’uwan sa wanda suke da bukatar ta, cikin talakawa da miskinai da msu bukata dan biyan bukatun su da kuma wadatar da su daga kaskancin roko, kuma ita wajiba ce akan dukkan musulmin da ya mallaki nisabi, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma ba’a umurce su da komai ba sai dai su bauta wa Allah suna masu tsarkake addi ni a gareshi su tsaida sallah kuma su bada zakka kuma wannan shi ne addini mikakke (5)
Duk wanda ya karyata wajabcin ta to ya kafurta, dan ya hana masu rauni daga cikin fakirai da miskinai hakkin su, kuma ita zakka ba wai haraji bace wanda daular musulunci ke karba daga mabiyan ta- kamar yadda wanda basu sam musulunci ba suke rayawa- dan da ace haraji ne to da zai wajaba ne akan dukkan wanda ke rayuwa a daular musuluncin ne cikin kafurai da musulmai, kuma sanannen abu ne cewa daga cikin sharadin zakka sai mutum ya zama musulmi ne, dan bata wajaba akan wanda ba musulmi ba.
Kuma tana da sharuddan da musulunci ya gidaya, sune:
1 mallakar nisabi: ya zama yana da dukiyar da ta kai iyakar da musulunci ya sa zakka a cikin sa, kuma yana ka kimanin ma’auni (85) na zinari.
2- cikar shekara: wannan a cikin dabbobi da kuma kudi da kuma kayan kasuwanci, duk abun da shekara bata zagayo akan shi ba to babu zakka a cikin sa, har sai shekara ta zagayo, amma su hatsi ana yin ta ne lokacin da suka nuna, su kuma iyaiyan itatuwa lokacin da suka fara nuna, kuma hakika shari’a ta iyakan ce wanda suka cancanta abasu zakka, saboda fadar Allah madaukaki: “lalli zakka ana bata ita ne ga fakirai da miskinai da masu aiki dan ita da wanda ake lallashin zukatan su da kuma iyanta wuyan bayi da kuma wanda ake bi bashi da kuma wurin daukaka addinin Allah da kuma matafiyi farillace da Allah ya farlanta daga gare shi kuma Allah masani ne me hikima (60)  
kuma nisabin zakka ana kaddara shi da 20%, kuma musulunci yana nufin kauda talauci ne daga al’umma da farlanta ta da kuma magance hatsarin sa wanda ke haifar da sata da kisa da ta’addanci ga mutunci, kuma a cikin ta akwai raya ruhin tamakekeniya ga al’umma a tsakanin musulmai, dan hakan na toshe bukatan mabukata da kuma wanda basa isa roko cikin talakawa da miskinai, bambancin ta da haraji shi ne, ita zakka musulme ne ke fitar da ita yana me farin cikin bada ita ba tare da tilastawa ko fin karfi ba, wanda ke tsaron sa ita ce ransa da tayi imani da wajabcin fitar da ita, kamar yadda sunan ta na nuna abun da e karkashin ta na tsarkake ran mawadaci da kuma tsaftace ta daga rowa da kuma mako da kuma dattin kwadayi, da kuma tsarkake zuciyar sa daga mugun san duniya da kuma nutsewa a cikin sha’awoyin ta wanda zai haifar masa da manta bukatun iyan uwan sa na talakawa da miskinai, Allah madaukaki yace: “duk wanda aka tsare daga rowar ransa yafi karfin ta to wadannan su ne masu babban rabo (9)” , kuma akwai tsarkake ran talakawa da miskinai daga kiyayya da hassada akan mawada, yayin da suka cewa suna fitar da abun da Allah ya wajabta akan su a cikin dukiyoyin su, kuma kulawa da su ta han yar basu dukiyar da kuma kyautatawa. Hakika nassoshi na shari’a sun zo suna masu tsoratarwa da hana zakka, Allah madaukaki na cewa: “kada wanda ke rowa da abun da Allah ya basu daga falalar sa suyi zatan cewa alkairi ne a gare su a’a sharri ne akan su za’a nada musu abunda sukayi rowa da shi ranar kiyama”
kuma annabi (SAW) yana cewa: ” babu wani me zinari ko azurfa wanda be bada zakkan su face ranar alkiyama sai an bude mai takaddu na wuta sai a tura shi a wutar jahannama dan ayi masa lalas da su a gefen jikin sa da fuskar sa da bayan sa, duk lokacin da sukayi sanyi sai a maida su zafi a wani yini wanda gwargwadon sa kamar shekaru dubu hamsin ne har sai Allah yayi hukunci a tsakanin bayi sai a nuna masa hanyar sa kodai wuta ko kuma aljanna”

4- rukuni na hudu: azumin watan ramadana:
Wata daya a cikin shekara musulmai ke yin azumi, zasu kame daga ci da sha da zuwa ma iyali, dan yiwa Allah da’a, tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana, kuma shi azumi ba wani abu ne da aka fara shi a musulunci ba, saboda fadar Allah madaukaki: “yaku wadanda sukayi imani an wajabta azumi akan ku kamar yadda aka wajabta shi akan wanda suka gabace ku dan ku sami tsoron Allah (183)”
Kuma ba wai abun nufi da azumi shi ne kame wa daga baben da ke karya shi ba kawai, a’a dole a kame daga ababen da ke karya shi na ma’ana kamar karya da gulma da annamimanci da yaudara da zamba da zancen da beda amfani da abun da yayi kama da hakan na munanan aiyuka, dan sanin cewa barin wadannan aiyukan munana wajibi ne akan dukkan musulmi a watan da ba na ramadana ba kuma wajibcin barin na kara karfi a cikin watan ramadan, sabida fadar sa (SAW), Allah madaukaki yace: “duk wanda be bar zancen zur ba da kuma aiki da shi to Allah baya bukatar yabar abincin sa da abun shan sa”
Kuma azumi jahadi ne tsakanin rai da abunda take so, yana hana musulmi munanan zantuka da aiyuka, Annabi (SAW) yana cewa, Allah madaukaki yace: “dukkan aiyukan dan adam nashi ne sai dai azumi wannan nawa ne kuma ni ne zanyi sakayya akan shi kuma azumi garkuwa ne idan dayan ku yana azumi to kada alfasha kuma kada yayi fushi idan wani ya zage shi ko kuma ya yake shi to yace ni ina azumi na rantse da wanda ran Muhammadu ke hannunsa warin bakin me azumi yafi kamshin almiski a wurin Allah me azumi nada farinciki guda biyu in yayi buda baki zai yi farin ciki kuma in ya hadu da ubangijin sa zaiyi farin ciki da azumin da yayi a duniya”
Kuma da azumi ne mutum ke iya gane bukatun iyan uwan shi wanda ba’a hore musu ba daga cikin talakawa na mabukata, sai yayi kokari wajen sauke hakkin su da kuma bincike halayen su da biyan bukatun su.

5- Rukuni na biyar: hajji:
Shi ne tafiya zuwa dakin Allah me alfarma dan yin wasu aiyuka na musamman a wasu wurare na musamman a wasu lokuta na musamman, kuma wannan rukunin wajibi ne akan dukkan musulmi baligi me hankali namiji da mace su yi shi sau daya a cikin rayuwar su, amma da sharadin samun iko na jiki da dukiya, duk wanda mara lafiya ne wanda ba’a tunanin warakar sa yadda bazaimiya yin hajji ba kuma shi mawadaci ne sai ya wakilta wanda zai yi mai, kuma wanda yake talaka ne shi bai da dukiyar da zata biya masa bukatun sa na wajibi, da kuma bukatun wanda yake daukar nauyin su, to hajji ba wajibi bane akan sa, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma Allah ya wajabta aikin hajji akan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa kuma duk wanda ya kafurce to lallai Allah mawadaci ne akan talikai (97)”  kuma hajji shi ne mafi girman abun da ke tattara musulmai, suna haduwa daga kowane wuri a wuri guda daya a lokaci na musamman suna rokon ubangiji guda daya suna sanye da tufafi iri daya suna yin inada iri daya, suna maimaita abu daya” labbaikallahumma labbaik, labbaika la sharika laka labbaik, innal hamda wanni’imata laka wal mulk laasharika lak” wato ma’ana” ya Allah munzo wannan wurin muna masu amsa kiran da kayi mana da kuma kwadayin samun yaddar ka, da kuma tabbatawar mu cewa kai kadai ne ka cancanta da bauta banda wanin ka, babu bambanci tsakanin me daraja da wamda be da daraja, haka nan babu banbanci tsakanin fari da baki da balarabe da wanda ba shi ba, dukkan su daya suke a wurin Allah babu banbanci a tsakanin su sai dai wurin tsoran Allah, kuma wannan ba komai bane sai dan karfafa iyan uwan taka tsakanin musulmai da hada kan su da burin su’

DAGA CIKIN ABABEN DA MUSULUNCI YA KEBANTA DA SHI NA KAYUTATAWA:
Duk da cewa addinin musulunci shi ne addinin karshe da yazo da Allah, to lallai zai zama yana da wasu kebantattun ababe na kyautatawa wanda ya kere wa sauran addinan da suka gabace shi, kuma zai zama da wadannan kebantattun abubuwan ya dace da kowane amani da kuma wuri har zuwa tashin alkiyama, kuma da wannan kyautatawa da kuma kebantattun abubuwa yana tabbatarwa dan adam rabauta da jin dadi a duniya da lahira.
Daga cikin wannan kebantattun ababe da kuma kyawawa akwai kamar haka:
1- lallai nassoshin sa sun zo karara suna masu nuni akan cewa addini a wurin Allah daya ne, kuma lallai Allah ya aiko annabawa sashin su na cika sashi tun daga annabi Nuhu har zuwa karshen su Annabi Muhammad (SAW), Annabi (SAW) yana cewa: “lallai misali na da kuma annabawan da suka zo kafin ni kamar mutum ne ya gina gida ya kawata shi kuma ya tsantsara shi sai dai ya barwurin bulo daya daga bangare daya, sai mutane suna zagayawa suna mamakin sa, sunacewa dama zaka sa wannan bulon da ka bari, sai Annabi yace, ni ne wannan bulon, ni ne cika maken Annabawa”
Sai dai duk da cewa Annabi Isa zai dawo a karshen zamani dan ya cika kasa da adalci kamar yadda aka cikata da zalunci da fajirci, sai dai bada sabon addini zai dawo ba, zai yi hukunci ne tsakanin mutane da musulunci wanda aka saukar wa Annabi Muhammad (SAW), saboda fadr manzan Allah (SAW: “alkiyama bazata tsayu ba har sai dan Maryam ya sauka a cikin ku, yana me hukunci me adalci, zai karya gumaka, zai kashe alade kuma zai sanya jiziya, kuma zai raba dukiya har zai zama babu mai amsa “
Dukkan Annabawan Allah da’awar su daya ce ita ce kira zuwa ga bautar Allah shi kadai da kuma tsarkake shi daga abokin taraiya, da kuma kamanceceniya da kuma tamka, da kuma kira a bauta masa kai tsaye da wurgar da dukkan iyan tsakiya tsakanin Allah da bayin sa, da kuma tsarkake zukatan mutane, da kuma fuskantar da su zuwa ga dukkan abu me kyau kuma zai dadada musu a duniya da lahira, Allah madaukaki yace: “allah ya shar’anta muku addini irin yadda yayi wanannabi Nuhu wasiya da kuma abun da mukayi wahayi zuwa gare ka da kuma abun da muka yiwa annabi Ibrahim wasiyya da shi da annabi Musa da annabi Isa cewa ku tsayar da addini kuma kada ku rarraba a cikin sa...”

2- Allah ya shfe abun da ya gabaci musulunc na addinaii da zuwansa, shi ne na karanshen su kuma cikon so, Allah be karbar bauta in bada shi ba, Allah madaukaki yace: “kuma mun saukar ma da littafi da gaskiya yana me gasgata abun da ya gabace shi na littattafi kuma yana me shafe su”
Kuma kasancewar addini na karshe sai Allah yayi alkawarin kare shi har zuwa karshen duniya, sabanin sauran addinan da suka gabaxe shi wanda Allah beyi alkawarin kare su ba, saboda su sun sauka ne dan amfain wani zamani, kuma dan wasu mutane, Allah madaukaki yace: “lallai mune muka saukar da alku’ani kuma lallai mu ne zamu kare shi (9) . Kuma wannan ke hukun ta cewa lallai manzan da aiko da musulunci Annabi Muhammad (SAW) shi ne karshen manzanni, babu wani manzo ko annabi da zai zo a bayan sa, Allah madaukaki yace: “annabi Muhammadu be zamo mahaifin daya daga cikin mazajen ku ba sai dai shi manzan Allah ne kuma cikamakin Annabawa”
Kuma wannan ba yana nufin rashin imani da gasgata annabawa da kuma littattafan da suka gabace shi bane, Annabi isa yan kammala addinin Aannnabi Musa ne, shi kuma Annabu Muhammad (SAW) yana kammala addinin Annabi Isa ne, da zuwan Annabi Muhammad ne aka cika annabawa da manzanni, kuma musulmi an umarce shu ne d a yin imani da dukkan littattafai da manzanni wanda suka gabaci she, duk wanda be yu imani da su ba ko kuma be yi imani da guda daya daga cikin su ba to ya kafurta kuma ya fita daga musulunci, Allah madaukaki yace: “lallai wadan da ke kafurce wa Allah da manzan sa kuma suke san raba tsakanin Allah da manzan sa kuma suke cewa munyi imani da wasu kuma mun kafurce wa wasu kuma suna son su riki wata hanya tsakanin haka (150) to wadannan su ne kafurai na gaskiya”

3- lallai addinin musulunci yafi addinan da suka gabace shi cika, shari’o’in da suka gaba ce shi sun kasance ne masu asula na ruhi wanda ke zance da rayuka kuma da yin kira ga tsarkake su, amma basu waiwayi al’amurran duniya ba da na rayuwa ta wurin tsari da fuskantarwa, sabanin musulunci wanda yazo dan kammala dukkan bangarorin rayuwa da kuma tsara su, sai ya shafi dukkan al’amurran addini da kuma duniya, Allah madaukaki yace: “a yau na cika muku addinin ku kuma na cika ni’ima ta a gare ku kuma na yadda da musulunci ne addinin ku “
Dan haka ne ya zama shi ne addinin karshe kuma mafificin su, Allah madaukki yace: “kun kasancde mafi alkairin al’umma wanda aka fito da su ga mutane kuna umarni da kyakkyawa kuma kuna hani daga mummuna kuma kuna imani da Allah da ace ahlul kitabi sun yi imani da ya fi musu alkairi daga cikin su akwai muminai amma mafi yawan su fasikai ne (110)”

4- lallai addinin musulunci addini ne na duk duniya an aiko shi ga mutane baki daya ba tugaciya acikin dukkan amani da wuri, ba’a saukar da shi dan wasu jinsi ba banda wasu, ko kuma wasu masu daraja ban da wasu, ko kuma wasu al’umma banda wasu, ko kuma dan wani zamani banda wani, shi addini ne wanda dukkan mutane daya ne a cikin sa, ba’a lura da kala ko yare ko wurin zama ko kuma tsatso ko wuri ko zamani, a’a shi ya ginu ne akan tushen aqida ta musamman ita ce wadda ke tattara su,
Duk wanda yayi imani da Allah ne abun bauta kuma musulunci ne addinin sa kuma annnabi Mhammadu (SAW) manzansa, to ya shiga karkashin tutar musulunci, Allah madaukaki yana cewa: “kuma bamu aiko ka ba face dan dukkan mutane kana me bushara da gargadi”  amma wanda suka gabata cikin annabawa, su ana aika su ne zuwa ga mutanen su ne kawai, Allah madaukaki yace: “hakika mun aika annabi Nuhu zwa ga mutanen sa”
Kuma Allah madaukaki yace: “kuma an aika zuwa ga a’dawa dan uwan su Annabi Hudu sai yace yaku mutane ku bauta wa Allah babu wani abun bauta koma bayan sa”
Kuma Allah madaukaki yace: “kuma mun aika zuwa ga samudawa dan uwan su Annabi Salihu sai yace ya ku mutane ku bauta wa Allah baku da wani abun bauta koma bayan sa” , kuma Allah madaukaki yace: “kuma Annabi Lud lokacin da yace wa mutanen sa” , kuma Allah madaukaki yace: “kuma mun aika zuwa madyana dan uwan su Annabi Shuaibu” , kuma Allah madaukaki yace: “sai muka aika da Annabi Musa a bayan su da a’yoyin mu zuwa ga fir’auna da jama’arsa” , kuma Allah madaukaki yace: “kuma lokacin da Annabi Isa dan Maryama yace ya ku bani isra’ila ni manzan Allah ne a gare ku ina me gasgata abun da ya gabace ni na attaura...”,
Kuma dan kasancewar musulunci addini na na duniya kuma da’awar sa ta game dukkan mutane a kowane lokaci da kowane wuri, sai aka umarci musulmai da isar da sako da bijiro da shi ga mutane, Allah madaukaki yace: “kuma hakannan muka sanya ku al’umma matsakaita dan ku zamo masu shaida akan mutane shi kumanzo ya zamo shaida akan ku “

5- addinin musulunci shari’ar sa da koyarwar sa daga ubangiji suke, kuma tabbatattu ne basa karbar canji da gurbatawa, ba gan adam bane ya kawo su wanda tawaya da kuskura ke iya auka masa, kuma yana tasirantuwa da abun da ke kewaye da shi na wayewa wanda ya gada da kuma wurin zaman sa, wannan shi ne abun da muke gani karara, sai muke ganin rashin tabbatuwar shari’o’i da tsare-tsare na dan adam, abun da ya dace da wannan mutanen bai dace da wannan mutanen ba, kuma abun da ya dace a wannan lokacin be dacewa a wani lokacin, dokoki da tsare-tsare a wurin iyan gurguzu be dacewa da irin tsarin iyan kashe mu raba, duk wanda ya samya dokoki da tsare tare to dole ne zai sanya su ne yadda zasu dace da abun da suke hasashe da inda suka fuskanta, bugu da kari akan tabbatuwarsu, za’a iya samun wani daga cikin masu kafa dokokin yafi wayewa da ilimi sama da wanda ya sa dokar farko sai yayi fito na fito da shi ko kuma yayi kari ko yayi ragi a ckin dokar farko, amma ita shari’ar musulunci, ita kamar yadda muka fada ne cewa daga Allah take, wanda ya kawo ta shi ne mahaliccin halittu baki dayan su, duniya da abun da ya dace da ita, kuma shi ke jujjuya al’amuran su, babu wani daga cikin mutane duk yadda matsayin shi ya kai ko kuma darajar shi da yake da hakkin fito na fito da Allah ko kuma ya canza wani abu cikin abun da Allah ya shar’an ta, ta hanyar kari ko ragi, saboda ita shari’ar musulunci tana kare hakkin kowa da kowa ne, Allah madaukaki yana cewa: “shin hukuncin jahiliyya suke so kuma babu wanda yafi Allah kyautata hukunci ga mutane masu yaqini (50)

6- adddinin musulunci addini ne me karbar ci gaba, wannan na sanya shi ya zama ya dace da kowane zamani da wuri, addinin musulunci yazo da asulla da tushe na bai daya, da kuma ka’idoji gamammu tabbattatu wanda basa canzawa a canzawar zamani ko wuri a ciin aqida da ibada, lamar imani da allah da adadin raka’o’inta da lokutan ta, da zakka da abunda za’a fitar da wanda za’a fitar a cikin sa, da azumi da lokacin yin sa, da hajji da siffar sa da lokacin sa da haddi.....har zuwa karshe, duk abunda ke faruwa kuma sabuntuwa na ababen bukatuwa to za’a bijiro da su ne ga alkur’ani, duk abunda ya dace sai ayi aiki da shi, abunda kuma ya saba sai a barshi a bincika cikin ingantattun ruwayoyi daga manzan Allah (SAW) in an samu sai ayi ruko da shi kumar wanda bashi ba, in kuma ba’a samu ba sai ayi bincike cikin ijtihadin malamai na Alllah a kowane zamani da wuri dan abun da zai tabbatar da maslaha ta baki daya, kuma wanda zai dace da kudirin zamani da halayan jama’arsu, kuma hakan zai zama ne ta hanyar bincike ne a alkur’ani da sunna, da bijiro da dukkan sabon abu akan ka’idoji na shari’a dukkan su wanda aka cirosu daga alkur’ani da sunna, misali, ka’idar (asali acikin abubuwa shi ne halacci), da ka’idar (kiyaye maslahohi), da kuma ka’idar (sauki da dauke tsanani), da kuma ka’idar (tunkude cutarwa), da ka’idar (toshe kafofin barna) da ka’idar (larurori suna halatta ababen da aka hana), da ka’idar (larurori ana ana duba su ne gwargwadan su), da ka’idar (tunkude cutarwa shi ake gabatarwa akan janyo amfani), da ka’idar (yin mafi saukin barna ciki abu biyu) da kuma (cutarwa ba’a tunkude ta da cutarwa), da ka’idar (hakuri akan cutarwar mutum daya dan tunkude cutarwar dukkan mutane) har dai zuwa karsh wadannan ka’idojin, ba wai ana nufin san rai ba da aka ce ijtihadin malamai, da kuma bibiyan sanrai, a’a ana nufin kokarin samun abun da amfanin sa zai dawo ga dan adam da alkhairi da amfanarwa ba tare da fito na fito da ko cin karo da nassin shari’a ba, kuma hakan ba dan komai ba sai dan musulunci ya tafi da ko wane irn zamani kuma ya dace da ababen da ko wane al’umma ke bukata.

7- adddinin musulunci ba bambanci ko wariyar launin fata a cikin sa ta fuskar dokokin sa da tsare tsaren sa, kowa daya ne, ba bambancin talaka da me kudi, ko me daraja da wanda beda ita, ko kuma shugaba da wanda shugabanta, ko kuma fari da baki, dukkan wurin dabbaka shari’a daya suke, akwai lokacin da kuraishawa al’amarin matarnan makzumiya ya damesu wacce tayi sata, sai suka ce waye zaiyi wa manzan Allah magana dan a kyaleta, sai sukace ai babu wanda zai iya hakan sai Usama dan Zaid masoyin manzan Allah (SAW), sai Usama yaje yayi wa annabi magana, sai manzan Allah (SAW) yace: “yanzu kazo ne dan kayi ceto a cikin haddi daga cikin haddojin Allah? Sai annabi ya mike yayi huduba, sai yace: ya ku mutane lallai abun da ya halaka wadanda suka gabace ku shi ne in me daraja yayi sata a cikin su sai su kyale shi in kuma me rauni yayi sata sai su sayar mai da haddi, ina rantsuwa da Allah da ace fatima zatayi sata to wallahi sai na datse hannun ta “

8- addinin musulunci inda ake ciro shi na asali ne, kuma nassoshin sa kubutattu ne daga tawaya da kari da cazawa da birkitawa, inda ake ciro- koyo- shari’ar musulunci su ne:
A) alkur’ani me girma. B) sunnar annabi me daraja.
Alkur’ani tun lokacin da ya sauka ga Annabi Muhammad (SAW) har zuwa wannan lokacin babu abun da ya canza cikin haruffan sa da a’yoyin sa, haka nan kuma babu ragi ko kari, hakika Annabi (SAW) ya zabi wasu marubutan wahayi cikin sahabbai masu daraja kamar Aliyu da Mu’awiya da Ubaiyu bun ka’ab da Zaid bun thabit, duk lokacin da wata a’ya ta sauka sai ya umarce su da su rubuta ta, kuma ya nuna musu inda za’a sata a cikin sura, sai aka kiyaye alkur’ani ta wajen rubutu, kuma aka kiyaye shi ta hanyar haddace shi a cikin kirazan mazaje, kuma musulmai hakika suna nuna kwadayin su akan alku’ani sosai, sai ya zama suna rige-rige wurin koyan sa da koyar da shi, dan neman saman alkairin da Annabi ya bada labari a cikin fadar sa: “mafi alkairin ku shi ne wanda ya koyi alkur’ani kuma ya koyar da shi”
Kuma suna bada rayukan su da dukiyoyin su wurin yimasa hidima da kula da shi da kare shi, sai musulmai suka gaje shi al’umma bayan al’umma, dan saboda tsaron shi wani abu ne wanda suke bautar Allah da shi, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda ya karanta harafi daya daga cikin littafin Allah to yana da lada daya, ita kuma za’a nunkata sau goma, ba wai ina nufin alif laam miim harafi daya kenan ba, a’a’ sai dai alif harafi ne, kuma laamun harafi ne, kuma miimun harafi ne”
-Amma ita kuma sunnar annabi me daraja, ita ce wuri na biyu da ake ciro addini, kuma tana bayani ne ga alkur’ani me girma, tana fassra hukunce-hukunce masu yawa na alkur’ani, to itama an kare ta daga wargi da karerayi da yayeyayen wani abu wanda baya cikinta, bayan tsaron da Allah yayi mata ta hanyar adalan mutane masu gaskiya, sun kebe kansu kuma sun bada rayukan su dan kula da hadisan Annabi (SAW), da kuma karanta hanyoyin sa da mutuun din sada kuma ingancin sa da raunin sa, da kuma halayen maruwaitan sa da martabobin su ta fuskan jarhi da ta’adili, sai suka tace dukkan hadisan da aka ruwaito daga Annabi (SAW), basu bar komai ba sai abun da ya tabbata daga Annabi (SAW), ta haka ne sai ta iso har wurin mu tana tatacciya kubutacciya daga hadisan karya, duk wanda ke san sani hanyar da aka tsare sunna da ita to ya koma littattafan masana ilimin hadisi wanda aka rubuta dan hidima ga hadisan Annabi (SAW), dan ya tabbatar da cewa babu kokwanto cikin abunda ya iso gare mu na hadisan Annabi (SAW) cewa maganar sa ce, kuma ya san irin kokarin da akayi wurin hidima ga sunnar annabi.

9- addinin musulunci yana daidaita tsakanin mutane baki daya a wurin asalin halittan su da rainon su, mazansu da matan su, farin su da bakin su, balaraben su da wanda ba balarabe ba, farkon wanda Allah ya fara halitta cikin mutane shi ne Annabi Adam, kuma shi ne baban mutane baki dayan su, sai ya halicci matar sa Hauwa’u ita ce mamar mutane, sai ya sanya iyaiya daga gare su, dan haka wurin asalin halitta mutane dukkan su daya ne, Allah madaukaki yace: “yaku mutane kuji tsoran ubangijin ku wanda ya halicce ku daga rai guda daya kuma ya halicci matar ta daga gare ta kuma ya yada maza da mata da yawa a tsakanin su kuma ku ji tsoran Allah wanda kuke rokon sa kuma ku kiyaye zumunci “
Kuma Annabi (SAW) yana cewa: “lallai Allah madaukaki ya tafiyar muku da jijida kai irin na jahiliyya, da alfahari da iyaye, mumini me tsoran Allah ne kuma fajiri me tabewa ne kuma mutane iyaiyan Adamu ne shi kuma Adam an halicce shi daga turbaya “
Duk wanda yake ban kasa a yanzu da kuma wanda zai zo nan gaba to cikin zurriyyar annabi Adam ne da kuma tsatson sa, farkon su suna kan addini daya ne da kuma yare daya, sai dai bayan sunyi yawa sai suka rarraba a ban kasa kuma suka warwatsu a wurare dam-daban, sai wannan warwatsuwa ya haifar da bambamce-banbancen yaruka da launuka da kuma banbancin dabi’u, kuma wannan abu ne na dole hakan zai kasance saboda yanayin wurin zama, wannan sai ya haifar da banbanci wurin hanyar tunanin su, da kuma yanayin rayuwar su, da kuma banbancin aqidu, Allah madaukaki yace: “kuma mutane basu kasance ba face al’umma guda daya sai suka rarraba ba dan wata kalma da ta gabata daga ubangijin ka ba da anyi hukunci tsakanin su cikin abun da suke sabani a cikin sa (19)
Karantarwar musulunci na dora mutane ne a ma’auni guda daya ne ba tare da kula da banbancin jinsi ko launi ko yare ko wurin zama ba, dukkan su a wurin Allah daya ne, banbancin su kawai gwargwadan nisanci da kusancin mutum ne da dabbaqa shari’ar Allah, Allah madaukaki yace: “yaku mutane lallai mu mun halicce ku ne daga na miji da mace kuma mun sanya ku al’ummu da kabilu dan kusan juna lallai mafi darajar ku a wurin Allah shi ne wanda ya fiku jin tsoron Allah”
Gini akan wannan daidaito wanda musulunci ya tabbatar da shi, dukkan mutane a mahangan shari’a duk daya suke ta fuskar iyanci me lunzami da lunzaman addini wanda ke nesanta su daga iyanci irin na dabbobi, akan wannan iyancin ne za’a bawa kowa daman abubuwa kamar haka:
A) iyancin tunani da kuma baiyana ra’ayi: musulunci yana kwadaitar da mabiyan sa akan fadan gaskiya da kuma baiyana ra’ayoyin su da tunanin su-ra’ayoyi na gari masu kyau- kuma kada suji tsoron zargin me zargi wurin baiyana gaskiya, Annabi (SAW) yana cewa: “mafi falalar jihadi shi ne fadin kalma ta adalci a wurin mugun sarki ko kuma mugun shugaba” , sahabbai suna rige-rige wurin dabbaqa wannan tushe, an ruwaito cewa wani mutum yace wa Umar dan Khaddabi sarkin muminai: “kaji tsoran Allah ya kai sarkin muminai, sai wani ya hana shi, yace masa: kana cewa sarkin muminai yaji tsoran Allah?, sai Umar yace masa: “ka rabuda shi ya fada domin babu alkairi a cikin ku in dai bakwai fada mana gaskiya irin haka kuma babu alheri a cikin mu in har bamu karbi nasihar ku ba” , kuma ya zo a wani wuri na daban cewa Umar Allah ya kara masa yadda lokacin yana sarkin muminai ya taba haduwa da wani mutum sai yace masa: me ka aikata? Sai yace: Aliyu da zaidu sun yi hukunci da kaza, sai yace: da ni ne da zanyi hukunci ne da kaza, sai mutumin yace: to me ya hana ka yin hakan alhali komai na hannun ka? Sai yace: da na so in maida ka zuwa ga littafin Allah da sunnar manzan sa (SAW) da na aikata, sai dai ni na maida ka zuwa ga ra’ayi na, kuma ra’ayi abu ne wanda kowa nada shi, abunda Aliyu da Zaid babu cin karo da juna”
b) kowa yana da iyancin yin mallaka da neman halal: Allah madaukaki yace: “kada kuyi fatan abun da Allah ya fifita sashin ku akan wani sashi da shi mazaje suna da kaso daga abun da suka nema kuma mata ma suna da kaso daga abun da nema”
c) kowa nada iyancin koyan ilimi da koyar da shi: musulunci ya kirga shi daga cikin wajibai, Annabi (SAW) yana cewa: “neman ilimiwajibi ne akan dukkan musulmi”
d) kuma kowa na da damar amfanuwa da dukkan abun da Allah ya halitta a wannan duniyar na alkairai daidai da tsarin shari’a, Allah madaukaki yace: “shi ne wanda ya sanya muku kasa a shimfide to kuyi tafiya a kanta kuma kuci daga arzikin Allah kuma a gare shi tashi yake (15)
e) kuma kowa na da dma ya zama shugaba a cikin al’umma: amma da sharadin cancanta da kuma iko da kuma dacewa, kuma musulunci ya kiraga jingina akl’amari zuwa ga wanda basu cancanta ba a matsayin abu ne na wulakan ta amana wanda hakan na nuni akan kusantowar halakar wannan duniyar da kuma tashin alkiyama, Annabi (SAW) yana cewa: “idan aka tozarta amana to ku jira tashin kiyama” sai aka ce: yaya ne tuzartar da ita ya manzan Allah? Sai yace: “idan aka bada wani aiki ga wanda be cancanta ba to ku jira tashin alkiyama”

10- addinin musulinci babu wasu shuwagabanni na musamman wanda aikin su shi ne kula da ruhi, kamar irin yadda sauran addinai ke jingina hakan ga masu addini, dan kuwa musulunci ya zo sai ya rusa dukkan abunda zai zama tsaka-tsaki ga bawa da ubangijin sa, sai ya aibanta mushirikai dan sun riki iyan tsakiya a wurin bauta, Allah ya fada yana me hikaitowa daga gare su: “ku saurara adini tatacce na Allah kuma duk wanda suka riki wasu masoya koma bayan sa suna cewa ne ba bauta musu mukeyi ba kawai mun rike su ne dan su kusantar da mu zuwa ga Allah kusantarwa “
Kuma Allah ya baiyana hakikanin wannan iyan tsakiyan da cewa basa iya amfanarwa ko kuma cutarwa kuma basu iya amfanar da su da komai, suma halitta ne irin su, Allah madaukaki yace: “lallai wadannan da kuke roko koma bayan Allah suma bayi ne irin ku to ku rokesu su amsa muku mu gani in kun kasance masu gaskiya (194)” , sai musulunci ya tabbatar da tushe na alaka ta kai tsaye tsakanin Allah da bayin sa, wacce take kafe akan imani da Allah da kuma komawa zuwa gare shi shi kadai dan neman biyan bukatu, da kuma neman gafara da taimako a ko wane wuri kuma a kowane hali, Allah madaukaki na cewa: “duk wanda ya aikata mummuna ko kuma ya zalunci kasan sa sai ya nemi gafarar Allah to zai samu Allah me gafara ne me jin kai (110)” , a musulunci babu wasu mazaje wanda keda alhakin halattawa ko haramtawa kuma suke gafara, kuma suke daukar kansu kamar wasu wakilai ne na Allah ga bayin sa, suna shar’anta musu kuma fuskantar da akidun su, kuma sune gafarta musu, kuma suna shigarda wana suke so aljanna kuma suna haramtawa wanda suka so, dan hakkin shar’antawa na Allah ne shi kadai, Annanbi(SAW) yana cewa cikin tafsirin fadar Allah madaukaki: “sun riki manyan malaman su da masu bautar su ababen bauta koma bayan Allah”  sai yace: “a’a ba wai bautan su sukeyi ba sai dai su sun kasance ne idan suka halatta musu wani abu sai mabiyan su halattaci idan kuma suka haramta musu wani abu sai su kuma mabiyan su haramta shi”

11- addinin musulunci addini ne na shawara acikindukkan al’amuran addini da na duniya na ciki da waje, Allah kadaukaki yace: “kuma da wadan a suka amsawa ubangijin su kuma suka tsaida sallah kuma al’amarin su shawara ne a tsakanin su kuma daga abun da muka azurta su suna ciyarwa (38)
Kuma ita shawara abun nema ne a shari’ar musulunci, dan haka ne manzan Allah yayi umarni da dabbaka ta a aikace, Allah madaukaki yace: “da rahamar ubangiji ce ka zama me sauki a gare su da ka zama me zafi me kaushin zuciya to da sun watse sun barka to kayi musu afuwa kuma ka nema musu gafara kuma ka shawarce su cikin al’amura “  da shwara ne ake cim ma gaskiya kuma ake samun mafi dacewar abunda aka fi kauna na halaye, yayin da musulmai suka kasance suna dabbaka wannan al’amari a cikin dukkan al’amuran su na addini da kuma na duniya a farkaon musulunci, sai al’amuran su suka kasance a mike, kuma halaiyan su a can kololuwa, amma yayin da suka kauce suka bar wannan asalin, sai suka kai in da suka kai yau ta fuskar koma baya cikin al’amuran addinin su da kuma duniyar su,

12- addinin musulunci ya sanya wasu hakkoki tsakanin bayi duk banbance-banbancen matsayin su, dan hadin kai da kaunar juna ya wanzu a cikin su, kuma suce amfanin ababen da addini yazo da su, kuma al’amuran su na duniya su tsayu da kyau, iyaye suna da hakki, iya iya suna da hakki, dangi nada hakki, makwabta ma na da hakki kuma abokai ma nada hakki....., Allah madaukaki yace: “ku bautawa Allah kuma kada kuyi taraiya da shi da komai kuma iyae ku kyautata musu, kuma ku kyautata wa makusanta da marayu da miskinai da makwabci na kusa da makwanci na gefe da aboki na gefe da matafiyi da kuma abunda hannayen ku suka mallaka lallai Alah baya san duk wanda ya kasance me takama me yawan alfahari (36)”, kuma Annabi (SAW) yana cewa: “kada kuyi wa juna hassada kuma kada kuyi wa juna mugunta kuma kada kuyi gaba da juna kuma kada ku juya wa juna baya kuma kada sahi yayi viniki akan cinikin sahi kuma ku kasance bayin Allah iyan uwan juna musulmi dan uwan musulmi ne baya zaluntar shi kuma baya tozarta shi kuma baya wulakan ta shi, tsoran Allah a nan yake sai Annabi ya nuna zuciyar sa har sau uku, ya isa mutum girman sharri ya wulakanta dan’uwan sa musulmi, dukkan musulmi akan musulmi haramun ne jinin sa da dukiyar sa da mutuncin sa” , kuma Annabi (SAW) yana cewa: “imanin dayan ku baya ciki har sai ya so wa dan uwan sa abun da yake so wa kansa”
Har makiyan musulunci suma suna da hakki, abu Azeez dan’uwan Mus’ab bun Umair yana cewa, na fada cikin fursuna ranar yakin badar, sai Annabi (SAW) yace: “ina muku wasiya ta alkairi game da fursuna” na kasance cikin jama’ar ansarawa, sun kasance in sun kawo abinci sai su ci dabino kawai, ni kuma sai su bani burodi, saboda wasiyyar da Annabi (SAW) yayi musu” , kai har ma ya wuce haka, dan ya baiwa dabbobi hakki kuma ya tsare musu shi, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda ya kashe tsuntsu dan wasa kawai zai zo wurin Allah yace ya ubangiji wane ne ya kashe ni dan wasa kawai ban dan ya amfana ba “
Kuma Annabi (SAW) yace: “lallai mafi girman zunubai a wurin Allah shi ne mutumin da zai auri wata mata yayi da ya biya bukatar sa daga gare ta sai ya sake ta kuma ya gudu da sadakin ta, da kuma mutumin da yasa wani aiki sai ya gudu da hakkin sa, da wanda ke kashe dabba dan wasa kawai” (assilsilatu assahihatu),
Kuma an ruwaito daga dan umar Allah ya kara masa yadda, cewa lalai shi ya wuce wasu mata sa na kuraishawa sun daure wane tsuntsu suna jifar sa, sun sanya wa me tsuntsun dukkan kibiyar da suka jefa amma ta kuskure a matsayin kudin tsuntsun sa, yayin da suka ga Abdullahi dan Umar sai suka watse, sai Dan Umar yace: waye ne ya aikata haka, Allah ya tsine wa wanda ya aikata wannan, lalli manzanAlllah (SAW) ya tsine wa duk wanda ya sa abu me rai yana koyan harbi akan sa” , kuma Annabi (SAW) yana cewa lakacin da ya wuce wani rakumi sai yaga cikin sa ya hade da fatar sa saboda yinwa;” kuji tsoran Allah game da wadannan dabbobin, ku hausu suna lafiya kuma ku ci naman su suna lafiya”
Musulunci ya tabbatar da jama’a akan mutun daya da kuma hakkin mutum daya akan jama’a, mutum daya na aiki dan maslahar jama’a suma jama’a suna aiki dan maslahar mutum daya, Annabi (SAW) yana cewa: “mumini ga mumini kamar gini ne sashe na karfafa sashe sai ya hada tsakanin yatsun sa”
Kuma idan aka samu cin kari tsakanin maslahar mutum daya da kuma maslaha ta al’umma ana gabatar da maslahar al’umma ne akan maslahar mutum daya, kamar misali, rusa gidan da ya karkace zai rush, dan tsoran kar ha ruso akan masu wucewa, ko kuma zabtara sa dan yin hanya dan amfanin kowa- amma bayan an biya shi-.

13- addinin musulunci addini ne na tausayi da jin kai, yayi kira dan watsi da tsanani da rashin tausayi a cikin koyarwar sa, Annabi (SAW) yana cewa: “masu tausayi Allah me tausayi zai ji tausayin su kuji tausayin wanda ke kasa sai wanda ke sama shima yaji tausayin ku” , kuma musulunci be takaita da’awarsa akan tausayawa mutane kawai ba, a’a hakan ya game har da ma dabbobi, saboda su ne wata mata ta shiga wuta, Annabi (SAW) yana cewa: “an azabtar da wata mata saboda mage ta daure ta har sai da ta mutu, sai ta shiga wuta saboda ita, bata ciyarda ita ba kuma ita bata shayar da ita ba kawai ta daure ta kuma ita bata kyale ta ba ta je ta ci kwari daga kasa “ , kuma ya sanya tausayin wadannan dabbobin sababi ne na gafarta zunubai da kuma shiga aljanna, Annabi (SAW) yana cewa: “kwai lokacin da wani mutum yana tafiya sai kishirwa ta bame shi sai ya samu wata rijiya a kan hanya sai ya shiga cikinta ya sha ruwa sai ya fito kawai sai ga wani kare yana lalllaga yana cin kasar da ke gefen rijiyar saboda kishi, sai mutumin yace: hakika irin yadda kishi ya kama ni shima wannan karen ya kamashi haka, sai ya koma cikin rijiyar ya ciko takalmin sa da ruwa ya shayar da wannan karen, sai Allah ya gode masa kuma ya gafarta masa, sai sahabbai suka ce: ya manzan Allah, shin dama zamu iya samun lada game da dabbobi? Ai Annabi yace: eh, akwai lada in aka kyautatawa dukkan abu me danyen hanta “ ,
idan wannan ya zama shi ne tausayin musulunci ga dabbobi to me kake tunani game da mutum wanda Allah ya fifita shi akan dukkan halittu kuma ya karrama shi, Allah madaukaki yace: “hakika mun karrama dan Adam kuma mun rike shi akan tudu da teku kuma mun azurta su daga dadadan abubuwa kuma mun fiifita su akn dayawa daga cikin abunda muka halitta fifitawa (70)”

14- addinin musulunci babu kebance kai dan bauta kawai da kuma barin duniya baki dayan ta da kore ababe masu dadi wanda Allah ya halitta dan bayin sa kuma ya halatta su, Annabi (SAW) yana cewa: “kada ku tsanan ta wa kan ku sai Allah ya tsanan ta muku, domin kuwa wasu mutane sun tsananta wa kawunan su sai Allah ya tsananta musu ga ragowar su can a wuraren bautar kiristoci da gidaje ((da kuma rahabaniyanci wanda suka kirkire shi wanda bamu wajabta shi akan su ba))..” , kuma Annabi (SAW) yana cewa: “kashedin ku da wuce iyaka a addini dan abunda ya halakar da wadan da suka gabace ku shi ne wuce iyaka a addini” , kuma Annabi (SAW) yana cewa: “lallai Allah yana san ya ga alamar ni’imar sa a wurin bawan sa” .
Kuma hakanan musulunci ba addini bane wanda ya fuskanci duniya kawai da nutsewa a cikin ababen sh’awar ta da jin dadin ta ba tare da iyaka ba, a’a shi addini na na tsakatsaki wanda ke hada tsakanin addini da duniya, kuma ya sanya kowannen dayan su yana cika dayan, to baya fifita daya akan dayan, kuma hakika yayi umurni da aunawa tsakanin ruhi da gangan jiki, sai ya umurci musulmi lokacin da ya nutse cikin al’amuran dunuya sai ya tuna da bukatun sa na ruhi, ta hanyar yin abun da Allah ya wajabta masa na ibadu, Allah madaukaki yace: “ya ku wadanda suka yi imani ida aka kira sallah a ranar juma’a to kuyi sauri zuwa ambatan Allah kuma kubar kasuwanci wannan shi ne mafi alkairi agare ku in kun kasance kuna sani (9) , kuma ya nema daga gare shi yayin da ya nutse cikin ibada to ya tuna da bukatun sa na rayuwa, na kasuwanci da neman arziki, Allah madaukaki yace: “kuma idan aka idar da salla to ku watsu a ban kasa kuma ku nema daga falalar Allah” , kuma musulinci ya yabe wanda ya hada tsakanin wadannan siffofin guda biyu, sai Allah madaukaki yace: “wasu mazaje se su wanda kasuwanci ko siye da siyarwa baya hana su ambatan Allah da tsaida sallah da bada zakkah suna jin tsoran wata rana wacce zukata da idanu ke jujjuyawa a cikinta (37)”  
Kuma hakika musulunci yazo da wani tsari wanda ke tsarewa ruhi da jiki da hankali hakkin su daidai da shari’ar Allah wacce babu wuce iyaka ko akaci a cikin ta, musulmi kamar yadda ake so ya kula da ransa da kuma yi mata hisabi akn aiyukan ta da dukkan abunda ke bullowa ta bangarenta, dan yin aiki da fadar Allah madaukaki: “duk wanda yayi aiki gwargwadan kawar zarra na alkairi to zai ganshi (7) kuma duk wanda yayi aiki gwargwadan kwayar zarra na sharri to zai ganshi (8)” , kuma bai kamata ba yayi wa kansa kwauro na ni’imar da Allah yayi na abunda ya halatta masa na abinci da abin sha da tufafi da aure, dan aiki da abun da Allah yace: “kace waye ya haramta kawa wacce Allah ya fitar ga bayin sa da kuma ababe masu dadi na arziki “ , kuma musulunci be haramta wani abu ba sai dai in ya kasance me muni ne, me cutarwa ga dan adam a hankalinsa ko jikin sa ko dukiyar sa ko kuma al’ummar sa, domin shi ran dan adam a mahangar musulunci, Allah ya halicce ta kuma ya maye ta a ban kasa dan bautar sa da kuma dabbaka shari’ar sa, babu me hakkin halakata ko wofintar da ita, kuma ya halitta ma wannan ran jiki cikakke wanda ya dace dan ita ran ta samu damar sauke nauyin da Allah ya dora mata na bauta ta hanyar wannan gangan jikin da kuma hakkoki da wajibai da kuma raya kasa, Allah madaukaki ya ce: “hakika mun halicci mutum a mafi kyawon tsayuwa (4)” , saboda haka ne Allah yayi umarni da tsare wannan jikin da kuma kula da shi gwargwada tsarin shari’a, wannan kuwa ta hanyoui kamar haka:
a) tsarki: Allah madaukaki yace: lallai Allah yana san masu tuba kuma yana san masu tsarki(222)” , sai ya sa alwala sharadi ne na ingancin sallah wacce musulmi ke yi sau biyar a yini da dare, Annanbi (SAW) yace: “ba’a karbar sallah sai da tsarki kuma ba’a karbar sadaka daga haram”
kamar yadda ya wajabta wanka da ruwa bayan janaba, saboda fadar sa madaukaki: “kuma in kun kasance masu janaba sai kuyi tsarki “ , kuma ya sa wanka daga cikin sunnoni masu karfi na wasu daga cikin aiyukan bauta, kamar sallar juma’a da idi guda biyu da hajji da umra.
b) ze wanke hannaye kafin cin abinci: an samo hadisi daga Aisha Allah ya kara mata yadda tace: Annabi (SAW ya kasance idn zai yi bacci kuma yana da janaba sai yayi alwala, kuma in zai ci abinci ko ya sha ruwa sai ya wanke hannaye sannan sai yaci ko ya sha “
- da kulawa da tsaftar hakora da kuma baki, ta hanyar kwadaitarwa akan yin asuwaki, saboda fadar manzan Allah (SAW): “badan kar in tsananta wa al’umma ta ba da na umarce su da yin asuwaki yayin kowace sallah “
- da gusar da dukkan abun da yake tattara datti da kuma tsaftace shi, Annabi (SAW) yana cewa: “fitira guda biyar ce, yin kaciya da cire gashin mara da cire gashin hammata da rage gashin baki da yanke kumba”
c) ci da sha daga dukkan abunda yake me dadi, Allah madaukaki yace: “ya ku wadanda sukayi imani ku ci daga abubuwa masu dadi wanda muka azurta ku da su kuma ku goda wa Allah in kun kasance shi kuke bauta ma (172)” , kuma ya togace ni’ima me dadi da rashin almubazzaranci wanda cutarwar sa bata boyuwa ga jiki, Allah madaukaki yace: “ku ci kuma ku sha amma kada kuyi almubazzaranci domin lallai shi Allah baya san masu almubazzaranci (31) .
kuma hakika Annanbi (SAW) ya baiyana hanyar da ta dace wurin cin abinci hakika Annabi (SAW) ya baiyana ta da fadin sa: “dan adam be taba cika wani abu ba mafi sharii irin cikin sa wasu iyan lomomi sun isa dan adam dan su tada bayan sa to in kuma ya zama dole sai yaci sosai to ya raba cikin sa kashi uku kashi daya dan abinci kashi daya dan abin shan sa kashi daya dan numfashin sa “
d) ya haramta cin dukkan abunda yake me muni ne hakan da dukkan abun sha, kamar mushe da jini da naman alade da giya da kayan maye da taba, hakan kuwa badan komai ba sai dan kiyaye lafiyan wannan jikin, Allah madaukaki yace: “hakika abun da Allah ya haramta a gare ku shi ne mushe da jini da naman alade da abunda aka ambaci sunan wanin Allah wurin yankashi duk wanda ya shiga halin tsanani ba wai ya wuce iyaka bane ko kuma dan ta’ada bane sai yaci to babu zunubi akan sa lallai Allah me gafara ne me jin kai (173)” , kuma Allah madaukaki yana cewa: “ya ku wadanda sukayi imani lallai giya da caca da gumaka da kibau datti ne daga aikin shaidan to ku nisance shi dan ku samu rabauta (90) lallai shaidan yana so ne ya kunna kiyayya da gaba a tsakanin ku a cikin lamarin giya da caca kuma ya kange ku daga ambatan Allah da kuma sallah to shin ko ku kun hanu (91)”
e) yin wasanni na motsa jiki masu amfani kamar kokowa, hakika Annabi (SAW) yayi kokkowa da sahabin sa Rukana, sai Annabi (SAW) ya kada shi” , da kuma yin tsere, an ruwaito daga Aisha Allahya kara mata yadda, cewa wani lokaci ta kasance suna tafiya tare da Annabi (SAW), sai tace: “munyi tsere da Annabi a kafa sai na tsere masa, lokacin da nayi kiba sai muka kara tsere sai ya tsere mun, sai yace: “wannan na rama wancan wucewar da kikayi mun” , da kuma yin iyo a ruwa da harbi da hawa dawakai, hakika ya zo a cikin asarai daga Abdullai dan Umar Allah ya kara masa yadda ya ce: ku koya wa yaran ku harbi da iya iyo a ruwa da hawan dawakai.
f) yiwa jiki maga ni in rashin lafiya ya same shi, Annabi (SAW) yana cewa: “kowace cuta tanada magani idan magani ya dace da cutar sai a sanmu waraka”
g) kuma ya umarce shi da yin ibada wacce Allah ya umarce shi da ita, wacce ita ce abincin ruhi ga dukkan musulmi daga damuwa wanda ke tasiri ga jiki sai jiki ya kamu da rashin lafiya, Allah madaukaki yace: “wanda sukayi imani kuma zukatan su na natsuwa da ambatan Allah ku saurara da ambatan Allah ne zukata ke samun natsuwa (28)”
kuma musulunci ya lissafa rashin kula da jiki da bashi abun da ya dace da shi na abinci da hutu da kuma hana shi biyan bukatar sa ta saduwa ta hanyar halal cikin haramtattun ababen da aka hana, an ruwaito daga Anas dan Malik Allah ya kara masa yadda yace: wasu mutane uku sun zo gidan Annabi (SAW) suna tambaya game da ibadar Annabi, yayin da aka basu labari kmar sun raina ibadar Annabi, sai sukace ya zamu hada kanmu da Annabi (SAW) ai shi Allah ya gafarta masa abunda ya gabata na laifin sa da wanda ma baiyi ba, sai dayan su yace, to ni zanta sallar dare har abada, sai dayan yace, ni kuma zanta azumi har abada ba hutawa, sai dayan ma yace, ni kuma zan nisanci mata bazanyi aure ba har abada, sai Annabi (SAW) ya zo yace shin ku ne kuka ce kaza da kaza, to ni wallahi na fikku tsoran Allah kuma na fiku takawa, amma ni ina azumi kuma in huta, kuma ina sallar dare in huta, kuma auren mata, to duk wanda ya kauda kai daga sunna ta to baya tare da ni”

15- addinin musulunci addini ne na ilimi da sani, ya kwadaitar akan ilimi, Allah madaukaki yace: “shin wanda suka sani zasuyi daidai da wanda basu sani ba” , kuma ya zargi jahilci da ma’abotan sa, Allah madaukaki yace: “ina neman tsarin Allah kar in zama cikin jahilai (67)”
sai ya sanya cikin ilimi akwai anda faradu ainin ne akan dukkan musulmi, shi ne dukkan abun da musulmi bai wadatuwa da daga gare shi na al’amuran addinin sa da rayuwar sa, kuma daga cikin ilimi akwai wanda faradu kifaya ne, in wasu suka iya to laifi ya fadi daga wuyan sauran, kuma ubangijin mu be umurci Annabin sa da neman karen komai ba sai ilimi, Allah madaukaki ya ce: “kuma kace ya ubangiji ka kara mini ilimi (144)” , kuma musulunci ya girmama ilimi da kuma malamai, Annabi (SAW) yace: “duk wanda baya girmama babban mu kuma baya tausin karamin mu kuma be san hakkinmalamin mu ba to baya tare da mu” , kuma ya sanya wa malami wani matsayi me girma da kuma daraja madaukakiya, Annabi (SAW) yace: “falalar malami akan me bauta kamar falala ta ce akan na kasanku”
kuma dan musulunci ya yda ilimi kuma ya kwadaitar wurin koyan shi sai ya lissafa tafiya neman ilimi da koyar da shi cikin aikin jihadi wanda mutum ke samun lada kuma hanya ta aljannah, Annabi (SAW) yace: “duk wanda ya fita dan neman ilimi to yana hanyar Allah ne har sai ya dawo “ , kuma Annai yace: “duk wanda ya bi wata hanya yana neman ilimi a cikin ta to Allah ze saukake masa hanya aljannah”
kuma ba wai kawai ilim shari’a ne musulunci ya kwadaitar akan ba, a’a ya kwadaitar ma akn neman ilim duniya da koyan su kuma ya sa su cikin ibada wacce ake ba mutum lada akan ta-su ne ilimomin da muka ce su faradu kifaya ne- saboda mutum na da bukatar wannan ilimomi, Allah madaukaki yace: “ashe baka gani ba cewa Allah ya saukar da ruwa daga sama sai muka fitar da kayan marmari masu banbancin kala da shi kuma daga cikin duwatsu kawai hanyoyi farare da jajaye wanda kalar su ta banbanta da kuma kuma wasu duwatsu masu tsanani duhu (27) kuma daga cikin mutane da dabbobi suma kalar su sun banbanta to lallai kawai masu jin tsoran Allah daga cikin bayin sa su ne malamai lallai Allah mabuwayi ne me gafara (28)” , a cikin wannan ayar akwai kira dan tunani da kuma lafiyayyen nazari wanda ke kaiwa ga ga tabbatar da samuwar mahalicci ga wadannan abubuwa, duma kira ga amfanuwa da abun da Allah ya halitta a wannan duniyar, babu kokwanto cewa malamai a wannan ayar ba wai ana nufin malaman addini kadai bane, a’a harda ma malaman da suke a sauran ilimomi, wanda suke iya binciko sirrorin abun da Allah ya halitta a wannan duniyar,misali akan haka, baza a san yadda giragizai suke ba da kuma saukar ruwan sama sai da ilim kimiyya, da fasaha, kuma baza’a san yadda za’a shuka bishiyoyi da tsirai ba sa ta hanyar sanin ilimim noma, kuma ba’a gane banbanci kala a duwatsu da kasa sai ta hanyar ilimin sanin kasa-giology-, kuma ba’a sanin halaiyar mutane da banbance-banbancen jinsin susai ta hanyar ilimin halaiya....da sauran su.

16- addinin musulunci yana barin kowa ya kula da kanshi, wannan ne ke sanya musulimi ke kokarin neman yaddar Allah a dukkan zantukansa da aiyukan sa, da kuma nisantar abun da ke kawo fushin Allah, sabo da yasan Allah na kula da shi kuma ya san duk abun da yake yi, sai yayi abun da aka umurce shi kuma ya nisanta daga abun da aka hane shi, misali lokacin da musulmi ya ki yin sata, to yakiyi ne dan jin tsoran Allah ba dan tsoran dan sanda ba, haka abun yake a cikin sauran laifukan, karantar musulunci na rainon musulmi ne akan cewa sirrin sa da baiyyanen sa duk daya ne, Allah madaukaki yace: “kuma in ma ka baiyana magana to shi yana sanin sirri da ma abun da yafi boyuwa (7)”
Annabi (SAW) yana cewa game da kyautatawa: “shi ne ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa in kai baka ganin sa to shi yana ganin ka”
Kuma musulunci ya sanya tushe game kula da kai:
Na farko: imani da samuwar abun bauta shi kadaime cikken iko a zatin sa da siffofin sa, masanin dukkan abun da ke gudana a wannan duniyar, ba abun da ke faruwa sai abun da yaso, Allah madaukaki yace: “yana sanin abun da ke shiga kasa da abun da ke fita daga gare ta da abun da ke sauka daga sama da abun da ke komawa cikin ta kuma shi yana tare da ku duk inda kuke kuma Allah me gani ne ga dukkan abun da kuke aikatawa (4)” , ai ilimin sa ma ya wuce ababen da ake iya gani ko tabawa ya kai har zuwa sanin abun da zuciya ke boyewa da waswasin rai, Allah madaukaki yace: “kuma hakika mun halicci mutum kuma muna sanin abun da ransa ke saka masa kuma munfi kusa da shi fiye da jijiyar wuyan sa (16)”
Na biyu: imani da tashi daga kabari da kuma bada sakamako, Allah madaukaki yace: “wadanda suka kafurta sun raya cewa baza’a tashe su ba kace musu na rantse da ubangiji na wallahi za’a tashe ku sannan za’a baku labarin abun da kuka aikata kuma wannan me sauki ne a wurin Allah (7)”
Na uku: imani da yin hisabi, Allah madaukaki yace: “wata rai bata daukan zunubin wata” { suratul an’am:(16) }, kowane mutum za’a yi mai hisabi a gaban Allah akan dukkan abun da zai zo da shi na aiyuka da zantuka, kananan su da manyan su, alherin su da sharrin su, sai a saka masa da kyawawa akan alheri kuma a saka masa da zunubi akan munanan aiyuka, Allah madaukaki yace: “duk wanda yayi aiki gwargwadan kwayan zarra na alheri to zai gan sa (7) kuma duk wanda yayi aiki gwargwadan kwayar zarra na sharri to zai gan sa (*)”
Na hudu: gabatar da da’a ga Allah da manzansa da kuma sansu fiye da san kowa koma waye.

17- addinin musulunci ana nunka lada a cikin sa zuwa niki da yawa, amma zunubai ba’a sakiya da su sai irin su, Allah madaukaki yana cewa: “duk wanda yazo da kyakkyawa to yana da goma irin sa kuma duk wanda yazo da mummuna to baza a saka mai ba sai da irin sa” , kuma yana bada lada akan niyya ta kwarai koda aiki bai biyo bayanta ba, da zai yi niyyar aikin kwarai sai bai samu damar yi ba to za’a bashi lada daya, abunm ma kan wuce haka wani lokaci, da mutum zai yi niyyar yin mummunan aiki sai ya ki aikatawa dan tsoran hukuncin Allah, to Allah zai mai sakamako da lada saboda ya bar abun da yayi niyyar aikatawa dan tsoran Allah, Annabi (SAW) yana cewa: “Allah madaukaki yana cewa: “iadn bawa na yayi yinkurin aikata laifi to kar ku rubuta masa zunubi har sai ya aikata, to in ya aikata ku rubuta masa zunubi daya, in kuma ya bari saboda ni to ku rubuta masa lada daya, in kuma yayi nufin aiki me kyau sai be aikata ba to ku rubuta masa lada daya in kuma ya aikata to ku rubuta masa lada goma har zuwa lada ninki dari bakwai” , kai hatta ma abun da rai ke so na sh’awa na halal a musulunci sukan juya zuwa ibada idan anyi niyya me kyau da kyakkyawan manufa, ci da sha idan mutum yayi niyyar kula da jikin sa da su da kuma kula da karfin sa dan ya nemi arziki da kuma sauke abunda Allah ya dora mai na ibada, da kuma ciyar da iyalan sa da yaran sa da wanda yake kula dasu, to wannan aiki nasa ibada ne za’a bashi ladan sa, Annabi (SAW) yana cewa: “idan mutum ya ciyar da iyalin sa yna me neman lada a wurin Allah to sadaka ne a gare shi “  
Kuma haka ma idan musulmi y biya bukatar shi ta hanyar halal da iyalinsa, idan yayi niyyar kamewa da katnge kansa da iyalin sa daga afkawa cikin haramun, to wannan aikin nasa ibada ne zai samu lada akan sa, Annabi (SAW) yana cewa: “kuma jima’in dayanku sadaka ne, sai suka ce, ya manzan Allah: ashe dayan mu zai iyan bukatar sa kuma ya samu lada? Sai Annabi yace: ya kukue gani in ya sanya ta a haramun shin zai samu zunubi?, to haka in ya sanya ta ta hanyar halal zai samu lada “
Kai duk wani aiki da musulmi zai yi in ya kautata niyya a cikin sa to zai samu lada, Annabi (SAW) yana vewa: “kowane musulmi zai iya sada, sai suka ce: in bai samu ba fa? Sai Annabi yace: sai yaje yayi kwadago da hannayen sa dan ya amfani kansa kuma yayi sadaka, sai sukace: to in bazai iya ba fa? Sai yace: to ya taimaki wanda ke cikin tsananin bukata, sai suka ce: to in bai aikata ba fa? Sai yace: to yayi umarni da aikin alheri, ko yace, da kyakkyawa, sai sukace: in bai aikata hakan ba fa? Sai yace: to ya kame daga sharri dan hakan ma sadaka ne a gare shi”

18- addinin musulunci ana juya zunuban masu zunubida suka tuba masu gaskiya cikin tuban da sukayi masu nadama akan abun da sukayi na zunabai masu yin niyya me karfi akan baza su kara komawa ga zunubi ba bayan sun tuba, zuwa lada, Allah madaukaki yace: “kuma da wadanda basa kiran wani abun bauta daban tare da Allah kuma basa kashe ran da Allah ya haramta a kashe da da hakki kuma basa zina to duk wanda ya aikat wannan zai hadu da uznubi (68) za’a ninka mai azaba ranar alkiyama kuma zai dauwama a cikinta yana wulakantacce (69) sai dai wanda suka tuba kuma sukayi imani kuma suka aikata aiyuka na kwarai to wadannan Allah zai juya munanan aiyukan su zuwa kyawawa kumaAllah ya kasance me fafara ne ma jin kai (70)”
Wannan abun da ya shafi hakkin Allah kenan, amma abunda ya shafi hakkin mutane to dole sai an maida wa masu hakki hakkokin su da neman afuwar su da yafiyar su na abun da ya aikata musu na hakkinsu.
Kuma shari’ar musulunci tayi magana da kwakwalwar me zunubi kuma ta magance abun da ke damun sa a rai wanda yasa shi cikin rudu hakan kuwa ta hanyar bude kofar tuba a gare shi daga zunubin sa, Allah madaukaki yace: “kace ya ku bayi na wanda suka wuce iyaka a kawunan su kada ku debe tsammani daga rahamar Allah lallai Allah yana gafarta zunubai baki daya “ , kuma ta saukake al’amarin tuba a gare shikuma ta sanya shi lamari me sauki babu wahala a cikin sa kuma babu takura, Allah madaukaki yace: “kuma duk wanda ya aikata mummunan aiki ko kuma ya zalunci kansa sai ya nemi gafarar Allah to zai samu Allah me gafara ne me jin kai (110)”
Wannan abunda ya shafe musulumai kenan, amma wanda ba musulmai ba cikin wanda ke shiga musulunci, to su za’a basu lada ninki biyu, saboda imanin su da annabin su, da kuma imanin su da Annabi muhammad (SAW), Allah madaukaki yace: “wnda muka basu littafi kafin sa su suna masu imani da shi (52) kuma idan aka ranta musu shi sai suce munyi imani da shi lallai shi gaskiya ne daga ubangijin mu lallai mu kafin zuwan shi musulmai ne (53) to wadannan a’a basu ladan su sau biyu saboda hakurin da sukayi kuma za’a tunkude musu munanan aiyukan da kyawawan aiuikan su kuma suna ciyar wa daga abun da muka azurta su (54)” , kari akan haka shi ne lallai Allah zai yafe musu dkkan zunuban su da kusakuran su wanda suka yi kafin su musulunta, saboda fadar Annabi (SAW) ga Amru ibnul Aas lokacin da yayi masa mubaya’a akan musulunci kuma ya shardanta sai an gafarta masa zunubai”.....ashe baka sani ba cewa musulunci yana rushe dukkan abun da akayi kafin sa”

19- addinin musulunci na tabbatar wa mabiyansa ci gaban samun lada a gare su bayan mutuwan su, hakan kuwa ta hanyar abunda suka bari na aikin kwarai, Annabi (SAW) yana cewa: “idan mutum ya mutu to aikin sa ya yanke saidai abu uku, sai dai sadaka me gudana ko kuma ilimi wanda ake amfanuwa da shi ko kuma yaro na kwarai wanda ke masa addu’a” , kuma Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda yayi kira zuwa shiriya to yana da lada irin ladan wanda suka bishi ba’a tauye komai daga ladansu kuma duk wanda yayi kira zuwa bata to yanada zunubi iri zunubin wanda suka bishi ba tare da a rage komaii daga zunuban su ba”  , wannan zai sa musulmi yayi kokari sosai wurin gyaruwar al’ummar sa ta hanyar aikin alkairi da taimaka masa da kira zuwz gare shi da yakar barna da tsoratarwa daga gare ta.

20- addinin musulunci ya girmam hankali da tunani kuma yayi kira ga amfani da su, Allah madaukaki yace: “lallai a cikin sammai da kasa akwai a’yoyi ga muminai (3) kuma a cikin halittar ku da abun da yake yadawa na dabbobi akwai ‘ayoyi ga mutane masu yakini (4) da kuma sabawar dare da rana da kuma abun da Allah ya saukar daga sama na arziki sai ya raya kasa da shi bayan mutuwar ta da kuma jujjuyawar iska akwai a’yoyi ga mutane masu hankali (5)” , kuma hakan nan da yawa daga cikin a’yoyin alkur’ani suke maga da hankali kuma suke kwadaitarwa akan sa” shin baza su hankalta ba, shin baza suyi tunani ba, sunbazasuyi hangen nesa ba, shin baza su sani ba....da sauran su”, akan cewa musulunci ya iyakance aikin hankali, dole aikin sa ya zama cikin abun da ake iya gani da tabawa, amma abun da ya shafi gaibu  wanda kafofin dan adam basa iya kaiwa, to hankali bai da mashiga anan, dan yin aiki da hankali a nan wurin zai zama wahalarwa ne da kallafa ma rai abun da beda amfani a gare.
Kuma daga cikin girmamawar da musulunci yayi wa hankali, shi ne ya iyanta shi daga abi yarima asha kida, sai ya zargi duk wanda yake kwaikwayo ba tare da ilimi ba, kuma yabi abunda na gaban sa suke kai ba tare da ilimi ko shiriya ba, kuma ya zarge shi akan wannan aiki na shi, Allah madaukaki yace: “kuma idan aka ce musu kubi abun da Allah ya saukar sai suce mu zamu bi abun da iyayen mu ke kai ne shin koda iyayen su basa gane komai kuma basa kan shiriya (170)”

21- addinin musulunci addini ne na lafiyayyar fidira, baya cin karo da dabi’ar dan adam wacce Allah ya halitta masa, kuma wannan fitirar haka Allah ya halicci mutane dukkan su akan ta, Allah madaukaki yace: “tsarin halitta na Allah wanda ya halicci mutane akan sa babu canji ga halittar Allah”, sai dai wannan tsari na halitta, abunda ke kewaye da ita kan mata tasiri, sai su karkatar da ita daga ingantacciyar hanyar ta sai ta karkace, Annabi (SAW) yana cewa: “babu wani wanda za’a haifa face ana haihuwar sa ne akan tsarin musulunci to iyayen sa su ne suke yahudantar da shi ko kiristantar da shi ko su majusantar da shi” , kuma shi addini ne me hanya mikakkiya, Allah madaukaki yace: “kace lallai ni ubangiji na ya shiryar da ni zuwa hanya madaidaiciya addini mikakke tafarkin Annabi Ibarahim me karkata zuwa addinin gaskiya kuma shi be kasance cikin mushirikai ba (161)” , babu abun da hankali bya dauka a cikin musulunci, kai lafiyayyun hankula ma suna shaida gaskiya da dacewa da amfanin abun musulunci yazo da shi, dukkan umurnin sa da hanehanan sa adalci ne babu zalunci acikin su, be umarni da wani abu ba sai in akwai amfani tatacce ko kuma mafi rinjaye acikin sa, kuma be hani daga wani abu sai in tsantsan sharri ne ko kuma citarwar sa tafi amfanin sa yawa, kuma wannan be boyuwa ga dukkan wanda yayi tadabburin a’yoyin alkur’ani da hadisan Annabi (SAW) ingantattu.

22- addinin musulunci ya ya iyanta rai daga bautar wanin Allah kowaye, annabi ne manzo ko kuma mala’ika makusanci, wannan kuwa da nufin kafa imani a ran musulmi cewa babu me amfanarwa ko cutarwa sai Allah, babu wanda zai iya amfanarwa ko cutarwa koma waye shi sai fa abun da Allah ya so kuma ya kaddara shi, Allah madaukaki yace: “kuma suka riki ababen bauta koma bayan sa wanda basa halittan komai sai dai su a halitta su kuma basa mallakar cutarwa ko amfanarwa ga kansu kuma basa mallakar mutuwa ko rayuwa ko tashi daga kabari (3)” .
dukkan al’amarin na Allah ne, Allah madukaki yace: “idan Alah ya daura maka cuta babu me warkar da kai sai shi kuma idan ya nufe ka da alheri to babu wanda zai iya maida falalar sa yana samu wanda ya so da shi”
Annabi (SAW) duk da shi ne mafi girman daraja da mafi girman matsayi a gun Allah, abun da ke hawa kan wanin sa yana hawa kan sa daga mutane, to ya kake tunan wanda ba shi ba, Allah madaukaki yace: “: kace musu bana mallakar amfanarwa ko cutarwa ga kaina sai abun da Allah ya so da ace na san gaibu da yawaita aikin alkairi kuma da wani mummunan abu be same ni ba kawai ni me gargadi ne da bushara ga mutane masu imani (188)” , kuma haka nan musulunci ya iyanta ran dan adm daga damuwa da tsoro da rashin kwanciyar hankali ta hanyar magance ababen da ke kawo su, misali: idan tsoran na mutuwa ne, to Allah madaukaki yana cewa: “babu wata rai da zata mutu sai da izinin Allah wannan abu ne rubutacce” , kuma ko yaya mutum yayi kokarin guje mata to bazai iya ba zai tadda tana jiran shi, Allah madaukaki yace: “kace musu to lallai mutawar da kuke guje mata to hakika zata same ku”
In kuma tsoran na talauci ne da fatara, to Allah madaukaki yana cewa: “babu wata dabba a ban kasa facea a wurin Allah arzikin ta yake kuma yana sanin matabbatar ta da ma’ajinta dukkan wannan yana cikin littafi mabaiyani (6)”
Kuma idan tsoran rashin lafiya ne da musibu, to Allah madaukaki yana cewa: “babu wata musiba da zata faru a ban kasa ko kuma a kawunan ku face tana cikin littafi a rubuce tun kafun a halicce ta lallai wannan me sauki ne a wurin Allah (22) dan kada kuyi bakin cikin abun da ya wuce ku kuma kada ku dinga farin ciki da abun da ya baku kuma Allah baya kaunar dukkan me takama me alfahari (23)”
Kuma idan tsoran halittu ne, to Annabi (SAW) yana cewa: “ya kai yaro lallai ni zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah zai kiyaye ka, ka kiyaye Allah zaka same shi a gaban ka, idan zakai roko to ka roki Allah, kuma idan zaka nemi taimako to ka nema daga Allah, kuma ka sani lallai al’umma da zasu taru akan su amfanar da kai to baza su iya amfanarka da komai ba sai da abunda Allah ya rubuta maka shi, kuma da zasu taru akan su cutar da kai to baza su iya cutar da kai da komai ba sai dai abun da Allah ya rubuta shi a kanka, an dauke alkaluma kuma takaddun sun bushe”

23- addinin musulunci addini na tsakatsaki a al’auran addini da rayuwa, Alllah madaukaki yace: “kuma hakanan muka sanya ku al’umma ta tsakiya dan ku kasance shaida akan mutane kuma Manzo ya zama me shaida kan ku” , kuma shi addini ne na sauki da saukakawa,Annabi (SAW) yana cewa: “allah be aikoni me tsanani ba ko me tsanantawa sai dai ya aiko ni ne me karantarwa me saukakawa”  
Karantarwar sa suna kwadaitarwa aknan saukakawa, kuma suna umarni da shi, Annabi (SAW) yana cewa: “kuyi bushara kada ku dinga korewa kuma ku dinga sauki kada ku dinga tsanani”
Kuma shi addini ne na sauki da yafiya da rangwame, an ruwaio daga Aisha Allah ya kara mata yadda tace: wasu yahudawa sun zo wurin Annabi (SAW) sai suka ce masa: -samu alaika-mutuwa akan ka, Aisha tace sai na gano su, sai nace musu: kuma samu ta tabbata a kanku da kuma tsinuwa, sai Annabi (SAW) yace: ya ke Aisha kiyi rangwame, lallai Allah me tausayi ne yana san tausayawa a ciin dukkan al’amari, sai nace: bakaji abunda sukace bane ya manzan Allah? sai Annabi (SAW) yace: nima ai nace kuma haka”
Kuma shi addini ne me san alkhairi ga mutane, Annabi (SAW) yana cewa: “wanda Allah yafi so a cikin mutane shi ne wanda yafi amfanar da su, kuma mafi soyuwan aiki a wurin Allah shi ne farincikin da zaka shigar da shi a zuciyar musulmi ko kuma ya yaye mai damuwa ko kuma ka biya masa bashi ko kuma ka kore masa yinwa, kuma intafi tare da dan’uwana musulmi dan biya masa bukata shi nafi so akan inje masallaci inyi i’itikafi na wata daya, duk wnda ya kame fushinsa Allah zai rufa asirin sa, duk wanda ya hadiye fushin sa duk da inda yaso zai iya fitar da shi, to Allah zai cika ziciyar shi da yadda ranar alkiyama duk wanda ya tafi tare da dan’uwan sa musulmi dan bukatar sa ya tsaya har bukatar ta biya to Allah zai tabbatar da dugadugan sa ranar da dugadugai ke zamewa, kuma lallai mummunar dabi’a na bata aiki kamar yadda kullu ke bata zuma”
Kuma shi addini ne na adalci, ba addinin zafi bane da wahala, Allah madaukaki yace: “Allah be daura ma wata rai sai abunda zata iya tana da ladan abunda ta aikata kuma abun da tayi na zunubi na kanta”
Umarnin musulunci sun ginu ne akan wannan tsarin, Annabi (SAW) yan cewa: “duk abun da na hane ku daga gareshi to ku hanu kuma duk abun da na umarce ku da yi to kuyi shi gwargwadan iko lallai abunda ya halakar da wadanda ke kafin ku shi ne yawan tambayon su da kuma sabawar su ga annabawansu” , kuma mafi alkhairin dalili akan haka shi ne labarin wannan sahabin da yazo wurin Annabi (SAW), sai yace ya manzan Allah: na halaka, sai annabi yace: me ya halaka ka? Sai yace: na sadu da iyalina kuma ina azumi, sai Annabi (SAW) yace: “kana da baiwa sai ka iyantata? Sai yace:a’a, sai annabi yace: to zaka iya yin azumin wata biyu a jere?, sai yace:a’a, sai annabi yace: to zaka iya ciyar da miskinai sittin? Sai yace:a’a, sai Annabi (SAW) yayi shiru, ana zaune cikin haka kawai sai aka kawo ma Annabi (SAW) wani baho cike da dabino, sai Annabi yace: ina wannan me tambayar? Sai yace: gani, sai Annabi yace: karbi wannan kaje kayi sadaka da shi, sai mutumin yace: shin akwai wanda ya fini talauci ne ya manzan Allah? na rantse da Allah babu wani gida a wannan unguwar wanda sukafi ni talauci, sai Annabi (SAW) yayi dariya har saida hakoran sa na gaba suka baiyana, sannan yace: je ka ciyar da iyalinka shi “ , dukkan iabdu da umarni a musulinci sun dace da iyawa ta dan adm, bata daura masa abunda baai iya ba, duk da kusani cewa wadannan umurni da ibadu da rukunnani sukan fadi a wasu halaye, misali:
-daga cikin wajiban sallah akwai tsayuwa in da iko, to da mutum zai kasa yinta a tsaye sai yayi ta a zaune, in kuma ya kasa yi a zaune sai yayi ta a kishingide, in kuma ya kasa sai yayi da ishara-nuni-.
- faduwar zakka akan wanda be mallaki nisabi ba, sai dai ma a bashi in talaka ne shi mabukaci.
- faduwar azumi akan mara lafiyan da ba’a tunanin warakar sa, da me ciki da me haila da me jinin haihuwa, duk da nann ba shi ne wurin bayanin su ba filla-filla.
- faduwar hajji akn wanda be da hali na dukiya ko kuma jiki, duk da tafsilin da ke cikin hakan, nan ba wurin bayanin su bane, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma Allah ya wajabta aikin hajji akan mutane amma ga wanda ya samu ikon zuwa”
- idan mutum yaji tsoran halaka, to zai iya cin ko shan abun da Allah ya haramta na mushe ko jini ko naman alade ko kuma shan giya - gwargwadan abun da zai tunkude masa halaka-, Allah madaukaki yace: “duk wanda ya shiga tsanani ba me nufin barna ba ko dan ta’adda to babu laifi akan sa” , wani daga cikin masu nazari yace game da fassarar wannan ayar: shi musulunci aqidah ce me kallan mutum a matsayin sa na mutum, ba dabba ba ko mala’ika ko shaidani, ta tabbatar da shi kamar yadda yake, da dukkan abunda ke tattare da shi na rauni da karfi, kuma tana kallan shi a matsayin abu guda daya wanda ya hadu daga jiki me bukatu kalakala da hankali me kaddara abubuwa da rai me shauki iri-iri, kuma tana wajabta masa abunda zai iya ne, kuma tana lura da daidaita tsakanin dora masa bauta da kuma iyawar sa ba tare da tsanani ba ko kuntatawa.

24- addinin musulunci yana wajabta wa dukkan musulmi yin imani da dukkan manzannin da Allah ya turo, misali Annabi Isa da Musa da Ibrahim da wasunsu amincin Allah ya tabbata a gare su, kuma yana umarni da girmama su da kuma san su, Allah madaukaki yace: “lallai wadanda suka kafurce wa Allah da manzansa kuma suke so su raba tsakanin Allah da manzan sa kuma suke cewa munyi imani da wasu kuma mun kafurce ma wasu.....”, kuma musulunci na hani daga zagin aqidar wasu da abun da suke addini da shi, Allah madaukaki yace: “kada ku zagi wadan da suke bautan wani abu koma bayan Allah sai suma su zagi Allah saboda kiyayya ba tare da wani ilimi ba”
Kuma yana umarni da tattaunawa da jayayya da wadanda suka saba amma da hikima da taushi, Allah madaukaki yace: “kayi kira zuwa ga hanyar ubangijin ka da hikima da wa’azi me kyau kuma kayi jayayya da su da abun da yafi kyau lallai ubangijin ka shi yafi kowa sanin wanda ya bace daga hanyar sa kuma shi ne yafi sanin shiryayyu (125)”
Yana kira zuwa tattauna wa me ma’ana wadda zata hana kai akn tafarkin Allah, Allah madaukaki yana cewa: kace yaku ma’abota littafi ku taho zuwa ga wata kalma sacce tak e daidaita tsakanin mu da ku ita ce kada mu bautawa kowa sai Allah kuma kada mu hada shi da wani abu kuma daga sashin mu su riki wasu shashin ababen bauta koma bayan Allah to in sun juya baya to kuce musu ku shaida lallai mu musulmai ne (64)

25- addinin musulunci addini ne na zaman lafiya cikke da dukkan abunda wannan kalmar ke kunshe da shi na ma’ana, a cikin al’ummar musulmai ne, saboda fadar Annabi (SAW): “ashe bazan baku labarin mumini ba, shi ne wanda mutane suka aminta da shi a dukiyar su da rayukan su, kuma musulmi shi ne wanda mutane suka kubuta daga harshen sa da hannun sa kuma me jihadi shi ne wanda ya tursasa ransa akan yiwa Allah da’a kuma me hijira shi ne wanda ya kauracewa kusakurai da zunubai” , ko kuma a matakin duniya wanda ke tsaye akan ginin alaka ta kauna wacce ka ginuwa akan zaman lafiya da tabbatuwa da kuma rashin ta’addanci a al’ummar musulmi ko wanda ba su ba, musamman ma irin mutanen da basa hana yada addini, Allah madaukaki yace: “Allah be hane ku game da wanda basa yakar ku a addini kuma basu kore ku ba daga gidajen ku kuma ku kyautata musu kuma kuyi musu adalci lallai Allah yana san masu adalci (8)” , kuma saboda kula da zaman lafiya da ci gan ta musulunci ya umarci mabiyansa da tunkude ta’addanci da yin fada da zalunci, Allah madaukaki yana cewa: “duk wanda yayi ta’addanci akan ku to kuma ku rama da irin misalin ta’addancin da yayi muku” , kuma saboda kwadayin musulunci aka zaman lafiya ya umarci mabiyan sa da su amince da sulhu a lokacin yaki kuma su kame daga yaki in makiya sun nemi haka, Allah madaukaki yana cewa: “kuma idan suka idan suka karkata zuwa ga sulhu to kuma sai ku karkata dan sulhu kuma ku dogara ga Allah lallai shi ne me ji masani (61)” , dudda kwadayin musulunci akan zaman lafiya sai dai be yadda ba mabiyan sa su kaskantar da kansu dan samun zaman lafiya kuma aci mutuncin su, a’a ya umarce su su kiyaye zaman lafiya tare da kiyaye izzar su kar su bari a wulakanta su ko aci mutuncin su, Allah madaukaki yana cewa: “kada kuyi rauni ka fara kira ga zman lafiya alhali kune a sama kuma Allah na tare da ku kuma ba zai tozarta aikin ku ba (35)”

26- addinin musulunci babu tilasta wani akan sai ya shige shi, a’a dole shigar shi ciki ta zama daga yadda dayayi ne da shi ba tre da tilstawa ba, tilastawa ba hanyar hada musulunci bace da karantarwar sa, saboda fadar Allah madaukaki: “babu tilastawa a addini hakika shiriya ta baiyana daga bata”
Idan da’awa ta isa ga mutane kuma akyi musu bayani to suna da iyancin zaban aqidar da suke so, Allah madaukaki yana cewa: “duk wanda yaso sai yayi imani kuma duk wanda yaso sai ya kafurta” , saboda imani da shiriya na hannun Allah, Allah madaukaki yace: “da ubangijin ka ya ga dama da yasa wanda ke ban kasa sun yi imani dukkan su to kai ne zaka dinga tilasta mutane har sai sunyi imani(99)”
Kuma daga cikin ababe masu kyau na musulunci shi ne ya bar wanda ya saba mai cikin ahlul kitabi suyi al’amuran addinin su, saboda fadar Abubakar assidiq Allah ya kara masa yadda: “....kuma da sannu zaku wuce wasu mutane sun kebe kawunan su a wuraren bautan su to ku rabu da su da abun da suke yi” , kuma ya bar musu iyanci wurin abinci da abun sha da abun da halal ne a addinin su na abinci da abinsha, ba’a kashe aldun su kuma ba’a zubar da zubar da giyar su, kuma bunda ya shafi harkar zaman takewa kamar aure da saki da mu’amalar dukiya to suna da iyancin dabbaka abun da suka kudirce kuma suke addini da shi daidai da sharudda da dokoki wanda musulunci ya baiyana, nan ba wurin su bane.

27- addinin musulunci ya iyanta bayi kuma ya shar’anta iyantasu, kuma yayi alkawarin lada da sakamako masu girma ga wanda ya iyanta bawa, kuma ya sanya hakan sababi ne na shiga aljanna, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda ya iyanta bawa to Allah zai iyan dukkan gabban sa daga wuta dai dai da gabobin bawan kai har farjin bawan da farjin sa” , kuma musulunci ya haramta dukkan hanyoyin bautarwa, bai halatta wata hanya ba sai da guda daya, ita ce hanyar kama mutum a yaki da sharadin shugaban musulmai shi ne zai ce sun zama bayi, dudda cewa musulunci ya kuntata kofofin bautarwa ta hanyar sanya shi ta kofa daya kawai, to kuma a gefe daya ya fadada hanyoyin iyantarwa ta hanyar sanya iyanta bayi kaffara ne na wasu daga cikin zunubai wanda musulmi ya aikata, misali:
-kisan kuskure, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma duk wanda ya kashe mumini da kuskure to ya iyanta wuyan bayi muminai da kuma diyya da zai bada zuwa ga dangin sa sai dai in sun yafe in kuma ya kasance daga mutane ne abokan gabar ku kuma shi mumini ne to a iyanta wuyan bawa mumini”
- kaffarar rantsuwa, saboda fadar sa madaukaki: “Allah baya kamaku cikin yasshiyar rantsuwar ku saidai yana kama ku ne da abun da kuka kudurce na rantsuwa to kaffarar sa ita ce ciyar da miskinai goma daga abunda kuke ciyar da iyalan ku na tsakiya ko kuma yi musu tufafi ko kuma iyanta wuyan bawa” (suratul ma’ida, (89)).
- zihari, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma wadanda sukeyi wa matan su zihari sai su dawo daga abun da suka fada to sai sun iyanta baiwa kafin su taba su”
- jima’i a ramdan, an ruwaito daga Abu huraira Allah ya kara masa yadda yace, lallai wani mutum ya auka wa iyalin saa watan ramadan sai ya tambayi manzan Allah (SAW) akan haka, sai Annabi yace:’ shin kana da bawa? Sai yace:a’a, to zaka iya azumin wata biyu a jere? Sai yace:a’a sai yace: to ka ciyar da miskinai sittin”.
- ya sanya shi kaffara ne na ta’addanci ga bayi, saboda fadar Annabi (SAW): “duk wanda ya mari wani bawa ko kuma ya dake shi to kaffarar sa shi ne ya iyanta shi”
Kuma daga cikin karfafan abun da ke nuna kwadayin musulunci ga iyanta bayi:
Umurnin da yayi na yin yarjejeniya dasu, shi ne yarjejeniya tsakanin me gida da bawansa,za’a iyan ta shi amma da wani wani kudi da zai ba me gidansa wanda sukeyi ittifaki tsakanin su, kuma wasu malamai  sun wajabta yin yarjejeniya idan har bawa ya nemi hakan, suna kafa hujja akan haka da fadar Allah madaukaki: “kuma wadanda suke son a kulla yarjejeniya cikin bayinku to ku rubuta yarjejenya da su in kun san alkhairi a tattare da su kuma ku basu daga dukiyar Allah wanda ya baku “ , kuma ya sanya iyanta bayi daya daga cikin wurare da ake bada zakka, shi ne iyanta bayi da fursuonin yaki, saboda fadar Allah madaukaki: “lallai zakka ta talakawa ce da miskinai da masu aiki dan ita da wanda ake rarrashin zukatan su da iyanta wuyan bayi da masu bashi da wurin daukaka hanyar Allah da matafiyi akan hanya wannan farilla ne daga wurin Allah kuma Allah masani ne me hikima (60)”  

28- addinin musulunci ya kewaye dukkan bangarorin rayuwa saboda fadin shi, ya zo da tsare-tsare da shri’o’i a bangaren mu’amala da yake yake da aure da tattalin arziki da siyasa da ibadu....wanda al’umma ta gari ke rayuwa akai wanda dukkan mutane sun kasa zuwa da irin sa, kuma gwargwadan nisa daga wannan dokoki da tsare-tsare gwargwadan ci baya da za’a amu, Allah madaukaki yace: “kuma mun saukar ma da littafi bani ne ga dukkan komai da shiriya da rahama da bushara ga musulmai (89)”  hakika musulunci ya tsara alakar mutum da ubangijinsa da kuma jama’ar sa da kuma duniyar da ke kewaye da shi ta mutane ko yanayi, babu abun da lafiyayar fidira ke ki a musulunci ko kuma lafiyayyun hankula su kore shi, kuma daga cikin abun da ke nuni akan wannan gamewa, kulawar sa da halaiya da ababe na gefe wanda ke da alaka da rayuwar mutane, kamar ladubban biyan bukata, da abun da ya kamata musulmi ya aikata kafin biyn bukar da lokacin biyan bukatar da kuma bayan biyan bukatar, Abdurrahman dan Zaid Allah yayi masa rahama yana cewa: ance wa Salman: Annabin ku ya koya muku komai yar biya bukata, sai salmanu yace: eh, ya hane mu daga fuskantar alkibla lokacin da muke kashi ko fitsari, ko kuma muyi tsarki da hannun dama, ko kuma muyi tsarki da duwatsun da basu kai uku ba, ko kuma muyi tsarki da kashin dabbobi ko kuma kashi”

29- addinin musulunci ya daga darajar mace kuma ya mutunta ta kuma ya sanya mutuntata alama ce ta cewa mutum nada hankali kuma yana da alkhairi, Annabi (SAW) yana cewa: “mafi cika muminai imani shi ne wanda yafi su kawon dabi’a kuma mafi alkairin ku sune mafiya alkairi ga matan su” , sai ya kiyaye mata mutuntakanta, ba ita bace tushen zunubi, kuma ba ita bace ta fitar Annabi Adam ba daga aljannah, kamar yadda masu addinin da suka gabata suke fada, Allah madaukaki yace: “yaku mutane kuji tsoran ubangijin ku wanda ya halicce ku daga rai guda daya kuma ya halitta ma amtar ta daga gare ta kuma ya watsa maza da mata masu yawa a tsakanin su kuji tsoran Allah wanda kuke rokon sa kuma kuji tsoran yanke zumunci lalali Allah ya kasance me kula ne akan ku (1)” , sai musulunci ya kore dukkan tsare-tsare na zalunci game da hakkin mace, musamman ma wanda ke daukar mace cewa koma baya take bata kai namiji ba,wannan yasa aka haramta mata da yawa daga cikin hakkokin ta, Annabi (SAW) yana cew: “lallai mata iyan’uwan maza ne” , kuma ya kiyaye mutuncin ta ya kuma kare karamarta, sai ya sanya yi mata kazaafi da bijiro mata da cutarwa,wani abu ne me kaiwa ga ladabtar da meyi ta hanyar tsaida masa da haddin kazafi, Allah madaukaki yace: “kuma wanda ke yiwa muminai mata kazafi sannan basu zoda shaidu hudu ba to kuyi musu bulala tamanin kuma kada ku kara karbar shaidar su har abada kuma wadannan sune fasikai (4)”
Kuma ya tabbatar mata da hakin ta na gado kamar yadda na miji yake bayan da an haramta mata shi, Allah madaukaki yana cewa: “mazaje nada kaso daga cikin abunda iyaye suka bari da makusanta kuma mata ma nada kaso daga cikin abun da iyaye da makusanta suka bari daga abunda yayi kadan ne ko yawa wannan kaso ne wanda aka farlanta (7)”
Kuma ya bata hakkin ta akan cikakkiyar cancanta da kuma iyancin jujjuya duakiyar ta na mallaka da siye da siyayarwa da sauransu ba tareda wani cutarwa ba kokuma kaidi ba sai dai abun da ya saba wa shari’a, Allah madaukaki yace: “ya ku wadanda sukayi imani ku ciyar daga dadadan abubuwan da kuka nemo”
Kuma musulunci ya wajabta karantar da ita, Ananbi(SAW) ya ce: “neman ilimi farilla ne akan dukkakn musulmi” , da kuma yimata tarbiya me kyau, kuma ya sanya haka cikin dalilan da ke sa a shiga aljannah,Annabi (SAW) yace: “duk wanda yake da yara mata hudu kuma yayi hakuri akan su ya ciyar da su ya shayar da su kuma ya tufatar da su daga dukiyar sa to zas kasance masa kariya daga wuta ranar alkiyama”

30- addinin musulunci addini ne na tsarki:
a) tsarki daga shirka, Allah madaukaki yace: “lallai shirka babban zalunci ne (13)
- da riya, Allah madaukaki yace: “azaba ta tabbata ga masu sallah (4) wanda suke rafkana daga sallan su (5) su ne masu riya da aiyukan su (6)nkuma suna hana taimako (7)”
- da jiji da kai, Allah madaukaki yace: “kuma kada ka kauda kanka daga mutane kuma kada kayi tafiya a ban kasa kana takama lallai Allah baya san dukkan me takama me yawan alfahari (18) kuma ka takaita a cikin tafiyar ka kuma ka rage sautin ka lallai mafi munin sauti shi ne sautin jakai (19)”
- da takama, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda yaja yufafin sa a kasa saboda takama to Allah bazai kalle shi ba ranar alkiyama”
- da girman kai, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda yake da girman kai dai dai da kwayar zarra a zuciyar sa bazai shiga aljanna ba” sai wani mutum yace: ya manzan Allah, lallai mutum kan so ace tufafin sa me kyau ne, kuma takalmin sa me kyau ne, sai Annabi yace: lallai Aallah me kyau ne kuma yana san kyau, girman kai shi ne kin gaskiya, da wulakanta mutane “
Kin gaskiya: shi ne tunkude ta da maida ita ga wanda ya fadeta, wulakanta mutane: shi ne tozarta su
-da hassada, Annabi (SAW) yana cewa:: “cutan al’ummu ta shigo gare ko wato hassada da kiyayya su ne masu aski ba ina nyfin suna aske gashi ba ne a’a suna aske addini ne na rantse da wanda raina ke hannun sa baza ku shiga aljanna ba sai kunyi imani kuma baza kuyi imani ba sai kun so juna shin bazan fada muku abunda zai tabbatar muku da hakan ba to ku yada sallama a tsakanin ku “
b) tsarki na ma’ana, Allah madaukaki yace: “ya ku wadan da sukayi imani idan kun mike zuwa sallah to ku wanke fuskokin ku da hannayen ku zuwa gwiwar hannu kuma ku shafa kanku da wanke kafafuwa zuwa idan sawu kuma in kun kasancekuna da janaba sai kuyi tsarki kuma in kun kasance marasa lafiya ko kuma kuna halin tafiya ko kuma dayan ku ya je biyan bukata ko kuma kun sadu da matan ku sai baku sam ruwa ba to kuyi taimama da kasa me tsarki ai ku shafi fuskokin ku da hannayen ku da ita Allah baya nufi ya sanya kunci a gare ku sai dai yana nufin ne ya tsarkake ku kuma ya cika ni’imar sa a gare ku dan kuyi godiya (6)”
kuma an ruwaito daga Abu huraira Allah ya kara masa yadda, lallai annabi (SAW) yace: “wannan a’yar ta sauka ne akan mutanen qubq: “a cikin sa akwai wasu mazaje da suke san tsarki kuma Allah yana san masu tsarki” , sai Annabi yace: “sun kasance ne suna yin tsarki da ruwa sai wannan a’yar ta sauka a kansu “  Allah madaukaki yace: “a cikin sa akwai wasu mazaje da suke san tsarki kuma Allah yana san masu tsarki” abu daud da tirmzy ne suka ruwaito shi kuma shaikh albany ya inganta shi a irwa’u: 45.

31- addinin musulunci me karfi ne wanda ke sashi cin nasara shigewa zukata da mamaye hankula, za’a iya lura da haka ta yadda yake saurin yaduwa, da yawanmasu shiga cikin sa, duk da rauni taimako na dukiya da karfi wanda ake zubawa sabo da shi ta bangaren musulmai, a kuma bangare daya abunda makiyan sa ke zubawa da masu masa hassada na hanyoyi daban- daban, na dukiya ko kuma mutanen da suke yakar sa da bata shi da kanga mutane daga gare shi ta hanyar tuhumar shi da abubuwan ba bau ruwan shi, amma duk da hakan mutane ke shiga cikin shi jama’-jama’a, kuma kadan ne wanda ke cikin sa ya fita ya barshi, hakika wannan karfin yayi tasiri mai girma wurin musulunta da yawa daga cikin mutanen gabaci wanda suke karantar musulunci dan sanin kofofin rauni a cikin sa sai su yake shi, sai kyawan musulunci da tushen sa na gaskiya da yazo da su, da kuma dacewar su da fitira lafiyaiya da kuma lafiyaiyan hankali, sai suyi tasiri wurin canza rayuwar su zuwa musulunci, kuma hakika makiyan sa ma sun shaida cewa shi addini ne na gaskiya, daga cikin su akwai” Margoliouth “wanda ansan shi makiyi ne na musulunci sai dai girman alkur’ani yasa shi ya fadi gaskiya inada yake cewa:  lallai daga cikin abunda kalaman masu bincike ya hadu akai shi ne lallai alkur’ani yanada matsayi me girma a litttafan addinai da suka shude, duk da cewa ya zo ne a bayan su-na karhen su- wanda sune suke kawo mana tarihi, sai dai ya na gaban su wajen yin tasiri ga mutu, wanda haka kan bada mamaki, lalai shi ya samar da sabon tunani ga dan adam, kuma ya tabbatar da tushen makaranta ta kyawawan halaye ta musamman.

32- addinin musuluci adddini ne na taimakon jama’a, ya wajabta wa musulmi damuwa da halin iyan’uwansa musulmai duk inda suke,Annabi (SAW) yana cewa: “zakaga muminai a wajen tausayawar su da kaunar su da taimakon su ga junan su kamar misalin jki ne guda daya idan wata gaba tayi rashin lafiya sai sauran jikin baki daya ya amsa da rashin bacci da kuma zazzabi” , kuma yayi umarni akan kyautata tanayin su ta hanyar sadaka ta wajibi wato (zakka) ko kuma ta mustahabbi, Annabi (SAW) yana cewa: “imanin dayan ku baya cika har sai yaso wa dan;uwan sa abun da yake so wa kansa “
Kuma da taimaka masa a halin damuwa da jarabawa, Annabi (SAW) yana cewa: “mumini ga mumini kamar gini ne sashi na karfafa sashi-sai Annabi ya hada yatsunsa wuri da “
Kuma yayi umarni da taimaka musu da kai musu dauki in suka bukaci haka, Allah madaukaki yace: “kuma idan suka nemi taimakon ku a addini to ku taimaka musu sai dai fa in akan mutanen da tsakanin ku da su akwai yarjejeniya ne kuma Allah yana ganin abunda kuke aikatawa (72)
Kuma ya hana a tozarta su, kamar yadda Annabi (SAW) ya fada: “musulmi dan’uwan musulmi ne baya zaluntar sa kuma baya tozarta shi, kuma duk wanda ya tsaya dan biyan bukatar dam’uwan sa to Allah zai biya masa bukatar sa “

33- addinin musulunci yazo da tsarin gado wanda ke raba abunda mamaci ya bare ga magadan mamacin wanda suke da hakkin cin gadan sa, karami da babba namiji da mace, rabo na adalci kyakkyawa ma’abot lafiyayyun hankula suna shaida da hakan, gwargwadan kusanci da nisanci da kuma amfani ga mamacin, ba wanda ke da hakkin raba gadan da san rai ta yadda yake so, daga cikinababen burgewa nawannan tsari shi ne yana rarrraba dukiya koyayya girmanta yake zuwa kananan abun mallaka, sai ya sanya lamarin tara dukiya a hannun wasu kebantattun mutane abu ne da bazai yiwu ba, kuma hakika alkur’ani yayi bayin kason yara da iyaye da mata da iyan’uwa a cikin suratun nisa’i a a’yoyi uku, a’ya ta 11 – 12- 176 a’ya ta karshe a suratun nisa’i, Annabi (SAW) yana cewa: “hakika Allah ya ba kowane me hakki hakkin sa babu wasiyya ta cin gado ga wanda zaiyi gado “

34- addinin musulunci ya kawo tsarin wasiyya, musulmi nada damar yin wasiyya a dukiyar sa bayan mutuwar sa da cewa a sata a aiyukan alheri, dan hakan ya zama sada me gudana gare shi bayan mutuwar sa, sai dai musulunci ya tgace wannan wasiya da cewa kar ta wuce daya bisa uku na dukiyar, an ruwaito daga Aamir dan Sa’ad Allah ya kara masa yadda yace, Annabi (SAW) yazo gaishe ni banida lafiya a garin makkah, sai nace: ina da dukiya me yawa, zan iya wasiyya da dukiyata dukkanta? Sai yace, a’a, sai nace, to rabin ta, sai yace, a’a, sai nace, to daya bisa ukun ta, sai yace: daya bisa uku, daya bisa uku nada yawa, kabar magadan ka a wadace yafi alheri akan ka bar su a talauce suna rokon mutane da hannayen su, kuma duk abun da ka ciyar to sadaka ne a gare ka hatta lomar da kake sawa a bakin matar ka “ , kuma kada ya zama akwai cutar da magada a cikin ta,Allah madaukaki yace: “bayan wasiyyar da zai yi ko kuma biyan bashi wanda ba cutarwa wannan wasiyyace daga Allah “

35- addinin musulunci yazo da tsarin ukuba (haddi da razanarwa) wanda dasu ne ake samun zaman lafi da kwanciyar hankali a al’umma daga laifuka da yaduwar su, sai kaga an tsare jini da su kuma a kare mutunci, kuma a tsare dukiya, kuma a tankwara shakiyai, kuma a kare mutane kada wasu suyi ta’addanci ga wasu, sai a toshe barna da wuraren ta ko kuma a saukaka damuwar ta, saboda haka ne ma zamuga musulunci yana iyankace wa ko wane laifi irin hukuncin da ya dace da shi, sai ya sanya laifin kisan ganganci shi ne kisasi, Allah madaukaki yace: “yaku wadanda sukayi imani an wajabta muku yin kisasi a gameda wanda aka kashe” , sai dai fa in iyan uwan wanda aka kashe sun yafe, saboda fadar Allah madaukaki: “duk wanda aka yafe mai wani abu game da dan’uwansa “
Kuma ya sanya wa laifin sata yanke hannu, Allah madaukaki yace: “kuma barawo da barauniya to ku yanke hannayen su sakamakon abunda suka aikata ukuba ce daga Allah kuma Allah mabuwayi ne me hikima (38) , idan barawo yasan cewa in yayi sata za’a yanke hannun sa to zai kame ya bar sata, sai ya tsare hannun sa daga yankewa, kuma sai dukiyar mutane ta kubuta daga sata,
Kuma ya sanya bulala ga laifin ta’addanci ga mutunci ga wanda beyi aure ba, Allah madaukaki yace: “mazinaci da mazinaciya to ku bulale kowane daya daga cikin su bulala dari “
Kuma ya sanya bulala ga laifin ta’addanci ga mutunci ta hanyar kazafi, Allah madaukaki yace: “kuma wadanda suke jifar kamammun mata sannan basu zo da shaidu hudu ba to kuyi musu bulala tamanin....” suratun nur, aya ta 4.
Sannan shari’a ta sanya doka ta bai daya wadda da ita ake kwatanta ukuba, Allah madaukaki yace: “kuma sakamakon mummuna shi ne mummuna irin sa “ , da kuma fadar Allah madaukaki: “idan akayi muku cin mutunci to kuma ku rama irin yadda akayi muku”
Kuma wadannan ukubobi suna da sharudda da tsari wajen dabbaka su, duk da sanin cewa musulunci bai sanya wadannan ukubobi ba cewa dole ne sai anyisu babu mafita,a’a ya bude kofa ta yafiya da rangwame a game da hakkokin mutane, Allah madaukaki yace: “duk wanda ya yafe kuma ya gyara to ladar sa na wurin Allah “ , lallai musulunci lokacin da yake tabbatar da wannan ukubar ba wai yana nufin huce haushi ba ne da tsanani, a’a yana nufin tsare hakkokin mutane ne da shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma, da kuma razana duk wanda ransa ke saka masa yin wasa da zaman lafiyan sa da kwanciyar hankalin sa, idan wanda yayi kisa yasan cewa shima za’a kashe shi ne, kuma barawo yasan cewa za’a yanke masa hannu, kuma mazinaci yasan cewa za’ayi mai bulala, kuma me kazafi yasan cewa shima za’ayi mai bulala ne, to duk zasu razana su fasa aikiata abun da sukayi niyya sai su huta kuma wanin su ma ya huta, kuma Allah yayi gaskiya yayin da yake cewa: “kuma kuna da wata irin rayuwa a cikin kisasi yaku ma’abota hankula “
Me magana zai iya cewa, wannan ukuba wanda Allah ua shar’anta ga wasu laifuka, sunyi tsauri! Sai ace masa, lalai kowa ya yadda cewa laifuka nada cutarwarsu ga al’umma kuma hakan baya boyuwa, kuma dole a yake su da tunkude su, da kuma wajabta ukuba akan su, amma sabani sai ya zama na nau’in ukubar ne dan kowa ya tambayi kansa kuma yayi nazari shin wannan ukubu da musulunci ya kawo sun fi samun nasara wurin kawar da abrna ko kuma rage su, ko kuma ukubar da mutane ne suka kawo wanda ke kara wa barna yaduwa? gabar da ta rube a jiki bata da magani sai dai yankewa dan ragowar jiki ya tsira.

36- addinin musulinci ya halatta dukkan mu’amala ta kudi na cinikaiya da hadaka da haya dan abunda ke cikin haka na yalwata wa mutane cikin al’amuran rayuwa, hakan kuwa dai-dai da tsarin shari’a wanda ya kunshi rashin cutarwa da kiyaye hakkoki ta hanyar yadda tsakanin bangarori biyu, da kuma sanin abunda ake cinikin dan shi da maudu’in sa da sharuddan sa, musulunci bai hana komai ba sai fa abunda keda cutarwa da zalinci, kamar riba da caca da dara da sayan abuunda ba’a sani ba, duk da cewa rike dukiya da iyanci jujjuyata dai-dai da shari’a hakkin kowa ne sai dai musulunci ya shar’anta kangewa akan mutum a hana shi amfani da dukiyar sa idan akwai cutarwa acikin hakan akan sa ko akan wanin sa, kamar kange mahaukaci da karamin yaro da wawa ko kuma kangewa akn wanda akebi bashi ahr sai ya biya wanda ke binshi bashin, to kuma a cikn haka akwai hikima da kuma tsare hakkoki, wanda hakan be boyuwa ga dukkan me hankali ta yadda yake kare hakkokin wasu daga wasa da kuma wargi.

37- addinin musulunci addini ne na kome a fili a musulunci babu wasu ababe wanda suke duhu wanda suke wajaba ayi imani da su ko kuma ba wanda ke da hakkin yayi tambaya akan su, Allah madaukaki yace: “ku tambayi masana in ku baku sani ba (43)”, kai musulunci ya tsawatar sosai game da boye abunda Allah yasaukar na bayani ga mutane, Allah madaukaki ya ce: “lallai wadanda suke boye abunda muka saukar na baiyanannun abubuwa da shiriya bayan munyi bayanin sa ga mutane a cikin littafi to wadannan Allah na tsine musu kuma masu tsinuwa na tsine musu (159)”

38- adinin musulunci addini ne na dunkulewa da hadin kai da sabo, wanda ke kiran musulmai baki daya da kasancewa sahu da kuma hannu daya, dan su samu izza da matsayi, hakan kuwa ta hanyar:
a) barin sanrai da sankai wanda ke kunno kankame mazhaba dakabilanci da jinsi, wanda hakan hanya ne daga cikin hanyoyin watsewa da rabuwar kai.
b) tace akidu da ibadu daga dukkan abun da ke bata su na gada shirka da bidi’o’i.
c) kyakkyawan shiri tsakanin musulmai a cikn dukkakn al’amuran siyasa da tattalin arziki..... na abun da zai kawo musu zaman lafiya da tabbaci, Allah madaukaki yace: “kuma kuyi ruko da igiyar Alllah gaba daya kada ku rarraba “
kuma yayi hana daga sabani da rarrabuwa, Allah madaukaki yace: “kuma kada ku kasance kamar wadan da suka rarraba kuma sasssaba bayan gaskiya baiyananna ta zo musu to wadannan suna da azaba me girma (105)” , sabani be cikin tsari irin na shari’a, Allah madaukaki yace: “lalai wadanda suka rarraba addinin su kuma suka zama jama’a daban-daban to baka tare da su da komai lallai al’amarin su yana wurin Allah sannan zai basu labarin abunda suka kasance suna aikatawa (159)”
kuma shari’a ta baiyana irin abunda ze faru in akayi sabani kuma aka rarrabu na gushewar kwarjini da dora makiya saman musulmai da kaskanci, Allah mdaukaki yana cewa: “kuma kada kuyi jayayya sai ku samu baraka kuma sai karfin ku ya watse” { suratul anfal, aya ta 46 }.

39- addinin musulunci ya bude wasu al’amara na boye ga mutane, kuma ya baiyana musu labaran wadanda suka shude cikin al’ummu, da yawa daga cikin a’yoyin alkur’ani Allah ya bamu labaran Annabawan da suka gabata a cikin su tare da mutanen su da irin abun da ya faru da su, Allah madaukaki yace: “hakika mun aika musa da ‘ayoyin mu da hujja baiyanna (96) zuwa ga fir’auna da mukarraban sa...” { suratu hud: aya ta 96 }, Kuma Allah madaukaki yace: “kuma lokacin da Isa dan Maryama yace yaku bani isra’ila lallai ni manzan Allah ne zuwa gare ku ina me gasgata abun da ya gabace ni na attaura..” { suratus saffi: aya ta 6 }, kuma Allah madaukaki yace: “kuma mun aika zuwa ga adawa dan’uwansu Hudu...” { suratul a’araf: aya ta 65 }, kuma Allah madaukaki yace: “kuma mun aika zuwa ga samudawa dan’uwansu Salihu....: { suratul a’araf: aya ta 73 }, haka nan sauran annabawan da manzanni alkur’ani yayi mana bayanin abun da ya faru tsakanin su da mutanen su’

40- addininmusulunci ya kalubalanci mutane baki dayan su akan su zo da irin alkur’ani duk da fa cewa shine littafi na karshe wanda ya sauka daga sama, kuma wannan kalubalen yana nan har zuwa tashin alkiyama, Allah madaukaki yace: “to sai suzo da wani labari irin shi in sun kasance masu gaskiya (34)” kuma kalubalen da alkur’ani yayi yazo ne daki-daki, ya fara da neman a zo da wasu surori irin na alku’ani, Alalh madaukaki yana cewa: “ko suna cewa ya kirkiro shi ne to kace musu ai sai ku zo da surori guda goma irin sa kirkirarru kuma ku kira shaidunku koma bayan Allah in kun kasance masu gaskiya (13}” { suratu hud: aya ta 13 }, kuma ya karfafa wurin kalubalantar kawo wata sura irin sa, Allah madaukaki ya ce: “kuma in kun kasance kuna kokwantan abunda mukasaukar wa bawanmu to kuzo da wata sura irin sa kuma ku kira shaidunku koma bayan Allah in kun kasance masu gaskiya (23)  ,
kalubalen ma na halittu biyu ne-aljanu da mutane- dukkan su, Allah madaukaki yace: “kace musu da ace aljanu da mutane zasu taru dan suzo da irin alkur’ani to baza su iya zuwa da irin sa ba koda kuwa sashin su me taimako ne ga sashi (88)”

41- addinin musulunci addini ne na jihadi wanda ake nufin da shi kare addini da rai da iyali da gari, da kuma yakar wanda ya hana a isar da shari’ar Allah, dan shi da’awa ne na duniya, ba wai ya takaita bane ga qasu mutane kebantattu, a’a ai dole ne kowa yaji labarin ta (da’awar musulunci) kuma yasanta da abunda take kunshe da shi na alkhairi da adalci da kauna, kuma hakanan ma da dunkude zalunci da kuma taimakon wand aka zalunta, Allah madaukaki yana cewa: “kuma ku yaki wadanda suke yakarku saboda daukaka kalmar Allah kuma kada ku ketare iyaka lallai Allah baya san masu ketare iyaka (190)” { suratul bakara: aya ta 190}>, shi jihadi a musulunci anayi ne dan daukaka kalmar Allah da kuma yada addini, Allah madaukaki yana cewa: “kuma ku yake su har kada wata fitinar da zata rage kuma adini dukkan sa ya kasance na Allah “ , kuma annabi (saw) yace ma wani mutum wanda ya tambaye shi: mutum ne yake yaki dan ganima da mutumin da ke yaki dan dan a yabe shi da mutumin da ke yaki dan aga masayin sa, to acikin su waye yake jihadi dan Allah? sai Annabi yace: “duk wanda yayi yaki dan kalmar Allah ta kasance itace a sama to shi ne yayi saboda Allah “ , bawai kwadayin abben diniy shi ne manufar jihadi ba, ko kuma wani buri na mutum da kwadayi na yalwatawa na shaidan ko kuma burin fansa, ko kuma alfahari da karfi, Allah madaukaki yace: “kuma kada ku kasance kamar wadanda suka fito daga gidajen su suna masu takama da kuma riya ga mutane “

42- addinin musulumci addini ne na umar ni da kykkyawa da kuma hani daga mummuna, wanda shi ne hakikanin zaman lafiyar al’umma saboda adini bai tsayuwa sai da wanzuwar ma’abotan sa da kuma tsatyuwar su akan shari’ar sa ta hanyar yin abunda yace ayi da nisantar abun da ya hana, kuma gyara ne ga wanda suka karkaci da kuma mikar da su da kange su daga munanan abubuwa, sai da wannan a tsare al’umma daga rushewa da kuma barna, Annabi (SAW) yana cewa: “misalin wanda ke tsaye akan iyakokin Allah da kuma wanda ya afka cikin su kamar misalin wasu mutane ne wanda sukaayi kuri’a wajen hawa jirgin ruwan su sai wasu suka samu gidan sama wasu kuma suka samu gidan kasa a cikin ta, sai ya zama wadanda suke kasa in suna bukatar ruwa sai sun biyu ta wurin wadanda ke sama, sai suka ce: da zamu bula wani wuri ta kasa cikin raban mu dan kar mu dinga cutar da na saman mu, to in suka bar su suka aikata abunda sukayi nufi to dukan su ne zasu halaka in kuma suka hana su to zasu tsira sai kuma dukkan su su tsira “

43- addinin musulunci alama ne daga cikin alamun kusantowar tashin alkiyama da kuma gushewar duniya, hakika Annabi (SAW) ya baiyana cewa shi ne annabin karshe kuma lalllai zuwansa alama ne na tashin alkiyama, an ruwaito daga Anas Allah ya kara masa yadda yace: Annabi (SAW) yace: “an aikoni ni da tashin alkiyama kamar wadannan yatsu guda biyu” sai anas yace: sai Annabi ya hada yatsun sa guda biyu manuniya da na tsakiya . , saboda shi ne (SAW) na karshen annabawa da kuma manzanni.


BANGAREN SIYASA A MUSULUNCI
Hakika shari’ar musulunci tazo da bangaren siyasa- kamar wanin sa na sauran bangarorin- da tsare- tsare da game gamrin ka’idoji, sune damba wanda ake samar da daular musulunci a kansu da kuma guzirin shugaba ga daular musulunci, yana me zartar da umarnin Allah ta hanyar dabbaka wadannan tsare-tsare da kuma ka’idoji, Allah madaukaki yace: “shin hukuncin jahiliyya suke so kuma babu wanda yafi Allah kyawon hukunci amma ga mutane masu yakini (50)”
Shugaba na daular musulunci wakili ne na al’umma, saboda wannan wakilcin to ya wajaba a kan sa:
1- yayi dukkan kokarin sa wurin dabbaka shari’ar Allah da kuma samar da wadatattun hanyoyun rayuwa me dadi a gare su, da kuma tsare addinn su da zaman lafiyar su da rayukan su da dukiyoyin su, Annabi (SAW) yana cewa: “babu wani bawa wanda Allah zai dorashi jagorance wasu mutane sai be kewayesu da kyautatawar sa ba face bazai ji kanshin aljanna ba” , shugaba a daular musulunci ya kamata ne ya zama kamar yadda saiyidina Umar dan khaddabi yace ne wata rana ga mutanen sa: ku nuna mun wani mutum wanda zan bashi wani aiki wanda ha dameni na al’amarin musulmai, sai suka ce: ga Abdrrahman bun Auf, sai yace: yana da rauni, sai suka ce: to wane fa. Sai yace: banda bukatar sa, sai suka ce: to wa kake bukata? Sai yace: ina bukatar mutum ne wanda in ya zama shugaban su zai zama kamar daya ne daga cikin su, kuma in ba shugaban su bane zai zama kamar shi ne shugaban su, sai sukace: to ba wanda muka sani haka sai dai Arrabi’i ibnul Harith. Sai yace kunyi gaskiya, say ya nadashi shugaba.
2- kuma kada ya jagorantar da wanda be cancanta ba kuma bazai iya daukar amana ba akan al’amarin musulmai, kamar ya jagorantar da abokin sa ko kuma dan’uwan sa sai ya kyale wanda ya fi su cancanta.
Kuma daga cikin abunda wadannan tsare-tsare da ka’idoji suka banbanta da shi, shi ne:
1- na Allah ne, Allah madaukaki ne ya kawo su, kowa daya ne a gaban su, shugaba da wanda ake shugabanta, me kudi da talaka, da me daraja da wanda beda ita, fari da baki, babu wani mutum da zai saba musu komai matsain sa, ko kuma ya kawo wata doka wacce zata ci karo da su ko kuma ta saba musu, Allah madaukaki yace: “be kamata ba ga wani mumini ko kuma mumina idan Allah da Manzan sa suka yanke wani hukunci ya zama suna da zabi a cikin al’amarin su kuma duk wanda ya saba wa Allah da manzansa to hakika ya bace bata baiyanana (36)” ,
Kuma ya wajabta ma kowa binsu da kuma kiyayesu da kuma dabbaka su shin shugaba ne ko kuma wanda ake shugabanta, Allah madaukaki yace: “lallai maganar muminai idan aka kirasu zuwa ga Allah da manzan sa dai yayi hukunci tsakanin su sai suce mun ji kuma munyi biyayya to wadannan sune masu babban rabo (51)”
Babu wani shugabanci na dundundun a musulunci ga wani daga cikin mutane, kai hatta shugaba dukkakn shugabancin sa kaiyadajje ne a a inda shari’a ta iyakance masa, da ace zai saba ya wuce iyakar sa to baza’a masa da’a ba kuma baza’a bishi ba, saboda fadar manzan Allah (SAW): “wajibi ne akan musulmi ya ji kuma yayi biyaiya cikin abunda ya so da kuma wanda ya ki sai dai in an umarce shi da saban Allah to in aka umurce shi da saban Allah to babu ji kuma babu biyaiya”
2- shawara, wannan tushe ne wanda tsarin siyasa a musulunci ke ginuwa aki, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma da wadanda suka amsa kiran ubangijin su kuma suka tsaida salla kuma al’amarin su shawara ne a tsakanin su kuma suna ciyarwa daga abun da muka azurta su da shi (38)”  kuma da fadar Allah madaukaki: “saboda rahamar Allah ce ka zama me tausasa musu da zaka kasance me tsanani me kaushin hali da sun watse daga gefen ka to kayi musu afuwa kuma ka nema musu gafara kuma kayi shawara da su a cikin al’amurra “
A cikin a’aya ta farko Allah ya hada tsakanin shawara da sallah wacce take gimshiki na musulunci wanda hakan ke nuna girman lamarin, dukkan abun da ke da alaka da maslahar al’umma to ya wajaba a nemi shawarar ma’abota hankali da lafiyayyan ra’ayi, kuma acikin karshen a’yar Allah ya yabi muminai dukkan su saboda suna sanya shawara a tsakanin su dole ce a cikin al’amuran su.
Kuma a cikin a’ya ta biyu Allah yana nema daga manzan sa shi ne shugaba na daular musulunci da ya dinga shawara a cikin dukkan al’amuran da suke da alaka da maslahar al’umma wanda babu wahayi a cikin sa, amma abun da akwai nassi a cikin sa ba bukatar shawara a cikin sa, kuma hakika Annabi (SAW) ya kasance yana shawara da sahabban sa, hakika Allah ya umarci annabin sa (saw) da shawartar sahabban sa, Allah madaukaki yace: “(kuma kayi shawara da su a cikin al’amura)
Kuma an ruwaito daga Abu huraira Allah ya kara masa yadda yace: ban taba ganin wani ba wanda yafi Annabi (SAW) shawartar sahabban sa “
Kuma hakika malaman fikihu sun ce wajibi ne shugaba ya dinga shawara da al’ummar sa acikin al’amuran da suka shafi maslahohin su ta yadda da zai ki yin shawara to ya zama dole akan al’umma su nemi da baiyana ra’ayoyin su kuma su tofa albarkacin bakin su, malaman sun kafa hujja ne da ‘ayoyin nan guda biyu da suka gabata, domin shari’ar musulunci tana dauka cewa shugaba wakili ne ya wajaba akansa ya tsayu da abunda aka dora masa, suka kuma al’umma abunda ke kansu shi ne su kula da cewa shugaba ya dabbaka shari’ar musulunci, kuma musulunci ya ba kowa iyancin baiyana ra’ayinsa da kuma warware na wasu amma ta hanyar da ta dace yana me lazimtar tsarin Allah a cikin hakan ta wurin warware ra’ayoyin wasu da baiyana nasa ra’ayin amma ta yadda ba zai janyo fitina ba, Annabi (SAW) yana cewa: “ku saurara kuji, lallai mafi falalar jihadi shi ne fadar gaskiya a wurin mugun shugaba “  
Abubakar as siddiq Allah ya kara masa yadda halifa na farko yana cewa: “ya ku mutane lallai ni an shugabantar da ni akan ku amma ba ni na fiku alkairi ba, idan na kyautata to ku taimake ni, kuma idan na munana to ku gyara mun... ku yi mun biyayya matukar inayiwa Allah da manzansa biyayya, amma ian na saba wa Allah da manzansa to banda hakki kuyi mun biyaiya”
Umar dan khaddabi Allah ya kara masa yadda, halifa na biyu ya hadu da Muhammad dan Maslama sai yace: me kake gani game da shugabanci na ya kai Muhammad? Sai yace: wallah ina ganin ka kamar yadda nake kauna, kuma kamar yadda dukkan me maka fatan alkairi yake ganin ka, ina ganin ka me karfi wajen tattara dukiya, amma kana tsantseni game da su, kuma me adalci wajen raba su, da ace zaka karkace to da zamu mikar da kai kamar yadda ake mikar da mashi a makera, sai Umar yace: mai mai ta mu ji, sai yace: da zaka karkace to da zamu mikar da kai kamar yadda ake mikar da mashi a makera, sai Umar yace: godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya ni a cikin mutanen da in na karkace zasu mikar da ni “
3- kuma yana bincike da kuma tambaya, an ruwaito daga Umar dan khaddabi Allah ya kara masa yadda cewa wata rana yayi huduba yana sanye da kaya biyu, sai yace: “yaku mutane ku saurara kuma kuyi biyaiya, sai wani mutum ya mike, sai yace: baza mu saurara ba kuma baza muyi biyaiya ba! Sai Umar yace: saboda me? Sai mutumin yace: saboda kasa kaya biyu mu kuma mun sa daya- a lokacin umar ya rabawa wa kowane musulmi kaya daya-! Sai umar yayi kira da madaukaki sautin shi, yace: ya kai Abdullahi dan Umar, basu labari, sai yace: kaya na ne na bashi kyauta, sai mutumin yace: to yanzo kam zamu saurara kuma muyi biyaiya.
Sai musulunci ya tsare hakkoki da wannan aiki, da kuma iyanci ta bai daya da kuma kebantatta, kuma ya nesanta matatsa shari’a daga sanrai irin na mutane, do min su tsare-tsaren su suna haifuwa ne daga san rai da bangaranci, amma abun da ya shafi sauran abubuwan na gefe musulunci be iyakance su ba, wannan kuwa ba dan komai ba sai dan barin kofa a bude ga musulumai dan su kawo dokoki da tsare-tsare wanda suka dace da halinsu daidai da yadda maslaha take hukuntawa a cikin kowani lakaci da wuri, amma da sharadin wadannan dukoki da ka’idoji kar su ci karo da mahanga ta musulunci da kuma ka’idojin shi na asali.


BANGAREN YAKI A MUSULUNCI:
Shi ne abunda ake kira (jihadi) a musulunci, kuma shi jihadi a musulinci a gamegarin ma’anarsa shi ne “yakan rai” wannan kuwa ta hanyar barin haramun da ababen da aka hana, da kuma aikata wajibai da ababen da aka yi umarni da su gwargwadan iko da kuma iyawa dan neman yaddar Allah.
Amma kebantacciyar ma’ananar jihadi: shi ne yaki dan yada addinin Allah da kuma isar da shi ga mutane baiki daya, da wannan ma’anar ti shi ba saban abu bane wanda musulunci ne kawai yazo da shi ba. A’a yana cikin dukkan shari’o’in da Alllah ya turo daga sama wanda suka gabata.
Hakika ya zo a cikin littafin Attaura wadda take hannun yahudawa, a cikin tafiya ta biyu dan tada mutane ashirin, tabbatar da shari’ar yaki ta mafi munin hanyar rusawa da lalatawa:
“har idan ka kusa da gai dan yakar sa to ka fara kiransu zuwa ga sulhu, to in sun amsa maka zuwa sulhu kuma suka bude maka kofa to dukkan mutanen da ke cikin garin za su dinga yi maka hidima da bauta, in kuma sunki sulhu suka sa saida kayi yaki to ka tsare su a garinsu, idn Allah ya baka nasara a kansu to ka kashe dukkan mazajen da wuka, amma mata da yara da dabbobi da dukkan abunda ke cikin garin da kuma dukkan abunda kaci ganimar sa, to ka tattarsu naka ne, kuma kaci ganimar makiyanka wacce Allah ya baka, ha zaka aikata ga dukkan garuruwa wanda suke da nisa da kai sosai wanda ba garin wadanan bane da suke nan, amma garuruwan wadannan kabilun wanda ubangiji abun bautarka ya baka rabo daga ciki to kar kabar komai a ciki ka haramta su haramtawa.....”
Kuma ya zo a cikin injilar mamma (bible) a cikin juzu’i na goma lamba ta 24 da abunda ke bayansa:
“kada kuyi zatan cewa nazo ne dan kawo zaman lafiya a kasa, banzo ba dan in karanta muku sallama ba kawai ‘a’a sai dai takobi, lallai ni nazo ne dan in tabbatar da mutum a matsayin kishiyan mahaifinsa kuma yarinya kishiyar mahaifiyar ta, kuma suruki kishiyan surukansa, kuma makiya mutum su ne mutanen gidan sa, duka wanda ya so baba ko mama fiye da ni to bai cancanta da ni ba, kuma duk wanda yaso yaro ko kuma yarinya fiye da ni to bai cancanta da ni ba, kuma duk wanda bai dauki kuros din sa ba ya bini to bai cancanta da ni ba, kuma duk wanda ya ji dadin rayuwarsa to yana tuzarta ta ne kuma duk wanda ya tozarta rayuwar sa saboda ni to zai same ta .”

Jihadi iri biyu ne:
1- jihadin kare kai: shi ne yakan wanda ke ta’addanci ga musulmai (ta’addanci a addini ko kuma mutunci ko dukiya ko gidaje da abubuwanda suka mallaka) kuma a wannan hali jihadi farilla ne akan duk wanda zai iya daukan makami har sai sun kora iyan ta’adda, Allah madaukaki yace: “kuma ku yaki wadanda suke yakan ku dan daukaka kalmar Allah kuma kada ku wuce iyaka lallai Allah baya san masu wuce iyaka (190)”
Idan suka ci nasara wurin kora makiya to yayi dai-dai, in kuma suka kasa to wajibi ne akan dukkan musulman da ke kewaye da su (na kurkusa) suma suzo dan ayi yakin dasu har sai an kore makiya, kuma wannan hakki ne shar’antacce ga dukkan mutane duk da banbance-banbancen addinan su da hanyoyin su.
2- Jihadin nema: shine yakan sarakuna iyan kama karya da miyagu wadanda suke zaluntar muminai kuma suke azabtar da su kuma suke kange duk wanda ke san ya yada addini musulunci ga mutane, ko kuma hana duk wanda ke san shiga musulunci ya shiga cikin sa, saboda musulunci da’awa ne na duniya ba ta takaita bane akan wasu kebantattun mutane, a’a dole ne kowa ya ji labarin ta kuma ya santa da abunda ta kunsa na alheri da adalci, wannan shi ne abu na asali da ke sawa a yi jihadi, saya daga cikin sahabbai yana cewa Rustum sarkin roma (burtaniya)lokacin da ya tambaye su dalilin zuwan su garin shi, sai yace: munzo ne dan mu fitar da bayi daga bautar bayi zuwa bautar ubangijin bayi kuma mu fitar da su daga kiunci na duniya zuwa yalwar lahira kuma mu fitar da su daga zalunci addinai zuwa adalcin musulunci.
Kuma hakanan an shar’anta jihadi dan tunkude zalunci daga wanda aka zalunta da taimakon wanda aka cuta, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma me ya same ku ne bakwa yaki dan daukaka kalmar Allah da kuma taimakon wadanda aka raunata daga cikin maza da mata da yara wadanda suke cewa ya ubangijin mu ka fitar da mu daga wannan gari wanda mutanenta azzalumai ne kuma ka sanya mana majibincin al’amuranmu daga gare ka kuma ka sanya mana me taimako daga gare ka (75)”
Amma yakoka dan fadadawa da kuma karfin iko ko kuma hakeyaken daukar fansa wanda sakamakon su shine rushewa da lalatawa ko kuma yakin nuna kwanji da alfahari da jijida kai da karfi dukkan su musulunci ya hana su kuma ya haramta su, domin shi yake a musulunci kamar yadda muka ambata dazun ana yi ne dan Allah da kuma yada kalmarsa, ba wai ana yi bane dan san rai da kuma abunda mutum ke kauna na shaidanci, Allah madaukaki yace: “kuma kada ku kasance kamar wadanda suka fito daga gidajen su suna masu takama da riya ga mutane”
Kuma Annabi (SAW) yana cewa ga mutuin da ya tambaye shi, sai yace:mutum ne yake yaki dan ganima da kuma mutumin da ke yaki dan a yabe shi da kuma mutumin da ke yaki dan aga matsayin shi to waye yayi dan Allah? sai Annabi yace: “duk wanda yayi yaki dan daukaka kalmar Allah to shi ne yayai dan Allah “
Kuma jihadi a musulunci yana da ma’aunai da ladubba, ba’a kashewa cikin makiya sai wanda ya shigo flin daga yayi yaki kuma yayi taimako akai, amma tsofaffi da kananan yara da mata da marasa lafiya da masu basu magani da wadanda aka jima rauni, da masu bauta wadanda suka kebe kawunan su dan bauta to dukkan su ba’a kashe su,kamar yadda ba’a karasa wanda akayiwa rauni a fagen daga, kuma ba’a wulakanta gawarwaki kuma ba’a kashe tsuntsaye, kuma ba’a rusa gidaje, kuma ba’a gurbata ruwan sha da rijiyoyi kuma ba’a bin wanda ya gudu daga yaki.
Kuma hakika wannan utace fuskantarwar Annabi (SAW) da halifofin sa a bayansa ga rundunar yaki wadanda suke turawa dan yada musulunci, Annabi (SAW) yana cewa: “kuyi yakai da sunan Allah dan daukaka kalmar Allah ku yaki wanda ya kafurce wa Allah, kuyi yaki amma kada kuyi yaudara, kuma kada ku wulakanta gawa, kuma kada ku kashe kananun yara”
Kuma Abubakar as siddiq Allah ya kara masa yadda, halifa na farko na manzan Allah (SAW) yana cewa:ga jagororin rudunanr shi wadanda yaki tura su dan yada addini:ku tsaya zan muku wasiyya da abubuwa guda goma sai ku kiyaye su daga gare ni:
“kada kuyi yaudara,kada ku wuce iyaka,kada ku ha’inci, kada ku wulakanta gawa,kada ku kashe karamin yaro, kada ku kashe tsoho ko mace, kada ku tumbuke bishiyar dabino kuma kada ku kona shi, kada ku yanke bishiya me fitar da iya-iya, kada ku yanka akuya ko saniya ko rakumi sai dai in da niyyar ci ne, kuma zaku wuce wasu mutane sun kebe kawunan su a cikin wararen bauta to ku rabuda su da abunda suka kebance kawunan su dan shi”
Amma wadanda aka kama a wurin yaki to a musulunci suna da hakkoki: be hallata a azabtar da su ko kuma wulakanta su ko kuma tsorata su, ko kuma tstsaga musu jiki, ko kuma yunwatar da su-hana su abinci da abun sha har sai sun mutu- ana mutunta su ne da yi musu kyakkyawar mu’amala, Allah madaukaki yana cewa: “kuma suna ciyar da abinci ga miskini da maraya da fursunan yaki (8) suna cewa kawai muna ciyar da ku ne dan fuskar Allah bama bukatar sakamako daga gare ku ko godiya (9)”  Kuma Annabi (SAW) yana cewa: “ku fanshi fursuna kuma ku ciyar da me jin yinwa kuma ku ziyarci mara lafiya”
Kuma daular musulunci tanada iyanci bayan haka cikin lamuran su, ko dai ta sake su ba tare da fansa ba ko kuma da fansa ta dukiya ko kuma fursunonin yaki na musulmai, har zuwa karshe.
Kuma jama’ar da aka ci galaba akan su sunada hakkoki suma: ba zubarda mutuncin su, kuma ba kwashe dukiyar su, kuma ba cin zarafin su da tozarta su,kuma ba rushe gidajen su, kuma ba tafiya dan fansa akan su ko kuma huce haushi, a’a sai dai dan gyara da kuma umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna da kuma tsaida adalci, kuma mafi alherin dalili akan haka shi ne alkawarin da Umar dan khaddabi Allah ya kara masa yadda ya baiwa mutanen baitul makdis lokacin da yayi galaba a kan su ya shige ta yana me cinta da yaki, sai yace: (da sunan Allah me rahama me jin kai, wannan shi ne abun da bawan Allah Umar dan khaddabi sarkin muminai ya baiwa mutanen baitul makdis na aminci: ya basu aminci akan rayukan su da dukiyoyin su da coci-cocin su da kros-kros din su..... baza a masa musu ba akan addinin su kuma baza a cutar da wani ba daga cikin su...) to shin tarihi ya taba shaida irin wannan adalcin da rangwame daga bangaren wanda yaci nasara yayi galaba ga wanda aka ci nasara a kansa kuma aka galabe shi?! Duk da cewa shi – Allah ya kara masa yadda _ yana da dama ya rubuta abunda yaga dama a game da su na sharudda, sai dai ina saboda adalci da kuma kokarin yada addinin Allah da kaunar alheri ga mutane, wannan ke nuna cewa jihadi a musulunci ba wai anayi bane dan kwadayin tara abun duniya.
Kuma kafin fara yaki za’a bada zabi tsakanin shiga musulunci ko kuma bada jiziya ga wanda bai san shiga musuluni yana san ya tsaya ne a addinin sa, kuma ita jiziya wani dan kudi ne mara yawa wanda ake baiwa daular musulunci, kuma ita kashi uku ce:
1- abunda ake karba daga mawadata.
2- abunda ake karba daga matsakaitan mutane na daga iyan kasuwa da manoma.
3- abunda ake karba daga ma’aikata da masu aikin hannu wadanda suke samun aiyuka.
Kuma wannan kudin ana karbar su saboda kariya daga dukkan makiyi na waje da kuma kulawa da kuma tsare mutuncin su da dukiyoyin su da rayukan su da kuma jin dadi da irin abunda musulmai ke jin dadi da shi, Khalid dan Walid Allah ya kara masa yadda a cikin daya daga cikin yakokin sa yana cewa: lallai ni nayi muku alkawari akan jiziya zamu baku kariya idan muka baku kariya to zaku bamu jiziya in kuma ba haka ba to kar ku bamu jiziya har sai mun kare ku “
Kuma jiziya ba wajiba bace akan dukkan kowa, a’a takan fadi akan talaka da yaro da mace da bayi da makafi da gajiyaiyu wadan da keda nakasu, kai musulunci ma ya kara dan ya daura wa daular musulunciwajibcin kula da wadannan da ciyar da su daga baitul mali na musulmai, saboda aikin sarkin muminai halifa na biyu Umar dan khaddabi Allah ya kara masa yadda lokacin da yaga wasi tsoho daga cikin yahudawa yana rokon mutane sadaka, lokacin da yayi bincike game da shi ya san cewa yana cikin masu bada jiziya, sai yace: zamu maka adalci,be kamata mu karbi jiziya a hannun ka ba lokacin kana matashi kuma mu wofintar da kai lokacin da ka tsufa, sai ya kama hannun sa ya tafi da shi gidan sa kuma ya bashi abunda ya samu na abinci da tufafi, sannan ya aika zuwa ga mai gadin baitul mali yana ce masa: ka duba gameda halin wannan da ireiren sa ka basu abunda zai ishe su da iyalansu daga cikin baitul mali, domin Allah madaukaki yana cewa: “lallai sadaka anayi ne ga talakawa da miskinai” talakawa sune musulmai, su kuma miskinai su ne ma’abota littafi-ahlul kitabi-
Kuma yazo acikin alkawarin Khalid dan Walid da yayi ga masu bada jiziya cewa: duk tsohon da bai iya aiki ko kuma wata cuta ta kama shi daga cikin cututtuka ko kuma da mawadaci ne sai ya talauce har ya zama wadanda suke addini daya ne ke bashi sadaka, to zamu sauke jiziyar da ke kansa, kuma za’a dinga biyansa gada baitul mal shi da iyalansa.
Wata me binciki iyar kasar Engila me suna (lise Lictenstadler) tana cewa: bada zabi a kasar farisa ruma be kasance tsakanin takobi ba ne ko kuma musulunci, a’a ya kasance ne tsakanin su musulunta ko kuma su bada jiziya kuma wanna ita ce hanya wanda ta cancanta da yabu, saboda hasken da ta kawo bayan an bita a ingila ya tabbatar da hukuncin sarauniya Elizebeth.  
Amma mu’amala da kafuranda aka kulla amana da su masu rayuwa a cikin daular musulunci, to ba’a zaluntar su, kuma babu mugunta a gare su kuma ba’a hana su hakkokin su ko kuma munanta musu mu’amala, Allah madaukaki yana cewa: “Allah baya hana ku game da wadanda basu yake ku ba a addini kuma basu fitar da ku daga gidajen ku ba ku kyautata musu kuma kuyi musu adalci lallai Allah yana san masu adalci (8)”  
Annabi (SAW) yana cewa: “ku saurara duk wanda ya zalunci kafurin da akayi yarjejeniya da shi ko kuma ya tauye shi ko kuma ya daura mai abunda yafi karfin shi ko kuma ya kwaci wani abu daga gare shi ba tare da san ransa ba to ni zanyi jayaiya da shi ranar alkiyama”
Wadannan sune ababen da muka tattara game da jihadi, amma duk me san karin bayani sai ya koma ya karanta littattafai wadanda aka rubuta su a wanan fagen.
BANGAREN TATTALI A MUSULUNCI
Dukiya itace jagorar rayuwa da abunda ke tallafa mata ta tsayu, shari’ar musulunci tana kokarin tsaida al’umma madaidaiciya ta bangaren shi, wanda dalci ke tabbatuwa akan su wadda ke samadda rayuwa ta karamci ga dukkan daidaikun da suke rayuwa a cikin ta, kamar yadda Allah madaukaki ya fada ne: “dukiya da iyaiya kawa ne na rayuwar duniya”  
Yayin da dukiya ta zama dole a mahanga ta musulunci daga cikin ababe na dole na rayuwa wanda ba wanda zai iya wadatuwa da ita daidakun mutane ko kuma jama’a-jama’a, sai ya wajabta wani kasu na musamman na dukiya wanda kae kaddara shi da 2.5% wanda ake kira “zakkah” ana karba daga dukiyar mawadata wanda tayi shikara, sai a raba ta ga talakawa, kuma hakika magana ta gabata game da haka, kuma ita hakki ce daga cikin hakkokin talakawa haramun ne aki bada ita.
Ba wai wannan yana nuna cewa musulunci ya jefar da cewa kowa nada hakkin ya mallaki dukiya bane da kuma kasuwanci daidaikun mutane na kebe, a’a musulinci ma ya tabbatar da ita kuma ya girmamata, kuma hakika nassoshi sun zo akan haramcin ta’addanci ga dukiyar wani da abubuwan da ya mallaka a cikin fadar Allah madaukaki: “kuma kada kuci dukiyoyin ku a tsakanin ku da barna “
Sai musulunci ya shar’anta wasu tsare-tsare wanda dabbaka su zai tabbatar da abunda ake bukata a isa zuwa gare shi na samar da kyakkyawar rayuwa ga kowane mutun daya daga cikin mutanen da suke zaune a cikin al’umma ta musulmai, sai yayi doka akan:
1- haramta riba dan hakan amfani ne da mutum yakeyi da kokarida kuma gumin dan’uwan shi mutum, da kuma karbar dukiyar shi ba tare da bashi wani canjin hakan ba, kuma su dukiyoyi suna da daraja me girma, kuma saboda abun da ke yaduwa na butulci game da riba a tsakanin mutane da kuma tattaruwar dukiya a hannun wasu kebantattun mutane a cikin jama’a, Allah madaukaki yace: “yaku wadanda sukayi imani kuji tsoran Allah kuma ku bar abunda yayi saura na riba in dai kun kasance ku muminai ne (279) in kuma kuka ki aikata haka to kuyi shirin yaki da Allah da manzansa in kuma kun tuba to kuna da asalain dukiyoyin ku baka zalunci kuma baza’a zalunce ku ba (279)”
2- shari’a ta kwadaitar akan bada bashi dan a magance matsalar riba da kuma hanyoyin ta.
3- kuma shari’a ta bada umarni akan a saurarawa wanda baida shi da kuma rashin kuntata mai, umarni na mustahabbi ba na wajibi ba – ga wanda yake dagewa dan biyan bashin da ke kansa amma me wasa da wargi banda shi-, Allah madaukaki yace: “in kuma ya kasance talaka ne to a jinkirta masa har sai ya samu “ , kuma hakika Buraidatal aslamy ya ruwaito cewa lallai Annabi (SAW) yace: duk wanda ya jinkirta wa wanda beda shi to yana da lada a kowace rana ninki biyu, sai yace masa: kowace rana sadaka irin bashinda yake bi kafin lokacin biyan bashin yayi, idan lokacin biyan bashin yayi sai ya jinkirta masa to ko wace rana yana da ladan sadaka ninki biyu na bashin da yake bi “
4- shari’a ta kwadaitar amma ba tare da tilastawa ba akan yafiyar bashi akan wanda ake bi bashi idan har biyan zai mai wahala kuma ya baiyana falalar hakan. Allah madaukaki yace: “kuma ku yafe shi ne yafi alhrri a gareku “ , kuma Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda yake so Allah ya kubutar da shi daga damuwa da bakin ciki a ranar alkiyama to ya yaye damuwar wanda baida hali ko kuma ya yafe masa”
5- ya haramta hadama da kuma taskacewa ko yaya kalar sa take, domin shi me taskacewa yana boye abincin mutane da abubuwan bukatun su har sai idan sun zama kadan a kasuwa sai ya fito da su ya tsabga irin kudin da hadamar shi da handamar shi suka yaddar mai, wanda hakan na haifar da cutarwa ga daidaikun al’umma, mawadaci da talaka duk daya suke, saboda fadar manzan Allah (SAW): “duk wanda ya boye abinci sai yayi tsada ya fitar da shi to shi me zunubi ne “
Abu yusuf dalibin imamu Abu Hanifa yana cewa: dukkan abunda boye shi yana cutar da mutane to wanna taskacewa ne koda kuwa zinari ne ko kuma azurfa”. Kuma duk wanda ya boye kayan amfani ana lissafashi cikin wadanda suka munana amfanuwa da hakkin su cikin abunda ya mallak, dan manufar hana boye kayan amfani shi ne hana cutarwa ga mutane, mutane nada bukatu daban-daban to boye baben amfanin su wana jefa mutane cikin wahala da kunci.
Kuma shugaba nada damar tilasta duk wanda ya boye kayan amfani akan dole ya siyar da su da riba matsakaiciya wanda ba cutarwa ga me siyarwa da kuma me siya, in kuma me kayan yaki siyarwa, to shugaba nada hakin dora hannun sa akan kayan ya saida su da matsakaiciyar riba dan ya toshe kofa ga wanda ransa ke raya masa shima ya boye kayan amfani da wannan aikin na shi da kuma amfanuwa da bukatar mutane wajen gallaza musu.
6- ya haramta jangali, shi ne abun da ake karba wajen dan kasuwa dan abashi damar siyar da wani kaya ko kuma bashi damar shiga da su gari, shi ne abunda ake kira haraji, saboda fadar Manzan Allah (SAW): “wanda ke karbar kudinharaji ga dan kasuwa bai shiga aljannah “ , dan hakan karbar abunda be hallata a karba bane da kuma baiwa wanda be halatta a gareshi ba ya karba, kuma duk wanda yayi taimako akan haka daga cikin masu tattarowa ko kuma marubuta ko kuma shaidu ko kuma iyan amsa duk zasu shiga cikin fadar Manzan Allah (SAW): “lallai duk tsoka da jinin da suka tsoro ta hanyar haramun to baza su shiga aljanna ba wutace tafi cancanta da su”
7- ya haramta tattare dukiya da kuma rashin bada hakkin Allah a cikin ta, na abunda zai kawu alheri ga daidaikun mutane da kuma dukkan jama’a da kuma amfani, dan ingantaccen wurin da ya kamata a aje kudi shi ne inda zasu dinga juyawa tsakanin mutane dan tattalin arziki ya amfana da shi da kuma dukkan mutane, Allah madaukaki yace: “kuma wadanda suke boye zinari da azurfa kuma basa jiyar da su dan daukaka kalmar Allah to kayi musu bushara da azaba me radadi (34)”  
Musulunci kamar yadda ya girmama mallakar daidaikun mutane ya sanya wasu hakkoki a cikin su da wajibai, daga cikinirin wadannan wajibai akwai wadanda suna kan me dukiyar ne na ciyarwa ga kansa da kuma wadanda yake daukar nauyin su na iyan uwansa wadanda dole ne ya ciyar da su, kuma daga ciki akwai wanda wajibi ne na daidaikun al’umma na zakkah da sadaka da kyautatawa, kuma akwai wanda wajibi ne na al’ummar sa na bada dukiya dan gina makarantu da asibitoci da gidajen marayu da masallatai, da dukkan abunda amfanin sa yana komawa ga al’umma ne, kuma ta hanyae wannnan aiki yana kokarin rashin taskace dukiya a wurin wasu daidaikun mutane daga cikin al’umma.
8- ya haramta rage kaili da ma’auni dan hakan wani nau’i ne na sata da sabce da yaudara da ha’inci, Allah madaukaki yace: “kalmar azaba ta tabbata ga masu tauye ma’auni (1) su ne wadan da idan suka siya a wurin mutane sai su ciki ma’auni (2) amma idan kuma suka siyar musu ko suka auna musu ai su dinga tauyewa suna ragewa (3) “
9- ya haramta babakere akan dukkan abun da amfanin sa gamamme ne ga dukkan mutane, kamar ruwa da wuraren shayarwa na dukkan dabbobi wanda ba mallakin kowa bane, da kuma hana wa mutane amfanuwa da su, saboda fadar manzan Allah (SAW): mutane uku Allah bazai yi magana da su ba ranar alkiya kuma bazai kalle su ba mutumin da yayi rantsuwa akan cewa ya siya kaya akan farashi sama da yanda ya siyar kuma alhali makaryaci ne da mutumin da ke rantsuwa ta karya bayan la’asar dan yaci dukiyar wani musulmi da mutumin da ya hana ragowar ruwa Allah zai ce a yau zan hana ka falalata kamar yadda ka hana ragowar abunda bakai wahala akai ba “ , kuma Annabi (SAW) yana cewa: “musulmai suna taraiya a cikin abubuwa uku, wurin kiyo da ruwa da wuta “
10- tsarin gado wanda ya raba kayan gado ga magada gwargwadan kusanci da nisanci da amfani ga mai dukiyar, ba wanda keda hakkin raba gado da san ransa da kuma yadda yake so, daga cikin kyawon wanna tsari shi ne yana gutsutsura dukiya duk yanda ta kai da yawa zuwa kananun rabo tayadda kowa zai samu, sai ya sanya al’amarin tattara dukiya a hannun wasu daidaikun mutane abu ne wanda kamar bazai yiwu ba, Annabi (SAW) yana cewa: “lallai Allah ya baiya dukkan me hakki hakkin sa to babu wasiyya ga wanda zaiyi gado “
11- tsarin wakafi, kuma shi iri biyu ne:
a) wakafi kebantacce ga iyalai da zurriyar me wakafin, dan ya kange su daga talauci da fatar da kuma rokon mutane, yana daga cikin sharuddan ingancin sa shi ne amfanin wannan wakafin ya dawo ga aiyuka na alheri bayan karewar zurriyar wanda yayi wakafin.
b) wakafi na gamegare na alheri, ana nufin amfani da abun da aka yi wakafin sa ko kuma ribar sa akan aiyuka na alheri da kyautatawa na daga gina asibitoci da makarantu da hanyoyi da dakunan karatu na kowa da kowa da masallatai da gidajen raino na al’umma wanda suke kebantattu ga marayu da wadanda aka tsunto da gajiyaiyu, da dukkan abun da yake me kyaune amfanin sa na komawa ne ga al’umma, Manzan Allah (SAW) yana cewa: “idan mutum ya mutu to aikin sa ya yanke sai abubuwa guda uku sai dai fa sadaka me gudana ko kuma ilimi wanda ake amfanuwa da shi ko kuma yaro na gari wanda yake mai addu’a “
12- tsarin wasiyya a musulunci ta yadda msulunci ya shar’anta ga musulmi yayi wasiya daga dukiyar sa abun da za’a sa a cikin aiyukan kyautatawa da alheri, sai dai ya iyakance wannan wasiya da cewa kar ta wuce daya bisa uku na dukiya saboda kar ya cutar da magadan sa. An ruwaito daga A”mir dan sa’ad Allah ya kara masa yadda yace, Annabi (SAW) ya kaw mun ziyara banda lafiya a garin makkah, sai nace: inada dukiya zan iya wasiyya da dukiya ta dukkan ta, sai Annabi yace, a’a, sai nace, to rabi fa, sai yace:a’a, sai nace to daya bisa uku fa, sai yace: daya bisa uku, daya bisa uku nada yawa, lallai kai kabar magadan ka mawadata yafi alheri akan ka barsu talakawa suna rokon mutane da hannayen su, kuma duk abun da ka ciyarar to sadaka ne a gare ka hatta lomar da kake sawa a bakin matar ka “
13- ya haramta dukkan abunda zai shiga karkashin fadar sa madaukaki: “yaku wadanda sukayi imani kada ku dinga cin dukiyar ku a tsakanin ku da barna “ , ta hanyar kwace ko wane irin kala ne kuwa saboda abunda ke cikin sa na zaluntar mutane da kuma barna ga al’umma, saboda fadar manzan Allah (SAW): “duk wanda ya sabci hakkin dan’uwansa musulmi ta hanyar rantsuwar sa to Allah ya wajabta masa wuta kuma ya haramta masa aljannah, sai wani mjutum yace: koda dan kramin abu ne ya manzan Allah? sai Annabi yace: “koda silin icce ne bishiyar arak “
Kuma da sata, Annabi (SAW) yana cewa: “mazinaci bayayi zina a lkacinda yake zina yana mumini kuma barawo baya sata lokacinda yake sata yana mumini kuma mashayin giya bai shangiyalokacin yana mumini ita kuma tana na bayan haka “ , domin ita sata hawa kan dukiyar mutane ce ba tare da gaskiya ba, Allah madaukaki yace: “kuma barawo da barauniya to ku yanke hannayen guda biyu dan sakamakon abunda suka aikata danyi musu ukuba daga Allah kuma Allah mabuwayi ne me hikima(38)”
Kuma da yaudara da ha’inci, saboda fadar Manzan Allah (SAW): “duk wanda ya dauki makami akan mu to bai tare da mu kuma duk wanda ya ha’ince mu to bai tareda mu “
Kuma da karbar cin hanci, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma kada kuci dukiyoyinku a tsakanin ku da barna kuma ku dinga mikasu uwa ga shuwagabanni dan ku dinga cin dukiyoyin wasu mutane da batanci alhali kuna sani (188)”
Kuma da fadar manzan Allah (SAW): “Allah ya tsinewa me bada cin hanci da wanda aka baiwa cin hancin a wurin hukunci”  ,
Arrashi, shi ne me mika cin hanci, almurtashi, shi ne me karbar cin hancin, kuma a cikin wata ruwayar: da “dan tsakiya” shi ne na tsakiyar su, a tsina wa me mika cin hancin ne saboda yana taimakawa wajen yaduwar wannan barnan me cutarwa ga al’umma, inda bai bada ba da ba’a samu me karbar cin hancin ba, shi kuma me karbar cin hancin an tsine mai ne saboda ya cutar da wanda ya bashi cin hancin ta hanyar karbar dukiyar sa ba tare da wata fuska ta gaskiya ba, kuma saboda shi ya ci amanar da aka bashi, saboda yana karbar wani abu na dukiya akan abunda ya wajaba a kansa ya aikata, kari akan wasu cutarwan wadan da zasu iya afkawa me cin hancin, amma dan tsakiyan su, shi kuma saboda zai karba wani abu wanda ba hakkin sa ba daga wanda ya mika cin hancin da kuma wanda ya karbi cin hancin, kuma ya taimaka shima wajen yada wannan barnan.
14- ya haramta mutum yayi ciniki akan cinikin dan’uwan sa, sai dai fa in shi ne ya bashi izini, dan hakan na daga cikin abun da ke haddasa gaba da kiyaiya tsakanin daidaikun al’umma, Annabi (SAW) yana cewa: “kada mutum yayi ciniki akan cinikin dan’uwansa kuma kada ya nemi aure akan neman auren dan’uwansa sai dai fa in shi ne yayi masa izini “


BANGAREN ZAMANTAKEWA A MUSULUNCI:
Musulunci yazo da tsare-tsare na zamantakewa kyawawa, ana iyakance hakkoki da wajibai na kowane mutum dan zamantare ya mike, daga cikin wadannan hakkoki da wajibai akwai wadanda kebantattu ne akwai kuma wadanda na kowa da kowa ne.
1- hakkin shugaba akan mabiya:
-ji da kuma biyaiya acin abun da ba sabon Allah bane, za’a mai biyaiya ne matukar bai yi umarni da sabawa Allah ba, yi masa biyaiya yiwa Allah biyaiya ne kuma saba masa sabawa Allah ne, Allah madaukaki yana cewa: “yaku wdanda sukayi imani kuyi wa Allah biyaiya kuma kuyi wa manzo biyaiya da kuma shuwagabanni daga cikin ku “
- yi masa nasiha da rashin yaudarar shi, ta hanyar tausasawa da saukakawa hakan kuwa ta hanyar fadakar da shi zuwa ga abunda zai amfane shi da talakawan sa, da kuma tuna masa bukatun talakawa, Allah madaukaki yana cewa ga Annabi Musa da dan’uwansa Annabi Harauna lokacin da ya aikesu zuwa wurin fir’auna dan su kirashi zuwa ga Allah: “kuma kuyi mai magana magana me taushi wata kila shi zai wa’azantu ko kuma ya ji tsoran Allah (44)”
-taimaka masa lokacin tsanani d damuwa da rashi yi masa tawaye da kin taimaka masa da tabar da shi.
2- hakkin mabiya akan shugaba:
Lallai hakkin mabiya akan shugaba suna shiga karkashin wasu mahimman abubuwa biyar, su ne:
a) yin adalci a tsakanin su, aba kowane me hakki hakkin sa, wajibi ne akan sa yayi adalci a cikin hakkoki da kuma adalci a cikin wajibai, da kuma yin adalci wajen rabaaiyuka, da kuma yin adalci wurin hukunci, kowa a wurin sa daya ne, ba fifita wani akan wani, kuma babu karkata daga wasu jama;a zuwa wasu jama’ar, saboda fadar Manzan Allah (SAW): “lallai mafi soyuwar mutane a gun Allah ranar alkiyama kuma wanda wurin zamansa fafi kusa da shi shi ne shugaba me adalci, kuma lallai wanda Allah yafi ki cikin mutane ranar alkiyama kuma yafi su shan azaba shi ne shugaba azzalumi” , kuma da fadarsa (SAW): “lallai wanda yafi kowa shan azaba ranar alkiyama shi ne azzalumin shugaba “
b) rashinzaluntar sa da ha’intar sa da yaudarar sa ga mabiyan sa, Annabi (SAW) yana cewa: “babu wani bawa wanda Allah zai bashi jagorancin al’umma sai ya mutum ran da ai mutu yana me ha’intar mabiyansa to sai Allah ya haramta masa shiga aljanna “
c) yin shawara da su a cikin al’amuran da suke da alaka da maslahar su ta siyasa da zamantakewa da tattali – shawartawa cikin abunda babu nasssi akai – da kuma basu iyanci da kuma dama ta baiyana tunanin su da ra’ayoyin su da abunda suke gane da kuma baiyana su, da kuma karbar wadannan ra’ayoyi idan har ya baiyana cewa akwai amfani a cikin su, Allah madaukakai yace: ““saboda rahamar Allah ce ka zama me tausasa musu da zaka kasance me tsanani me kaushin hali da sun watse daga gefen ka to kayi musu afuwa kuma ka nema musu gafara kuma kayi shawara da su a cikin al’amurra “(suratu a’li imran: a’ya ta 109)
annabi (SAW) a yakin badar lokacin da ya sauka a wani wuri bayan rijiya me ruwa sai wani daga cikin sahabbai ya tambayeshi Allah ya kara masa yadda, sai yace ya manzan Allah:shin wannan wurin Allah ne yace ka sauka a wannan wurin koko dubara ce ta yaki? Sai Annabi yace: dubara ce ta yaki, sai sahabin yace: to ya kamata ne mu tsaya a gaban rijiyar dan mu hana makiya isowa gare ta, sai annabi (SAW) ya inganta ra’ayin sa kuma yayi aiki da shi “
d) ya zama inda zai dinga ciro hukunci da tsare-tsare wanda zai yi mu’amala da mabiyan sa da su shi ne shari’a, ra’ayi baida mashiga ko kuma sanrai da hukunce-hukunce marasa kangado wadanda zasu iya kuskure kuma zasu iya yin daidai, Umar dan khaddabi Allah ya kara masa yadda halifa na biyu, bayan ya karbi halifanci sai yace wa Abu marya assaluly wanda ya kashe dan’uwansa Zaida dan khaddab (wallahi ni ina sanka har sai kasa ta so jini) sai yace: shin haka bazai yuwu bane? Sai umar yace:a’a, sai yace: to babu damuwa, dama damuwata kawai akan soyayyar mata ne.
e) rashin kangewa daga talakawan shi da rufe kofa a fuskokin su, ko kuma yi musu girman kai, da kuma sanya iyan iso tsakanin shi da su, suna bada izini ga wanda suka so kuma suna hana wanda suka so, saboda fadar Manzan Allah (SAW): “duk wanda ya jibinci wani abu cikin al’amuran musulmai sai ya kange daga biya musu bukatun su da damuwar su to shima Allah zai kange daga gare shi ranar alkiyama tsakanin abokan sa da bukatun sa da damuwar sa “
f) tausayin sa ga talakawan su da kuma rashin dora musu abun da basu iyawa ko kuma takura musu cikin rayuwar su, Ananbi (SAW) yana cewa: “ya Allah duk wanda ya jibinci wani abu cikin al’amarin al’ummata sai ya tsananta musu to shima ka tsananta masa, kuma duk wanda ya jibinci wani lamari na al’umma ta sai ya tausaya musu shima ka tausaya masa “
Umar dan khaddabi Allah ya kara masa yadda yana baiyana hadarin wannan lamari inda yake cewa: “walahi da wata rakuma zata yi tuntube a garin iraki to sai na ji tsoran kada Allah ya tambayeni game da ita ranar alkiyama dan me ban shinfida mata hanya ba “
Lallai shugaba musulmi yana wajaba ya zama kamar yadda Alhasan albasri ya siffanta shi a cikin wata wasika da aika da ita zuwa ga Umar dan Abdulaziz Allah yayi masa rahama inda yake cewa a cikin ta: “ka sani ya kai shugaban muminai lallai Allah ya sanya adalin shugaba me gyara ne ga dukkan abunda ya karkata kuma me hanawa ne ga dukkan azzalumi kuma gyara ne ga dukkan abunda ya baci kuma karfi ne ga dukkan me rauni kuma me adalci ne ga dukkan wanda aka zalunta kuma wurin shi dukkan mabukaci ke zuwa. Kuma shi adalin shugaba ya kai shugaban muminai kamar makiyayi ne da ke tausayawa rakuman sa me tausayin da yake nema mata mafi kyawun wurin kiwo kuma yake koreta daga wurin halaka kuma yake kare su daga zakuna kuma yake nema musu inuwa saboda su kubuta daga cutarwar zafin rana da kuma gajiyar tafiya.
Kuma shi shugaba me adalci ya kai shugaban muminai kamar mahaifi ne ma karamci ga yaransa yana kokari dan su kuma yana basu ilimi bayan sun girma, yana fita nema musu abinci a halin rayuwar sa kuma yana tattala musu bayan mutuwa.
Kuma shi shugaba me adalci ya kai shugaban muminai kamar mahaifiya yake me tausayi me kyautatawa ga yaranta,ta dauki cikin sa tana wahala kuma ta kula da shi yana karami bata bacci in baiyi ba kuma tana samun natsuwa da samun natsuwar sa tana shayarda shi wani lokaci kuma tana yaye shi wani likacin kuma tana farinciki da lafiyar sa kuma tana damuwa da abun da ke damun sa.
Kuma shugaba me adalci ya kai shugaban muminai shi ne wasiyyin marayu kuma ma’ajiyin miskinai yana rainan karamin su kuma yana kulawa da manyan su.
Kuma shugaba me adalci ya kai shugaban muminai shi ne dan tsakiya tsakanin Allah da bayin sa, yana jin maganar Allah sai ya isar musu da ita.....kada ka kasance ya kai shugaban muminai cikin abun da Allah ya mallaka maka kamar bawanda me gidan sa a amince masa kuma ya ba shi tsaran dukiyar sa da iyalan sa sai ya halaka dukiyar kuma ya kora iyalan.
Kuma ka sani ya kai shugaba muminai lallai Allah ya saukar da haddi dan ya tsawar da su game da munanan abubuwa da alfahasha to ya kake gani idan wanda ke kula da su ne ya aikata su, lallai Allah ya sanya kisasi rayuwa ne ga bayin sa to ya kake gani idan wanda zai karbar musu hakki shi ne wanda ke kisan?
Kuma ka tuna mutuwa da abunda zai faru a bayan ta ya kai shugaban muminai da kuma karancin mabiyanka da kuma mataimakan ka akan ta, to sai kayi tattali dan zuwan ta da kuma abun da ke bayan ta na babban tashin hankali ranar alkiyama.
Kuma ka sani ya kai shugaba muminai kana da matsayi banda matsayinda kake ciki yana nan yana bibiyan ka kuma masoyan ka zasu rabu da kai zasu saka ka a cikin sa kai kadai tilo sai kayi shiri dan shi, zai abokan ce ka: “ranar da mutum ke gudan ma dan’uwan sa da mahaifin sa da mahaifiyar sa da matar sa da iyaiyan sa “
Kuma ka tuna fadar Alah ya kai sarkin muminai “idan aka tada abun da ke cikin kaburbura kuma aka fitar da abun da ke kiraza “to duk wani siiri a ranar a baiyani yake, shi kuma littafi “baya barin wani karamin abu ko kuma babba sai ya lissafa su “to yanzu ya kai shugaban muminai kanada dama kafin ajali ya riske ka, da kuma yankewa duk wani buri.
Kada kayi hukunci ya kai shugaban muminai ga bayin Allah da hukuncin jahiliyya kuma kada ka bi da su hanyar azzalumai kuma kada ka dora masu girman kai akan masu rauni domin su basa jin tsoran Allah game da su kuma ba ruwansu da dangi ko alkawari sai ka dauki laifinka da kuma wani laifin tare da naka, kuma sai ka dauki wani nauyi akan nauyin ka, kuma kada wadanda suke cikin ni’ima saboda kai su rudeka kuma suke cin me dadi da tafiyar me dadin ka a lahirar ka, kada kayi dubi zuwa ga kokarin ka a yau sai dai kayi dubi zuwa ga kokarin ka gobe alhali kai kana daure a tarkon mutuwa da kuma tsayuwar ka a gaban Allah a cikin taron mala’iku da Annabawa da manzanni kuma hakika “kuma fuskoki sun kaskanta ga rayiye dawwamamm “kuma lallai ni ya kai shugaban muminai dk da ban kai inda ma’abota hankula suka kai ba da wa’azi na to ni ban boye maka tausayi na da nasihata ba to ka aje wannan wasika tawa a matsayin me baiwa masoyin sa magani yana bashi magani masu daci saboda abunda yake mai fata a cikin hakan na samun waraka da lafiya, kuma amincin Allah ya tabbata a gareku ya kai shugaban muminai da rahamar Allah da albarkar sa “.
3- hakkin iyaye:
Kuma shi ne yi musu biyayya – matukar basuyi umarni da sabon Allah ba – kuma da rashin saba musu da kuma kyautata musu ta hanyar basu dukiya da basu kyaututtuka, da samar da abunda suke bukata na dolen rayuwa na abinci da abin sha da tufafi da wurin zama, da kuma kaskantae da kai a gare su a wurin magana da kuma rashin daga kai a gare su, da kuma hakuri akan yi musu hidima da kuma kulawa da damuwar su, babu yin labarin da zai cutar da su kuma ya sa su a damuwa kuma babu sa su bakin ciki, Allah madaukaki yana cewa: “kuma ubangijin ka ya hukunta cewa kada ku bautawa kowa sai shi kuma iyaye a kyautata musu idan har dayan su ya kai matake na girma suna tre da kai ko kuma dukkan su biyun to kada kace musu tur kuma kada kayi musu tsawa kuma ka fada musu magana magana me karamci (23) kuma ka saukar musu da fukafukan ka na kaskanci dan tausayi kuma kace ya ubangiji kayi musu rahama kamar yadda suka ji kan mu muna kanana (24) “
Kuma usulunci ya lissafa saba msu cikin manya-manyan zunubai, an ruwaito daga Abdylahi dan Amru Allah ya kara masa yadda yace: wane balarabe yazo wurin Annabi (SAW) sai yace ya manzan Allah: meye manyan zunubai? Sai Annabi yace: su ne yi shirka da Allah sai yace, sai me? Sai Annabi yace: sai sabawa iyaye, sai yace: sai me? Sai Annabi yace: sai sabawa iyaye,yace sai me? Sai Annabi yace: sai rantsuwar karya, sai nace, meye rantsuwar karya? Itace wadda me yinta ke cin dukiyar musulmi da ita alhali makaryaci ne “
Kuma saboda musulunci ya baiyana darajar iyaye, Annabi (SAW) yana cewa: “yandar Allah na cikin yaddar iyaye kuma fushin Allah na cikin fushinniyaye “
Kuma wadannan hakkokin wajibai ne ga iyaye,koda kuwa sun saba maka a adddini, an ruwaito daga Asama’u iyar Abubakar assiddiq Allah ya kara musu yadda tace: mahaifiyata tazo wuri na alhali tana mushirika a zamanin manzan Allah (SAW) sai na tambaye manzan Allah (SAW) nace: lallai mahaifiyata ta zo wuri na kuma tana kwadayin kawo min ziyara, to zan iya sada zumunci na da ita? Sai Annabi yace: eh ki sada zumuncin mahaifiyar ki “
Kuma mhaifiya tana gaban mahaifi wurin kyautatawa da zumunci da tausayawa da tausasawa, saboda hadisin Abu huraira Allah ya kara masa yadda yace, lallai wani mutum yace wa Annabi (SAW): ya manza Allah, waye cikin mutane yafi cancanta in kyautata masa sai yace, mahaifiyar ka sai mahaifiyar ka sai mahaifiyarka sai mahaifin ka sai na kasa da kai sai na kasa da kai “ , sai ya kebance uwa da hakkoki guda uku shi kuma uba da hakki daya, ba dan komai ba sai dan ita uwa tana daukar wahalhalu da kunci wanda uba baya daukar irin su, ita uwa kamar yadda Allah ya bada labarin ta ne a cikin fadar sa: “kuma munyi wasiya ga mutum game da iyayensa ya kyautata musu mahaifiyar sa ta dauki cikin shi cikin wahala “ , ita tana wahaluwa wajen daukar cikin sa a cikin cikin ta yana ci daga abincin ta, kuma tana wahala wurin haifar sa, kuma tana wahala warin shayar da shi, da kuma rashin bacci saboda shi bayan haihuwar shi.
4- hakkin miji akan matar sa:
a) jagoranci, yana daga hakkinsa ya zama jagora gameda harkokin gida dan zartar da abun da yake ganin malaha ne ga iyali, saboda fadar Allah madaukaki: “mazaje su ne jagorori akan mata saboda abun da Allah ya fifita sashin su akan sashi da kuma abunda suka ciyar daga dukiyar su “
 saboda su maza- mafi yawa- suna amfani da hankulan su wajen magance wani abu da ya faru, sabanin mata, su tausayi shi ne abunda ya fi rinjaye game da aiyukan su, kuma wannan ba wai yana nufin cewa kada ayi shawara da ita ba da kuma saurarar ra’ayin ta cikin abunda ya kebanci rayuwar su ta aure.
b) yi masa biyaiya matukar beyi umarni da saban Allah ba, an ruwaito daga Aisha Allah ya kara mata yadda tace: nace: ya manzan Allah, waye hakkin sa yafi girma akan mace a cikin mutane? Sai yace: mijin ta, sai nace: to waye hakkin sa yafi girma akan namiji cikin mutane? Sai yace” mahaifiyar sa “
c) kada dora masa abun da bai iyawa kuma kada ta nemi abunda baida shi kuma bai iya samu.
d) ta kiyaye dukiyar sa da yaran sa da mutuncin sa,Annabi (SAW) yana cewa: “mafi alherin mata itace wacce in ka kalleta sai ta faranta maka rai kuma in ka bata umarni sai tayi maka biyaiya kuma idan kayi tafiya ka barta sai ta kiyaye ka gameda kanta da dukiyar ka ya ce, sai ya karanta wannan ayar:(mazaje tsayaiyu ne akan mata) har zuwa karshen ayar “
e) kada ta shigarda wanda bai so cikin gidansa, Annabi (SAW) yana cewa: “lallai kunada hakki akan matan ku kuma matanku suna da hakki akan ku amma hakkinku akan matanku kada su zaunar da wani akan shimfidar ku wanda bakwa so kuma kada suyi izini ga wani ya shiga gidanku wanda kuke ki ku saurara su kuma hakkin su akan ku shi ne ku kyautata musu wajen tufafin su da abincin su “
kuma hakika musulman farko sun kasance suna dabbaka wadannan wasiiiyoyi na shari’a, an samo daga Auf iyar muhallam ash shaibany tana yiwa yarinyar ta wasiyya lokainda zatayi aure tace mata: “ya ke iya ta! Lallai ke kin rabu da gidanku wanda daga ciki kika fito da bukkarki wadda a ciki kika girma zuwa wani utum wanda baki saniba kuma abokin zama wanda baki saba da shi ba, to ki zama kamar uwa a gare shi, zai zama kamar bawa a gare ki kuma ki kiyaye masa halaye guda goma zasu zama masu taimako a gareki:
amma na fark da na biyu: kaskantar da kai a gare shi da wadatar zuci da kuma jin maganar sa da biyaiya.
Amma na uku da hudu: ki kiyaye idansa da hancin sa, kada idansa ya fada akan wani abunda baya so a gare ki kuma kada ya shaki kamshin wani abu sai mafi dadin kamshin ki.
Amma na biyar da shida: ki kiyaye lokacin baccin shi da cin abincin shi, domin damuwar yinwa tana rikitarwa kuma damu lokacin bacci yana fustarwa.
Amma na bakwai da takwas: tsare dukiyar shi da kare mutuncin iyalin shi, kuma mattarar al’amarin gameda dukiya shi ne kyautatawa wajen juya su kuma game da iyali shi ne iya kula da su.
Amma na tara da goma: kada ki saba masa wani umarni kuma kada yada wani sirrin shi in kuma kika saba umarnin shi ko kuma kika sa damuwa a kirjin shi kuma kika yada sirrin shi to kada ki kiyi tunanin za ki aminta daga makircin shi.
Sannan kada kiyi farinciki lokacin da yake cikin damuwa da kuma bata rai lokacin da yake cikin farin ciki.
5- hakkin mata akan mijin ta:
a) sadaki, kuma shi hakki ne na wajibi ga mace akan mijin ta, saboda fadar Allah madaukakai: “kuma ku ba mata sadakin su da dadin rai in kuma sun baku wani abu daga cikin sa da san ransu to ku ci shi kuna masu jin dadi da annashuwa (4)”
b) adalci da daidaito- ga me mata biyu ko sama da haka- ya wajaba a kanshi yayi adalci tsakanin wurin abinci da abin sha da tufafi da wurin zama da kwana, saboda fadar sa (SAW): “duk wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ga dayar su zai zo ranar alkiyama barin jikinshi a karkace “
c) ciyar da su da yaran su, ya wajaba akan miji ya samar da wurin zama da ya dace da neman abunda rayuwa ke tsayuwa da su na abinci da abin sha da tufafi da kuma bata kudi dan bukatun ta, amma gwargwadan yadda zai iya da kuma samun sa, saboda fadar Allah madaukaki: “mawadaci ya ciyar daga wadatar sa shi kuma wanda aka kuntata masa arzikinsa to ya ciyar daga abunda Allah ya bashi Allah baya dora ma wata rai wani abu sai daidai da abunda ya bata”
kuma saboda musulunci ya kwadaitar da musulmai kuma ya zaburar da su akan haka sai ya sanya wannan ciyarwa cikin sada wadda ake bashi lada akanta, saboda fadar sa (SAW) ga Sa’ad dan Abi wakkas”.....kuma lallai kai duk yadda ka ciyar na wani abu to sadaka ne a gare ka hatta ma lomar da kake sawa a bakin matar ka...”
kuma tanada hakkin diba cikin dukiyarsa batare da sanin sa ba idan yayi musu kwauro ita da yaranta wajen ciyarwa,saboda hadisin Hindu iyar Utbah, lallai ita tace: ya manzan Allah: lallai Abu sufyan mutum ne me kwauro kuma baya bani abunda ke isana ni da yarana sai da fa abinda na dauka daga gare shi alhali bai sani, sai yace: “ki diba abunda zai iysheki da yaranki daidai da al’ada”
d) kwana da mu’amala, kuma su suna cikin hakkoki masu mahimmanci wanda shari’a ta nema miji ya sauke su da kuma kulawa da su,ita matsayinta na mata tana bukata wata zuciyar da zata bata kulawa da kuma miji wanda zai dinga wasa da ita kuma yana kosar da bukatar ta har kada ta bukaci yin wasu abubuwa wanda karshen su ba kyau.
e) kiyaye sirrorin ta da kuma rashin fallasa aibinta da kuma boye abunda yake gani da wanda yake ji daga gare ta da kuma kiyaye abun da ke tsakanin su na kebantacciyar alaka, saboda fadar sa (SAW): “lallai cikin mafi sharrin mutane a wurin Allah ranar alkiyama shi ne mutumin da zai isa ga matarsa ya biya bukatar sa itama ta biya bukatar ta sai kuma ya yada sirrin ta “
f) yi mata kyakkyawar mu’amala da zama me dadi da ita da kyautatawa da yin shawara da ita cikin al’amuranda suka shafi rayuwar su, kada ya kadaita da ra’ayisa kuma ya dungga wajabta abunda ya zartar, kuma ya sama mata hanyoyin jin dadi da walwala na baiyana mata gaskiyar kauna,ta hanyar zaulayar t da yi mata wasa da tausaya mata, saboda fadarsa (SAW): “mafi cikin muminai imani shi ne wanda yafi su kyawon dabi’a kuma mafiya alkairin ku sune mafiya alkairi ga matan su “
g) hakuri akan cutarwar ta da kuma jurewa kurakuranta, kuma ba’a bin diddiginta, Annabi (SAW) yana cewa: “kada mumini ya ki wata mumina in ya kyamaci wata dabi’a daga gare ta to zai so wata da’ar daga gareta”
h) kishinta da kula da ita, kada ya je da ita wurare na sharri da fasadi, saboda fadar Allah madaukaki: “ya ku wadanda sukayi imani ku kare kawunan ku da na iyalan ku daga wuta kuma abun kunnata sune mutane da duwatsu “
i) tsare mata dukiyar ta ta musamman, kada ya diba komai a cikin tasa da izinin ta kuma kada ya taba sai da sanranta da kuma amincewar ta da kuma sanin ta, Allah madaukaki yana cewa: “kuma kada ku ci dukiyoyin ku a tsakanin ku da barna “ , kuma Annabi (SAW) yana cewa: “dukiyar mutum musulmi bata halatta sai da san ransa “
6- hakin makusanta (dangi):
Su ne iyalin mutum da dangin sa da wadanda suke da zumunci da shi, musulunci ya kwadaitar akan sada zukuncin su da dukiya-in me wadata ne- da hanyar biyan bukatun su da taushe damuwar su daga zakkar shi da sadakar shi, da kuma sada zumunci na ma’ana ta hanyar tambayar halinda suke ciki da bibiyan halayen su da tausaya musu da yin taraiya da su cikin bakin cikin su da farin cikin su, Allah madaukaki yace: “kuji tsoran Allah wanda kuke tambaya dan shi kuma kuji tsoran zumun ta “ , kuma hakika musulunci ya kwadaitar da musulmi akan sada zumunci koda su basa sada zumuncin, kuma ya yafe musu koda sun zalunce shi kuma sun munana masa, kuma ya kusance su koda suna yin nesa da shi kuma suna munana masa, saboda fadar sa (SAW): “me ramuwa ba shi ne me sada zumunci ba, shi me sada zumunci shi ne wanda in aka yanke zumuncin sa sai ya sadar da shi “
Kuma musulunci ya tsawatar akan yanke zumunci da rashin sada ta kuma ya sanya hakan cikin manyan zunubai, Annabi (SAW) yana cewa: “Allah ya halicci halitta bayan ya gama da su sai zumunta ta mike ta ce, wannan shi ne matakin da ka dauka ga me yanke zumunci, sai Allah yace: ashe be wadatar da ke ba in sada wanda ya sada ki kuma in yanke wanda ya yanke ki sai tace eh hakan ya ishe ni ya Allah sai yace to na baki wannan matsayin, sai Abu huraira ya karanta wannan ayar ((ashe ku ba kunyi saboba in kuka juya baya zakuyi barna a bayan kasa kuma ku yanke zumuntar ku (22)))
7- hakkin yara:
a) yana cikin kula da rayuwar su da damuwa da lamuran su da kulawa da tarbiyyar su da samar da bukatun su na abinci da abin sha da tufafi da wurin zama, saboda fadar sa (SAW): “ya isa mutum girman laifi ya tozarta wanda yake daukar nauyin su “
b) zaba musu sunayen da suka dace, saboda fadar sa (SAW): “lallai ku za’a kiraku ne ranar alkiyama da sunayen ku da sunayen iyayen ku to ku kyautata sunayen ku “”
c) kafa dabi’u kyawawa a zukatan su, kamar kunya da girmama na gaba da gaskiya da amana da bin iyaye...da sauran su, da nisantar da su munanan halaye na zance da aiyuka kamar karya da yaudara da ha’inci da sata da sabawa iyaye,,,,d sauran su.
d) da koyar da su ilimi me amfani da koya musu tarbiya ta kwarai da nema musu abokai na kwarai, Annabi (SAW) yana cewa: “dukkan ku makiyaya ne kuma dukkan ku za’a tambaye ku game da kiwon ku shugaba makiyaye ne kuma za’a tambaye shi game da kiyan sa kuma mutum makiyayi ne ga iyalan sa kuma za’a tambaye shi game da kiwan sa kuma mace a gidan mijin ta me kiyo ce kuma za’a tambaye ta game da kiyan ta kuma me hidima ma kiyayine a dukiyar me gidan sa kuma za’atambaye shi game da kiwan sa “
e) kwadayi akan zaman lafiyan su ta hanyar rashin yi musu muguwar addu’a, Annabi (SAW) yana cewa: “kada kuyi muguwar addu’a akan kawunan ku ko kuma yaran ku ko kuma iyan aikin ku ko kuma dukiyar ku dan kada ku dace da lokacin amsar addu’a daga Allah madaukaki sai ya amsa addu’ar ku “
f) kamar yadda wajibi ne ayi adalci a tsakanin su da kuma rashin fifita sashin su akan sashi wajen kyauta da kuma wurin mu’amala ta tausayawa, domin rashin daidaito a tsakanin su zai janyo saba wa iyaye da kuma sanya gaba a tsakanin su, an ruwaito daga Nu’uman dan bashir Allah ya kara masa yadda yace: babana ya bani sadakar wasu kudi na shi sai mamata Amratu iyar Rawaha tace, bazan yadda ba har sai ka shaidawa Manzan Allah (SAW), sai babana ya tafi wurin Annabi (SAW) dan ya shaida masa sadakar da ya bani sai Manzan Allah (SAW) yace masa: “shin ka ba wa dukkan sauran yaranka irin haka? Sai yace:a’a, sai Annabi yace: “ku ji tsoran Allah kuma kuyi adalci tsakanin yaran ku” sai babana ya amshe wannan sadakar da ya bani”
8- hakkin makwabta:
a) musulunci yayi umarni da kyautatawa makwabta da dukkan ma’anar kyautatawa, saboda fadar Allah madaukakai: “kuma ku bautawa Allah kada kuyi shirka da shi da komai kuma ku kyautatawa iyaye da makusanta da marayu da miskinai da makwabci na kusa da mkwabci na gefe da aboki na kusa da matafiyi da abunda hannayenku suka mallaka lallai Allah baya san duk wanda ya kasance me takama me yawan alfahari (36)”
b) kuma ya haramta cutar da makwabci shin da magana ne ko aiki, an ruwaito daga Abu huraira Allah ya kara masa yadda yace, ancewa Annabi (SAW): “lallai wacce tana azumi da rana kuma tana tsayuwar dare amma tana cutar da makwabtanta da harshen ta sai yace: “babu alheri a cikin ta tana wuta” sai aka ce: ita kuma wacci tana sallaolin farillane kawai kuma tana azumin ramadana kuma tana sadaka da da ragowar cikwi amma bata cutar da kowa da harshen ta sai yace: “tana aljannah”
c) kuma musulunci ya baiwa makwabci daraja me girma da hakki babba inda Annabi (SAW) yace: “jibirilu bai gushe ba yana mun wasiyya da makwabci har sai da nayi tunanin zaai sa yaci gado “
d) kuma ya lissafa cutar da shi cikin ababen da ke tauye imani, Annabi (SAW) yana cewa: “wallahi imani sa baya cikia wallahi imanin sa baya cika wallahi imanin sa baya cika “sai aka ce waye ne ya Manzan Allah: sai yace: shi ne wanda makwabcin sa be kbuta daga cutarwar sa ba “
e) kamar yadda yake kamata a jurewa cutarwar sa da kuma tausaya masa, waniutum yace wa Ibn Abbas Allah ya kara musu yadda: inada wani makwabci yana cutar da ni kuma yana zagi na kuma yana kuntata mun, sai yace masa: ka tafi in shi ya sabawa Alah gameda hakkin ka to kai ka yiwa Allah biyaiya game da hakkin sa”
kuma makwabt kashi uku ne:
-makwabci na jini, yanada hakkoki uku, hakki na dangantaka, hakkin makwabtaka, da hakkin musulunci.
- makwabci musulmi, yanada hakki biyu, hakkin makwabtaka da hakkin musulunci
- makwabcin da ba musulmi ba, yanada hakki daya, hakkin makwabtaka, Abdullahi dan Amr an yanka mai wata akuya a gidansa, lokacin da ya shigo sai yace: shin kai kyautan naman gidan makwabcin mu bayahude? Kun kai wa makwabcin mu bayahude? Naji Manzan Allah (SAW) yana cewa: “mala’ika jibrilu be gushe ba yana miniwasiyya da makwabci har sai da nayi zatan zai sa yaci gado “
9- hakkin abokai:
a) musulunci ya kwadaitar akan kulawa da abokai, kuma ya sanya wa abokantaka hakkoki wanda ya kamata a kiyaye su ga aboki na kyautatawa da yin nasiha, saboda fadar sa (SAW): “mafi alkairin abokai a wurin Allah shi ne mafi alkairin su ga abokin shi, kuma mafi alherin makwabci a wurin Allah shi ne mafi alheri ga makwabcin shi “
b) kuma ya sanya hakkokin su me zarcewa nw har bayan rasuwar dayan su, wani mutum daga kabilar bani salmata ya tambayi Manzan Allah (SAW) sai yace: ya manzan Allah, shin akwai ragowar wata biyaiya da zanyi ga iyaye na bayan rasuwar su? Sai yace: eh: “yi musu addu’a da nema musu gafara da zartar da alkawarin da sukayi a bayan su da sada zumuncin da ba’a sada shi sai da su da kuma girmama abokin su “
10- hakkin bako:
a) yana daga cikin hakkin bako a musulunci a karrama shi,saboda fadar sa (SAW): “duk wanda yayi imani da Allah da rana ta karshe to ya girmama makwabcin sa kuma duk wanda yayi imani da Allah da rana ta karshe to ya karrama bakon sa da zamansa” sai yace: me zaman sa ya Manzan Allah? sai yace: yini daya da dare daya da kuma liyafar kwana uku duk abunda ya wuce haka to ya zama sadaka a gare shi kuma duk wanda yayi imani da Allah da rana ta karshe to ya fadi alheri ko yayi shiru”  
b) kuma ya lissafa karrama bako cikin aiyuka masu falala, Annabi (SAW) yana cewa: “a cikin mutane babu kamar wanda ya ja linzamin dokin sa yaje jihadi dan daukaka kalmar Allah kuma ta nisanci sharrin mutane da kuma wani mutum a kauye a cikin dabbobin sa yana karrama bakon sa kuma yana kula da hakkin shi “
c) kuma ya sanya wasu ladubba na karrama baku, daga cikin su akwai kyakkyawan tarbar sa da murmushi a gare shi dakyautata rakiya a gare shi, manzan Allah (SAW) yace: “lallai Allah madaukakai karimi ne kuma yana san karamci da kuma kyawawan dabi’u kuma yana kin munanan su “
d)kamar kuma yadda yana wajaba shima bako ya kula da halin wanda ya bakunce shi yake ciki, kada ya dora mai abun da bazai iaya ba, saboda fadar sa (SAW): “be halatta ga musulmi ya tare wuin dan’uwansa har ya sa shi yayi zunubi” suka ce: ta yaya zai sha shi yayi zunubi ya mAnzan Allah? sa yace: a zauna a wurin shi alhalin baida abunda zai tarbe shi da shi “
Algazaly yana cewa a cikin littafin sa Ihya’u ulumuddin – daga manzan Allah (SAW) wanda shi ne abun koyin musulmai: kuma hakika manzan Allah (SAW) ya kasance yana karrama wanda ke zuwa wurin shi harma wani lokaci yana shinfida tufafinsa ga wanda baida wani kusanci tsakanin shi da shi sai ya zaunar da shi akai, kuma yana fifita wanda yazo mai sai ya bashi fulo wanda yake kishingida da shi, in ya ki amsa sa ya matsa masa har sai ya karba kuma babu wani bako da ya taba zuwa wurin sa har sai yaji cewa yafi kowa karamci har yakan bawa wanda ke zama tare da shi kasan sana murmushi har sai da wurin zamansa da jin sa da maganar sa da kyawawan tausasawar sa da shiryatarwar sa ga mazauna wurin sa, kuma majalisin sa duk da haka ya kasance majalisi ne na kunya da tawalu’u da amana, kuma hakika ya kasance yana kiran sahabban sa da alkunyar su dan girmamawa a gare su...kuma yafi kowa nesa da fushi kuma ya fi su saurin yadda.
11- hakkokin ma’aikata:
Kuma a bangaren aiki da ma’aikata musulunci yazo da tsare-tsare da ka’idoji wanda suke iyakance alakar me aiki da wadanda suke aiki tare da shi da kuma alakar su da ma’abocin aikin.
a) musulunci yayi umarni da cewa alaka tsakanin ma’abocin aiki da wanda ke kasan shi ta zama alaka ce ta iyan’uwantaka da kuma daidaito wurin mutuncin dan Adam, saboda eadar manzan Allah (SAW): “iyan’uwan ku masu aiki a karkashin ku Allah ya sanya su a karkashin kulawar ku duk wanda dan’uwansa ya kasance karkashin kulawar sa to ya ciyar da shi daga abin da yake ci kuma ya tufatar da shi daga abiunda yake tufafi da shi kuma kada ku dora musu abun da ze gallabe su in kun basu aiki to ku taimaka musu “
b) kuma ya tabbatar da hakkin m’aikaci cewa a bashi ladar sa,annabi (SAW) yace: “Allah madaukaki yace: mutum uku ni ne zanyi husuma da su ranar alkiyama, mutumin da yai alkawari da sunana sai yayi yaudara, da mutumi da ya siyar da da sannan ya ci kudin sa, da mutumin da ya dauki dan aiki da ya gama masa aikin sa sai ya ki basa hakki sa “
c) kuma yayi umarni da tambayar hakkin me aiki kafin ya fara aiki, Abu sa’ed ya ruwaito daga cewa: Annabi (SAW) ya hana daukar me aiki har sai ya baiyana masa hakkin sa “
d) kuma yayi umarni da bashi hakkn sa a take bayan ya gama abunda aka nema yayi, Annabi (SAW) yace: “ku ba me aiki ladar sa tun kafin gumin sa ya bushe “
e) kamar kuma yadda yayi umarni da rashin dora musu abunda yafi karfin su na aiki, in kuma hakan ya faru to ya zama dola a taimaka musu ta hanyar kara musu kudi ko kuma da jiki ta hanyar taya shi aiki, saboda fadar sa (SAW): “kada ku daura musus abunda zai galaba a kan su in kuma kun basu aiki to ku taimaka musu “
kuma dan musulunci ya daga darajar aiki sai ya sanya shi hanya mafi tsabta wajen neman arziki in ya kasamce ta halaliyar hanya, Annabi (SAW) yana cewa: “wani bai taba cin abincin da yafi alheri ba irin ya ci daga aikin hannun sa kuma lallai Annain Allah daud amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance yana cin abinci da aikin hannun sa “
koma dan kwadaitarwa akan aikin hannu, Annabi (SAW) yana cewa: “dayanku ya dauki igiyar sa sai yazo da curin itace a bayan sa sai ya siyar da su sai Allah ya tsare masa mutuncin sa da su yafi alheri a gare shi akan ya dinga rokon mutane sun bashi ko ko sun hana shi “
12- hakkokin wanda ya bada aiki:
Kamar yadda musulunci ya nemi wanda ya bada aiki ya kiyaye hakkokin ma’aikata to kuma ya nema suma ma’aikatan su kiyaye hakkokin wanda ya bada aiki, idan ya basu wani aiki ya wajaba su kyautata shi da kuma yin shi a mafi kyawon yanda ya kamata ba tare da jinkiri ba ko kuma takaitawa ba, saboda fadar sa (SAW): “lallai Allah yana san idan dayan ku yayi wani aiki ta ya kyautata shi “
Kuma dan ya kwadaitar da ma’aikata akan kyautatawa a wajen aiki sai ya sanya hanyar neman si itace mafi alherin hanyar neman arziki kuma tafi tsabta idan suka kyautata a cikin aiyukan su, Annabi (SAW) yace: “mafi alherin hanyar nema ita ce hanyar da ma;aikaci ya nema halal da hannun sa in ya kyautata “

Amma abunda ya shafi hakkoki da wajibai na baki daya:
1- hakika musulunci ya wajabta wa musulmi ya damu da halinda iyan’uwansa suke ciki a duk inda suke, Annabi (SAW) yana cewa: “zakaga muminai a wurin tausayawa junan su da kaunar junan su da tausasawa junan su kamar jiki ne guda daya idan wata gaba ta kamu da rashin lafiya sai sauran jiki baki daya ya kamu da rashin bacci da kuma zazzabi “
2- kuma yayi umarni akan kokarin inganta halinda suke ciki, Annabi (SAW) yana cewa: “imanin dayan ku baya cika har sai ya so wa dan’uwansa abunda yake so wa kansa “
3- da kuma mara musu baya yayin wata matsala da kuma damuwa, Annabi (SAW) yana cewa: “mumini ga mumini kamar gini ne sahi na karfafa sashi-sai ya hada sakanin yatsun sa” .
4- kuma yayi umarni da taimakon su da kai musu agaji in sun bukaci haka, Alalh madaukaki yace: “kuma idan suka nemi taimakon ku a cikin addini to ku taimaka musu sai dai fa in akan mutanen da akwai alkawari tsakanin ku da su kuma Allah me ganin abunda kuke aikatawa ne (72)”
5- kuma yayi hani akan tabar da su, manzan Allah (SAW) yana cewa: “babu wani mutum da zai tabar da dan’uwan sa musulmi a wani wuri wanda ake cin mutuncin shi kuma ake tauye darajar shi face sai Allah ya tabar da shi a wani wuri wanda yake neman a taimake shi, kuma babu wani mutum da zai taimake musulmi a wani wuri wanda ake tauye darajar shi kuma ake nakasa alfarmar shi face sai Allah ya taimake shi a wani wuri wanda yake bukatar taimako “

BANGAREN KYAWAWAN DABI’U A MUSULUNCI
Musulunci ya zo dan ya cika kyawawan dabi’u,Annabi (SAW) yana cewa: “an aikoni ne dan na cika kyawawan dabi’u”
Babu wata dabi’a me kyau face sai da yayi umarni da ita kuma ya kwadaitar akan ta, kumababu wata dabi’a mummuna face sai da yayi hani daga gareta kuma ya tsawatar akanta. Allah madaukaki yana cewa: “kayi rangwame kuma kayi umarni da kyakkyawa kuma ka kauda kai daga jahilai (199)”  kuma Annabi (SAW) yana cewa: “ko kunsan waye fallasashshe?! Sai suka ce: fallasashshe a cikin mu shi ne wanda baida kudi ko kaya, sai Annabi (SAW) yace: “fallasashshe a cikin al’ummata shi ne wanda zaizo ranar alkiyama da sallah da azumu da zakkah, amma zai zo ya zagi wannan, kuma yayi wa wannan kazafi, kuma ya zubar da jinin wannan, kuma ya daki wannan, sai aba wannan daga ladar sa, shima wannan daga ladar sa, idan ladan sa suka kare kafin abiya abinda ke kansa, sai a debo daga zunuban su sai a zuba mai sannan a jefa shi a cikin wuta “
Kuma ya baiyana irin tsarinda musulmi ke tafiya akai wajen alakar shida al’ummar sa da kuma alakar shi da wasu, manzan Allah (SAW) yana cewa: “ka kiyaye haramtattun abubuwa sai ka zama wanda yafi bauta a cikin mutane kuma ka yadda da abunda Allah ya baka sai ka zama mafi wadatar mutane kuma ka kyautata wa makwabcinka sai ka zama mumini kuma ka so wa mutane abunda kake so wa kanka sai ka zama musulmi kuma kada ka yawaita dariya domin yawaita dariya na kashi zuciya “ , kuma da fadar sa (SAW): “musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga cutarwar harshen sa da hannun sa kuma me hijira shi ne wanda ya kauracewa abunda Allah ya hana “
Kuma musulunci yana nufin samar da al’umma ce me hadin kai da tausayi me kaunar juna ta hanyar abunda yake umarni da shi ko kuma yake hani daga gare shi.

Bari mu ambaci wasu ababe da musulunci ya haramta dan misali ba iyakancewa ba:
1) ya haramta shirka da Allah, Alalh madaukaki yana cwa: “lallai Allah baya gafarta ma wanda yayi shirka da shi kuma yana gafarta abunda bai kai haka ba ga wanda ya ga dama”  
2) ya haramta sihiri, an ruwauto daga Abu huraira Allah ya kara masa yadda, lallai manzan Allah (SAW) yace: “ku nisanci abubuwa masu halakarwa shirka da Allah da sihiri “
3) ya haramta zalunci da mugunta, kuma shi da ma’anar da tafi gamewa shi ne ta’addanci ga wani da magana ko aiki, da rashin maida hakkokii ga ma’abotan su, Allah madaukaki yana cewa: “kace lalai ubangijina ya haramta alfahsha abunda ya baiyana daga cikin ta da kuma wanda ya boyu da zunubi da mugunta ba tare da wani hakki ba “suratul a’araf, aya ta 33.
4) ya haramta kisan wata rai wacce Allah ya haramta sai da hakki, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma duk wanda ya kashe mumini da gangan to sakamakon shi shine jahannama zai dawwama a cikin ta kuma Allah yayi fushi da shi kuma ya tsine masa kuma ya masa tanadin azaba mai grma (93)” suratun nisa’i, aya ta 93.
5) ya haramta yanke zumunta da kuma kauracewa dangi, saboda fadar Allah madaukaki: “shin ase baku saba ba in kuka juya baya kuma kuyi barna a bayan kasa kuma ku yanke zumuntan ku (22) to wadanan su ne wadanda Allah ya tsine musu sai ya kurumtar da su kuma ya makantar da ganin su (23)” , da kuma fadar sa (SAW): “me yanke zumunta bazai shiga aljanna ba “
Kuma bun nufi da yanke zumuntar su, shi ne rashin kai musu ziyara da binciken halayen su, da girman kai a gare su da rashin ziyartar masu rauni da talakawa daga cikin su, in ya kasance shi mawadaci ne to yana daga sada zumunci a kan shi kyautatawa da ihsani, domin sadaka akan talaka na nesa sadaka ce amma kuma akan talaka na kusa sadaka ce da kuma sada zumunci, in kuma talaka ne, to ya sada zumunci da sallama a gare su da kuma tambayar halin da suke ciki, da tausasa musu magana, da yi musu murmushi, saboda fadar sa (SAW): “ku sada zumuncin ku koda da sallama ne “
6) ya haramta zina da dukkan abun da ke kaiwa gareta, Alalh madaukaki yace: “kuma kada ku kusanci zina domin lallai ita ta kasance alfahsha ce da kuma mummnar hanya (32)” , badan komai ba sai dan kiyaye mutunci kada a keta su da kuma kare dabi’u daga barna, da kuma tsare al’umma daga rushewa, da kuma tsare nasaba da kuma rashin cakudata da abunda zai haifar na bada gado ga wanda bai cancanta ba da kuma aure da muharramai, da kuma kiyaye al’umma daga yaduwar mugayen dabi’u da kuma abunda zai haifar na yaduwar rashin lafiya da cututtuka, kuma hakika manzan Allah (SAW) yace: “ya ku taron muhajirai abu biyar in aka jarabceku da su kuma ina neman tsari ga Allah kar su riske ku to kun halaka, zina bata taba baiyana a cikin wasu mutane ba har suka baiyanata face sai annoba ta hadu a cikin s da yinwa wadda ba’a taba irinta ba a cikin al’ummar da suka gabata.....”
7) ya haramta luwadi, Allah madaukaki yana cewa: “lokacin da umarnin mu ya zo musu sai muka juya saman su ta koma kasan su kuma muka musu ruwan duwatsun na wuta a jere (82) masu alama daga wurin ubangijin ka kuma su ba nesa suke ba daga azzalumai (83)” , wato duka me aikata irin aikin su to ya kiyaye dan kar irin abunda ya same su shima ya same shi.
8) ya haramta cin dukiyar maraya, saboda abunda ke cikin haka na bannatar da hakkokin masu rauni, saboda fadar Allah madaukaki: “lallai wadanda suke cin dukiyar marayu bisa zalunci to lallai suna cima cikinsu wuta ne kuma zasu shiga cikin wutar sa’ira (10)”
 kuma hakika Allah ya togace wakilin maraya wanda yake talaka ne daga wannan alkawarin azabar,zai iya ci amma da kyautatawa dan kulawa da yakeyi da shi da kuma rainon shi da tsayuwa akan al’amuran shi na ciyar da shi da tufatar da shi da kuma jujjuya dukiyar shi da kasuwanci da ita a cikabunda zai komo ma marayan da alheri da amfani, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma duk wanda ya kasance mawadaci ne to ya kame kuma duk wanda ya kasance talaka ne to ya ci amma da kyautatawa “
9) ya haramta shaidar zur, kuma musulunci ya sanya ta cikin manyan zunubai, saboda abunda ke cikin wannan shaidar na halakar hakkoki a cikin al’umma, da kuma yaduwar zalunci, da kuma abunda ke cikin ta na munanawa ga wanda yayi shaida a gare shi na taimaka masa akan zaluncin shi da muguntar shi, da kuma munanawa ga wanda yayi shaida akan shi saboda hakkin shi ne zai halaka, Annabi (SAW) yana cewa: “ashe bazan baku labarin mafi girman zunubai ba?” sai suka ce:eh bamu labari ya manzan Allah, sai yace: shirka da Allah da kuma sabawa iyaye kuma lokacin ya kasance a kishingide sai ya zauna sai ya ce ku saurara da maganar zur da kuma shaidar zur da maganar zur da kuma shaidar zur yanata maimaitawa har saida nace bazeyi shiru ba”
10) ya hana caca da karta, saboda abunda ke cikin su na barnatar da karfin da Allah ya horewa dan adam da kuma barnatar da dukiya ba tareda wani amfani ba da zai koma daidaikun mutane ba da wa al’umma, Allah madaukaki yace: “lallai giya da caca da gumaka da kibau datt ne daga cikin aikin shaidan to ku nesance su ko zaku rabauta (90) “ , saboda in neman kudine to yaci dukiyar wanin sa da barna, kuma ma san yin nasara kan iya turashi zuwa yin amfai da wasu dubaru da zamba dan yaci nasara wani karan ma, in kuma shi yayi asara to ya barnata dukiyar sa cikin abunda baida amfani barnatarwar da zata iya sahi yin sata da fizge idan har abunda ke hannun sa ya kare na kudi dan ya sake komawa wasan wata kila ko zai dawo da abunda yayi asarar shi.
11) ya haramta rantsuwar karya me halakawa, ita ce wadda me yinta yake rantsewa akan karya da gangan dan ya ci hakkin wanin sa, an kirata me nutsarwa ne dan tana nutsarda me yinta a cikin wuta, Allah madaukaki yace: “lallai wadanda suke saida alkawarin Allah da rantsuwarsu da iyan kudade kadan to wadannan basuda rabo a lahira kuma Allah bazai yi magana da su ba kuma bazai dube su ba ranar alkiyama kuma bazai tsarkake su ba kuma suna da azaba me radadi (77)”
Da kuma fadar sa (SAW): “duk wanda yaci hakkin wani musulmi da rantsuwar sa to hakika Allah ya wajabta masa wuta kuma ya haramta masa aljannah” sai wani mutum yace masa: koda dan abu kadan ne ya manzan Allah? sai yace: “koda icce daya ne na bishiyar arak”
12) ya haramta mutum ya kashe kansa, Allah madaukaki yana cewa: “kuma kada ku kashe kawunan ku lallai Allah ya kasance me tausayi ne a gare (29) ku kuma duk wanda ya aikata haka yana me ta’addanci da zalunci to da sannu zamu jefa shi wuta kuma wanna me sauki ne a wurin Allah (30)”
Kuma Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda ya kashe kansa da wani abu to za’a azabtar da shi da wannan abun ranar alkiyama “
13) ya haramta karya da yaudara da ha’inci da sabawa alkawari, Allah madaukaki yace: “ya ku wadanda sukayi imani kada ku yaudari Allah da manzo kuma in kunyi hakato kun yaudari amanar ku alhali kuna sane (27)”  
Kuma Annabi (SAW) yana cewa: “abu hudu duk wanda suka kasance a cikin sa to ya zama tataccen munafuki kuma duk wanda abu daya ya kasance tare da shi to akwai alamar munafunci tare dashi har sai ya daina: idan aka amince masa sai yayi ha’inci kuma idan yayi magana sai yayi karya kuma idan yayi yarjejeniya sai yayi yaudara kuma idan yayi husuma sai yayi fajirci “  kuma a cikin ruwayar muslim  : “koda yayi salla kuma yayi azumi kuma yayi zatan cewa shi musulmi ne”
14) ya haramta kauracewa da hassada ga daidaikun al’ummar musulmai, saboda fadar sa (SAW): “kada kuyi gaba da juna kuma kada kuyi hassada da juna kuma kada ku juya wa juna baya kuma ku kasance bayin Allah iyan uwan juna kuma baya halatta ga musulmi ya kaurace wa dan’uwansa fiye da kwana uku” , kuma hakika Annabi (SAW) ya baiyana abunda hassada ke haifarwa – domin galibi ita ce sababi na dukkan kiyaiya da gaba – sai Annabi (SAW) yace: “annobar al’ummar da suka gabace ku ta kunno kai a cikin ku: hassada da gaba, gaba itace me aski ba ina cewa ne tana aske gashi ba a’a tana aske addi ne kuma na rantse da wanda raina ke hannun sa baza ku shiga aljanna ba har sai kunyi imani kuma baza kuyi imani ba har si kun so juna to ashe banabaku labarin wani abu ba wanda in kun aikata shi zaku so junan ku? To ku yada sallama a tsakanin ku”  
15) ya haramta tsinuwa da munanan lafuzza na harshe na daga zagi, Annabi (SAW) yana cewa: “lallai mumini ba mai yawaita tsiniwa bane ko kuma me yawan suka kuma ba me alfahsha bane da munanan lafuzza “
Kai hatta ma makiya ya kamata ne musulmi ya dung yi musu addu’a ta shiriya zuwa hanya madaidaiciya da kuma barin yi musu muguwar addu’a. Saboda hadisin Abu huraira Allah ya kara masa yace: “ance wa Manzan Allah (SAW). Ya manzan Allah kayi mummunar addu’a akan mushirikai, sai yace: “ni ba’a aiko ni ba dan in zama mai yawan tsiniqa lallai ni an aiko ni ne dan in zama rahama”
16) ya tsawatar kuma yayi hani gameda rowa da mako, dan musulunci yana kallon dukiya ne a matsayin na Allah ne ya bai wa mutum ne a matsayin ajiya da amana dan ya ciyar da kansa daga gareta da kuma wanda yake daukar dawainiyar su da kyautatawa kuma a ciki akwai hakkin iyan’uwan sa mabukata, Annabi 9SAW) yana cewa: “babu wata cuta da tafi muni irin cutar rowa “ , kuma hakika Manzan Allah (SAW) ya baiyana irin abunda zai samu al’umma na mummunan karshe in dai har cutar rowa da mako ta yadu a cikin su, Annabi (SAW) yace: “kuji tsoran zalunci domin shi duhu ne ranar alkiyama kuma kuji tsoran rowa domin itace ta halaka wadanda ke gabanin ku ta kaisu ga zubar da jinanen su kuma suka halatta ababen da aka haramta musu “
Lallai addinin musulunci yana kallan mutum mawadaci wanda ke kallan iyan’uwansa mabukata suna jiran taimakon sa sai kuma yaki taimaka musu dan ya ceto su daga abunda suke ciki kokuma ya saukaka musu wani sashi na radadin da suke ji to yayi nisa daga imani, saboda fadar sa (SAW): “halaye biyu basa haduwa a cikin mumini rowa da mummunar dabi’a”
17) yayi hani da kuma tsawatarwa game da almubazzaranci da tozarta dukiya a inda ba hakkin ta ba, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma ka baiwa makusanci hakkin sa da miskini da matafiyi kuma kada kayi almubazzaranci almubazzaranci (26) lallai almubazzarai iyan’uwan shaidan ne kuma shaidan ya kasance me kafurcewa ne da ubangijin sa (27)”
 Kuma da fadar sa (SAW): “lallai Allah ya haramta muku sabawa iyaye mata, da hana baunku da san na wasu,da kashe yara mata, kuma ya karhanta muku ance yace da yawan tambaya da wulakanta dukiya”
18) ya tsawatar kuma yayi hani akan tsanantawa da kuma wuce iyaka a addini, saboda fadar Allah madaukaki: “Allah yana san sauki ne a gare ku kuma baya nufin tsanani a gareku “{suratulbakara, aya ta 186 }, kuma Annabi (SAW) yana cewa: “lallai addini me sauki ne kuma babu wanda zai tsananta wa kansa a wannan addini face sai ya gallabe shi to ku takaita kuma ku kusanta kuma kuyi bushara kuma ku nemi taimako da safiya da kuma yammaci da wani bangare na dare “
19) ya tsawatar da kuma hani akan ruduwa a kuma girman kai da kuma takama, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma kada ka juya kumatunka g mutane kuma kada ka dunga tafiya a kasa kana takama lallai Allah baya san dukkan me takama me yawan girman kai (18) kuma ka takaita a cikin tafiyar ka kuma ka rage sautin ka lallai mafi munin sauti shi ne sautin jakai (19)”
Kuma Annabi na cewa gameda girman kai: “duk wanda akwi daidai da kwayar zarra na girman kai a zuciyar sa bazai shiga aljanna ba” sai wani mutum yace: ya manzan Allah lalai mutum yakan so ace tufafinsa me kyau ne kuma takalmin sa me kyau ne, sai yace: “lallai Allah me kyau ne kuma yana san kyau, girman kai shi ne kin gaskiya da yiwa mutane kallan banza”
Kuma yana fade akan takama da jiji da kai: “duk wanda ya ja tufafin sa a kasa saboda takama to Allah bazai kalle shi ba ranar alkiyama”
20) ya haramta leken asirin mutane da bin diddikin su da yi musu mummunan zato da gulmar su,Allah madaukaki yace: “ya ku wadanda sukayi imani ku nisanci da yawa daga cikin zato lalai sashin zato zunubi ne kuma kada ku dinga bin diddigi kuma kada sashin ku su dunga gulmar sashi shin dayanku na so ya ci naman dan’uwansa bayan ya mutu to ai kun kyamaci haka to kuji tsoran Allah lallai Allah me yawan karbar tuba ne me jin kai (12)”
Kuma Annabi (SAW) yana cewa: “shin ko kunsan meye gulma?” sai sukace Allah da Manzan sa ne suka fi sani, sai yace: “ka ambace dan’uwanka da abunda ya ki” sa aka ce: to me ka gani in abunda na fada gameda dan’uwana a kwai shi? Sai yace: in abunda ka fada gameda shi a kwai shi to kayi gulmar shi, in kuma abunda ka fada game da shi babu shi to hakika ka kirkira masa karya “
Kuma yayi hani akan mutum ya saurari maganar wasu mutane ba tare da sanin su ba, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda ya saurarai maganar wasu mutane wanda su basa san hakan ko kuma suna gudu daga gare shito za’a zuba ruwan dalma a kunnen shi ranar alkiyama”
21) ya tsawatar kuma yayi hani akan baiyana izgilanci ga mutane, saboda fadar sa (SAW): “kada ka yi izgilanci ga dan’uwanka sai Allah yayi masa rahama kai kuma ya jarabeka”
22) ya tsawatar kuma yayi hani akan mutum ya shiga abunda babu ruwan shi kuma be shafe shi ba, saboda fadar sa (SAW): “lallai yana daga kyautata musuluncin mutum shine ya bar abunda babu ruwan shi”
23)ya haramta cifa da munanan lakubba da zunde da yafuce shin da zance ne ko kuma aiki ko kuma nuni da kuma raina su da wulakanta su, saboda fadar Alah madaukaki: “yaku wadanda sukayi imani kada wasu mutane suyi izgilanci ga wasu mutane babu mamaki ma sunfi su alheri kuma kada wasu mata su dinga izgiliga wasu matan babu mamaki sun fi su alheri kuma kada ku dinga nune ga kawinan ku kuma kada ku dinga jifan juna da lakubba tir da sunan fasikanci bayan imani kuma duk wanda basu tuba ba to wadannan su ne azzalumai (11)”
24) ya haramta zaluncin alkali a wurin hukunci dan shi alkali a musulunci ana mai kallan me dabbaka shari’ar Allah, me zartar da hukuncin sa, shi a musulunci shi ne hukuma me zartarwa ba shar’antawa ba, da zaiyi zalunci to da yaci amanar da aka daura masa, Alalh madaukaki yace: “duk wanda basuyi hukunci da abunda Allah ya saukar ba to wadannan su ne kafurai”
Kuma Annabi (SAW) yana cewa: “alkalai iri uku ne daya na aljanna su kuma biyun suna wuta, amma wanda zai shiga aljanna shi ne mutumin da yasan gaskiya kuma yayi hukunci da ita, amma mutumin da yasan gaskiya sai yayi zalunci a cikin hukunci to yana wuta da kuma mutumin da yayi hukunci ga mutane da jahilci to shima yana wuta”
25) ya haramta rashin kishi, shi ne nuna rashin kishi ga iylai da kuma yadda da mummunan abu a cikin su, Ananbi (SAW) yana cewa: “mutum uku Allah bazai kalle su ba ranar alkiyama me sabawa iyayen shi da mace me shigan maza da kuma mara kishi....”
26) ya haramta kamanceceniyar maza da mata da kuma kuma kamanceceniyar mata da maza, an ruwaito daga Ibn Abbas Allah ya kara musu yadda yace: manzan Allah (SAW) ya tsine wa maza masu kama da mata da kuma mata masu kama da maza”
27) ya haramta yin gori, shi ne ka ambata ma wanda ka kyautata ma abunda kayi masa, saboda fadar sa (SAW): “kashedin ku da gori domin shi yana yana lalata godiya kuma ya shafe lada” sai ya karanta fadar Allah: “ya ku wadanda sukayi imani kada ku lalata sadakar ku da gori da cutarwa”
28) ya haramta kwace kyauta, Annabi (SAW) yana cewa: “me komawa a cikin kyautar sa kamar karane yana yin amai sannan ya koma ya lashe aman sa “
29) ya haramta annamimanci kuma ya yi alkawarin azaba ga annamimi, annamimi shi nemutumin dayake daukar magana daga nan zuwa can tsakanin mutane dan yada barna tsakanin su da kuma fitina, Allah madaukaki yace: “kuma kada kayi da’a ga dukkan me yawan rantsuwa wulakantacce (10) me zunde me yawo da annamimanci (11)” ,Kuma Annabi (SAW) yana cewa: “annamimi bazai shiga aljanna ba”
Kuma sanannan abu ne cewa sakamakon yada maganganu tsakanin mutane da nufin barna shi ne ya haifar da gaba da kauracewa wanda Annabi (SAW) ya hana da fadar sa: “baya halatta ga musulmi ya kaurace wa dan’uwansa sama da kwana uku su hadu wannan ya kauda kai kuma shima wancan ya kauda kai kuma mafi alhrin su shi ne wanda ya fara sallama” , kuma mummunan zato zai iya haihuwa daga haka da kuma bin didigi dan bincike akan abunda aka ce ya fada da hakan sai ya zama ya aikata abubuwa da yawa wanda Allah yayi hani daga gare su da fadar sa: “lallai wani sashi na zato zunubi ne kuma kada ku dinga bin diddigin juna...”
30) ya haramta babakere ga me rauni, sawa’un me rauni na jiki kamar mara lafiya da gajiyaiye da tsoho ko kuma rauni na dukiya kamar talaka da miskini da mabukaci, ko kuma wanda walitakar su ke hannun sa, ba dan komai ba sai dan samar da al’umma me hadin kai wanda rahama da son juna da iyan uwantaka ke jagorantar su, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma ku bautawa Allah kada kuyi shirka da shi da komai kuma iyaye ku kyautata musu da makusanta da marayu da miskinai da makwabci ma’aboci kusanci da makwabci na gefe da aboki na kusa da matafiyi da abunda hannayen ku suka mallaka lallai Allah baya san duk wanda ya kasance me takama me yawan alfahari (36)”
31) ya haramta cutar da wasiyya, kamar yayi wasiya cewa ana binsa bashi alhali ba haka bane, ba dan komai ba sai dan ya cutar da magada, saboda fadar Allah madaukaki: “bayan wasiyya da yayi wasici da ita ko kuma bashi ba mai cutar wa ba (12)”

Abubuwan da aka haramta na abinci da abin sha da tufafi:
1) ya haramta shan giya da dukkan abunda zai dauki ma’anar ta na kayan maye ko wane iri ne, naci ko sha ko na shinshinawa ko kuma allura, Allah madaukaki yace: “lallai giya da caca da gumaka da kibau datti na aikin shaidan to ku nisance su dan ku rabauta (90) lallai shaidan yana so ne ya jefa kiyayya da gaba a tskanin ku a gameda giya da caca kuma ya hanaku ambatan Allah da kuma sallah to shin ku ko kun hanu (91)”
Kuma dan musulunci ya datse hamya ga dukkan wanda ransa ke saka masa yin sana’a ta wadannan hanyoyin ko kuma taimakawa akan yadasu koda bai shaba, Annabi (SAW) yace: “Allah ya tsine wa giya kuma ya tsinewa me shayarda ita da mai shanta da me samar da ita da me daukanta da wanda aka dauko masa da me siyar da ita da me siyan ta da me cin kudin ta “
Da wannan alkawarin azabar me tsanani ne musulunci ya kare hankali da ji na dan adam daga dukkan abunda zai iya mai tasiri kuma ya lalata aikin sa, domin yana bukatar mutum ne wanda bazai sauka daga darajar sa ta dan adam ba zuwa wata darajar wasu haluntun ba wanda basu da hankali kuma basa gane abubuwa, abu ne sananne cewa duk me shan kayan giya da kayan maye kuma suka mai yawa, to zai iya aikata komai dan ya samu kudi wanda zai taimaka masa wurin ci gaba da shaye-shayen sa koda kuwa sata ce zaiyi ko kuma kisa, kari akan irin abunda zai iya faruwa na aukawa ga mata da kuma abubuwan da aka haramta saboda haka ne musulunci ya samata suna uwar manyan laifuka.
2) ya haramta in naman mushe da naman alade da dukkan abunda zai shiga fadar sa madaukaki: “an haramta muku cin mushe da jini da naman alade da abunda aka kira sunan wanin Allah da dabbar da ta mutu saboda shakewa da wacce aka bigeta ta mutu da wacce ta fado ta mutu da wacci aka tunkureta ta mutu da wacce namun daji suka cinye saifa abunda kuka yanka da abunda aka yanka akan kibau kuma an haramta muku rantsuwa da masu wannan dukkan su fasikanci ne”
3) kuma ya haramta dukkan abunda aka yanka ba tare da an ambaci sunan Allah ba da gangan, ko kuma abunda aka kira sunan wanin Allah lokacin yankawa, Allah madaukaki yace: “kuma kada kuci daga abunda ba’a ambaci sunan Allah ba a kanshi domin lallai shi fasikanci ne”
4) ya haramta dukkan dabbar da keda fika kamar zaki da damisa da kerkeci da sauran su, cikin tsuntsaye kuma ya haramta masu kumbar farauta kamar angulu da shaho da sauran su.
5) kuma ya haramta dukkan abunda cutarwarsa ta baiyana ga jiki na daga abun sha ko kuma abun ci kamar taba da makamancin ta, Allah madaukki yace: “kuma kada ku kashe kawunan ku lallai Allah ya kasance me tausayi ne a gareku (29)” suratun nisa’i.
6) ya haramta sanya zinari da alhariri ga maza, amma su mata wannan halal ne a gare su, saboda fadarsa (SAW): “an halalta sanya zinari da alhariri ga matan al’ummata amma haramun ne ga mazan su”

Kuma bari mu ambaci wasu abubuwa da musulunci ayi umarni da su kuma ya kwadaitar akan aikata su dan misali kawai ba wai tattarosu duka ba:
1) yayi umarni da adalci cikin magana da aiki, Allah madaukaki yace: “lallai Allah yana umarni da adalci da kyautatawa da baiwa makusanta hakkin su kuma yana hani daga alfahsha da munkari da zalunci yana muku wa’azi ko zakuyi tunani (90)”
Kuma daga cikin maganganun halifa na farko Abubaka assiddiq Allah ya kara masa yadda lokacin da ya karbi kalifanci fadar sa: “me rauni a cikin me karfi ne a wuri na har sai na kwato masa hakkin sa in Allah ya yadda, shi kuma me karfi a cikin ku to me rauni nr a wuri na har sai na kwatto hakki daga wrun shi in Allah ya yadda....kuyi mun biyaiya matukar nayi biyaiya ga Allah da manzan sa in kuma na sabawa Allah da manzan sa to banda hakkin kuyi min biyaiya”
Adalci abun nema ne ga makusanci na na nesa, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma idan kunyi magana to kuyi adalci koda game da makusanci ne kuma ku ciki alkawarin Allah wannan shi ne abunda yake muku wasiyya da shi dan kuyi tunani (152)”
Kuma a cikin hali na yadda da kuma fushi da musulmi da wanda ba musulmi ba, Allah madaukaki yana cewa: “kuma kada kiyayyarku da wasu mutane ta hana ku yin adalci kuyi adalci hakan shine yafi kusa da tsoran Allah” { suratul ma’ida, aya ta 8}
Kuma hakika Allah madaukaki yayi umarni da ayi adalci koda sai anyi amfani da karfi ne kuwa,Allah madaukaki yace: “hakika mun aiko manzannin mu da hujjoji kuma mun saukar da littafi tare da su da ma’auni dan mutane su tsayu da adalci kuma mun saukar da karfe a cikin sa akwai karfi me tsanani da kuma amfani ga mutane “
Ibnu taimiyya a karkashin tafsirin wannan ayar yace(manufar aiko manzanni da saukar da littattafai itace mutane su tsawu da adalci ta bangaren hakkokin Allah da hakkokin halittun sa, duk wanda kuma ya karkace yaki bin littafin Allah to sai a mikarda shi da karfe) {majmu’ul fatawa 28:263}.
2) yayi umarni da mutum ya fifita wani akan kan sa, kuma ya kwadaitar akan haka, domin hakan na nuni zuwa ga gaskiyar kauna wanda amfaninsa ke mamaye al’umma sai daidaikun ta su kara shakuwa da juna da kuma yin iya kokarin su wajen taimakon sashinsu ga sashe,Allah madaukaki yace yana me yabo akan wadanda suke gabatar da mutane wajen alheri da kuma kyautatawa akan kawunan su: “kuma suna fifita wasu akan kawunan su koda kuwa sunada bukata kuma duk wanda aka kare shi daga rowar ransa to wadannan sune masu babban rabo (9)”
3) yayi uamarni da abokamtaka da mutane na kwarai da kuma lazumtar su, kuma ya tsawatar akan abota da mutanen banza da kuma zama da su, sai yace: “misalin abokin zama na kwarai da kuma na banza kamar misalin me dauke da turare nw da kuma me hura wuta shi me dauke da turare kodai ya ya baka kyauta ko kuma ka siya daga gare shi ko kuma ka shaki kamshi mai dade daga gare shi, shi kuma me hura wuta ko dai ya kona tufafin ka ko kuma ka samo mummunan wari daga gare shi “
4) yayi umarni da sasantawa tsakanin mutane yayin da aka samu rashin jituwa da jayaiya a tsakanin su, saboda fadar Allah madaukaki: “babu alheri a cikin mafi yawan tattaunawar su sai dai wanda yayi umarni da sadaka ka kuma kyakkyawa ko kuma sasantawa tsakanin mutane kuma duk wanda ya aikata haka dan neman yaddar Allah to da sannu zamu bashi lada mai girma (114)”
Kuma sasanta tsakanin mutane yanada daraja me girma a musulunci, darajarsa bata kasa da darajar sallah da azumu da sauran wajibai na ibada, saboda fadar sa (SAW): “ashe bana baku labarin abunda yafi darajar azumi da sallah da sadaka ba? Shi ne sasanta tsakanin mutane, domin raba tsakanin mutane shine me aske ladan aiki “
Kuma hakika musulunci yayi rangwame da yin karya a cikin wannan maudu’in dan hada zukata da tattaruwar su da hadin kai da rashin rarrabuwa, saboda fadar sa (SAW): “bana kirga shi karya: mutumin da ke sasanta tsakanin mutane zai kirkiri wata magana amma baya nufi komai da ita sai dai gyara da mutumin da zai yi karya a wurin yake da kuma namiji yayiwa matar sa karya ita ma kuma mata tayiwa mijinta karya “
Kuma Ananbi (SAW) yana cewa: “ba makaryaci bane wanda ke sasanta tsakanin mutane sai ya samarda alheri ko kuma ya fadi alheri “
5) yin umarni da kyakkyawa kuma da yin hani daga mummuna da dukkan hanyoyi kowa gwargwadan ikon shi da kuma iyawar shi domin shi ne hakikanin aminci wanda ke tsare al’umma kar zalunci ya yadu a cikin ta da barna kuma hakkoki su narke, kuma dokar dajji ta mamaye su, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda yaga wani mumminan abu a cikin to ya canza shi da hannun sa in kuma baai iya ba to da harshen sa in kuma bazai iya ba to da zuciyar sa kuma wannan shi ne mafi raunin imani “
Ta hanyar umarni da kyakkyawa da kua hani daga mummuna ne ake ilimantar da jahili kuma ake tunatar da wanda ya gafala kuma ake mikarda me munanawa, kuma ake taimakon mikakke kuma ake dabbaka shari’ar Allah, Allah madaukaki yana cewa: “kuma kuyi taimakekeniya akan yin da’a da kumatsoran Allah kuma kada kuyi taimakekeniya akan sabo da kuma zalunci”
Kuma Annanbi (SAW) ya buga wani misali ya baiyana abunda ke faruwa in aka bar yin umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna, sai yace: “misalin wamda ke tsaye akan iyakokin Allah da kuma wanda ya fada cikin su kamar misalin wasu mutane ne sukayi kuri’a wajen hawa jirgin ruwa sai wasu suka samu wuri a samanta wasu kuma a kasa sai wadanda suke kasa suka kasance duk lokacin da suke bukatar ruwa sai sun hauro sama sai sukace: dama kawai mu bula wani bangare daga kasan mu dan kar mu dinga cutar da na saman mu to in har na saman suka barsu suka aikata abunda sukayi nufi to dukansu ne zasu halaka in kuma suka kama hannayen su suka hana su zasu tsira su duka”
Kuma Allah ya baiyana ukubar da zata faru in aka bar umarni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna da fadar sa: “an la’anci wadanda suka kafurta daga cikin bani isara’ila akan harshen annabi Dauda da Isa dan maryam wannan kuwa saboda sabawar su da kuma abunda sukeyi na ta’addanci (87) sun kasance basa hani daga mummunan abu da suke aikatawa tir da irin abunda suka aikatawa (79)”
Kuma umarni da kyakkyawa da hani dga mummuna nada ladubba da tsari da ka’idoj, daga cikin su:
-ya kasance masani akan abunda yake umarni da shi da kuma abunda yake hani daga gare shi, dan kada ya bata wa mutane addinin su, an ruwaito daga Sufyan ibn Abdullahi assakafi yace: nace ya Manzan Allah: ka fadamun abunda zan yi ruko da shi sai yace: “kace ubangijina shi ne Allah sannan kuma ka tsayu akan haka” sai nace ya manzan Allah: me mafi tsoran abunda kake ji mun? Sai yace: sai ya kama harshen sa yace: wannan!”
- kada yin hanin sa ya haifar da barnan da tafi girma akan abunda ya hana.
- kada ya dinga aikata abunda ya hana ko kuma ya bar abunda yake umarni da shi, saboda fadar Allah madaukaki: “ya ku wadanda sukayi imani dan me kuke fadan abunda bakwa aikatawa (2) zunubi yayi girma a wurin Allah ku dinga fadan abunda bakwa aikatawa (3)”
- ya kasance me hakuri yana umarni da tausasawa kuma yana hani da sassautawa, saboda fadar sa (SAW): “lallai tausasawa bai shiga wani abu face sai ya kawata shi uma ba’a cire shi daga wani abu face sai ya munana shi “
- ya kasance zai iya jurewa abunda zai sam shi na cutarwa saboda umarni da kyakyawa da kuma haninsa daga mummuna, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma kayi umarni da kyakkyawa kuma kayi hani daga mummuna kuma kayi hakuri akan dukkan abunda zai sameka lallai wannan yana cikin manyan al’amura (17)”
6) yayi umarni da kyawawan dabi’u da kuma kwadaitarwa akan siffantuwa da dabi’u na gari, saboda fadar sa (SAW): “babu abunda yafi nauyi a cikin mizani kamar kyakkyawar dabi’a”
Kuma Annabi (SAW) ya baiyana ladan me kyakkyawar dabi’a da fadar sa: “lallai wanda nafi so a cikin ku kuma wanda yai kusanci da ni a wurin zama ranar alkiyama shi ne wanda yafi ku kyawan dabi’a kuma lallai wanda wanda nafi ki a cikin ku kuma wanda yafi nesa da ni ranar alkiyama sume masu surutu da yawa da masu feleke da masu girman kai “sai sika ce ya manzan Allah: mun san sarsarun da mutashaddiku to su waye mutafaihiku? Sai yace: su ne masu girman kai”
7- yayi umarni da kyautatawa, an ruwaito daga Ja’afar dan Muhammad daga mahaifin shi daga kakan shi yace: manzan Allah (SAW) yace: ka kyautata zuwa ga ma’abotan shi da kuma wanda ba ma’abotan shi ba in ka dace da ma’abotan shi to ya fada gidan shi in kuma baka dace da ma’abotan shi ba to kai ne ma’abocin shi “
8- yayi umarni da tantancewa yayin ruwaito labari da bincike kafin zartar da hukunci, saboda fadar Alalh madaukaki: “yaku wadanda sukayi imani in wani fasiki yazo muku da wani labari to kuyi bincike dan kada ku afkawa wasu mutane akan rashin sani sai ku wayi gari kuna masu nadama akan abunda kuka aikata (6)”
9- yayi umarni da yin nasiha, saboda fadar sa (SAW): “addini nasiha ne sai muce: ga waye ya manzan Allah? sai yace: ga Allah da littafinsa manzan sa da manzan sa da shuwagabannin musulmai da kuma game garin su”
-nasiha ga Allah, tana kasancewa ne ta hanyar imani da shi da kuma bauta masa shi kadai,da kore abokin taraiya a gare shi, d tsarkake shi a cikin sunayen sa da siffifin sa, kuma shi ne me jujjuya wannan duniya, duk abunda yaso shi yake kasancewa, kum abunda baya so baya kasancewa, da bin umarnin sa da kuma nisantar abun da ya hana.
- nasiha ga littafin Allah, tana kasancewa ne ta hanyar kudurce cewa maganar Allah ne saukakke ne daga gare shi kuma shi ne littafi na karshe daga sama, da halatta dukkan abun da aka halatta a cikin shi da kuma haramta dukkan abunda aka haramta a cikin shi, da kuma sanya shi tsai da ake koyi da shi.
- nasiha ga manzansa (SAW) tana kasancewa ne ta hanyar yi masa da’a cikin abunda yayi umarni da gaskata shi cikin labarin da ya bada da nisantar abunda yayi hani daga gare shi kuma ya tsawatar da kaunar shi da girmama shi da darajta shi, da kuma yin aiki da sunnar shi da yada ta cikin mutane.
- nasiha ga shuwagabannin musulmai tana kasancewa ne ta hanyar yi musu biyaiya matukar basuyi umarni da sabon Allah ba da nuna musu alheri da taimaka musu akan yi shi da rashin yi kusu tawaye da yi musu nasiha da tausasawa da tunatar da su hakkokin mutane.
- nasiha ga gamegarin mutane tana kasancewa ne ta hanyar yi usu nuni zuwa ga abun da yake alheri ne a gare su a cikin addinin su da duniyar su da kuma taimaka musu akan su biya bukatun su da kamewa akan cutar da su, kuma ya so musu abunda yake so ma kansa, kuma ya ki musu abunda yake ki ma kansa kuma yayi musu mu’amala irin yadda yake so suyi mai mu’amala.
Kuma abunda ke tattaro karamci shi ne fadar Allah madaukakai: “kuma kada ka sanya hannunka kulalle akan wuyanka kuma kada ka bude shi dukkan budewa sai ka zauna kana abun zargi mai hasara (29)”
10- yayi umarni da rufawa mutane asiri, kuma ya kwadaitar akan yayi damuwar su da saukaka al’amuran su, saboda fadar sa (SAW): “duk wanda ya yaye ma wani mumini wata damuwa daga cikin damuwar duniya to Allah zai yaye masa damuwa daga cikin damuwar ranar alkiyama, kuma duk wanda ya aukakama wanda yake cikin tsanani to Allah zai saukaka masa a duniya da lahira, kuma duk wanda ya rufa wa musulmi asiri to Allah zai rufa masa asiri a duniya da lahira kuma Allah yana taimakon bawa matukar bawa yana taimakon dan’uwansa “
11- yayi umarni da hakuri kuma ya kwadaitar akan shi, shin hakuri ne akan da’a ko kuma hakuri akan barin abunda aka hana, saboda fadar Alllah madaukaki: “kayi hakuri da hukunci ubangijin ka lallai kai kana karkashin kulawan mu “ , ko kuma hakuri akan ababen da Allah ya kaddara, kamar hakuri akan talauci da yunwa da kuma rashin lafiya da tsoro, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma lallai zamu jarabce ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawayar dukiya da rayuka da kayan itatuwa kuma kayi bishara ga masu hakuri (155) wadanda iadan musiba ta same su sai suce lallai mu na Allah ne kuma zuwa gare shi zamu koma (156) to wadannan akwai salatai akan su daga ubangijin su da kuma rahama kuma wadannan sune shiryaiyu “
12- kuma yayi umarni da hadiye fushi da yafiya lokacin da aka samu damar daukar fansa, wannan kuwa saboda abunda ke cikin su na karfafa zumunci tsakanin daidaikun al’umma, da kuma kokarin nrsanta dukkan yake kawo kiyaiya da kauracewa juna da kin juna, kuma ya sanya sakamakon wannan aiki me girma ne, dan haka ne ma Allah madaukaki ya yabi wadanda suka siffantu da wadannan siffofi kuma ya kawatu da su, Allah madaukaki yace: “kuma kuyi gaggawa zuwa ga gafarar ubangijinku da aljannah wacce fadinta kamar fadin sammai da kasa ne an tanade ta dan masu tsoran Allah (133) sune wadanda suke ciyarwa acin halin yalwa da kuma tsanani da kuma masu hadiye fushi da kuma masu yiwa mutane afuwa kuma Allah yana san masu kyautatawa (134)”  
13- yayi umarni da fukantar mummuna da kyautatawa dan zukata su kusanta da juna, da kuma shafe abunda ke cikinta na gaba, kuma ya yanke tunanin daukar fansa, Allah madaukaki yace: “ka tunkude mummuna da abunda yafi kyau sai wanda tsakaninka da shi akwai gaba ya zama kamar masoyi na kusa (34)” {suratu fussilat, aya ta 34}.


Bangaren ladubba na musulunci
Lallai shari’ar musulunci ta zo da wasu ladubba wanda ta kwadaitar da musulmai akan dabbaka su dan cikan mutum musulmi, daga cikin wadannan ladubabn akai:
Ladubban cin abinci:
1- cewa Bismillah a farkon cin abinci, da kuma cewa Alhamdulillah lokacin gamawa, da kuma cin abunda ke gaban sa, da kuma ci da hannun dama- Umar dan Abi salimata yana cewa: na kasance yaro karami a wurin Annabi (SAW), kuma in muna cin abinci sai sai in dinga zagayawa da hannu na a cikin kwanan abinci sai Annabi (SAW) yace mun: “ya kai yaro kace bismillah kuma kaci da daman ka kuma kaci abunda ke gabanka “
2- rashin kushe abinci ko wane iri ne, saboda hadisin da Abu huraira ya ruwaito, yace: “Manzan Allah (SAW) bai taba kushe wani abinci ba, in yana marmari sai ya ci ina kuma kuma baya bukata sai ya barshi “
3- kada ya yawaita cin da sha, saboda fadar Alllah madukakai: “ku ci kuma ku sha amma kada ku wuce iyaka lallai shi Allah baya san masu wuce iyaka (31)”
Kuma Annabi (SAW) yana cewa: “dan adam bai taba cika wani abu ba wadda fafi cikin sa sharri, wasu lomomi sun isheka ya kai dan adam wanda zasu tada bayanka in kuma ba makawa sai kaci da yawa to ka kasa cikinka kashi uku kashi daya na abincinka kashi daya na abun shanka kuma kashi daya na numfashinka”
4- rashin numfashi a shikin abunci ko abun sha, Ibn Abbas Allah ya kara musu yadda yana cewa: “Annabi ya hana yin numfashi a cikin kwanan abunci ko kuma a hura a cikin ta “”
5- kada ya kazanta abincin ga wanin sa ko kuma abun shan sa, sa’ed alkhudry Allah ya kara masa yadda yana cewa: naji Manzan Allah (SAW) yana hani daga daga bata abun sha, sai Abdullahi yace, M’aa mar ko wanin sa sai yace: shi ne sha daga bakin su”
6- yaci tare tare da wanin sa kada ya ci shi kadai, wani mutum ya tambayi Manzan Allah (SAW) ya ce: mu muna cin abinci amma bama koshi! Sai Annabi yace: “kuna cin abinci na tare koko a war-watse? Sai yace: a war-watse, sa yace: “ku hadu kuci abincin ku kuma ku ambaci sunan Allah sai asa muku albarka a ciki “
7- ya nemi izini idan aka gaiyace shi cin abinci sai wani ya biyo shi,, wani mutum cikin mutanen madina da ake yiwa kinaya da Aba shu’aib ya gaiyaci Annabi (SAW) su biyar sai wani utum ya biyo su sai Annabi (SAW) yace: “wannan mutumin ya biyo mu in kaso ka mai izini to ka mai izini in kuma ka so ya koma sai ya koma, sai mutumin yace: “a’a na mai izini”

Ladubban neman izini:
1- ya kasu kashi biyu:
-neman izini daga wajen gida, saboda fadar Allah madaukaki: “yaku wadanda sukayi imani kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nema izini kuma kuyi salllama ga ma’abotan su “
- neman izini a cikin gida, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma idan yara suka kai lokacin balaga to su dinga nemi izini kamar yadda wadanda suka gabacesu suke neman izini “
Duk wannan saboda a kiyaye abunda ke cikin gidaje ne na sirrori da kuma boye abunda ke ciki na kebantattun abubuwa, wanu mutum ya leko ta wata kofa daga cikin kofofin gidan Annabi (SAW), kuma a hannun Annabi akwai matajin kai yana taje kansa da shi sai ya ce: “da nasan cewa kana leke da na soki idanka da shi, an sanya neman izini ne saboda ido”
2- rashin takurawa wurin neman izinin, saboda fadar sa (SAW): “neman izini sau uku ne in anyima izini sai ka shiga in kuma ba’a maka ba sai ka koma”
3- me neman izini ya ambaci sunan shi in aka tambaya, an ruwaito daga Jabir Allah ya kara masa yadda yace: nazo wurin Annabi (SAW) saboda wani bashi da ke kan babana sai na buga kofa sai yace: waye wannan? Sai nace: ni ne, ai yace: “ni ne ni ne, kamar ya kyamaci hakan”

Ladubban sallama:
1- musulunci ya kwadaitar akan yada sallama tsakanin mutane saboda abunda take gadarwa na kaunar juna da kuma sabo, Annabi (SAW) yana cewa: “na rantse da wanda raina ke hannun sa baza ku shiga aljanna ba har sai kunyi imani kuma baza kuyi imani ba har sai kun so junan ku to ahe bana nuna muku wani abu ba wanda inkun aikata shi zaku so juna shi ne ku yada sallama a tsakanin ku “
2- wajabcin maida sallama ga wanda yayi maka, saboda fadar Allah madaukaki: “kuma aka gaishe ku da wata gaisuwa to ku mayar da abunda ya fita ko kuma irin ta”
3- musulunci ya baiyana hakkokin sallama, Manzan Allah (SAW) yace: “wanda ke kan abun hawa zaiyi wa me tafiya a kasa sallama shi kuma me matafiya a kasa zai yisallama ga na zaune mutane kadan zasuyi sallama ga mutane da yawa”

Ladubban wurin zama:
1- yin sallama ga wadanda ke wurin zaman lokacin shigar sa da fitar sa, Annabi (SAW) yana cewa: “idan dayanku ya zo wurin zama to yayi sallama idan yaga cewa zai zauna to ya zauna idan kuma ya mike to yayi sallama dan ta farko bata fi ta biyu ba “
2- yalwatawa a wurin zama, saboda fadar Allah madaukaki: “yaku wadanda sukayi imani idan aka ce muku ku yalwata a wurin zama to ku yalwata sai Allah ya yalwata muku kuma idan aka ce ku matsa to ku matsa Allah zai daga darajar wadanda sukayi imani daga cikin ku da wadanda aka basu ilimi da wasu darajoji kuma Allah masani ne ga abunda kuke aikatawa (11)”
3- rshin tada wani daga wurin zaman sa da kuma zaunawa a wurin nasa, Annabi (SAW) yana cewa: “kada wani ya tada wani daga wurin zamansa sai shi kuma ya zauna a wurin nasa sai dai ku yalwata kuma ku marmatsa”  
4- duk wanda ya tashi daga wurin zaman sa sannan ya dawo to shi ne yafi canvanta da shi, saboda fadar sa (SAW): “duk wanda ya tashi daga wurin zaman sa sai ya dawo wurin to shi yafi cancanta da shi”
5- rashin raba tsakanin mazauna sai da izinin su, saboda fadar sa (SAW): “baya halatta ga wani mutum ya raba tsakanin mutum biyu sai da izinin su “
6- kada mutum biyu su kebe banda na uku, saboda fadar sa (SAW): “idan kun kasance ku uku to kada mutane biyu su kebe banda na uku har sai kun hadu da mutane saboda hakan zai bakanta masa rai”
7- kada wurin zaman ya shagaltu da maganganun da basuda fa’ida, ya zamo ba’a ambatan Allah, da bitar abunda zai kawo ma al’umma alkairi cikin lamuran addinin su da duniyar su, saboda fadar sa (SAW): “babu wasu mutane da zasu zauna a wani urin zama har su tashi basu ambaci Allah a cikin sa ba, face sun tashi kamar mushen jaki kuma aki hasara a tattare da “
8- rashin fuskantar mazauna da abunda suke ki, an ruwaito daga Anas dan Malik Allah ya kara masa yadda, wani utum ya shigo wurin Manzan Allah (SAW) kuma akwai alamun yello a tare da shi, kuma Annabi (SAW) sau dayawa baya fuskantar mutum idan yayi wani abu da yake kyama, lokacin da ya fita sai Annabi yace: “da kun umarci wannan yaje ya wanke gwiwar hannayen sa “

Ladubban taro:
1- lallai musulunci yana kula da damuwar mutane baki day ga masu tattaruwa a wuri daya, ba dan komai ba sai dan taron ya zama abun ban sha’awa, kuma a samu fa’idar da ake nema daga taran, kuma yana ko karin tunkudr dukkan abunda zai sa a kyamaci taron, musulunci yana umartar mabiyan sa su zama masu tsafta a jikin su, dan kada a samu mummunan wani wari da zai cutar da abokin zama, kuma masu tsafta a tufafin su, ba kazanta da zata sa rai ta kyamaci hakan, kamar yadda kuma yake umarni da saurarawa ga me magana da kuma rashin yanke shi, da zama inda suka samu wuri ba tsallake wuyan mutane kuma babu matsatstsi a gare su, saboda fadar sa (SAW) lokacin yana magana a wurin wani taro daga cikin tarukan musulmai a wurin sallar juma’a: “duk wanda yayi wanka ranar juma’a kuma yayi asuwaki kuma ya shafa turare in yanada shi, kuma ya sa mafi kyawon tfafin sa, sannan ya fito har ya isa masallaci kuma bai tsallake wuyan mutane ba sannan yayi sallah gwargwadan abunda Allah ya kaddara masa sannan yayi shiru lokacin da liman yake huduba kuma baiyi magana ba har sai da ya idae da sallar sa to wannan kaffara ne gare shi na abunda ya aikata tsakanin wannan juma’ar da wata juma’a ta daban “
2- ana so duk wanda yayi atishawa sai yace alhamdulillah, Annabi (SAW) yana cewa: “idan dayanku yayi atishawa sai yace: alhamdulillah,sai dan’uwan sa ko abokin sa yace masa yarhamukalla, idan yace:yarhamukalla, shi kuma sai yace: yahdikumullahu wa yuslihu balakum”
3- kuma daga ladubban sa akwai abunda Abu huraira ya ruwaito Allah ya kara masa yadda, daga Manzan Allah (SAW) yace: “idan dayanku yayi atishawa sai ya dora tafin hannayen shi a fuskar sa kuma ya rage sautin shi “
4- ansso ga wandazai yi hamma ya kore hammar hi gwargwadan iko, domin alama ce ta kasala, saboda fadar sa (SAW): “lallai Allah yana san atishawa kuma yana kin hamma, idan mutum yayi atishawa sai yave alhamdulillah to hakki ne a akan dukkan musulmin da ya ji shi ya ce mai yarhamukallah, amma hamma ita daga shaidan ce to wanda ta zo mai sai yayi kokarin maida ita gwargwadan iko idan yace hahhh lokacin da yake hamma sai shaidan yayi masa dariya ‘
5- barin yin gyatsa a wurin zama, saboda fadar Ibn Umar Allah ya kara musu yadda: wani mutum yayi gyatsa a wurin manzan Allah (SAW) sai yace masa: “ka kame mana gyatsar ka, domin wanda yafi koshi a duniya to yafi jin yunwa mai tsawo a ranar alkiyama “

Ladubban magana:
1- sauraran wanda ke magana da rashin katse shi har sai ya gama, saboda fadar manzan Allah (SAW) a hajjin bankwana: “kace wa mutane suyi shiru “
2- baiyana zance dan wanda ake magana da shi ya gane, an ruwaito daga Aisha Allah ya kara yadda a gare ta tace: maganar manzan Allah (SAW) ta kasance ne dalla-dalla duk wanda ke jin shi zai fahimce shi “
3- sakin fusk daga bangaren me magana da kuma wanda ake magana da shi,saboda fadar sa (SAW): “kada ka raina wani abu daga aikin alkairi koda kuwa ka hadu da dan’uwanka ne da sakin fuska “
4- dadada zance ga wanda ake magana da shi, Annabi (SAW) yana cewa: “dukkan gaba daka jikin mutane tanada sadaka kowane yini da rana ta futo ka sasanta tsakanin muyane biyu sadaka ne, kuma ka taimaki mutum akan dabbar sa ka dora shi akai ko kuma ka dora masa kayansa akanta sadaka ne, kuma magana mai dadi sadaka ce, kuma kowane taku daya da zaiyi zuwa masallaci sadaka ne, kuma ya kauda abu me cutarwa akan hanya sadaka ne “

Ladubban gaida mara lafiya:
1- musulunci ya kwadaitar game da ziyaratar mara lafiya kuma ya lissafa shi cikin hakkin musulmi akan musulmi, Annabi (SAW) yana cewa: “hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne amsa sallam da gaida mara lafiya da raka gawa da amsa gaiyata da cema me atishawa yarhamukalla “ , kuma dan ya kwadaitar da musulmai akan ziyartar mara lafiya sai ya baiyana ladar da ake samu akan haka, manzan Allah (SAW) yace: “duk wanda yaje gaida mara lafiya bazi gushe ba yana ikin aljanna, sai akace ya manzan Allah menene khurfatul jannah? Sai yace: farfajiyar ta”
2- baiyana so da tausayawa a wurin ziyarar, an ruwaito daga Aisha iyar Sa’ad, lallai baban ta yace: nayi rashin lafiya a makkah sai Annabi (SAW) yazo wurina dan ya gaishen ni sai ya dora hannun sa akan goshi na sannan ya shafa kirji na da ciki na sannan sai ya ce: ya Allah ka ba Sa’a lafiya kuma ka cika masa hijirar sa “
3- yin addu’a ga mara lafiya, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda ya ziyarci mara lafiya matukar ajalin sa bai zo ba sai yace a wurin sa sau bakwai, ina rokon Allah me girma ubangijin al’arshi mai girma ya baka lafiya face sai Allah ya bashi lafiya daga wannan rashin lafiyar “

Ladubban wasa (zolaya):
Lallai rayuwa a musulunci ba kamar yadda wasu ke tunani bane cewa dole ta zama ba wasa a cikin ta da kuma shakatawa da ta halatta a ciki, an ruwaito daga Hanzala al asady yace: sayyidina Abubakar ya haduda ni sai yace: ya kake ya kai Hanzala? Sai yace, sai nace: Hanzala ya zama munafuki! Sai yace: subhanallah, me kake fada, sai yace: muna zama wurin Manzan Allah (SAW) yana tunatar da mu wuta da aljannah har ya zamto kamar muna ganin su, amma idan muka bar wurin manzan Allah (SAW) muka yi wasa da matan mu da yara kuma muka koma wurin sana’o’in mu sai mu manta abubuwa masu yawa, sai Abubakar yace: wallahi muma dukkan mu irin wannan na faruwa da mu, si ni da Abubakar muka tafi wurin Manzan Allah (SAW) har si da muka shiga inda yake, sai nace: Hanzala ya zama munafuki ya manzan Allah, sai manzan Allah (SAW) yace: me ya faru? Sai nace:: muna zama wurin ka kana tunatar da mu wuta da aljannah har ya zamto kamar muna ganin su, amma idan muka bar wurin manzan Allah (SAW) muka yi wasa da matan mu da yara kuma muka koma wurin sana’o’in mu sai mu manta abubuwa masu yawa, sai manzan Allah (SAW) yace: na rantse da wanda raina ke hannun sa da zaku dawwama akan irin halin da kuke kasancewa a wuri na kuma da kuma tunawa da mala’iku sun dinga musafaha da ku akan shimfidun ku da kuma kan hanyoyin ku sai dai ya Hanzala a tuna wani lokaci bayan wani lokaci har sau uku “ , sai manzan Allah (SAW) ya baiyana a cikin wannan hadisin cewa lallai wasa wanda aka halatta da kuma shakatawa abun nema ne dan rai ta dawo da nishadin ta da kuma karfin ta.
1- Annabi (SAW) ya baiyana wa sahabban sa ladubban zolaya lokacin da suka tambaye shi sai suka ce: ya manzan Allah lallai kai kana zaulayar mu, sai yace: “dudda cewa bana fadan komai sai gaskiya”
2- kamar yadda zaulaya ke kasancewa da magana hakanan tana kasancewa da aiki, kuma hakika manzan Allah (SAW) ya kasance yana zaulayar sahabban sa da aiki, an ruwaito daga Anas dan Malik Allah ya kara yadda a gare shi yace: wani mutum daga cikin mutanen kauye sunan shi Zahir ya kasance yana kawo ma manzan Allah (SAW) kyaututtuka daga kauye sai Annabi (SAW) ya tsare shi idan yana so ya koma, sai Annabi (SAW) yace: “lallai Zahir shi ne kauyen mu mu kuma mune birnin sa sai Annabi (SAW) yazo wurin sa wata rana alhali yana saida kayan sa sai Annabi ya cabke shi ta bayan shi kuma shi bai ganshi ba kuma bazai iya ganin shi ba sai yace: waye wannan? Sake ni, sai ya juya sai ya ga Annabi (SAW) ne, sa ya manne da jikin Annabi (SAW), sai Annabi (SAW) yaketa cewa: wa zai siya wannan bawan? Sai Zahir yace, ya Manzan Allah zaka sameni da arha, sai Annabi (SAW) yace: “sai dai kai a wurin Allah ba mai arha bane, ko kuma yace: “kai a wurin Allah me tsada ne”
3- kada ya zama a cikin zaulayar akwai abunda zai cutar da musulmi ko kuma ya bata masa rai, saboda fadar sa (SAW): “baya halatta ga musulmi ya tsorata dan’uwansa musulmi”
4- kada zaulayar tashi ta fitar da shi daga kewayen gaskia, sai yayi karya dan ya ba mutane dariya, saboda fadar sa (SAW): “tu da wanda zai dinga bada labari sai yayi karya dan ya ba mutane dariya daita, tir da shi kuma tir da shi “

Ladubban ta’aziya:
1- an shar’anta ta ne dan lallashin iyalan mamaci da sassauta damuwar su da saukaka musibar su, Annabi (SAW) yana cea: “babu wani mumini da ai yi ta’aziyya ga dan’uwan sa da musiba ta same shi face sai Allah ya tufatar da shi daga kayan ado na karamci ranar alkiyama”
2- yin addu’a ga iyalan mamacin da kuma kwadaitar da su akan yin hakuri da neman lada a wurin Allah, an ruwaito daga Usama dan zaid yace:mun kasancea a wurin annabi (SAW) sai daya daga cikin yaransa mata ta aiko tana kiran shi kuma tana bashi labari cewa yaranta yana kan halin mutuwa, sai yace wa dan aiken kaje ka ce mata lallai abunda Allah ya karba nashi ne kuma abunda ya bayar nashi ne kuma kowane abu a wurinsa yanada lokaci na musamman ka umarce ta tayi hakuri kuma ta nemi lada a wurin Allah, sai dan aike ya dawo yace: lallai ita tayi rantsuwa akan lallai kazo wurinta, sai yace: sai Annabi (SAW) ya mike sai Sa’ad dan Ubadah shima ya mike da Mu’az dan jabal nim a sai na bisu muka tafi tare, sai aka kawo mai yaran kuma lokacin ransa na yunkurin fita kamar tana gab da fita sai iadansa suka zubda hawaye sai Sa’ad yace masa meke faruwa ne ya manzan Allah? sai yace: “wannan tausayi ne da Allah ke sawa a zukatan bayinsa kuma lallai shi yana tausayawa bayinsa masu tausayawa “
3- yin addu’a ga mamaci da nema masa gafara, kuma Shafi’i Allah ya kara yadda a gareshi ya kasance yafi san ace: Allah ya girmama ladanka, kuma ya kyautata ta’aziyyarka, kuma ya gafarta wa mamacin ka.
4- anso a dafa abinci a kaiwa iyalan mamaci, sboda fadar manzan Allah (SAW): “kuyi abinci ku kaiwa iyalan ja’afar dan su hakika al’amarinda zai shagaltar da su ya same su”

Ladubban bacci:
1- yin bisimillah da kuma kwantawa a gefen dama, da kuma tabbatar da cewa babu abunda zai cutar da mutum a inda zaiyi bacci, Annabi (SAW) yana cewa: “idan dayan ku ya zo wurin baccin sa to ya dauki gefen wandan sa sai ya kakkabe shimfidar sa da shi kuma ya ambaci sunan Allah domin shi bai san abunda ya maye bayan sa ba akan shimfidar shi bayan sa kuma idan yana so ya kwanta to ya kwanta ta gefen daman sa kuma yace” subhanaka rabbi bika wada’atu janbi wa bika arfa’uh in amsakta nafsi fagfir laha wa in arsaltaha fahfazha bima hafizta bihi ibadakassaliheen “
2- idan ya tashi daga bacci yayi addu’a da abunda yazo daga Manzan Allah (SAW), an ruwaito daga Huzaifa Aallah ya kara yadda a gare shi yace: Annabi (SAW) ya kasance idan ya zo wurin baccin sa da daddare sai ya daura hannun sa a karkashin kumatun sa annan sai ya ce: “allahumma bismika amutu wa ahya, kuma idan ya farka sai yace:alhamdulillahi allazi ahyana ba’ada ma amatana wa ilaihinnushuur “
3- yayi kokarin yin bacci da wuri sai dai in akwai wata lalura, saboda abunda aka ruwaito daga gareshi (SAW) cewa lallai shi yana kin bacci kafin sallar isha’i da kuma zama hira a bayan ta “
4- karhanci yin baci a ruf da ciki, an ruwaito daga Abu huraira Allah ya kara yadda a gare shi yace: Manzan Allah (SAW) ya wuce sai yaga wani mutum ya kwanta ruf da ciki sai ya shure shi da kafar sa sai yace: “lallai irin wannan kwanciyar Allah baya kaunar ta “
5- gujewa wurare masu hatsari ta hanyar daukar mataki akan su, saboda fadar sa (SAW): “lallai wannan wutar abokiyar gaba ce a gare ku idan zakuyi bacci to ku kashe ta”

Ladubban biyan bukata:
1- yin addu’a lokacin shiga bayi,an ruwaito daga Anas cewa lallai Annabi(SAW) ya kasance idan zai shiga bayi sai yace: “bismillah allahumma inni a’uzubiki minal khubuthi walkhaba’ith”
2- yin addu’a lokacin fita daga bayi, an ruwaito daga Aisha matar Annabi(SAW) Allah ya kara yadda a gare ta tace: “Manzan Allah (SAW) ya kasance idan ya fito daga bayi sai yace: “gufranak”
3- kada ya fuskanci alkibila ko kuma ya juya mata baya lokacin da yake biyan bukata, an ruwaito daga Abu huraira Allah ya kara yadda a gare shi, daga Annabi (SAW) yace: “lallai ni matsayina a gare ku kamar matsayin uba ne ga dansa kada dayanku ya fuskanci alkibila kuma kada ya juya mata baya- wato wurin biyan bukata- kuma kada yayi tsarki da kasa da dutse uku babu kashi awaki a ciki ko kuma kashi “
4- suturtuwa daga idanun mutane, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda ya shiga bayi to ya suturtu”
5- kada yayi amfani da hannun daman sa a abunda ake kyamar sa, Annabi (SAW) yana cewa: “idan dayanku nashan abun sha to kada yayi numfashi a cikin kofi kuma idan yaje bayi to kada ya rike zakarin sa da hannun daman sa kuma idan zai share to kada ya share da daman sa”

Ladubban zamantakewar aure:
1- ambatan Allah, ta hanyar da Ananbi (SAW) ya baiyana da fadar sa: “da ace dayanku idan zaije wa iyalin sa sai yace bismillah allahumma jannibnashhaidan wa jannibi shshaidana ma razaktana, in aka kaddara musu samun yaro yo shaidan bazai iya cutar da shi ba”
2- yin wasanni da zolaya, saboda fadarsa (SAW) ga jabir: “kayi aure ya kai Jabir?: “sai nace:eh, sai yace:budurwa ko bazawara?sai nace: bazawara ce, sai yace: “ya baka auri budurwa ba kayi mata wasa kuma itama tayi maka wasa ka bata dariya itama ta baka dariya”
3- soyaiya da tausayawa ga iyalan sa ta hanyar sumbata, an ruwaito daga Aisha Allah ya kara yadda a gare ta tace: Manzan Allah (SAW) ya kasance yana sumbata alhali yana azumi kuma yana runguma alhali yana azumi sai dai shi yafi ku iya mallakar sha’awar shi”
4- yaji dadi shi da iyalin sa ta kowace hanya suka so amma da sharadin da Annabi (SAW) ya baiyana shi ga Umar lokacin da ya zo wurin Manzan Allah (SAW) sai yace: ya manzan Allah na halaka,sai yace: “me ya halaka ka?” sai yace:na sadu da iyali na da daddare ta baya amma a gaban ta,sai yace: sai Manzan Allah (SAW) bai ce masa komai ba, sai yace: sai wahayi ya sauka ga Manzan Allah (SAW) na wannan ayar (matanku gonaki ne a gare ku to kuzo wa gonakin ku ta yadda kuke so) ka zo ta gaba ko ta baya, sai dai ka kiyayi dubura da kuma lokacin haila”
5- tsare abunda ke sakanin su na kebantacciyar alaka, saboda fadar sa (SAW): “lallai daga cikin mafi sharrin mutane matsayi a wurin Allah shi ne mutumin da zai sadu da matar sa itama ta sadu dashi sai kuma ya koma yana yada sirrin ta”

Ladubban tafiya (balaguro):
1- mayarda kayan zalunci da kayan ajiya ga ma’abotan su, da kuma biyan bashi da ajiya abunda iyalinshi zasu ci, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda yasan ya zalunci wani a mutuncin shi ko kuma wani abu to ya nemi yafiyar shi yau,kafin wata rana tazo da babu dinari ko dirhami in yanada aiki na kwarai sai a diba daga ciki gwargwadan zaluncin da yayi, in kuma baida lada sai a dibo zunuban abokin sa sai a zuba masa”
2- an karhanta yin tafiyar sa shi kadai, saboda hanin da Annani (SAW) yayi akan haka, sai dai in yana cikin larura kuma bai samu kowa ba, saboda fadar manzan Allah (SAW) ga wani mutum da ya dawo daga tafiya: “dawa kayi tafiya?” sai yace ba kowa, sai Manzan Allah (SAW) yace: “me tafiya shi kadai shaidan ne, kuma matafiya su biyu shaidanu ne, mutum uku kuma matafiya ne”
3- zaban abokai na kwarai kuma su zabi daya su shugabantar da shi, saboda fadar sa (SAW): “idan mutum uku suka fita dan tafiya to su shugabantar da dayan su”
4-ya sanar da iyalin sa lokacin da zai dawo gare su, hakika Manzan Allah (SAW) ya kasance yana aikata haka, kuma kada ya fado musu cikin dare, saboda fadar sa (SAW): “idan dayanku ayi tafiya mai tsawo to kada ya fadowa iyalan sa cikin dare”
5- yayi bankwana da iyalan sa da abokan sa da iyan rakiyar sa, saboda fadar sa (SAW): “mafi alkairin abokai a wurin Allah shi ne wanda yafi alkairi ga abokin sa, kuma mafi lakairin makwabci a wurin Allah shi ne wanda yafi alkairi ga makwabcin sa”
6- yayi saurin komawa ga iyalan sa idan ya biya bukatar sa, saboda fadar sa (SAW): “tafiya wani yanki ne na azaba ana hana dayanku cin abincin sa da abin shan sa da baccin sa, idan dayan ku y agama biyan bukatar sa- abunda yaje yi-t0 yayi saurin komawa ga iyalin sa”

Ladubban hanya:
1- Annabi (SAW) yana cewa: “kashedin ku da zama a kan hanyoyi” sai suka ce: ya manzan Allah babu makawa sai munzauna a wuraren zaman mu muna labara a cikin su, sai Manzan Allah (SAW) yace: to in kun doge sai kun zauna to ku baiwa hanya hakkin ta” sai sukace: meye hakkin hanya ya manzan Allah? Sai yace: “runtse ido, da kamewa daga cutarwa, da maida sallama, da umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna”  kuma a cikin wata ruwaya: “kuma ku taimaki mabukaci kuma ku shiryar da batacce”
2- ya kiyaye hanya kada ya bata abben amfani na kowa da kowa, Annabi (SAW) yana cewa: “kuji tsoran wanda ake la’anta guda biyu sai suka ce: meye suke aikatawa su wanda ake la’anta su biyu? Sai yace: “wanda ke biyan bukata a kan hanyar mutane ko kuma inuwar su”
3- kada ya dauko abunda zai cutar da wanin sa tare da shi, saboda fadar sa (SAW): “idan dayan ku ya wuce ta masallacin mu ko kuma kasuwar mu kuma tare da shi akwai mashi to ya rike tsininta ko kuma y ace ya rufe da tafin hannun sad an kada ya sami wani daga cikin musulmai da shi”

Ladubban siye da siyarwa:
1-asali a cikin kasuwanci shi ne halacci domin shi yana tsaye ne akan bani in baka na amfani tsakanin me siya da me siyarwa, amma in aka sami cutarwa ga daya daga cikin su buyun ko kuma gare su su duka to sai ya canza daga halcci zuwa haramci, saboda fadar Allah madaukaki: “yaku wadanda sukayi imani kada ku dinga cin dukiyoyin ku a tsakanin ku da barna”
2- kuma musulunci ya sanya neman arziki ta hanyar kasuwanci daga cikin mafi tsabtar hanyoyin neman arziki kuma mafi falala, an tambaye manzan Allah (SAW) wane nema ne yafi tsabta? Sai yace: mutum yayi aiki da hannun sa da kuma kowane kasuwanci karbabbe”
3- kuma hakika musulunci ya kwadaitar akan amana a cikin kasuwanci, annabi (SAW) yana cewa: “dan kasuwa me gaskiya me amana yana tare da annabawa da siddikai da shahidai”
4- baiyana aibobin da ke cikin kayanda za’a siyar in an samu, Annabi (SAW) yana cewa: “baya halatta ga wani ya saida wani abu sai ya baiyana abunda ke cikin sa, kuma baya halatta ga wanda ya san hakan yayi shiru sai yayi bayanin sa”
5- rashin yin algush a cikin kayan siyarwa da bayanin aibi ga mai siya, an ruwaito daga Abu huraira Allah ya kara yadda a gare shi, cewa lallai Annabi (SAW) y wuce ta kusa da wani buhu na hatsi sai ya sa hannun shi a cikin sa sai yatsunshi suka jike, sai yace: “me wannan ya kai me awan hatsi? Sai yace: ruwan sama ne ya bige shi ya manzan Allah, sai yace: to dan me baka sa shi ba a saman hatsin dan mutane su gan shi! Duk wanda yayi algush to bai tare da ni”
6- gaskiya da kuma rashin karya, Annabi (SAW) yana cewa: “mutum biyu masu ciniki suna da zabi matukar basu rabu ba, ko kuma yace har sai sun rabu, in sukayi gaskiya sukayi wa juna bayani sai a sa musu albarka a cikin cinikin nasu su in kuma suka boye kuma suka yi karya sai a shafe albarkar da ke cikin cinikin nasu”
7- yin sauki a wurin siye da siyarwa, dan shi hanya ce da ke karfafa alaka tsakanin me siya da siyarwa, da kuma lalata kokarin gudu bayan amfanin da ke yanke alaka ta iyan’uwantaka da mutumtaka, Annabi (SAW) yana cewa: “Allah yayi rahama ga mutumin da yake me sauki in zai siyar kuma me sauki in zai siya kuma me sauki in ai bi hakkin sa”
8- rahin rantsuwa a kasuwanci, saboda fadar sa (SAW): “kashedin ku da yawan rantsuwa a kasuwanci, domin ita tana sa a sakaya amma tana tafiyar da albarka”
9- ya kwadaitar akan warware ciniki da wanda yayi nadama ya fasa cinikin, Annabi (SAW) yana cewa: “duk wanda ya warware wani ciniki da yayi da dan’uwan sa to shima Allah zai warware masa matsalolin s ranar alkiyama”
Wadannan sune wasu daga cikin ladubba na musulunci, amma kuma akwai wasu ladubban daban, inda zamu bibiye su da zancen zaiyi tsawo, ya wadatar mu sani cewa babu wani abu da yake da alaka da al’amuran mutane kebantattu ko kuma dukkan su face akwai fuskantarwa na kur’ani ko kuma hadisi da zai iyakance ta kuma ya tsara ta, badan komai ba said an rayuwar musulmi ta zama dukkan ta ibada ce ga Allah da yake yin guzuri da ita na lada.
KARSHEN LITTAFI:
Bari mu rufe wannan binciken da maganganun mutum biyu da suka shiga musulunci, (F. Filweas) yana cewa : “akwai baraka me girma ta zuciya a yammaci, babu wani tsari ko kuma aqida da suka iya taushe shi kua su samar da jin dadi ga mutum a can, duk da irin yalwar dukiya da kuma abunda ake kira habakar tattalin arziki...da tabbatar da dukkan bukatun mutane na kudi, sai dai mutumin yammaci baya gushewa yana jin rudu a cikin rayuwar sa kuma yana tambaya: saboda me nake rayuwa? Kuma ina zan je? Kuma saboda me? Kuma har yanzu babu wanda ya bashi amsa akan wadannan tambayoyin, miskinin bai sani ba cewa maganin da yake nema yana cikin addini mikakke wanda amma bai san komai ba gameda shi sai dai shubuha, sai dai haske ya fara bullowa kuma gari ya fara wayewa, da shigar wasu mutane koda kadan ne cikin turawa zuwa addinin musulunci, kuma baturen yamma ya fara gani karara da idanuwansa, maza da mata suna dabbaka musulunci kuma suna rayuwa da shi, kuma kowace rana wasunsu suna shiga cikin addinin gaskiya, lallai wannan farawa ne ma akayi......... har zuwa karshe.
Kuma (D. Potter)  tana cewa..... musulunci wanda shi ne tsarin Allah, muna samun shi a baiyane a cikin dabi’ar wadanda suke kewaye da mu, da umarnin Allah ne shi kadai duwatsu ke matsawa da tekuna da taurari kuma suke gane hanyoyin su, su suna karkashi umarnin Allah ne mahaliccin su, kamar yadda mutane suke mika wuya ga wata ruwaya cikin ruwayoyi, misali madaukaka ya tabbata ga Allah, su basa magana kuma basa aikata komai sai abunda marubuci ya tabbatar, to hakanan dukkan wata kawar halitta a wannan duniyar- hatta daskararrun abubuwa – dukkan su musulmai ne, sai dai mutum ne yafi cancanta da wannan ka’idar, hakika Allah ya bashi iyanci na zabi, yanada iyanci ko dai ya mika wuya ga Allah, ko kuma ya kawo ma kansa tsare=tsare kuma ya cigaba da tafiya akan addinin sa wanda ya kirkire shi, sai dai abun bakin ciki sai ya zabi na biyu a wurin da yawa daga cikin mutane....... lallai mutane a kasashen turai da america suna karbar addinin usulunci da adadi mai yawa, domin suna kishirwar samun natsuwar rai da kwanciyar hankali, kai da yawa daga cikin wadanda basu damu da addini ba da kuma kiristoci masu bushara wadanda suka fara yunkurin karad da musulunci da kuma baiyana aibobin shi kamar yadda suke rayawa, to suma da kansu sun wayi gari sun zama musulmai, ba dan komai ba sai dan kasancewar ita gaskiya hujjarta me karfi ce babu yadda zayi inkarin ta. Har zuwa karshe.

Ya cika da godiyar Allah
Kuma Allah yayi salati ga Annabin mu Muhammad da iyalan sa da sahabban sa kuma yayi sallama.

 
www.islamland.com
[email protected]