ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI A CIKIN ALKUR’ANI

ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI A CIKIN ALKUR’ANI

ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI A CIKIN ALKUR’ANI

عيسى عليه السلام في القرآن بلغة الهوسا

 

 

 

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha

د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة

 

Fassara

European Islamic Research Center (EIRC)

المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية

& Muhammed Khamis

Wanda ya bibiyi fassara

Faiz Shuaib Adam

 

www.islamland.com

 

ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI A CIKIN ALKUR’ANI

da sunan allah mai rahama mai jin kai

GABATARWA

Kafin mu shiga cikin bayani game da rayuwar shugaban mu Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi a cikin alkur’ani ya kamata ne mu dan yi shinfida ga wannan maudu’in da wata iyar gabatarwa wacce zamu bayyana farkon halitta a cikinta da kuma tushen dan adam da kuma hikimar halittar su da kuma matsananciyar bukatuwar su ga abincin ruhi wanda yake tabbatar musu da natsuwa da kuma kwanciyar hankali, wanda yake rikiduwa cikin aqidar tsara al’amuran su da kuma na al’ummar su da kuma inda tunanin su ke fuskanta da ababaen da suka fatan su samu na ingantaccen inda suka fuskanta, hakan kuwa na cikin ababen da aka shar’anta wanda ke tabbatar musu kiyaye hakkoki da tsare rayuka da kuma kare mutunci da dukiya, kuma wadannan shari’u basa zuwa sai ta hanyar wasu mutane wanda suke isar da sako daga Allah sune Annabawa da Manzanni tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su.

Dukda cewa Alkur’ani mai girma shima daya ne daga cikin littattafan da suka sauko daga sama, hakika Allah ya saukar da shi ga Annabi Muhammad (S.A.W) cikamakin manzanni dan ya zama shi ne littafi na karshe wanda ya sauko daga sama, saboda haka ne ya zama littafi na duk duniya baki daya wanda ya dace da kowane zamani da kuma lokaci kuma ya tattaro dukkan dukkan abunda murtane ke bukata dan tabbatar da jin dadin su a nan duniya da kuma lahira.

Daga cikin abunda Alkur’ani yayi bayanin sa a kwai jerin labarin faruwar halitta da kuma samuwar wannan duniyar da kuma ci gaban da aka samu a cikin ta, ta hanyar uslubi na gaske wanda hankali lafiyayye ke karba da kuma fidira tatacciya da mandiki ingantacce wanda aka tace shi daga kwaikwayo, hakika Alkur’ani mai girma ya maida halittan wannan duniyar da abunda ke cikin ta zuwa ga Allah shi kadai bashi da abokin taraiyya.

Kuma hakika manzan musulunci Muhammad (S.A.W) me isar da sako daga Allah yayi bayanin yadda aka fara halitta a cikin hadisin Imran binil Husain inda yace: “ wasu mutane daga cikin mutanen yaman sun zo wurin manzan Allah (S.A.W) sai suka ce: ya manzan Allah munzo wurinka ne dan ka fahimtar da mu addini kuma mu tambaye ka game da farkon wannan al-amari (farkon halitta)? Sai Annabi (S.A.W) yace:” Allah ya kasance tun farko babu komai a tare da shi kuma al’arshin sa ya kasance akan ruwa sai ya rubuta komai a cikin lauhil mahfuzi sa’nnan sai ya halicci sammai da kasa” “sahihu ibn Hibban”.

Sai Annabi (S.A.W) ya baiyana musu abunda yafi mahimmancin abunda suka tambaya shi ne tabbatar da cewa Allah na nan tuntuni shi kadai, sai yace: “Allah ya kasance yana nan tun tuni kuma babu komai sai shi” wato ma’na Allah ya kasance tun farkon lamari yana nan kuma babu kowa tare da shi, sai ya fa’idantar da su cewa dadantaka ta kai tsaya ta Allah ce shi kadai, kuma lallai wanda babu farkon samuwar sa shi ne Allah tsarkakakke madaukaki kawai, babu wanda ke taraiyya da shi cikin wannan siffan tashi cikin halittu, domin Allahn taka bata inganta tare da tabbatar da wani abu tare da Allah cikin samuwar sa tun farko, kuma hakika Allah ya tabbatar a cikin Alkur’ani mai girma cewa shi samamme ne tuntuni shi kadai da ma’ana ta bai daya wacce ta tattaro dukkan ma’anoni dan ya baiyana ma halittun sa cewa wannan duniyar dukkanta halitta ce, an halicce ta daga babu zuwa samuwa, sai Allah madaukaki yace: abunda ke cikin sammmai da kasa suna tasbihi ga Allah kuma shi ne mabuwayi mai hikima (1) mulkin abunda ke cikin sammai da kasa nashi ne yana rayawa kuma yana kashewa kuma shi mai iko ne akan dukkan komai (2) shi ne na farko da karshe kuma na baiyane da boye kuma shi masani ne akan dukkan komai (3)” suratul Hadeed, aya ta: 1-3.

Allah shi ne na farko tun tuni wanda babu farkon samuwar shi, ya kasance shi kadai ne tun farko kuma babu wata halitta tare da shi cikin halittu, yana da dukkan siffofi na kamala da kuma kyau wanda babu wani wanda ke kama da shi a cikin su kuma babu wanda yake daidai da shi a cikin su cikin halittu kamar yadda Allah ya baiyana haka cikin fadar sa madaukaki: “ mahaliccin sammai da kasa ya sanya muku mata daga gare ku kuma ya sanya dabbobi jinsi biyu dan ya yawaita ku ta hanyar su babu wani abu wanda yayi kama da shi kuma shi mai ji ne mai gani (11) mabudan sammai da kasa nashi ne yana shimfida arziki ga wanda yaga dama kuma ya kaddara lallai shi masani ne ga dukkan komai (12)” suratush shurah, aya ta: 11-12.

Kamar yadda Allah ya baiyana rashin yiwuwar iya siffanta shi dari bisa dri da kuma kewawa wurin sanin sa da girman wannan abun bautan ya baiyyana ga bawa wanda yake bauta masa sai tsoransa da firgicin sa su auko a cikin zuciyar sa sai ya kankan da kai a gare shi kuma sai ya tabbatar da rububiyyar sa da Allahn takakar sa, Allah madaukaki ya fada yana mai bayani akan gaskiyar wannan lamarin: yana sanin abunda ke gaban sau da bayan su kuma su baza su iya kewaye shi ba da sanin su (110) kuma fuskoki sun kaskanta ga rayaiyye madawwami kuma duk wanda ya dauko zalunci to hakika ya tabe (111) kuma duk wanda ya aikata aiki na kwarai alhali shi mumini ne to baya tsoran zalunci ko kuma tawaya (112)” suratu Daha, aya ta: 110-112.

Duk wanda ba Allah ba to fararre ne kuma halitta ne Allah ya halicce shi da ikon sa sai ya fito da shi daga rashi zuwa samuwa, kamar yadda Allah ya baiyyana haka cikin fadar sa: wannan shi ne Allah ubangijin ku mahaliccin dukkan komai babu abun bauta da gaskiya sai shi to ta yaya ake juyadda ku daga bin gaskiya (62) haka nan ake juyad da wadanda suka kasance da ayoyin Allah suke karyatawa (63) shi ne wanda ya sanya muku kasa tabbatatta da sama ginanna kuma ya suranta ku sai ya kyautata suran halittarku kuma ya azurta ku daga kayan marmari wannan shi ne Allah ubangijin ku Allah yayi albarka ubangijin talikai (64) shi ne rayaiyye babu abun bauta da gaskiya sai shi to ku bauta masa kuna masu tsarkakae addini a gare shi godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai (65) kace lallai ni am hane ni daga bautar abunda kuke bauta ma koma bayan Allah lokacin da hujjoji suka zo mini daga ubangiji na kuma an umarce ni da in mika wuya ga ubangijin talikai (66)” suratu Gafir, aya ta: 62-66.

Kuma daga cikin tabbatacciyar aqidar musulmai akwai cewa lallai Allah yana halittan abunda yaga dama kuma yana aikata abunda yake so babu mai mayadda hukuncin sa kuma babu mai gyara ga lamarin sa abunda ya so mai aukuwa ne kuma umarnin sa mai kasancewa ne, kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: kuma ubangijinka yana halitta abunda yaga dama kuma ya zabazabi ba a wurin su yake ba tsarki ya tabbata a gare shi kuma ya daukaka daga abunda suke shirka da shi (68) kuma ubangijin ka yana sanin abunda zukatan su ke boyewa da kuma abunda suke baiyanawa (69) kuma shi ne Allah babu abun bauta da gaskiya sai shi godiya a gare shi take farko da karshe kuma hukunci nashi ne kuma zuwa gare shi zaku koma (70)” suratul Kasas, aya ta: 68-70.

Allah baya halitta dan wasa kuma baya barin halittun sa kara zube, ba’a halicci wata halitta ba a wannan duniyar sai dan wata hikima kuma ba’a halicce su ba sai dan suyi wani aiki, kuma wannan hikimar zata iya zama mun santa kuma zata iya zama bamu santa ba, hakika ilimin zamani ya baiyanar a wannan zamanin irin shakuwar da halittu masu rai sukeyi da junan su cikin abunda ake kira jerin gwanan hanyar abinc[1] da kuma shakuwar halittu da wasu wanda ba suba cikin sauran halittu daskararu, kamar tasirin haske da duhu da kuma rana da wata da kuma dare da yini a gare su, wannan shi ne abunda aka sanar da mu kuma nan gaba za’a zo da sababben bincike, Allah yayi albarka mafi kyautata halitta wanda yace: lallai mu mun halicci kowane abu da kaddara (49)” suratul Kamar, aya ta: 49

 

 

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha

../../../../../../../Documents/MY%20SITES%20&%20PROJECTS/PROJECTS%20&%20SITES/ISLAML

www.islamland.com

[email protected]

 

 

BABI NA FARKO

FARKON ABUNDA AKA FARA HALITTA

Alkur’ani wanda yake maganar Allah ne yayi bayani cewa lallai farkon duniya an halicce ta ne ba daga wani abu ba kawai da kaddarawar Allah da kuma ikonsa ya halicce ta da kuma umarnin sa kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: wanda ya kirkiro halittan sammai da kasa kuma idan ya hukunta faruwar wani abu to kawai yana ce masa ne kasance sai ya kasance (117)” suratul bakara, aya ta: 117.

Kuma Annabi Muhammad (S.A.W) yayi bayani cewa lallai ruwa shi ne farkon abunda aka halittun da Allah ya samar kuma shi ne tushen komai cikin halittu, Allah ya halicce shi da ikon sa ba tare da wani tushe ba kuma ya sanya shi tushe na halittar duniya baki daya, sai yace: “ an halicci komai daga ruwasahihu ibn Hibban.

 

HALITTAN SAMMAI DA KASSSAI

Allah ya bada labari a cikin Alkur’ani cewa ya halicci sammai guda bakwai da kassai guda bakwai a cikin kwanaki shida ba tare da gajiya ba, sai yace: kuma hakika mun halicci sammai da kassai da abunda ke tsakanin su a cikin kwanaki shida kuma babu abunda ya same mu na gajiya (38)” suratu Qaaf, aya ta: 38.

Duk dacewa yana da iko madaukaki akan halittar su cikin kiftawar ido ko kuma abunda yafi kusa da haka, kamar yadda ya baiyana haka cikin fadar sa: kuma umarnin mu bai kasance ba face sai daya kamar kiftawar ido (50)” suratul Kamar, aya ta: 50.

In aka ce: to dan me bai halicce su ba cikin sakan daya matukar yana da iko yace musu kasane sai su kasance?

Ibn jauzy ya fada game da baiyana wasu daga cikin hikimar hakan:

Na farko: lallai Shi yayi nufin samar da wani abu a kowace rana wanda mala’iku zasu dinga girmama hakan da kuma dukkan wanda yake kallon sa.

Na biyu: lallai hakan tabbaci ne na shimfida ga abunda za’a halitta ga Annabi Adam da zuriyar sa tun kafin a halicce shi, hakan zai fi girma wurjen girmama shi a wurin mala’iku.

Na uku: lallai gaggawa yafi karfi ta bangaren iko, shi kuma tabbata yafi tasiri ta bangaren hikima, sai yayi nufin baiyana hikimar sa a cikin haka, kamar yadda yake baiyana ikon sa cikin fadar sa: kasance sai ya kasance”.

Na hudu: lallai shi ya koyarda bayin sa tabbatatuwa, duk abunda ya tabbata bazai gushe ba, abunda yake gushewa shi ne yafi kamata da tabbatuwa.

Na biyar: lallai wannan jinkirin wurin halittar wani abu bayan wani abu, yafi nisantuwa wurin tunanin cewa hakan ya auku ne da dabi’a ko kuma da yarjejeniya.

Da kuma wata hikimar wacce Kurdaby Allah yayi masa rahama ya ambata- a cikin tafsirin sa “ Aljam”i li Ahkamil Kur’an” sai yace: Allah ya halicce su ne cikin kwanaki shida, saboda komai nada lokaci a wurin sa, da wannan sai ya baiyana rashin gaggawa wajan yin ukuba ga masu sabo, saboda komai yana da lokaci n sa.

Kuma bayani filla-filla ya zo a cikin Alkur’ani game da halittar sammai da kasa cikin fadar Allah madaukaki: kace shin yanzu ku za ku dinga kafurce ma wanda ya halicci kasa a cikin kwana biyu kuma ku dinga sanya masa kishiyoyi wannan shi ne ubangijin talikai (9) kuma sai dora mata duwatsu a samanta kuma ya sanya albarka a cikin ta kuma ya kadda abincin ta a cikin ta a cikin kwanaki hudu dai dai ne ga masu tambaya (10) sa’nnan sai ya daidaita a sama alhali lokacin ita hayaki ce sai yace mata da kasa ku taho kuna masu biyaiya ko kuma rashi biyaiya sai suka ce mun zo muna masu biyaiya (11) sai ya kaddara su sammai bakwai a cikin kwana biyu kuma yayi ahayi a ckin kowace sama da al’amuranta kuma muka kawata saman duniya da fitilu da kuma tsaro wannan kaddarawa ne na mabuwaye masani (12)” suratu Fussilat, aya ta: 9-12.

Sayyid qutub yana cewa a cikin littafin sa “ Fi zilalil kur’an” .....wadannan kwanaki biyu wanda Allah ya halicci kasa a cikin su, da kuma kwanaki biyu wanda ya halicci duwatsu a cikin su kuma ya kaddara abinci kuma ya saukar da albarka a cikin su sai suka cika daidai cikin kwanaki hudu.....lallai su babu kokwantu kwanaki ne cikin kwanukan Allah wanda shi ne yasan irin su, su ba irin kwanukan mu bane na duniya.....kuma kwanakin da aka halicci kasa a cikin su da farko, sa’annan sai aka samar da duwatsu a cikin su, kuma aka kaddara abinci a cikin su, su wasu kwanuka ne na daban wanda ake kiyasta su da wani ma’auni na daban wanda basu san hi ba, sai dai mu mun san cewa sunfi kwanakin duniya da muka sani tsawo sosai kuma mafi kusan abunda zamu sawwara da shi daidai da abun da ilimin mu ya kai na iyan adam cewa lallai su wasu lokuta ne wamda suka gabata a ban kasa zamani bayan zamani, har ta tabbata kuma bayan ta yayi kauri, kuma ta zama dai dai da hadda za’a iya rayuwa a cikin ta wadda muka sani.

 

 

 

HIKIMAR HALITTAN MUTANE

A nan ne tambaya ta hankali ke zuwa cewa: me dalilin halittar mutane wanda Allah ya yi musu irin wannan karramawar ta hanyar hore musu dukkan abun da ke cikin wannan duniyar? Kuma miye dalilin halittar su?

Hakika Alkur’ani mai girma ya baiyana hikimar halittan mutane a fili ta yadda kar ya bar fage dan lalube da hange na kwakwale da tunane-tunane, sai Alkur’ani yayi bayani cewa lallai su an halicce su ne dan wani abu mai girma kuma babba saboda shi ne Allah ya halicci sammai da kasa kuma saboda shi ne aka halicci aljannah da wuta, wannan kuwa ba komai bane face bautar Allah shi kadai bashi da abokin taraiyya kamar yadda Allah ya baiyana hak da fadar sa: kuma ban halicci aljanu da mutane ba sai dan su bauta mini (56) bana nufin wani arziki daga wurin su kuma bana nufin su ciyar da ni (57) lallai Allah shi ne mai azurtawa ma’abocin karfi mai tsanani (58)” suratuz Zariyat, aya ta: 56-58.

Rayuwar ba kamar yadda i’yan gurguzu da mulhidai suke tunani bace cewa babu tashi bayan mutuwa kuma babu hisabi kuma babu ukuba kawai rayuwa ce da karewa, kamar yadda Allah ya bada labarin su da fadar sa: ´kuma suka cea ba wani abu bane face rayuwar mu ata duniya muna mutuwa kuma muna rayuwa kuma babu abunda ke halaka mu face zamani kuma su basu da wani ilimi akan haka kawai su suna zato ne (24)” suratul Jasiya, aya ta: 24.

Babu abunda yafi wahala irin ace mutum ya rayu da wannan t tunanin kuma babu ran da tai tozarta feye da ran da ta kudurce wannan , saboda mutum kamar yada yake da bukatuwa ta kosarda burin sa na jiki a cikin a bunda yake bukata haka nan ma bukatun sa na ruhi, kuma wannan bai yiwuwa sai ta hanyar sanin Allah shi kuma wannan bai yuwuwa sai ta hanyar bin abunda manzanni suka zo da shi, kuma ita kadiyyar ilhadi da kuma inkarin tada mutane bayan mutuwa zance ne wanda ba wannan zamanin aka fara shi ba, a a zance ne da yake ta yawo tsakanin mutane tun da wanda suke mulhidai ne suna koyar da ita daga wasu a’umma zuwa wasu wadanda ke bayan su dan wanda Allah ya tayshe basirar sa daga gaskiya ya rungume ta saboda kauda kai da yayi daga manhajin Allah da kuma hukuntar da hankali da yayi a inda ba’a hukuntar da hankali a cikin sa, Allah madaukaki yana cewa: sai muka aika da manzo daga cikin su zuwa gare su cewa ku bauta wa Allah baku da wani abun bauta koma bayan sa shin baza ku ji tsoran Allah ba (32) sai manya suka ce daga cikin mutanen sa cikin wadanda suka kafurta kuma suka karyata da haduwar lahira kuma muka jiyar da su dadi a rayuwar duniya wannan ba komawai bane face wani mutum daga cikin ku yana cin irin abunda kuke ci na abinci kuma yana shan irin abunda kuke sha (33) kuma idan har kuka yi biyayya ga wani mutum irin ku to lallai ku hasararru ne (34) yanzu zai dinga muku alkawari cewa lallai ku in kun mutu kuma kuka kasance turbaya da kasusuwa wai lallai za’a fitar da ku (35) har abada abunda yake muku alkawari bazai faru ba (36) kawai ba wane abu bane face rauwar mu ta duniya muna mutuwa kuma muna rayuwa kuma mu baza’a tashe mu ba (37)” suratul muminuun, aya ta: 32-37.

Hakika mutane sun kasance a farkon halitta al’umma ne guda daya kansu a hade ba a rarrabe ba saboda suna zaune ne a wuri daya iyakantacce kuma basu da yawa sai dai bayan da yaran Adam sukayi yawa kuma inda suke zaune yayi musu kadan sai hakan ya tilasta ma wasun su tashi daga inda suke zuwa wasu bangarori na ban kasa da kuma yaduwa cikin ta dan bincike da neman arziki, kuma hakika Alkur’ani ya baiyyana wannan hakikar zancen inda Allah madaukaki ya fada: kuma mutane basu kasance ba a da face al’umma guda daya sai suka rarrabu badan wata kalma wadda ta gabata daga ubangijin ka ba da anyi hukunci tsakanin su cikin abunda suka kasance suna sabani a cikin sa (19)” suratu Yunus, aya ta: 19.

Sai wannan warwatsuwar a bayan kasa ta haifar da sabanin ta bangaren yaruka da al’au haka nan ma da kuma nisanta daga tushen addini na farko, yana daga cikin adalcin na Allah wanda baya zalunci da mugunta shi ne cewa baya yin azaba sai bayan yayi gargadi ta hanyar wanda yake aikowa cikin Manzannin sa dan suyi wa mutane bayanin ingantacciyar hanya ta gaskiya wacce take kaiwa zuwa gare shi, sai rahamar Allah ga mutane ta hukunta cewa bazai yi musu ukuba ba har sai ya aiko musu da manzanni wadan da suke nuna musu hanyar shiriya, kuma suna tsawatar da su daga bin hanyar bata, kamar yadda mukayi bayani a baya, saboda haka ne ma babu wata al’umma da ba’a aika mata da manzo ba da kuma sako cikin koane amani, kamar yadda Allah madaukaki ya baiyyana haka cikin fadar sa: lallai mu mun aiko ka da gaskiya kana mai bushara da kuma gargadi kuma babu wata al’umma face sai mai gargadi ya je mata (24)” suratu Fadir, aya ta: 24.

Allah madaukaki ya kasance yana aikawa da manzanni da Annabawa tsakanin wani lokaci zuwa wani lokaci dan su maida mutane zuwa ga kadaita ubangijin su da kuma bauta masa bayan sun kauce wa a kidar su kuma manhajin su ya samu matsala, dukkan su tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su tun daga na farkon su har zuwa na karshen su da’awar su iri daya ce wacce ta hadu akan tauhidi wanda shi ne kadaita Allah da bauta wurin kudurcewa da zantuttuka da kuma aiyyuka da kuma kafurce ma dukkan abunda ake bauta mawa koma bayan sa saboda fadar Allah madaukaki: kuma hakika mun aika da manzao a cikin kowace al’umma cewa ku bauta ma Allah kuma ku nisanci dagutu daga cikin su akwai wadanda Allah ya shiryar kuma daga cikin su akwai wadanda bata ta tabbata a kan su kuyi tafiya a ban kasa sai kuyi dubi kuga yaya karshen masu karyatawa take kasancewa (36)” suratun Nahl, aya ta: 36.

Kuma wadannan manzanni Allah madaukaki yana aiko su ne saboda kada ya zamo an samu wata hujja akan Allah ga mutane bayan manzanni, kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari da fadar sa: manzanni ne masu bushara da kuma gargadi saboda kada a samu wata hujja akan Allah bayan aiko da manzanni kuma Allah mabuwayi ne mai hikima (165)” suratun Nisa’i, aya ta: 165.

Dukda sanin cewa dukkan manzanni da annabawa sun kasance mutane ne su kuma basuda wani abu na siffan Allahn taka,babu wani bambanci tsakanin su da wasun su cikin mutane sai da abunda Allah ya kebance su da shi kawai na ma’asumanci cikin abunda suke isarwa daga gare shi da kuma abunda ya kebance su da shi na mu’ujiza wacce take gudana ta hannayen su dan ta zama aya ga mutanen su dan suyi imani kuma su tabbatar da gaskiyar manzancin su da Annabtakan su, Allah madaukaki yana cewa: kuma bamu aiko ba gabanin ka cikin manzanni face su suna cin abunci kuma suna zuwa kasuwa kuma muka sanya sashinku fitina ne ga sashi ko zaku iya hakuri kuma ubangijin ka ya kasance mai hakuri (20)” suratul Furkan, aya ta: 20.

Kuma Allah ya baiyyana mutuntakan su da kuma irin abunda suke da shi na fidira hakika sun kasance suna da mata da kuma zurriyya saboda kada wani yayi tunanin cewa su da ban ne da mutane, Allah madaukaki yana cewa: kuma hakika mun aika da manzanni tun gabanin ka kuma muka sanya musu mata da kuma zuriyya kuma baya kamata ga wani manzo yazo da wata aya sai da izinin Allah kowane abu yana da lokaci rubutacce (38)” suratul Ra’ad, aya ta: 38.

Kuma Allah madaukaki yana cewa: hakika wadanda sukace lallai Allah shi ne masihu dan Maryam sun kafurta kuma masihu yace yaku bani isra’ila ku bautawa Allah ubamgiji na kuma ubangijin ku lallai duk wanda yayi shirka da Allah to hakika Allah ya haramta masa shiga aljannah kuma makomar sa wuta kuma azzalumai basuda mataimaka (72) hakika sun kafurta wadanda sukace lallai Allah dayan uku ne kuma babu wani abun bauta sai dai abun bauta guda daya kuma idan basu hanu ba daga abunda suke cewa to lallai azaba mai radadi zata shafi wadanda suka kafurta daga cikin su (73) shin baza su tuba ba zuwa ga Allah kuma su nemi gafarar sa kuma Allah mai yawan gafara ne mai jin kai (74) masihu dan Maryama ba kowa bane face manzo wanda manzannin sun shude gabanin sa kuma mahaifiyarsa ta kasance mai gaskiya dukkan su biyun sun kasance suna cin abinci ka duba yadda muke musu bayanin ayaoyi sa’annan kuma ka duba yadda ake juya su (75) kace shin yanzu zaku dinga bauta ma wani abu daban koma bayan Allah wanda baya mallakar cutarwa ko amfanarwa gare ku kuma Allah shi ne mai ji masani (76) kace ya ku ma’abota littafi kada ku wuce gona da iri cikin addinin ku da abunda ba gaskiya ba kuma kada ku dinga bin san ran wasu mutane wadanda sun bace tun gabanin haka kuma sun batarda mutane da yawa kuma sun bata daga hanya madaidaiciya (77)” suratul Ma’idah, aya ta: 72-77.

Kuma basu da wani abu da ya shafi al’amuran ubangiji da bauta, basuda ikon yin tasarrufi cikin duniya kuma basa mallakawa kansu ko wanin su cutarwa ko amfanarwa kuma basa mallakar mutuwa ko rayuwa ko kuma tashi daga kabari, Allah madaukaki yana cewa yana bada labari gameda manzan sa Annabi Muhammad (S.A.W) wanda shi ne mafi falalar mutane kuma mafi tsarkin su: kace bana mallakar amfanarwa ko cutarwa ga kaina sai abunda Allah ya so kuma da ace nasan gaibu da na yawaita aikin alheri kuma da ba wani abu da zai same ni na cutarwa ni ba kowa bane face mai gargadi da bushara ga mutanen da sukayi imani (188)” suratul A’araf, aya ta: 188.

 

 

 

HALITTAR ANNABI ADAM UBAN MUTANE

Hikimar Allah da nufin sa sun zartu akan cewa zai sanya halifa a ban kasa wanda zai raya ta kuma za’a samu yaduwa cikin zurriyyar sa wadanda hakan da izinin Allah zai tabbatar da abunda hikimar sa ta hukunta na raya kasa, kuma dan ta zama gidan jarabawa da fitina a gare su, dan mai biyaiyya a cikin su gare shi ya baiyyana cikin bayin sa kuma waye mai sabawa kuma waye mumini sannan kuma waye zai kafurta, Allah madaukaki yana cewa: kuma lokacin da ubangijin ka yace wa mala’iku lallai ni zan sanya halifa a ban kasa sai suka ce yanzu zaka saka a cikinta wadanda zasu yi barna a cikin ta kuma su zubarda jini kuma alhali mu muna tasbihi a gare ka kuma muna tsarkake ka sai yace lallai ni na san abun da baku sani ba (30)” suratul Bakara, aya ta: 30.

Sai wannan halifan ya zama shi ne Annabi Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi uban mutane na karshe cikin nau’o’in abunda Allah madaukaki ya halitta, kuma an halicce shi ne ranar juma’a kamar yadda manzan Allah (S.A.W) ya baiyana haka cikin fadar sa: mafi alherin yini da rana ta bullo a cikin sa shi ne ranar juma’a, a cikinta ne aka halicci Adam, kuma a cikin ta ne aka shigar da shi aljannah, kuma a ciki ta ne aka fitar da shi daga cikin ta, kuma alkiyama baza ta tsayu ba sai ranar juma’a” sahi hu muslim.

Saboda haka ne Allah madaukaki ya zabe ta dan ta zama ranar idi ga musulmai a duk sati, kuma saboda darajar Adam da matsayin sa a wurin Allah sai ya umarci mala’ikun sa da suyi masa sujada dan matsayin sa da darajta shi da kuma karamci a wurin halittar sa kuma ya yi busa a cikin sa daga ruhin sa sai dukkan mala’iku suka yi biyaiyya ga umarnin Allah sai dai Iblis wanda ya saba wa Allah kuma yaki yin sujada dan hassada da kuma girman kai daga kansa ga wannan abun halittan wanda Allah ya fifita shi a kan sa, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa:lokacin da ubangijin ka yace wa mala’iku lallai ni zan halicci wani mutum daga turbaya (71) idan na daidaita shi kuma na busa masa daga rai na to ku fadi a gare shi kuna masu sujada (72) sai mala’iku dukkan su sukayi sujada (73) sai dai ibilis ne yayi girman kai kuma ya kasance cikin kafirai (74) sai yace ya kai ibiis meye ya hanaka yin sujada ga abunda na halitta da hannaye na biyu shin kayi girman kai ne ko kuma ka kasance ne cikin madaukaka (75) sai yaceni na fi shi alhri ka halicce ni daga wuta shi kuma ka halicce shi daga turbaya (76) sai yace to ka fita daga cikin ta domin lallai kai tsinanne ne (77) kuma lallai akwai la’anta ta akan ka har zuwa ranar sakamako (78) sai yace ya ubangiji to ka jinkir ta mun har zuwaranar da za’a tada su (79) sai yace lallai kai kana cikin wadanda za’a yi musu jinkiri (80) har zuwa ranar da aka sa lokaci sananne (81) sai yace to saboda buwayarka lallai ni sai na batar da su baki dayan su (82) sai dai bayin ka a cikin su wadan da aka tsiratar (83) sai yace magana ta gaskiya kuma wallahi gaskiya nake fada (84) wallahi lallai sai na cika wutar jahannama da kai da kuma wadanda suka bi ka cikin su baki daya (85)” suratu Saad, aya ta: 71-85.

Sai halittan sammai da kasa ya zama shinfida ne na halittar Adsam amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda hikimar Allah ta hukunta yaduwar mutane zata fara ne daga gare shi da kuma matar sa Hauwa’u, sai Allah madaukaki yayi bayani cewa wannan duniyar da dukkan abbunda ke cikin ta an yi su ne dan dan Adaman halicce su ne dan ya amfana da abunda Allah ya sanya a cikin ta na alheri kuma dan ya zama fili e mai fadi a gare shi wanda ta hanyar sa ne zai iya gano abunda zai tabbatar masa da rayuwa ta karamci, inda Allah madaukaki yace: ashe baku gani ba cewa lallai Allah ya hore muku abunda ke cikin sammai da kasa kuma ya cika muku ni’imar sa a gare ku ta baiyyane da boye kuma daga cikin mutane akwai wadanda suke jayaiyya game da Allah ba tare da wani ililimi ba ko kuma shiriya ko kuma wani littafi mai haskakawa (20)” suratul Luqman, aya ta: 20.

Kuma dan ya zama wuri mai fadi dan tunani da kuma lura wadanda suke kaiwa zuwa ga sanin wannan mahaliccin mai girma wanda ya cancanta da bauta kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: lallai a cikin halittar sammai da kasa da kuma sabawar dare da rana akwai ayoyi ga masu hankali (190) wadanda suke ambatan Allah a tsaye da zaune da kuma kan gefen jikin su kuma suna tunani cikin halittar sammai da kasa suna cewa ya ubangijin mu baka halicci wannan dan wasa ba tsarki ya tabbata a gare kato ka kare mu daga azabar wuta (191) ya ubangijin mu lallai kai duk wanda ka shigar da shi wuta to hakika ka tabar da shi kuma azzalumai basu da mataimaka (192) ya ubangijinmu lallai u munji wani mai kira yana kira zuwa ga imani cewa kuyi imani da ubangijin ku sai mukayi imani ya ubangijinmu to ka gafarta mana zunuban mukuma ka kankare mana kurakuran mu kuma ka kashe mu tare da masu biyiaiyya (193) ya ubangijinmu kuma ka bamu abunda kayi mana alkawari da shi ta hanyar manzannnin ka kuma kada ka tozarta mu ranar alkiyama lallai kai baka saba alkawari (194)” suratu Ali imran, aya ta:190-194.

 

 

FITAR DA ADAM DA MATAR SA HAUWA’U AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SU DA KUMA SHAIDAN DAGA ALJANNAH

Bayan shaidan ya sabawa ubangijin sa yaki yin sujada ga Adam sai Allah ya rubuta masa tabewa da kuma fitarwa daga aljannah, sai shaidan yayi alkawarin batar da iyan adam da kuma kautar da su daga hanya ingantacciya saboda hassadar da ke ransa kamar yadda yayi hassada ga babansu Annabi Adam kamafin haka, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: lokacin da ubangijin ka yace wa mala’iku lallai ni zan halicci wani mutum daga busashshen tabo mai canzawa (28) to idan na daidaita shi kuma na busa masa daga ruhi na to ku fadi a gare shi kuna masu sujada (29) sai mala’iku dukkan su sukayi sujada baki daya (30) sai dai iblis shi yaki ya zama tare da masu sujada (31) sai yace ya kai iblis me ya same ka baka tare da masu sujada (32) sai yace ban zama mai sujada ba ga wani mutum wanda ka halicce shi daga tabo baki busashshe mai caccanzawa (33) sai yace to ka fita daga cikinta domin lallai kai korarre ne (34) kuma kai lallai akwai tsinuwa akan ka har zuwa ranar sakamako (35) sai ya ce ya ubangiji to ka mun jinkiri har zuwa ranar da za’a tada su (36) sai yace lallai kai kana cikin wadanda za’ayi wa jinkiri (37) har zuwa ranar da aka sa lokai sananne (38) sai yace ya ubangiji saboda batar dani da kayi sai na kawata musu duniya kuma wallahi lallai sai na batar dasu baki daya (39) sai dai bayinka a cikin su wadan da ka kubutar (40) sai yace wannan itace hanya ta madaidaiciya (41) lallai bayina baka da wani iko akan su sai dai wadanda suka bika cikin batattu (42) kuma lallai wutar jahannama itace inda akayi musu alkawari dukkan su (43)” suratul Hijr, aya ta: 28-43.

Kuma hakika farkon gabar da iblis yake yiwa Adam ta fara ne cikin a gidan aljannah tun farkon fara halittar shi, sai ya fara dakun sa yana kulla masa makirci kuma yana rudar shi da yaci daga wannan bishiyar da Allah ya hane shi ci daga gare ta dan ya samu ya fitar da shi da matar sa daga cikin ta da kuma irin ni’imar da suke cikin ta, sai shaidan ya samu damar batar da Adam amincin Allah ya tabbata a gareshi har sai da Adam yaci wannan bishiyar sai daga baya yayi nadama akan wannan sabon da yayi kuma ya tabbatar da kuskuran sa sai ya tuba kuma ya nemi gafarar Allah sai Allah ya karbi tubar sa, to sakamakon wannan laifin sai aka fitar da shi daga aljannah da matar shi kuma aka saukar da su zuwa kasa kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: kuma lokacin da mukace wa mala’iku kuyi sujada ga Adam sai sukayi sujada sai dai Iblis ne yaki yin sujada (116) sai mukace ya Adam lallai wannan makiyin ka ne da matar ka to kada ku yadda ya fitar da ku daga aljannah sai ku tabe (117) lallai kai baza ka ji yunwa ba a cikinta kuma baza kayi tsiraici ba (118) kuma lallai kai baza ka ji kishi ba a cikinta kuma baza ka yi walha ba (119) sai shaidan ya samai wasiwasi sai yace ya kai Adam shin bazan nuna maka wata bishiya ba ta dawwama da kuma wani irin mulki da baya yanke wa (120) sai suka ci daga gare ta sai al’aurar su ta baiyana a gare su sai suka fara boye ta da ganye na aljannah kuma sai Adam ya saba wa ubangijin sa sai ya bace (121) sa’annan sai ubangijin sa ya zabe shi sai ya karbi tubarsa kuma ya shirya shi (122) sai yace ku fita daga cikin ta dukkan ku sashinku yana makiyi ga sahi to idan shiriya tazo muku daga gare ni to duk wanda yabi shiriya ta to bazai bata ba kuma bazai tabe ba (123) kuma duk wanda ya kauda kai daga ambato na to lallai shi yana da wata irin rayuwa ta kunci kuma zamu tada shi ranar alkiyama makaho (124) sai yace ya ubangiji dan me ka tada ni makaho alhali da na kasance ina gani (125) sai yace hakannan ayoyin mu suka zo maka sai ka manta da su to haka nan kaima yau za’a manta da kai (126) kuma haka nan muke sakawa duk wanda ya ketare iyaka kuma bai yi imani da ayoyin ubangijin sa ba kuma lallai azabar lahira tafi tsanani kuma tafi dauwama (127)” suratu Daha, aya ta: 116-127.

Bayan karni goma daga sauko da Iblis daga aljannah zuwa ban kasa saboda sabawa umarnin Allah madaukaki da yayi na kin yin sujada ga Adam kuma shima Adam aka sauko da shi daga aljannah saboda sabawa umarnin Allah da yayi na cin bishiyar da aka hana shi ci daga gare ta, sai sabani da shirka da kuma ninsanta daga manhajin Allah da ya tsara wa Adam da zuriyyar sa suka auku, wanda ke tabbatar musu da jin dadi a gidaje biyu na duniya da lahira, saboda farkon manzanni bayan Adam shi ne Nuhu amincin Allah ya tabbata a garesu wanda a cikin mutanen sa ne shirka ta fara baiyana sai aka aike shi zuwa gare su dan ya maida su zuwa manhajin Allah, Allah madaukaki yana cewa yana mai hikaito da’awar Annabi Nuhu ga mutanen sa: sai Nuhu yace ya ubangiji lallai su sun saba mini kuma sun bi wanda bazai kara musu komai ba a cikin dukiyar su da yaran su sai dai hasara (21) kuma sunyi makirci makirci mai girma (22) kuma suka ce kada ku bar ababen bautar ku kuma kada ku bar Wuddu da Suwa’a da Yagusa da Ya’uka da Nasra (23) kuma hakika sun batar da mutane da yawa kuma kada ka karawa azzalumai sai dai bata (24) saboda sabun da sukeyi ne aka nutsar da su a cikin ruwa sannan za’a sa su a cikin wuta kuma baza su samu wasu masu taimaka musu ba koma bayan Allah (25) kuma Annabi Nuhu yace ya ubangiji kada ka bar wani gida na kafiri a ban kasa (26) domin lallai kai in ka kyale su to zasu batar da bayin ka kuma baza su dinga haihuwa ba sai fajirai kafurai (27) ya ubangiji ka gafarta mini da iyayena da duk wanda ya shiga gidana yana mumini da muminai maza da mata kuma kada ka kara wa kafurai sai dai halaka (28)” suratun Nuh, aya ta: 21-28.

 

 

 

BUKATAR MUTANE GA MANZANNI DA KUMA MANZANCI

Mutane suna da bukatar manzanni da kuma karantar war su irin yadda suke da bukata ga abinci da abin sha, su suna da bukatuwar su dan su san mahaliccin su ta hanyar su kuma dan karantarwar su ta zama hanya ta gyaran rayuwar su da kuma haskaka zukatan su da kuma shiryar da kwakwalen su, kuma dan su san inda zasu dosa a cikin rayuwa ta sanadiyyar su da kuma alakar su da rayuwa da abunda ke cikin ta, ta yadda baza su kauce ba su auka cikin alfasha da zunubai kuma dan su san hakkin su da kuma abunda ya wajaba a kan su ta fuskar mahaliccin su da kawunan su da kuma mutanen da ke kewaye da su.

Ibn alkayyim yana cewa yana mai baiyyana wannan lamari: kuma daga nan ne zaka san irin matsananciyar bukatar bawa zuwa ga sanin manzannin cewa ta wuce kowace bukata, da kuma abunda yazo da shi, da gaskata shi cikin abunda ya bada labarin shi, da yi masa biyayya cikin abunda ya bada umarni, domin kuwa lallai babu wata hanya ta jin dadi da rabauta a duniya da kuma lahira sai ta hanyar manzanni, kuma babu wata hanya ta sanin kyawawa daga munana filla-filla sai ta bangaren su, kuma ba’a samun yaddar Allah ko kadan sai ta hannun su, abu mai kyau na aiyuka da zantuttuka da halaye ba komai bane face shiryarwar su da kuma abny da suka zo da shi, su ne ma’auni mai rinjaye, wanda da aiyukan su da zantuttakan su da halayen su ne ake auna halaye da aiyuka, kuma da bin su ne shiryaiyyu suke banbanta da batattu, bukata zuwa gare su tafi bukatuwar gangan jiki zuwa ga ruhin sa, da bukatauwar ido zuwa ga hasken sa, da bukatuwar ruhi zuwa ga rayuwar sa, duk wata irin bukatuwa da matsantuwa da za’a kwatanta to bukatuwar bawa zuwa ga manzanni tafi tsanani sosai, meye tunanin ka da wanda idan shiriyar sa ta kubce maka da kuma abunda ya zo da shi ko da da kiftawar ido ne zuciyar ka zata baci, kuma ta zama kamar kifi idan ya bar cikin ruwa aka jefa shi cikin kaskon suya, to halin da bawa zai samu kansa idan zuciyar sa ta rabu da abunda manzanni suka zo da shi kamar irin wannan halin ne kai yama fi haka tsanani sai dai babu mai jin hakan sai dai zuciya rayaiyya.

 

 

 

HIKIMAR ALLAH A CIKIN ZABAN MANZANNI DA ANNABAWA

Lallai manzanci da Annabci kyauta ce ta ubangiji da kuma zabi na Allah kuma tagomashi ne daga ubangiji Allah yana yin kyautar sa ga wanda yaga dama cikin bayin sa bata da alaka da dangantaka ko alfarma ko daraja, Allah masani ne mai hikima a inda yake sanya manzancin sa, inda Allah madaukaki yake cewa: ya ku mutane an buga wani misali sai ku saurare shi lallai wadanda kuke kira kuna bauta musu koma bayan Allah baza su iya halittan kuda ba koda sun tarun masa ne kuwa kuma idan kuda ya fisgi wani abu a wurin su baza su iya kwato shi daga wurin shi ba me nema da wanda ake nema duk masu rauni ne (73) basu girmama Allah ba yadda ya kamata su girmama shi ba lallai Allah mai karfi ne mabuwayi (74) Allah yana zaban manzanni daga cikin mutane da mala’iku lallai Allah mai ji ne mai gani (75)” suratul hajj, aya ta: 73-75.

Shi yasa bai kamata ba ayi wa Annabi Muhammad (S.A.W) hassada ba kamar yadda akayi wa Annabi Isah hassada kafun haka ta bangaren bani isra’ila, domin ita kamar yadda mukayi bayani ne kyauta ce daga Allah yana yin ta ga wanda ya ga dama, Allah madaukaki yana cewa: shin ko suna yi wa mutane hassada ne akan abunda Allah ya basu na falalar sa to hakika mun baiwa mutanen gidan Annabi Ibrahim littafi da hikima kuma mun basu mulki mai girma (54)” suratun Nisa’i, aya ta: 54.

Kuma manzannin Allah amincin Allah ya tabbata a gare su matsayin su da darajarsu sun banbanta su ba daidai suke ba ta wurin falala kuma hakan falala ne daga Allah yana bada shi ga wanda ya so cikin bayin sa, Allah madaukaki yana cewa: wadannan manzanni ne mun fifita sashin su akan sashe daga cikin su akwai wanda Allah yayi wa magana kuma ya daga darajar wasun su kuma mun baiwa Isa dan Maryama ayoyi baiyanannu kuma mun karfafa shi da ruhi mai tsarki inda Allah ya ga dama da wadanda suke bayan su basuyi kashe-kashe ba bayan hujjoji sun zo musu sai dai su sunyi sabani daga cikin su akwai wadanda sukayi imani kuma daga cikin su akwai wadanda suka kafurce kuma da Allah ya ga dama da basyi yake-yake ba sai dai Allah yana aikata abunda yake so ne (253)” suratul bakara, aya ta “ 253.

 

 

 

WADANDA SUKA FI DARAJA CIKIN MANZANNI

ANNABI NUHU AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI

Shi ne na farkon manzanni, Allah ya aiko shi bayan mutanen shi sunyi shirka kuma halin su ya baci, kuma suka manta da tushen shari’ar Allah wacce ya saukar wa Annabi Adam, sai suka koma bautan gumaka, kamar yadda Allah ya baiyana hakan da fadar sa: lallai mu mun aika da Nuhu zuwa ga mutanen sa cewa ka yi gargadi ga mutanen ka tun kafin wata azaba mai radadi ta zo musu (1) sai yace ya ku mutane na lallai ni mai gargadi ne a gare ku mabiyyani (2) ku bauta wa Allah kuma kuji tsoran sa kuma kuyi mun biyaiya (3) zai gafarta muku zunuban ku kuma zai muku jinkiri har zuwa wani lokaci na musamman da aka aje lallai lokacin da Allah yasa in yazo to ba’a jinkirta shi da kun kasance kuna da sani (4)” suratu Nuh, aya ta: 1-4.

Sun riki gumaka guda biyar na su, sun kasance suna nufin su da bauta kuma suna bauta musu koma bayan Allah: (Wudu – Suwa’u – Yagusu – Ya’uqu – Nasra), Allah yayi bayanin su a cikin Alkur’ani da fadar sa: “kuma suka ce kada kubar ababen bautar ku kuma kada ku sake ku bar Wuddu da Suwa’u da Yagusu da Ya’uqu da Nasra (23)” suratun Nuh, aya ta:23.

Kuma shi Annabi Nuhu amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance mai tsoran Allah ne mai gaskiya, ya kira mutanen sa da da hakuri da kuma tabbatuwa, kuma yabi hanyoyi daban daban wurin kiran mutanen sa wadanda sukayi masa isgili kuma suka karyata shi,kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: sai yace ya ubangiji lallai ni na kira mutane na dare da rana (5) amma kiran da nake musu bai kara musu komai ba sai dai guduwa (6) kuma lallai ni a duk lokacin da nake kiran su dan ka gafarta musu sai su sanya yatsun su a cikin kunnuwan su kuma su nannada tufafin su kuma su kangare kuma suyi girman kai girman kai (7) sa’annan lallai ni na kira su a baiyane (8) sannan lalli ni na baiyana musu kuma na musu a sirrance sirrantawa (9) sai nace musu ku nemi gafarar ubangijin ku domin lallai shi ya kasance mai yawan gafara ne (10)” suratu Nuh, aya ta: 5-10.

Ammma duk da haka ya ci gaba da kiran su tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi kuma duk lokacin da ya kara dagewa wajan kiran su da tunasar da su sai su kara kaimi wajen kauda kai da dogewa akan barna, sai ya cigaba da yin hakuri a kan su kuma ya ci gaba da kiran su zuwa ga addinin Allah sai a ka samu mutane kadan suka bi shi, su kuma kafurai sai suka ci gaba cikin kangarewar su sai Allah ya hana musu ruwan sama sai Annabi Nuhu ya kira su zuwa ga yin imani dan Allah ya dauke musu wannan azabar sai sukayi imani sai Allah ya dage musu wannan azabar sai dai su daga baya sun koma cikin kafurcin su, kuma yaci gaba da kiran su har tsawan shekaru dari tara da hamsin sai daga baya Annabi Nuhu ya kai koke zuwa ga ubangijin sa cewa mutanen sa sun saba masa kuma sun bi batattu daga cikin su, sai ya roki ubangijin sa kuma yace: “kuma Annabi Nuhu yace ya ubangiji kada ka bar wani gida na kafiri a ban kasa (26) domin lallai kai in ka kyale su to zasu batar da bayin ka kuma baza su dinga haihuwa ba sai fajirai kafurai (27) ya ubangiji ka gafarta mini da iyayena da duk wanda ya shiga gidana yana mumini da muminai maza da mata kuma kada ka kara wa kafurai sai dai halaka (28)” suratun Nuh, aya ta: 26-28.

Sai Allah ya karba addu’ar sa sai Allah ya umarce shi da gina jirgin ruwa- kuma dama shi kwararre ne a bangaran kafintanci- wannan farkon shiri ne na tsiratar da shi shi da wadanda suke tare da shi cikin mutanen sa daga ruwan dufana wanda zai wanke kasa daga kafurci, kuma aka ce ya dauki jinsi biyu na kowane nau’in abu, sai ruwan dufana ya zo hakan kuwa ya auku ne ta yadda Allah yayi umarni ga sama da tayi ruwa ita kuma kasa ta fitar da idanun ruwa sai Allah ya nitsar da su baki dayan su, kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: “ mutanen Nuhu sun karyata gabanin su sai suka karyata bawan mu kuma sukace mahaukaci ne kuma suka yi mai tsawa (9) sai ya roki ubangijin sa yace lallai ni an rinjaye ni to ka kawo mun agaji (10) sai muka bude kofofin sama da wani rirn ruwa mai bubbugowa mai yawa (11) kuma muka bude kasa da idanu ruwa sai ruwan ya hadu akan wani lamari wanda an riga an kaddara shi (12) kuma muka dauke shi akan jirgin ruwa ma’abociya katakai da kusoshi (13) tana gudana kan kulawar mu wannan sakamako ne ga wanda suka kasance sun kafurce (14) kuma hakika mun barta aya ce shin ko akwai mai tunani (15)” suratul Kamar, aya ta: 9-15.

Kuma Annabi anuhu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance daga gare shi ne da yaran sa guda uku wadanda suke tare da shi sauran mutane suka yadu, su ne: Saam (baban larabawa da farisawa da rumawa), Haam: (baban bakake da ifranjawa da kibtawa da indiyawa da sindawa), Yafis: (baban turkawa da chinisawa da sakalibawa da ya’juju da ma’juju).

ANNABI IBRAHIM AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Maji dadin Allah baban Annabawa an haifa masa Isma’il da Ishaq bayan ya tsofa amincin Allah ya tabbata a gare su, su ne wadanda aka samu mafi yawancin Annabawa daga cikin zurriyar su, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani Isma’il da Ishaq bayan na manyanta lallai ubangiji na mai karbar addu’a ne (39) ya ubangiji ka sanya ni mai tsaida sallah da kuma zurriya ta ya ubangiji ka karbi addu’a ta (40)” suratu Ibrahim, aya ta: 39-40.

Allah ya zabe shi da manzancin sa kuma ya fifita shi akan da yawa daga cikin halittun sa, kuma Annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance yana rayuwa a tsakanin wasu mutane da ke shirka da Allah kuma suke bauta wa taurari, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ kuma lokacin da Ibrahim yace wa mahaifin sa Azara shin yanzu zaka riki gumaka a matsin ababen bauta lallai ni ina ganin ka da mutanen ka kuna cikin wata irin bata baiyananna (74) kuma haka nan muka nuna wa Ibrahim mulkin sammai da kasa dan ya zama cikin masu yakini da tabbaci (75) lokacin da dare ya shigo masa sai yaga wani tauraro sai yace wannan shi ne ubangiji na lokacin da ya gushe sai yace ni bana san masu gushewa (76) lokacin da yaga wata ya fito a fili sai yace wannan shi ne ubangiji na lokacin da ya gushe sai yace in dai har ubangiji na bai shiryar da ni ba to lallai ni zan kasance cikin mutane batattu (77) lokacin da yaga rana ta fita a fili sai yace wannan shi ne ubangiji na dan wannan yafi girma lokacin da ta fadi sa yace ya ku mutane na lallai ni na barranta dag abunda kuke shirka da shi (78) lallai ni na fuskantar da fuska ta ga wanda ya kagi halittar sammai da kasa ina mai karkata zuwa gare shi kuma ni bana cikin masu shirka (79)” suratul An’am, aya ta: 74-79.

Hakan bai burge shi kuma da fiirar shi yaji a jikin sa cewa akwai abun bauta da yafi wadannan halittun girma wadan da basa cutarwa ko amfanarwa, har Allah ya shiryar da shi zuwa ga sanin sa kuma ya zabe shi da manzancin sa, kuma shi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance yana yawan jayaiyya da mutanen sa musamman ma da dalilai na hankali wadanda basa barin wani wuri na kokwanto wajen bata abun da suke kudurcewa da kuma abunda suke bautawa komabayan Allah, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “ kuma ka karanta musu labarin annabi Ibrahim (69) lokacin da yace wa mahaifin sa da mutanen sa me kuke bauta ma (70) sai sukace muna bauta wa wasu gumaka ne sai mu doge muna masu gurfana a gare su (71) sai yace shin suna jin ku in kuna kiran su (72) kuma suna amfanar da ku ne ko cutarwa (73) sai suka ce a’a mu mun samu iyayen mu ne haka suke aikatawa (74) sai yace kun ga ababen nan da kuke bautawa (75) ku da iyayen ku na da (76) to lallai su makiya ne a gare ni sai dai ubangijin talikai (77) wanda ya halicce ni to shi ne zai shiryar da ni (78) kuma wand yake ciyar da ni da shayar da ni (79) kuma in nayi rashin lafiya to shi ne yake warkar da ni (80) kuma shi ne wanda yake kashe ni sannan ya rayar dani (81) kuma shi ne wanda nake kwadayin ya gafarta mun zunubai na ranar sakamako (82) ya ubangiji ka bani wani hukunci kuma ka riskar da ni da salihai (83) kuma ka sanya mun harshe na gaskiya a cikin masu zuwa (84)” suratush Shu’ara’i, aya ta: 69-84.

Ya ci gaba da kirn mutanen sa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi zuwa ga kadaita Allah da bauta masa da kuma jifa da dukkan abunda suke bautawa koma bayan Allah sai dai su sun karyata shi kuma suka musa manzancin sa kuma sukayi yunkirin kona shi da wuta sai Allah ya tsiratar da shi daga gare su, kamar yadda Allah ya bada labarin sa da fadar sa: kuma hakika mun baiwa Ibrahim shiriyar sa tun gabanin haka kuma mu game da shi masana ne (51) lokacin da yace wa mahaifinsa da mutanen sa wadannan wasu irin gumaka ne da kuke bautama wa (52) sai sukace mun samu iyayen mu ne muma suna bauta musu (53) sai yace hakika ku da iyayen ku kun kasance cikin bata baiyananna (54) sai suka e shin kazo mana da gaskiya ne ko kuwa kai kana cikin masu wasa ne (55) sai yace ai ubangijin ku shi ne ubangijin sammai da kasa wanda ya halicce su kuma ni mai shaida ne akan haka (56) kuma wallahi sai na rusa gumakan ku bayan kun juya baya kun tafi (57) sai ya sanya su a farfashe sai dai babban su dan wata kila zasu komo zuwa gare shi (58) sai sukace waye ya aikata haka ga allolin mu lalli shi yana cikin azzalumai (59) sai sukace munji wani saurayi yana ambaton su da batanci ana kiran shi Ibrahim (60) sai sukace to kuzo da shi a gaban idan mutane ko zasu bada shaida (61) sai sukace shin kai ne ka aikata haka ga allolin mu ya kai Ibrahim (62) sai yace a’a wannan babban na cikin su ne ya aikatato ku tambaye su mana in suna magana (63) sai suka koma zuwa ga kawonan su sai sukace lallai kune azzalumai (64) sa’annan sai suka sunkuyar da kawunan su suka ce hakika ka san cewa wadancan basa magana (65) sai yace to yanzu zaku dinga bautawa wani abu koma bayan Allah wanda bazai amfane ku da komai ba ko kuma ya cutar da ku (66) tur da ku da kuma abunda kuke bautawa koma bayan Allah shin baza ku hankalta ba (67) sai sukace ku kona shi kuma ku taimaki allolin ku in har zaku aikata (68) sai mukace yake wuta ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahim (69) kuma sunyi nufin makirci a gare shi sai muka sanya su sune masu hasara tababbu (70)” suratul Anbiya’i, aya ta: 51-70.

Bayan mutanen shi sun karyata shi sai Allah ya umarci shi da barin garin shi da matar shi Hajara da yaran sa Isma’il zuwa makkah a inda Allah ya nuna wa Annabi Ibrahim wurin da dakin ka’abah yake sai ya ginashi kuma yaran sa Ismail ya taimake shi wanda ta tsatson shi ne na karshen Annabawa ya fito wato Annabi Muhammad (S.A.W) wanda aka aiko shi zuwa ga mutane baki daya har zuwa ranar alkiyama, dan wannan gidan ya zama alkiblar musulmai dukkan su a gabas da yamma, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: kuma lokacin da Ibrahim yace ya ubangiji ka sanya wannan gari ya zama amintacce kuma ka azurta mutanen cikin sa da kayan marmari wanda sukayi imani daga cikin su da Allah da rana ta karshi sai yace kuma duk wanda ya kafurce to zan jiyar da shi ddi dan kadan sannan zan jefa shi cikin azabar wuta kuma makoma tayi muni (126) kuma lokacin da Ibrahim yake daga tushe na ginin ka’abah da kuma Isma’il sai suka ce ya ubangiji ka amsa mana lallai kai mai ji ne masani (127) ya ubangiji kuma ka sanya mu mu zama masu mika wuya a gare ka da kuma zurriyyar mu su zama al’umma masu mika wuya a gare ka kuma ka nuna mana wuraraen bautan mu kuma ka yafe mana lallai kai mai yawan karbar tuba ne mai jin kai (128) ya ubangijin mu kuma ka aika da wani manzo daga cikin su zuwa gare su wanda zai dinga karanta musu ayoyin ka kuma ya sanar da su littafi da hikima kuma ya tsarkake su lallai kai mabuwayi ne mai hikima (129) kuma babu mai kauda kai daga tafarkin Ibrahim sai dai fa wanda ya wawantar da kansa kuma hakika mun zabe shi a nan duniya kuma lallai shi a lahira yana cikin salihai (130) lokacin da ubangijin sa yace masa ka mika wuya sai yace na mika wuya ga ubangijin talikai (131) kuma sai Ibrahim yayi wasiyya da ita ga yaran sa da Yaqub cewa ya ku yarana lallai Allah ya zabar muku addini kada ku sake ku mutu sai dai kuna musulmai masu mika wuya (132)” suratul bakara, aya ta: 126-132.

 

 

 

 

 

ANNABI MUSA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Shi ne wanda yayi magana da Allah, Allah ya mai magana ba tare da wani shamaki ba, kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: lokacin da Musa yazo mikatin mu kuma ubangijin sa yayi masa magana sai yace ya ubangiji ka nuna mun kai in ganka sai yace baza ka iya gani na ba sai dai kayi dubi zuwa ga wancan dutsen idan har ya tabbata a inda yake to da sannu zaka ganni lokacin da ubangijin sa yayi tajalli zuwa ga dutsen sai ya mai da shi a farfashe a warwatse sai Musa ya fadi yana sumamme lokacin da ya farfado sai yace tsarki ya tabbata a gare ka na tuba a gareka kuma ni ne farkon muminai (143)” suratul A’raf, aya ta: 143.

Kuma shi ne wanda aka fi ambato cikin manzanni bani isra’ila a cikin Alkur’ani mai girma, an ambace shi a wurare dari daashirin da tara wannan yana nuni akan matsayin wannan Annabin da darajar sa mai girma, Allah ya karfafa shi da mu’jizozi guda biyu, ta farkon su itace sanda wacce ta koma kamar katon macijiya, amma dayar mu’jizar ita ce hannun sa wanda yake shigar da shi cikin hammatan sa sai ya fito da shi ya koma fari ba tare da mis ba, wannan na nuni akan gaskiyar mazancin sa ga firauna da mutanen sa dan ko watakila su zama dalili na gaskatawar su da imanin su ga Allah kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: kuma Musa yace ya kai fir’auna lallai ni manzo ne daga ubangijin talikai (104) da gaskene bazan fadi komai bai game da Allah sai dai gaskiya hakika nazo muku da hujjoji daga ubangijin ku to ka saki mutanen bani isra’ila su tafi tare da ni (105) sai yace in har kazo da hujjoji to ka kawo su mu gani in har kai ka kasance cikin masu gaskiya (106) sai ya wurga sandar shi sai gashi ta zama katon kumurcin maciji a baiyane (107) kuma sai ya fito da hannun sasai ga shi yana haske fari tas ga masu kallo (108)” suratul A’araf, aya ta: 104-108.

Allah ya aike shi zuwa wurin fir’auna da mutanen sa dan ya kirasu zuwa ga bautar Allah shi kadai da watsar da dukkan wani abu koma bayan sa bayan sun karkace daga addinin gaskiya kuma sukayi girmankai da dagawa da kuma zalunci, ta yadda fir’auna ya dunga kiran mutanen sa da su bauta masa kuma yana umurtar su da yin bauta a gare shi irin wadda basa yi wa Allah madaukaki, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: kuma sai fir’auna yace ya ku mutanen gari ban san wani abun bauta a gare ku ba sai ni to ya kai Hamana ka dauke ni akan tabo sai ka gina mun babban gidan sama dan wata kila ko na leko Allahn Musa kuma lallai ni ina zatan shi yana cikin makaryata (38)” suratul Kasas, aya ta: 38.

Sai Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kira shi ta hanyar hikima da sassaukan zance zuwa ga kadaita Allah da bautar Allah shi kadai, sai Fir’auna ya yake shi kuma ya tara mai bokaye dan su mai makirci, sai dai Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi ya yi rinjaye a kansu da ikon Allah, bayan ya jefa sandar sa wacce ta hadiye sandunan bokayen da igiyoyin su wadanda aka juyar da su suka koma suna tafiya saboda tsafi suka zama kamar macizai kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: sai iyan lagwada daga cikin mutanen fir’auna sukace lallai wannan mai sirhiri ne masani (109) yana so ne ya fitar da ku daga kasarku to meye kuke umarni da shi (110) sai suka ce a kore shi da dan uwan shi kuma ku tura gari gari dan tattaro mutane (111) dan a zo maka da kowane mai sihiri masani (112) sai masu sihirin fir’auna suka zo sai suka ce lallai mu munada wata lada ne in mun kasance mu ne masu galaba (113) sai yace eh kuma lallai ku zaku zama cikin makusanta (114) sai suka ce ya Musa ko dai ka fara jefawa ko kuma mu ne zamu fara jefawa (115) sai yace ku jefa lokacin da suka jefa sai suka sihirce idanun mutane kuma suka firgitar da su kuma sun zo da sihiri mai girma (116) sai mukayi wahayi zuwa ga Musa cewa ka jefa sandar ka sai gashi tana hadiye abunda suke jefawa (117) sai gaskiya ta baiyyana kuma abunda suka kasance suna aikatawa ya blalace ya baci (118) kuma sai aka rinjaye su a wannan wurin sai suka komo suna kaskantattu (119) sai masu sihiri suka fadi suna masu sujada (120)” suratul A’araf, aya ta: 109-120.

Fir’auna da mutanen sa sun karyata Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi sai Allah ya daura musu ukubobi iri-iri saboda karayatawar da sukayi da kuma barna da suke yi aban kasa, sai Allah ya aiko musu da ruwan dufana da fari da kwarkwata da kwadi da jini, ayo yi filla-filla sai sukayi girman kai kuma suka zama kafurai, sai daga baya Allah ya dage su daga gare su saboda addu’ar Annabi Musa bayan sun nemi da yayi addu’a ya roki ubangijin sa dan ya yaye su daga gare su wta kila zasu gaskata kuma suyi imani, sai dai hakan bai kara musu komai ba sai dai kangare wa da kafurci da girman kai, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da gadar sa:kuma sukace duk abunda zaka zo mana da shi na ayoyi dan ka sihirce mu da su to mu baza muyi imani da kai ba (132)sai muka aika musu da dufaan da fari da kwarkwata da kwadi da jini ayoyi ne a rarrabe sai sukayi girman kai kuma sun kasance mutane mujirimai (133) lokacin da girgije ya fado a kan su sai suka ce ya Musa ka roka mana ubangijin ka da abunda ya saba maka da shi dan idan ka dauke mana wannan girgijen to wallahi lallai zamuyi imani da kai kuma lallai zamu saki bani isra’ila tare da kai (134) lokacin da muka yaye musu girgijen zuwa wani lokaci wanda su zasu kai shi sai gashi suna warware alkawari (135)” suratul A’araf, aya ta:132-135.

Bayan wanna sabawar da taurin kai da kafurci baiyananne daga Fir’auna da mutanen sa sai Allah ya umarci Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi da fita shi da mutanen sa cikin dare sai ya fita daga masar shi da muminai cikin mutanen sa daga cikin mutanen bani isra’ila dan su gudu da addinin su, si Fir’auna da rundunar sa suka bi shi saboda kiyaiyya da zalunci, lokacin da jama’ar biyu suka hango juna kuma ga teku a gaban su kuma fir’auna da rundunar shi suna bayan su, sai mutanen Annabi Musa suka ce:” lallai mu an kama mu” sai Annabi Musa fada yana mai tabbaci da ubangijin sa cewa zai kubutar da su da kuma irin alkawarin da yayi masa na samun nasara akan abokan gaban sa:” a’a” sai Allah yayi masa wahayi cewa ya bigi tekun da sandar sasai ya tsage biyu sai ya zama kamar dutse mai girma dan Allah ya tsiratar da Annabi Musa da wadan da suke tare da shi kuma ya nutsar da Fir’auna da rundunar sa, kamar yadda Allah ya baiyyana haka d fadar sa: lokacin da jama’r biyu suka ga juna sai mutanen Annabi Musa suka ce lallai mu za’a riske mu (61) sai yace a’a lallai ni akwai ubangiji na a tare da ni zai shiryar da ni (62) sai mukayi wahayi zuwa ga musa cewa ka bigi tekun da sandar ka sai tekun ya rabe sai kowane bangare ya zama kamar dutse mai girma (63) kumai sai muka kusanto da wadancan jama’ar na daban (64) kuma sai muka kubutar da Musa da wadanda suke tare da shi baki daya (65) sa’annan sai muka nutsarda wadancan da suka rage (66)” suratush Shu’ara’i, aya ta: 61-66.

Allah ya karfafa Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi da wannan mu’ujizar wacce Fir’auna da mutanen sa basu taba tsammanin ta ba, sai dai al’amarin Allah mai zartuwa ne kuma abunda yayi nufi mai kasantuwa ne dan ya zama a cikin haka akwai kubutar Annabi Musa da wadanda suke tare da shi cikin muminai kuma dan ya zama a cikin ta akwai halakar fir’auna da mabiyan sa dan ya zama aya ga wadanda suke bayan sa da kuma abun izina, ta yadda tekun ya jeho shi waje bayan ya halaka, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: kuma muka ketarar da bani isra’ila teku sai fir’auna da rundunar sa suka bisu dan mugunta da kiyaiyya har zuwa lokacin da nutsewa ta riske shi sai yace nayi imani cewa lallai babu abun bauta sai wannan wanda bani isra’ila sukayi imani da shi kuma nima ina cikin musulmai masu mika wuya (90) shin a yanzu kuma alhali a baya ka bijire kuma ka sance cikin masu barna (91) a yau zamu tsiratar da kai da gangan jikin ka dan ka zama aya ga wadanda zasu zo a bayan ka kuma lallai da yawa daga cikin mutane gafalallu ne game da ayoyin mu (92)” suratu Yunus, aya ta: 90-92.

 

 

ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Shine shugaban mu Isah dan Maryam Annabi na karshe na bani isra’ila, Allah ya aiko shi bayan Annabi Musaamincin Allah ya tabbata a gare shi zuwa ga mutanen bani isra’ila lokacin da suka baci kuma suka kauce daga ingantacciyar hanya, kamar yadda Allah yabaiyana haka da fadar sa: kuma sai muka zo da Isah dan Maryama a bayan su yana mai gaskata abunda ya gabace shi na attaura kuma mun bashi injila a cikinta a kwai shiriya da haske kuma yana gaskata abunda ya gabace shi na attaura kuma shiriya ne da kuma tunatarwa ga masu tsoran Allah (46)” suratul Ma’ida, aya ta: 46.

An haife shi ba tare da uba ba saboda wata hikima da Allah yake nufi, hakika ya so ne ya baiyana wa halittunsa ikon sa ga ga halittar sa, ta yadda ya halicci Adam ba uwa ba uba, kuma ya halicci Hauwa’u daga namiji ba mace, sai kuma ya halicci Isah ba namiji, saboda haka ne Allah ya fada a cikin suratu maryam: kuma dan sanya shi ya zama aya ne ga mutane “ suratu Maryam, aya ta:21.

Misalin halittar sa kamar misalin halittar Adam ne Allah ya halcce shi daga turbaya sannan sai ya ce masa “ kasance” sai ya kasance, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa:” lallai misalin Isah a wurin Allah kamar misalin Adam ne Allah ya halicce shi daga turbaya sa’annan sai yace masa kasance sai ya kasance (59)” suratu Ali imaran, aya ta: 59.

An aike shi zuwa ga bani isra’ila sai sukakaryata shi kuma suka yake shi kuma suka cutar da shi, sai yayi hakuri kuma yaci gaba da isar da sakon manzancin sa, kuma saboda yasan cewa ba shi ne na karshen manzannin Allah ba sai yayi bushara da wani manzo da zai zo a bayan sa sunan sa Ahmad[2] (S.A.W), Allah ya sanar da shi littafi da hikima da attaura da injila kuma ya karfafa shi da mala’ika Jibrilu kuma ya kasance mai daraja a nan duniya da kuma lahira kuma ya kasance cikin makusanta, Allah ya bashi wasu mu’ujizozi wadanda suka ruda mtanen lokacin sa, hakika shi yayi wa mutane magana alhali yana cikin tsumman goyo, kuma ya kasanceyana hada tsuntsu na tabo sai yayi busa a ci sai ya tashi sama ya zama tsuntsu da izinin Allah, kuma yana warkar da mai kyasfi da kuturu kuma yana raya matattu dukkkan wannan na faruwa ne da izinin Allah, kuma yana baiwa mutane labarin abunda suka ci da abun da suka taskace, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: lokacin da mala’iku suka ce ya ke Maryam lallai Allah yana miki bushara da wata kalma daga gare shi sunan sa almasihu Isah dan Maryama mai daraja ne a duniya da lahira kuma yana cikin makusanta (45) kuma yana magana da mutane a cikin tsumman goyo da kuma bayan ya manyanta kuma yana cikin salihai (46) sai tace ya ubangiji ta yaya zan samu yaro kuma alhali babu wani mutum da ya taba taba ni sai yace haka nan Allah yake halitta abunda yaga dama idan ya kaddara wani lamari to kawai yana ce masa ne kasance sai ya kasance (47) kuma zai sanar da shi littafi da hikima da Attaura da Injila (48) kuma manzo ne zuwa ga bani isra’ila cewa lallai ni nazo muku da hujjoji daga ubangijin ku lallai ni ina halitta muku daga daga tabo wani abu mai kama da tsutsu sai in yi busa a cikin sa sai ya zama tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da mai kyasfi da kuturu kuma ina raya matattu da izinin Allah kuma ina baku labarin abunda kuka ci da abunda kuke taskacewa a cikin gidajen ku lallai a cikin haka akwai ayoyi a gare ku in kun kasance muminai (49)” suratu Ali imran, aya ta: 45-49.

Da’awarsa ta kasance irin da’awar sauran iyan uwansa manzanni kafin sa, sai ya kira mutanen sa zuwa ga bautar Allah madaukaki, sai dai shi ya hadu da abun da ya hadu dashi daga gare su na karyatawa da girmankai, kuma ba wanda yayi imani da shi sai dai masu rauni cikin mutanen sa, yahudawa sun yi yunkurin halaka shi da da’awar sa sai Allah ya tsiratar da shi daga gare su ta yadda ya dauke shi zuwa sama, sai yahudawa suka kashe mutumin da Allah ya sanya mai kama irin ta Annabi Isah, sai yahudawa da wadanda suka rako su cikin kiristawa sukayi zatan cewa an kashe shi, kuma shi zai sauko a karshen zamani zuwa kasa kma zaiyi hukunci da shari’ar Annabi Muhammad (S.A.W) daga baya sai Allah ya dau ran sa dan tabbatar da fadar Allah madaukaki:” dukkan wanda ke kanta mai karewa ne (26) kuma fuskar ubangijin ka ce zata rage ta wanzo ma’abocin girma da karamci (27)” suratur Rahman, aya ta: 26-27.

 

 

 

ANNABI MUHAMMAD AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Manzan Allah Muhammad (S.A.W) Annabin da bai san karatu ba ko rubutu balarabe daga tstson Annabi Isma’ila dan Ibrahima baban Annabawa, shi ne karshen manzanni kuma mafificin su baki daya, an aiko shi zuwa ga mutane baki daya, an haife shi a makkah bayan rasuwar mahaifin shi da watanni kadan, sannan sai daga baya mahaifiyar shi ta rasu alhali yana jariri, sai kakan sa Abdul mutallib ya raine shi, sai dan uwan baban sa Abu dalib, kuma yayi kiwon dabbobi na wani lokaci ga mutanen makkah, Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki daya ba wai larabawa ba kawai, ya aiko shi dan jin dadin mutane baki daya kuma dan ya baiyana musu hanyar gaskiya da alheri kuma ya tsawatar da su daga hanyar barna da sharri, rayuwar sa dukkanta ta kasance gaskiya ce da amana, ba’a sanshi da yaudara da karya ba, ko cin amana da zamba,an sanshi tsakanin mutane da amintacce sun kasance suna aje amanaonin su a wurin sa, kuma suna aje kayan su a wurin sa in zasuyi tafiya, kuma sun sanshi da gaskiya, saboda irin abunda aka san shi da shi na gaskiya cikin abunda yake fada da kuma bada labarin sa, wahayi ya sauka a gare shi yana da shekaru arba’in, ya zauna a garin makkah shekaru goma sha uku yana kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da kuma barin bautar gumaka sannan sai yayi hijira zuwa madinah mai haske ku a ya kira mutanen ta zuwa musulunci sai suka musulunta sai Allah ya saukar masa da sauran aiyuka na shari’o’in addini, kuma ya ci makkah da yaki bayan shekaru takwas da yin hijiran sa kuma ya rasu shekariun sa sittin da uku bayan an saukar masa da Alkur’ani cikakke kuma shari’a ta cika dukkan ta kuma larabawa suka shiga cikin musulunci kuma mabiyan sa suka fara yada musuluni a bayan sa a cikin lunguna na doran kasa wacce aka raya kai har zuwa wannan ranar tamu mutane suna shiga cikin wannan addinin mai girma dan yarda da sukayi da shi da kansu cew hi ne addini na gaskiya wnnan kuwa bayan sun san hanyoyin ushen sa ingantattu.

 

 

 

IYALEN IMRAN IYALAI NA GARI

Aiko da manzanni da kuma annabawa ya ci gaba har zuwa wani lokaci mai tsawo bayan Annabi Nuhu amincin Allah ya tabbata a gare shi har zuwa Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda da shi ne aka cike Ammabawan bani isra’ila dan al’amarin manzanci da annabci ya koma ga Annabi Muhammad (S.A.W) dan ya zama na karshen Annabawa baki daya, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: Muhammadu bai zamo mahaifin daya daga cikin mazajen ku ba sai dai shi manzan Allah ne kuma cikamakin Annabawa kuma Allah ya kasance masani ne ga dukkan komai (40)” suratul Ahzab, aya ta: 40.

Lallai Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi yana da wta irin daraja ta musamman a cikin zukatan musulmai saboda shi zamanin sa yafi kusa da su kuma yana cikin wadanda sukayi bushara a fili da zuwan Annabin su Muhammad (S.A.W), kuma hakika mamakin kiristoci zai karu in suka san cewa sunan Annabi Isah ya maimaitu a cikin Alkur’ani har sau ashirin da biyar a lokacin da shi kuma Annabi Muhammad (S.A.W) manzan musulunci wanda shi ne aka saukar wa Alkur’ani cewa ba/a ambaci sunan ba sai sau biyar kawai!! Wannan yana cikin ababen da ke nuni karara akan cewa lallai Annabi Muhammad (S.A.W) shi Annabi ne da aka aiko kuma lallai abun da ake saukar masa da shi wahayi ne ake yi masa ba daga zancen shi bane, da ace kur’ani maganar shi ne to da sunan shi zai fi maimaituwa fiye da kowane mutum na daban.

Saboda matsayin wannan Annabi mai girma wato Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi alkur’ani ya kunshi ayoyi masu yawa wadanda sukayi magana game da shi da kuma dangin sa na gari masu albarka.

Haka nan ma Maryam mai tasrki mahaifiyar Annabin Allah Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi da danginta suna da matsayi na musamman a cikin zukatan musulmai, hakika Alkur’ani yayi yabo a gare ta kuma ya siffanta mahaifiyarta da cewa ita mai bauta ce mai tsarki wadda take da tushe mai albarka da kuma matsira mai kyau da kuma dangi na gari, kuma ya daure sunan dangi ta –iyalan Imran- iyalai masu karamci da kuma zurriyya masu albarka tsatsaon Annabawa da manzanni wadda Annabi Isah yake dangantuwa zuwa gare ta da sura ta uku a cikin Alkur’ani ita ce suratu Ali imaran, dan girmamawa da kuma karramawa a gare su kuma dan wannan iyalan su zama sunan zaune cikin kwakwalen musulmai suna mau karamci da daraja a wurin su, Allah madaukakai yace: lallai Allah ya zabi Adam da Nuhu da iyalan Ibrahim da iyalan Imrana ya fifita su akan talikai (33) zurriyya ne sashin su daga sashi kuma Allah mai ji ne masani (34)” suratu Ali imaran, aya ta: 33-34.

 

 

 

MARYAM AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE TA

Alkur’ani mi girma yayi yabo ga Maryam iyar Imran mahaifiyar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi, mai gaskiya mai daraja mai tsarke wacce ta taso a gidan kamewa da tsarki, a cikin wurare da dama a Alkur’ani an siffanta ta da salihanci da tsarki da kuma tsoran Allah, Allah madaukaki yace: da kuma Maryam yarinyar Imrana wacce ta tsare farkinta sai muka yi busa a cikin sa daga ruhin mu kuma ta gaskata da kalmomin ubangijin ta da littattafan sa kuma ta kasance cikin masu kankantar da kai (12)” suratut Tahrim, aya ta: 12.

Kuma Alkur’ani ya baiyana cewa lallai Maryam amincin Allah ya tabbata a gare ta ta samu ne ta sanadiyyar addu’a mai albarka da ta fito daga uwa mai albarka, Allah madaukaki yana cewa: lokacin da matar Imrana tace ya ubangiji lallai ni nayi alwashi a gare ka na abunda ke ciki na cewa zaiyi bauta ne a gre ka to ka amsa daga gare ni lalli kai mai ji ne masani (35)” suratu Ali imran, aya ta: 35.

Kuma lallai wannan addu’ar mai albarka itace ta zama sababi na tsare ta da yaranta Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi kar shaidan ya samu galaba a kan su, ta yadda ubangijin ta ya amshe ta kuma ya karfafa ta da wasu karamomi wadanda suke nuni akan kyawon inda ta taso, ta yadda arzikinta ke zuwa mata alhali tana zaune awurin ta kuma abunda ke zuwa mata na arziki yana zuwa ne a lokacin da ba nashi ba na kayan marmari da sauran su, kuma lura da ita ya zama karkashin Annabi Zakariyya amincin Allah ya tabbat a gare shi mutumin kirki dan ya kula da ita da kuma damuwa da lamuran ta kamar yadda Allah ya baiyyana haka a cikin Alkur’ani da fadar sa: lokacin da ta haife ta sai tace ya ubangiji lallai ni haifeta mace kuma Allah yafi ni sanin abunda na haifa kuma amma mace ba kamar namiji ba kuma lallai ni na sa mata suna Maryama kuma lallai ni ina nema mata tsarin ka da zuriyyarta daga shaidan jifaffe (36) sai ubangijin ta ya karbe ta karba mai kyau kuma ya raya ta rayuwa mai kyau kuma Annabi Zakariyya ya jibinci lamuran ta lokacinda Zakariyya ya shiga wurin ta a wurin bauta sai ya samu arziki a wajen ta sai yace ya Maryam a ina kika samu wannan sai tace shi daga wurin Allah yake lallai Allah yana azurta wanda yaga dama ba tare da lissafi ba (37)” suratu Ali imaran, aya ta: 36-37.

Ita ta kasance cikin masu bauta tsira da amincin Allah ya tabbata a gare ta cikin wadanda babu kamar su a wajen bauta a lokan su, Allah yayi mata baiwa da zabinta da yayi a cikin matan lokacin ta, sai mala’iku sukayi mata bushara da hakan, kamar yadda Allah ya bada lagarin haka a cikin Alkur’ani da fadar sa: kuma lokacin da mala’iku suka ce ya ke maryam lallai Allah ya zabe ki kuma ya tsarkake ki kuma ya zabe ki ya fifita ki akan matan talikai (42) ya ke Maryam ki kankan da kai ga ubangijin ki kuma kiyi sujada kuma kiyi ruku’i tare da masu ruku’i (43)” suratu Ali imaran, aya ta: 42-43.

Kuma ma kari akan karamcin ta da bayanin falalar ta amincin Allah ya tabbata a gare ta ya karu ta yadda Allah ya saukar da sura kacukan da sunan ta (suratu Maryam) kuma itace sura ta goma sha tara a cikin Alkur’ani, kuma it ce sura daya tilo wacce take dauke da sunan mace a cikin Alkur’ani, kuma a cikin wannan surar akwai yabo da girmamawa ga Maryam wanda babu irin shi a cikin littattafan kiritoci ko bible- bible din su, duk da cewa babu wata sura ko daya a cikin Alkur’ani mai dauke da sunan daya daga cikin matan Annabi (S.A.W), kamar Khadijah ko Aisha ko kuma yaran sa mata kamar Fadima ko kuma iyan uwan sa Allah ya kara yadda a gre su, haka nan kuma babu sura mai dauke da sunan dangin sa, sai dai ma an samu sura ne mai dauke da alkawari na narkon azaba ga daya daga cikin dangin sa shi ne baffan sa Abu Lahab wanda Alkur’ani yayi hukunci cewa shi dan wuta ne, kuma wannan babu kokwanto a cikin sa wanda haka ke nuni akan gaskiyar manzancin sa, saboda da ace daga abunda ya rubuta ne da kansa kamar yadda suke cewa da sun samu kwarzanta kansa a cikin sa da kuma iyalan sa.

Kuma hakika Manzan musulunci Muhammad (S.A.W) yayi yabo akan Maryama amincin Allah ya tabbata a gare ta kuma ya lissafa ta cikin mafiya alherin matan duniya, a inda yace: mafi alherin matan duniya su ne: Maryam iyar Imran da Khadija iyar Khuwailid, da fatima iyar Muhammad (S.A.W) , da Asiya matar Fir’auna” sahihu ibn hibban.

Kuma Manzan musulunci Muhammad (S.A.W) yayi mata shaida da cewa tana cikin mafiya falalan matan aljannah, sai yace: “ mafiya falalan matan aljannah: Khadijah iyar Khuwailid, da Fatima iyar Muhammad, da Maryam iyar Imran, da Aiya iyar muzahim matar Fir’auna”. Sahihu ibn hibban.

 

 

BABI NA BIYU

RAYUWAR ANNABIN ALLAH ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Alkur’ani mai girma yayi yabo ga Annabi Isah dan Maryam amincin Allah ya tabbata a gare shi kuma ya siffanta shi da wasu irin siffofi da suke nuni akan daukakar darajarsa a wurin Allah madukaki, ta yadda ya sanya shi ya zama bushara ne ga mahaifiyar sa Maryam amincin Allah ya tabbat aa gare ta, ta yadda zai bata kayutan yaro zai halicce shi wata irin halitta da ta sabawa hanyar halittan sauran mutane, zai halicce shi da kudurarr shi da kuma ikon shi da kalmar “kun” kuma zai zama mai daraja a duniya da lahira kuma yana cikin makusanta kuma Annabi mai karamci mai tsarki wanda za’a karrama shi kum a karfafe shi da wau irin mu’ujizozi, kuma manzo ne zuwa ga bani isra’ila, kamar yadda Allah madaukaki ya ce: kuma yana magana da mutane a cikin tsumman goyo da kuma bayan ya manyanta kuma yana cikin salihai (46) sai tace ya ubangiji ta yaya zan samu yaro kuma alhali babu wani mutum da ya taba taba ni sai yace haka nan Allah yake halitta abunda yaga dama idan ya kaddara wani lamari to kawai yana ce masa ne kasance sai ya kasance (47) kuma zai sanar da shi littafi da hikima da Attaura da Injila(48)” suratu Ali imran, aya ta: 45-48.

 

 

 

HAIHUWAR SA

Allah yayi bayani a cikin Alkur’ani mai girma hakikanin Annabi Isah dan Maryam amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma irin abunda Allah madaukaki ya kebance shi da shi na mu’ujizozi, sai ya baiyyana yadda aka haife shi bayani mai warkarwa isasshe lafiyaiyyen hankali na karbar sa da kuma ingantaccen mandiki, ta yadda ya ajiye shi a inda ya dace da shi a matsayin sa na Annabi sai ya sanya shi mutum bawa ga Allah wanda aka tsarkake daga alfasha da kuma abunda yahudawa suka jefe shi da shi cewa wai shi dan zina ne- Allah ya tsare shi daga hakan- da kuma irin abunda wasu suka jefe shi da shi na cewa shi dan Allah ne ko kuma shi Allah ne- Allah ya daukaka daga haka daukaka mai girma-, Alkur’ani baya ganin cewa haihuwar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi ba da uba ba abu ne da zai sa a bauta masa ko kuma ya maida shi dan Allah- - Allah ya daukaka daga haka daukaka mai girma- a’a ai a cikin haka akwai dalili da ke nuni akan cikan ikon Allah akan nau’o’in halitta, domin Allah ya halicci Adam ba tare da namiji da macce ba, kuma ya halicci Hauwa’u daga namiji ba macce, kuma ya halicci Annabi Isah daga macce ba namiji, kuma sai ya halicci sauran halittu daga namiji da macce, Allah madaukaki yana cewa: “ lallai misalin Isah a wurin Allah kamar misalin Adam ne ya halicce shi daga turbaya sannan sai yace masa kasance sai ya kasance (59) gaskiya ce daga ubangijin ka kada ka kasance cikin masu jayaiyya (60) duk wanda yayi jayaiyya da kai game da shi bayan abunda yazo maka na ilimi to kace ku taho mu kira yaran mu da yaran ku da matan mu da matan ku da mu kan mu da ku kan ku sannan sai muyi mubahala sai mu sanya tsinuwar Allah ta tabbbata akan makaryata (61) lallai wannnan shi ne labarin gaskiya kuma babu wani abun bauta da gaskiya sai dai Allah kuma lalllai Allah shi ne mabuwayi mai hikima (62) kuma idan suka juya baya to lallai Allah masani ne ga mabarnata (63) kace yaku ma’abota littafi ku taho zuwa ga wata kalma wacce take daidaita tsakanin mu da ku cewa kada mu bautawa kowa sai Allah kuma kada muyi shirka da shi da komai kuma kada shashin mu su riki sashi ababen bauta koma bayan Allah to in sun juya baya to kuce musu ku shaida lallai mu musulmai ne (64) ya ku ma’abota littafi dan me kuke jayaiyya game da Ibrahim alhalin ba’a saukar da Attaura da Injila basai a bayan sa shin baza kuyi hankali ba (65) ku dunnan yanzu kunyi jayaiyya a cikin abunda kuke da ilimi to dan me kuke jayaiyya a cikin abunda baku da ilimi akan sa kuma Allah ya san komai kuma ku baku sani ba (66) Ibrahim bai zama bayahude ba ko kuma banasare sai dai shi ya kasance ne mai mika wuya ga Allah musulmi kuma bai kasance cikin mushirikai ba (67)” suratu Ali imaran, aya ta: 59-63.

Haihuwar Annabi Isah haihuwa ce irin ta mutane, Allah ya halicce shi a cikin mahaifa kamar yadda ya halicci sauran halittu, ikon mahalicce ya baiyyana a cikin haihuwar sa ta yadda ya halicce shi ba uba kamar yadda ta baiyyana ga sauran halittu da yawa, sai Allah madaukaki ya baiyyana hakikanin Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi kafin halittar sa da kuma bayan halittar sa da fadar sa madaukaki: kuma ka ambata a cikin littafin Maryama lokacin da ta fita tabar mutanen ta ta tafi wuri mai nisa (16) sai ta riki wurin buya daga gare su sai muka aika mata da mala’ikan mu sai yazo mata a siffar mutum madaidaici (17) sai tace lallai ni ina neman tsarin mai rahama daga gare ka in kai me tsoran Allah ne (18) sai yace lallai ni dan sako ne na ubangijin ki dan in baki kyautar yaro mai tsarki (19) sai tace ta yaya zai zamu inada yaro alhali babu wani mutum da ya taba ni kuma ni ba karuwa ba (20) sai yace haka ubangijin ki ya ce kuma hakan mai sauki ne a gare ni kuma dan mu sanya shi ya zama aya ga mutane da kuma rahama daga gare mu kuma hakan al’amari ne da aka riga a hukunta (21) sai ta dauki cikin sa sai ta tafi da shi wani wuri mai nisa (22) sai nakuda ta zo mata a gefen wani tushen bishiyar dabino sai tace kaice na dama na mutu kafin wannan lokacin kuma in zama abr mantawa (23) sai ya kirata daga kasanta cewa kada kiyi bakinciki hakika ubangijin ki ya sanya idn ruwa a kasanki (24) kuma ki girgiza tushen dabinonnan dabinai danyu masu dadi zasu fado akan ki (25) to ki ci kuma ki sha kuam ki ji sanyin ido idan har kin ga wani daga cikin mutane to ki ce lallai ni nayi alwashin azumi ga mai rahama bazan yi magana da wani mutum ba a yau (26) sai ta zo da shi wurin mutanen ta tana dauke da shi sai sukace ya ke Maryam hakika kinzo da wani babban al’amari (27) ya ke iyar uwar Annabi Haruna mahaifin ki ba mutumin banza bane kuma mahaifiyarki ba karuwa bace (28) sai tayi nuni zuwa gare shi sai sukace ta yaya zamuyi magana da wanda ke cikin tsumman goyo jariri (29) sai yace lallai ni bawan Allah ne ya bani littafi kuma ya sanya ni a matsayin Annabi (30) kuma ya sanya ne mai albarka a duk inda nake kuma yayi mun wasiyya da sallah da kuma zakkah matukar ina raye (31) kuma ni mai biyaiyyane ga mahaifiyata kuma bai sanya ni na zama mai girman kai ba tababbe (32) kuma aminci ya tabbata a gare ni ranar da aka haife ni da kuma ranar da zan mutu da kuma ranar da za’a tashe ni rayaiyye (33) wannan shi ne Isah dan Maryam zance na gaskiya da suke kokwantu a kan sa (34) bai kamata ba ga Allah ya riki wani a matsayin yaro tsarki ya tabbata a gare shi idan yayi nufi aukuwar wani abu to kawai yana ce masa ne kasance sai ya kasance (35)” suratu Maryam, aya ta: 16-35.

Kuma Alkur’ani mai girma ya baiyyana cewa lallai daukar cikin da Maryam tayi na Annabi Isah ya faru ne da busa daga mala’ika Jibrilu amincin Allah ya tabbata a gare shi ta yadda ya zo mata a siffa ta mutum kuma Allah ya umarce shi ya hura gefen hannun rigar ta, sai iskar ta sauka zuwa farjin ta, sai ta dau ciki nan take, Allah ya tsare ta ta zama kamar yadda yahudawa suke tuhumarta cewa ita mazinaciya ce kuma yaran ta dan zina ne, shi tsarkakakke ne daga haka da mahaifiyar sa Maryam amincin Allah ya tabbata a gare ta tsarkakakkace daga datti kuma tsarkakakka ce daga alfasha, Alkur’ani ya barrantar da ita daga dukkan haka, kamar yadda Allah ya baiyyana haka a cikin Alkur’ani da fadar sa: da kuma wcce ta tsre farjin ta sai muka yi busa a cikin sa daga ruhin mu kuma muka sanya ta ita da yaran ta suka zama aya ga talikai (91)” suratul Anbiya’i, aya ta:91.

 

 

 

MUTUNTAKAR ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Alkur’ani ya yi bayanin hakikanin Isah dan Maryam amincin Allah ya tabbata a gare shi kuma ya bada labari cewa shi bawan Allah ne Allah yayi ni’ima a gare shi kuma ya zabe shi dan isar da sakon sa zuwa ga bani isra’ila bayan Annabi Musa, kuma ya baiyyana cewa mahaifiyar sa ta kasance mai gaskiya ce mai tsarki duk irin abunda ke samun mutane to itama yana samunta da yaran ta, su suna ci kuma suna sha kuma suna bacci su tashi kuma suna ji zafin ciwo kuma suna kuka, to duk wanda haka shi ne siffar sa to taya zai zama abun bauta? Kuma shi Allah abun bauta ya tsarkaka daga dukkan wannan, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: Msihu dan Maryam ba kowa bane face Manzo wanda hakika manzanni sun gabata kafin sa kuma mahaifiyar sa mai gaskiya ce sun kasance suna cin abinci ka duba kaga yadda muke baiyyana musu ayoyi sannan ka duba kaga yadda ake kirkira musu karya (75)” suratul Ma’ida, aya ta: 75.

Allah bai cancanta da mata ba ko yaro domin shi tsarki ya tabbata a gare shi shi ne ubangijin halittu baki daya babu abun bautawa da gaskiya sai shi kuma babu abun bauta koma bayan sa, dan haka jingina wa Allah da yana daga cikin karya mafi girma a gare shi, duk wani abu da ba Allah ba to halitta ne bawan sa ne kuma yana karkashin klawar sa yana mai jayuwa a gare shi makaskanci a gare shi yana mai tabbatar da haka kodai da harshen sa ko kuma fidirar sa kamar yadda Allah ya baiyyana hak da fadar sa: “ kuma sukace Allah mai rahama yana da da (88) hakika kunzo da wani abu mai girma (89) sama ta kusa ruguzowa saboda shi kuma kasa ta tsasttsage kuma duwatsu su fadi a farfashe (90) saboda sunce Allah yana da yaro (91) kuma baya kamata ga mai rahama ya riki wani a matsayin yaro (92) babu wani abu a cikin sammai da kasa face sai duk sun je wurin mai rahama suna bayi (93)” suratu Maryam, aya ta: 88-93.

To ta yaya zai zama yanada yaro kuma yaro ba’a samun shi sai da sakamakon abubuwa biyu daidai da juna kankankan ko kuma kusa da juna, alhali shi Allah babu irin shi kuma babu kama da shi, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: kace shi ne Allah makadaici (1) Allah wanda ake nufin sa dan biyan bukatu (2) bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba (3) kuma babu wanda ya kasance daidai da shi (4)” suratul Ikhlas, aya ta: 1-4.

Kuma kirkirawa Allah yaro maganace ba sabuwa ba ta dade sosai kamar yadda mutum ya dade, ta fara bayana ne bayan fara baiyanar shirka a cikin mutane, mushirikan larabawa sun yi karyan cewa wai Allah yayi surukuntakata da aljanu sai ya haifi mala’iku wanda suke cewa su yaran Allah ne mata- Allah ya daukaka daga abunda suke fada daukaka mai girma- sai Allah madaukaki yace: ka tambaye su shin ubangijinka nada yara mata su kuma suna da maza (149) kuma shin mun halicci mala’iku mata ne alhali su suna gani (150) ku saura lallai su suna fadan haka ne daga abunda suka kirkira na karya (151) cewa Allah ya haihu kuma lallai su makaryata ne (152) ya zabi mata fiye da maza (153) me yasame ku ne yaya kuke yin hukunci (154) shin baza kuyi tunani ba (155) ko kuma kunada wata hujja ne baiyyananna (156) to kuzo da littafin ku in har kun kasance kunada gaskiya (157) kuma suka sanya dangantaka tsakaninsa da aljanu kuma su aljanu sun san cewa lallai su za’a gurfanar da su (158) tsarke ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffantashi da shi (159) sai dai bayin Allah wanda aka kubutar (160)” suratus Saffat, aya ta:149-160.

Kuma da yawa daga cikin yahudawa da kiristoci sun jinginawa Allah yaro saboda zalunci da kuma karya, dan koyi da wadanda suka gabace su a fadan wannan maganar wacce lafiyaiyyen hankali bai yadda da ita kamar yadda Allah ya baiyyana haka a cikin Alkur’ani da fadar sa: “ kuma yahudawa sunce Uzairu dan Allah ne su kuma kiristoci suka ce Almasihu dan Allah ne wannan shi zantuttukan su da bakunan su suna kwaikwayon zantuttukan wadanda suka kafurta gabanin su, Allah ya tsine musu ta yaya suke kirkirawa Allah karya (30) sun riki manyan malaman su da kuma masu bautan su ababen bauta koma bayan Allah da kuma almasihu dan Maryam kuma ba’a umarce su ba sai dai su bautawa Allah shi kadai babu wanin abun bauta da gaskiya sai shi tsarki ya tabbata a gareshi daga abunda suke shirka da shi (31)” suratut Taubah, aya ta: 30-31.

Kuma hakika Alkur’ani yayi hukunci dakafurta duk wanda ya kudurta cewa Annabi Isah dan Maryam shi Allah ne ko kuma shi yaran Allah ne ko kuma shi ne Allah daya cikin uku, kuma ya baiyyana cewa da’awar almasihu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ta kasance ne dan tabbatar da tauhidi da kuma kira zuwa gare shi da kuma rashin yin shirka da Allah dan koyi da wadanda suka gabace shi cikin Annabawa da manzanni kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ hakika wadanda sukace lallai Allah shi ne Almasihu dan Maryam sun kafurta kuma Almasihu yace ya ku mutanen bani isra’ila ku bautawa Allah ubangiji na kuma ubangijin ku lallai duk wanda yayi shirka da Allah to hakika Allah ya haramta masa aljannah kuma makomarsa wuta kuma azzalumai basuda wasu mataimaka (72) hakika wadanda suka ce lallai Allah daya ne cikin uku sun kafurta kuma babu wani abun bauta sai dai abun bauta guda daya kuma idan basu hanu ba daga abunda suke fada to lallai azaba mai radadi za ta shafi wadanda suka kafurta daga cikin su (73) shin baza su tuba zuwa ga Allah ba kuma su nemi gafarar sa kuma Allah mai yawan gafartawa ne mai jin kai (74)” suratul Ma’idah, aya ta: 72-74.

Kuma hakika dalilai na hankali wadanda Alkur’ani ke korowa sun kasance suna nuni akan cewa lallai Allah shi ne mahalicci mai iko mai jujjuya al’amura ubangijin komai kuma mamallakin sawanda yake halitta abunda yaga dama kuma yake aikata abunda yake so, kuma ababen da suke aukuwa ta hannun Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi na mu’ujizozi suna faruwa ne da umarnin Allah da ikon saba wai daga wani umarni bane ta bangare Annabi Isah, kuma suna baiyyana cewa lalai Annabi Isah da mahaifiyar sa basa mallakan cutarwa ko amfanarwa ga kawunan su ko ga wanin su cikin mutane kuma basa mallakar rayuwa ko tashi daga kabari, kuma Allah madaukaki baya da bukatuwa a gare su ko kuma wata halitta daga cikin halittun sa, sai dai su halittu ne suke da bukata a gare shi dukkan su suna tsananin bukatar rahamar sa, inda Allah madaukaki ya fada: hakika wadanda sukace lalai Allah shi ne almasihu dan Maryama sun kafurta kace musu to waye ke mallakar wani abu a wurin Allah in ya so ya halakarda Almasihu dan Maryama da mahaifiyar sa da wadanda suke ban kasa baki daya kuma abunda ke cikin sammai da kasa da abun da ke tsakanin su na Allah ne yana halitta abunda ya so kuma Allah mai iko ne akan dukkan komai (17)” suratul ma’idah, aya ta: 17.

Kuma hakika Allah ya saukar da ayoyin Alkur’ani suna tsawatar da bani isra’ila suna hana daga wuce iyaka a cikin addinin su duka fadan wani abu game da Allah ba tare dagaskiya ba, kuma suna baiyya cewa lallai Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda kiristoci ke raya cewa shi Allah ne ko kuma dan Allah ne ko kuma shi daya ne cikin uku cewa shi mutum ne kamar sauran mutane, yana kira zuwa ga Allah kuma yana bautan Allah kuma baya girman kai ya zama bawa mai kaskantar da kai ga Allah da umarnin sa, kuma duk wanda toge kuma yayi girman kai ga bautar Allah to lalo makomar sa itace azaba da kuma dauwwama a cikin wutar jahannama, kamar yadda Alkur’ani mai karamci ya baiyyana haka da fadar Allah madaukaki: “ ya ku ma’abota littafi kada ku wuce gona da iri a cikin addinin ku kuma kada ku fadi komai game da Allah sai dai gaskiya lallai shi Almasihu Isah dan Maryaam Manzan Allah ne kuma kalmarsa ce da ya jefata ga Maryama kuma ruhi ne daga gare shi to kuyi imani da Allah da manzannin sa kuma kada kuce Allah uku ne ku hanu daga haka shi yafi alheri a gare ku lallai Allah abun bauta ne guda daya tsarki ya tabbata a gare shi a ce yanada yaro dukkan abunda ke cikin sammai da kasa nashi ne kuma Allah ya isa ya zama wakili (171) Almasihu bazai yi girman kai ba dan ya zama bawa ga Allah hakanan ma mala’iku makusanta kuma duk wanda ya doge ya ki bauta masa kuma yayi girman kai to zai tada su zuwa gare shi baki daya (172) to amma wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiyuka na kwarai to zai cika musu ladan su kuma ya kara musu daga falalar shi amma kuma wadanda suka bijire sukayi girman kai to zai azabtar da su azaba mai radadi kuma baza su samu wani masoyi ko mataimaki ba koma bayan Allah (173) ya ku mutane hakika gaskiya ta zo muku daga ubangijin ku kuma mun saukar da wani haske zuwa gare ku mabaiyyani (174) to duk wadanda sukayi imani da Allah kuma sukayi ruko da shi to da sannu zai shigar da su cikin wata rahamadaga gare shi da wata irin falala kuma zai shiryar da su wata hanya mukakkiya zuwa gare shi (175)” suratun Nisa’i, aya ta: 171-175.

Kuma a bangare guda na masu cewa shi Allah ne kokuma yaran Allah ne ko kuma shi Allah daya ne cikin uku hakika su kuma yahudawa sun kasance suna zargin Annabi Isah ne amincin Allah ya tabbata a gare shi da cewa shi rai ne na shaidan mai sharri kuma shi mayaudari ne makaryaci, sai Alkur’ani ya baiyyana lalacewar zancen su kuma ya baiyyana cewa Annabi Isah Annabi ne da aka aiko me gaskiya ne cikin abun da yake isarwa daga ubangijin sa, kamar yaddad Allah madaukaki ya fada: “ lallai Almasihu Isah dan Maryama manzan Allah ne kuma kalmar sa ce da ya jefa ta zuwa ga maryam kuam ruhi ne daga gare shi to kuyi imani da Allah da kuma manzannin sa....” suratun Nisa’i, aya ta: 171.

Sai dai wannan ruhin irin sauran ruhi ne da aka halitta an jingina ta ne zuwa ga Allah ta fuskar darajtawa da kuma karramawa a gare shi, kuma ita kalmar ruhi bawai wani kebantaccen abu bane da aka kebance Annabi Isah da shi ba shi kadai Annabi Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi an jingina ransa zuwa ga Allah dan girmamawa da karramawa a gare shi, kamar yadda Allah ya bada labarin haka a cikin littafin sa da fadar sa: “ lokacin da ubangijin ka ya ce wa mala’iku lallai ni zan halicci wani mutum daga tabo (71) to idan na daidaita shi kuma na busa masa daga rai na to ku fadi a gareshi kuna masu sujada (72)” suratu Saad, aya ta: 71-72.

Kuma kamar yadda ya gabata wurin haihuwar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi, inda Allah ya kira mala’ika Jibril amincin Allah ya tabbat a gare shi ruhi daga Allah madaukaki lokacin da ya aike shi zuwa wurin maryam amincin Allah ya tabbata a gare shi dan ya bata kyautar Annabi Isah: “ kuma ka ambata a cikin littafin Maryam lokacin da ta bar mutanen ta ta tafi wuri mai nisa (16) sai ta riki wurin buya daga gare su sai muka aika mata da ruhin mu sai ya zo mata a matsayin mutum madaidaici (17)” suratu Maryam, aya ta: 16-17.

Hakanan ma Allah ya kira Alkur’ani da suna ruhi saboda zukata na rayuwa da shi saboda irin abunda ya ke kwararo mata na kwanciyar hankali da natsuwar zuciya haka nan kuma al’umma na rayuwa da shi da abunda ke tabbatar msusu da maslahohin duniya wanda ke ba kowane me hakki hakkin sa sai rayuka tsaru da mutunci da dukiyoyi, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “haka nan kuma mukayi maka wahayin ruhi daga gare mu kai baka kasance kasan meye rubutu ba ko kuma imani sai dai munsanya shi ya zama haske muna shiryadda wanda muka gada da shi cikin bayin mu kuma lallai kai kana shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya (52)” suratush Shura, aya ta: 52.

ANNABTAKAR ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Alkur’ani mai girma ya baiyana cewa dukkan Annabawa su daga zurriyyar Annabi Nuhu suka fito da Annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare su, kuma dukkan littafan da suka sauka daga sama an saukar da su ne akan manzanni ne daga zurriyyar wadannan Annabawan ne biyu masu karamci, kuam yana daga cikin abunda ba kokwanto a cikin sa cewa lallai Annabin mu Muhammad (S.A.W) yana daga cikin zuriyyar Annabi Isma’ila dan Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare su, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “ kuma hakika mun aiki Nuhu da Ibrahim kuma muka sanya Annabci da littafi a cikin zurriyyar su su biyu daga cikin su akwai shiryaiyyu kuma da yawa daga cikn su fasikai ne (26)” suratul Hadeed, aya ta: 26.

Kuma yana daga cikin tushe na imani a wurin musulmai imani da manzannin Allah madaukaki dukkan su, hakika umarni ya zo a cikin Alkur’ani na cewa a girmama su da kuma sansu da kwarzanta su da kuma kariya a gare su da kuma yada soyaiyyar su a cikin mutane da kuma imani da abunda aka saukar musu daga Allah madaukaki, kuma daga cikin wadannan manzannin akwai Annabi Isah dan Maryam amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda yake da daraja mai girma da matsayi madaukaki a wurin musulmai, Allah madaukaki yana cewa: “ kuce munyi imani da Allah da abunda aka saukar mana da abunda aka saukar wa Ibrahim da Isma’il da Ishaq da Ya’aqubu da Asbad da abunda aka baiwa musa da Isah da abunda aka baiwa Annabawa daga ubangijin su bama rarrabe wa tsakanin daya daga cikin su kuma mu masu mika wuya ne a gare shi (136) idan sunyi imani da irin abunda kukayi imani da shi to hakika sun shiryu in kuma suka juya baya to lallai su suna cikin tabewa da sabani kuma da sannu Allah zai kareka daga gare su kuma shi mai ji ne masani (137)” suratul Bakara, aya ta: 136-137.

Hakika bani sra’ila kafin aiko da Annabi musa sun kasance masu rauni kaskantattu kuma ana bautar da su a ban kasa kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ kuma lokacin da muka tsiratar da ku daga mutanen Fir’auna suna gana muku muguwar azaba suna kashe yaran ku maza kuma suna raya yaran ku mata kuma a cikin haka akwai jarabawa mai girma daga ubangijin ku (141)” suratul A’araf, aya ta: 141.

Sai Allah ya yi musu baiwa na aiko da Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi sai Allah ya daukaka su da wannan aikowan mai daraja sai halin da suke ciki ya canza daga kaskanci zuwa daukaka kuma daga talauci zuwa wadata kuma daga tozarci zuwa daraja sai suka zama sunyi nasara.

Sai zamani yayi tsawo akan mutanen bani isra’ila sai da yawan su suka kauce daga tsarin Allah wanda Annabi Musa ya zo da shi sai sukayi zalunci kuma sukayi barna a ban kasa sai suka karyata kuma suka kashe Annabawa da salihai daga cikin su sai wasu daga cikin su suka karyata tasi alkiyama da hisabi da azaba kuma suka nutse a cikin bin san rai da ababen more rayuwa kuma suka ci ukiyoyin mutane da barna, sai Allah ya aiko musu da Annabi Isah dan Maryam a matsayin manzo kuma ya sanar da shi Attaura da Injila dan ya maida su zuwa tsarin ubangiji da kuma mabubbuga tatacciya ingantacciya wanda zai kubutar da su daga abunda suke ciki na bata kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ kuma sai biyo da Annabi Isah dan Maryam a bayan su yana mai gaskata abunda ya gabace shi na Attaura kuma mun bashi Injila a cikin ta akwai shiriya da haske kuma yana gaskata abunda ya gabace shi na Attaura kuam shiriya ne da tunatarwa ga masu takawa (46)” suratul Ma’idah, aya ta: 46.

Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi ya tsayu da kiran mutanen bani isra’ila zuwa ga bautar Allah da kuma isar musu da sakon sa da kuma yin aiki da abun da ya zo a cikin Injila na hukunce-hukunce mafi alherin tsayuwa, Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ lokacin da Isah ya zo da hujjoji baiyyanannu sai yace hakika nazo muku da hikima kuma zan baiyyana muku sashin abunda kuke sabani a cikin sa to kuji tsoran Allah kuma kuyi ini biyaiyya (63) lallai Allah shi ne ubangiji na kuma ubangijin ku to ku bauta masa wannan itace hanya madaidaiciya (64)” suratuz Zukruf, aya ta: 63-64.

Lokacin da Annabi Isah ya ga irin yadda suke karyata shi da kuma kafurcewar su ga da’awar sa sai yayi kira a cikin mutanen sa yana cewa waye zai taimake ni kuma yayi hakuri akan abunda zai same shi saboda yada addinin Allah? sai hawariyawa sukayi imani da shi kuma adadin su mutum goma sha biyu ne suka kulla alkawi da shi akan zasu yda addinin Allah da kuma kira zuwa gare shi a cikin mutanen su da kuma hakuri akan abunda zai same su akan wannan hanyar kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ lokacin da Isah ya ga kafurci daga garesu sai yace waye zai taimake ne saboda Allah sai hawariyawa suka ce mu ne mataimaka Allah munyi imani da Allah kuma ka shaida cewa lallai mu musulmai ne (52)” suratu Ali imran, aya ta: 52-53.

 

 

 

SIFFAR ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI DA KAMANNIN SA DA FALALOLIN SA

Hakika Alkur’ani ya siffata Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi da wasu irin siffofi da suke nuni akan darajar wannan manzan mai karamci a wurin Allah madaukaki kuma hakika shi ya tattaru siffa ta kamala ta dan dam wanda ke nuni akan wannan darajar mai girma, kamar yadda Alllah ya baiyyana haka da fadar sa: “ kuma sai biyo da Annabi Isah dan Maryam a bayan su yana mai gaskata abunda ya gabace shi na Attaura kuma mun bashi Injila a cikin ta akwai shiriya da haske kuma yana gaskata abunda ya gabace shi na Attaura kuam shiriya ne da tunatarwa ga masu takawa (46)” suratul Ma’idah, aya ta: 46.

Kuma Alkur’ani mai karamci ya bada labari cewa lallai wannan manzan abun karfafawa ne daga Allah madaukaki kuma abun tsarewa ne da tsaran sa, Allah madaukaki yace: “ kuma hakika mun baiya Musa littafi kuma muka biyo da Annabawa a bayan sa kuma muka baiya Isah dan Maryam hujjoji baiyyanannu kuma muka karfafa shi da mala’ika Jibrilu to yanzu duk lokacin da wani manzo yazo muku da abunda ranku basa so sai kuyi girman kai wasun su ku kashe su wasun su kuma ku karyata (87)” suratul Bakara, aya ta: 87.

Kuma manzan Allah (S.A.W) ya siffanta shi da cewa shi abun koyi ne mai kyau kuam misali ne lafiyayye wurin imani da ibada da iklasi ga Allah madaukaki, kuma lallai saukar sa a karshen zamani alama ne me girma cikin alamun tashin alkiyama kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “ lokacin da aka sanya dan Maryam abun buga misali sai ga mutanen ka suna kangewa daga gare shi (57) kuma sukace shin allolin mu sun fi alheri ko kuwa shi basu buga wannan misalin ba sai dai dan jayayya a’a su mutane ne masu san yin jayaiyya (58) shi bawa ne wanda mukayi ni’ima a gare shi kuma muka sanya shi ya zama misali ga mutanen bani isra’ila (59) kuma da ace mun so da mun sanya mala’iku daga cikin ku suna mayewa a ban kasa (60) kuma lallai shi alama ne na tashin alkiyama to kada kayi jayayya da ita kuma ku bini wannan ita ce hanya madaidaiciya (61)” suratuz Zukruf, aya ta: 57-61.

Amma siffar sa kuwa ta jiki hakika manzan Allah (S.A.W) ya siffanta shi sai yace:” annabawa iyan uwan juna ne iyayen su mata daban daban ne amma kuma adinin su daya ne, kuma lallai ni ne nafi kowa cancanta gameda Isah dan Maryam, domin babu wani annabi tsakani na da shi, kuma lallai shi zai sakko, in kun ganshi to ku gane shi: mutum ne matsakaici kuma kalar sa tsakanin fari da baki take, zai zo yana sanye da kaya biyu masu kalan shudi, kansa na zubar da ruwa koda kuwa bai zuba ruwan a kansa ba saboda tsafta, zai karya gumaka, kuma ya kashe aladu, kuma ya sanya jiziya, kuma zai kira mutane zuwa ga musulunci, kuma a lokacin sa Allah zai hallaka addinai dukkan su sai dai musulunci kawai, kuma Allah zai halaka Dujal a zamanin sa, sai aminci ya wanzu a ban kasa, harma a samu rakumi na kiwo tare da zaki,damisa da kuma shanu, da kyarkyace tare da dabbobi, kuma kananan yara zasu dinga wasa da macizai amma baza su cutar da su ba, zai zauna tsawan shekaru arba’in, sai ya rasu kuma musulmai suyi masa sallah.” Duba cikin umdatut Tafseer.

Kuma manzan Allah (S.A.W) yace a cikin wani hadisi na daban: “naga Isah da Musa da Ibrahim, amma shi Isah, ja ne shi, yana da cukwikwiyayyen gashi, yana da fadin kirji, amma shi kuma Musa, baki ne, maii kiba ne, gashin shi mai santsi ne, kamar shi daga cikin mazajen zaddi ya fito, amma shi kuma Ibrahim to ku kalli mutumin ku, yana nufin kan sa.” Sahihul Jami’i.

Kuma Manzan Allah (S.A.W) ya baiyyana cewa yin imani da shi na daga cikin ababen da ke cika imani kuma yana daga cikin dalilan da ke sa a shiga aljan nah, inda yace: duk wanda ya shaida cewa lallai babu abun bauta da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin taraiyya, kuma lallai Muhammad bawansa ne kuma manzan sa ne, kuma lallai Isah bawan Allah ne kuma manzansa nekuma kalmar sa ce da ya jefa ta ga Maryam kuam ruhi ne daga gare shi, kua aljannah gaskiya ce, kuma wuta gaskiya ce, to Allah zai shigar da shi aljannah akan abunda yake kai na aiki.” Al bukhari.

Haka nan kuma imani da shi na daga cikin dalilan rubanya lada da daraja, inda Manzan Allah (S.A.W) yace: in mutum ya tarbiyyantar da baiwar sa sai ya kyautata tarbiyyanta, kuma ya kuyarda ita ya kyautata koyarda itan, sai ya iyanta ta kuma ya aure ta to yana da lada nin ki biyu, kuma idan yayi imani da Isah, sai kuma yazo yayi imani da ni to yanada lada ninki biyu, kuma bawa idan yaji tsoran ubangijin sa kuma yayi biyaiyya ga mai gidan sa to yanada lada ninki biyu.” Al bukhari.

Kuma Annabi (S.A.W) ya baiyyana irin tsarkin zuciya da wannan manzan mai karamci yake da ita wacce hassada bai bata ta ba o keta ko kiyaiyya, wacce take cike da kyautata zato ga mutane da kuma girmama Allah da kwarzanta shi, inda yace: “ Annabi Isah yaga wani mutum yana sata sai yace masa: kana sata ne? Sai yace: a’a ina rantsuwa da wanda babu abun bauta da gaskiya sai shi, sai Isah yace: nayi imani da Allah kuma idanu na sunyi karya.” Al bukhari,

 

 

 

ANNABI ISAH AMINCI ALLAH YA TABBATA A GARE SHI DA KUMA DUJAL

Alkur’ani ya baiyana cewa saukowar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi a karshen zamani alama ce daga cikin alamun kusantowar tashin alkiyama kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa:“ lokacin da aka sanya dan Maryam abun buga misali sai ga mutanen ka suna kangewa daga gare shi (57) kuma sukace shin allolin mu sun fi alheri ko kuwa shi basu buga wannan misalin ba sai dai dan jayayya a’a su mutane ne masu san yin jayaiyya (58) shi bawa ne wanda mukayi ni’ima a gare shi kuma muka sanya shi ya zama misali ga mutanen bani isra’ila (59) kuma da ace mun so da mun sanya mala’iku daga cikin ku suna mayewa a ban kasa (60) kuma lallai shi alama ne na tashin alkiyama to kada kayi jayayya da ita kuma ku bini wannan ita ce hanya madaidaiciya (61)” suratuz Zukruf, aya ta: 57-61

Kuma saboda falalar shi ne Allah zai aiko shi dan ya kashe Dujal da kuma yada musulunci da kuma kira zuwa gare shi, hakan kuwa zai faru ne in kasahe-kashe yayi yawa kuma fidirar mutane ta gurbata kuma kyakkyawan abu ya zama mummua mummuna kuma ya koma kyakkyawa, kuma dan ya tsayar da adalci kuma ya yada aminci a karshen zamani kamar yadda Annabi Muhammad (S.A.W) ya baiyyana haka da fadar sa: “ ya ku mutane! Lallai babu wata fitina a ban kasa tun lokaci da Allah ya halicci zurriyyar Adam wacce tafi girma irin fitinar Dujal. Kuma lallai Allah madaukaki bai taba iako wani Annabi ba face sai ya tsawatar da mutanen sagameda Dujal, kuma ni ne na kaeshen Annabawa, kuma kune na karshen al’ummu, to shi a cikin ku zai fito babu makawa, in har ya baiyana alhali ina cikin ku, to ni ne zan kare kowane musulmi, in kuma ya fito a bayana ne, to kowa ya kare kansa, kuma Allah shi ne halifa na akan dukan musulmi, kuma lallai shi zai baiyyana ne ta wata kofa tsakanin sham da iraqi, sai yayi yekuwa dama da hagu, ya ku bayin Allah! ya ku mutane! To ku tabbata dan zan siffanta muku shi siffantawar da babu wani Annabi da ya taba siffanta shi irin haka,.... zai ce: ni ne ubangijin ku, amma ku baza ku ga ubangijin ku na har sai kun mutu, kuma shi yana da ido daya ne, kuma ubangijin ku ba ido daya gare shi ba, kuma an rubuta a tsakanin idanun sa: kafuri, kowane mumini zai karanta, ya iya karatu ko bai iya ba, kuma daga cikin fitinarsa lalai zai zo tare da shi akwai aljannah da wuta, wutarsa aljannah ce, kuma aljannarsa wuta ce, duk wanda aka jarabce shi da wutar sa to ya nemi agajin Allah, kuma ya karanta ayoyin farko na suratul Kahfi...... kuma daga cikin fitinar sa zai ce wa mutumin kauye: ya kake gani in na dawo ma da mahaifin ka da mahaifiyar ka to zaka shaida cewa ni ne ubangijin ka? Sai yace: eh, sai shaidanu biyu su siffantu da siffar mahaifin sa da mahaifiyar sa, sai suce masa: ya kai yaran mu ka bi shi, domin shi ne ubangijin ka, kuma daga cikin fitinar sa, zai samu iko akan wata rai ya kashe ta, zai tsagata da zarto har sai gangan jikin ya rabu biyu, sai kuma yace:kuyi dubi zuwz ga wannan bawan nawa, ni zan tada shi sai kuma ya traya cewa yana da wani ubangiji ba ni ba, sai Allah ya tada shi, sai mabarnacin ya ce masa: waye ubangijin ka? Sai yace: ubangiji na shi ne Allah, kuma kai makiyin Allah ne, kai ne Dujal, wallahi ni ban taba samun tabbaci ba akan ka irin yau, kuma daga cikin fitinar sa zai umarci sama tayi ruwa, sai kuma ta zubar da ruwa, kuma ya umarci kasa ta fitar da tsirrai sai ta fitar da tsirrai, har ma dabbobin su a wannan ranar zasu koma masu kiba fiye da yadda suke a sauran kwanakin kuma zasu fi tudu da fadi kuma da hantsa cike da nono, kuma babu wani wuri da zai yi saura a cikin kasa face sai ya shige shi yayi gallaba akan sa, sai dai makkah da madiinah, babu wata kofa da zai zo tasu face sai ya samu cewa akwai mala’iku da takubba a zare, har ya sauka a wani wuri mai jan kala, wurin da kasar gishiri ta yanke, sai madinah ta girgiza sau uku, babu wani munafuki ko munafuka da zasu rage a cikin ta face sai sun fito zuwa gare shi, sai ta kore abarnatan da ke cikin ta, kamar yadda zugazugi ke kore dattin karfe, kuma wannan ranar ana kiranta ranar gamawa, sai aka ce: to ina larabawa suke a wannan lokacin? Sai yace su a wannan lokacin iyan kadan ne..... kuma shugaban su mutumin kirki ne, wata rana shugaban su zai shiga gaba dan ya jagoranci sallar asubah, sai ga Annabi Isah dan Maryan zai sauka a gare su da asubah, sai wannan shugaba nasu zai ja da baya dan Isah ya jagorance su, sai Isah ya daura hannunsa a kafadar sa, sai yace masa zo kayi sallah, domin takace kai akyi wa iqama, sai shugaban su yayi musu sallah, idan ya idar sai Isah yace: ku bude kofa, sai a bude kofa a bayanta a kwai Dujal, tare da shi a kwai yahudawa dubu saba’in, dukkan su suna dauke da takubbah masu ado da kuam kaho, idan Dujal ya hango Annabi Isah sai ya zagwanye kamar yadda gishiri ke zagwanyewa a cikin ruwa, sai ya juya zai gudu..... sai Annabi Isah ya tare shi a kofar ludd ta gabas, sai ya kashe shi, sai Allah ya eusa yahudawa, babu wani abu da Allah ya halitta da bayahude zai boye a bayan sa face sai Allah yasa yayi magana, babu duwtsu ko bishiya ko bango ko kuma dabba, sai dai tumfafiya, domin ita tana cikin bishiyoyin da bat magana, face sai yace: ya kai bawan Allah musulmi ga wani bayahude nan zo ka kashe shi, sai Isah dan Maryam ya zama a cikin al’umma ta mai hukunci mai adalci, kuma shugaba mai adalci yana karya gumaka, kuam ai yanka aladu, kuma zai sanya jiziya, kuma zai bar sadaka, baza a fita neman akuya ba ko kuma rakumi, kum a dauke mugunta da kiyaiyya, kuma a cire cutarwa dukkan dabba mai cutarwa, har dan karamin yaro zai tura hannun sa cikin ramin macijiya amma baza ta cutar da shi ba, kuma iyar karamar dabba zata hadu da zaki amma bazai cutar da ita ba, kuma kyarkeci zai shiga cikin dabbobi kamar shi ne karan su, kuma kasa ta cika da zaman lafiya kamar yadda a ke cika kofi da ruwa, kuma kalma zata hadu ta zama daya, ba’a bautawa kowa sai Allah, kuma yaki zai kwanta, kuma kuraishawa zasu karbi mulkin su, kuma kasa zata zama kamar kwallan azurfa, zata fitar da tsirranta kamar yadda take fitarwa a zamanin Adam, har ma mutane su taru su ci inabi reshe daya kuma ya ishe su, kuma wasu tawaga na mutane su taru akan rumman guda daya kuma ya kosar da su, kuma bijimin sa zai zama kaza da kaza da kaza na dukiya,kma doki ya koma iyan dirhami kadan.....kuma lallai kafin fitowar Dujal akwai wasu shekaru uku da za’a samu masu tsanani, yunwa mai tsanani zata kama mutane a cikin su, a shekara ta farko Allah zai umarci sama da ta rike daya bisa uku na ruwanta, kuma ya umarci kasa da ta rike daya bisa uku na shukar ta, sai Allah ya umarci sama da rike kashi biyu cikin uku na ruwanta a shekara ta biyu, kuma ya umarci kasa da rike biyu bisa uku na shukarta, sai kuma Allah ya umarci sam ada rike ruwan sama dukkan shi a cikin shekara ta uku, ko dugo daya na ruwan sama bazai sauka ba, kuma ya umarci kasa da rike tsirranta dukka ko ciyawa daya baza ta fito ba, babu abunda zaiyi saura mai hanta face sai ya mutu sai dai abunda Allah yaga dama kawai, sai akce: to da me mutane zasu rayu a wannan lokaci? Sai yace: hailala, da kabbara, da hamdala, kuma wannan zai kosar da su kamar abinci.” Sahihul Jami’i.

 

 

 

MU’UJIZOZIN ALLAH GA MANZANNINSA

Allah yana aiko da manzannni kuma yana karfafa su da mu’ujizozi wadanda ake iya gani dan su zamo ayoyi an gaske masu gaskata manzancin su, kuma lura da cewa wadannan mu’ujizozin wadanda ake gani ne to hakika sun kare tare da karewar zamunan su kuma ba wanda yayi imani da su sai wanda ya gan su, lokacin da sakon Annabi Muhammad 9S.A.W) yazo kuma sakon sa ya kasance na duk duniya ne kuma na karshe sai ya ama ba maka ta zama mu’ujiza mai dauwwama wacce zata wanzu komai dadewan lokaci har zuwa tashin alkiyama dan ta tsaida hujja akan mutane baki daya kuma ta zama mai shaida akan mutanen zamuna masu zuwa da nuna gaskiyar manzancin Annai Muhammad (S.A.W), saboda haka ne mu’ujizar shi bata zama zbunda ake gani ba kamar irin mu’ujizar sauran Annabawa gabanin sa, saboda mu’ujizar da ake gani baza ta iya tsayawa da wannan aikin ba kua bata ingant ba ga wannan aikin, saboda ita tana yankewa da yankewar aikinta kuma ba mai imani da ita sai wanda ya ganta, saboda haka ne mu’ujizar Annabi Muhammad (S.A.W} ta kasance wahayi ne da ake saukar masa kuma ana karanta hi har zuwa tashin alkiyama, hakika yazo da wani rirn zance mai keta al’ada wurin usulubin shi da balagar shi dukda cewa ya zo ne da shi a wani lokaci wanda an san mutanen sa da fasaha da iya magana, kuma duk da dogewar masu saba masa a zamanin sa da kuma ma dukkan zamuna a bayan sa akan bijire masa da kuma kokarin tabbatar da rashin mu’ujizancin maganar da akayi masa wahayi, sai dai su sun kasa zuwa da wata sura irin sa ko kuma wata aya daya irin sa, kuma dag cikin mu’ijizar Alkur’ani mai karamci shi cewa lallai shi ya bada labarurruka na gaibi, shi Alkur’ani mai girma shi ne mu’ujizar Annabi Muhammad (S.A.W) madauwwamiya, Annabi (S.A.W) yana cewa yana mai bayanin wannan hikakanin zancen: “ babu wani Annabi face sai anbashi wani abu wanda zai sa mutane suyi imani da shi, kuma ni abunda aka bani shi ne wahayi da Allah yake yi mini, to ni ina fatan in fi su yawan mabiya ranar alkiyama.” Sahihul bukhari.

 

 

 

MU’UJIZOZIN ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Kamar yadda muka ambata a baya cewa wasu mutane suna jayaiyya da kuma kafurce wa manzanni amincin Allah ya tabbata a gare su kuma basa imani sai da hujjoji da ido ke iya gani, saboda haka ne Allah ya karfafa manzanni da mu’ujizozi wadanda suke nuni akan gaskiyar sakonsu da Allah ya turo su da shi, sai dai mu sani cewa ko wce mu’ujiza tana aukkuwa ne da ikon Allah da izinin sa da karfafawar sa, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: kuma hakika mun aika da manzanni gabanin ka kuma muka sanya musu mata da zurriyya kuma bai kamata ba ga wani manzo yazo da wata aya ba sai da izinin Allah kowane abu yanada lokaci (38)” suratu Ra’ad, aya ta: 38.

Haka nan ma mu’ujizozin da Allah ke gudanar da su ta hanyar manzannin sa ta bangaren abunda mutanen su suka shahara da shi, mutane Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi sun shahara da tsafi sai mu’ujizar Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gre shi ta zama sanda wacce ke hadiye abunda bokaye suka hada, ta yadda bokayen suke ta jefa sandnan su da igiyoyin su akan kasa sai daga baya su koma suna tafiya kamar macizai,, sai suka tsafe idanun mutane sai suke ganin sanduna da igiyoyi kamar macizan gaske, har shi ma Annabi Musa sai da yaji tsoro a ransa lokacin da ya gansu, Allah madaukaki yana cewa: “ sai bokayen Fir’aua suka zo sai sukace muna da kyauta in mu kasance mu ne masu nasara (113) sai yace eh ai lallai ku kuna cikin makusanta (114) sai sukace ya kai Musa kodai ka jefa ko kuma mu muama masu jefawa (115) sai yace ku jefa lokacin da suka jefa sai suka tsfe idanun muta kuma suka tsoratar da su kuma suka zo da sihiri mai girma (116) sai mukayi wahayi zuwa ga Musa cewa ka jefa sandar ka sai gashi tana hadiye abunda suke jefawa (117) sai gaskiya ta baiyana kuma baunda suka kasance suna aikatawa ya baci (118) sai akayi galaba akan su a wannan wurin sai suka juwa suna kaskantattu (119) sai bokaye suka fadi suna masu sujada (120) sai sukace munyi imani da ubangijin talikai (121) ubangijin Musa da Haruna (122)” suratul A’araf, aya ta: 113-122.

Haka nan ma Annabi Isah amincin Allah ya tabbata agare shi an aike shi zuwa ga wasu mutane da basa imani sai da abun da ido ke iya gani wanda suke gani karara da idanun su,kuma hakika wasu cututtuka sun yadu a cikin su, sai mu’ujizrsa ta zama ta dace da wannan, sai Allah ya karfafa shi da wasu mu’ujizozi masu girma masu tunatarwa akan ikon Allah kuma tana karfafa imani da shi, sai yayi magana da mutane yana tsumman goyo kuma ya kasance yana halittar tsuntsu daga tabo sai yayi busa a cikin sa sai ya zama tsutsu da izinin Allah, kuam ya kasance yana warkar da mai kyasfi da kutare, kuma yana raya matattu da ikon Allah, kuma yana ba mutane labarin ababen da suke ci da wanda suke adanawa a gidajen su, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ lokacinda Alah ya ce ya kai Isah dam Maryam ka tuna ni’imata a gare ka da mahaifiyarka lokacinda na karfafe ka da mala’ika Jibrilu kana magana da mutane a tsumman goyo da kuma bayan ka tsufa da kuma lokacin da na sanarda kai littafi da hikima da Attaura da Injila da kuma lokacinda kake halitta daga turbaya lamae tsunstu sai kayi busa a cikin sa sai ya zama tsutsu da iko na kuma kana warkar da mao kyasfi da kuturu da iko na da kuma lokacinda kake raya matattu da iko na da kuma lokacin da na kange bani isra’ika daga gare ka lokacin da kazo musu da gaskiya sai wadanda suka kafurta daga cikin su suka ce wannan ba komai bane sai dai sihiri mabaiyyani (110)” suratul Ma’ida, aya ta: 110.

kuma daga cikin mu’ujizozin sa da karamar sa wadda Allah yayi masa kyautar su she ne cewa lallai shi an amsa addu’ar sa lokacinda mabiyansa suka nemi a saukar musu da wani faranti na abinci daga sama dan zukkztan su su samu natsuwa kuma su tabbatar da gasiyan manzancin sa, Allah madaukaki yace: kuma lokacin da nayi wahayi zuwa hawariyawa cewa kuyi imani da ni da kuma manzo na sai sukace munyi imani kuma ka shaida cewa lallai mu musulmai ne (111) lokacin da hawariyawa sukace ya kai Isah dan Maryam shin ubangijin ka zai iya saukar mana da wani teburi na abinci daga sama sai yace kuji tsoran Allah in har kun kasance ku muminai ne (112) sai sukace muna so ne muci daga gare shi kuma zukatan mu su samu natsuwa kuma mu tabbatar da cewa gaskiya ka fada mana kuma mu zama masu shaida a kanta (113) sai Isah dan Maryam yace ya Allah ka saukar mana da wani teburi na abinci daga sama dan ya zama idi a gare mu ga nafarkon mu da na karshen mu da kuma aya daga wurinka kuma ka azurtamu dan kaine mafi alherin masu azurtawa (114) sai Allah yace lallai ni zan saukar da she a gare ku to duk wanda ya kafurce bayan haka daga cikin ku to lallai ni zan azabtar da shi wata irin azabar da bazan taba yiwa wane irinta ba cikin talikai (115)” suratul Ma’ida, aya ta: 111-115.

 

 

 

ANNABAWA DA KUMA DA’AWAR TAUHIDI

Lallai tushen addinin Manzanni baki dayan su guda daya ne saboda tushensa daga Allah ne, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ ko sun riki ababen bauta ne koma bayan sa to kace musu ku zo da hujjojin ku wannan shi ne tunatarwar wadanda suke tare da ni da wadanda suka gabace ni sai dai da yawan su basu san gaskiya ba sai suka koma suna juya baya (24) kuma bamu aiko wani manzo ba gabanin ka face sai munyi wahayi zuwa gare shi cewa lallai babu abun bauta dagaskiya sai ni to ku bauta mini ni kadai (25)” suratul Nbiya’i, aya ta: 24-25.

Tauhidi shi ne abuda dukkan karantarwar shari’ar musulunci ke zagaye a kan sa kamar yadda haka yake a cikin dukkanin shari’o’in sama da suka gabata, kirane zuwa ga kadaita Allah da kuma tsarkake bauta a gare shi shi kadai, kuma wannan shi ne abun da Allah ya halicci mutane domin sa kuma aka halicci aljannah da wuta saboda shi, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: an shar’anta muku addini irin abunda akayiwa Nuhu wasiyya da shi da kuma abunda mukayi wahayi zuwa gare ka da kuma abunda mukayi wa Ibrahim wasiyya da shi da Musa da Isah cewa ku tsaida addini kuma kada ku rarraba a cikin sa abunda kuke kira zuwa gare shi yayi girma akan mushirikai Allah yana zabar wanda ya so a gare shi kuma yana shiryarwa zuwa gare shi wanda ya koma zuwa gare shi (13)” suratush Shura, aya ta: 13.

Kuma wannan itace wasiyyar Annabawa baki dayan su ga mutanen su dukkan su da kuma zurriyyar su a kebe da yin tauhidi da kuma tsrkake bauta ga Allah shi kadai, kamar yadda Alah ya bada labarin haka gaemda Yaqub amincin Allah ya tabbata a gare shi da fadar sa: “ shin ko kuna nan ne lokacin da mutuwa ta riski Ya’qub lokacin da yace wa yaran sa me zaku bautawa baya na sai sukace zamu bautawa ubangijin ka da kuma ubangijin iyayen ka Ibrahim da Isma’ila da Ishaq duka abun bauta ne guda daya kuma masu mika wuya ne a gare shi (133)” suratul Bakara, aya ta: 133.

Ingantaccen mandiki da kuma lafiyaiyyen hankali suna kin shirka ga Allah domin shika tawaya ne kuma wannan abu ne korarre ga Allah mahalicci wanda ya samar da wannan duniyar, idan shirka ta zama daga cikin abaebn da halittu basa kauna cikin abunda ke tsakanin su to me kak tunani game da ubangijin halittu, ita wasa ce da warge kuma bata kamata ga Allah, Allah madaukaki yana cewa: “ kuma bamu halicci sammai da kasa da abunda ke tsakanin su ba dan wasa (16) da ace mun so mu riki wasa da mun rikeshi daga gare mu in har mun kasance masu aikatawa (17) a’a mu muna jefa gaskiya akan karya sa ta ruguza ta sai ta wayi gari rusasshiiya kuma kuna da zaba saboda abunda kuke siffanta shi (18) kuma abunda ke cikin sammai da kasa nashi ne kuma wadanda suke tare da shi basa girman kai daga bautar sa kuma basa hasara (19) suna tasbihi dare da rana kuma basa yankewa (20) shin ko sun riki ababen bauta ne a kasa su ne suke tayar da su (21) da ace a cikin su akwai ababen n bauta koma bayan Allah to da sun lalace tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin al’arshi daga abunda suke siffantawa da shi (22) ba a tambayar sa game da abunda yake aikatawa sune ake tambayar su (23)”suratul anbiya’i, ayata:16-23

Allah ya kasance abun tsarkakewa daga wasa da wargi da shagala kuma shi abun tsarkakewa ne daga rike wani a matsayin yaro saboda daga cikin ababen da suka tabbata a hankalce cewa samuwar yaro yana yana hukanta samuwar mata kuma wannan abu ne korarre ga Allah kuma abun tsarkakewa ne daga gare shi, samuwar mata da yaro ma’anar sa shi ne suma sunada zati na allantaka kamar zatin Allah kuma su samammu ne tuntuni ba farko kuma ba karshe, kuma wannan korarren abu ne, mahalicci daya ne shi ne Allah madaukaki bashi tamka ko kuma makamanci, kuma duk wanda ke da bukatar mata to dan me bazai riki wasu mata ba da kuma masoya ba mace daya ba kawai! Kuma shi Allah madaukaki tsarkakakke ne daga wannan dukkan sa, kamar yadda rike yaro ke nuni akan rauni da bukatuwa zuwa ga taimako daga wannan yaron to kuma dan me zai riki yaro daya kawai ba yara da yawa ba sai kuma jikoki da dangantaka! Kuma shi Allah tsarkakakke ne daga bukatuwa zuwa ga wani kuma tsarkakakke ne daga wannan dukkan sa, kuma duk wanda yake da yaro ma’anar haka shi ne yanada iko akan haihuwa kenan to kuma wannan ke nuna cewa shima haifan sa akayi, duk wanda keda yaro to hakika shima yana da baba ko kuma mahalici, kuma hakan dkkan sa korarre ne daga Allah mahalicci shi daya makadaici wanda bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba, kuma duk wanda ya riki yaro to wannan na nuna cewa shi zai tsufa kuma yaronsa nada gado a cikin kayan sa da zai bari, wannan dukkan sa korarren abu ne daga Allah mahalicci shi kadai makadaici, Allah madaukaki yana cewa: “ makagin halittan sammai da kasa ta yaya zai zama yanada yaro alhali bashi da mata kuma shi ne ya halicci dukkan komai kuma shi masani ne ga dukkan komai (101) wannan shi ne Allah ubangijin ku babu abun bauta da gasikiya sai shi mahaliccin dukkan komai to ku bauta masa kuma shi wakili akan dukkan komai (102) gani baya iya riskansa kuma shi ne yake riskan gani kuma shi ne mai tausasawa mai bada labari (103)” suratul An’am, aya ta:101-103.

Kuma abu ne sananne cewa bukatuwa zuwa ga abokin taraiyya na nuni ne akan rauni ga dayan abokin taraiyyan kowane dayan su na cika da dayan, shi kuma Allah madaukaki baya bukartar wani daga cikin halittun sa dan ya cika tawayar da ke tare da shi ko kuma dan ya taimake shi wajan gudanar da wannan duniyar da kula da lamuran halittun sa sai dai halittunsa ne ma ke da bukatuwa zuwa gare shi suna kwadayin abunda ke wurin sa tsarki ya tabbata a gre shi shi ne mawadaci, Allah madaukaki yana cewa: “ kuma kace godiya ta tabbata ga Allah wanda bai riki wani yaro ba kuma baida abokin taraiyya a cikin mulki kuma bashi da wani maji dadi na daga kaskanci kuma ka girmamashi girmamawa (111)” suratul Isra’i, aya ta: 111.

Kuma hakika Alkur’ani ya baiyyana shirka a game da hakkin Allah wanda shi ne ya samar da wannan duniyar, kuma ya tabbatar da sabubba na lafuzza da hankali wanda ingantaccen mandiki ke karba kuma lafiyaiyyen hankali ke yarda da su:

  • Yawaitar ababen bauta yana hukunta cewa kowane daya daga cikin su na da cikakken iko saboda cikakken iku siffa ce ta abun bauta, shirka na hukunta cewa kowanen su zai bukaci wani abu sabanin dayan sai sakamakon haka jayaiya ya auku da sabani da fada tsakanin masu taraiyya biyu wanda zai haifar da lalacewar duniya dukkan ta, Allah ya yi girman da za’a ce yana da wanda ke taraiyya da shi a cikin mulkin sa saboda shirka barna ce sai a tsarkake Allah daga gare ta, kuma hakika Alkur’ani mai girma ya baiyyana haka sai Allah madaukaki ya ce: “ shin ko sun riki wasu ababen bauta ne a doran kasa su ne suke tada su (21) da ace a cikin su akwai wani abun bauta da ba Allah ba to da sun lalace tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin al’arshi daga irin abunda suke siffanta shi (22)” suratul Anbiya’i, aya ta: 21-22.
  • Lallai samuwar wasu ababen bauta daban tare da Allah yana hukunta cewa kowanne daya daga cikin su yana da karfin da zai iya yin galaba da yaki a tsakanin su dan samun iko da kuma juya duniya wannan shi ne abun da Alkur’ani ya kore shi, Allah madaukaki yana cewa: “ kace da ace akwai wani abun bauta tare da shi kamar yadda suke cewa kenan da sun nemi hanya zuwa ga darewa kan kujerar mulki (42) tsarke ya tabbatan masa kuma ya daukaka game da abunda suke fada daukaka mai girma (43) sammai bakwai suna tasbihi a gare shi da kasa da abunda ke cikin su kuma babu wani abu face yana tasbihi da gode wa ubangijin sa sai dai bakwa fahimtar tasbihin su lallai shi ya kasance mai yawan hakuri mai yawan gafara (44)” suratul Isra’i, aya ta: 42-44.
  • Lallai samuwar wasu ababen bauta tare da Allah yana hukunta raba duniyar tsakanin su su biyu dan kowannen su ya kebanta da abunda ya halitta kuma hakan korarre ne ga Allah, Allah madaukaki yana cewa: “ Allah bai riki wani ba a matsayin yaro kuma babu wani abun bauta tare da shi kenan da kowannen su ya tafi da abunda ya halitta kuma da sashinsu yayi rinjaye akan sashi tsarki ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffanta shi (91)” suratul Muminuun, aya ta: 91.

Saboda haka ne shirka ta zama daga cikin mafi girman zunubain da Allah baya gafarta wa ga wanda ya mutu akai kuma lali aljannah haramtacciya ce a gare shi kuma matabbacin sa wuta kuma tir da makoma saboda haka ne mafi yawan ayoyin Alkur’ani suna tsawatarwa daga wannan zunubin wanda mukace kamar yadda ya gabata tawaya ne ga Allah kuma zance ne a gare shi ba tare da ilimi ba, Allah yana cewa: “ lallai Allah baya gafarta wa in akayi shirka da shi kuma yana gafarta abunda bai kai haka ba ga wanda ya so kuma duk wanda yayi shirka da Allah to hakika ya kirkiri zunubi mai girma (48)” suratun Nisa’i, aya ta: 48.

 

 

 

 

ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI DA BARRANTAR SHI DAGA SHIRKA

Alkur’ani mai girama ya baiyyana cewa Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi Annabi ne kamar sauran Annabawa halittane kuma bawan Allah ne, kuma hakika ya kasance cikin masiu kira zuwa ga tauhidi bai kasance yana tabbatar da mutanen sa ba akan abunda suke kai ba na shirka, ya kira mutanen sa zuwa ga imani da Allah shi kadai da watsar da duk abunda ba shi ba na sauran ababen bauta kuma ya baiyyana musu da yawa cikin abunda bani isra’ila suke sabani a cikin sa na shari’u, Allah madaukaki yace: “ lokacin da Isah ya zo musu da hujjoji sai yace hakika nazo muku da hikima kuma dan i baiyana muku wasu daga cikin abunda kuke sabani a cikin sa to kuji tsoran Allah kuma kuyi mun biyaiyya (63) lallai Allah shi ne ubangijina kuma ubangijin ku to ku bauta masa shi kadai wannan itace hanya madaidaiciya (64)” suratuz Zukruf, aya ta: 63-64.

Kuma Alkur’ani ya barrantar da shi akan cewa zai kira mutanen sa zuwa ga shirka da shi ko kuma yayi umarni da shi kuma ya baiyana cewa lalai shi zai tsaya gaban ubangijin talikai ranar alkiyama kuma a gaban halittu dukkan su dan ya kore abunda bani isra’ila suke tuhumar shi da shi na cewa hi ne ya kira su da su bauta masa shi da mahaifiyar sa, kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: “ kuma lokacin da Allah yace ya kai Isah dan Maryam shin kaine kace wa mutane ku rikeni da mahaifiyata ababen bauta koma bayan Allah sai yace tsarki ya tabbata a gare ka bai kamace ni ba in fadi wani abu wanda bani da hakki indai har ni na fadi haka to hakika ka sani da shi kana sanin abunda ke cikin raina ni kuma bana sanin abunda ke cikin ranka lallai kai masani ne ga abunda yake boye (116) ban ce musu komai ba sai a bunda ka umarce ni da shi cewa ku bautawa Allah ubangiji na kuma ubangijin ku kuma na kasance mai shaida akan su lokacinda nake cikin su lokacin da ka dau rayuwta ka kasance kaine mai kula da su kuma kai mai shaida ne akan dukkan komai (117) in ka azabtar da su to lallai su bayin ka ne in kuma har ka gafarta musu to lallia kai ne mabuwayi mai hikima (118)” suratul Ma’idah, aya ta: 116-118.

 

 

 

BUSHARAR ANNABI ISAH DA ZUWAN ANNABI MUHAMMAD AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Alkur’ani mai girma ya baiyyana cewa lallai Allah madaukaki ya riki alkawari akan dukkan manzanni cewa sashin su zasu gaskata sashi, da kuma cewa in Allah ya aiko da wani manzo yana gaskata abunda ya ke tare da su to suyi imani da shi kuam su gaskata shi kuma su riki wannan alkawarin ga mutanen su, su Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su Allah ya wajabta musu da cewa sashen su yayi imani da sashi, kuma sashinsu ya gaskata sashi saboda duk abunda ke tare da su daga Allah yake, Allah madaukaki yace: “ lokacin da Allah ya riki alkawari akan Annabawa cewa saboda abunda na baku na littafi da hikima sai wani manzo yzo muku yana gaskata abunda ke tare da ku cewa lallai ku zakuyi imani da shi kuam lallai zaku taimake shi sai yace shin kun tabbatar da haka kuma kun riki alkawari akan haka sai suka ce mun tabbatar sai yace ku shaida kuma ni ina tare da ku cikin masu shaida (81) duk kuma wanda ya juya baya a bayan haka to wadannan su ne fasikai (82) shin yanzu wani addini da ba na Allah ba suke kauna kuma alhali gareshi ne duk wanda ke cikin sammai da kasa suka mika wuya suna so da kuma basa so kuma gareshi zasu koma (83)” suratu Ali imran, aya ta: 81-83.

Kuma Alkur’ani yazo da wasu ayoyi da suke kiran wadanda ba musulmai ba musamman ma ahlul kitabe daga cikin su (yahudawa da kiritoci) zuwa ga yin imani da Annabi Muhammad (S.A.W) da kuma bin sakon sa, kamar yadda Allah ya baiyyana haka a cikin Alkur’ani da fadar sa: “ ya ku bani isra’ila ku tuna ni’imata da nayi muku kuma ku cika alkawari na a zan cika alkawarin da nayi muku kuma kuji tsorona ni kadai (40) kuma kuyi imani da abunda na saukar yana gaskata abunda ke tare da ku kuma kada ku kasance na farkon kafurce masa kuma kada ku siyar da ayoyi na da iyan kudi kadan kuma kuji tsorona ni kadai (41) kuma kad ku cakuda gaskiya da karya kuma sai kuke boye gaskiya alhali kuna sane (42)” suratul Bakara, aya ta: 40-42,

Kuma hakika Annabi Isah ya amsa umarnin Allah saboda kuwa yayi bushara da da wani manzo da zai zo a bayan sa kuma ya baiyyana wa mutanen sa cewa shi manzo ne na bani isra’ila kawai, hakika yazo a cikin Injilar Matta 15/24 lallai shi yace: “ ni ba’a aiko ni ba sai dai zuwa ga battan gidaje bani israila kawai”.

Kuma daga cikin maganar saamincinAllah ya tabbata a gare shi hakikanin gaskiyar abubuwa biyu zasu baiyyana:

gaskiya ta farko: lallai shi ba’a aike shi ba dan mutane baki daya sai dai shi an aike shi ne zuwa fga wasu mutane kebantattu a wani zamani kebantacce, kuma wannan shi ne abun da injiloli suka ruwaito.

To idan wannan shi shi ne abun da Injilolin su suek fada to saboda me da’awar kiristoci bata takaita akan bani isra’ila ba kawai (yahudawa) da kuma kiran su zuwa ga kiritanci dan tabbatar da maganar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi mai makon su sabawa maganar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi kum su koma kiristantar da wadanda ba bani isra’ila ba?!

Kuma lallai wannan nassin na Injila a cikin sa akwai dalili a fili akan cewa kiristanci ba addini ne na duniya baki daya ba kuma lalli bushara da shi baya cikin rukunnan addinin kiristanci.

Gaskiya ta biyu: shi ne cewa matukar dai shi ba’a aiko shi ba sai dai zuwa ga wasu batattu daga cikin bani isra’ila wannan ke nuna cewa akwai wani Annabi da za’a aiko a bayan sa kuma da’awar sa zata zama ta duniya ce baki daya kuam shi ne zai zama na karshe, kuma wannan shi ne abunda Annabi Isah yayi bushara da shi ta yadda ya zama daya daga cikin aiyyukan Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi shi ne bushara da zuwan annabi na karshe Muhammad (S.A.W), ta yadda Alkur’ani ya baiyyana wannan gaskiyar, Allah madaukaki yana cewa:” kuma lokacinda Isah dan Maryam yace yaku bani isra’ila lallai ni manzan Allah ne zuwa gare ku ina mai gaskata abunda ya gabace ni na Attaura kuma ina bushara da wani manzo da zai zo a baya na sunan sa Ahmad lokacin da yazo musu da hujjoji sai sukace wannan sihiri ne mabaiyyani (6)” suratus saffi, aya ta: 6.

Kuma mutum mai adalci wayaiyye wanda ya iyanta hankalin sa daga makauniyar biyaiyya ga wanin sa da kuma sake linzami ga addinin iyaye da kakanni zai tambayi kansa cewa shin akwai wani abu da zai hana manzan Allah (S.A.W) zama Maznzo aiyakke daga Allah madaukaki kuma hakika an aiko Annabawa da Manzanni da yawa kafin sa? Idan dai har amsar ta zama cewa babu wani abu da zai hana a hankalce da kuma shar’ance to saboda me ake inkarin Manzancin sa da Annabcin sa amincin Allah ya tabbata a gare shi ga mutane baki daya amma kuma aka tabbatar da manzancin Annabawan da suka zo kafin sa?!.

 

 

 

MATSAYAR MANYAN MALAMAI DA MASU BAUTA SALIHAI NA KIRISTOCI GAME DA MANZANCIN ANNABI MUHAMMAD

Hakika da yawa daga cikin malamai da masu bauta na kiristoci sunyi imani da Manzan Allah Muhammad (S.A.W) bayan sun san cewa abunda Annabi Muhammad yazo da shi gaskiya ne, hakika littattafan su masu tsarki sunyi bushara da baiyyanar wani manzo bayan Annabi Musa da Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gre su, duk da irin abun da ya shiga wadannan littattafan na canji da juyarwa da wasannni wurin tarjama a tsawon lokuta mabanbanta da kuma bacewar asalin bugun su sai dai siffofin Annabi Muhammad (S.A.W) dawan syu sun rage a cikin su kuma su siffofi ne da ke nuni akan sa nuni mabaiyyani babu kokwanto a cikin su, saboda haka ne har zuwa yau ake samun adadi mai yawa na kiristoci da suke shiga cikin addinin musulunci duk da irin batashi da ake yi da gangan ta bangaren kafofin sadarwa na zamani na turawa, Allah madaukaki yace: “ su ne wadanda suke bin manzo Annabi wanda baya rubuto ko karatu wanda suke samunshi a rubuce a wurin su a cikin Attaura da Injila yana umartar su da kyaikkyawa kuma yana hana su daga mummuna kuma yana halatta musu abubuwa masu dadi kuma yana haramta musu abubuwa masu cutarwa kuma yana sauke nauyin da ke kansu da kuma kulli da ke wuyan su to duk wanda sukayi imani da shi kuma suka bashi kariya kuma suka taimake shi kuma suka bi hasken da ak saukar tare da shi wadannan sune masu rabauta (157)” suratul A’araf, aya ta: 157.

Hakika Annabi (S.A.W) ya baiyyana wa sahabban sa cewa shi busharar dan uwan sa ne Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi lokacin da suka tambaye shi sai suka ce: ya manzan Allah ka bamu labarin kanka, sai yace: ni ne addu’ar mahaifina Ibrahim kuma busharar Isah, kuma lokacin da mahaifiyata ta dauki cikin na ta ga kamar wani haske ya fita daga gare ta sai ya haskaka manyan gidajen busra na kasar sham.” Tafsirin Alkur’ani na Ibn kaser.

Lokacin da aka aiko Annabi Muhammad (S.A.W) wanda suka imani da shi sun yi imani kuma wadanda suka kafurta suka kafurta ciin mutanen ahlul kitabi, Safiyyah iyar Huyaiyyi dan Akhtab Allah ya kara mata yadda matar Manzan Allah (S.A.W) tana cewa kuam ita bayahudiya ce kafin ta musulunta: “ babu wani daga cikin yaran mahaifi na da mahaifiyata da suka fi soyuwa a gare su kamar ni, ban taba zuwa wurin su tare da sauran yaran su ba face sai sun dauko ni sun bar sauran, lokacin da Manzan Allah (S.A.W) ya zo qubq- kauyen bani Amru bnAuf- sai mahaifi na ya tafi wurin sa da dan uwan baba na Abu Yasir bnAkhdab da duku-duku, wallahi basu dawo wurin mu ba sai bayan faduwar rana, sai suka dawo mana jikin su yayi sanyi kasalallu gajiyayyyu suna tafiya a hankali, sai na je tarbar su kamar yaddda nakeyi kullum wallahi ba wanda ya kalleni a cikin su, sai naji baffa na Abu Yasir yana cewa mahaifi na: shin shi ne kuwa? Sai yace: eh wallahi! Kana gane shi da kamar sa da kuma siffar sa? Sai yace: eh wallahi! Sai yace: to me ye a ranka game da shi? Sai yace” kiyaiyyar sa wallahi matukar ina raye.” Sirah ta Ibn Hisham 2/165 da kuma Baihaqi a cikin Addala’il 2/532.

Kuma hakika da yawa daga cikin malamai da masuu bauta cikin kiristoci a da da yanzu sun karbi gaskiyar da ta Annabi Muhammad yazo da ita, kuma daga cikin wadanda sukayi sauri suka shiga musuliunci akwai sarkin habasha Annajjashi a zamanin Manzan Allah (S.A.W), kuma ya kasance cikin kiristoci kuma yana cikin wadanda suka san littattafan kiristoci masu tsarki kuma ya san busharorin da suke magana akan cewa akwai wani Annabi da za’a aiko bayan Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi, kuam ya kasance mutum ne da ke dauke da imani mai haske kuma ya rungumi ingantacciyar kiristanci mai hankali, wacce take nesa ga barin san rai, Ummu Salmah matar Annabi (S.A.W) tana cewa: “ lokacin da muka sauka a garin habasha sun amshe mu hannu bibbiyu mafi alherin su she ne Najjashi, mun aminta akan addinin mu, kuma mun bautawa Allah, ba’a cutar da mu, kuma bama jin wani abu da muke ki, lokacin da labarin haka ya isa wurin kuraishawa sai suka yanke shawarar turo mutane biyu zuwa wurin Najjashi masu karfi, kuma su kawo ma najashi kyauta cikin abunda yafi so na kayan makkah, kuma daga cikin abunda ake kawo masa da yafi kauna shi ne fatun dabbobi, sai suka tara masa fatu, kuam basu bar wani waziri ba cikin waziran sa face sai da suka zo masa da kyauta, sai suka aiko Abdullahi dan Abi Rabi’ah Almakhzumy da kuma Amru dan Aas dan wa’il Assahamy da su, kuma suka basu labarin abunda ya wajaba su aikata, sai suka ce musu: ku ba kowane waziri kyaut kafin kuyi wa Najjashi magana game da su, sai ku ba Najjashi nashi kyautan, sai ku neme shi da mika muku su kafin yayi musu magana, sai tace: sai suka fito, sai suka zo wurin najjashi kuma a lokacin muna wurin shi a cikin alherin gida, kuma a wurin mafi alherin makwabci, babu wani waziri face sai da suka bashi kyautar sa kafin suyi wa Najjashi magana sai suka ce wa kowane waziri daga cikin su: hakika su wadancan sun kafurcewa addinin mu ne, kuam suka bi wani karamin yaro dan wauta, sun rabu da addinin mutanen su, su kuma basu shiga cikin adinin ku ba, kuma sun zo da wani addini sabo wanda mu bamu san shi ba haka nan ku, kuma hakika sarki ya turo mu babba a cikin mutanen su, dan ya dawo da su zuwa gare shi, in har mun ma sarki magana game da su to ku bashi shawarar ya mika su zuwa gare mu kuma kada yayi magana da su, saboda mutanen su sunfi su hangen nesa, kuma sunfi sanin abunda suka aibata su da shi, sai suka ce musu: to, sai daga baya suka kaiwa Najjashi tashi kyautar, sai ya karba, sai suka mai magana suka ce masa: ya kai sarki, lallai wasu wawayen yaran mu sun gudu ne suka zo gurin ka, sun rabu da addinin mutanen su, su kuma basu shiga adinin ka ba, kuma sun zo da sabon addini, wanda ko mu ko kai bamu sanshi ba, kuma hakika mun turo maka masu daraja daga cikin mutanen su daga iyayen su da baffannin su da dangin su, dan ka basuu su, dan sun fiso hangen nesa, kuma sunfi sanin irin aibantawan da sukeyi, kuma suka zarde su game da shi, sai tace: kuma babu abunda yafi ba Abdullah bn Arrabi’ah da Amru bn Al’aas haushi irin ac Najjashi zai saurari zancen su, sai waziran da ke tare da shi suka ce: sunyi gaskiya ya kai sarki, mutanen su sunfi su hangen nesa, kuma sunfi sanin aibantawar da suke yi, ka mika su a gare su kawai, sai su maida su zuwa garuruwan su da mutanen su, sai yace: sai Najjashi ya fusata, sai yace: kada Alah ya taimake ni in ban mikasu zuwa gare su ba, kuma ni bazan ha’inci mutanen da suka zo makwabtaka da ni ba kuma suka sauka a gari na ba kuma suka zabeni suka bar kowa, har sai na kirasu inji ta bakin su game da abunda wadannan mutanen ke fada game da su, in har abunda suka fada gaskiya ne ti zan mika su zuwa gare su kuma zan maida ga mutanen su, in kuma ba haka bane to zan kare su daga gare su kuma zan kyautata makwabtaka da su matukar sunyi makwabtaka da ni, sai tace: sai ya turo yana kiran sahabban Manzan Allah (S.A.W), lokacin da dan sakon shi ya zo musu sai suka taru sai sashinsu yace wa sashi: me zamu ce wa wannan mutumin in mun zo wurin sa? Sai sukace: wallahi zamu fadi abunda muka sani ne da kuma abunda Annabin mu ya umarce mu da shi, ko mai zai faru akan haka sai dai ya faru, lokacin da suka zo- kuma lokacin Najjashi ya tara malaman sa na fada sai suka bubbude littattafan su a gaban sa- sai ya tambaye su yace: wane addini ne kuka rabu da mutanen ku saboda shi kuma ku baku shiga cikin addini na ba ko addinin wani a duniya? Sai tace: wanda yayi masa magana shi ne Ja’afar dan Abi dalib, sai yace masa: ya kai sarki, mu mun kasance mutane a jahiliyya muna bautan gumaka ne, kuma muna cin mushe, kuma muna aikata alfasha, kuma muna yanke zumunta, kuma munana makwabtaka, mai karfi na danne marar karfi a cikin mu, mun kasance akan wannan halin har zuwa lokacin da Allah ya aiko mana da wani Manzo a cikin mu mun san dangin sa da gaskiyar sa, da manar sa da kamewar sa, sai ya kiramu zuwa ga Allah dan mu kadaita shi kuma mu bauta masa kuma mu bar abunda muke bautawa mu da iyayen mu koma bayan sa na duwatsu da gumaka, kuma ya umarce mu fadar gaskiya, da tsare amana, da sada zumunci, da kyautata makwabtaka, da kamewa daga aikata haramun, da kashe-kashe, kuma ya hane mu daga alfasha, da fadar karya, da cin dukiyar maraya, da yin kazafi ga kamammun mata, kuma ya umarce mu da bautar Allah shi kadai kada mu hada shi da komai, kuma ya umarce mu da sallah da zakkah da azumi- tace: sai ya lissafa masa al’amuran musulunci- sai muka gaskata shi kuma mukayi imani da shi, kuma muka bishi akan abun da yazo da shi, sai muka bauta wa Allah shi kadai muka daina hada shi da komai, kuma muka haramta abunda ya haramta mana, kuma muka halalt abunda ya halalta mana,sai mutanen mu sukayi ta’addanci akan mu sai suka azabtar da mu, kuma suka fitine mu akan addinin mu, dan su maida mu zuwa ga bautar gumaka mubar bautar Allah, kuma mu cigaba da hallata abunda muke halattawa na munanan ababe, lokacin da suka yi mana fin akrfi kuma suka zalunce mu kuam suka cutar ad mu kuam suka kangemu tsakanin mu da addinin mu, sai muka guda zuwa garin ka, kuma muka zabeka akan wanda ba kaiba, kuma muka kaunaci makwabtaka da kai, kuam muna fatar baza’a zalunce mu ba a wurinka ya kai sarki, sai tace: sai Najjashi yace masa: shin a tare da kai akwai wani abu da Allah ya saukar? Sai Ja’afar yace masa: eh, sai Najjashi yace masa: to ka karanta mun shi, sai ya karanta mai farkon suratu maryam, sai Najjashi yayi kuka har sai da wallahi ya jika gemun sa, sai suka fadawansa suka fashe da kuka har sai da suka jika littattafan su, lokacin da suka ji abunda ya karanta musu, sai Najjashi yace: lallai wannan –wallahi- wannan da abunda Annabi Musa yazo da shi sun fito ne daga mahaskaka daya, sai yace wa wadanda kuraishawa suka aiko, ku koma, na rantse da Allah bazan mika muku su ba har abada kai ko sa da haka ma bazan yi ba, sai Ummu salmah tace: lokacin da suka fito daga wurin sa sai Amru dan Aas yace: wallahi gobe sai na fada masa aibun su sai ya kore su daga wurin sa, tace: sai Abdullahi dan Abirrabi’ah yace masa: kuma yafi tsoran Allahm dayan mu: kada ka aikata, domin su sunada iyan uwa a tare da mu duk da cewa su sun saba mana, sai yace: wallahi sai na bashi labare su suna cewa Annabi Isah bawa ne, tace: sai washe gari yaje wurin sa, sai yace masa: ya kai sarki lalai su na fadan wata magana mai girma game da Annabi Isah dan Maryam, to ka aika dan a tambaye su gameda abunda suke fada akan shi! Tace: sai ya tura yana tambayar su game da shi, tace: ba abunda ya same mu mai tsanani irin wannan abun, sai mutanen suka taru, sai sashin su yace wa sashi: me zaku ce gameda Annabi Isah idan ya tambaye ku gameda shi? Sai sukace: wallahi zamu fadi abunda Allah ne ya fada game da shi, da kuma abunda Amnzanmu yazo da shi, duk abunda zai faru akan haka saida ya faru, lokacin da suka zo wurin sa, sai yace musu: me kuke cewa game da Isah dan Mryam? Sai Ja’afar dan Abi dalib yace masa: muna fadan abunda Annabain mu yazo da shi ne game da shi, shi bawan Allah ne kuma Manzan sa kuma ruhin sa ne kuma kalmarsa ce da ya jefa zuwa ga Maryam mai tsarki, tace: sai Najjashi ya buga hannun s ad kasa sai ya dauko wasu itace , sai yace: kamar yadda wannan icen yake haka Isah dan maryam yake kamar yadda ka fada, sai fadawan sa suka fara guna-guni lokacin da ya fadi abunda yafada! Sai yace: wallahi kun fadi gaskiya, ku tafi dan ku amintattu ne a kasa ta, duk wanda ya cutar da ku to sai an hukunta shi, sannan duk wanda ya zage ku sai na hukunta shi, ni bana bukatar ace inada zinari cike da gonakin habasha alhali ni na cutar wani daya daga cikin ku,ku maida musu da kyaututtukan su bamu da bukatar su, wallahi Allah bai amshi cin hanci daga gare ni ba lokain da ya maida mun da mulki na, kuma matukar yasa mutane sun mun biyaiyya to ni mai za sa bazan masa biyaiyya ba, tace: sai suka fita daga wurin sa suna tababbu an maida musu da abunda suka zo mai da shi, sai muka zauna a wurin sa a mafi alherin gida, tare da mafi alherin makwabci, sai tace: wallahi mu muna kan haka har lokacin da wani ya nemi kwace mai mulkin sa, sai tace: na rantse da Allahbamu taba bakin ciki ba kamar yadda zamuyi bakin ciki in akace wani yai galaba akan Najjashi, sai wani mutum da bai san hakkin mu ba kamar yadda najjashi ya san hakkin mu ba yayi rinjaye, sai tace: sai najjashi ya fita yaki da daddare, sai tace: sai sahabban Manzan Allah (S.A.W) sukace: waye zai fita yaje wurin yakin dan ya kawo mana labari? Sai Zubair dan Auwam yace:ni ne,tace: kuma ya kasance cikin mafi karanci shekarun sauran mutanen , sai tace; sai suka busa masa fata sai ya sanyata a kirjin sa, sai ya tafi cikin dare inda mutanen zasu hadu, sai yaje har ya shiga cikin su, tace: kuma muka dinga yin addu’a ga Najjashi da samun nasara akan makiyan shi, da kuma tabbatar da shi akan garin sa, sai al’amarin habasha ya tabbata a gareshi daga baya, sai muka kasance a wurin sa a mafi alherin masauki har zuwa lokacin da muka koma wurin Manzan Allah (S.A.W) lokacin yana garin makkah.” Musnadul imam Ahmad.

Kuma mai adalci daga cikin ahlul kitbi bayan ya karanta abunda Alkur’ani yake fada game da Annabi Isah da mahaifiyarsa amincin Allah ya tabbata a gare su ya san cewa wannan gaskiya ne daga Allah, kuam hakika kiristocin da suke karbar musulunci sunfi yawa daga wadanda ba su ba kuma suna yadda da kusancen da ke tsakanin su da musulmai, kuam labarin hirqala sarkin ruum tare da Abi Sufyan kafin musuluntar sa shahararriya ce a cikin littattafan tarihi kuma tana nuna yadda kiristoci suka san gaskiyar manzancin Annabi (S.A.W) , Abdulllahi dan Abbas yana cewa: “ lallai abu Sufyan dan Harb ya bashi labari, cewa lallai Hirqala ya aika yana neman shi a cikin wata tawaga ta kuraishawa, lokacin su iyan kasuwa ne a garin sham a cikin lokacin da Manzan Allah (S.A.W) yayi sulhu tsakanin shi da Abu Sufyana da kuma kuraishawa, sai suka zo wurin sa a lokacin suna garin Iniyaa, sai ya kira su zuwa fadar sa, kuma a gefen shi a kwai manyan rumawa, sai ya kirasu kuma ya kira mai masa fassara, sai yace: a cikin ku waye yafi kusancin dangantaka da wannan mutumin da ke raya cewa shi Annabi ne? Sai Abu sufyan yace: sai nace: ni ne na fi su kusa da shi, sai yace: ku kawo shi kusa da ni, kuam suka kusanto da mutanen sa sai suka sanya shi a gaban shi, sai yace wa mai masa fassara: kace musu ni ina tambaya ne game da wannan mutumin, in sun mun karya to kum fada mun cewa karya yake yi, wallahi ba dan kunyar ace nayi karya ba da na sharara masa karya, sai ya zama farkon abunda ya tambaye ni sai yace: yaya dangantakar sa take a cikin ku? Sai nace: shi a cikin mu yana da dangantaka madaukakiya, sai yace: shin ko akwai wanda ya taba yin irin wannan maganar da yayi a cikin ku kafin sa? Sai nace: a’a, sai yace: shin a cikin iyayen sa akwai mai mulki? Nace: a’a, sai yace: mabiyansa masu daraja ne ko kuma masu rauni? Sai nace: masu rauni ne a cikin su, sai yace: suna karuwa ne ko raguwa? Sai nace: karuwa suke yi, sai yace: shin a cikin su akwai masu ridda dan haushin addinin sa bayan ya shiga cikin sa? Nace: a’a, sai yace: shin kuna tuhumar shi da karya kafin ya fadi abunda ya fada? Sai nace: a’a, sai yace: to shin yana yaudara? Sai nace: a’a, mu yanzu haka muna cikin yarjejeniyar zaman lafiya ne da shi bamu san abunda zai aikata a ciki ba, sai yace: ban samu wata kalma ba da zan soke shi da ita ba sai dai wannan, sai yace: to kun yake shi? Sai nace: eh,sai yace: yaya yakin naku da shi ya kasance? Sai nace: yaki tsakanin mu dan zagaye ne, yana cin galaba akan mu mu ma muna cin galaba akan shi, sai yace: da me yake umartar ku? Sai nace: yana cewa ne: ku bautawa Allah shi kadai kuma kada ku hada shi da komai, kuma ku bar abunda iyayen ku ke fada, kuma yana umurtar mu da sallah da azumi da gaskiya da kamewa da sada zumunci, sai yace wa mai fassarar: kace masa: na tambaye ka akan dangantakar sa sai ka ambaci cewa shi a cikin ku yanada dangi masu daraja, hakanan manzanni ana aiko su ne daga mafi darajar dangin mutanen su, kuma na tambaye ka shin a cikin ku akwai wanda ya taba fadar irin wannan maganar, si kace a’a, sai nace da ace wani ya fada irin wannan maganar kafin sa da nace shi mutum ne da yake kwaikwayon abun da wani ya fada kafin sa,, kuma na tambaye ka shin a cikin iyayen sa akwai sarki, sai kace a’a, si nace: da ace akwai sarki a cikiniyayen sa da nace mutum ne da ke san ulkin baban sa, kuma na tambaye ka shin kuna tuhumar shi da karya kafin yace shi annabi ne, sai ka ce a’a, hakika na sani cewa bazai bar karya ba akan mutane amma kuma yayi wa Allah karya, kuma na tambaye ka shin masu daraja ne ke binsa ko kuma masu rauni, sai kace masu rauni ne ke binsa, to kuma su ne mabiya manzanni, kuma na tambaye ka suna karuwa ne ko raguwa, sai kace suna karuwa ne, haka al’amarin imani yake har ya cika, kuma na tambaye ka cewa mutanen sa na ridda daga addinin sa dan jin haushibayan ya shiga, sai kace, a’a, haka ima ni yake har sai zuciya ta cakuda da dandanon sa, kuma na tambaye ka shin yana yaudra, sai kace, a’a to haka manzanni suke basa yaudara, kuam na tambayeka dame yake umurtar ku, sai kace yana umurtar ku da bautar Allah shi kadai kum kada ku hada shi da komai, kuma hana hana ku dag bautar gumaka, kuma yana umartar ku da salllah da gaskiya da kamewa, idan har abunda ka fada gaskiya ne to da sannu zai mallaki in da kafafuwa na suke dinnan, kuma ni hakika nasan zai zo amma ban tunanin cewa a cikin ku bane da ace ni na san cewa zan kai zuwa gare shi da na dau dawainiyar tafiya zuwa gare shi, kuma da zan kai wurin sa to da na wanke kafafun sa sai yace a kawo masa sakon da manzan Allah (S.A.W) ya aiko masa ta hannun Dihya zuwa ga sarkin Ruum Busra, sai ya mika shi zuwa ga Hirqal sai ya karanta shi, sai ga shi a bunda ke cikin sa shi ne: da sunan Allah mai rahama mai jin kai, daga Muhammadbawan Allah kuma manzan sa zuwa ga Hirqala sarkin ruum: aminci ya tabbata ga wanda yabi shiriya, bayan haka, lalai ni ina kiranka da kira na musulunci, ka musulunta sai ka kubuta, Allah zai baka ladarka nin ki biyu, in kuma har ka juya baya to kana da zunubin arisawa a kan ka kuma: {ya ku ma’abota littafi ku taho zuwa ga wata kalma wacce take daidaita tsakanin mu da ku cewa kada mu bautawa kowa sai dai Allah kuma kada mu hada shi da komai kuam kada sashin mu su riki wasu sashi ababen bauta koma bayan Allah in kuma suka juya baya to kuce musu ku shaida lallai mu musulmai ne}. Sai Abu Sufyan yace, lokacin da ya fadi abunda ya fada, kuma ya gama karanta wasikar, sai muryoyi sukayim yawa a inda yake kuam sautuka suka dagu sai muka fita, sai nace wa abokai na lokacin da muka fito: hakika lamari dan baban Kabsha ya girmama, lallai bizandawa suna shakkar ka, ban gushe ba inada yakini cewa zai ci nasara kuma addinin shi zai yadu a nan kusa har sai gashi Allah ya sa mun san shiga musulunci.” Sahihul bukhari.

Haka nan ma lokacin da tawagar kiristocin Najran suka zo wurin manzan Allah (S.A.W) kuma su sitin ne akan abun hawa, al’amarin su na komawa ga mutane sha hudu daga cikin su, dukkan su kuma al’amuran su na komawa ga mutane uku sune mafiya darajar su da kuma jagororin su, su ne: Al aqib da Assayyid da Abu Harisa bn Alqamah, sai suka fara jayaiyya game da al amarin Isah amincin Allah ya tabbata a gareshi, kuma suna raya cewa shi dan Allah ne ko kuma shi ne Allah, kuma su sun kafe akan batar su, bayan da Manzan Allah (S.A.W) ya tsaida musu hujjoji cewa Isah shi bawan Allah ne kuma manzansa ne, sai suka tambaye Annabi me yake fada game da Annabi Isah? Sai yace: shi bawan Allah ne kuma ruhinsa ne da kuma kalmar sa, sai suka ce: a’a shi ne Allah, ya saukao daga mulkin sa sai ya shiga cikin Maryam, sai ya fito daga cikin ta dan ya nuna mana ikon sa da lamarin sa,! Shin ka taba ganin wanda aka halitta ba da uba ba cikin mutane? Sai Allah madaukakai ya saukar da fadar sa: “ lallai misalin Isah a wurin Allah kamar misalin Adam ne ya halicce shi daga turbaya sa’annan sai yace masa kasance sai ya kasance”. haka Allah ya baiyyana al’amarin Annabi Isah amincin Allah ya tabata a gareshi kuma ya kirkiri halittar sa da kuma mahaifiyar sa tun gabanin haka, kuma ya umarci manzan Allah (S.A.W) da yayi mubahala da su in har basu amsa kiran sa ba kuma suka bishi bishi ba, sai Annabi (S.A.W) ya kirasu dan yin mubahala, da cewa shi zai zo da iyalan sa da yaran sa, suma su zo da iyalan su da yaran su, sai su roki Allah madaukaki da ya saukar da azabar sa da tsinuwar sa akan makaryata, sai Annabi (S.A>W) ya zo da Aliyu dan Abi Dalib da Fatimah da Hassan da Hussain Allah ya kara musu yadda, sai yace: “ wadannan su ne iyalai na”. Sai tawagar mutanen Najrana suka yi shawara a tsakanin su: shin su amsa masa ne akan hakan? Sai ra’ayin su ya zo daya akan cewa baza su amsa masa ba saboda sun san cewa in har sukayi mubahala to sun halaka su da yaran su da iyaln su, sai sukace masa: “ ya kai baban Kasim, barmu muyi shawara game da al’amarin mu, sai muzo maka da labarin abunda muke so mu aikata cikin abunda ka gaiyyace mu zuwa gare shi”. Sai suka tafi suka barshi, sai suka kebe da Aqib, kuma shi ne yafi kowa hangen nesa a cikin su, sai suka ce: “ ya kai bawan Annabi Isah, mai kake gani?” sai yace:” wallahi ya ku taran kiristoci hakika kun san cewa lallai Muhammad Annabi ne da aka aiko, kuma hakika yazo muku da gaskiya game da labarin Annabi Isah, kuma ku kun san cewa babu wasu mutane da suka taba tofin Allah tsine tsakanin su da Annabin su kuma manyan su su rayu, kuam kananan su baza su girma ba, kuma wannan shi ne karshen ku in har kuka aikata, to idan har kuka ki yadda sai dai ku dauwwama akan addinin ku da kuma dogewa akan abunda kuke fada gameda Isah, to kuyi bankwana da Muhammad sai ku koma garin ku”. Sai suka zo wurin manzan Allah (S.A.W) sai suka ce: ya kai baban Qasim, munyi shawarar baza muyi tofin Allah tsine da kai ba, kuma mu zamu barka akan addinin ka zamu koma da addinin mu, sai dai muna so ka tura wani mutum daga cikin sahabban ka wanda ka yardar mana da shi, wanda zai yi hukunci tsakanin mu cikin abunda muke sabani na dukiyoyin mu, domin ku yaddar du ne a wurin mu.

 

 

 

SIFFOFIN MABIYA ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Allah ya siffanta mabiya Annabi Isah a cikin Alkur’ani na gaskiya da rangwame da tausayi da san addini da ruko da shi, Allah madaukaki yace: sannan muka biyo da manzannin mu a bayan su kuma muka biyu da Isah dan Maryam kuma muka bashi Injila kuma muka sanya rangwame a cikin zukatan wadanda suka bishi da tausayi da kuma rahabaniyanci wanda suka kirkire shi wanda bamu wajabta shi akan su ba sunyi haka ne badan komai ba sai dan neman yaddar Allah amma basu kula da ita ba hakikanin kula sai muka baiwa wadanda sukayi imani a cikin su ladar su kuma da yawa daga cikin su fasikai ne (27)” suratul Hadeed, aya ta: 27.

Kamar yadda Allah madaukakai ya siffantasu a cikin Alkur’ani cewa su suna cikin wadanda sukayi gaggawar kamar gaskiya da kuma taimakon Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi wajen yada da’awar sa, sai Allah ya umarci musulmai da su zama irin mataimaka Annabi Isah kua suyi gaggawa wajen taimakon Annabi Muhammad (S.A.W) kua su agaza masa wajan yada da’awar sa, sai ya neme su da su da yin koyi da su a cikin wadannan kyawawan halayen, Allah madaukaki yace: “ ya ku wadanda sukayi imani ku zamo mataimaka Allah kamar yadda Isah dan Maryam yace wa hawariyawa waye zai taimaki Allah sai hawariyawa sukace mu ne mataimaka Allah sai wasu jama’a sukayi imani daga cikin mutanen bani isra’ila wasu kuma suka kafurta sai muka karfafa wadanda sukay imani akan makiyan su sai suka zama masu cin nasara (14)” suratus Saffi, aya ta: 14.

Sannan Allah ya siffan su da cewa sune mafi kusa da kaunar musulmai cikin mutane fiye da wanda ba su ba, saboda Annabi Muhammad (S.A.W) ya zo ne bayan Annabin su, lokacin gajere ne ba kamar yadda lokacin yake ne ba tsakanin Annabi Muhammad (S>A.W) da kuma Annabi Musa amincin Allah ya tabbat a agare shi, wannan ne yasa yahudawa sukafi kiyaiyya ga musulmai, idan har yahudawa suna iyaiyya da kiristoci duk da cewa Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi zamanin shi na kusa da na Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi kuma yana cikin dangin mutanen bani isra’ila, to ya kake tunani idan har zamani ya tsawaita kuma shi Annabi Muhammad (S.A.W) ya fito ne daga tsatsan Annabi Ibrahim amma ta bangaren dansa Annabi Isma’il amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya!! Kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ lallai zaka samu cewa mafiya tsananin gaba ga wadanda sukayi imani cikin mutane sune yahudawa da wadanda suke shirka kuma lallai zaka samu mafi kusa da kauna ga wadanda sukayi imani su ne wadanda sukace mu kiristoci ne saboda kuwa a cikin su akwai masu bauta da malamai kuma lallai su basa girman kai (82) kuma idan suka ji abun da aka saukar akan Manzo sai kaga idanun su suna kwarara da hawaye saboda abunda suka sani na gaskiya suna cewa ya ubangijin mu unyi imani ka rubuta mu cikinmasu shaida (83) kuma saboda me baza muyi imani da Allah ba da kuma abunda ya zo mana na gaskiya ba kuma muna kwadayin ubangijin mu ya shigar ad mu cikin mutane salihai (84) sai Allah ya saka musu da abunda suka fada da aljannah wacce koramu ke gudana a karkashin ta suna masu dauwwama a cikin ta kuma wannan shi ne sakamakon masu kyautatawa (85)” suratul Ma’idah, aya ta: 82-85.

 

 

 

DAUKE ANNABI ISAH ZUWA SAMA DA CEWA BA’A RATAYE SHI BA

Hakika yahudawa sun saba da karyata Annabwansu cikin abunda ya gabata da kuma kashe su, kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: “ kuma hakika mun ba Musa littafi kuma muka biyo da Manzanni a bayan sa kuma mun ba Isah dan Maryam hujjoji kuma mun karfafe shi da mala’ika Jibrilu to yanzu duk lokacin da wani manzo yazo muku da abunda rayukan ku basa kauna sai kuyi girman kai sai kuke karyata wasu kma kuke kashe wasu (87)” suratul bakara, aya ta: 87.

Saboda haka ne am sun yi yunkurin kashe Annabi Isah sosai sai dai Allah ya kare shi daga gare su, kuma lallai aqidar musulmai game da Annabi Isah dan Maryam ita cewa shi bai mutu ba kuma ba’a kashe shi ba kuma ba’a rataye shi ba sai dai shi an daga shi zuwa sama ne da ransa da jikin sa kuma lallai shi zai dawo kafin tashin alkiyama kuma ahlul kitabi zasu yi imani da shi dukkan su, kakamr yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “ saboda warware alkawuran su da kafurcewarsu da ayoyin Allah da kuma kisan su ga Annabawa ba tare ad hakki ba da kuma cewar su zukatan mu sun rufe a’a Allah ne ya yi rufi akan su saboda kafurcin su basa imani sai iyan kadan (155) kuma da kafurcin su da kuma abunda suke fada gameda maryam na karya mai girma (156) da kuma fadar su cewa lallai mu mun kashe Isah dan Maryam manzan Allah su basu kashe shi ba kuma basu rataye shi ba sai dai an kamanta shi ne a gare su kuma lallai wadanda sukayi sabani a game da shi to suna cikin shakka akan shi basu ad wani ilimi sai dai bin zato kuma su basu kashe shi ba da gaske (157) sai dai Allah ya dauke shi zuwa gare shi kuma Allah ya kasance mabuwayi mai hikima (158) kuma babu wani daga cikin ahlul kitabi face sai yayi imani da shi kafin mutuwar sa kuma ranar alkiyama zai zama mai shaida a kan su (159)” suratun Nisa’i, aya ta: 155-159.

Ibn Abbas Allah ya kara masa yadda yana cewa:” lokacin da Allah ya so dauke Annabi Isah zuwa sama ya fito wurin mutanen sa kuma a cikin gidan akwai mutane goma sha daya daga cikin hawariyawa, wato sai ya fito wurin su ta wata kofa daga cikin gidan, kuma kansa yana digarda ruwa, sai yace: lallai a cikin ku akwai wanda zai kafurce mun sau goma sha biyu bayan yayimimani da ni, sai yace: waye a cikin ku zai yadda a daura mai kamat asai a kashe shi a maimako na si ya kasance tare da ni a daraja ta? sai wani matashi da yafi su kankantan she karu ya mike, sai yace masa: zauna, sai kara maimaita musu abunda ya fada, sai wannan matashin ya mike, sai yace: zauna, sai ya kara maimaita musu abunda ya ce, sai wannan matashin ya mike, sai yace: ni ne, sai yace: to shi kenan kai ne din, sai aka saukar mai da kammanin Annabi Isah sai aka dauke Isah ta wani gefe na gidan zuwa sama, yace: sai gashi yahudawa sun zo neman shi, sai suka kama wanda yayi kama da shi sai suka kashe shi sai suka rataye shi sai wasun su suka kafurce masa sau sha biyu bayan sunyi imani da shi, sai suka rabu kashi uku, sai wasu sukace: Allah ya kasance a cikin mu har zuwa wani lokaci sai ya koma zuwa sama, wadannan su ne Ya’aqubiyya, sai wasu kuma suka ce: shi dan Allah ne a cikin mu ya zauna na wani lokaci a cikin mu sai Allah ya dauke shi zuwa saama, wadannan sune Annasdoriyyah, sai wasu kuma suka ce: shi a cikin mu bawan Allah ne kuma Manzan sa ya zauna na wani lokaci sai Allah ya dauke shim zuwa sama, wadannan su ne musulmai, sai kungiyoyinnan biyu sukayi taimakekeniya suak hade kai akan musulmai, sai suka kashe su, musulunci bai gushe ba yana boye cikin daidaikun mutane ahr zuwa lokacin da Allah ya aiko da Annabi Muhammad (S.A.W), sai Ibn Abbas yace: kuma wannan shi ne fadar Allah madaukaki { sai muka taimaki wadanda sukayi imani akan makiyan su sai suka wayi gari suna masu nasara }.” Al bidayatu wannihaya ta Ibn kaseer.

Allah madaukaki yana cewa yana mai baiyyana hakikanin dauke Annabi Isah zuwa sama: “ sun kulla makirci kuma Allah ya na maida musu da kullin su na makirci kuma Allah shi ne mafi alheri daga masu makirci (54) lokacin da Allah yace ya kai Isah lallai ni zan kashe ka kuma zan dauke ka zuwa wuri na kuma zan tsarkake ka daga wadanda suka kafurta kuam zan sanya wadanda suka bika sama da wadanda suka kafurta har zuwa ranar alkiyama sannan wurina za’a maida ku sai inyi muku hukunci tsakanin ku cikinabunda kuke sabani a cikinsa (55) amma wadanda suka kafurta to zan azabtar da su azaba mai tsanani a cikin duniya da lahira kuma basu da mataimaka (56) amma kuma wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiyyuka na kwarai sai a cika musu ladan su kuma Allah baya san azzalumai 957)” suratu Ali imaran, aya ta: 54-57.

Lallai aqidar cewa an kashe Annabi Isah da rataye shi da fansa a cikin kiristanci yana daga cikin abunda yahudawa suka shigar da shi da kiristoci da masu bautar gumaka da mabiyan su a cikin addinin Annabi isah dan maryam amincin Allah ya tabbata a gare shi,, saboda suna raya cewa wai Allah ya bada yaransa da a kashe shi da rataye shi dan ya ceci mutanebabu laifi akan kowa ya aikata baunda yaga dama hakika Annabi Isah ya dauke mai dukkan zunubai, babaumakawa wannan na daga cikin abunda ke kawo barna baya gyara mutane ta yaya rayuwar mutane zata inganta ba tare da wani tsari wanda suke tafiya a kan sa ba da kuma iyakoki da suke tsayawa a wurin su, ya za’a hada wannan da tsarin ubangiji wanda musulunci yazo da shi kuam ya baiyyana cewa lallai kowace rai tana rataye nwe da abunda ta aikata kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: “ ko wace rai tana rataye ne da abunda ta aikata (38)” suratul Muddassir, aya ta: 38.

Sai dai ita aqidar kisa da rataya da fansa a cikin addinin kiristanci yana daga fadin magana akan Allah ba tare da ilimi ba da kuma karya a gare shi kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ azaba ta tabbata ga wadanda suke rubuta littafi da hannayen su sai su dinga cewa wannan daga Allah ne da su dinga siyar da su da iyan kudade kadan tir da su saboda abunda hannayen su suka rubuta kuma tir da su saboda abunda suke aikatawa (79)” suratul Bakara, aya ta: 79.

Kuma hakika Allah ya dauki alkwari akan bani isra’ila da cewa suyi imani da abunda Annabi Isah yazo da shi kuma suyi aiki da shi kuma suyi imani da abunda yayi bushara da shi na cewa za’a aiko da wani manzo da zai zo a bayan sa sai dai su sun canja kuma sun juya sannan kuma sunyim sabani saisuka bijire kuma suka karyata sai Allah yayi musu ukuba da jefa gaba da kikaiyya tsakanin su a nan duniya da kuma azaba a lahira kamar yadda Allah madaukaki yace: “ kuma daga cikin wadanda suka ce lallai mu kiristoci ne mun riki alkawari daga gare su sai suka manta da rabanda aka tunatar da su shi sai muka jefa gaba da kiyaiyya a tsakanin su har zuwa ranar alkiyama kuma da sannu Allah zai basu labarin abunda suka kasance suna aikatawa (14)” suratul Ma’idah, aya ta:14.

 

 

 

DAWOWAR ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI

Yana daga cikin tabbatacciyar akidar musulmai cewa lallai Annabi Isah amincin Allh ya tabbata a gare shi zai dawo a karshen zamani zuwa kasa lokacin da ilimi zaiyi karanci kuma jahilci zai yawaita kuma mutane zasuyi nesa daga addini kuma kasa zata cika da zalunci, dan shi amincin Allah ya tabbata a gare shi ya zama shi ne mai ceto mutane daga abunda suke ciki na dagawa sai ya cikata da adlci da haske kuma zaman lafiya zai mamaye ko ina da kwanciyar hankali afadin duniya, kuma hukuncin musulunci zai yi nasara Annabi Isah zai yi hukunci da shi akan mutanen duniya baki daya zai karya gumaka wanda ke nuni a aikace akan bacin akidun kiristoci akan cewa an rataye shi ne, kuma zai kashe aladu dan yayi nuni akan bacin akidar kiristoci a game da halatta shi, sai albarka ta yawaita a zamanin sa kuma dukiya su kwararo ta ko ina kuma zukatan mutane za su cika da kana’a a zamanin sa da tsantsane har mutane zasu rasa wanda zai karbi sadaka daga wurin su, kamar yadda manzan Allah 9S.A.W) ya baiyyana haka da fadar sa: “ na rantse da wanda raina ke hannun sa, lallai Isah dan Maryam ya kusa sauka a cikin ku yana maihukunci mai adalci, sai ya karya gumaka, kuam ya kashe aladu, kuma ya sauke jiziya, kuma dukiya ta yawaita har ma babu wanda zai karba, har sujada daya zata fi alheri fiye da duniya da abunda ke cikin ta,” bukari da muslim ne suka ruwaito.

Kuma wanna dukkan sa shimfida ne na tashin alkiyama waddan a abyanta mutane ke barin rayuwar duniya mataki na aiki zuwa matakin lahira matakin sakamako da kuma rayuwa madauwwamiya ta hanya dauwama a gidan aljannah ko kuma a cikin wuta ta yadda ake cika wa kowace rai sakamakon abunda ta aikata mai rabo shi ne wanda yayi shiri dan zuwan wannan ranar kuma yayi aiki dan ita ta hanyar aikata kyawawan aiyuka da kuma nisantar munanan aiyuka da kuma bin manzanni, Allah madaukaki yana cewa: “ ranar da zamu kira kowane mutane da jagoran su to duk wanda aka ba littafin sa da daman sa to wadannan suna karanta littafin su kuma ba’a zaluntar su daidai da kwayar zarra (71) kuma duk wanda ya kasance makaho a nan duniya to shi a lahira makaho ne kuma yafi mace hanya (72)” suratul Isra’i, aya ta: 71-72.

 

 

RUFEWA

Lallai Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi shi ne manzo guda daya da mutane sukayi sabani mai tsanani akan sa, daga cikin yahudawa akwai masu zagin sa kuma suka zagi shi da kalmomi mafi girma na zagi kuma suka siffanta shi da mafi munin siffa kma mafi kazanta, kuma daga cikin kiristoci akwai wadanda suka wuce iyaka wurin girmama shi kuma suka raya cewa shi Allah ne da kuma cewa dan Allah ne da kuma cewa shi daya ne cikin uku, kuma yana daga falalar Allah akan al’ummar musulmai- kuma wannan falalar Allah ce yana bada ita ga wanda ya so- sai Allah ya shiryar da ita zuwa gaskiya gameda hakikanin lamari akan Annabi Isah matsaya ta tsakiya a tsakanin wadannan alummu biyu da suka gabata, sai suka girmamashi da tsarkake shi daga maganar yahudawa, kuma basu wuce iyaka ba akan shi irin na kiristoci, kuma abunda suke cewa game da shi shi ne shi bawan Allah ne kuma manzan sa kamar yadda Allah ay saukar da haka ga manzan sa a cikin Alkur’ani mai girma.

Wannan itace hakikanin Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda mu musulmai muke sansa kuma muna neman kusance zuwa ga Allah da san sa, shi manzo ne mai karamci daga tsatsan Annabawa da manzanni masu daraja kuma muna kudar cewa rashin kaunar sa da imani da shi da kuma sakon sa fita ne daga musulunci kuma karyatawa ne da Alkur’ani da kuma fiyaiyyen halitta Muhammad (S.A.W) kuma yana daga cikinabunda ke sa a dauwwama a cikin wuta.

Kuma wannan shi ne hakikanin zance game da Maryam amincin Allah ya tabbata a gare ta kamar yadda Alkur’ani mai girma ya baiyyana kuma Manzan Allah (S.A.W) ya baiya cewa ita mai tsarki ce mai kame wa ce mai tsafta ce barrantacciya ce daga dukann barna da alfasha daga tsatsan gida mai daraja, kuam lallai ni inada yaki ni cea dukkan mutum ami adalci da ya karanta abunda Alkur’ani yazo da shi game ad wannan Annabin mai daraja zai tabbar da cewa wannan shi ne gaskiyar da ya kamata yabi, kuma inada yakini akan cewa babu wani littafi ko kuma addini da ya girmama kuma ya daukaka darajar wannan mutanen gidan da wannan manzan kamar musulunci, ta yadda ya aje shi a matsayin da ya dace da shi, shi ne matsayin bauta ga Allah wadda Allah ya sharrafa shi da ita kamar yadda ya sharrafa wasun sa daga cikin Annabawa, kuma hakika dukan Annbawa sun dan dana abunda suka dandana daga mutanen su – a hanyar tabbatar da wannan bautar- na bijirewa da karyatawa, daga cikin su akwai wanda aka kashe kuma daga cikin su akwai wanda aka azabtar kuma daga cikin su kwai wanda ak rufe a kurkuku, hakan kuwa saboda sun zo da abunda ke sabawa abubuwa da yawa da suke aikatawa na ibadu da kudurce-kudurce na karya da tsarin zamantakewa na zalunci kuma suna dankwafar da mafi yawa daga cikin san rai na shaidan karkatattu, Annabi Nuhu amincin Allah ya tabbata a gare shi ya dandani cutarwa daga mutanen sa har sawan shekaru dari tara da hamsisai yayi hakuri kuma ya nemi ladan sa a wurin Allah sai Allah ya tsiratar da shi kuma ya hallaka mutanen sa da suka kafurta da ruwan dufana, shi kuma Annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi mutanen sa sun karyata shi suka jefa shi cikin wuta sai Allah ya maidata sanyi da aminci a gare shi kuma Allah ya halaka makiyan sa kuam ya bashi nasara a kan su, shi kuma Annnabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi Fir’auna ya karyata shi kuma yanata kulla masa makirci dan ya kashe shi sai Allah ya tsiratar da shi kuma ya taimake shi kuma ya halakar da kuma nutsar da makiyin shi da rundunar sa, shi kuma Annabi Isah maincin Allah ya tabbata a agre shi shima yana cikin jerin wadannan manzannin wadanda suka hadu da karyatawa daga bani isra’ila da kuma fadan da bunda yake shi kubutanci ne akan sa, na cewa shi dan zina ne kuma mahaifiyar shi mazinaciya ce- Allah ya tsare shi kuma ya tsare ta daga haka- duk wannan na daga cikin yunkuri na kange mutane daga bin sa kamar yadda sukayi kokarin kashe shi da gangan sai Allah ya tsiraar da shi kuma ya dauke shi zuwa sama, shi ma kuma Annabi Muhammad (S.A.W) ya hadu da karyatawa daga mutanen sa mushirikai da kuma da yahawa daga cikin yahudawa da kiristoci da izgili da raini da yunkirin kisa sai ya tabbata sai kuma Allah ya taimake shi ya bashi nasa sai yayi rijaye akan makiyan shi kuma ya daga addinin sa ya daura shi akan sauran addinai dukan su koda kuwa kafurai basa so.

Lallai annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi shi ba kamar yadda kiristoci suke rayawa bane cewa shi Allah ne ko kuma shi dan Allah ne ko kuma shi Allah daya ne cikin uku- Allah ya daukaka kuma ya tsarkaka daga dukkanhakan- saboda da ace shi kamar yadda suke fada ne to da zai iya saukar da imani a zukatan mutane dukakn su sau suyi imani matukar shi yana da wannan darajar, kuma matukar wannan shi ne abunda ya ke kauna kuma yake fata saboda ya zai kasa tabbatar da haka?! Haka nan ma da ace shi ne Allah to wannan waen irin Allah ne da bazai iya kare kansa ba kuma ya bawa halittu dama akan kashe shi?! Kuma da ace shi ne dan Allah to ya za ace Allah ya yadda a kashe dan sa- Allah ya tsarkaka?

Lallai Allah madaukaki yayi mana ni’imar hankali kuma ya sanya shi ne mai banmanta tsakanin mu da wanda ba mu ba cikin halittu, to muyi amfani da wannan hankalin kuma muyi tunani dan gaskiya ta baiyyana a gare mu daga karya da kuma ingantacce da wanda ba ingantacce ba, babu abunda ke sabawa fidira ingantacciya a cikin addinin Annabawa dukkan su da kuma lafiyaiyyen hankali, duk abunda yake irin wannan to shigo da shi akayi cikin addinin Allah kuma yana daga cikin samun damar da shaidan yayi akan iyan Adam dan ya karkaatr da su daga hanya madaidaiciya kuma ya kai su zuwa hanyar bata, to ka kasance ya kai mai karatu mai daraja cikin wadanda idan sun karanta zasuyi tunani kuma idan yayi tunani zai gwama kuma idan ya gwama sai yabi magana mai kyau dan ka zama cikin wanda Allah ya yabe su da fadar sa: “ kuma wadanda suka nesanci dagutu dan kar su bauta musu kuma suka maida al’amuran ga Allah to suna da ajannh to kayi wa bayi bushara (17) wadanda suke jin zance sai su bi mafi kyawon shi wadannan su ne wadanda Allah ya shiryar da su kuam wadannan su ne ma’abota hankula (18)” suratuz Zumar, aya ta: 17-18.

Kira ne da muke fuskantar da shi ga wanda ba musulmai ba dukkan su kuma zuwa ga ahlul kitabi a kebe kira na gaskiya da fuskantarwa na ubangiji wanda Annabi Muhammad 9S.A.W) ya kira wanda suka saba masa da ita tun tuni a baya kuma ya wayi gari alama ne na mabiyan sa a bayan sa, inda Allah madaukaki yace: kace yaku ma’abota littafi ku taho zuwa ga wata kalma wacce take daidaita tsakanin mu da ku cewa kada mu bauta wa kowa sai dai Allah kuma kada mu hada shi da komai kuma kada sashin mu su riki wasu sashi ababen bauta koma bayan Allah idan suka juya baya to kuce musu ku shaida lallai mu musulmai ne (64)” suratu Ali imaran, aya ta: 64.

Hakika yahudawa da kiristoci sun kasance suna bushara da zuwan wani manzo na karshe daga littattafan su kuma tunanin su she ne zai kasance ne daga bani isra’ila kuma sun san cewa zai fito ne ta bangaren madinah wacce ake kiranta da suna Yasrib a wancan lokacin, saboda haka ne suka taru a cikin madinah da kewayenta lokacin da sabanin abunda suke tsammani ya baiyyana da kuma abunda suke tunani da aiko AnnabiMuhammad (S.A.W), sai suka kafurce kuma suka juya baya, kuma Allh ya wadata da barin su kuma Allah yafi sanin inda yake sanya manzancin sa, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “ lokacin da wani littafi yazo musu daga Allah yana gaskata abunda ke tare da su kuma su kafin haka sun kasance suna bada labarin shi ga wanda suka kafurta lokacin da abunda suka sani yazo musu sai suka kafurce da shi to tsinuwar Allah ta tabbata a kan kafurai (89) tur da abunda suka siyawa kansu na su kafurce wa abunda Allah ya saukar dan haushin Allah ya saukar da falalar shi akan wanda ya so cikin bayin sa sai suka koma da fushi akan fushi kuma kafurai suna da azaba ta wulakanci (90)” suratul Bakara, aya ta: 89-90.

Lallai da’awar da musulmai suke dauke da ita kuma suke kokarin isar da ita ga wasun su ta fito ne ta bangaren san su ga alheri a gare su, alherin duniya ko wane iri ne saboda shi musulmi yana cikin abunda ke amfanar sa akwai tabbar abunda ke kewayen sa dan iya isar da sakon ubangijin sa da kuma kokarin aiki da tabbatar da karantarwar sa wadanda suke samar da al’umma mai falala, ko kuma alheri na lahira ta hanyar abunda suke isar da shi na karantarwar ta Allah wadda zata zamo sababain shigar su aljannah da kuam tsamar da su daga wuta, kuma mai motsa wannan fuskantarwa ta ubangiji wadda ke umurtar su da haka, hakika Allah madaukaki yace: “ kuma a samu mutane daga cikin ku wadanda suke kira zuwa ga alheri kuma suna umarni da kyakkyawa kuma suna hani daga mummuna kuma wadannan su ne masu babban rabo (104)” suratu Ali imrana, aya ta: 104.

Kuma karshen burina shi ne wanna dan karamin littafin ya zama farkon binciki ne da da zai kre makauniyar biyaiyya na tunani ga wanda ke da tsananin bukata ta sanin ingantacciyar hanya, kuma fata na ta gaskiya ga dukkan mutum da ya isa zuwa ga jin dadi na gaske wadda imani da Allah ne tushen sa, inda Allha yabaiyyana haka da fadar sa: “ wadanda sukayi imani kuma zukatan su ke natuwa da ambatan Allah ku saurara da ambatan Allah ne zukata ke natsuwa (28)” suratur ra’ad, aya ta: 28.

Wadda a mtsayi na na musulmi nake kudurta cewa mutum bazai ni’imtu da ita ba sai a karkashin addini mai girma wanda ke baiwa kowane mai hakki hakkin sa a cikin abunda ya shafi mu’amalolin mutane ko kuma na jiki da na ruhi kuma wannan dukkan sa ina samunsa a cikin addinin musulunci da yawa, lallai abunda ke samun mu na bacin rai da damuwar rai a cikin al’ummar da ba musulmai ba duk da irin abunda suka kai na jindadin rayuwa da ci gaba,ya samu ne saboda nesanci da sukayi da imani da Allah da ingantaccen imani wanda aka gina shi akan tauhidi, kuma rashin imani da Allah shi ne tushen tabewa da rashin rabo, kuma Allah mai girma yayi gaskiya inda yace: “ kuma duk wanda ya juya baya daga ambato na to lallai shi yana da wata irin rayuwa ta kunci kuma zamu tada shi ranar alkiyama yana makaho (124) sai yace ya ubangiji saboda me ka tadani makaho alhali da ina gani (125) sai yace haka nan ayoyin mu suka zo maka sai ka manta da su kaima haka yau za’a manta da kai (126)” suratu Daha, aya ta: 124.

Lallai nassoshin Alkur’ani mai girma sun zo a baiyyane wajen nuni akan cewa lallai addini a wajan Allah daya ne kuma lallai Allah yana aiko da Annabawa amincin Allah ay tabbata a gare su sashin su na cika sashi, tun daga Nuhu amincin Allah ya tabbata a gre shi har zuwa ga Annabi Muhammad (S.A.W) kamar yadda Annabi Muhammad (S.A.W) ya baiyyana haka da fadar sa: lallai misali na da misalin Annabawan da suka gabace ni, kamar mutum ne da ya gina gida, sai ya kyautata shi kkuma ya kawata shi sai ya bar wani gefe ba bulo, sai mutane suke zagaye gidan kuma suna mamakin sa kuma suke cea: ai da ka dora wannan bulon, sai yace: ni ne bulo din, kuma ni ne karshen Annabawa.” Sahihul bukari.

Kuma karshen kiranmu shi ne cewa godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai

Kuma Allah yayi amincin ga Manzannin sa baki daya.

 

www.islamland.com

 

 

 

[1] - hanyar abinci.

[2]- Ahmad daya ne daga cikin sunayen Annabi Muhammad S.A.W.