SHIN LOKACI BAIYI BA DA ZAKA ZAMA MUSULMI???

SHIN LOKACI BAIYI BA DA ZAKA ZAMA MUSULMI???

SHIN LOKACI BAIYI BA DA ZAKA ZAMA MUSULMI???
ألم يأن لك أن تكون مسلما؟ بلغة الهوسا

 

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha
د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة

Fassara
European Islamic Research Center (EIRC)
المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية
& Faiz Shuaib Adam
Wanda ya bibiyi fassara
Hashim Muhammad Sani
 

www.islamland.com

 

SHIN LOKACI BAIYI BA DA ZAKA ZAMA MUSULMI???
da sunan allah mai rahama mai jin kai
godiya ta tabbata ga allah, tsira da amincin allah su tabbata ga annabi muhammad da iyalansa da sahabbanshi.
DAN UWANA MAKARANCI:
acikin wannan littafin na yi kokarin tattara wasu daga cikin abubuwan da musulunci ya kebanta dasu a takaice domin ya zama mabudi don yin bincike da kuma da zurfafa tinanin masu bincike akan hakikanin, wadda kuma ya tabbata cewa da masu adalci daga cikin wadanda ba musulmai ba da ya zama sanadiyyar musuluntarsu tare da wasu sharuddah kaman hakan:
= niyya ta gaskiya domin neman gaskiya da saninta da kuma bin ta, ba wai farautar laifuffuka ba da kuma bincikensu, domin lallai allah madaukakin sarki ya jibinci shiryar da wanda yake neman gaskiya domin ya shiryu, hakan zai zama ne ta hanyar samun jin dadi da budewar kirji da kuma sawwake hanyoyin da zasu kaishi ga hakan, allah yace; duk wanda allah yake son ya shiryar dashi sai ya budemai kirjinshi ga musulunci, wanda kuma yayi niyyar batar dashi saiya sanya kunci akirjinshi da kuma laifi, ya zama kaman wanda zai tashi zuwa sama, hakane allah yake sanya datti a zukatan wadanda basuyi imani ba.
= rokon allah na gaskiya gareshi shi kadai, da kuma maimaita hakan a gareshi domin sanin gaskiya da samun dacewa wajen ansan aikin, allah madaukakin sarki yana cewa: mutane sun kasance a farkonsu alumma ce guda daya, sai allah ya aiko annabawa da manzanni suna masu bushara da kuma gargadi kuma ya saukar da littafi tare dasu da gaskiya domin suyi hukunci tsakanin mutane cikin abinda skayi sabania cikinshi, ba abinda ya sanyasu sabani face abinda aka basu na daga littafi domin kiyayya ko hassada a tsakaninsu, sai allah ya shiryar da wadanda sukayi imani daga cikinsu bisa ga abinda sukayi sabani acikinshi daga bin gaskiya tare da izininshi, kuma allah yana shiryar da wanda yaso zuwa ga hanya madaidaiciya, suratul baqara aya ta 213.
= barin son kai na addini da makahuwar biyayya ga addinin iyaye da kakanni wanda aka ginashi ba akan ilimi ba da lura, da karanta littafan koyar da addinin musulunci da hankali da kuma ilimi ba tare da wani raayi ba na addini da wasu hanyoyi na tinani wadda aka gada, allah yana cewa; idan aka ce musu su bi abinda allah ya saukar sai suce mu dai zamubi abinda muka samu iyayanmu akanshi ne, ko dai ana tinanin iyayansu basa hankaltar komai ne ko kuma basu da shiriya. suratul baqara aya ta 170.
dole ne mai bincike wanda ba musulmi ba yasan cewa lallai musulunci ba na larabawa bane kawai, shidai na duka duniya ne gaba daya, babu bangaranci a musulunci, duk wanda yayi imani dahsi kuma yayi aiki to shine musulmi koda kuwa ya kasance a karshen duniya yake, ko ya zama farar fata ne ko baqi, haka kuma duk wanda baiyi aiki dashi ba kuma baiyi imani dashi ba bai zama muslmi ba koda kuwa ya kasance daga tsatson annabin musulunci annabi muhammada tsira da amincin allah su tabbata a garesghi, sahabi bilal dan rabah allah ya yarda dashi ya kasance mai kiran sallah ga annabi muhammad allah ya karin tsira a gareshi kuma bawa ne dan qasar habasha, shi kuma suhaib mutumi qasar room ne, shi kuma salman dan qasar faris ne, kaman yadda musulunci bai takaitu ga garin makkah, madina da yankin larabawa ba kawai, ko wace daula inta gina muslunci to sunanta daular musulunci koda kuwa ta kasance a qasashen afirka.
= daukan musulunci da yin hukunci acikinshi itace hanya ko sharia cikakkiya amman ba daukanshi ko hukunci akanshi aiki ne na mutum daya ba ko wani gari da ba wajibinsu bane, akwai qasashe da dama da kuma bangarori na addinai wadanda suke jingina kansu da musulunci amman a hakika musulunci yayi hannun riga dasu, da kuma wadda take da tasiri mai girman gaske wajen jirkita musulunci ingantacce da kuma koran wdanda ba musulmai ba daga gareshi da kuma toshe hanyoyin isa zuwa gareshi saboda dalilin wasu ayyuka ko abubuwan da aka qudurce da kuma ayyuka kodai na magana ko kuma na aiki da suke aikatawa ta fadi a baki amman zukatansu ba haka bane, kuma hankali ingantacce baya daukansu, kuma halitta mai inganci tana kin hakan da kuma zamantakewar zamani kuma su alakantata da musulunci, akan hakane ya kamata asan cewa duk wani abin qudurcewa ko aikin da yake cin karo da ingantaccen hankali da cikakkiyar halittar dan adam kuma dandano madaukaki ya ki wannan abun kuma musulmia basuyi ittifaqi akan wannan abun ba to tabbas wannan abun ba musulunci bane, domin musulunci kadaita allah ne kawai ba abinda ke cudanya dashi na daga shirka, da kuma bautar da babu riya acikinta, da dabiun da babu fitsara acikinsu, da tsari na rayuwa wanda babu batanci acikinshi, da bayanin da babu rudu acikinshi, saidai musulmai suna shan baban wajen ansan abu ko qinshi, wani yanayi ne kadan wani kuma da yawa, allah yayi bayani haka cikin qurani inda yake cewa; sannan muka gadar da littafinmu ga wadanda muka zaba cikin bayinmu, daga cikinsu akwai mai zalintar kanshi, akwai kuma mai kyakyywara niyya sannan akwai mai rigegeniya da alkhair da izinin allah, wannan shine rabo mai girma, suratul fadir aya ta 32.
= daukan ilikmomin addini ta hanyar bincike da neman gaskiya ba ta hanyar sadar da zumunta ba wadda take ba mai adalci ba, ko kuma wasu mutane da masu kama dasu, hakan ya zama wajibi ga mai neman sanin musulunci ya nemeshi ta hanyoyinshi ingantattu da kuma inda aka samoshi na asali wato qurani mai girma da hadisai ingatattu sannan kuma abinda alummah suka tafi akanshi a karkashin fadin annabi; na bar muku abubuwa biyu indai kukayi riko dasu bazaku bace ba, littafin allah ya sunnata wato hadisanshi ingantattu’ albani yace hadisi ne mai kyau.
= ko wani mutum yana neman cikakken abu mai kyau dangane da alamuranshi na duniya, kuma wannan haline na rai na dan adam, wadda akanta allah ya halicci mutum kuma hakan yana faruwa ne ta bangaren lura da yake da abinda yafi falala a gareshi ta bangaren fifikon da yake samu cikin abinda zai dauka ko kuma ya jefar, haka kuma ya dace ace yana neman abinda yafi ko wanne ingaanci a addininshi wanda da shine zai samu natsuwar zuciyarshi da kubutar da jikinshi da hankalinshi, da mutuncinshi sannan kuma dukiyarshi, hakan kuma bazai smu ba saita dalilin karatu mai natsuwa da kuma kimantawa mai kyau da kuma rashin gaggawa wajen hukunci dauan hukunci lokacin da hukuncin ke hannunka
= ya sani sani na hakika lallai halin da mutum zai shiga bayan mutuwa kodai ya zama zuwa aljannah wadda fadinta kaman fadin sama da qasa, ko kuma zuwa wuta wadda ake rurata wadda makamashinta sune mutane da duwatsu akanta akwai malaiku masu tsananin karfi wadanda basa sabawa allah cikin umarnin da ya basu kuma suna aikata abinda ya musu umarni, allah madaukakin sarki yana cewa; hakane kuma muka maka wahayin alqurani da harshen larabci domin ka gargadi maabota wanann alqaryar (makkah) da kewayenta kuma kayi gargadi ga ranar da babu shakku acikinta wasu sashin na mutane suna aljannah dayan sashin kuma suna jahim (wuta) suratu shura aya ta 7.
ina rokon allah ga duk wanda ya karanta wannan littafi da allah ya datar dashi da kuma budewar kirji domin karban gaskiya da binta

 

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha

 
www.islamland.com
MENENE MUSULUNCI??

 musulunci shine mika wuya ga allah ta yadda zai zama kaman yadda allah yayi umarni dashi kuma yadda yakeso a bautamai da barin hadashi da wani abokin tarayya da aikata umarninshi da kuma barin abubuwan da ya hana, musulunci shine tsani tsakanin bawa da ubangijinshi, yana ganawa dashi sau biyar a rana daya a dare da rana acikin sallolin da allah ya farlanta akan bayinshi, wanda ya hada da sauran sunnonikaman yadda ya zama akwai alaqa sosai tsakanin allah da bawanshi wadda mai ci gaba ce a cikin adduoin da zikirori wadda mutum ke fadansu acikin ayyukanshi na yau da kullun wadda kuma taje kara karfin alaqarsu, akwai anbaton allah na cin abinci, da kuma bayanshi, da kuma adduar shiga bayi da adduar fitowa daga bayin, da adduar shiga gida da adduar fitowa daga gidan, da adduar bacci da adduar tashi daga bacci, da adduar yin alwala da adduar gamawa, da addua yayin saduwa da iyali, da adduar hawan abin hawa, rayuwar mutum gaba dayanta tana daure ne da bin hanyoyin ubangiji kaman yadda allah yake cewa; kace lallai sallah ta da yankana da rayuwata d mutuwa ta suna ga allah ubangijin talikai
Surat Al-An‘aam Aya ta 162


DAGA CIKIN ABUBUWAN DA MUSULUNCI YA KEBANTA DASU

duk da cewa ddinin musulunci shine addinin karshen da allah ya saukar kuma shine addinin da allah bai yarda a bautamai ba sai dashi, kaman yadda yace; duk wanda ya nemi wani addini koma bayan musulunci to lallai ba zaa karba mai ba kuma aranan qiyama yana daga cikin masu asara, hakan yada wannan addinin ya kebanta da wasu abubuwa ta yadda zai kasance tare dasu ta bangaren inganci har zuwa ranar qiyama, daga cikin wadanna kebantattuun abubuwa akwai;
1- cikar hankali;
addinin musulunci addinine na cikar hankali lafiyayye wadda akanta ne allah ya halicci mutane wadda ta zama mai girma wajen abinda mutum zai qudurce na tabbatar da samuwar allah abin bauta wadda ta hanyarshice zai tabbatar da samuwar allah da sanin niimominsu da tinaninsa acikin wannna duniyar wadda zata kaimu gareshi, allah yana cewa; ka tsayar da fuskarka akan addini kana mai bin gaskiya kuma kana kin qarya, halittar allah ce daya halicci mutane akanta, kuma babu mai canza halittar allah, wannan shine tsayayyen addini amman da yawan mutane basu sani ba, suratu rum aya ta 30.
wannan shine asalin akan halitta gaba daya kuma wannan halittar ta mutum akwai abubuwa da zasu iya yin tasiri cikin abubuwan da suke kewaye da mutum saita zagayeta acikin tafiyarta ingantacciya sai hakan yasa ta karkace daga hanya mai kyau har mutum yayi shirka da allah ko ya bautama waninshi ko ya musanta samuwarshi, manzan allah tsira da amincin allah su tabbata a gareshi yana cewa; babu wani abin halitta face an haifeshi akan asalin cikar mutum ta musulunci, amman saidai iyayanshi su mai dashi koo bayahude, ko banasare, ko bamajuse,maana iayyanshi su mayar dashi bayahude k o bamajuse bisa gwargwadon yadda suke bin addinin kuma ya burgesu.

2- KADAITAWA
musukunci shine addinin kadaitawa da tsarkake ibada ga allah shi kadai ba tare da abokin tarayya ba hakan saiya hafar da alaka ta kai tsaye tsaknin allah da bawanshi wadda ta tsayu aka imanin tsantsa da kuma komawa zuwa ga allah shi kadai, wajen neman biyan buqatu da neman gafara da taimako daga gareshikai tsaye ba tare da shamaki ba ko tsani, kuma hakan ya rusa duk abinda ake sawa na tsaknin allah da bawanshi domin mena kusanci zuwa ga allah kuma ya aibanta mushrikai na bubuwan da suke sawa tsakninsu da allah, allah yana cewa; lallai ku saurara domin addini na allah ne his kadai kuma a tsarkakeshi, wadanda suka riki wasu abubuwan neman kusanci ga allah sun acewa bas bauta musu dan komai sai dan su kusantar dasu zuwa ga allah, suratu zumar aya ta 3.
kalmar tauhidi wato ‘la ilaha illallah’ tana nufin babu abin bautawa da gaskiya sai allah kuma wanna kalmar itace mabudin shiga addinin musulunci, kuma saaboda ita ne allah ya halicci dukkan halittu domin su bautamai, kuma ta dalilinta ne allah ya halicci aljannah da wuta, kuma itace abinda annabwa sukayi kira da ita tin daga zamnin annabi nuhu zuwa ga cikamakon annabawa manzan allah annbai muhammad tsira da amincin allah su tabbata agareshi, allah yana cewa; babu aika gabanainka ba cikin annabawa face sai mun yi musu wahayin cewa babu abin bautawa da gaskiya sai allah kuma ku bautamun, suratul anbiyai aya ta 25

KALMAR TAUHIDI TANA NUFIN:
= kadaita allah shi kadai cikin bautarshi ba tare da abokin tarayya ba dukanshi da kuma tabbatar da ita gareshi da kadaitashi cikin bauta ba tarea da anyi mai shirka da komai ba cikin bautarshi, allah yana cewa; wancananku shine allah babu abin bautawa da gaskiya saishi shine mahaliccin komai da komai ku bauta mai, kuma shine mai wakilci akan komai, suratul an’am aya ta 102.
= kadaita allah cikin abubuwan da ya halitta da kuma qudurta cewa shine mamallakin komai da komai kuma wanda ya halicci dukkan halittu kuma shine mai azurtasu kuma shine mai rayasu kua mai kashesu kuma hsine zai tashesu ranar da babu shakku acikin aukuwarta, babu mamallaki ko mahalicci ko mai sarrafa abubuwa kamanshi acikin wannan duniyar, babu mai tsara yadda zaayi rayuwa ko muamala amatakin mutum daya ko kuma duka dukkan halittu saishi, kuma babu mai haramtawa ko halattawa saishi, allah yana cewa; shine rayayye babu abin bautawa da gaskiya saishi ku rokeshi kuna masu tsarkake zuciyarku gareshi acikin addini, godiya ta tabbata ga allah ubangijin talikai, suratul gafir 65.
= kadaita allah cikin sunayanshi da siffofinshi tare da duka siffofinshi da suka dace dashi ba tare da wani aibu ba ko tawaya da kuma tsarkakeshi daga dukkan wwata halitta kar tayi kama dashi ko shige dashi, allah yana cewa; shine wanda ya kirkiri halittar sammai da kassai kuma ya halitta muku mataye daga gareku haka kuma ya halicci mataye ma cikin dabbobi domin ya dinga halittarku daga garesu, babu abinda yayi kama dashi kuma shine maiji mai gani, suratu shura aya ta 11.

3- BAUTAR ALLAH
allah madaukakin sarki bai halicci bayinshi ba sai dan su bauta mai kaman yadda yace; ban halicci mutane da aljanu ba sai dan su bauta mun, suratu dur aya ta 56.
buqatuwar mutane zuwa ga allah buqata ce wadda ya halicesu akanta kaman yadda jikinsu suke da buqata zuwa ga abinci da kuma abinsha domin su rayu, kaman hakane rayukansu suke da buqata zuwa ga bautar allah domin kwanciyar hankali da nutsuwa, anan ne zamuga ni a fili cewa lallai su halittun allah ba tare da cire kowa ba suna da buqatar abin bautar da zai dinga biya musu buqatunsu na yau da kullun, tare da kwanciyar hankali da nutsuwa domin komawa gareshi tin daga zamanin annabi adam zuwa lokacin annabi nuhu allah madaukakin arki kawai ake bautama wa ba tare da shirka ba, daga wannan lokacin ne aka fara samun shirka cikin bautama allah sai aka samu masu bautama duwatsu da bishiyoyi da kuma wasu dabbobin, da wasu abubuwa na rayuwa, hakan sai yasa allah ya aiko da manzanni domin su mayar da mutane zuwa ga bautar allah shi kadai, har wanda yake ganin ma babu allah – allah ya tsarkaka daga wannan batu- shima duk da haka yana da abinda yake bauta mawa wato zuciyarshi da kuma shaidanin da yake sashi aikata wadannan abubuwan, da kuma abinda zuciyarshi ke sanya mai na shaawa, wannan kuma shine karshen zalincin da mutum zaima kanshi da kuma waninshi, domin shi mai yin haka yana rayuwa ne cikin wannna duniyar ba tare da wata manufa ba, da kuma kekashewar zuciya, kuma a lahira sakamakonshi itace wutar da ake rurata, babu mai shiganta sai shakiyyi, wanda ya karyata ayoyin allah kuma ya juya musu baya, kuma hakan zalici ne ga waninshi domin komai zai daura alhakinshine akan waninshi, kuma bazai samu abinda zai iya bi ba, ko kuma inda zai tsaya, kuma bazai san abinda ya dace ba da wanda bai dace ba, hakan yana gasgata fadin allah ne; shin ka bani labarin wanda ya riki abin bautarshi itace zuciyarshi kuma hakan yasa allah ya batar dashi daga sanin wani ilimi kuma allah ya shafe zuciyarshi yasa mata murfi shin waye zai shiryar dashi bayan allah?? shin bakwa tinani ne, suratul jasiya aya ta 23.
a bisa yanayi na duniya ka duba gefenka zakaga wanda baya bautawa allah kuma yana mai shirka wanda ba musulmi ba maabota aqida ingantacciya wadanda suka bautawa allah shi kadai, yahudawa sun canza addini suna kiran uzairu wato dan allah ne, haka nasara suma sun canza addini suna kiran isa almasihu cewa dan allah ne, banda ma wadanda suke bautawa abinda ko a hankalce bai dace ba, da kuma cikakkiyar halittar mutun, kuma zukata na gaskiya suna kin wannan abun, daga bautar gumaka ko dabbobi da taurari allah yayi gaskiya inda yake cewa; lallai abinda kuke kira koma bayan allah suma bayi ne kaman ku, ku kirasu mana su ansa muku indai kun kasance masu gaskiya, suratul aaraf aya ta 194.

4- HANKALTUWA
musulunci addinine na girmama hankali da tinani, akwai ayoyi da dama na qurani da suka zo da lura da hankalin mutum kuma allah ya kira mutane domin yin tinani da hankaltuwa akan halittarshi yake cewa; shin bazaku hankalta ba, shin bazaku yi tinani ba, shin bazaku sani ba, shin ba zaku lra ba,,,,,,,,,,,,,,,,,allah yana cewa; lallai acikin halittar sama da qasa akwai abubuwan lura ga masu imani, acikin halittarku da kuma abubuwan da allah ya watsa muku na dabbobi akwai ayoyi ga masu yaqini, da kuma canje-canjen dare da yini da abinda allah ya saukar na daga ruwan sama wanda yake rayar da qasa dashi bayan mutuwarta akwai abubuwan lura ga masu hankali, suratul jasiya aya ta 3-5.
saidai allah madaukakin sarki ya kididdiga iya inda ya kamata mutun yayi amfani da hankalinshi, baya halatta sai cikin abinda ana iya fahimtarshi da gabobin nan guda 5 na jikin dan adam, kaman abinda mutum zai iya gani, ko yaji da wasunsu, amman abubuwan gaibu wanda allah ne kawai ya sansu wanda mutum baya iya ganinsu ko jinsu, babu daman yin amfani da hankali acikinsu domin gasgata su, domin amfani da hankali a cikinsu ya zama abinda mutum baida halin aikatashi ne, kuma mutum bai isa yasan hakan ba aita hanyar wahayin da allah yama manzanni, allah yana cewa; allah shine masanin gaibu( ) kuma bayan bayannawa kowa shi, saidai wanda ya yarda dashi daga cikin annabawa domin sine wanda zai iya anuna mai abu a gabanshi, suratul jinni aya ta 26.
duka koyarwatr musulunci suna, hankalin dan adam yana shaidah gaskiyarsu da kuma ingancinsu da amfaninsu a wajen dan adam domin duka umarnin allah da abubuwan da ya hana adalcine babu zalinci acikinsu, allah bai taba umarni da wani abu ba face akwai amfani acikinshi kuma zai zama akwai alkhairi acikinshi, haka bai taba hani ba ga wani abu face ya zama sharri nw da barna acikinshi, kuma wannan baya boyuwa ga wanda yayi tinani ga ayoyin allah, da kuma hadisan annabi tsira da amincin allah su tabbata a gareshi.

5- UBANGIJINTAKA
koyarwar musulunci cikin abubuwan da allah ya halitta ada kuma aqida da bauta da haqqoqin suna nan tabbatattu babu abinda zai canza su ko sauyawa, allah yana cewa; shi qurani saukakkene daga wajen allah, suratul waqia aya ta 80.
ba aikin mutum ane wanda zai iya samun cikas ko ko kuskure da tasirantuwa da wasu abubuwa na waje wanda suke kewaye da mutum na cigaba da abunda aka gada na zamantakewa, allah yana cewa; shin hukuncin jahiliyya kuke nema, waye zaifi allah iya hukunci a wajen masu yaqini, suratul maida aya ta 50.
musulunci shi kadaine addinin da babu wani abu daya shigeshi na canzawa ko juyawa, kuma hujjojinshi sun kubuta daga ragi ko qari abubuwan da ake hujja dasu a cikin musulunci sune:
1- qurani mai girma shine dai yadda yake tin da aka saukarwa manzan allah tsira da amincin allah su tabbata gareshi, da harufanshi da ayoyinshi da surorinshi kuma ba bu wani abu da aka canza ko aha juyashi ko ragi ko qari, kuma an cirantoshi ne daga jamaa masu yawan gaske wanda alada bata yadda da cewa su taru dukansu akan karya ba, kuma ya zama sun jinginashi ga abu wanda mutum zai iya gani, ta hanyar haddaceshi acikin littafai da zukatan mutane, kuma musulai sun kwadaitar dukkan kwadaitarwa akan littafin allah wajen kula dashi da kuma koyanshi da koyar dashi domin alkhairin da annabi ya fada cikin hadisi yace; mafi alkhairinku shine wanda ya koya qurani kuma ya koyar dashi, bukhari ya ruwaitoshi.
kuma qurani ya zama shine ake bautawa allah da haddaceshi da kuma karantar dashi manzan allah yana cewa; duk wanda ya karanta wai harafi acikin qurani yana da lada goma, ita goman kuma zaa ninka mai ita, bana cewa alif lam mim harafi daya ne, ah ah saidai alif harafi ne, lamun ma harafi ce, haka mimun ma harafi ce, imam tirmizi ya ruwaitoshi, kuma yaa cikin littafin sahihul jami mai lamba ta 6469.
2- Hadisan annabi muhammad tsira da amincin allah su tabbata a gareshi itace hujja ta biyu wajen gina shariar musulunci kuma mai bayanin qurani kuma mai fassara wasu da yawa cikin hukunce hukuncen shi, kuma hakika an kareta daga baraka ko qarya wajen shigar duk wani abun da ba daga gareshi ba, kuma hakan ya faru ne dagawajen wasu mazaje amintattu masu adalci, wanda suka bada lokacinsu da rayuwarsu wjen karantar hadisa annabi da kuma karantar isnadin wadannan hadisai da lafuzzansu da kuma darajojinsu daga inganci zuwa rauni, da halayen masu ruwaitosu ta bagaren adalcinsu ko kuma illarsu, sai suka tsaftace dukkan hadisai wadanda aka ruwaitodaga manzan allah, basu bar komai ba face wadanda suka inganta daga gareshi, kuma suka iso garemu suna sua masu inganci.

6- GAME DUNIYA
addinin musulunci addinine na duka duniya ba tare da cire wasu ba, bakaken fata da farare, larabawa da kuma ajamawa, ako wani lokaci da kuma zamani, shine addinin da kowa da kowa aka zama daya ba banbancin launi, ko yare, ko gari, ko dangi, ko zamani balle kuma lokaci, shidai kadai aqida ce guda daya bayyananniya kuma tabbatacciya kuma itace ta hadasu suka zama daya, domin duk wanda yayi imani da allah shine abin bauta, kuma yayi imani da musulunci shine addinin gaskiya, kuma yayi imani da manzan allah shine annabi gaskiya, ya shiga karakashin inuwar wannan addinin a ko wani zamani kuma ako wani guri, amman sauran addinai koda su yi ittifaqi da musulunci wajen suna amman su suna kebantane kawai ga wasu mutane daban, kuma a wani lokaci da ban, baya wuce wannan zamanin nasu zuwa wasunsu, annabi musa ba zuwa ga bani israila kawai aka aikeshi ba, allah yana cewa; mun baiwa annabi musa littafi kuma muka sanyashi shiriya akan bani israila cewa kada su riki wani a matsayin mai jibintar lamarinsu koma bayan allah, suratul israi aya ta 2, lokaci da zamani ya ja akan banu israila bayan annabi musa sai suka caza addininsu da annabi musa ya bayyana musu shi kuma suka bace hanya, sai allah ya aiko anabi isa domin ya mayar dasu zuwa ga gaskiya kuma ya canza musu addininsu zuwa ga musulunci, allah yace; kuma muka hada a karshensu da annabi isa dan nana maryam, yana mai gasgata abinda ya gaba ceshi na daga attaura, kuma mun basahi littafin injila acikinshi akwai shirya da haske kuma yana gasgata littafin attaurar da ya gaba ceshi tareda shirya da waazantarwa ga masu tsoron allah, suratul maidah aya ta 46.
sannan bayan wani lokaci mai tsayi allah ya aiko annabi muhammad tsira da amincin allah su tabbata a agareshi kuma ya aikoshine gaba daya zuwa ga mutane da aljanu kuma dashine aka rife dukan manzanni, maana babu wani manzo bayanshi, allah yana cewa; albarkun allah su tabbata gareshi shine wanda ya saukar da qurani mai rarrabe qarya da gaskiya domin ya zama abin gargadi ga dukkan talikai, suratul furqan aya ta 1.
shi addinin musulunci duk da wannan game duniya da yayi baya tilasta mutane wajen sai sun shigeshi, saidai shi yabar ma kowa daman yayi zabi ga wanda addinin ya riskeshi wajen ya ansheshi ko ya barshi, amman kuma du da haka ya bayyana makomar wanda ya juya mai baya, allah yana cewa; ka fada gaskiya daga ubangijinka, duk wanda yaso yayi imani, wanda kuma yaki ya kafirce, mudai mun taadarwa azzalumai wuta wadda makamashinta suka gewayeta, idan suka nemi agaji ana agazamusu ne da wani ruwan da yake zagwanyar musu da fuska, tir da abin shansu kuma makomarsu tayi muni, suratul kahfi aya ta 29.
    
7- TSAKA TSAKIYAR ADDINI DA YANAYINSHI
daga ciki abubuwan da suka taimaka wajen wanzuwar musulunci shine abinda ya kebantashi na tsaka tsakiya, da kua daidaito da kuma saukakawa wajen fahimtarwa, da saukin koyanshi da kuma rangwantawa wajen muamala, annabi ya bayyanasu da cewa; mafi soyuwan addini zuwa ga allah shine banbance qarya da gaskiya, da kuma rangwantawa. bukhari ya ruwaitoshi.
hanyar koyarwar musulunci itace umartan kowa da kowa abinda zai iya aikatawa, kuma shine addinin asalin halittar mutum, wanda yake bibiyar da ita kuma yake kwaikwayonta domin ibadojin gwargwadon yadda zai iya yinsu, da halayenta, allah yana cewa; kuma allah bai sanya muku wani abu cikin addini da yake na gajiyarwa ba, suratul hajji aya ta.
kuma rangwamen addinin musulunci tana bayuwa ne ta banhgaren saukin hukunce hukuncenshi da saukin ibadojinshi dakuma saukin da dukkan wadannan hukunce hukuncen, kuma ya dauke duk wani laifi da tare dukkan wata wahala, domin ya zama kowa yana da halin aikata wannan bautar, duka umarnin allah na sharia sunzo ne a yanayin da kowa zai iya aikatasu, kuma basu fi karfin mutum ba, tare da cewa duka umarnin da allah yayi na bauta suna iya sauka akan mutum a lokacin lalura, wadda itama tana da hkunce hukuncenta da ban, allah yana cewa: duk wanda ya shiga hali na lalura ba mai taaddanci ba ko wuce gona da iri babu laifi a tare dashi, suratul baqara aya ta 172.
hakan bai kasance ba face shariar da allah ya saukar da ita ga bayi kuma yasan su din sunada rauni, kuma abubuwan da zasu iya yi a kididdige suke, shiyasa shariar musulunci take lura da halin mutane da abubuwan da zasu iya aikatawa bisa ga dabiarsu tayau da kullun kaman yadda allah yace: allah yana son ya saukaka muku domin an halicci mutum ne mai rauni, suratun nisai aya ta 28.
duk umarnin musulunci sun ginu ne akan wadannan qaidoji na ubangiji da sawwakewa jamaa rayuwarsu ta ibada kaman yadda yace: ubangiji baya dora ma wata rai abinda ba zata ita aikatawa ba, tana da ladan aikin da tayi haka kuma tana da laifi abinda ta aikata na zunubi, suratu baqara aya ta 286.
manzan allah tsira da amincinallah ya tabbatar da cewa: duk abinda na haneku ku barshi, duk abinda na umarceku kuma ku aikatashi daidai iyawarku, domin abinda ya halakar da mutanan da suke gabaninku shine yawan tambayoyinsu da kuma sabaninsu ga annabawansu, bukhari da muslim suka ruwaitoshi.
rangwantawa da saukakawa na shariah hakan baya nufin a rusa wasu daga cikin amanufofin shariah da addini to kaga mutum ya zama yana halasta haram, shi kuma haram yana halastashi, ko kuma wuce gona da iri wajen ayyukan shariah ko wajen aikata umarnin allah, ko kuma rusa fahimtar shariah akan wasu abubuwa, da ladubba na gaba daya, amman yafi son saukakawa wadda tayi nesa akan wahalarwa ko takurawa akan laifi da kiyayya, nana aisha allah ya kara mata yarda tana cewa: manzan allah baa taba bashi zabin tsakanin wasu ayyuka guda biyu ba face ya dauki mai saukinshi muddin bai zama zunubi bane, amman inya zama laifi ne to ya fi kowa nesa-nesa dashi, bukhari da muslim suka ruwaitoshi, abinda ake nufi da alamura guda biyu shine alamuran duniya ko kuma duniya da addini.

8- KAMMALUWA DA CIKAR ADDINI
addinin musiulunci shine cikakken addini wanda allah ya cikashi akan saukan addininai da suka gaba ceshi kuma akan hakan ne niimar allah ta cika da yardarshi akan bayinshi, ainda yake cewa: yaune na cika muku addininku kuma na cika muku niimata kuma na yardar muku da musulunci shine addini, suratul maidah aya ta 3.
da wannan ayar ne aka goge duk wani addini da yazo gabanin manzan allah, kuma allah baya karban wani addini daga bayinshi face wannan din, domin duk sauran sharioin da suka gabata sun kasance masu asali na ruhin mutum wadda suke isar da sako zuwa gareta kuma take kira zuwa ga tsarkake ita rai, kua suna kira ne zuwa ga abinda zai zama maslaha da alamuran duniya da tsarata da wayar da kai sabanin shi kuma musulunci da yazo domin ya cika duka bangarorin dan adam na rayuwarshi, ya kunshi abubuwa na duniya da na addini duka, manzan allah ya bayyana hakan cewa lallai musuunci shine kadai addini agun allah kuma dashine ya aiko duka annabwa da manzanni sashinsu yana cika sashi farawa tin daga zamanin annabi nuhu zuwa ga manzan allah tsira da amincin allah su tabbata a gareshi domin dashine aka rife annabci kuma ya cika shariah, yana cewa acikin hadisi: lallai mislai na da misalin sauran annabawa kaman misalain mutum ne ya gida gida uma ya ingata gininshi amman sai waje daya baa cike ba, har gidan ya burge mutane suna ta yabawa amman suna cewa inama ace ka cike inda akwai hujin nan, sai annabi yace: to nine cikon wannan hujin da ya rage, bukhari da muslim suka ruwaito.
bugu da kari, bayan wannan cikar da addini yayi da kammaluwarshi allah yayi alkawarin cika musulunci har lokacin da allah zai karar da duniya da abubuwan dake cikinta sabanin addinan da suka zo kafin musulunci allah baiyi alkawarin kiyayesu ba, domin su sun sauka ne ga wasu mutane daban, kuma a wani zamani daban, allah yana cewa: lallai mune muka saukar da qurani kuma mune zamu bashi kariya, suratul hijr aya ta 9.
    
9- BAYYANAR ALAMURAN ADDINI    
addinin musulunci addini ne a bayyane babu rudani acikinshi ko boye-boye hakan kuma aka siffanta qurani wanda shine madogara ta farko wajen bayanin musulunci da cewa shi littafi ne mabayyani kuma shiriya ne ga mutane kuma shine mai bayyana komai acikin addini, allah yana cewa: hakika haske da littafi bayyananne yazo muku daga wajen ubangijinku, suratul maidah aya ta 15.
ko wani mutumi yana da haqqin tambaya abinda bai gane ba cikin addini ko kuma abinda ke mai yawo cikin tinaninshi bai gamsu dashi ba, domin babu abinda zai hana shi tambaya, amman muslunci bai sa hakkin ansa tambayoyin masu tambaya ba a hannun kowa face maabota ilimi da masaniya ta addini, da wadanda suka karanci shariah sosai da sosai wadanda suka bada lokacinsu wajen karantar addinin da bincike acikinshi, domin ilimin magunguna ana nemanshi ne agun likitoci, haka ilimin kere-kere ana nemanshi ne wajen injiniyoyi, haka ilimin shariah ana nemanshi ne wajen cikakkun mallamai masana ilimin addini, allah yana cewa: ba mu aiko kowa gabaninka ba face mazaje wadanda muke musu wahayi, ku tambayi maabota sani indai baku san abu ba, suratun nahli aya ta 43.
acikin musulunci babu wata mas’alar da ba bayyananniya bace, kuma zamuyi imani dasu kuma bazamu yi tambaya ba saidai abinda hankalin mutum bazai iya kaiwa gareshi ba na abubuwan gaibu, wadanda allah bai bayyana mana su ba, kuma wannan itace amfanin imani da abubuwan boye na gaibu wanda allah ya yabi wadanda suka siffanta da ita, kuma shine gurin da ake banbance tsakanin mumini da wanda ba mumini ba, allah yana cewa: alif lam mim, wancan littafi babu shakku acikinshi shiriya ne ga masu jin tsoron allah, wadanda suke imani da abin boye wato gaibu kuma suke tsayar da sallah sannan suna ciyarwa daga cikin abin da muka azurtasu, kuma sune masu imani da abinda aka saukar gareka da wanda aka saukar gabaninka kuma game da lahira su masu yaqini ne, su wadannan suna kan shiriya ta ubangijinsu, kuma sune masu samun babban rabo, suratul baqara aya ta 1-5.

10: CIGABAN MUSULUNCI:
shari'ar musulunci a yanayinta da 'dabi'arta mai samun nasara ce ba mai rafkana bace akaran kanta, ba kuma mai karkata bace ga barin abunda ke kewaye da ita na samammu (halittu), bari dai ita dai shari'a ce bu'da'd'diya tana umurni da ya'da kyautatawa da kuma son alkhayri ga waninka, kasancewar musulmi akaran kansa baya isa, dole sai ya kasance mai samar da masalaha ga waninsa, mai tasirantuwa ga al'ummar da yake rayuwa acikinta, mai ya'da alkhayri acikin al'ummar, ya koyar da jahili (wanda bai sani ba), kuma ya nusar da 'batacce, yana kuma mai umurni da alkhayri, yana kuma mai hani da mummuna, yana kuma mai qira zuwa ga bautar allah da ka'daita shi, allah ma'daukakin sarki yana cewa: kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alkhayri, kuma suna umurni da alkhayri, kuma suna hani daga abunda ake 'ki, kuma wa'dannan sune masu cin nasara." suratul ali-imran aya ta 104..
sai dai a shari'ar kyautatawa ga mutane da kuma son alkhayri gare su na daga cikar ibada, saboda fa'din manzon allah (saw): " kaso wa mutane abunda kasowa kanka zaka kasance musulmi." tirmizi da ibn majah suka ruwaito shi, kuma albani ya inganta shi- 930.
saboda tasirin wannan tabbatarwa da kuma 'karfafata shari'ar musulunci ta sanya falala mai girma ga mai ya'da alkhayri, manzon allah (saw) yana cewa: " wanda yayi 'kira zuwa ga shiriya to ya kasance yana da lada kwatankwacin ladan wa'danda suka bisa kuma ba za'a tauye wani abu ba daga cikin ladansu ba, hakanan kuma duk wanda yayi 'kira zuwa ga 'bata to za'a basa zunubi kwatankwacin zunubin wanda suka bisa kuma ba za'a tauye wani zunubi daga zunubansu ba.
    
11- TABBACI DA KUMA CIGABA
lallai musulunci addini ne da yake zama maslaha ga kowane zamani da kuma kowane muhalli, to addinin musulunci yazo da dokoki da tushe na baki 'daya da kuma qa'idodi da tusheshina gamammu baki 'daya tabbatattu basa musanyuwa kuma basa chanzuwa da chanzawar zamani ko kuma muhalli a aqida da ibadu kamar sallah da adadin raka'o'inta da kuma lokutanta da kuma zakka da kuma gwargwadonta da kuma abunda take wajaba acikinsa da kuma azimi da lokacinsa da kuma hajji da siffarsa da kuma lokacinsa da kuma haddi.... abubuwanda suka zama fararru kuma yake sabunta na daga abubuwan bu'kata a rayuwa to an bijiro dasu ga alqur'ani mai girma da kuma abunda ya inganta daga manzon allah (saw) idan ya samu to yayi riqo dashi ya kuma bar waninsa, idan kuma bai samu ba to yayi bincike da kuma duba na tsanaki ga 'ko'karin malamai masu ilimi ako wani zamani da kuma muhalli na daga abunda zai tabbatar da maslaha gamammiya kuma ya dace da abubuwan bu'katar zamanin su da kuma halin al'ummarsu duk wa'dannan ta hanyar duba zuwa ga alqur'ani da sunnah da kuma bijiro da abunda yake sabuntawa abisa qa'idodi ta shari'a wanda aka cirota daga alqur'ani da sunnah, wannan da manufar isa zuwa ga abunda amfaninsa zai dawo ga 'dan adam ba tare da cin karo da wani nassi na shari'a ba, don musulunci ya zamto yana tafiya daidai da kowane zamani, kuma yana tare da abubuwan bu'kata na kowace al'umma.

12 - CIKAR ADDINI
lallai musulunci yana amsa bu'katun 'dan adam na ruhi da jiki da daidaito na ban mamaki kuma yana 'kin zaluncin wani 'bangare akan wani, allah ma'daukakin sarki yana cewa:"kuma ka bi'da, acikin abunda allah ya baka, gidan lahira, kuma kada ka manta da rabonka daga duniya. kuma ka kyautata, kamar yadda allah ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nemi 'barna acikin 'kasa, lallai ne allah ba ya son masu 'barna." suratul qasas aya ta 77.
a mahanga ta addinin musulunci allah ya halicci ran 'dan adam kuma ya halifantar dashi a bayan 'kasa saboda yi masa ibada da kuma tabbatar da shari'ansa kuma ya halicci gangan jiki ga wannan ran cikakke tsararre saboda rai yayi abunda allah ya umurce sa da yi ta hanyar wannan jikin na daga ibada da kuma ha'k'ko'ki da kuma jagoranci a bayan 'kasa wanda allah ya halifantar dashi aciki, allah ma'daukakin sarki yana cewa; kuma shine wanda ya sanya ku masu maye wa juna ga 'kasa. kuma ya 'daukaka sashenku bisa ga sashe da darajoji: domin ya jarraba ku, acikin abunda ya baku, lalkai ne allah mai gaggawar uquba ne kuma lallai ne shi ha'ki'ka mai gafara ne mai jin 'kai." suratul an'am aya ta 165.
a musulunci babu rahbaniyyah (barin jin duniya da kuma ka'daituwa ga barin ahlinta) da kuma daina bin komai sai ibada da kuma yankewa ga barin duniya da kuma barin da'da'da da kyawawa abubuwanda allah ya halitta ga bayin sa kuma ya halattasu gare su, allah ma'adaukakin sarki yana cewa: kace: wanene ya haramta 'kawar allah, wadda ya fitar saboda bayinsa da masu da'di daga abinci? kace: su domin wa'danda suka yi imani suke acikin rayuwar duniya, suna ke'bantattu a ranar 'kiyama. kamar wannan ne muke bayyana ayoyi daki-daki ga mutanen da suke sani." suratul aaraf aya ta 32.
abunda zamu fuskanta anan shi ba addinin fuskantar duniya bane da kuma kwa'dayi zuwa ga sha'awowinta da kuma jinda'dinta ba tare da dokokin kiyaye hakan ba, sai dai shi musulunci addini ne na dai-daito da kuma tsakatsakiya wanda ya ha'da da addini da duniya wani 'bangaren bazai yi rinjaye akan wani ba, anyi umurni da daidaito tsakanin rai da jiki sai aka umurci musulmi ahalin sonsa cikin al'amuran duniya da tuna bu'katuwarsa na rai ta yin abunda allah ya wajabta masa na daga ibada, allah ma'daukakin sarki yana cewa:
"ya ku wa'danda suka yi imani idan anyi 'kira zuwa ga sallah daga ranar jumma'a, sai kuyi aiki zuwa ga ambaton allah kuma ku bar ciniki, wancan dinku ne mafi alkhayri agare ku idan kun kasance kuna sani." suratul jumu'a aya ta 9.
aka nema daga garesa acikin ha'din 'ko'karinsa da himmatuwa cikin ibada ya ringa tuna bu'katuwarsa na jiki da rai da daga samu da kuma neman arziki, allah ma'daukakin sarki yana cewa:" sa'annan idan an 'kare sallah sai ku watsu cikin 'kasa kuma ku nema daga falalar allah kuma ku ambaci sunan allah da yawa tsammaninku ku samu babban rabo." suratul jumu'a aya ta 10.
kuma musulunci yabi dukkanin wa'dannan siffofi guda biyu, allah ma'daukakin sarki yace:" wa'dansu maza wa'danda wani fatauci ba ya shagaltar dasu, kuma sayarwa bata shagaltar dasu daga ambaton allah da tsaida sallah da bayar da zakkah, suna tsoron wani yini wanda zukata suna bibbirkita acikinsa da gannai." suratul noor aya ta 37
musulunci ya kiyaye ha'k'ko'kin rai da kuma gangar jikk daidai da shari'ar allah babu wuce gona da iri ayin hakan, kamar yadda aka nema daga musulmi lura da ransa da kuma yiwa ran nasa hisabi akan ayyukan ran nasan da kuma dukkanin abunda yake bijirowa daga ran nasa saboda yin aiki da fa'din allah ma'daukakin sarki:
"to wanda ya aikata wani aiki gwargwadon nauyin zarra na alkhayri zai ganshi* wanda kuma ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri zai ganshi." suratul zalzala aya ta 7-8.
hakanan an nema daga garesa kiyaye jikinsa ta hanyar ni'imtuwa da abunda allah ya halatta na da daga da'da'dan abincine wannan abun ko abun sha ko tufafi ne ko abun aure da kuma da kuma kiyaye ni'imtuwa da wa'dannan da'da'da tare da rashin 'barna wanda cutuwarsa baya 'boyuwa ga jiki, allah ma'daukakin sarki yace:
"ya 'dan adam, ku riqi qawarku a wurin ko wani masallaci, kuma kuci kuma ku sha kuma kada kuyi 'barna lallai ne shi (allah) baya son masu 'barna." suratul a'araf aya ta 31.
ka lura a hane hanen musulunci daga cikinsu akwai al'amuran da aka hana da kuma wa'danda aka haramta su a shari'a. anas 'dan malik (ra) yana fa'da cewa:" wasu mutane guda uku sunzo gidajen matayen manzon allah (saw) suna tambaya dangane da ibadar manzon allah (saw) yayin da aka basu labari sai suka ga kamar tayi ka'dan, sai suka ce mu asuwa ga annabi (saw) alhalin an gafarta masa zunubansa abunda ya gabata na zunubansa da abunda zai zo nan gaba (amma yana ibada) sai 'daya daga cikinsu yace: "ni zanyi tayin sallah ko wane dare baki 'dayansa har'abada" sai 'dayan yace: "zan tayin azumi duka sheka bazan sha ruwa ba" sai 'dayan yace: "ni kuma zan nisanci mata bazanyi aure ba har'abada" sai manzon allah (saw) yazo yace: kune wa'danda kuka ce kaza da kaza ko? to na fiku tsoron allah kuma na fiku cikakkiyar biyayya ga allah, sai dai ni ina azumi kuma ina shan ruwa kuma ina sallar dare kuma ina yin bacci kuma ina auren mata, duk wanda ya 'yamaci sunnata to ba ya tare dani." bukhari ya ruwaito.

13- CI GABA DA WANZUWA
tare da cewa shari'ar musulunci ita ce cikamakin shari'o'in da allah ya sauqar daga sama kuma ta qarshensu ta yadda ta tattara dukkanin koyarwar allah kuma wadda ta zama ma'kura wajen zama maslaha ga kowane zamani da kumamuhalli, allah ya wajabta ma ta wanzuwa da kuma cigaba har izuwa lokacin da allah zai tashi 'kasa da abunda ke kants, kuma ya ji'binci kiyayeta da kansa sa'banin sauran shari'o'in, kuma ba tare da wani abu na chanji ya sameta ba. alqur'ani shine reference na farko a shari'a allah ya ji'binci kiyayesa ba tare da anyi wani 'kari acikinsa ba ko kuma a tauye wani abu da yake acikinsa, kuma shi alqur'ani mu'ujizar manzon allah ce madawwamiya sa'banin mu'ujizozin sauran annabawa kafinsa wanda mu'ujizarsu take 'karewa da shu'dewar zamaninsu, kuma take kasancewa shaida akan gaskiyar manzancinsu a lokacinta sai wanda ya ganta yayi imani da ita. amma shi alqur'ani mu'ajiza ne da take tafiya har izuwa tashin al'kiyama, kuma shi alqur'ani shaida ne akan gaskiyar manzon allah (saw), allah ma'daukakin sarki yana cewa:"lallai mune muka sau'kar da ambato (alqur'ani) kuma lallai mu masu kiyayewa ne agare shi." suratul hijri aya ta 9.
manzon allah (saw) kuma yana cewa:" wata jama'a daga cikin al'ummata bazasu gushe ba ana taimakonsu akan gaskiya, guje musu bazai cutar dasu da komai ba har tashin al'kiyama." muslim ya ruwaito shi.
wannan shine abunda ake lura dashi na chanzawar da yawa daga cikin ma'abota sauran addinai ga musulunci duk da rauni na jiki da ake samu wajen gabatar da shi da kuma taimako na jikin 'dan adam da ake samu wanda bashi da iyaka domin ya'karshi da toshe duk wata hanyar ru'dani daga ma'kiyansa hakanan ka'dan suke fita daga cikinsa bayan rungumarsa

14- GAMEWA
addinin musulunci a 'dabi'arsa ya game dukkanin 'bangarori na rayuwa sai yazo da tsaruka da kuma shari'o'i wadda take daidaita al'umma bata bar wani 'bangare daga cikin 'bangarorin rayuwar 'dan adam da dukkan 'bangarorin ta na raine 'bamgarorin ko na gangar jiki, na addini ne ko na duniya ne, na 'dai'dai kun mutane ne ko na jama'a da yawa ne face ta tsara masa hanya mafificiya. allah ma'daukakin sarki yana cewa:
"kuma mun sau'kar da littafi akanka domin yin bayani ga dukkan komai na shiriya da rahama da bushara ga masu mi'ka wuya (musulmai)." suratul nahl aya ta 89.
sai musulunci ya tsara ala'kar musulmi tare da ubangijinsa da kuma al'ummarsa da kuma halittun da suke kewaye dashi, daga cikin abubuwan da suke nuni abisa wannan 'dabi'ar shine damuwarsa da kulawarsa ga 'kananan am'dabi'u wa'danda suke da alaqa da rayuwar 'dan adam, manzon allah (saw) yace: ankar'bo daga abu-hurairah (ra) yace: "manzon allah (saw) yace: "imani yanki saba'in da 'doriya ne ko kuma yanki sittin da 'doriya ne mafificiyarta. (a wata ruwayar kuma ma'daukakiyarta) itace fa'din la'ilaha illallahu (babu wani sai allah), mafi 'kas'kantarta kuma shine 'dauke abun cutarwa daga hanya, kunya wani yanki ne daga imani." bukhari da muslim ne suka ruwaito amma wannan lafazin na muslim ne.
)bidi'un) abunda ke tsakanin biyu zuwa goma. (shu'abatun) 'dabi'a. (ima'datul-aza) gusar da wani abu na cutarwa.
sai aka wayi gari aka gina wa'dannan 'dabi'u ma'abociyar banbanci daga cikinsu:
★ Karrama 'dan adam ta yadda allah ya fifita shi akan dukkanin halittu a wannan duniya kuma ya hore shi. allah ma'daukakin sarki yace: "kuma lallai ne mun girmama 'dan adam kuma muka 'dauke su acikin 'kasa da teku kuma muka azurtasu daga abubuwa masu da'di kuma muka fifita su akan masu yawa daga wa'danda muka halitta, fifitawa." suratul isra'i aya ta 70.
★ Sanayyar juna sai aka kwa'daitar da samar da ala'ko'ki masu kyau tare da al'ummar musulmi da kuma al'umman da suke kewaye dashi na kyakykyawar ma'kotaka da kyautatawa da son alkhayri da musayar abunda zai zama maslaha. allah ma'daukakin sarki yace: "ya ku mutane lallai ne mu mun halittaku daga namiji da mace kuma muka sanya ku dangogi da 'kabiloli domin ku san juna, lallai mafificinku daraja awurin allah (shine) wanda ya fiku taqawa (tsoron allah) lallai allah masani ne mai 'kididdigewa." suratul hujurat aya ta 13.
★ Tabbatar da 'daukan nauyi na zaman tare ta yanda aka wajabta akan musulmi lura da kulawa ga halin 'yan uwansa abisa dukkanin wani mataki. manzon allah (saw) yana cewa: zaka ga mumini acikin jin'kan junansu da son junansu da taimakon junansu kamar jiki ne guda 'daya idan wata ga'ba ta kai 'kara na wuta cuta sai ya kaiwa dukkanin jiki da rashin yin bacci da kuma zazza'bi." muttafaqun alaihi.
)tarhamuhum) jin'kan sashensu ga sashe.(tawaduhum) son junansu ga junsnsu. (ta'adifuhum) taimakon junansu. (aljasadu) jiki guda 'daya ta hanyar duba ga dukkanin ga'b'bansa. (ishtaka udwan) saboda wata cuta da ta same sa shi jikin. (tada'a) tayi tarayya dashi cikin abunda yake cikinsa. (as-saharu) rashin yin bacci saboda ra'da'di.
 ★ 'yanci wanda yake abun lura da dokokin addini ya banbanta da 'yanci na dabbanci wanda bai da wani tsari na lura da kulawa. saboda haka gini akan wannan 'yanci zai bawa kowa dama kamar haka:
1-'yancin yin tunani da bayyana ra'ayi tare da lura cikin hakan. allah ma'daukakin sarki yana cewa:" ya ku wa'danda kuka yi imani kubi allah da taqawa kuma ku fa'di magana madaidaiciya." suratul ahzab aya ta 70.
2-'yancin mallakar wani abu da kuma samun halal, allah ma'daukakin sarki yana cewa:
"kuma kada kuyi gorin abunda allah ya fifita sashenku dashi akan sashe, maza suna da rabo daga abunda tsirfanta, kuma mata suna da rabo daga abunda suka tsirfanta." suratul nisa'i aya ta 32.
3-'yancin ilimi da koyo, manzon allah (saw) yana cewa: "neman ilimi wajibi ne akan kowane musulmi." sahihu ibn majah.
4-'yancin amfanuwa da abunda allah ya sanya a wannan duniya na alkhayrai, allah ma'daukakin sarki yana cewa: "shi (allah) ya sanya muku 'kasa horarriya sai ku tafi cikin sasanninta, kuma zuwa gare shi ne tashi yake." suratul mulk aya ta 15.
★ Tabbatar da aminci gamamme wanda ya halatta ga abubuwa masu zuwa:
→ aminci akan addini ta hanyar rashin yin shirka da allah da kuma zuwa ibadarsa, allah ma'daukakin sarki yana cewa:"kuma ku ya'ki wa'danda suke ya'kanku acikin hanyar allah kuma kada kuyi tsokana lallai ne allah baya son masu tsokana." suratul baqara aya ta 190.
→ aminci akan ran 'dan adam, allah ma'daukakin sarki yana cewa: kuma wanda ya kashe wani mumini da ganganci to sakamakonsa jahannama yana madawwami acikinta kuma allah yayi fushi akansa kuma la'ance shi kuma yayi masa tattalin azaba mai girma." suratul nisa'i aya ta 93.
→ aminci akan dukiya, allah ma'daukakin sarki yana cewa: kada kuci dukiyoyinku a tsakaninku da 'karya kuma ku sadu da ita zuwa ga mahukunta domin kunci wani yanki daga dukiyoyin mutane da zunubi, alhali kuwa ku kuna sani." suratul baqara aya ta 188.
→ aminci abisa mutunci, allah ma'daukakin sarki yana cewa: " kuma kada ku kusanci zina lallai ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munanana ga zama hanya." suratul isra'i aya ta 32.
→aminci ga hankali ga barin sha'awace-sha'wace kamar giya da kayan shaye-shaye. allah ma'daukakin sarki yana cewa: "ya ku wa'danda kuka yi imani, abun sani kawai giya da caca rufe da kiban 'kuri'a 'kazanta ne daga aikin shai'dan sai ku nisance shi wa la'alla kuci nasara." suratul ma'idah aya ta 90.
★ Ji'bintar haqqoqii ta yadda musulunci ya wajabta haqqoqi tsakanin halittu abisa sassa'bawar matsayinsu/ matakansu domin ha'din kai ya tattaru gare su kuma amfanikan addini su tabbata gare su kuma al'amuransu na addini si daidaita to wannan ya kasu kashi biyu:
(a)    HAQQOQI KE'BANTATTU,
 Allah ma'daukakin sarki yana cewa: "kuma ku bautawa allah kuma kada ku ha'da wani dashi, kuma ga mahaifa kuyi kyautatawa, kuma ga ma'abocin zumunta da marayu da matalauta da maqobci macabocin kusanta da maqobci manianci d aboki. gefe da 'dan hanya d abunda hannayenku na dama suka mallaka lallai ne allah baya son wanda ya kasance mai taqama mai yawan alfahari." suratul nisa'i aya ta 36.

(b)    HAQQOQI GAMAMMU,:
Manzon allah (saw) yace: " kada kuyi hassada kada kuyi tanajushi kada kuyi 'kiyayya kada ku juya baya kada sashinku yayi ciniki akan cinikin sashenku, ku kasance bayin allah 'yan uwa, musulmi 'dan uwan musulmi ne kada ya zalunce sa kada ya wulaqanta shi kada ya qasqantar dashi tsoron allah yana nan (sai ya nuna qirjinsa sau uku) ya ishi mutum sharri ya qasqantar da 'dan uwansa musulmi, dukkanin musulmi haramun ne ya fitar da jinin 'dan uwansa da kuma dukiyarsa da kuma mutuncinsa." muslim ne ya ruwaito.
(tanajushi) shine mutum ya yabi hajarsa don ya siyar da ita ko kuma yayi 'kari acikin 'kimarta kuma baya son sayar da ita.
★ Rahama ta yadda ta tattara halittu daga cikinta:
→ jin'kai ga 'dan adam, manzon allah (saw) yana cewa: "masu jin'kan mutane allah yana jin'kansu ku ji'kan wanda suke 'kasa daku wanda suke sama zasu ji'kanku, zumunta wanda ya sadar da ita allah zai sadar dashi wanda kuma ya yanketa allah zai yankesa." ahmad da abu-dauda da hakim ne suka rawaito albani kuma ya inganta shi.
→ rahama jin'kai ga dabbobi, ta yadda jin'kai gare su ya zama sababi na gafarta zunubai da shiga aljannah, manzon allah (saw) yace: "lokacin da wani mutumin yakai makurar jin kishi sai ya shiga wata rijiya,sai yasha ruwan har ya koshi, yana fitowa sai yaga wani kare yana zaro harshenshi ta kai har yana cin qasa saboda tsananin jin kishi, sai mutumin yace a ranshi: lallai wannan karen yakai inda na kai sanda nake jin kishi, sai ya kara shiga rijiyar ya ciko takalminshi da ruwa, sai ya ba karen yasha kuma ya gode ma allah, sai ubangiji ya gafarta mai, sai sahabbai suka ce ya manzan allah har acikin dabbobi ma muna iya samun lada ?? sai annabi yace: acikin duk wata halitta mai hanta akwai aikin lada." bukhari da muslim suka ruwaito shi.
(yalhas) yana nishi da 'kyar ko yana fito da harshensa saboda tsananin qishin ruwa. (assara) ji'ka'k'kiyar 'kasa ko kuma gwaguyar 'kasa. (wa ina lana fil bahaimu ajran) shin an samu lada a shayar da dabbobi da kuma kyautata musu. (fi kulli kabidin) acikin kyaitatawa ga duk wanda yake cikin qunci. (radbatun) a mayar da wani abu 'danye bayan ya bushe.
★ yin shawara ta yadda ya umurci mabiyansa ya ri'ke hakan tsari gare su acikin dukkanin al'amuran addini dana duniya na ciki da na waje, allah ma'daukakin sarki yana cewa: saboda wata rahama ce daga allah kayi sanyin hali agare su kuma da ka kasance mai fushi mai kaurin zuciya da sun watse daga gefenka, sai kayi yafevmusu laifinsu kuma ka nema musu gafara kuma kayi shawara dasu acikin al'amarin, sannan kuma idan kayi niyyar zartarwa toh ka dogara ga allah lallai ne allah yana son masu tawakkali." suratul ali-imran aya ta 159.
★ daidaito tsakanin mutane baki 'daya a tsakanin halittarsi mazansu da matansu farinsu da ba'kinsu larabawansu da wa'danda ba larabawa ba, babu banbanci a tsakaninsu sai dai wanda yafi wani taqawa. allah ma'daukakin sarki yana cewa: "ya ku mutane, kubi ubangijinku da taqawa wanda ya halicce ku daga rai guda kuma ya halitta daga gare shi, ma'auransa kuma ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata, kuma kubi allah da taqawa wanda kuke roqon juna da sunan shi da kuma zumunta, lallai ne allah ya kasance akanku mai tsaro ne." suratul nisa'i aya ta 1.
★ gamammen adalci ga rai da kuma mutane, allah ma'daukakin sarki yana cewa:" lallai allah na yin umurni da adalci da kyautatawa da baiwa ma'abocin zumunta kuma yana hani ga alfasha da abunda aka 'ki da rarrabe jama'a yana yi muku garga'di tsammaninku kuna tunawa." suratul nahli aya ta 90.
★ yin aminci gamamme akan matakin ciki da na waje, manzon allah (saw) yana cewa:" shin bana baku labarin mumini ba shine wanda mutane suka aminta dashi akan dukiyarsu da rayukansu, musulmi shine wanda mutane suka ku'buta daga harshensa da kuma hannunsaai jihadi kuma shine wanda yaqi ransa wajen yiwa allah biyayya, mai hijira kuma shine wanda ya 'kauracewa zinubai da sa'bo." sahihi ne hadisin ibn majah ya fitar dashi da ibn hibban (assahiha 549).
★ kwa'daitarwa da yin aiki da kuma samun da'da'da, manzon allah (saw) yana cewa:" 'dayanku ya 'dauki igiyarsa yaje yayi kirare ya sayar dasu, allah ya karesa ta dalilin wa'dannan kiraren kada mutuncin fuskarsa ya gushe kuma ya qasqantar da kansa da tambayar mutane, hakan yafi alkhayri gare shi akan ya tambayi mutane su bashi ko su hanashi." bukhari ne ya ruwaito.
)fa kayya fallahu biha wajhahu) mutane su hanasa kuma allah ya karesa ta dalilin yin tambaya.
★ yin tsafta koyarwar musulunci tana kwa'daitarwa da yinta kuma tana umurni da ita ta hanyar wasu halaye daga cikinsu:
→ tsaftace baki bayan cin abinci da kuma lura da tsaftar haqora ta hanyar kwa'daitarwa da yin aswaki, saboda fa'din manzon allah (saw): "ba don kada na tsanantawa al'ummata ba, da na umurce su da yin aswaki yayin ko wace sallah." musulm ne ya ruwaito.
→ gusarwa da tsaftace abunda sha'aninsa ne ya kasance matsaya da mstabbata na 'kwayoyin cuta da kuma dukkanin dau'duka, manzon allah (saw) yana cewa:"sunnoni biyar: yin kaciya, da aske gashin gaba, da cire gashin hammata da rage gashin baki da yanke farce." muttafaqun alaihi.
)al-istihidadu) aske gashin gaba, shine gashin da ke kewaye da farjin namiji ko mace. (al-ibdu) hamnata. (taqleem) an samo kalmar ne daga qallama shine yankewa ko ragewa.
→ tsaftace abunda ke fita daga mafita guda biyu (fitsari da bayan gida) salman (ra) yana cewa:"manzon allah (saw) ya hanemu mu fuskanci alqibla domin yin fitsari ko bayan gari, ko kuma muyi tsarki da hannun dama ko kuma muyi tsarki da dutse 'kasa da guda uku, ko kuma muyi tsarki da kashin dabbobi ko 'kashi." muslim ya ruwaito shi.
→ sanya kaya masu kyau masu tsafta da qamshi mai da'di, allah ma'daukakin sarki yace:" ya 'dan adam ku riqi qawarku a wurin kowane masallaci." suratul a'araf aya ta 31.
★ tsarki ta yadda da yawa cikin ibadu suke kewayawa akanta to kaso biyu ce: (hissiyatun) wadda za'a iya riskarta da five sense organs. (ma'anawiyya) wadda ba za'a iya riskarta da five sense organs ba sai dai a risketa ta hanyar hankali ko qwaqwalwa:
1-daharatul hissiyahu: ita ce tsaftar jiki da tsarkake shi daga najasa da hadasi, ta yadda aka sanya hakan ya zamto shara'din inganci da kuma amsar wasu ibadu, kuma aka sanya alwala daga cikin sharu'dan ingancin salkah wadda musulmi yake yinta sau biyar a kowane dare da yini, manzon allah (saw) yana cewa: baza a kar'bi sallah babu tsarki ba ko kuma sadakar da akayi guluwi acikinta (wato akayi ha'inci acikin ganima)." muslim ya ruwaito.
)la yaqbalallahu) kar'bar allah ga aiki shine yardarsa ga wannan aikin da kuma bada lada ga aikin, rashin kar'barsa ga aiki kuma shine rashin bada lada saboda aikin. (illa bi 'duhurin) a'd'duhuru da yiwa 'da'un damma yansma nufin aiki mai tsarki shi ake nufi anan, amma idan akayi wa 'da'un fataha to suna ne na kalma lamar ruwa da 'kasa. (min gululin) shine ha'inci acikin dukiyar ganima abunda dai ake nufi anan yin hakan haramun ne.
an wajabta kuma yin wanka saboda janaba da ta samu mutum ta hanyar amfani da ruwa wajen wankan, saboda fa'din allah ma'daukakin sarki yace: kuma in kun kasance kuna da janaba kuyi tsarki." suratul ma'idah aya ta 60.
kuma aka sanya yin wanka ya zamto sunnah mai qarfi ga wasu alamomi na addini kamar: sallar juma'a da kuma idi guda biyu (babba da qarama) da hajji da umra.... da sauransu.
2. a'd'daharatul ma'anawiyya shine ta hanyar tsarkake zuciya daga shirka, allah ma'daukakin sarkk yana cewa:"kuma ku bautawa allah kuma kada ku ha'da shi da komai." Suratul Nisai aya ta 36.
→ ko kuma yin riya, allah ma'daukakin sarki yana cewa: "to bone ya tabbata ga masallata* wa'danda suke masu shagala daga sallarsu* wa'danda suke yin riya (ga ayyukansu)* kuma suna hana taimako." suratul ma'un aya ta 4,5,6,7.
→ ko kuma jiji da kai, allah ma'daukakin sarki yana cewa: " kada ka karkatar da kundunkukinka ga mutane kada kayi tafiya acikin 'kasa kana mai nuna fa'din rai, lallai allah baya son dukkan mai taqama mai alfahari." suratul luqman aya ta 18.
→ko kuma girman kai, manzon allah (saw) yana cewa: "wanda ya kasance da akwai koda kwatankwacin zarra na girman kai a zuciyarsa bazai shiga aljannah ba" sai wani mutum yace: ya manzon allah mutum yana son tufafinsa ya zama mai kyau, sai manzon allah (saw) yace: "lallai allah mai kyaune kuma yana son kyau, abunda ake nufi da girman kai shin qin gaskiya (mai da magana mai kaushi ga wanda ya fa'da ma gaskiya) da wulaqanta mutane (wulaqanta su)." muslim ne ya ruwaito.
)al-ba'daru) girman kai ga gaskiya da qin amsarta. (al-gamdu) wulaqantarwa da qasqantarwa.

15- HALAYYA/HALAYE
musulunci addini ne na hakaye na karamci da kuma cika kyawunsa, manzon allah (saw) yana cewa: kawai dai an aiko ni ne don na cika halaye na karamci (a wata ruwayar kuma kyawawa)." ahmad ya ruwaito da kuma bukhari acikin adabul mufrad albani kuma ya inganta shi.
babu wata 'dabi'a tagari face musulunci yayi umurni da ita kuma ya kwa'daitar da aikatata, hakanan kuma babu wata 'dabi'a mummuna face musulunci yayi hani da ita kuma ya tsawatar akanta, kuma yana bayyana tsari wanda musulmi zai tafiyar da rayuwa cikin alaqarsa da al'ummarsa da kuma sauran al'umma, manzon allah (saw) yana cewa: kaji tsoron haramtattun ayyuka zaka zama mafi ibadar mutane ka kuma yarda da abunda allah ya kasa ya baka zaka zamto mafi wadatar mutane ka kyautatawa maqobcinka zaka kasance mumini ka sowa mutane abunda kake sowa kanka zaka kasance musulmi kada ka yawaita dariya saboda yawan dariya yana kashe zuciya." sahihi ne hadisin tirmizi ne ya fitar dashi da ahmad.
wannan tafarkin zai tabbatar da zukata masu laifuka idan suka jajirce akanshi wato zai chanzasu daga zunubi zuwa lada.
shin kunsan waye matsiyaci ? sai suka ce: matsiyaci acikinmu shine wanda bai da dirhami ko 'daya kuma bai da wani qadara, sai manzon allah (saw) yace: matsiyaci daga cikin al'ummata shine wanda zai zo ranar alqiyama da sallah cikakkiya da zakka da azumi amma ya zalunci wancan yayiwa wannan qazafi ya fitar da jinin wannan ya doki wannan, sai a 'dauki ladansa a biya wannan a biya wancan idan ladarsa ya qare kafin a gama biya, wa'danda ya zalunta sai a ringa 'daukan zunubansu ana jibga masa sannan daga qarshe a saka shi a wuta." muslim ruwaito shi.
musulunci ta hanyar wannan tsarin yana da manufar samar da al'umma masu qulla alaqa kuma masu jinqan juna, kuma mai tsayar da soyayya da gabatar da amfani ga waninka, musulunci addini ne na 'dabi'u da ladabi da abubuwa da ya qunsa baki 'daya, allah ma'daukakin sarki yana cewa: " ya ku wa'danda kuka yi imani kada wa'dansu mutane suyi izgili game da wa'dansu mutane mai yuwuwa ne (abun yiwa izgili) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin) kuma wa'dansu mata kada suyi izgilil ga wa'dansu matan mai yuwa ne su kasance mafifita daga gare su, kuma kada ku aibanta kanku,kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na laqabobi, tir da suna na fasiqanci a bayan imani, wanda bai tuba ba, to wa'dannan sune azzalumai* ya ku wa'danda suka yi imani ku nisanci abu mai yawa na zato, lallai sashen zato laifi ne, kuma kada kuyi rahoto, kuma kada sashenku yayi giban sashe, shin 'dayanku nason yaci naman 'dan uwansa yana matacce? to ku qishi (cin naman) kuma kubi allah da taqawa lallai allah mai kar'ban tuba ne mai jinqai." suratul hujurat aya ta 11-12.
musulunci addinin amana ne gaba 'dayansa, tsakaninsa da tsakanin ubangijinsa da kuma tsakaninsa da mutane, allah ma'daukakin sarki yana cewa: "lallai ne allah yana umurtarku bayar da amanoni zuwa ga masu su kuma idan kunyi hukunci a tsakanin mutane kuyi hukunci da adalci lallai ne allah madallah da abunda yake yi muku wa'azi dashi, lallai allah ya kasance mai jine mai gani." suratul nisa'i aya ta 58.
musulunci addinin gaskiya ne, allah ma'daukakin sarki yana cewa: "ya ku wa'danda suka yi imani kubi allah da taqawa kuma ku kasance tare da masu gaskiya." suratul tauba aya ta 119.
musulunci addinin cika alqawari ne, allah ma'daukakin sarki yana cewa: "ya ku wa'danda suka yi imani ku cika alqawaura, an halatta muku dubbobin jin da'di face abunda ake karantawa akanku, ba kuna masu halattar da farauta ba alhali kuwa kuna masu harama lallai ne allah yans hukunta abunda yake nufi." suratul ma'dah aya ta 1.
musulunci addinin sauqi ne da tausayawa da sauqaqawa, manzon allah (saw) yace: "lallai sauqi baya kasancewa acikin wani abu face sai ya qawata shi hakanan baza'a ciresa ba face ya munana shi." muslim ya ruwaito.
musulunci addinin soyayya ne da ha'din kai, manzon allah (saw) yana cewa: "imanin 'dayanku bazai cika ba har sai ya sowa 'dan uwansa abunda yake sowa kansa." bukhari da muslim suka ruwaito shi.
shari'ar musulunci ta fa'da'da ya'da wa'dannan falaloli da 'dabi'u da ladabai a al'umma ta hanyar wasu hanyoyi daga cikinsu akwai abubuwa masu zuwa:
1-umurni da kyakykyawa da hani da mummuna, allah ma'daukakin sarki yana cewa: " kuma ku kasance mafi alkhayrin wannan al'umma wadda aka fitar ga mutane kuna umurni ga alkhayri kuma kuna hani daga abunda ake 'ki kuma kuna imani da allah kuma da mutanen littafi sunyi imani lallai ne da (haka) ya kasance mafi alkhayri agare su, daga cikinsu akwai muminai, kuma mafi yawansu fasiqai ne." suratul ali-imran aya ta 110.
2-nasiha da yin wasiya da bayyana ra'ayi da shawara ta gaskiya, allah ma'daukakin sarki yace: " ina rantsuwa da zamani* lallai ne mutum yana acikin hasara* face wa'danda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na qwarai, kuma suka yiwa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yiwa juna wasiyya da yin haquri (su kan basa cikin hasara)." suratul asri aya ta 1-3.
YA MAI GIRMA MAI KARATU:

lallai biyayya ga addinin musilunci kyauta ce ta Allah ba wanda yake samun damar hakan sai dai wanda allah ya datar dashi, kayi kwa'dayi ka kasance daga cikin wa'danban datattun don samun damar biyayya ga wannan addini gangariya wanda allah baya kar'ban bautawa waninsa, kar ka tsaya a iya wannan ka'dai, bari dai ka kasance kuma mai qira zuwa gare shi, to shigarka wannan addini ya zama dole ka isar dashi ga wanda ya bayyana shi ga wanda bai isa gare sa ba, tare da haqiqannin yadda yake ga wanda yayi masa fahimta maras kyau, manzon allah (saw) yana cew: " ku isar daga gare ni ko da aya 'daya ce." sahihul bukhari.
acikin tunani na lallai cewa abubuwa da aka ambata na wa'danda suka ke'banta da musulunci kwai acikin wannan littafin yana rainon cewa lallai ka motsa asalin hankalinka tsaftacecce kuma mai inganci domin sanin wannan addinin, kuma da gusar da duk wani datti ko mayafin da ya rufe zuciya wanda 'kofofin ya'da labarai masau 'batar da mutane suke, ta yanda ba abunda zaka iya gani wajen siffanta musulunci sai koma baya da ta'addanci ko kuma wasu al'amura wanda ba ruwan wasu musulmai dashi wa'danda basu san komai ba cikin musulunci sai sunan shi, sune suka zama sanadiyyar gudun musulunci da kafirai suke yi, tare da addu'ata agareka ta gaskiya domin allah ya haskaka tunaninka kuma ya nuna maka gaskiya kuma ya azurtaka da binta, kuma ya nuna maka 'barna 'barna ce kuma ya baka ikon gudunta.


BUSHARA:

mai karatu mai girma lallai na daga cikin kyawawan abubuwa na musulunci cewa duk wanda ya riqesa wad'anda ba musulmi ba zai samu ladansa sau biyu saboda imaninsa da annabinsa da kuma imaninsa da saqon manzon allah (saw) allah ma'daukakin sarki yana cewa:
" wa'danda muka basu littafi daga gabanninsa (alqur'ani), su masu imani ne dashi* kuma idan ana karanta shi akansu, sai suce munyi imani da shi, lallai shine gaskiya daga ubangijinmu, lallai mu mun kasance a gabanninsa masu sallamawa* wa'dancan ana basu ladarsu sau biyu, saboda haqurin da suka yi, kuma da kyautatawa suna tunku'de munanawa, kuma daga abunda muka azurta su suna ciyarwa." suratul qasas aya ta 52,53,54.
riqon ishara ta biyu shine allah yana shafe dukkanin zunubai da mutum yayi kafin ya shigo musulunci, saboda fa'din manzon allah (saw): " musulunci yana rushe duk abunda ke gabanninsa ....." muslim ya ruwaito.
riqi bushara ta uku ita ce allah yana chanzawa mutum zunubansa da yayi da lada, wannan falalar allah ce da yake bawa wanda yaga dama, allah ma'daukakin sarki yana cewa:
"kuma wa'danda basu qiran wani ubangiji tare da allah, kuma basu kashe rai wanda allah ya haramta face da hakki ba, kuma basu yi zina ba, kuma wanda ya aikata wancan zai gamu da laifuffuka* a ri'banya masa azaba a ranar qiyama, kuma ya tabbata acikinta yana wulaqantacce* sai wanda ya tuba kuma yayi imani, kuma ya aikata aiki na qwarai, to wa'dancan allah yana musanya miyagun ayyukansu da masu kyau, allah ya kasance mai gafara mai jinqai." suratul furqan aya ta 68,69,70.
dama ce mai kyau ga wanda ya riba ce ta, ina jan kunnenka da jinkirta tuba, mai kaifin basira shine wanda ya kusantar da ransa yayi aiki don abunda zai so bayan mutuwa, gajiyayye shine wanda ya biyewa zuciyarsa da son ransa da kuma burace-burace.
tsira da amincin allah su tabbata ga annabinmu muhammad da iyalansa da sahabbansa baki daya, godiya ta tabbata ga Allah ubangijin halittu baki daya.


 
www.islamland.com