SOYAYYA TA MUSULUNCI

SOYAYYA TA MUSULUNCI

SOYAYYA TA MUSULUNCI
الرومانسية الإسلامية بلغة الهوسا

 

Dr. ‘Abd Ar-Rahman bin ‘Abd Al-Karim Ash-Sheha
د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة

Fassara:
EUROPEAN ISLAMIC RESEARCH CENTER (EIRC)
المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية
& Muhammad Khamis
Wanda ya bibiyi fassara
& Hashim Muhammad Sani


WWW.ISLAMLAND.COM

 

 

GABATARWA

Da sunan Allah me rahama me jin kai.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da iyalan sa da sahabban sa baki daya.
    Kasancewar magana akan soyayya a cikin musulunci ga mata, ya zama dole ya kasance Muhammad manzon Allah s.a.w shine tushen wannan magana kasancewar sa manzon allah wanda aka aiko shi zuwa ga mutune baki dayan su domin ya karantar dasu abunda Allah ya shar'anta kuma su samu ginshiki da dabi'un sa, shine abun koyi ga musulmai wanda ya wajaba a garesu su bishi da kuma koyi da sunnar sa domin aiki da umurnin Allah madaukaki wanda yake cewa:
“ hakika ya kasance kuna da abun koyi me kyau daga manzon Allah s.w.a ga wanda ya kasance yana kwadayin haduwa da Allah da rana ta karshe kuma ya ambaci Allah dayawa ” suratul ahzab ayata 21.
    Shine me isarwa game da Allah saboda haka ne babu wani abu daya buya ga musulmai game da al'amuran rayuwan sa baki daya kananan su da manyan su, ke bantaccen su da game garin su face an sansu kuma ya shahara a tsakanin su kuma a rawaito shi daga wannan jama'ar zuwa wata jama'ar kasancewar maganganun sa da ayyukan sa hukunce hukunce ne da shari'a wanda ta hanyar su ne musulmi yake sanin addinin sa wanda yake isar dashi zuwa ga soyayyar Allah da yardan sa da aljannar sa, Allah madaukaki yace:
“ kace masu idan kun kasance kuna son Allah to ku bini Allah zai so ku kuma zai gafarta maku zunuban ku, Allah ya kasance me gafara kuma me rahama (31) ” . Surat Aal ‘Imran ayata 31
    Lallai ginshikin musulunci shine soyayya wanda zata sanyaka ta sanadiyyar ta kayi biyayya ga wanda kake so kuma kabi umurnin sa da kuma hanuwa daga abunda ya hana , kuma kayi kokari matukar iyawan ka na ganin ka kusance sa ta hanyar aikata abuuwan da yake so, lallai mafi girman so da daukaka shine son Allah madaukaki wacce ta hanyar hakan ne ake samun damar fadakar da musulmi halaye na gari wanda zai rabu son kai kuma ya samu daukaka da alamomin sa sai ya yada soyayya da rahama ga halittun Allah ba tare da jiran wani ladaba na kudi daga gare su, sai ya rabu da son kai wacce ta ginu akan maslaha da amfanin karon kan mutum shi kadai, daga ita kuma sai soyayyar manzon Allah s.a.w ya biyo baya soyayya tsarkakakkiya wacce ake gabatar da ita akan son ran mutum da dukiya da yara kasancewar sa shine sababin shiriya da kuma nuni zuwa ga Allah da kuma addini na gari wanda Allah ya sanya shi tsira daga wuta ga duk wanda ya bishi da kuma shiga aljanna saboda hakane ya cancanci wannan matsayi da daraja me girma tare kuma da ajiye shi a matsayin da Allah ya ajiye shi watan matsayi na bauta da Kankan dakai ga Allah, Allah madaukaki yana cewa:
“ kace idan ya kasance cewa iyayen ku da yaran ku da ‘yan uwan ku da matayen ku da dangin ku da dukiyoyin ku wanda kuka tara da kasuwancin ku wanda kuke tsoron karyewan sa da kuma gidajen ku wanda suke burgeku da son rayuwa a cikin su sunfi soyuwa a gare ku sama da Allah da manzon sa da kuma jihadi domin daukaka addinin sa to ku saurara ku jira har Allah yazo maku da al'amarin sa, lallai Allah baya shiryar da mutane fasikai ” suratul taubah ayata 24.
    Duk wanda ya qudurce cewa musulunci addini ne na tsanani da kausasawa to hakika yayi kuskure, gaskiyar itace musulunci addini ne wanda ya kunshi komai watan ma'ana be bar kananan abubuwa ba ko kuma manya na rayuwan musulmi shin hakan ya shafi kudi ne ko kuma zuciya face ya fadakar da ita fadakarwa me kyau ya kuma sanyata a wurinta daya dace, musulunci ba addinin aqida bane da hukunce hukunce da dabi'u bane kadai a'a addini ne kuma har wayau na soyayya ta fuskar fahimtar sa a musulunce wanda ya kunshi komai hakan ya tattaru cikin so da kauna da rahama da tausayi da kyautatawa da dajara alamomi da dabi'u masu daraja da mu'amala masu kyau ga dukkanin abunda yake kewaye da mutum cikin wannan duniya na halittu bawai kawai ya takaitu bane akan wani bangare guda bane wanda ya tattaru tsakanin namiji da mace na mu'amala na magana ko kuma na aiki kawai, baya cikin soyayya ka kasance me kyakyawan mu'amala ga wanda kakeso kadai ba da kuma munana mu'amala ga wanin sa, saboda haka ne zamu kawo wasu daga cikin siffofi da dabi'u na musulmi, har mu gane ma'anar so cikin musulunci ga dukkanin wanda yake kewaye da musulmi.


Dr. ‘Abd Ar-Rahman bin ‘Abd Al-Karim Ash-Sheha
 
WWW.ISLAMLAND.COM
[email protected]

HALAYEN MUSULMI

•    Musulmi shine wanda mutane suka amintu dashi aminci wanda ya kunshi komai akan rayukan su da dukiyoyin su da mutuncin su dashi saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa:
“ shin na baku labarin wanene mumini shine wanda mutane suka amintu dashi akan dukiyar su da rayukan su shi kuma musulmi shien wanda mutane suka tsire daga harshen sa da hannun sa ” . Hadisi ne ingantacce Ahmad da Ibn hibban ne suka rawaito shi (al sahihah) (549).
•    Bawannan bane kawai musulmi shine wanda yakeson alheri kuma yake yadashi ga mutane kuma yana aiki tukuru domin isar dashi zuwa gare su ba tare da amsan wani hasafi ba daga garesu akan hakan, saboda fadin sa manzon Allah s.a.w:
“ ka kiyaye abubuwan da Allah yayi umurni dasu da kuma wanda yayi hani dasu zaka zama cikin mutane masu bauta, ka yarda da abunda Allah ya baka zaka zama mafi arzikin mutane kuma ka kyautata wa makwabcin ka zaka zama mumini, kasoma mutane abunda kake soma kanka zaka zama musulmi… ” (Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito shi kuma albani ya ingantashi).
•    Musulmi shine wanda yake kasancewa me adalci a kansa da kuma al'ummar sa hatta makiyan sa, baya daukan fansa akan wani da zunubin wanin sa manzon Allah s.a.w ya kasance idan zai tura rundunar yaki cikin musulmai zuwa ga mushrikai wanda suka cutar dashi kuma suka fitar dashi daga gidan sa da kuma taimakawa wasu akan fitar dashi suka kuma kashe sahabban sa da azabtar da duk wanda yabi addinin sa yanayin wasiyya ga shugaban wannan runduna gareshi karan kansa da jin tsoron Allah da kuma wanda suke tare dashi cikin musulmai da alheri. Sa'annan yace (kuyi yaki da sunan Allah domin Allah. Ku yaki wanda ya kafurcewa Allah. Kuyi yaki kada ku wuce gona da iri kuma kada kuyi yaudara kuma kada kuyi gunduwa gunduwa kuma kada ku kashe yara kanana) (sahihu muslim)
•    Musulmi shine wanda yake kiyaye mahallin da yake kewaye dashi da dukkanin abunda ke cikinta na dabbobi, baya yarda da azabtar da ita domin kuwa an wuce gaban manzon Allah s.a.w da wani jaki wanda aka masa zane a fuskar sa sai yace:
“ Shin be isa gare ku bane cewa na tsinema wanda yayi ma dabba zane a fuskanta ko kuma ya duke ta a fuska? ” . (Sunan Abi dawud kuma albani ya inganta shi.)
Kuma yana mu'amala da ita da tausayi da rahama, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa: “ manzon Allah s.a.w yana karkatawa mage kwarya tasha ruwa ” . (hadisi ne ingantacce) dayalisi ne rawaito shi kuma yana cikin littafin sahihul jami'u 4958.
Kuma yana kiyaye abunda dake cikinta na tsuntsaye baya tsorata su kuma baya farautan su haka kawai ba tare da wani amfani ba, Ibn mas'ud Allah ya kara masa yarda yana cewa mun kasance tare da manzon Allah s.a.w cikin tafiya sai ya tafi domin biyan wata bukatar sa sai mukaga wata tsuntsuwa karama tare da ita akwai jaririyan ta sai muka dau wannan jaririya nata sai wannan tsuntsuwa tazo tana bude fuka fukanta tana goga su a kasa sai manzon Allah s.a.w yazo sai yace: “ wanene ya tinzira wannan da jaririnta? Ku mayar mata da jaririnta ” sai kuma yaga wani gidan tururuwa wanda muka kona sai yace:
“ wanene ya kona wannan? ” sai mukace mune sai yace: “ lallai baya halatta yin azaba da wuta sai ga ubangijin wutan ” (abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi).
•     Musulmi shine wanda yake kiyaye wuraren mutane da wurin shakatawar su, baya samar da wani abu a wurin wanda zai hana su amfanuwa dashi ta hanyar jefar da bola a wuraren da makamantan su, saboda faduin manzon Allah s.a.w:
“ ku kiyaye abunda suke jawo tsinuwan mutane: shine wanda yake bayan gida a kan hanyar mutane ko kuma a wurin inuwar su ” (abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi).
•    Hasalima musulmi shine wanda yake kawar da dukkanin wani abu wanda yake cutar da mutane saboda fadin manzon Allah s.a.w:
“ .. kawar da cuta daga kan hanya sadaka ce ” (abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi).
•    Musulmi shine wanda yake kiyaye abunda yake da amfani ga muhalli da mutane kamar bishiya saboda fadin manzon Allah s.a.w: “ kada ka sare bishiyar da take iyaiya, kuma kada ka kashe dabbar da baka da bukatar ta, kuma ka kiyaye cutar da mumini ” (abu dawud ne ya rawaito shi cikin littafin “ marasil ” , da Sa'id dan Mansur cikin littafin san a “ sunan ”).
•    Musulmi shine wanda yake kira zuwa ga kiyaye muhalli ta hanyar fadakarwa akan dasa bishiya da gyara kewayenta, saboda fadin manzon Allah s.a.w:
“ da ace duniya zata tashi a hannun wanin ku akwai karamin bishiyar da binu wanda ta fado daga jikin mamanta to idan ya samu daman shukata ya shukata kafin duniyar ta tashi ” (buhari ne ya rawaito shi).
•    Musulmi shine wanda yake kiyaye ruwa baya lallatashi ko kuma sanya masa datti da kazanta, Jabir Allah ya kara masa yarda yana cewa:
“ manzon Allah s.a.w yayi hani da mutum yayi fitsari a cikin ruwan da baya tafiya ” (muslim ne ya rawaito shi).
Yana kuma yin kokari wurin kiyaye ta da kuma yi mata dukkan hidima wanda take bukata, saboda fadin manzon Allah s.a.w:
“ musulmai suna tarayya cikin abubuwa uku: tsirrai ko karare, da ruwa da kuma wuta ” hadisi ne ingantacce (ahmada ne da abu dawud suka rawaito shi).
Yana kuma yin kokari iyakan iyawan sa domin kiyaye hanyoyin samun ruwa da kuma raya su domin al'umma su amfanu da ita da dabbobi da shuka ta hanyar rashin yin almubazaranci da bannatar da ita ta hanyar da bashi da amfani saboda fadin manzon Allah s.a.w ga Sa'ad lokacin daya wuceshi yana alwalla:
“ wannan wane irin barnan ruwa ne? ” sai yace: yanzu akwai barnan ruwa ne a cikin alwalla, sai yace: “ eh akwai koda kuwa ka kasance ne a wurin rafi me gudana ” . (Ibn majjah ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi).
Kasancewa an umurce mu dabin Manzon Allah Muhammad s.a.w wanda ya tattara halaye da dabi'u masu daraja na dukkafin ma'ana wanda ya kunshi haka da mu'amala me kyau da dukkanin abunda kewaye dashi na halittu wannan bin da koyi ya zama aqida ga musulmi wanda yayi imani da ita kuma yake kokarin aiwatar da ita cikin ayyukan san a rayuwan sa domin neman yardan Allah, Allah madaukaki yace:
“ kace masu idan kun kasance kuna son Allah to ku bini Allah zai so ku kuma zai gafarta maku zunuban ku, Allah ya kasance me gafara ne me rahama (31) ” Surat Aal ‘Imran ayata 31


Wannan shine musulunci

    Wannan shine musulunci soyayya ga dukkanin abunda Allah ya halitta wanda ake aiwatar dashi ta hanyar umurnin Allah mutum kamar yadda yake raya gangan jikin sa daci da shah aka yake raya zuciyar sa da addini wanda yake daukaka da ita cikin duniyan falala ya kuma nisanta shi daga cikin duniyar dabbobi da sha'awa ya kuma tace alamomin sa , a cikin wannan littafi karami zamuyi magana akan bangare guda cikin bangarori na soyayya cikin rayuwan manzon Allah s.a.w tare da mata wanda aiko shi ya zama haske me kyau ga duniya baki dayanta da kuma mata a kebance ya daukaka darajarta ya kuma wajabta girmamata ya kuma kawar da zulumci akanta, hakika mata sun kasance gabanin zuwan musulunci suna rayuwa ne a mataki na can kasa yadda Umar dan kaddab Allah ya kara masa yarda shugaban muminai kuma khalifa na biyu na manzon Allah s.a.w ya sawwarata cikin fadin sa cewa:
“ wallahi mun kasance cikin jahiliyya bama daukan mace a bakin komai, har zuwa lokacin da Allah ya saukar da abunda ya yasaukar akan su ya kuma raba ya basu abun da zai basu na gado ” . (Buhari da muslim ne suka rawaito shi).

A lokacin da musulunci yazo fadakarwan sa akan mata ya kaance bayyananne ya kuma bayyana cewa daga cikin mafi alherin maza da dabi'u masu kyau shine kyautata mu'amala tare da mata, manzon Allah s.a.w yace:
“ mafi alherin ku shine wanda yafi alheri ga mata ” (hakim ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi).
     Sai mace ta rabautu da daraja me girma a karkashin musulunci da kuma matsayi kololuwa wanda be ba maza ba kuma wasu mata na wata al'umma na daban basu same shi ba, manzon Allah s.a.w ya kasance yana son mace a matsayin san a mutum, sai manzon Allah s.a.w yace:
“ an samun son wannan abubuwan a cikin kayan duniya: mata da turare kuma an sanya mun natsuwana da farin cikin rayuwa na a cikin sallah ” (Ahmad da nasa'I da Baihaki ne suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi cikin littafin mishkat 5261).
Soyayya wacce take zagaye da tausayi da so da tausasawa yadda yace s.a.w:
“ ….. ina maku wasiyya na kyautatawa ga mata ” (muslim ne ya rawaito shi).
Sannan kuma an kare mata hakkokin ta daga lalace aka kumayi umurni da yin mu'amala dasu me kyau da karrama su da kuma hana wulakanta su, kuma tana kiransa da yi mata taushi tare da ita da kuma darajata, manzon Allah s.a.w yana cewa:
“ wanda yafi cikin imani cikin muminai shine wanda yafisu kyaukyawan dabi'u, kuma zababben mu shine zababbe ga matan sa ” Tirmizi ne ya rawaito shi, kuma yace: (hadisi ne me kyau kuma ingantacce) kuma albani ya ingantashi.
Sai ya daurata a matsayinta wanda aka haramta mata gabanin zuwan musulunci ya daidaita ta da maza cikin komai sai abubuwan da shari'a ya kebance kamar gado da bada sheda da sauran su cikin abubuwan da dalilai suka nuna akan hakan ya sanyata ta zama abokiyar na miji kuma rabin jikin sa wanda yake samun kamala da ita, sai manzon Allah s.a.w yace:
“ lallai mata iyan’uwan maza ne ” Ahmad da abu dawud da tirmizi ne suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
Hasalima manzon Allah s.a.w ya sanya ta cikin mafi falalar kyautan Allah cikin wannan duniya sai yace:
“ duniya jin dadi ne kuma mafi alherin jin dadin duniya itace mace ta gari ” muslim ne ya rawaito shi.
Ya kuma sanyata mubudin farin ciki cikin wannan duniya, sai yace:
“ abubuwa hudu suna cikin farin ciki, mace ta gari da wurin zama yalwatacce da makwabci na gari da abun hawa me lafiya ” Ibn hibban da hakim ne suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi cikin “ littafin al sahihah ” (282).
Ya kuma sanyata s.a.w rabin addinin mutum itace mace ta gari wacce take sababi wurin gfadakar da mijinta fadakarwa na gari sai yace:
“ idan mutum yayi aure to hakika ya ciki rabin addinin sa sai yaji tsoron Allah cikin sauran rabin ” baihaki ne ya rawaito shi kuma yana cikin sahihul jami'u: 6148.
Kuma kamar yadda manzon Allah s.a.w yaso mace a matsayinta na mutum ya kuma so ta a matsayin uwa sai ya wajabta girmamata da kuma wajabta mata biyayya da kuma damuwa da kula da ita ya kuma sanya hakan cikin sababi na shiga aljanna, hakika Jahimatu al salami yazo wurin manzon Allah s.a.w sai yace masa:
“ ya manzon Allah nazo ne neman shawararka inason zuwa yaki, sai yace masa: kanada mahaifiya? Sai yace: eh sai yace: kaje ka lazimce ta domin lallai aljannarka tana karkashin tafikan kafarta ne ”. nisa'I ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.
Ya kuma sanyata tana gaba da namiji wurin biyayya da sada zumunci yadda hakan ya kasance umurnin manzon Allah s.a.w ga mutumin daya tambaye shi:
“ ya manzn Allah wanene mafi cancantan mutane ga mafi kyawun zamana? Sai yace: mahaufiyar ka, sai yace: sai kuma wa? Sai yace mahaifiyar ka, sai yace: sai kuma wa? Sai yace mahaifiyar ka, sai kuma wa? Sai yace: mahaifin ka ” buhari ne ya rawaito shi.
Kamar kuma yarda manzon Allah yaso mace a matsayin uwa ya kuma sota a matsayin mata, yadda yace ma Amru dan Aas lokacin daya tambaye shi:
“ wanene kafi so cikin mutane? sai yace: “ Aisha ” ,sai yace cikin maza fa? Sai yace: “ mahaifinta ” sai yace: sai kuma wa? Sai yace: “ Umar ” , sai ya irga maza sai nayi shiru saboda tsoron kada yasanya ni a karshen su ” . Buhari ne ya rawaito shi.
Kuma kamar yadda manzon Allah s.a.w yaso mace a matsayin mata yaso ta a matsayin diya, Aisha tana cewa Allah ya kara mata yarda:
“ bantaba ganin wani mutum ba wanda yaki kama da manzon Allah ta wurin dattaku da kama da shiriya cikin tsayuwarta da zamanta kamar fadima diyar manzon Allah s.a.w sai tace: ka kasance idan ta shiga wurin manzon Allah s.a.w sai ya tashi ya rungume ta sannan ya zaunar da ita a wurin zaman sa kuma manzon Allah s.a.w ya kasance idan ya shiga wurinta sai ta tashi daga wurin zamanta da rungume shi ta zaunar dashi a wurin zamanta… ” Tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
Wannan mu'amalar ta kwarai ga dukkanin mutane da kuma mata a kebance ya samu asali ne daga fadakarwan Allah ga dukkanin musulmai na tausayi da rangwame da tausasawa ga mata da kuma girmama su yadda yace:
“ … kuma ku zauna dasu da kyawawan dabi'u wanda aka sani, idan kun kyamace su to kusani fa sau dayawa kuna kyamatar abu kuma sai Allah ya sanya masa alheri me yawa ” surat an-nisa' ayata 19.
Ibn kasir yace cikin tafsirin wannan ayar: watan ku kyautata maganar ku a garesu sannan kuma ku kyautata ayyukan ku da adonku gwargwadon ikonku a garesu kamar yadda kuke son haka daga garesu, ka aikata kwatankwacin haka a gareta, kamar yadda Allah madaukaki yace:
“ suma suna da kwatankwacin abunda ke kan su na kyautatawa ” . [suratul bakar ayata: 228]

Kuma hakika sahabban manzon Allah s.a.w sun kasance suna rigegeniya wurin aiwatar da wannan manhaji da fadakarwa na Allah, wannan dan Abbas ne malamin wannan al'umma yana cewa:
“ lallai na ksance ina yin kwalliya ga matata kamar yadda takemun, kuma banason amsan hakkokina duka dake kanta saboda kada hakkokinta dake kaina ya wajaba akaina saboda Allah madaukaki yace: “ suma suna da kwatankwancin abunda suke dashi akan su na kyautatawa ” [suratul bakar ayata: 228]. Qurdubi an Ambato haka cikin littafin sa na Jami'un li ahkamul kur'an.


Wasiyyar mahaifi Musulmi ga dansa a daren angoncin sa

Lallai cefanen soyayya da kyautata mu'amala da tausayi da hakuri da mutane shine manhajin musulmi na gari wanda yake tafiya akan sa da kuma aiwatar dashi da aiki dashi da kuma tallar sa domin aiwatar da umurnin Allah, wanann shugaban Ahlussunah ne waljama'a yakeyima dansa wasiyya ranan angoncin sa yana sanar dashi hakkokin matar sa akansa da cewa:
“ ya kai dana ka sani fa bazaka taba samun farin ciki ba a gidan ka sai da wannan abubuwa guda goma wanda zaka rika yima matarka dan haka ka kiyaye su kuma ka himmatu dasu:
Na farko da na biyu:
Lallai mata suna son shiryarwa kuma suna son ka nuna masu soyayya a bayyane, kada kayima matarka rowan wannan, saboda idan kayi mata rowa zaka sanya shamaki ne tsakanin ka da ita na tsanani da kuma tawayan soyayya.
Na uku kuma:
Su mata suna kyaman namiji me tsanani mara sakin fuska kuma suna bautar da namiji me rauni da taushi saboda haka ka sanya ko wace siffa a wajenta saboda hakan yana kawo soyayya da natsuwar zuciya.
Na hudu:
Lallai mata suna son irin abunda miji yake so daga gare su na kyautata magana da sura da kuma tsafta na kaya da kamshi saboda haka ka kasance haka cikin dukkanin lokutan ka.
Na biyar:
Lallai gida mulki ne na mata kuma acikinsa ne takejin cewa lallai ita tana da gadara da akan kujeran mulkin ta kuma ita shugaba ce, saboda haka kashedin ka da ruguza wannan mallaka nasu wanda take rayuwa aciki, kuma kashedin ka dayin kokarin nesantar da ita daga wannan kujeran mulki, saboda idan ka aikata haka ka kwace mata mulkinta, kuma babu adawar da tafi adawa ga mutumin da zai kwace maka mulki koda kuwa ya bayyana maka akasin haka.
Na shida:
Lallai mace tana son ta mallaki mijinta ba tare da tayi asarar iyalanta ba, saboda haka kashedin ka da sanya kanka da iyalanta a ma'auni daya, kodai kai ko kuma iyan’uwanta, domin kuma koda ta zabe ka akan iyalanta to zata kasance cikin bakin ciki wanda zai rika haifar da gaba zuwa ga rayuwan ka na kullum.
Na bakwai:
Lallai mace an halicceta ne daga kasha karkatacce wannna kuma shine sirrin kyau dinta, da kuma sirrin jayuwa zuwa gareta wannan kuma ba aibu bane a gareta “ girakarkacewarta shi ne kyawan ta ” , kada kayi kokarin daura mata kaya me nauyi idan tayi kuskure domin kokarin gyara wannan lankwasa nata sai ka karyata kuma karyata shine sakinta, kuma kada ka kyaleta idan tayi kuskure sai ya kara karkacewan kuma ka rufema kanka koma a kanta wanda bazata kara maka taushi ba kuma bazata saurare k aba, ka kasance a koda yaushe tare da ita a matsayin me mata bayani.
Na takwas:
Lallai mata an halicce su ne akan kafurcewa zaman takewa na aure da kuma inkarin abun alheri, idan ka kyautatawa dayan su na shawan shekaru sai ka saba mata na lokaci daya zatace: ban taba ganin alheri ba a tare dakai duk zamana dakai ko sau daya ba saboda haka kada wannan hali ya sanya ka kyamatar ta da nisantarta, domin idan ka kyamace wani hali daga gareta zaka yarda da wani hali daga gareta wanda bashi ba.
Na tara:
Lallai mace tana wuce wa cikin wasu yanayi na raunin jiki da ciwon zuciya, har Allah madaukaki ya dauke mata wasu daga cikin wasu wajibai akanta na ibada wanda ya daura mata cikin wannan yanayi ya dauke mata salla baki dayan sa cikin wannan yanayi ya kuma dakatar mata da azumi a cikin su har sai ta dawo cikin lafiyar ta yanayinta ya daidaita, dan haka ka kasance da ita cikin wannan yanayi da tarbiyya na Allah kamar yadda ya saukaka mata wajibobi kaima ka saukaka mata neman tayi maka wasu abubuwa da kuma bata umurni.
Na goma:
Kasani cewa mace baiwa ce a wurin ka, ka tausayawa wannan bauta nata kuma ka kawar dakai daga raunin ta zata kasance maka mafi alherin abun jin dadi da abokiyar zama..


Wasiyya mahaifiya musulma ga yarinyarta daren amarcin ta

Kamar yadda maza ke cefane a tsakanin su na soyayya ta musulunci haka suma mata musulmai suna da rabo cikin wannan cefane a tsakanin su al'amarin kyautata zamantakewa da mu'amala me kyau tare da miji, wannan Ummu Iyas ce diyar Auf dan Alamul shaibani lokacin da Amru dan Hajar sarkin kasar Kanada ya nemi auren yarinyanta daren amarcin ta yazo sai ta kebe da ita tayi mata wasiyya wacce ta bayyana mata ginshinkin rayuwan aure na farin ciki a cikinta, da kuma abunda ya wajaba agareta na hakkin mijinta, tace mata: yake diyata da ace ana barin nasiha saboda falalar ladabi da nabar maka haka, sai dai tana tunatar da wanda ya manta, da guzuri game hankali, da ace mace tana wadatuwa daga miji da iyayenta sun wadatu, saboda kuma tsananin bukatar su zuwa gareta yasa ta zama mafiya wadatan mutane akan sa, sai dai mata saboda maza aka halicce su, kuma suma saboda su ne aka halicci maza.
“ Ya diyata: lallai zaki bar wani wuri da rayuwan da kika fito daga ciki, kuma zaki bar rayuwa wacce aka tarbiyyance ki aciki zuwa ga wani wuri da gida wanda baki sanshi ba, da gari wanda bakyasomn sa, zai wayi gari da mulkin sa akanki a matsayin me sa ido da iko, saboda haka ki zaman masa baiwa zai zaman maki bawa da maki hidima, ki kiyaye masa wannan abubuwa goma zai zaman maki madogaro:
Abu na farko dana biyu: Kankan da kai a gareshi da qana'a, da kyakyawan biyayya da jin maganar sa.
Abu na uku da hudu: ki kiyaye ganin sa da hancin sa akanki, kada ki kuskura ya ganki a cikin mummunan siffa ko kuma ya shaka daga gareki sai kamshi me dadi.
Abu na biyar da shida: ki kiyaye lokacin baccin sa da abincin sa, domin zafin yunwa akwai tunzurar wa kuma yunwan bacci yan ahaifar da kiyayya
Na bakwai da na takwas: ki tsare masa dukiyan sa, da kuma kula da hidimar sa da iyalan sa, kuma hikimar mallakan dukiya shine: kyautata kimantawa, a cikin iyali kuma shine kyautata tafiyar dasu.
Na tara dana goma: kada ki saba masa umurnin sa, kuma kada ki yada masa sirrin sa, saboda idan kika saba umurnin sa zuciyar sa zatayi kunci kuma idan kika yada sirrin sa bazaki samu aminci ba daga tarkon sa, sa'annan kashedin ki dayin farin ciki a gaban sa idan ya kasance yana cikin damuwa da bakin ciki kuma kada ki rika nuna bakin ciki a gaban sa idan yana cikin farin ciki. “
    A cikin wannan dukan sa zai bayyanan mana girman matsayi da daraja na kololuwa wanda mace take dashi a karkashin inuwar shari'ar musulunci wannan kuma raddi ne ga wanda yace lallai musulunci ya zalumci mace, taya wanda yaso ta ya kumadayaw adaga cikin fadakarwan sa tattare da kula da himmatuwa da ita zai zalumce ta da take mata hakki, wannan shine abunda zai bayyanan maka yakai me karatu me daraja cikin wannan littafi dan karami wanda zayyi magana a cikinta a bangaren soyayya cikin rayuwan rahama na shiriyan Muhammad dan Abdullahi s.a.w tare da iyalan sa wand akasancewar sa me isar da addini da kuma shugaban al'umma be sanya shi ba ya manta da kula da iyalan sa yadda ya takaita wannan himmatuwa cikin kalmomi kadan wanda suka kunshi ma'anoni daya ya kuma sanya shi wasiyya ga al'ummar sa yadda yace:
“ mafi alherin ku shine mafi alheri ga iyalan sa kuma ni ne mafi alherin ku ga iyalai na ” buhari ne ya rawaito shi.
    An kiyasta alherin maza da gwargwadon alherin su ga iyalan su da kuma kyautata zamanta kewa dasu wannan alheri wanda take kaiwa ga soyayy da rahama shine s.a.w mafi alherin mutane wanda alherin sa yasanya sa cikin kololuwan tsani na kamalar mutum cikin rahama da soyayya da kyautata mu'amala tare da mutane baki daya da kuma iyalansa musamman kuma daga cikin abunda zayyi nuni akan haka shine lokacin da ayar zabi ya sauka akan matar sa lokacin da suka tambaye shi ciyarwa sama da abunda yafi karfin sa da kyalkelin rayuwan duniya sai suka zabe shi suka kuma yarda da zama dashi cikin rayuwa kamewa Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa: lokacin da aka umurci manzon Allah s.a.w da yaba matan sa zabi sai ya fara dani, yace:
“ lallai zan Ambato maki wani abu amma babu laifi ki shawarci mahaifin ki akai ” sai tace: hakika kasan cewa mahaifina bazai taba umurtana da rabuwa dakai ba, sai tace: sai yace: “ lallai Allah madaukaki yace: ((yakai wannan annabi kace ma matan ka idan kun kasance kuna son rayuwna duniya ne da kyalekelinta to ku zo zan jiyar daku kuma sai na sake ku saki mekyau. Idan kuma kun kasance kuna son Allah da manzon sa da gidan lahira to lallai Allah ya tanadar da wani irin lada me girma ga masu kyautatawa daga cikin ku)) [suratul ahzab ayata: 28-29] sai nace tab yanzu akan wannan abu ne zan shawarci mahaifi na? lallai ni inason Allah da manzon sa da gidan lahira. Sai tace: sa'annan matan manzon Allah s.a.w suka aikata irin abunda na aikata nima ” muslim ne ya rawaito shi.
Wannan idan yana nuni akan wani abu to hakika nuni yake akan so da suke masa da yarda da kuma rikon da suke masa na abunda suka samu daga gareshi na halaye masu girma da kuma kyawu cikin mu'amala da so da kaskantar dakai wanda suka kunsa dukan su kuma sun samun yakini cewa fa bazasu taba samun Kaman sa ba, hakika manzon Allah s.a.w ya kasance yana da mata tara wanda suke rayuwa a karkashin sa kuma suna rayuwa me kyau da farin ciki, Ha'inata tace game dashi wata marubuciya yar kasar italiya L.Veccia Vaglieri cikin littafin ta me suna kariya game da Musulunci wacce take kare sag a wanda ya zargesa da sha'awa: lallai Muhammad a tsawon shekarun san a samar taka wanda sha'awar mutum yafi karfi a cikin sa kuma dukda cewa ya rayu cikin al'ummar larabawa wacce aure ya zama kamar wata cibiya ce ta zamanta kewa wacce aka rasa ko kuma ace babu kuma auren mata da yawa shine ka'aida a wurin su, kuma saki abu ne me sauki wanda bashi da wani iyaka amma dukda haka be aura ba face mace daya kawai wacce itace Khadija Allah ya kara mata yarda waccce shekarun ta ya kasance sama da nashi shekarun ya kasance yana da shekaru ashirin da biyar ya aure ta ne saboda tsabar so kuma be sake aure ba har sai bayan rasuwan ta bayan yakai shekaru hamsin da haiwuwa kuma hakika auren sa dayayi ya kasance dalilin zaman ta kewa ne ko kuma siyasa saboda burin sa cikin wannan auren shine karrama wannan matan wanda suka siffatu da tsoron Allah zuwa samar da alaka ta aure tare da wasu jama'a da kabilu na daban saboda fatan hada wani hanya sabuwa na yaduwan musulunci da hakan idan aka cire Aisha Allah ya kara mata yarda a cikin su, manzon Allah s.a.w ya aure matan da ba masu kyau bane sosai ko kuma halitta me ban sha'awa ko kuma budurwa shin idan haka ne ya kasance mutum me yawan sha'awa ne kenan? Ina bah aka abun yake ba hakika ya kasance mutum ne me tauhidi, kuma ta yiwu cewa kwadayin da yake dashi na yara shi yasa shi yin wani aure sabo, saboda yaran da Khadija ya haifa Allah ya kara mata yarda sun mutu bama ba tare da cewa yana da dukiya ba me tarin yawa ya dauki wannan nauyi na iyalai masu yawa sai dai kuma ya lazimci daidai to cikakke tsakanin su cikin ko wani hali be taba karkara ba ko sau daya wurin nuna banbanci na hakki tare da daya daga cikin su kuma hakika yayi harkokin sa ne yana me koyi da sunnar annabawa wanda suka gabata amincin Allah ya tabbata a garesu kamar musu da makamantan sa wanda be bayyana ba cewa wani daga cikin mutane yana kalubalantar su akan yawan matan da suke dashi shin sakamakon hakan zai iya koma wa zuwa da cewa mun jahilci daya ne daga cikin yanayin rayuwan su ta yau da gobe kamar yadda muka san komai na rayuwan manzon Allah s.a.w tare da iyalan sa.
Lallai manzon Allah s.a.w me daraja mutum ne me girma wanda tarihi tasan shi wacce take da tasiri me girma wurin canza yanayin duniya a cikin shaidar masu adalci cikin mutanen da ba musulmai ba da kuma wanda suka kwarai wurin karanta tarihin sa suka kuma yi dubi me zurfi zuwa ga sakon sa da kuma yaduwar ta da tasirin ta da misali ana cewa gaskiya shine abunda makiya suka shaida yadda (Mickel Hart) yake cewa cikin littafin sa me sunan mutum dari wanda sukayi tasiri cikin rayuwan dan adam: lallai zabi na ga Muhammad shine na martaban farko cikin jerin mutanen duniya da sukayi tasiri ga mutane zai iya batama wasu makaranta rai wasu kuma zasu iya ja da hakan sai dai ya kasance shine mutum daya tilo cikin tarihi wanda yacimma nasara a bayyane a fannin addini da kuma duniya.
Wannan shine abunda da mutanen da suke tare damu suke gani na saurin yaduwar da'awar sa da kuma kwadayin mabiyan sa akan riko da shari'ar sa da kuma kokari tukuru wajen yada sunnar sa mutane dayawa suna shiga addinin sa kuma yan kadan ne matuka masu fita daga cikin sa ita gaskiya idan ta taba fadin zuciya ta hadu ruhi sai su zama suna bin ta, Bilal ,utumin habasha a lokacin daya musulunta an azabtar dashi da bulala an kuma daura masa dutse me zafi akan kirjin sa kuma an kifa fuskar sa akan sahara me zafi na makka domin ya bar addinin sa amma hakan be kara masa komai ba face tabbatar dashi da kara masa kwarin gwewa yana maimaita kalamar sa ta tabbata akan haka na tauhida Allah daya ne Allah daya ne.
Haka shima Sa'ad dan abi Waqqas ya kasance mutum ne me tsananin biyayya ga mahaifiyar sa, mahaifiyar sat ace masa a lokacin daya musulunci bazan kara cin abinci ba ko shan ruwa har sai na mutu, sai a rika tozarta ka dani a rika cewa: ya wanda ya kashe mahaifiyar sa. sai yace: kada ki aikata haka ya mahaifiyata domin ni dai bazan bar wannan addini ba. sai yace: sai ta zauna rana daya bataci abinci ba, sai ta fara rashin lafiya, sai yace: ta kara zama rana na biyu bataci abinci ba sai wannan rashin lafiya nata ya karu. Sai yace: a lokacin dana ga haka sai nace: ki sani fa wallahi ya mahaifiya ta da ace kina da rai guda dari zasu rika fita daya bayan daya har su gama fita bazan taba barin wannan addinin nawa ba domin wani abu ba, idan kin so kici abinci, idan kuma kinso kada kici, a lokacin da taga haka sai taci abinci.


Mu'amalar manzon Allah Muhammad s.a.w tare da matan sa:

•    Manzon Allah ta fuskan shakatawa da iyalan sa.
Musulunci yana koyar da musulmi laluran bawa kai hakkinta na hutu da shakatawa na halal cikin iyaka na shari'a domin ka nisantar da ita daga kosawa da kuma samun kwarin gwewa na kaiwa zuwa ga hanyar Allah madaukaki cikin nishadi da kokari, sai dai hakan yana da sharadin cewa kada mutum ya wuce gona da iri cikin wannan bangare na wasanni sama da bangaren rahiran sa sai rayuwan musulmi ta canza zuwa ga wasa wanda bashi da wani amfani ya kuma mantar da mutum abunda aka halicce sa domin sa, hakika sahabban manzon Allah s.a.w Allah ya kara masu yarda sun kasance a farkon musulunci suna kudurce cewa lallai musulunci addini ne wanda baisan hutu ba da wasa na halal ba da kuma shakatawa hanzalat dan hazim al hanafi yana cewa:
“ Abu bakar ya hadu dani sai yace mun yaya kake? Ya hanzalata! Sai nace masa ni hanzalata nayi munafunci. Sai yace subhanallah (tsarki ya tabbata ga Allah)! Me kake cewa? Sai nace: idan muna wurin manzon Allah s.a.w yana tunatar damu wuta da aljanna kamar muna ganin su da idanun mu, amma idan muka bar wurin sa sai ya shagala da wasa da matan mu da yaran mu da kuma neman duniya, sai mu manta abunda makaji a wurin manzon Allah dayawa. Sai Abubakar yace: wallahi muma haka yake faruwa damu. Sai muka tafi gun manzon Allah s.a.w ni da Abubakar bayan mun shiga wurin sa sai nace: hanzalata yayi munafurci ya manzon Allah s.a.w! sai manzon Allah s.a.w yace ” me yayi? ” sai nace: ya manzon Allah! Mun kasance idan muna wurin ka kan atunatar damu wuta da aljanna kamar muna ganin su da idanun mu amma idan mun bar wurin ka sai mu shagala da matan mu da yaran mu da neman duniya mu manta da dayawa. Sai manzon Allah s.a.w yace: “ ina rantsuwa da wanda raina ke hannun sa! da zaku dawwama akan halin da kuke ciki a wurina da kuma tunanin wuta da aljanna da mala'iku sun rika gaisawa daku hannu da hannu akan hanyar ku da kuma gadon baccin ku. Sai dai ya hanzalata! Lokaci bayan lokaci- watan idan kayi tunanin lahira da bautan Allah ka huta sannan ka sake haka dai ” ya fada masa hakan har sau uku. Muslim ne ya rawaito shi.
Sai dai wannan mahanga ta canza a lokacin da musulunci ya sanya wasa tare da iyalai da kuma sanya masu farin ciki arai cikin addini kuma ba bu mamali akan haka kasancewar musulunci addini ne wanda ya kunshi komai domin ya tattara jiki da ruhi da rai da hankali manzon Allah s.a.w yana cewa:
“ dukkan abun da ba anbaton Allah bane to wasa ne da bata okaci sai abu hudu kawai: wasan mutum da matar sa, da koyan hawa doki, da koyan harbi da kuma koyan nunkaya cikin ruwa ” . Hadisi ne ingantacce Ahmad da nasa'I da baihaqi ne suka raaito shi.
    Kuma wannan mahangar ta kara canzawa har wayau a lokacin da suka gani daga manzon Allah s.a.w a bunda yake nuni akan haka, jabir dan samurata yana cewa: manzon Allah s.a.w ya kasance baya tashi daga inda yayi sallar asuba har sai rana ta fito, idan rana ta fito sai ya tashi. Sun kasance suna fira, har fira yazo kan al'amuran lokacin jahiliyya sai suyi daria da murmushi. Muslim ne ya rawaito shi.
    Bawai wannan bane kuma kawai a'a ya tsananta akan awajabcin bama kai hakkinta na shakatawa da kuma hutu wannan shine abunda manzon Allah s.a.w yace ma Abdulahi dan Umar:
“ yakai Abdullahi, an bani labarin cewa kana azumi kullum da rana sannan da daddare kayi sallar dare. Sai yace haka ne ya manzon Allah, sai manzon Allah s.a.w yace:
“ kada ka aikata haka, ka rika yin azumi kana hutawa, kuma ka rika sallar dare kana yin bacci, domin jikinka yana da hakki akanka, idon ka shima yana da hakki akanka, sannan matarka itama tanada hakki akanka, haka bakonka shima yana da hakki akanka ” buhari ne ya rawaito shi.

1.    Manzon Allah me daraja s.a.w yana shakatawa da iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance yana shakatawa da iyalan sa domin canza yanayi da kuma samun dama ya sanya masu farin ciki da kuma kore masu kosawa da damuwa, Aisha matar manzon Allah s.a.w tana cewa: yan habasha sun shigo masallaci suna wasa aciki sai manzon Allah s.a.w yace:
“ yake iyar fara kinason ki kalli wasan su? ” sai nace eh inaso sai ya tashi ya tafi bakin kofa nazo na sameshi a bakin kofa sai ya sanya gemuna akan kafadar sa, tace: daga cikin abunda suke fadi a wannan rana itace: baban kasim mutum ne na kwarai, sai manzon Allah s.a.w yace: “ ya isheku haka ” sai nace: kada kayi gaggawa ya manzon Allah. Aisha tace: banso kallon suba face kawai inason na nunama mata matsayi na a wurin sa ne da kuma matsayin sa aguna ”

2.    Manzon Allah yana kawar dakai da hakuri domin farin cikin iyalan sa:
Ubangijin sa ya ladabtar dashi sai ya kyautata masa ladubban sa, ya kaance cikin dabi'ar sa s.a.w baya yima wani abun da bayaso kuma yana yafiya da kawar dakai akan wasu abubuwa wanda iyalan sa suke aikatawa wanda be sabama shari'a ba, ma'anar kawar dakai shine bayyanar da rashin damuwa da abu tare da ilimi da kuma sanin abunda za'a kawar dakai akai, Aisha matar manzon Allah s.a.w tana cewa: Abubakar Allah ya kara mata yarda ya shigo wurinta ya tarar da wasu bayi biyu a lokacin ranakun muna suna mata kida, manzon Allah s.a.w kuma ya rufe da tufafin sa, sai Abubakar yayi masu tsawa, sai manon Allah s.a.w ya bude fuskan sai yace:
“ ka kyale su ya Abubakar, domin ranakun idi ne ” , ranakun muna kenan. Sai Aisha tace: naga manzon Allah s.a.w yana kare ni, ina kallon habashawa suna wasa cikin masallaci, sai Umar ya tsawatar masu sai manzon Allah s.a.w yace: “ ka kyale su kuyi was an ku cikin aminci yaku yayan Arfida ” buhari ne ya rawaito shi.

3.    Manzon Allah s.a.w ya kasance yana tabbatar da farin cikin iyalan sa:
Daga cikin alamun soyayya da kuma daidaito da tabbata tausayi shine neman dukkanin abunda zai shigar da farin ciki cikin zuciyar wanda kake so, hakika manzon Allah s.a.w ya kasance yana kokarin ganin ya kawo abunda zai shigar da farin ciki ga iyalan sa, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ ta kasance tana wasa da yara mata a wurin manzon Allah s.a.w kuma kawayenta suna zuwa mata sai su rika boyewa cikin gidanta domin kunyan manzon Allah s.a.w. sai tace: manzon Allah s.a.w ya ksance yana turo su wuri na ” msulim ne ya rawaito shi.

4.    Manzon Allah s.a.w yana wasa da iyalan sa:
Kamar yadda cikin karantarwan musulunci akwai abunda yake gyara gangan jiki da ruhi haka akwai abunda yake gyara rai na shigar mata da farin ciki da murna hakika manzon Allah s.a.w ya kasance baya mantawa da wannan bangaren yana bashi hakkin sa na himmatuwa dashi yana wasa da sahabban sa da iyalan sa kuma baya fadi sai gaskiya, kuma an sani cewa wasa yana daga cikin abunda rai keso wanda yake Koran damuwa da kosawa daga zuciya da sharadin iyakance sa da iyakoki da sharudda na shari'a kada ayi karya acikin sa ko kuma munanawa wani dashi, Aisha Allah ya kara mata yarda tanan cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya dawo wurina wata rana daga jana'iza a makabartan baqi'a, sai ya tarar dani ina fama da ciwon kai ina cewa wayyo kaina! Sai yacemun ya Aisha! ni nafiki jin ciwon kai dinnan (domin ciwon ki zai wuce ki warke ni kuma nawa bazai warke ba domin na kusan mutuwa), sai yace mata: me zai dameki da zaki mutu kafin ni, zan maki wanka na sanya maki likafani na kuma yi maki salla da birneki?! Sai tace: ni kuma kamar ina kallon ka cikin wannan hali wallahi da zaka aikata dukkanin abunda ka Ambato daka koma gidana ka zama ango da sauran matan ka! Sai manzo Allah s.a.w yayi murmushi, sa'annan ya fara rashin lafiyar daya mutu a cikinta ” darimi ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.

5.    Manzon Allah yana kewaya dan shakatawa tare da iyalan sa:
Rayuwan sa baya rabuwa da abunda yake hutar da kai, hakika manzon Allah s.a.w ya kasance yana fita tare da iyalan sa ya kewaya dasu, isar da sakon sa da kuma shugabancin al'umma baya shagaltar dashi daga kula da wannan bangare na rayuwa, ga Aisha nan tana rawaito mana labarin wani daga cikin tafiyar ta tare da manzon Allah s.a.w:
“ ….. kuma manzon Allah s.a.w ya kasance idan dare yayi yana fita tare da Aisha suna fira da ita… ” muslim ne ya rawaito shi.

6.    Manzon Allah s.a.w yana dariya daga wasan da yakeyi da iyalan sa:
Dariya al'amari ne na fidira tare da mutum yanada rabo cikin karantarwan musulunci, manzon Allah s.a.w yace:
“ murmushin ka ga fuskar dan uwanka sadaka ce ” tirmizi ne ya rawaito shi kuma hadisi ne ingantacce.
Haka addinin mu ya koya mana cewa ya dace ga musulmi ya kasance me sakin fuska ba me murtukewa ba da daure fuska a koda yaushe, hakika manzon Allah s.a.w ya kasance yana dariya kuma yana bada dariya domin ya kori daure fuska daga majalisin say a kuma cika yanayin da farin ciki da natsuwa, shin me fadin cewa:
“ kada ka raina kankancin aikin lada koda kuwa ka hadu da dan uwanka ne cikin sakin fuska da murmushi ”

7.    Manzon Allah s.a.w yana yada ruhin farin ciki ga ilayan sa:
Ya kasance daga cikin dabi'ar sa wasa da tsokanar wanda suke tare, iyalan sa suna da rabo daga cikin saukin sa da fara'ar sa da tausayin sa da kuma zaulaya tare dasu domin yak ore masu daure fuska da kosawa daga garesu ya kuma sanya masu farin ciki cikin zukatan su, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa: nazo wurin manzon Allah s.a.w da wani irin abinci kamar tuwo da miya sai nace ma saudat kici ga manzon Allah a tsakanin mu sai taki ci, sai nace mata kodai kici ko kuma na yaba maki shi a fuska, sai taki ci sai na sanya hannuna cikin wannan abinci na yaba mata shi a fuska sai manzon Allah s.a.w yayi dariya sai manzon Allah s.a.w ya daga kafarsa daya daura akan saudat domin ta iya rama abunda na mata, sai yacema saudat kema ki yaba mata a fuska, sai ta yaba mata sai manzon Allah s.a.w yayi dariya sai ga umar ya wuce yana cewa ya Abdullahi ya Abdullahi sai manzon Allah s.a.w yayi zaton zai shigo ne sai yace mana ku tashi kuje ku wanke fuskan ku, sai Aisha tace bangushe ba inajin tsoron Umar saboda kwarjinin sa a wurin manzon Allah s.a.w ” Abu ya'ala al musili ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.

8.    Manzon Allah yana halartan wurin mutane masu farin ciki:
Daga cikin hikimar sa s.a.w shine yana mu'amala da kuma aiki da kowa da irin abunda ya dace dashi matukar be sabama shari'a ba, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya dawo daga yakin tabuka ko khaibara acikin lalitar ta akwai wani labule sai iska tazo ta daga gefen wannan labule na kayan was an Aisha sai yace: “ menene wannan ya Aisha? “ sai tace kayan wasana ne! sai yaga wani doki a cikin su yana da fuka fukai guda biyu fata wanda ake rubutu akai, sai yace: menene wannan nake gani a tsakiyar su? Sai tace: doki ne, sai yace menene akanshi?, sai tace: fuka fuki ne, sai yace: wani irin doki ne da fuka fuki? Sai tace: bakiji cewa Sulaiman yanada doki me fuffuke bane? Sai tace: manzon Allah s.a.w yayi dariya har hakoran sa na dadashi suka bayyana ” abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.

9.    Manzon Allah s.a.w yana farin ciki da murnan iyalan sa:
Shigar da farin ciki da murna a zuciyar iyalai alama ce ta alherin mutum ga iyalan sa kuma manzon Allah s.a.w ya kasance na gaba-gaba wurin shigar da farin ciki da murna a zuciyar iyalan sa, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance yana zaune sai yaji sauti mabanbanta da kuma sautin yara sai ya mike sai yaga wata mata yar habasha tana wasa ga yara a gefenta sai yace: “ ya Aisha zo ki gani ” sai nazo na daura gemuna akan kafadar manzon Allah s.a.w ina kallon ta sai yacemun: “ ke ishe ki bane kallon haka ” sai nace eh be isheni ba domin naga matsayina a wurin sa, sai ga Umar yazo yan akoran mutane daga wannan mata sai manzon Allah s.a.w yace: “ lallai ina ganin shedanun aljanu da mutane suna guduwa idan Umar yazo ” sai tace sai nadawo ” . Tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.

10.    Manzon Allah s.a.w yana zama da fira da iyalan sa:
Ya kasance daga cikin al'adar sa cewa yana zama da fira da iyalan sa wanda yake wanke masu zuciya daga cikin haka daga cikin abunda sakamakon mu'amalar yau da gobe zai haifar kuma yanada tasiri me girma wurin kara shakuwa da dankon soyayya, safiyyat diyar hayiyi matar manzon Allah s.a.w tana cewa:
“ tazo wurin manzon Allah s.a.w domin masa zaria a masallaci yana cikin ittikafi, cikin kwanaki gomam karshe na watan ramadana, sai tazauna suka fira tare na tsawon awa daya, sa'annan ta tashi zata tafi gida, sai manzon Allah s.a.w ya tashi yi mata rakiya, bayan ya kawo kofar masallaci kusa da kofar ummu salmata, sai wasu mutum biyu cikin mutanen madina suka ganshi, sai sukayi sallama ga manzon Allah s.a.w, sai manzon Allah s.a.w yace masu: “ ku dakata safiyya ce diyar hayiyi ” . Sai sukace: tsarki ya tabbata ga Allah ya masnzon Allah, abun yayi masu girma, sai manzon Allah s.a.w yace: “ lallai shedan yana yawo jikin mutum kamar yadda jini yake yawo, ina tsoron ya jefa wani abu cikin zuciyar ku ” buhari ne ya rawaito shi.

•    Manzon Allah s.a.w ta bangaren tausayin sa ga Iyalan sa:
Lallai musulunci yana kula da bangaren mutum wanda aka halicce sa akai wanda daga ciki akwai bangaren tausayi tsakanin miji da mata, sai yayi dubi zuwa ga sha'awa na jinsin mutum akan lalura wacce ya wajaba a kosar da ita da kuma rashin dadasheta, sai dai kuma dauketa daga kasance warta sha'awa kawai na dabbanci abun kyama saboda haka ne ya sanya hanyar biyan wannan sha'awa ta hanyar aure wanda ya ginu akan tsarki da kamewa da kuma samar da natsuwar rai da tabbatar da tausayi da kuma lamunce hakkoki na ma'aurata, Allah madaukaki yana cewa:
“ kuma daga cikin ayoyin sa ya halatta maku mataye daga jikin ku domin ku samu natsuwa a garesu kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakanin ku lallai acikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani ” suratul rum ayata 21.
Saboda haka ne musulunci ya umurci mabiyan sa da saurin yin aure idan suka samu ikon haka ya kuma yi bayanin dalilin haka, sai manzon Allah s.a.w yace:
“ yaku taron samari! Duk wanda ya samu abun yin aure to yayi aure, domin hakan yafi wurin kame kallo da kuma kiyaye farji, wanda kuma be samu ba to ya rika yin azumi domin hakan kariya ne a gareshi ” Muslim ne ya rawaito shi.
Ya kuma yi hani daga ruhubanan ci (kebewa domin bauta kullum) da kuma barin yin aure da kuma gudun duniya baki daya, an karbo daga anas dan malik Allah ya kara masa yarda yace:
“ wani mutum uku sun zo gidan manzon Allah s.a.w suna tambayar matan sa game da bautan sa bayan sun fada masu suka jinjina haka sai sukace mu kuma muna ina ace manzon Allah wanda aka gafarta masa zunuban sa baki daya wanda ya gabata da wanda zaizo yana aikata irin wannan bauta, sai dayan su yace ni daga yau kollum sallar dare zantayu har nabar duniya dayan kuma yace ni daga yau kullum azumi zantayi har nabar duniya dayan kuma yace ni daga yau ba ruwa na da mace har Abadan sai manzon Allah s.a.w yazo yace masu kune wanda sukace kaza da kaza, ku sani cewa wallahi na fiku tsoron Allah da takawa amma ni ina azumi kuma ina hutawa kuma ina bacci da yin sallar dare kuma ina auren mata kuma duk wanda ya kyamaci sunnata to baya tare dani ” buhari ne ya rawaito hadisi.
Muslunci ya girmama bangaren tausayi tsakanin miji da mata ya sanya shi ya zama ibada wanda ake ba musulmi lada akai kamar yadda ake bayar da alada akan ayyukan alheri a lahira, manzon Allah s.a.w yace:
“ …. ” Kuma acikin jima'in dayan ku shima akwai sadaka ” sai sukace: ya manzon Allah yanzu dayan mu zai biya sha'awar sa kuma abashi lada? Sai yace: “ ku bani labari yaya kuke gani idan yaje ya biya sha'awar sa ta hanyar haramun shin za'a bashi zunubi? To Kaman haka ne idan ya biya sha'awarsa ta hanyar halal za'a bashi lada ” muslim ne ya rawaito shi.
Ya kuma kwadaitar a wannan bangare saboda muhimmancin dake cikin sa cikin rayuwan musulmi saboda ta hanyar sa ne ake samun dawwama na zuciya da natsuwa ta bangaren soyayya wanda zai bashi damar yin ibadar sa cikin natsuwa kwakwalwa.
Kuma ya kamata mu kawo wasu daga cikin bangarori na rayuwar manzon Allah na tausayi da soyayya tare da iyalansa:
1.    Manzon Allah s.a.w baya ha'intar iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance misali abun koyi wurin kamewa, ya bayyana abunda ya dace musulmi ya aikata a lokacin da shedan ya jefa masa abunda zai kaishi zuwa ga aikata alfasha a cikin zuciyar sa, Jabir dan Abdullahi Allah ya kara masu yarda yana cewa:
“ idan dayan ku yaga wata mace ta burge shi to ya koma ga iyalin sa domin itama tanada irin abunda wancan mace take dashi ” Tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantahi cikin littafin al sahiha 235.

2.    Manzon Allah s.a.w da shaukin sa ga iyalan sa:
Lallai saurin dawowan mutum ga iyalan sa daga tafiyar sa dalili ne akan soyayyar sa da shaukin sa a garesu kuma akwai amfani cikin haka wanda baya boyuwa na tabbatan zuciya da tausayi da soyayya saboda haka ne ya kasance cikin karantarwan manzon Allah s.a.w ya kasance a bayyane akan haka a lokacin day ace:
“ tafiya bangare ce ta azaba, yana hayan ku baccin sa da abincin sa da abun shansa, saboda haka idan dayan ku y agama biyan bukatar sa a tafiyar sa to ya gaggauta dawowa ga iyalan sa ” buhari ne ya rawaito shi.

3.    Manzon Allah yana sabanta soyayya da kauna ga iyalan sa:
Kyauta tana da muhimmanci kuma tana kara daraja idan ta kasance daga wanda kake so saboda haka ne karantarwan manzon Allah s.a.w ta kasance a bayya ne a lokacin da yace: “ kuyi kyauta zaku so junan ku ” buhari ne ya rawaito shi cikin littafin sa na adabul mufrid kuma albani ya inganta shi.
Ya kuma kara fadi har wayau s.a.w: “ yaku matan musulmai kada wata ta raina wata kyauta da zata ba wata koda kuwa da misalin akuya ne mara nama ” buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.

4.    Manozn Allah s.a.w yana kame kallonsa akan iyalan sa kawai:
Kiyaye gabbai da kuma rage su akan iyalai dalili ne na daidaitan mutum kuma shedan yana kokari akan karkatar da wannan hali da kuma amfani da ita cikin dabi'u makaskanta hakika an rubutama dan adam rabo na zina wanda dole ya aikata hakan babu makawa: idanu suna zina kuma zinan su shine kallo, kunne shima yana zina kuma zinan shi shine sauraro, harshe ma yana zina kuma zinan shi shine magana, hannu yana zina zinan shi shine tabawa, kafafuwa suna zina kuma zinan su shine tafiya, zuciya yana buri da sha'awa sai farji ya gasgata hakan ko kuma ya karyata kamar yadda manzon Allah s.a.w ya bada labari akan haka, kuma hadisin buhari da muslim ne suka rawaito shi. Wannan kuma lafazin muslim ne, ruwaiyar buhari a takaici take.

Kuma hakika manzon Allah s.a.w ya kasance abun koyi ne akan haka, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ muminai mata sun kasance idan sunyi hijira zuwa ga manzon Allah s.a.w yana masu jarabawa da kuma masu mubaya'a saboda fadin Allah madaukaki cewa yakai wannan Annabi idan mata muminai sun zo maka suna maka mubaya'a akan cewa bazasu hada Allah da wani ba cikin bauta kuma bazasu yi sataba kuma bazasuyi zina ba har zuwa karshen ayar sai Aisha tace duk wacce ta tabbatar da hakan cikin wannan mata muminai to hakika tayi mubaya'a na shari'a manzon Allah kuma ya kasance idan sun tabbatar da hakan da maganar su sai yace masu ku tafi hakika nayi maku mubaya'a, kuma wallahi manzon Allah s.a.w be taba shafan hannun wata mace ba ko sau daya kawai yana masu mubaya'a ne da magana , Aisha tace wallahi bai taba amsar komai ba daga wurin mata sai abunda Allah yayi masa umurni kuma tafin hannun sa be taba shafan tafin hannun wata mace ba ko sau daya, ya kuma kasance yana cewa masu idan ya amsa daga garesu cewa hakika nayi maku mubaya'a da magana ” muslim ne ya rawaito shi.

5.    Manzon Allah s.a.w yana bayyana soyayyar sa ga iyalan sa:
Ya kasance manzon Allah s.a.w baya samun nauyi a zuciya wurin bayyana soyayyar sa ga iyalan sa hasalima ya dauki hakan cikin kyawawan dabi'u da kuma kyautata zaman takewa da tarayya, kuma musamman ma kasancewar an aiko shi cikin al'ummar jahilai wanda basa ganin mace da wani kima, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ banyi kishi ba akan matan manzon Allah s.a.w sai akan Khadija kawai kuma ban risketa ta mutu gabanin manzon Allah s.a.w ya aure ni. Sai tace: manzon Allah s.a.w ya kasance idan ya yanka akuya sai yace: ko aika ta zuwa ga kawayen Khadija. Sai tace: sai wata rana kishinta ya kamani sai nace: Khadija kuma?!! Sai manzon Allah s.a.w yace: “ lallai ni an azurtani da soyayyanta ” muslim ne ya rawaito shi.

An kuma karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance idan aka abmaci kahdija sai ya yabeta ya kuma kyautata yabon nata sai tace: sai wata rana kishin hakan ya kama ni sai nace ya naga kana yawan anbatonta ne bayan Allah ya canza maka ita da wacce tafita alheri! Sai yace: “ Allah be canzamun da wacce tafita alheri ba: hakika tayi imani dani a lokacin da mutane suka kafurta dani kuma ta gasgatani a lokacin da mutane suka karyata ni, kuma ta yalwatani da dukiyar ta a lokacin da mutane suka hanani nasu, kuma Allah ya azurtani da yaro daga dagare a lokacin daya hanani yara daga sauran mata ” Ahmad ne ya rawaito shi, kuma shu'aibu al arnu'ut yace: wannan hadisi ne ingantacce kuma silsilan sa ingantacce ne cikin littafin mutabi'at.

6.    Manzon Allah s.a.w yana tsabta domin kyautata zama na auratayya:
Karantarwan musulunci yana nuni akan cewa Allah madaukaki me kyau ne kuma yana son kwalliya kuma me karamci ne da kyauta kuma yana son masu karamci da kyauta, me tsabta ne kuma yana son masu tsabta kamar yadda manzon Allah s.a.w ya bada labari kuma wannan umurni ne ga musulmi ya kasance cikin yanayi me kyau da shiga me kyau tare da mutane musamman ga iyalin sa, saboda haka ne manzon Allah s.a.w yayi umurni da himmatuwa da wannan bangare kuma ya jaddada hakan:
“ idan dayanku ya kusanci iyalin sa kuma yana so ya koma to yayi alwalla ” Muslim ne ya rawaito shi.
Ya kuma kara fadi har wayau: “ wannan shi yafi tsabta da tsari da kuma tsarki ” abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.

7.    Manzon Allah yana musayar soyayya da iyalin sa:
Lallai soyayya ta hakika ita cw wadda take lizimtar mutum cikin dukkanin halinsa baya canzawa cikin wani lokaci kuma wannan shine halin manzon Allah s.a.w tare da iyalin sa yadda Aisha Allah ya kara mata yarda take cewa:
“ na ksance ina wanka tare da manzon Allah s.a.w cikin kwarya daya, dukkanin mu muna da janaba. Ya kasance yana umurtata dana daura zani daga kirjina zuwa gwewata sai yayi wasa dani na debe sha'awa ina cikin al'ada. Kuma ya kasance yana fitomun da kansa ya mikomun yana cikin ittikafi na wanke masa ina cikin al'ada ta ” buhari ne ya rawaito shi.

8.    Manzon Allah s.a.w baya yada sirrin iyalan sa:
Lallai alaka ta aure da abunda ke cikin ta sirri ne cikin sirrori wanda musulunci ya tsananta akan kiyaye su da kuma rashin yada su musamman ma irin wanda babu kunya a cikin jin su kuma tana tafiyar da mutuncin mutum, manzon Allah s.a.w yana cewa:
“ lallai daga cikin mafiya sharrin mutane a wurin Allah ranan alkiyama shine mutumin da yake kwanciya da matar sa sai yazo ya yada sirrin ta ” muslim ne ya rawaito shi.

9.    Manzon Allah s.a.w yana magana ta soyayya da ban mamaki ga matan sa:
Hakika manzon Allah s.a.w ya kasance me saukin hali ne me kyauwun siffa ne yana jiyar da iyalan sa magana wacce take nuna soyayya da tausayi kuma yana kiran ko wanne daga cikin su da abunda yake so na sunaye ya kasance yana kiran Aisha Allah ya kara mata yarda da suna:
“ yake iyar fara ” kuma ya kaiwa matuka wurin tausasa masu magana na soyayya ya wani lokaci kuma ya kankanta sunan su domin ya bayyana masu abunda zuciyar sa yake masu suna dashi na soyayya sai yace “ yake iyar Aisha… ” Muslim ne ya rawaito shi.

10.    Manzon Allah s.a.w yana kusantar iyalan sa hatta a lokacin uziri na shari'a:
Hatta a lokacin uziri na shari'a ga iyalan say a kasance yana zama dasu kuma yaci abinci tare dasu da shan ruwa da kuma wasa dasu na debe sha'awa ba tare dayin jima'i dasu ba domin ya kosar da raunin zuciyar su kuma ya bayyana hukunce hukunce na shari'a cikin irin wannan matsaloli, da kuma abunda ya halatta ga miji tare iyalin sa da kuma abunda zayyi daidai da halinta da yanayin ta, wanda yake sabanin karantarwa da kuma shari'a na littafi me tsarki na kiristoci wacce take mace me al'ada a matsayin najasa kuma tana umurtan miji da nisantar matanshi a halin uziri na shari'a (ka duba cikin littafin safar allaween 15:19), Aisha uwar muminai Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance yana wasa da ita na debe kewa a cikin rigan ciki na mutum ina cikin al'ada, sai dai kuma shi yafi ku mallakar kansa cikin halin da kame kansa ” baihaqi ne ya rawaito shi.

11.    Manzon Allah s.a.w ya kasance yana kiyaye yanayi na damuwar iyalan sa:
Bukatar mace ga namiji da kuma bukatar maniji ga mace abune na fidira kuma dawwamamme bawai abu bane na dan lokaci kamar sauran halittu na daban wanda suke da wani lokata wanda suke aure a cikin sa sai kuma a rabu kowa ya tafi harkokin sa, kada na miji ya kaurace masu alokacin uzirin su na shari'a ya kwana tare dasu kuma yaji dadi dasu suma suji dadi dashi banda yin jima'a, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance yan asallar dare ni kuma ina gefen sa kuma ina cikin al'ada na lulluba da mayafi wanda akayishi daga sufi shima ya lullaba da gefen wannan mayafi “ muslim ne ya rawaito shi.

12.     Manzon Allah s.aw ya kasance yana debe kewa tare da iyalan sa:
Lallai dukkanin ayyukan sa baki dayan su karantarwa ne ga al'ummar sa da kuma bayanin hukunce hukunce na fiqihu wanda acikin su mutanen sa zasu iya aiwatar da rayuwan su na addini, was an da yakeyi da iyan san a debe kewa a lokacin al'adar su da bacci tare dasu yana nuni ne ga hakan a shari'an ce na bayanin tsarkin jikin mace da kuma tsarkin wurinta da halaccin bacci tare da ita cikin bargo daya da sauran sun a hukunce hukunce wanda za'a ciro daga cikin wannan aiki nasa, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance yana kishin gida akan kirjina ina al'ada ya karanta alkur'ani ” Muslim ne ya rawaito shi.

13.     Manzon Allah s.a.w yana wanka da iyalin sa:
Lallai manzon Allah s.a.w ya kasance me kwadayin shigar da farin ciki ga zuciyar iyalan sa cikin dukkanin yanayi hatta a bayan gama jima'I wanda mafiya yawan lokuta mutum yana kasancewa ne a cikin su karancin nishadi na jikin sa da kuma rashin karfi na jiki da sanyi manzon Allah s.a.w ya kasance yan awanka tare da iyalin sa kuma harda wasa da zaulaya a lokacin wankan, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ na kasance ina wanka ni da manzon Allah s.a.w cikin kwarya daya, muna rigangeniya wani lokaci na rigashi wani lokaci ya rigani ta fuskan wasa, har yace a cikin wasa: ki ragemun ruwan. Nima nace: ka ragemun ruwan ” nisa'i ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.

14.     Manzon Allah s.a.w yana sunbatar iyalin sa:
Debe kewa lamuni ne ga ci gaban rayuwan ma'aurata bayan gam da katar din Allah kuma da biyan dukkanin abunda yake fado mata ta hanyar wasa yan kadan da kuma magana yar kadan zaka samu soyayyar iyalin ka kuma zaka kashe mata kishin ruwan ta na damuwa kuma ka zama dalili na tabbatan kwanciyar hankalin su hakika manzon Allah s.a.w ya kasance yana lura da wannan bangare dan karami baya mantawa dashi, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa: “ manzon Allah yazo zai sunbace ni sai nace masa ina azumi fa sai yacemun ai nima ina azumin sai ya sun bace ni. Nisa'i da Ahmad da Ibn kuzaima ne suka rawaito shi kuma hadisi ne ingantacce.

•    Manzon Allah s.a.w tare da iyalan sa ta bangaren dan adamtaka:
•    Manzon Allah s.a.w mutum ne kamar sauran mutane an bashi falala ne akan mutane da annabta ya kuma samu daukaka ne akan su da isar da sako kuma an aiko shi zuwa garesu domin ya fitar dasu daga bautan bayi zuwa bautan Ubangijin bayi kuma ya sanar dasu shari'ar Allah wannan falala ce ta Allah wanda yake ba wanda yaso cikin bayin sa saboda fadin sa madaukaki:
“ kace masu ni ba komai bane face mutum irin ku anyi mani wahayi cewa Allahn ku shi daya ne duk wanda yake kwadayin haduwa da ubangijin sa sai ya aikata ayyuka na kwarai kuma kada ya hada Allah dawani cikin ibadar sa ” suratul kahafi ayata 110.
•    Bashi da wani siffa na allantaka besan gaibu ba kuma baya amfanar wa baya kuma cutarwa kuma baya juya komai cikin duniyan nan, Allah madaukaki yana cewa akan sa:
“ kace masu bana mallakawa kaina amfani ko kuma cutarwa sai abunda Allah yaso kuma da ace nasan gaibu da ban yawaita aikata alheri kuma da wani mummunan abu be same nib a nib a komai bane face me gargadi da bishara ga mutane muminai ” suratul a'araf ayata 188.
•    Duk da falalar sa da daukakan sa da kuma matsayin sa da darajar daya samu da sakon annabta yana kin a wuce gona da iri akan yabon sa ko kuma a kaishi matsayi wanda ba matsayin bawa ba ga Allah wanda Allah ya zaban masa shi domin girmamashi da ita, manzon Allah s.a.w yana cewa:
“ kada ku rika kurantani kamar yadda kiristoci suka koranta dan maryan, lallai ni bawa ne, dan haka kuce: bawan Allah kuma manzon sa ” buhari ne ya rawaito shi.
•    Siffofin sa na mutum ne dukanin abunda ke gudana akan mutane ya gudana masa masu bijirowa, shi bame dawwama bane cikin wannan duniya, Allah madaukaki yace akan sa:
“ Muhammadu be kasance ba face manzo wanda manzanni sun gabata gabanin sa yanzu shin idan yam utu ko kuma aka kashe shi zaku juya akan duga duganku ne? duk wanda ya juya akan duga dugan sa to bazai cutar da Allah ba da komai kuma da sannu Allah zai sakama masu godiya ” suratu al'imran ayata 144.
•    Abunda yake samun su na cuta da rashin lafiya shima yana samun sa yana rashin lafiya da cuta kuma yana neman magani, Abdullahi dan mas'ud yana cewa:
“ na shiga wurin manzon Allah s.a.w yana zazzabi sai nace: ya manzon Allah kana zazzabi ne me zafi? Sai yace: “ eh mana ina zazzabi kamar yadda wanin ku yake yi ” sai nace: hakan kana da lada biyu kenan? Sai yace: eh kwarai haka ne, babu wani musulmi wanda wata cuta zata same shi na kaya ne zuwa saman ta face Allah ya kankare masa zunuban sa dashi kamar yadda bishaya take kankare ganyen ta ” buhari ne ya rawaito shi.
Abin nufi cikin wannan hadisi wanda ya gabata cikin fadin sa cewa: hakan kanada lada biyu kenan? Ma'anar hakan zai fito fili ne cikin hadisi me girma wanda Sa'ad dan Abi waqqas Allah ya kara masa yarda yace: “ nace ya manzon Allah wanene yafi mutane girman bala'i sai yace “ annabawa sai wanda suke biye masu a wurin imani haka har zuwa kasa ana rajabtan mutum ne gwargwaon addinin sa idan addinin sa ya kasance tsantsa to bala'in sa zaifi tsanani idan kuma akwai tauni a cikin addinin sa za'a jarabe sa ne gwargwadon addinin sa kamar yadda bala'i yake wanke bawa har sai ya barshi yana tafiya a kasa bashi da zunubi ko daya ” “ hadisi ne ingantacce Tirmizi ne ya rawato shi.
•    Yana so kuma yana ki, Umar dan kaddab yana cewa wani mutum yazo wurin manzon Allah s.a.w sai yace:
“ bani da abunda zan baka amma ka dan nemo bashi har na samu abunda zan baka ” sai Umar dan kaddab yace: ya manzon Allah baka mahaifi na da mahaifiyata fansa agareka Allah be daura maka wannan b aka bashi abunda kake dashi idan baka da komai kada ka daurama kanka sai yace: sai manzon Allah s.a.w yaki maganar, sai Umar yace: idan yayi fushi kuma ana gane hakan daga fuskar sa sai wani mutum ya mike cikin mutanen madina yace: na bada mahaifin ada mahaifiyana fansa a gareka ya manzon Allah ka bayar kada kaji tsoron takaitawa domin wani me mulki sai yace: sai manzon Allah s.a.w yayi murmushi yace: “ da wannan ne aka umurce ni ” dabari ne ya rawaito hadisin cikin littafin tahazib da kuma Barraz cikin littafin san a sanadi.
•    Yana murna kuma yana bakin ciki, a lokacin da yaron sa Ibrahim ya rasu sai manzon Allah yayi kuka sai me ta'aziyya yace masa:
“ kodai Abubakr ko Umar lallai kaine mafi cancantan wanda Allah ya girmama hakkin sa sai manzon Allah s.aw yace: “ lallai idanu sunayin hawaye kuma zuciya tana bakin ciki amma bazamu fadi abunda zai fusata Ubangijin mu ba badan yayi alkawari na gaskiya ba da kuma lokaci na taro kuma lallai karshe yana bin na farko ne da mun samu akan ya Ibrahim mafificin abunda muka samu kuma lallai muna bakin ciki dakai ” Ibn majjah ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.
•    Yana dariya kuma yana kuka, Usama dan zaid yace wani yaro na daya daga cikin yaran manzon Allah s.a.w mata ya rasu, sai ta aika masa domin yazo mata, sai ya aiko mata:
“ lallai ga abun ya Allah ya amsa nashi ne kuma abunda ya bayar nashi ne kuma dukkan komai a wurin sa yana kasancewa ne zuwa wani lokaci sananne kiyi hakuri kuma jure ” .
Sai ta aiko masa tayi masa rantsuwa sai manzon Allah s.a.w ya tashi sai na mike nima nabishi da mu'azu dan jabal da ubayyu dan ka'ab da ubadata dan samit a lokacin da muka shiga sai manzon Allah s.a.w ya dauki yaron ransa yana jijjiga da motsi a cikin zuciyar sa sai yace: ran ya fita sai manzon Allah s.a.w yayi kuka sai ubada dan samit yace masa: menene wannan ya manzon Allah? Sai yace: “ rahama ce wanda Allah ya sanya cikin zukatan dan adam kuma lallai Allah yanayin rahama ne ga bayin sa musu jin tausayi ” buhari da muslim ne suka rawaito shi da kuma Ibn majjah kuma lafazin nashi ne.
•    Yana farin ciki kuma yana jin radadi , a lokacin da jafar yazo gun manzon Allah s.a.w daga kasan habasha, sai idanun manzon Allah suka gashi sai yace: “ bansan da zuwan jafar ba shin dashi ne zanyi farin ciki ko kuma da bude garin khaibara? ” hakan sai yayi daidai da bude garin khaibara. Silsilatul sahiha.
•    Yana rafkana kuma yana mantuwa, hakika yayi mantuwa cikin sallar sa kuma aka tunatar dashi, Abdullahi dan Umar yana cewa:
“ manzon Allah s.a.w yayi mana sallah cikin daya daga sallar azahar ko kuma la'asar raka'a biyu sai zul yadaini yace: ya manzon Allah ka manta ne ko kuma an rage raka'ar sallar ne? sai yace: “ banyi mantuwa ba kuma ba'a rage raka'ar sallar ba ” . Sai yace: ai raka'a biyu kayi, sai ya juyo ya kalli mutane yace: “ shin abunda zul yadaini ya fada haka ne? ” sai suka ce: eh haka ne, sai ya mike ya ciko raka'a biyun sa'annan yayi sujjada biyu na rafkanuwa ” buhari ne ya rawaito shi.
•    Kuma ba ma'asumi bane cikin mu'amular sa da ijtihadin san a mutum ta yadda yana dacewa yana kuma yin kuskure, sai dai ma'asumi ne cikin abunda yake isarwa na wahayi akan Allah, hakika manzon Allah ya wuce wurin bishiyan dabino sai yaga mutane suna barbarian dabino, sai yace:
“ menene haka suke aikatawa? ” sai sukace suna daukan namiji ne su hadashi da mace, sai yace: “ bana tunanin hakan yana amfanar da wani abu ” sai hakan ya isa zuwa garesu, sai suka daina aikata hakan, sai dabinon su ya lalace suka sanar da manzon Allah s.a.w sai yace: “ ai tsammani ne, idan yana amfanar da wani abu ku aikata, ni mutum ne irin ku, kuma me zato yana dace wa kuma yanayin kuskure, sai dai bance maku Allah yace ba, saboda bazanyi karya ga Allah ba ” muslim ne ya rawaito shi.
•    Manzon Allah s.a.w yana tsayawa a matsayin mutum cikin mu'amalar sa da mutane, yadda yake cewa:
“ ya Allah! Lallai Muhammad mutum ne yana fushi kamar yadda mutane ke fushikuma lallai na rike alkawari agunka wanda baka sabamun shi ba, duk wani muminin da na cutar dashi ko kuma na zage shi ko na duke shi kasanya hakan ya zama kaffara ce a gareshi da kuma kusanci wanda zaka kusanto shi zuwa gareka dashi rana alkiyama ” muslim ne ya rawaito shi.
•    Kuma mutum ne cikin hukuncin sa dayake masu da kuma akan sa, yadda yake cewa:
“ lallai ni mutum ne kuma kuna kawomun sa'in san ku na maku hukunci, me yuwa wasu sufi wasu karfin hujja sai na bashi gaskiya na hukunta mashi wannan abu gwargwadon abunda naji, to duk wanda ya bashi hakkin dan uwan sa kada ya amsa saboda yanki ne na wuta nabashi ” buhari ne ya rawaito shi.
•    Kuma mutum ne cikin rayuwan sa na al'umma yana aure kuma yanason zuriya kmaar yadda sauran annabawa suke wanda suka gabace shi, Alah madaukaki yana cewa:
“ hakika mun aika da manzanni gabanin ka kuma mun sanya masu mata da zurriyya, kuma babu wani manzo da zai iya zuwa da wata aya sai da izinin Allah, ko wani ajali an rubuta shi cikin littafi ” suratul ra'ad ayata 38.
•    Kuma a wannan gabar zamu kawo wasu bangarori na mu'amalar sa a matsayin mutum da iyalan sa:
1.    Manzon Allah me karamci yana yin yafiya game da kurakuran iyalan sa:
Kishi dabi'a ce ta mutum manzon Allah s.a.w ya kasance yana tunkaran sa daga iyalan sa da budaddiyar zuciya annan kuma ya magance shi da hikima da kuma hakuri, Anas Allah ya kara masa yarda yana cewa: manzon Allah s.a.w ya kasance a wurin daya daga cikin matan sa, sai daya daga cikin su ta aika masa da kwano da abinci aciki, wai matar dayake gunta ta bigi hannun dan sakon sai wannan kwano ya fadi ya fashe, sai manzon Allah s.a.w ya tattara shi sai ya fara tattara abincin cikin kwanon yana cewa: (mahaifiyar ku tana kishi) sa'annan ya tsayar da wannan dan sako har sai da aka kawo sabon kwano irin wannan wanda yake gidan wannan mata inda yake, sai yaba wannan dan sakon wannan kwanon me kyau ya rike wannan wanda ya fashe a wannan gidan wacce ta fasa. Buhari ne ya rawaito shi.

2.    Manzon Allah me karamci ya kasance yana cika alakwari ga iyalan sa:
Cika alkawari da kiyaye soyayya da kuma rashin inkarin me kyau sifface wacce take nuna akan asalin me ita da kuma kyauwun halayen sa hakika manzon Allah s.a.w ya kasance:
“ idan aka ambaci Khadija sai ya yabe ta kuma ya kyautata yabon ta, sai yace: wata rana sai kishi ya kamani akan sai nace me yasa kake yawan ambaton me jan haba bayan Allah ya canza maka da wacce ta fita alheri. Sai yace Allah be canzamun ba da wanda tafita alheri ba hakika tayi imani dani a lokacin da mutane suka kafurce mun kuma ta gasgatani a lokacin da mutane suka karyta ni, kuma ta yalwatamun da dukiyar ta a lokacin da suka haramtamun dukiyar su kuma Allah ya azurtani da yaronta a lokacin daya haramtamun yaron sauran mata. Bayanin ingancin hadisin ya gabata a baya.

3.    Manzon Allah s.a.w yayi mu'ama me kokoluwan kyau da iyalan sa:
Cikin rayuwan sa baki daya tun gabanin bashi annabta zuwa bayan bashi annabta ba'a taba hakaitowa ba cewa ya daga hannun sa masu albarka ya duki mace wannan kenan mu'amalar sa da jama'an gari yaya kake gani to zai kasance tare da iyalan sa kuma mun sani cewa gidan ma'aurata dai baka raba shi da yar matsala kuma gidan manzon Allah s.a.w irin haka ne shima bawai ya sabama asali bane amma kasancewar be taba dukan daya daga cikin matar sa ba ko kuma ya fada mata magana mara dadi Aisha Allaha ya kara mata yarda tace:
“ manzon Allah be taba dukan wata mace ba ko sau daya ” sahihu Ibn hibban da baihaqi da nasa'I ne suka rawaito shi.
Kuma Aisha ta kara fadi har wayau Allah ya kara mata yarda: “ be taba dukan wani dan aiki ba ko sau daya ko kuma wata mace, kuma manzon Allah be taba dukan wani abu ba da hannun sa ko sau daya sai dai yayi jihadi domin Allah, kuma ba'a taba bashi zabi ba tsakanin abu biyu face ya zabi wanda yafi sauki daga cikin su matukar bas abo bane hakan, idan hakan ya kasance sabo ne to ya kasance wanda yafi koma nisantar haka, kuma manzon Allah s.a.w be taba daukan fansa ba akan laifin da akayi mashi a karon kansa sai dai idan an keta hurumin Allah madaukaki sai ya dau fansa akan hakan ” silsilatul sahiha.

Taya hakan bazai faru ba bayan shine wanda aka aiko shi rahama ga talikai, wannan Sahal ne dan Sa'ad yana cewa: “ naga manzon Allah s.a.w a lokacin da aka karya masa hakoran sa na gaba da ji masa rauni a fuska aka kuma karya kariyan da yasa akai, lallai nasan wanda ya wanke masa jinin fuskan sa, da wanda yake zuba masa ruwa da abunda da aka sanya masa a raunin har jinin ya tsaya, fadima diyar manzon Allah s.a.w ta kasance tana wanke jinin fuskan sa Aliyu kuma yana zuba mata ruwa, bayan ta wanke jinin fuskan mahaifinta sai ta kona ciyawa bayan ya zama toka sai ta dauka wannan toka ta sanya masa a fuskan say a tsayar da wannan jini, sa'annan yace: a wannan rana fushin Allah ya tsananta akan mutanen da suka jima fuskan manzon Allah s.a.w rauni, sa'annan ya zauna na tsawan awa daya, sai yace: ya Allah ya gafartawa mutane na lallai basu sani bane ” silsilatul sahiha.

4.    Manzon Allah s.a.w yana tausayin iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance mijin mata tara wanda yake da dalilai da kuma abunda ya sanya shi hakan daga cikin dalilan hakan shine rahama da tausayi da kuma sanin da aka masa da kyautatawa ga wanda yayi imani dashi ya kuma bishi ya kuma hadu da cutarwa ta sanadiyyar haka daga cikin irin wannan dalili ne yasa ya aure Saudat diyar zam'ata Allah ya kara mata tana da shekaru hamsin da biyar a lokacin kuma hakika mutanen makka sunyi mamaki akan wannan aure saboda bata kasance ba tanada kyau ko kuma wani abunda da maza suke so ba tare da ita kuma tana da yara biyar amma tausayin sa na mutum ya sanya tausayama halin ta, da kuma tausayi akanta da karramata da kuma dauke mata hatsarin dake biye da ita na dawowan ta daga habasha da kuma rasuwan mijin ta, manzon Allah yaso ya sake ta bayan wasu lokuta masu yawa saboda tausayin dayake yi nata na ganin kada ya daura mata nauyi na rayuwan aure wanda bazata iya dauka ba amma alokacin da taji haka sai tace manzon Allah s.a.w: kada ka sake ni ka rike, ka sanya ranaku na ga Aisha, sai ya aikata hakan sai aya ya sauka cewa:
“ babu laifi a garesu da suyi sulhu atsakanin su kuma sulhu alheri ne ” saboda kwadayin da takeyi na ganin an tashe ta cikin matan manzon Allah s.a.w ranan alkiyama ” . Tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.

5.    Manzon Allah s.a.w da rahamar sa ga iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya shiga masallaci sai yaga igiya an daura su a tsakanin ginshikin masallaci guda biyu sai yace: wannan igiyar kuma fa, sai sukace: igiyar Zainab ce ta daura idan tana salla ta gaji sai ta jingina ajiki domin ta dawo cikin nishadin ta, sai manzon Allah s.a.w yace: “ ku kwancw ta lallai dayanku ya rika salla cikin nishadin sa idan ya gaji sai ya zauna ” sahihu muslim da Abu dawud da nasa'i da Ibn Hibban ne suka rawaito shi.
Addinin ne daga Allah manzon Allah bayason iyalan sa su daurama kan su wani Ibadan da bazasu iya ba wanda hakan zai tasirantu cikin harkokin sun a rayuwa taya hakan bazai faru ba bayan shine me fadin ga sahabin sa wanda ya shagaltu da aikin bauta yabar duk wani abubuwan dadin rayuwan duniya na halal: “ lallai idanun ka suna da hakki akan ka, kuma jikin ka yana da hakkin akanka, kuma matar ka tanada hakki akanka, kuma bakon ka yanada hakki akanka, kuma abokin ka yanada hakki akanka ” hadisi ne ingantacce Nisa'i ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.

6.    Manzon Allah s.a.w yana neman yardan iyalan sa:
Hakika manzon Allah s.a.w ya kasance wanda yafi kowa hakuri musamman ga iyalan say a kasance yanajin abunda zai bata masa rai daga garesu sai ya kawar dakai kuma yana ganin cutarwa daga garesu yayi hakuri da yin yafiya daga abunda suke aikatawa na laifi matukar be sabama shari'a ba yana tunkarar haka da murmushi wacce take kara dankon soyayya da yafiya da tausayi, kayi nazarin wannan tsabar hakuri na manzon Allah s.a.w ka gani akan matan sa lokacin da Aisha Allah ya kara mata yarda ta daga muryanta akansa cikin wani magana da suke yi a tsakanin su sai Abubakar Allah ya kara masa yarda yaji haka sai ya shiga yana neman ta ya bugeta yace mata bazan ina ganinki ba kina daga sautin ki ga manzon Allah s.a.w ya kyale ki, sai manzon Allah s.a.w ya koma kareta kada ya duketa sai Abubakar ya fita cikin fushi sai manzon Allah s.a.w yace a lokacin da Abubakar ya fita:
“ ya kika ganni ina kareki daga wani kada yadukeki ” sai Abubakar ya zauna na tsawon wasu kwanaki sa'anan ya nemi izinin manzon Allah s.a.w na shigowa sai ya same su sun sasanta sai yace masu: ku sanya ni cikin sulhun ku kamar yadda kuka sanya ni cikin fadan ku sai manzon Allah s.a.w yace: “ hakika mun aikata hakika mun aikata ” Abu dawud ne ya rawaito shi.

7.    Manzon Allah s.a.w yana saukakawa iyalan sa:
Ya kasance manhajin manzon Allah s.a.w na mu'amala tare da mutane yin sauki da rangwane da tausasa masu, an karbo daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace:
“ wani bakauye ya shiga masallaci… kawai ba'a farga ba sai akaga yana fitsari a wani bangare cikin masallaci, sai mutane sukayi masa ca akai, sai manzon Allah s.a.w ya hanasu yace: lallai an aiko ni ne domin saukakewa ba dan tsanantawa ba, ku zuba bokitin ruwa akan fitsarin nasa ” hadisi ne ingantacce Abu dawud ne ya rawaito shi.
Aisha Allah ya kara mata yarda uwar muminai tana cewa game da saukin da tausayin manzon Allah akan iyalan sa:
“ an kawo mana kyautan abinci ni da Hafsa kuma muna azumi sai daya daga cikin su tace ma dayar: shin zaki iya karya azumin? Sai tace: eh, sai suka karya azumin su biyu, sai ga manzon Allah s.a.w ya shigo sai tace mashi: ya manzon Allah! An kawo mana kyautan abinci sai ya bamu sha'awa muka karya azumin mu, sai yace: babu komai akan ku, ku azumci wani rana a maimakon sa ” Ibn hibban ne da abu dawud suka rawaito shi, albani yace: hadisi ne me rauni, shu'aibu alarnut yace: silsilan sa ingantacce ne akan sharadin muslim.

8.    Manzon Allah s.a.w yana tausasawa wajen mu'amala da iyansa:
Lallai daukan abinci da hannun ka zuwa bakin matar ka da kuma bata ruwa bawai kawai aiki ne wanda yake nufin mallakan zuciyar matar ka da kuma nuni akan kyakyawan mu'amala tare da ita da nuna mata so bane kawai hakan sadaka ne wanda ake baka lada akai daga Allah kuma a sanadiyyar haka akwai kulla akala tsakanin abunda yake na duniya ne da kuma na lahira wanda yake ci gaba da dauke kewa kuma yana tafiyar da damuwa da kuma samarwa iyalai da natsuwa da kwanciyar hankali, manzon Allah s.a.w yace ma Sa'ad dan abi waqqas:
“ kuma baka ciyar da wani ciyarwa wanda kake neman yardan Allah d ahakan face an baka lada akanta hatta lomar da kake sanyawa abakin iyalinka ” buhari ne ya rawaito shi.

9.    Manzon Allah baya nuna rashin kula ga iyalan sa:
Lura da yanayi dalili ne na tsabtar zuciyar mutum manzon Allah s.a.w ya kasance yana lura da yanayin iyalan sa baya daure fuskan sa daga labarin da suke bashi wanda ya fita daga abunda suke so, Ammar dan yasiri Allah ya kara masa yarda yana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya yada zango domin baccin karshen dare da hutawa cikin tafiyar sa sai mutane suka sauka cikin wani wuri da ake kira da suna aulatul jaishi tare dasu akwai Aisha matar sa sai sarkanta ya fadi wanda aka kawo mata daga kasar yeman sai ya tsare mutane anan wurin domin neman wannan sarka nata har hasken alfirir ya fito kuma mutane basu da ruwan yin alwalla sai abubakar ya kausasa mata mata yace mata kawai kin rike mutane a wurin nan kuma basu da ruwa sai Allah ya saukar da ayar sauki dayin taimama da kasa sai musulmai suka tashi tare da manzon Allah s.a.w suka shafi kasa da hannun su ba tare da sun goge dattin ba suka shafa a fuskar su da hannun su har zuwa kafada da kuma cikin hannun su har zuwa hammatan su ” . Ahmad da abu dawud da nasa'I ne suka rawaito hadisin kuma albani ya inganta shi.

10.    Manzon Allah s.a.w yana kwalliya da tsabta da sanya turare domin iyalin sa:
Lallai shiga me kyau da kamshi yana daga cikin abunda yake dadada rai da kawo natsuwar zuciya da kuma ido ke jin dadi da natsuwan kallon sa, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ kaman ina kallon farfashi na turaren miski akan manzon Allah s.a.w yana cikin haraman aikin hajji a cikin gashin kansa s.a.w ” . buhari da muslim ne suka rawaito shi kuma lafazin na buhari ne.
Kuma a lokacin da aka tambayi Aisha Allah ya kara mata yarda cewa: dame manzon Allah s.a.w yake faraway idan ya shiga gida wurinku? Sai tace yakasance idan ya shigo asuwaki yake farawa dashi ” . Ahmad da abu dawud da Ibn majjah ne suka rawaito shi kuma albani ya ingantashi.
Kuma hakika turare tsabta ya kasance dabi'ar manzon Allah s.a.w cikin dukkanin halin sa hatta a halin baccin sa baya kwanciya sai da tsarki da tsabta, me masa hidima Anas dan Malik wanda ya samu daukaka da masa hidima na shekaru goma yana cewa:
“ ban tama jin wani irin kamshi ba wanda yafi kamshin manzon Allah s.a.w. kuma bantaba taba wani abuba me taushi hatta Hariri wanda yakai hannun manzon Allah s.a.w taushi ” muslim ne ya rawaito shi.

11.    Manzon Allah s.a.w yana bayyana soyayyar sag a iyalan sa:
Kunya baya zuwa sai da alheri kamar yadda manzon Allah s.a.w ya fadi sai wanda ya kasance sababi na buye wani al'amari cikin addinin musulmai ko kuma na rayuwan sun a duniya, manzon Allah s.a.w ya kasance yana bayyana soyayyar sag a iyansa domin bada tarbiyya ga mabiyan sa dan su rika babbaya son su akan iyalan su domin daurewar soyayya da rayuwan aure, Amru dan Aas yana cewa:
“ nazo wurin manzon Allah s.a.w sai nace masa: wani ne kafi so cikin mutane? Sai yace: “ Aisha ” , sai nace cikin maza fa? Sai yace: “ mahaifinta ” , sai nace sai kuma wane? Sai yace: “ Umar ” , sai ya irga mutane sai nayi shir daga nan ina tsoron kada ya sanyani a karshen su ” . Buhari da musulim ne suka rawaito shi kuma lafazin na buhari ne.

12.    Manzon Allah s.a.w yana tsoron wani abunda zai cutar da iyalan sa:
Tsoro abune na dabi'ar mutum kuma abune na fidira matukar be wuce tsoro na dabi'a ba amma abunda ya wuce hakan to ciwo ne, kuma manzon Allah s.a.w ya kasance yana tsoron abunda zai cutar da iyalan sa kuma yana kokarin ganin wani abun ki be same su ba, Anas yana cewa:
“ sun fita tare da manzon Allah da Abu dalha, kuma tare da manzon Allah akwai safiyyat wanda ya daurata a bayan sa akan rakumi, akan hanyar su sai wannan rakumi ta zauna sai manzon Allah s.a.w ya firgita da matar, kuma abu dalha yace: ina tsammanin sun fadi a kasa, Sai yazo wurin manzon Allah s.a.w yace: ya annabin Allah Allah ya sanyani fansa a gareka, wani ya sameka? Sai yace: “ a'a babu abunda ya same ni amma dai ka kula da matar ” sai abu dalha ya jefa rigan sa akan fuskar matan ya nufi wurin ta, sai ya jefa mata rigan sa, sai ta tashi, sai ya daura su akan abun hawar sa. buhari ne ya rawaito shi.

13.    Manzon Allah s.a.w yana himmatuwa akan tsarin iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasanc eyana son alheri ga iyalan sa yana kuma kokari wurin kara masu alheri musamman ma abunda zai gadar masu da yardan ubangijin talikai da kuma kusantar dasu zuwa aljanna ya kuma nisantar dasu daga wuta wannan shine rabon da Allah yayi bayanin sa cikin fadin sa cewa:
“ ko wace rai sai ta dandani mutuwa kuma ana baku ladan ku ne a ranan alkiyama duk wanda aka nisantar dashi daga wuta aka shigar dashi aljanna to hakika ya rabauta rayuwa duniya kuma ba komai bace face jin dadi na rudu ” suratu al'imran ayata 185.
Manzon Allah ya kasance yana bibiyan iyalan sa da nuna masu hanyar alheri da kuma shiryar dasu zuwa gareta, Ummu salmata matar manzon Allah s.a.w tana cewa: manzon Allah s.a.w ya tashi cikin dare a firgice yana cewa:
“ tsarki ya tabbata ga Allah menene abubuwan da Allah ya saukar na dumbin rahamar sa, kuma menene ya saukar na fitina! Wanene zai tayar da mutanen dakin sa watan iyalan sa suyi salla, me yuwa kaga mutum cikin ni'ima a duniya amma a lahira ya kasance cikin akasin haka ” buhari ne ya rawaito shi.

14.    Manzon Allah s.a.w baya shigo ma iyalan sa babu sanarwa ko izini:
Manzon Allah s.a.w ya kasance yana kyamar bazata ko kuma kishi wanda ya wuce iyaka na dabi'a kuma yanason ganin iyalan sa cikin yanayi me kyau da kamala hakan yan afaruwa ne domin kwadayin say a ganin ya tabbatar masu da alaka na soyayya tare dasu, ya kasance baya zuwa masu bazata idan ya dawo daga tafiya, dabi'ar sa shine sanar da isowar sa domin ya kasance iyalan sa sunada lokaci me yalwa wanda zasuyi kwalliya da tsabta da kuma shiryawa tarban sa sai yaga iyalan sa cikin siffa me kyau da yanayi domin tabbatar da alakar soyayya, jabir dan Abudllahi yana cewa mun kasance tare da manzon Allah s.a.w cikin tafiya lokacin da muka kusa shigiwa gari sai yace:
“ ku sassauta tafiyar ku domin mu isa cikin dare domin masu gashi su gyara kuma macen da mijinta yayi tafiya ta aske gashin jikin su ” buhari da muslim ne suka rawaito shi.

15.    Manzon Allah s.a.w yana gabatar da alheri ga iyalan sa:
An daura shi akan dabi'a na karamci da kyauta ya kasance yana gabatar da iyalan sa akan karon kansa yana kuma basu abunda aka kawo mashi kyauta ko kuma wanda ya samu, taya bazai zama haka ba bayan shine me fadin cewa:
“ idan Allah yaba dayanku alheri to ya fara da kansa da iyalan gidan sa ” dabari ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.
Maganar sa bawai kawai na fatan baki bace a'a ya kasanc eyana aiwatar da abunda da yake fadi a kasa, Anas Allah ya kara masa yarda yana cewa:
“ Ummu sulaim ta aikeshi da kwano a ciki akwai dabino yakaima manzon Allah s.a.w, sai ya rika debo wannan dabino da hannun sa yana aikawa zuwa ga matan sa kuma yana sha'awar wannan dabino ya aikata hakan sau da dama alhali yana sha'awar abun ” Ahmad da Ibn Hibban ne suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi.

16.    Manzon Allah s.a.w ya kasance yana Kankan dakai ga iyalan sa:
Duk wanda ya Kankan dakan sa domin Allah, to zai daga darajar sa da wannan kalmomi ne manzon Allah s.a.w yake yima sahabban sa magana kuma ya kasance yana aiwatar da haka a aikace cikin mu'amalar sa tare da mutane kuma be haramtawa iyalan sa haka ba, maganar Anas:
“ Cikin hadisin san a dawowar su madina tare da manzon Allah daga khaibara tare da manzon Allah s.a.w akwai matar sa safiyya Allah ya kara mata yarda yana rike da abayarta a bayanta, sa'annan yana tsugunawa ta taka shi tahau kan abun hawa ” buhari ne ya rawaito shi.

17.    Manzon Allah s.a.w ya kasance yana yafema iyalan sa laifin da sukayi:
Manzon Allah s.a.w ya kasance yana daraja kishin matar sa baya fushi idan suna kishi kuma baya kyamatar sakamakon wannan kishin na ayyukan su sai dai yana magance hakan ne da salo na daki daki wanda yake nuni akan kwarewa da kuma hikima, Anas dan Malik yana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance a dakin daya daga cikin matar sa sai daya daga cikin su ta aiko maa da kwano da abinci aciki sai ta bigi hannun manzon Allah s.a.w wannan kwano ya fadi ya fashe, sai manzon Allah s.a.w hada wannan kwano wanda ya fashe ya fara tattara abincin yana cewa: “ mahaifiyar ku tayi kishi kuci sai sukaci! Sai ya rike wannan kwano anan gidan ya aikama wancen matar da kwanon wannan gidan me kyau ita kuma ya bata wannan kwanon data fasa ya zama nata ” buhari ne ya rawaito shi.

18.    Manon Allah s.a.w yana sanin labarin zuci wanda iyalan sa ke ciki:
Saukin sa ta kula da kuma aikin say a sanya manzon Allah s.a.w yana jin damuwar iyalan sa kuma yana jin abunda sukeji sai ya tare abunda yake mara kyau aciki da lafiya da hakuri, Aisha uwar muminai Allah ya taka mata tarda tace manzon Allah s.a.w yace mata:
“ ni ina sanin idan kina cikin annashwa dani, kuma idan kina fushi dani shima nasani ” sai tace: sai nace taya kasan haka? Sai yace: “ idan kina cikin fara'a kina cewa ne: a'a ina rantsuwa da ubangijin Muhammad, amma kuma idan kina cikin fushi cewa kikeyi: a'a ina rantsuwa da ubangijin Ibrahim ” , sai tace: sai nace kwarai kuma wallahi haka ne ya manzon Allah bana kaurace maka sai sunan ka kawai ” buhari ne ya rawaito shi.

19.    Manzon Allah s.a.w ya kasance yana adalci a tsakanin iyalan sa:
Hakika adalcin sa tare da iyalan sa yakai kololuwa ya kasance yana masu adalci cikin dukkanin al'amuran sa cikin tafiyar sa da lokacin da yake gida, Aisha Allah ya kara mata yarda tace:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance baya fifita wasun mu akan wasu wurin raba kwana kuma ya kasance cikin ko wani rana yana kewaya mu sai tsuguwa har sai ya koma zuwa dakin wacce yake wurin ta… ” abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
Kuma baya sakace ina bada mahaifiyata da mahaifina fansa a gareshi wurin yin adalci wanda Allah ya halicce sa akan haka hatta a lokacin rashin lafiyar sa, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ lallai manzon Allah a lokacin rashin lafiyar sa wanda mutuwa yazo masa aciki, yana cewa: “ a ina nake gobe, a ina nake gobe ” yana son yaji ance dakin Aisha, sai matan sa suka masa izini daya zauna a inda yake so, sai ya kasance a gidan Aisha har mutuwa yazo mashi anan ” buhari ne ya rawaito shi.

•    Manzon Allah s.a.w ta bangaren zamantakewa da iyalan sa.

1.    Mazon Allah s.a.w ya kasance me sauki da tausayi ga iyalan sa:
Sauki be taba shiga cikin wani abu ba face ya daga darajarsa kuma sauki be taba fita daga cikin wani abu ba face sai abun ya lalace, karantarwan manzon Allah me daraja wanda ya tarbiyyanci mutanen sa akai, ya kasanc eme sauki cikin dukkanin al'amuran sa yanason sauki kuma yana umurtan iyalan sa dashi baya umurtan su kuma baya sauraro daga wurin su kuma baya daura masu abunda zai tsananta masu, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa manzon Allah s.a.w yace mata:
“ ya Aisha ki saukaka domin lallai Allah idan ya so mutanen wani gida da alheri sai ya shigar masu da sauki ” Ahmad ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi cikin littafin al sahiha 523.

2.    Manzon Allah s.a.w ya kasance yana hidimar iyalan sa:
Daga cikin kyawawan halayen sa ya kasance baya barin hidimar iyalan sa da kuma tayasu wasu ayyuka, hakika an tambayi Aisha Allah ya kara mata yarda:
“ menene manzon Allah s.a.w yake aikatawa a gidan sa? sai tace: yana dinke takalmin sa kuma yana aikata abunda namiji yake aikatawa agidan sa. acikin wata ruwaya kuma tace: abunda wanin ku yake aikatawa agidan sa: yana dinke takalmi kuma yana wanke kayansa da dinki. [buhari ne ya rawaito shi cikin littafin adabul mufrad.

3.    Manzon Allah s.a.w yana yima kansa hidima:
Kowa a cikin mu yana da lalurorin sa wanda suka shafe shi manzon Allah s.a.w ya kasance yana ayyukan san a hidimar sa domin saukakewa iyalan sa da kuma taimakon su, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa a lokacin da aka tambayeta:
“ menene manzon Allah yake aikatawa a gidan sa? sai tace: ya kasance mutum ne cikin mutane yana duba kayansa ko akwai datti, kuma yana tatsan nonon daga akuya da kan sa da kuma yima kansa hidima ” . [Buhari ne ya rawaito shi cikin littafin adabul mufrid].

4.    Manzon Allah s.a.w yana ciyar da iyalan sa:
Kyauta da ciyarwa shi ginshiki ne wanda yake dasasu cikin zukatan mabiyan sa yana cewa:
“ lallai Allah me karamci ne kuma yana son masu karamci kuma me yalwa ne da kyauta yana san masu yalwata wa ” silsilatul sahiha 1378 da 1626.
Ya kasance yana yalwatawa iyalan sa wurin ciyarwa baya masu rowa yana cewa:
“ dinarin da ka ciyar domin daukaka Kalmar Allah da kuma dinarin da ka ciyar wurin yanta wuya da kuma dinarin da kayi sadaka dashi ga miskini da dinarin daka ciyar da iyalan ka dashi, wanda yafisu lada shine wand aka ciyar da iyalan ka dashi ” muslim ne ya rawaito shi.
Be tsaya nan ba kawai ya sanya shi hakki ne na wajibi akan namiji ga iyalan sa a lokacin da wani sahabi ya tambaye shi cewa ya manzon Allah menene hakkin matan dayan mu akan shi? Sai yace:
“ ya ciyar da ita idan yaci abinci kuma ya tufatar da ita idan ya tufatar da kan sa ” Ahmad ne da abu dawud da nasa'I da ibn majja suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi.

5.    Manzon Allah s.a.w yana son iyalan sa su rika hutawa:
Ya kasance s.a.w yana neman hutun iyalan sa yana kuma aiki wurin ganin ya tabbatar dashi musamman a halin tafiya wanda ya kasance matattarin wahalada gajiya yana ji masu tsoron gajiyan tafiya, Anas dan malik yana cewa: manzon Allah s.a.w ya kasance acikin tafiya sai wani yaro yana ya fara masu waka da sauti me kara wanda ake kira da suna Anjashata sai manzin Allah s.a.w yace masa: “ bi a hankali ya Anjashata kada ka karya kwalabe - anan wurin kwalabe ana nufin mata saboda zuciyar su saurin karaya yake dashi kamar kwalba shi yasa manzon Allah s.a.w daya ga yana sauri yace masa yabi a hankali saboda mata kada su gaji - ” buhari ne ya rawaito shi.
hakan saboda iyalan manzon Allah sun kasance cikin wata yar bukka akan rakumi idan kuma ana masu waka da sauti babba sai rakumi ta fara sauri wurin tafiya sai manzon Allah s.a.w yaji tsoron kada wani abu ya sami iyalan sa.

6.    Manzon Allah s.a.w yana hakuri da danniya akan rikicin iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance yana kalubalantar rikicin iyalan sa da tarairaya da kuma musifar su da sakin fuska da kuma kaurace warsu da soyayya yana masu hakuri da yafiya akan abunda suka aikata na kura kurai wanda be sabama shari'a ba kumayawan rashin sani baya kara masa komai a gunsa face hakuri, Umar dan kaddab Allah ya kara masa yarda yana cewa:
“ mun kasance jama’ar kuraishawa muna da rinjaye akan mata, amma bayan mun dawo madina sai mukaga su mutane ne wanda mata ke da rinjaye akan su, sai matan mu suka fara daukan halayen matan madina, sai nayima matata tsawa sai ta rika maimaitamun magana tana kallona sai nayi inkarin haka, sai tace: me yasa kake inkarin maimaita maka maganar dana keyi? Na rantse matan manzon Allah s.a.w suna maimaita masa magana, kuma wata daga cikin su tana kaurace masa na tsawon yini, sai hakan ya fusatani na tafi wurin Hafsa nace mata: wai dagaske ne kuna sa'in sa da manzon Allah s.a.w na tsawon yini? Sai tace: eh, sai nace: hakika kinyi asara kuma kin tabe, shin yanzu kin yarda da fushin Allah domin fushin manzon sa sai ki halaka? Ki daina neman dayawa daga wurin manzon Allah kuma ki daina maimata masa magana kuma kada ki kaurace masa, ki rika tambayata duk abunda kike so ” buhari ne ya rawaito shi.

7.    Manzon Allah yana tabbatar da abunda iyalan sa suke so:
Ya kasance mafi gaggawa cikin tabbatar da abunda matar sa ke so da kuma jawo masu farin ciki hakika Aisha ta tambayi manzon Allah s.a.w tace: ya manzon Allah dukkan matan ka suna da sunan shagube bandani sai amnzon Allah s.a.w yace mata:
“ zan maki sunan shagube da yaron ki Abdullahi yana nufin dan zubair kece maman Abdullahi ” ya kasance yana kiranta sa suna mamar Abdullahi har yam utu bata taba haihuwa ba ” buhari ne ya frawaito shi cikin littfain adabul mufrid kuma albani ya ingantashi.

8.    Manzon Allah s.a.w yana yima iyalansa likitanci:
Mutum yanada bukata matuka da hakan da kuma lura dashi da tashi tukuru da sha'anin sa cikin halin lafiyar sa wanda a halin rashin lafiya da rauni yafi bukatar haka, kuma hakika manzon Allah s.a.w ya kasance be manta da wannan bangare ba yana bibiyan iyalan sa cikin halin rashin lafiyar su domin yi masu likitanci da hatsarin da suke ciki da kuma girmama su, Aisha uwar muminai Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance idan daya gada cikin iyalin sa ba lafiya yana mata tofi da kula'uzzai (watan yana karanta masu suratul ikhlasi da falaki da nasi ya tufa masu). A lokacin daya kwanta rashin lafiyar sa ta ajali sai ya fara yi masa tofi ajikin sa sai na tofa a hannun san a shafa masa domin hannun sa yafi nawa albarka ” muslim ne ya rawaito shi.

9.    Manzon Allah yana nuna kula ga iyalan sa:
Duk da yawan ayyukan da yake dashi masu yawa na shugabancin mutanen sa amma hakan baisa ya manta da iyalan sa ba da kuma shagaltuwa da mantawa dasu ba , Umar dan kaddab yana cewa: manzon Allah s.a.w ya kasance idan yayi sallar asuba sai ya zauna a wurin da yayi salla mutane su zo su zauna a gefen sa har sai rana ta fito daganan sai ya tashi ya shiga gida wurin matan sa yabi dakin kowa cikin su daya bayan daya yana masu sallama da masu addu'a idan ranan daya ne sai ya zauna a dakinta. Dabarani ne ya rawaito shi cikin ausat.

10.    Manzon Allah s.a.w yana shawarantan iyalan sa:
Manhajin sa da dabi'ar sa itace yin shawara cikin al'amuran sa wanda suka shafe sa da kuma ayyukan da suka shafi jama'a ya kasance yana shawartan iyalan sa da amfana daga ra'ayoyin su da hangen nesan su yana tarayya dasu har acikin al'amuran sa shugabancin jama'a sai ya duba shawarar da tafi acikin su da wanda tafi dacewa kafin ya yanke hukunc na karshe, an karbo daga Urwata dan Zubair daga Mirwan dan Hakam da miswara dan makhrama cewa sun fada masa cewa, an Ambato labarin su a sulhul hudaibiya sunce: bayan an gama rubuta yarjejeniya na sulhun hudaibiya sai manzon Allah s.a.w yace: yaku mutane! Ku mike ku yanka dabbobin ku sannan kuma ku cire ihramin ku, wallahi babu wanda ya tashi saboda abun haushin daya kama mutane, sai manzon Allah s.a.w yace: ku yanka dabbobin ku kuma ku cire haraman ku wallah babu wanda ya tashi daga cikin su, ya kara maimaita hakan har sau uku babu wanda ya tashi, sai manzon Allah s.a.w ya tashi ya shiga wurin ummu salimata yace mata: ya ummu salimata! Bakiga abunda ke faruwa bane ina umurtan mutane amma sunki aikata abunda na umurce su dashi? Sai tace masa: ya manzon Allah! Kada ka damu dasu domin mutane lallai wani abu babba ya shiga cikin zuciyar sun a ganin ka daura kanka akan sulhun nan, abunda za'ayi ka fita ne ya manzon Allah! Kada kayiwa kowa magana har sai ka yanka dabbarka sannan ka cire haramar ka, domin mutane idan sukaga ka aikata hakan zasu aikata da sauri, beyima kowa magana ba ya wuce aka kawo masa hadayar say a yankata sai yayi aski, a lokacin da mutane sukaga manzon Allah ya aikata hakan sai kowa ya tashi ya yanka hadayar sa, wasu daga cikin su sukayi kwal kobo wasu kuma sukayi saisaiye, sai manzon Allah s.a.w yace: Allah ya gafartawa wanda sukayi kwal kobo, sai wani yace: ya manzon Allah! Da wanda sukayi saisaye suma? Sai ya ambaci masu kwal kobo sau uku sannan ya fadi cikin na ukun da masu saisaye. Buhari ne ya rawaito shi.

11.    Manzon Allah s.a.w yana neman izinin iyalan sa:
Allah me girma yayi gaskiya dayake siffata shi da cewa: “ lallai kana kan halaye na kwarai masu girma ” suratul kalam (4).
Daga cikin girman halayen sa s.a.w be bar yin adalci ba a tsakanin matan sa hatta a lokacin rashin lafiyar sa be bar raba masu kwana ba sai bayan ya nemi izinin su suka amince masa suka yafe masa hakkokin su, Aisha Allah ya kara mata yarda tace: “ lallai manzon Allah s.a.w ya aika zuwa ga matan sa a lokacin rashin lafiyar sa suka zo suka taro sai yace:
“ bazan iya yawo ba a tsakanin ku idan kunga zaku iyamun izini na kasance a gun Aisha ina neman haka sai suka masa izini da hakan ” abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.

12.    Manzon Allah s.a.w yana son sanya farin ciki ga iyalan sa:
Lallai sanya farin ciki da murna ga zuciyar mutane abune wanda shari'a tayi umurni dashi kuma wannan umurnin yafi karfi a bangaren yan uwa wanda yafi kusa haka haka, Aisha uwar muminai Allah ya kara mata yarda tace alokacin danaga annashawa a fuskar manzon Allah s.a.w sai nace ya manzon Allah ka mun addu'a sai yace:
“ ya Allah ka gafartawa Aisha abunda ta aikata na zunubai da kuma wanda zata aikata da wanda tayi a bayyane da wanda tayi a asirce ” sai Aisha tayi dariya har dan kwalinta ya fadi saboda dariya sai manzon Allah s.a.w yace: “ wallahi addu'ar danake yima al'ummata kenan cikin dukkanin sallata ” ibn hibban ne da hakim suka rawaito shi, kuma albani ya inganta shi cikin littafin “ al sahiha ” (2254).

13.    Manzon Allah s.a.w yana koya ma iyalan sa ladabi:
Duk da irin wannan zaman takewa tashi na taushi da mu'amala me sauki wada yakeyi ma iyalan sa ya kasance kuma me hikima cikin mu'amalar sa da kuma ayyukan sa ta yadda zamanta kewa me kyau ta kasance me amfani wurin tsara zance idan kuma ya kasance cewa ladabtar tafi cancanta idan akwai wani kuskure bazai yiwu ba shawo kan hakan da tsawa da tsoratarwa da kuma hani, Aisha Allah ya kara mata yarda tace nace ma manzon Allah s.a.w:
“ ai kaza ya isheka daga safiyya- matar manzon Allah s.a.w- watan kaza da kaza- tana nufin! Ita gajeruwa ce- sai manzon Allah yace: “ hakika kin fadi wata kalma wacce da za'a cudanyata da ruwan rafi da sai ta batashi ” abu dawud ne da tirmizi suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi.

14.    Manzon Allah s.a.w yana kyautatawa wajen magance matsalar iyalan sa:
Salon san a magance matsala iyalan sa karkashin hukunce hukuncen musulunci ya sanya su suna muwafaka da yarda da ita, dan me yasa hakan ma zabai faru ba bayan yana masu magana ne ta hankali da fasaha wanda yake magance matsala, Anas dan malik Allah ya kara masa yarda yana cewa:
“ labari yazo kunnen safiyyat cewa Hafsat tace mata yarinyar bayahude, sai tayi kuka, sai manzon Allah s.a.w ya shigo ya sameta tana kuka, sai yace mata me yasa kike kuka?! ” sai tace: Hafsat ce tace mun ni yarin yan bayahudiya ce, sai manzon Allah s.a.w yace: “ lallai ke yarinyar annabi ce kuma baffanki annabi kuma kina auren annabi, to kuma dame zata maki alfari dashi?! Sa'annna yace: kiji tsoron Allah ya hafsa ” tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.

15.    Manzon Allah s.a.w yana karban uzirin iyalan sa:
Kuskure dole ne musamman ma ga wanda kake zama dashi kullum kuma karban uzri dalili ne na tsarkin zuciya da kyawun ta wanene yafi ka kyawun zuciya ya manzon Allah, ya kasance yana jiran Aisha sai ta bata mashi lokaci sai yace:
“ me ya rike ki ne? ” sai tace ya manzon Allah: na kasance inajin karatun wani mutum ne wanda bantaba jin murya me dadin nashi ba, sai manzon Allah s.a.w ya tashi yaje ya saurare shin a dan lokaci sai ya dawo yace: “ wannan salim ne maula abu huzaifa godiya ya tabbata ga Allah daya sanya irin wannan cikin al'ummata ” . Bazzar ne ya rawaito shi kuma haisimi ya kawo shi cikin littafin “ al mujamma'a ”, kuma bazzar yace: mutanen cikin hadisin mutanen cikin littafin sahihul buhari ne.

16.    Manzon Allah s.a.w yana sanya farin ciki ga iyalan sa:
Ya kasance yanason fadama iyalan sa abunda zai sanya su farin ciki da murna da saukar da natsuwa da kwanciyar hankali a cikin zukatan su, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa manzon Allah yace mata:
“ bazaki yarda ba ace kin zama matata a nan duniya da kuma lahira? Sai tace zan yarda, sai yace: to ke matatace anan duniya da lahira ” hakim ne ya rawaito shi cikin mustadrak kuma albani ya inganta shi.

17.    Manzon Allah s.aw ya ksance me tausasawa wurin mu’amala da iyalan sa:
Hakika mu'amalar manzon Allah s.a.w ya kasance tare da mutanen da suke rayuwa dashi cikin kololuwan kyawu da sauki da tausayi da kamala kamar yadda ubangiji ya siffatashi da hakan yace:
“ hakika kana kan halaye na kwarai masu girma ” suratul kalam (4).
Iyalan sa sun kasance masu rabo me waya cikin haka, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa akan mu'amalar manzon Allah s.a.w tare da ita: “ na kasance inasha ruwa cikin kwarya ina cikin al'ada sai mikama manzon Allah sai ya sanya bakin sa akan wurin dana sa baki na shima yasha ruwan kuma niacin kasha ina cikin al'ada sai na mikawa manzon Allah s.a.w yasa bakin sa a wurin dana sa baki na shima yace ” nisa'I ne ya rawaito shi kuma ingantacce ne hadisin.

18.    Manzon Allah s.a.w ya kasance yana da saukin hali ga ilayan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance mutum ne me saukin hali da saukin kai cikin dukkanin al'amuran sa yana amsan kuskure koda kuwa da gangan aka aikata kuma har yayi ma mutum uziri koda kowa daya daga cikin sahabban sa ne ko kuma makiyan sa ne, iyalan sa ma sun kasance suna da rabo acikin yafiyan sa me girma, ya kasance yana shiga gida wurin iyalan sa bayan hantsi sai yace: “ shin kuna da abincin rana? ” sai suce: a'a, sai yace: “ to ina azumi ” nasa'I ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.
Babu tsawatarwa kuma babu kunyatarwa sai raddi wanda yake kunshe da sauki da kuma kyauwun amsan uzirin su.
Karshen littafi:

Alaka tsakanin namiji da mace a musulunci alaka ce ta soyayya da kuma girmama wa da rahama da darajawa, soyayya ga mace a mastayin mata da tausayi a gareta kamar yarin ce da kuma girmamata da darajata kamar uwa, lallai mace a cikin musulunci duk lokacin da shekarunta yaja haka darajata zai kara da kuma girmamata, a cikin musulunci babu matsala a tsakanin namiji d mace ko wanne daga cikin su an halice sa ne domin dayan domin samun kamalar sa ko wanne daga cikin su yana da siffar sa wanda ya banbanta dashi akwai siffofi na tawaya ga namiji wanda mace take cike masa shi kuma akwai siffofi na tawaya ga mace wanda namiji ke cike mata shi saboda haka ne musulunci ya wajabta wa mace wasu wajibai na shari'a da zamantake wa wanda zai dace da ita da kuma yanayin ta na jiki ne ko kuma na zuciya kuma Kaman haka ne shima na miji an wajabta masa irin haka, sannan kuma ya sanyawa namiji hakkoki nashi da kuma wanda suka wajaba akan sa wanda zai dace da dabi'ar sa haka itama mace take nata hakkoki wanda zai dace da dabi'ar ta a karkashen wannan kwatantawan da musulunci ya wajabta a tsakanin su ake samun natsuwa da kwanciyar hankali da so da kauna a tsakanin su, Allah madaukaki yana cewa:
“ Allah shine wanda yasanya maku mata daga gare ku ya kuma sanya maku yara daga matayen ku da jikoki ya kuma azurta ku da abunci da sha masu dadi, shin da gumaka da wasu abun bauta suke yin imani su kuma kafurta da ni'imomin Allah ” suratun nahali ayata 72.
Musulunci lokacin da yake halatta wasu abubuwa ga namiji ya kuma haramtawa mace daga cikin su ko kuma ya halattama mace wasu abubuwan ya haramtawa namiji daga cikin su hakan zai dace a karkashin yanayi na halitta na jikin su ko kuma hzuciyar su, saboda zalumci ne a daura ma mutum namiji ne ko kuma macece abunda bazai iya ba, misali motan da take dauko mai na gas bazata iya dauko man fetur ba dukda kasancewar fetur yafi man gas saurin konewa ko kuma akasin haka.
Wannan su ne halayen mu tare da matan mu wanda muka koyo su daga abin koyin mu Muhammad s.a.w wanda ya sanya mana cikin ko wani mu'amala me kyau tare da mutum da kuma iyalan mu a kebance akwai lada da sakamako akan sa ya kuma sanya mana dukkanin wani mu'amala mummuna tare da mutane ko kuma da iyalai akwai zunubi da sabo akai.
Wannan shine halayen muslunci wanda yake a aikace a fili bawai rubuce ba cikin littafi da misalai kamar yadda zaka rubuta labarai na soyayya da wanda aka kirkiro wanda bazai taba yiwuwa ba kaga wanda ya rubuta ya aikata.
Ka fadamun gaskiya tsakanin ka da ubangijin ka shin ka taba haduwa da irin wannan mu'amar me kyawu wanda manzon Allah s.a.w yake mu'amalantar iyalan sa dashi, idan kayi koyi dashi ya isa magance dukkanin matsala na ma'aurata wnada yake samuwa dalilin rashin sanin hakkin kowa tsakanin ma'aurata wanda aka gina shi akarkashin manhajin musulunci ya kuma sanya gazawa da sakaci wurin aikatashi sabo ne wanda ya cancanci ukuba ga wanda ya aikata shi, sannan kuma aiki dashi da aikatashi biyayya ne ga umurnin Allah wanda yake jawo rahama da gafara , abunda yake faruwa cikin wannan duniya da abunda ke faruwa tsakanin wasu musulmai na matsaloli tare da iyalan su ya samo asali ne saboda rashin bin wannan manzon me daraja da kuma masa biyayya cikin karantarwan sa, wannan shine halayen mu na musulunci halaye cikakku da mu'amala me kyawu tare da duk wanda yake kewaye dakai kamar mutum.