
Allah (s.w) yana cewa : a'a ha idan bai bari ba zamu damqeshi a gaban gwagwalwa* kwakwalwa mai Qarya mia kuskure" Al-alaq 15-16
Allah (s.w) yana cewa : a'a ha idan bai bari ba zamu damqeshi a gaban gwagwalwa* kwakwalwa mai Qarya mia kuskure" Al-alaq 15-16:
Haqiqar ilimi:
kwakwalwar mutum ya kumshi tsagi huxu: tsagin gaba "frontal lobe" da tsagin baya" Occipital Lobe" tsayin tsakiya" Temporal lobe" da tsagin kewaye" parietal lobe" ko wane tsagi nada nasa aiki da yake yi na musamman amma agefe xaya suna cika junansu ne. tsagin gaba shi yake kula da abinda ya shafi suluki da magana kamar yadda yake xauke da wasu vangarorin kula da garkuwar jiki , sannan vangaren gaba na kwakwalwa shi yake kula da abinda ya shafi tunani da rabewa tsakanin abubuwa. Akwai wani yanki da ake kira da Broca shi yake haxa kwakwalwar mutum da sauran gavovinsa wurin isar da saqo kamar baki da hanki da maqogwaro da sauransu. Amma sauran abinda ya shafi vangaren goshi shi yake kula da dulkkan abubuwan da mutum yake aikatawa na vangaren tunani da aikata wasu abubuwa da warware dukkan matsalolinsa .
Fuskacin mu'ujiza:
ba agano waxannan abubuwa sai bayan cigaban ilimi awannan zamani, kuma ga Al-kur'ani mai girma ya kevance wannan vangare na gaban goshi da ambato na cewa mai qarya mai kuskure, sannan yace kuma zai damqeshi , wato wurin yin masa hisabi domin shi yake kula da dukkan gavovin mutum.
Saboda da hikimar unbangiji ya sanya wannan yanki shine zai riqa yin sujjada da kusanta zuwa ga Allah …. ( lalle sallah tana hani ga Alfasha da abin qi ,Ambaton Aallah shine mafi girma , Allah na sane da abanida kule aikatawa")"al-ankabut 45.
© Copyright Islam land أرض الإسلام . All Rights Reserved 2017