DUKKAN BIDI’A A CIKIN ADDINI BATA CE

DUKKAN BIDI’A A CIKIN ADDINI BATA CE​

DUKKAN BIDI’A A CIKIN ADDINI BATA CE

كل بدعة في الدين ضلالة بلغة الهوسا

 

Mawallafi

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha

د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة

 

Fassara

European Islamic Research Center (EIRC)

المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية

& Muhammad Khamis

Wanda ya bibiyi fassara

Hashim Muhammad Sani

www.islamland.com

 

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Gabatarwa:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakon sa kuma muna neman shiriyar sa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da kuma munanan ayyukan mu.

Duk wanda Allah ya shiryar da shi to babu mai iya batar da shi. hakanan kuma duk wanda Allah ya batar da shi to babu mai iya shiryar da shi, kuma ina shaidawa lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shida abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai annabi Muhâmmadu bawansa ne kuma manzonsa ne, Allah yayi dadin tsira a gare shi da mutanen gidan sa da sahabban sa, kuma yayi aminci mai yawa har zuwa ranar sakamako, Bayan haka:

Lallai al'amuran addini ya wajaba a karbe su (da kuma mika wuya a gare su) da kuma rashin bijire musu, dan yin aiki da fadar Allah madaukaki: " duk abinda Manzo yazo muku da shi to ku rike shi kuma duk abinda ya hane ku da shi to ku hanu kuma kuji tsoron Allah lallai Allah mai tsananin uquba ne".[1]

Kamar yadda yadda koyi da Annabi ke wajaba a cikin su da kuma rashin ijtihadi a cikin abinda bai karbar ijtihadi a cikin sa, dan yin aiki da fadar Allah madaukaki: " kace musu in kun kasance kuna san Allah to ku bini sai Allah ya so ku kuma ya gafarta muku zunuban ku kuma Allah me gafara ne me jin kai (31)"[2].

Kamar yadda ya wajaba kada a shigar da wani abu wand aba addini ba a cikin sa da kuma jingina shi a gare shi domin yin hakan abu ne da zai janyo baraka kuma ya bude hanyoyi daban daban masu nesantarwa daga hanyar Allah ingantacciya kuma a qarshe yin hakan zai mutum ga azabar Allah da kuma uqubar sa. Annabi (SAW) yana cewa: " duk wanda ya qirqiro wani abu a cikin alamarin mu wannan (addinin mu) wanda babu shi a cikin sa to an mayar masa (baza a karba ba)".[3] Bukhari da muslim ne suka ruwaito shi.

Dayawa daga cikin masu iqrarin musulinci suna aikata wasu ayuyyuka na daban wadan da suka shafi al-amuran ibadu wadan da suka saba wa karantarwa musulinci ko kuma su dinga aikata wasu ayyuka wadanda suka qirqira wadan da basu da asali a addini kai suna bin san rayukan su ne da kuma abin da zukatan su ke raya musu, suna aikata hakan suna abin zargi saboda fadar Allah madaukaki: " shin ko kaga wanda ya riqi san ran sa ya zamo masa abun bauta shin ko kai zaka iya zama wakili a gare shi (43)" [4].

Kuma wannan sabawa da kuma bidioyin a cikin addini da ace cutarwar su na taqaituwa ne akan mutumin da ya yi da da sauqi. Duk da cewa- ba muna goyon bayan su bane akan hakan- sai dai wadannan bidioin suna da tasiri a kan sauran musulmai wadan da zasu tasirantu da su ko kuma su dinga ganin kyawan su. kuma wadannan fararrunn abubuwa masu rusa addi ni a tsawon lokaci. Kamar yadda suke da mummunan tasiri ga wadan da ba musulmi ba a duk lokacin da suka wasu ayyuka na wasu musulman wadan da lafiyayyun hankula basu daukar su. Kuma suna kore tauhidi da ingantacciyar hanyar da Allah ya dora mutun a kai, sai hakan yasa su dinga gujewa musulinci kuma su dinga daukar shi tamkar sauran addinai wadan da aka gina su akan qarerayi da kuma rashin hankali.

Masu yin wadannan ayyuka da bidioi kasha uku ne:

· kashi na farko: ko dai aikin su ya zamo dan jahiltar su ne ga alamuran addini, musulinci bai yafe mai hakan ba, domin maganin jahilci shi ne tambaya, ba aiki da san rai ba, Allah madaukaki yace: " ku tambayi masu ilimi in ku baku sani ba. (7)"[5]

Ko kuma ya zamo makauniyar kwaikwayo ne ga wadanda suka gabace su, to irin wadannan aikin su abin zargi ne, Allah madaukaki na fadi game da irin wadannan: " kuma idan kace musu ku bi abin da Allah ya saukar sai suce zamu bi abin da muka sami iyayen mu ne akai, shin koda shaidan yana kiran su ne zuwa ga azaba mai tsanani (21)"[6] to wadannan jamaar suna kan bata saboda saba abinda Allah ya shar0anta, kuma yawan bautar su bazai amfane su ba, domin ibadar da mutum zaiyi koyi da Annabi (SAW) a cikin ta koda kadan ce tafi alkhairi da wanzuwa fiye da ibada mai yawa wacce ba'ayi koyi da Annabi ba acikin ta.

· kasha na biyu: masu kwadayin abin duniya, da kuma tara abin duniya wadan da suke amfani da jahilcin mutane game da al'amuran addinin su, sais u dinga amfani da wannan damar wurin tara mabiya dan su samu wani wuri na shugabantar al0umma da kuma tastar dukiya, to irin wadannan mutanen sunyi nesa daga addini, daga cikin su akwai masu amfani da sunan addini ammam addini yayi nesa da su, irin wadannan mutanen sun saw a musulinci tufafin da ba nashi ba sai suka bata kyawon sa saboda bidi'o'in su da kuma fararrun al0amuran su.

· kasha na uku: maqiya musulinci da kuma masu qoqarin yada bidi'a acikin addini dan rarrabe kan al'ummar musulinci, kuma suna kasha dukiya mai yawa ga dukkan mai bidi0a acin addini dan ya yada bidi'ar sa, dan samar da kungiyoyi masu sabawa tsarin Allah, masu barin ingantacciyar aqidar su, dan a qarshe wadannan qungiyoyin su dinga sabani tsakanin su, saboda sabanin mashayar su, sai abin da maqiya addini suke so ya auku na juyar da musulmai daga addinin su da kuma ingantacciyar aqidar su, ta hanya mai sauqi da kuma qaracin asara.

Bidi'a a cikin addini yana daga cikin aikin shaidan a waswasin sa da kuma dabar barun sa wadan da yake amfani da su dan batar da mutane, ya kuma sa subar addinin su baki dayan sa.

Abdullahi dan Abbas yana cewa game da fadar Allah madaukaki: " kuma suka ce kada kubar ababen bautar ku kuma kada kubar wudda da suwa'a da yagusa da ya'uqa da nasra (23)"[7], yace: wadannan sunayen bayin Allah ne salihai na mutanen annabi nuhu, yayin da suka mutu sai shaidan yay a raya wa mutanen su cewa ku kafa gumakan su a inda suke zama kuma kusa musu sunayen su, sai suka aikata, ammam basu bauta musu ba har sai bayan da suka mutu dukkan su kuma aka manta ilimi sai aka bauta musu.[8]

Ibnul qayyim Allah yayi masa rahama yana cewa a lokacin da yake Magana akan matakan da shaidan yake bi dan batar da mutum[9]: lallai shaidan yana so ya farauci dan adam ta tarkoi guda bakwai masu wahala tsallakewa baya barin wani tarko har sai ya kasa farautar mutum da shi, wadannan tarkuna su ne kamar haka:

  1. Tarkon kafirce wa Allah, da addinin sa da siffofin sa da kuma abin da annabin sa yafada game da shi, to idan ya iyan kama mutum da wannan tarkon sai wutar gaba ta mutu shi kuma shaidan sai ya huta, in kuma mutum ya tsira daga wannan tarkon sai ya kafa masa tarko nag aba.

 

  1. Tarkon bidi’a, kodai qudirce sabanin gaskiyan da Allah ya aiko manzon sa da ita, kuma ya saukar da littafin sa da ita, ko kuma yin bauta ba da abin da Allah ya saukar ba (qirqirarrun al’amura) a cikin addini wanda Allah bazi karba ba, shaidan ya kama mutum ta tarkon bidi’a yafi soyuwa a gareshi, saboda bidi’a na warware addini kuma tana kore abinda Allah ya aiko manzon sa da shi, kuma ma’abocin ta galibi baya tuba kuma baya barin ta, sai dai ma zai dinga kiran mutane zuwa gare ta, kuma hakanan ta qunshi qirqira wa Allah qarya ba tare da ilimi ba, bidi’a na qiyya ne ga sunnah, bidi’a takan dauki mutum daga karama zuwa babba, har zuwa ta fitar da mai yin ta daga addini. Barnan bidi’a babu mai gane wa sai ma’abota sani, dan idan ta zo ta wani salo sai yayi amfani da hasken sunnah wurin kore ta, kuma sai ya nemi kariya daga gare ta ta hanyar koyi da Annabi da magabata, sahabbai da tabi’ai da wadan da suka bisu da kyautatawa. Sai tarko nag aba.

 

  1. Tarkon manya manyan zunubai, idan shaidan ya kama mutum a ciki sai ya qawata masa yin su, wata qilq ma ya dinga sashi yana cewa: " zunubi bai cutarwa indai akwai tauhidi, kamar yadda kyakkyawan aiki bai amfani tare da shirka", in kuma ya tsira daga wannan tarkon sai ya kafa masa nagaba.

 

  1. Tarkon qananan zunubai, shaidan bazai gushe ba yana qanqanta masa yin su, yana raya masa cewa ai ana gafarta su in dai ka guji manya manyan zunubai, da kuma yin kyawawan ayyuka? Shaidan bazai gushe ba har sai ya sa mutum ya auka a cikin wannan tarkon sai ya fara aikata qananan laifuffuka har ya fada zuwa ga manyan laifuka, sai ya zama mai jin tsoron Allah ya fi shi, domin dogewa akan zunubi yafi zunubin muni, domin babban laifi bai wanzuwa matuqar ana tuba kuma ana istigfari, kuma hakanan qaramin zunubi kan zama babba matuqar an doge a kan sa. Annabi (SAW) yana cewa: " kashedin ku da wulaqntattun zunubai, domin su kamar mutanen da suka sauka a daji ne, sai kowa a kawo ice guda daya har suka dafa wainar su, lallai qanan zunubai a duk lokacin da mai yin su ya doge akan su to zasu halaka shi"[10].

In kuma mutum ya tsira daga wannan tarkon ta hanyar kula da kuma kiyayewa, da kuma tuba da istigfari, sai shaidan ya kafa masa tarko nag aba.

 

  1. Tarkon halal, su ne ababen da babu laifi akan mai yin su, sai ya shagaltar da shi wurin aikata su kuma ya hana shi yin kyawawan ayyuka masu yawa da kuma guziri dan lahira, sai ya gangara da shi har ya bar sunnoni, daga nan kuma zuwa barin wajibai. In kuma mutum ya tsira ta hanyar sanin girman ibada da kuma yawaita aikin ibada, sai shaidan ya kafa masa tarko nagaba.

 

  1. Tarkon ayyukan da basu da lada da yawa, sai shaidan yazo ya umurci mutum yayi ta aikata su kuma ya qawata masa su, kuma ya nuna masa cewa suna da lada mai yawa, dan ya shagaltar da shi daga abin da yafi lada kuma yafi falala, domin duk lokacin da shaidan ya kasa sawa mutum yayi asarar asalin lada, sai yayi kwadayin hana shi samun cikakken lada, sai ya shagaltar da shi da daga ayyukan da suka fi lada, da kuma abin da Allah yafi so.

 

Daga cikin mafi girman abin da zai shiga wannan babin shi ne qirqira wa Annabi (SAW) qarya da jingina masa abin da bai fadi ba, haqiqa alqawarin azaba mai tsanani yazo ga dukkan mai aikata haka, Annabi (SAW) yace: [11]

Sahabi mai daraja Abdullahi bun mas’ud Allah ya qaramasa yana cewa: (kuyi koyi kada kuyi qirqire domin ku an wadatar da ku) dabarany ne ya fitar da shi.

 

 

Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha

[email protected]

 

 

 

SHIN ADDININ MUSULINCI CIKAKKE NE?

Yana daga cikin abinda kowa ya sani cewa lallai musulinci ya cika, saboda fadar Allah madaukaki: " a yau nacika muku addinin ku kuma na cika ni’ima ta a gare ku kuma na yarje muku musulinci a matsayin addinin ku"[12]

kuma musulinci ya tattaro dukkan abinda ke da alaqa da mutum a duniyar sa da lahirar sa, Allah madaukaki yace: " kuma mun saukar maka da littafi (Alqur’ani) bayani ne ga dukkan komai"[13]

 Duk abinda ba’ayi bayaninsa ba a cikin alqur’ani, da hadisai to wannan abun ba addini bane, domin alqur’ani shine madogara ta farko a addini, sai madogara ta biyu it ace sunnar annabi, ko dai abinda ya fada ko kuma ya aikata ko kuma abinda ya tabbatar (abinda akayi a gabansa bai hana ba), wadda aka kawo mana ita ta hanya ingantacciya, Allah madaukaki yana cewa: " kuma Allah ya saukar maka da alqur’ni da hikima (sunnaah) kuma ya sanar da kai abinda baka sani ba, kuma falalar Allah ta kasance a kanka mai girma ce (113)"[14].

kuma yana daga cikin abinda wajibi ne mutum ya sansu a cikin addini cewa lalle annabi (SAW) ya isar da sako kuma ya sauke amana kuma yayi wa al’umma nasiha, Allah madaukaki yace: " kuma mun saukar maka da alqur’ani dan kayi wa mutane bayanin abinda aka saukar musu wataqila zasuyi tunani (44)"[15],

kuma lallai babu wani alheri face sai da annabi ya nuna wa al’umma shi, kuma babu wani sharri face sai da ya tsoratar da al’ummar sa daga gare shi, Annabi (SAW) yace: " lallai babu wani annabin da yazo kafin ni face haqqi ne akan say a nuna wa mutanen sa abinda ya sani na alheri a gare su, kuma ya tsoratar da su daga sharrin abin da ya sani (abin da zai iya zama sharri ne a gare su) …."[16]

Kuma duk wanda yaqudurce sabanin haka to haqiqa ya kafirta, kamar yadda alqur’ani ya ambata.

Lallai mai yin bidi’a a cikin addini yana kudurce cewa lallai addini Allah bai cika ba, aikin sa yana nuna cewa yanayin bidi’ar ne dan ya cika abin da ya tawaya a cikin addini.

Hakanan kuma yana tuhumar Annabi (SAW) da yin zamba da kuma rashin isar da saqo kamar yadda aka dora masa, kamar yana nuna cewa musulinci yana buqatar wannan bidi’ar ta shi dan ya zamo cikakke, alhali Annabi (SAW) yana cewa: " na barku akan hanya mai haske, daren ta tamkar ranar ta yake babu mai sauka daga kanta sai dai halakakke"[17]

 

 

 

HUKUNCIN KARA WANI ABU A CIKIN ADDINI WANDA ALLAH DA MANZON SA BASU SHAR’ANTA BA

Allah madaukaki yace: " to duk wanda ya mika wuya ga Allah alhalin yana kuma me kyautatawa to ladar sa na wurin ubangijin sa kuma babu tsoro a gare su kuma baza suyi baqin ciki ba (112)"[18],

wato ma’ana: duk wanda ya tsarkake ayyukan sag a Allah, kuma ya fuskanci Allah da zuciyar sa haka nan kuma yana kyautata ibadar ubangijin sa (ya bauta wa Allah da abin da ya shar’anta)[19], to wannan yana cikin iyan al’janna.[20]

Imam Ahmad ya ruwaito daga Abdullahi dan masa’udu Allah ya qara masa yadda yace: wata rana Annabi (SAW) ya zana mana wani layi, sai yace: " wannan it ace hanyar Allah, sannan sai yayi wasu zane a hagu da dama, sai yace:wadannan kuma su ne barayin hanyoyi, akan kowace barauniyar hanya akwai shaidanin da ke kira zuwa gare ta" sai Annabi ya karanta fadin Allah: " kuma lallai wannan ita ce hanya ta mikakkiya to ku bi ta, kuma kada ku bi barayin hanyoyi sai su raba ku da bin hanya ta, wannan shi ne abin da yake muku wasici da shi dan kuji tsoron sa (153)"[21].

Kuma Annabi (SAW) yana cewa: " lallai mafi gaskiyan zance shi ne littafin Allah, kuma mafi kyawuun shiriya it ace shiriyar Annabi Mhammadu (SAW), kuma mafi sharrin al’amura suna qirqirarrun su, kiuma ko wane qirqirarren abu bidi’a ne, kuma ko wacce bidi’a bat ace, kuma ko wacce bidi’a tana wuta"[22]

Daga wadannan a’yoyin da kuma hadisai zamu ga ne girman laifin qirqirq wa Allah da Manzon sa qarya, sannan kuma da girman qirqiro wani abu a addini na Magana ko aiki ko qudircewa wanda Allah da Manzon sa basu yi izini da shi ba, Allah madukaki yana cewa: " kace musu lallai ubangiji nay a haramta al fahsha a bayyane da boye, kuma ya haramta zunubi da zalinci ba tare da wani haqqi ba, kuma ya haramta ayi taraiya da shi da wani abu wanda bai saukar da hujja akan sa ba, kuma ya haramta ku dinga kirkiran karya kuna jingina masa abin da baku sani ba (33)"[23]

 kuma Allah madukaki yana ewa: " kada ka fadi abin da ba kada ililmi akan sa, domin lallai ji da gani da kuma zuciya (abin da ke zuciya) dukkan su abin tambaya ne (36)"[24]

 kuma Allah yana cewa: " sun ko suna da wasu abokan tarayya ne wadanda suka shar’anta musu wani addini wanda Allah baiyi umurni da shi ba?"[25].

Duk wanda ya qirqiri wata bidi’a a cikin addini ya kawo wani abun da Allah ko manzan sa basu shar’anta ba, ta fuskan halatta abunda Allah ya haramta ko kuma haramta abun da ya halatta to ya kafirta- in har bai tuba ba-, haka nassin hadisin Annabi (SAW) ya fada, annabi yace a karkashin fadan Allah madaukaki a cikin suratul bara’a: " sun riki malaman su da masu bautar ababan bauta koma bayan Allah"[26] sai Annabi yace: " a'a ba wai bautar su suke yi ba (yi musu ruku’i da sujjada) bane, sun kasance in sun hallata musu wani abu sai mabiyan suma su halatta shi, in kuma suka haramta musu wani abu sai su ma mabiyan su haramta shi"[27].

Alkawarin azaba kan shafan wanda ya biye musu cikin hallata abin da Allah ya haramta ko kuma haramta abin da ya halatta. ash sheikh Abdurrahman ibn as sa’ady yana cewa a qarqashin tafsirin wannan a’yar: ...suna shar’anta musu wasu ababe wadan da suka saba wa addinin manzanni, su kuma mabiyan sai su bi su akan haka, kuma su mabiyan sun kasance suna qetare iyaka wurin bin malaman su da masu bautar su (saliyan cikin su), kuma suna girmama su kai har suna bautawa qaburburan su koma bayan Allah, suna zuwa wurin qaburburan suna yanka kuma suna addu’a da kuma neman a’gaji,[28]

 

 

 

MEYE BIDI’A?

Dan musan ma’anar bidi’a, ya wajaba mu fara sanin meye sunnah?

Sunnah itace:

(dukkan abin da Manzan Allah (SAW) yake kai shi da sahaban san a aqida ko aiki), al hafiz ibn rajab Allah ya qara masa yadda yana cewa: sunnah itace hanyar da ake bi, wannan ya hada da riqo da abinda Annabi (SAW) yake kai da sahabban sa, na aqida da ayyuka da zantuttuka, wannan it ace sunnah cikakka.[29].

Riko da sunnah wurin zance da aiki da qudiri wajibi ne, saboda fadar Allah madaukaki: " hakika ababan koye masu kyau sun kasance a gare daga Manzan Allah (SAW) ga wanda yake qaunar Allah da rana ta qarshe kuma ya ambaci Allah da yawa (21)"[30]

 kuma hakan da umarnin Manzan Allah (SAW) ga al’ummar sa da suyi riqo tsarin sa kuma suyi koyi da shi, Annabi (SAW) yana cewa: " ina yi muku wasiyya da jin tsoron Allah da ji da kuma biyayya koda an dora muku bawa ne a matsayin shugaban ku, lallai duk wanda ya rayu daga cikin ku to zai ga sabani mai yawa, to kuyi riqo da sunnah ta da kuma sunnar halifofi na shiryayyu kuma masu shiryarwa, kuyi riqo da ita da qarfi, kuma ina kashedin ku da qirqirarrun al’amura, domin kowanne qirqirarren abu a addini bidi’a ne, kuma kowace bidi’a bata ce"[31]

Shehul islam ibn taimiyya yana cewa: …Annabi Muhâmmadu (SAW) an aiko shi zuwa ga dukkan mutane da aljanu, dan suyi koyi da shi a cikin dukkan abinda ya shafi addinin su nabayyane da boye,, a cikin aqidar su da shari’ar su, babu wata aqida ingantacciya sai ta sa kuma babu wata shari’a sai ta sa, kuma babu wani da zai isa zuwa ga Allah sa ta hanyar koyi da shi a baiyane da boye, a cikin zantuttuka da kuma aiyuka na baiyane da boye, kuma Allah baida wani masoyi sai wanda ya bi sa a baiyane da kuma boye, ya gasgata shi a cikin labaran da ya bada na gaibi, kuma ya lazimci yi masa biyayya a cikin abin da ya daura akan bayi na yin wajibai da kuma nisa daga haram…….kuma duk wanda ya qudirce cewa daya daga cikin wadannan da basa yin wajibai kuma basa barin haramun yana daga cikin masoya Allah masu jin tsoran sa kuma masu rabauta a duniya da lahira, duk da cewa basa yin wajibai kuma basa barin haram to wanda ya qudirce hakan ya qaryata Allah, kuma duk wanda ya qaryata Allah shi kafiri ne, ya fita daga musulinci, kuma bai shaida cewa Annabi Muhâmmadu (SAW) manzan Allah ba ne, irin wannan ya qaryata Annabi Muhâmmadu ne (SAW), domin Annabi ya bada labara cewa masoya Allah su ne muminai masu jin tsoron sa, Allah madaukaki y ace: " ku saurara lallai masoya Allah babu tsoro a tare da su kuma baza suyi baqin ciki ba (62) su ne masu imani kuma m su taqawa (masu jin tsoron Allah) (63)[32].

Kuma Allah madaukaki yana cewa: "yaku mutane lallai mun halicce ku daga namiji da macce kuma muka sanya ku jama’a da qabiloli daban-daban dan kusan juna, lallai mafi karamcin ku a wurin Allah shi ne mafi jin tsoron Allah a cikin ku, lallai Allah masani ne kuma mai bada labara ne (13)"[33].

Jin tsoran Aallah (taqwa), shi ne mutum yayi wa Allah biyayya ta hanyar da Annabi ya koyar, yana mai qaunar rahamar Allah, haka nan kuma ya bar sabon Allah kamar yadda Annabi ya koyar saboda tsoran azabar Allah, masoyin Allah baya kusantar Allah sa ta hanyar yin farillai da kuma nafiloli, Allah madaukaki y ace a cikin hadisin qudisi: “bawa bait aba kusantata da wani abu ba irin abin da na farlan ta akan sa, kuma bawa bazai gushe ba yana kusanta ta da nafiloli har sai na so shi”.. kamar yadda hadisi ingantacce ya tabbatar wanda buhari ya ruwaito.[34]

 

Amma ita kuma ma’anar bidi’a (game garin ma’ana):

Samar da wani abu wanda babu shi, Allah madaukaki yace: "Allah shi ne maqagin halittan sammai da kasa"[35]. Al sheikh Abdurrahman ibn sa’ady Allah yayi masa rahama yana cewa a qarqashin wannan a’yar: ai ma’ana Allah shi ne wanda yay a qagi halittan sammaim da qassai kuma ya kyautata halittan sub a tare da ya kwaikwaya ne a wurin wani ba.[36]

Kuma Allah madaukaki yana cewa: " kace musu ba ni ba ne na farko a ciki manzanni ba"[37]. Al sheikh Abdurrahman as sa’ady Allah yayi masa rahama yana cewa: ai wato ban i ne farkon mazon da yazo muku da gaskiya ba balle ku dinga mamakin saqon da nazo da shi ba, haqiqa annabawa da manzannni sun zo kafin ni kuma kun gasgata su, to saboda me kuke qin saqo na (manzanci).[38]

 

Da wannan game garin fahimtar ne zamu gano bidi’a ta kasu kasha biyu:

1 – bidi’a a addini: ita ce dukkan abin da aka kirkira a addini, sabanin abin da Manzan Allah (SAW) yaka kaida sahabban sa, na aqida da aiki, wannan it ace haramtacciyar bidi’a da nassin alqur’ani mai girma, Allah madukaki yace: " duk wanda ya saba manzobayan shiriya ta bayyana a gare shi kuma yabi wata hanya wacce ba ta muminai ba, to zamu jibinta masa abinda ya janyo kuma zamu wurga cikin wutar jahannama, kuma makoma tayi muni (115)"[39]

Kuma Annabi (SAW) yana cewa: " dukkan al’umma ta zasu shiga aljanna sai fa wanda yaqi, sai aka ce ya manzan Allah: waye zai ki? Sai yace: " duk wanda yayi min biyayya to zai shiga aljanna, kuma duk wanda ya saba mini to haqiqa ya qi"[40]

Shehul islam ibn taimiyya Allah yayi masa rahama yana cewa: saboda haka ne Allah ya umarce mu mudinga cewa a cikin ko wace sallah: " ya Allah ka shiryar da mu hanya madaidai ciya (6) hanyar wadanda kayi ni’ima a gare su, ba wadan da kayi fushi da su ba kuma ba batattu ba (7)" (wadan da Allah yayi fushi da su su ne wadanda sun san gaskiya amma suke takewa, su kuma batattu su ne masu bauta wa Allah da jahilci duk da sun san hakan ya saba wa qur’ani da sunnah.[41].

Bidi’a a addini ta kasu kasha uku:

  • Bidi’a mai fitar da mutum daga musulinci, kamar wacce ta shafi aqeedah, misali, wanda ke yanka ga wanin Allah, da kuma mai kewaye qabari, da kuma wanda ke roqon wanin Allah a cikin abin da babu wanda zai iya yi sai Allah, da makamantan su, Allah maaukaki yace: " kace musu lallai sallah ta da yanka na da rayuwa ta da mutuwa na duka ga Allah suke ubangijin talikai (6) ba shi da abokin tarayya, kuma da haka aka umarce ni, kuma ni ne farkon ma su mika wuya (162)"[42].
  • Bidi’ar da bata fitarwa daga musulin ci, amma hanya ce wacce zata kai mutum zuwa ga fita daga musulincim, kamr misalign gina masallaci akan qaburbura, da yi musu ado, da yin addu’a a wurin, saboda gudun haka ne Annabi (SAW) ya hana al ummar sa su riqi qabarin sa wurin idi (wurin da zasu yawaita zuwa), saboda tsoran kar su bauta masa koma bayan Allah, Annabi (SAW) yana cewa: " kada ku sanya gidajen ku kamar maqabarta, kuma kada ku sanya qabari na kamar wurin idi, ku dinga yi mini salati, domin lallai salatin kun a riska na a duk inda kuke"[43]
  • Bidi’a mai daukar hukuncin sabi, kamar misalign qinyin aure, da kuma misalign yin azumin nafila kullun kullun ba hutawa, da kuma yin tsayuwar dare ba hutawa (kullun kullun), saboda hadisin Anas dan malik Allah ya qara masa yadda yace: wasu mutum uku sun zo gidan Annabi (SAW) suna tambaya game da ibadar sa, yayin da aka basu labarin ibadar Annabi, kamar sun raina, sai suka ce: ina zamu hada kanmu da manzan Allah, shi Allah ya gafarta masa abinda yayi da wanda baiyi ba, sai dayansu yace: ni zanta kiyamullaili ba hutawa har abada, shi kuma ayan yace: ni kuma zanta azumi har abada ba hutawa, shi kuma na qarshen su sai yace: ni kuma zan nisanci mata bazan yi aure ba, sai Annabi yazo wurin su sai yace musu: " ku ne kuka fadi kaza da kaza da kaza? Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fi ku taqawa, amma ni ina sallar dare kuma ina bacci, ina azumi kuma ina hutawa, kuma ina auren mata, duk wanda ya kyamaci sunnah ta to baya tare da ni"[44].

 

            Daga haka ne zai baiyana ceawa duk wanda ya bauta wa Allah da wani abu wanda bai shar’anta ba, kuma Annabi bai zo da shi ba, kuma halifan Annabi shiryayyu basuyi aiki da shi ba, to wannan abun bidi’a ne, saboda fadar Annabi (SAW): " ina muku wasiyya da jin tsoran Allah da ji da biyayya kuda an shugabantar muku da bawa ne mai yankakken gabbai, domin lallai dukm wanda ya rayu a baya na to zai ga sabani mai yawa, to ku riqe sunnah ta da sunnar halifofi na shiryayyu, kuyi riqo da ita kuma ku kama ta gam-gam, kuma kashedin ku da qiriqirarrun al’amura, domin dukkan qirqirarrun abubuwa a addini bidi’a ne, kuma kowace bidi’a bat ace"[45]

 

2 – bidi’a a cikin al’amuran duniya: sune dukkan abin da aka qirqiro na rayuwar duniyawanda basu da alaqa da shari’a, kamar kere-kere da abin da makamantan hakan, wannan halas ne, kuma ba’a kiran su bidi’a a addini, dudd da cewa a harshen larabci ana kiransu bidi’a, ba irin wannan bidi’ar bace Annabi (SAW) ya tsoratar game da ita, domin asali a cikin al’ada da kuma al’amuran duniya shi ne halacci matuqar babu dalili akan haramci, haka nan ma mu’aamala,

 

 

 

MATSAYAR SHARI’AH GAME DA QIRQIRARRUN AL’AMURA A ADDINI

Idan musan shaidawa lallai Annabi Muhâmmadu manzan Allah ne na nufin: yi masa biyayya cikin abinda yayi umarni, da gasgata shi a cikin abina ya bada labara, da kuma nisantar abinda ya hana kuma ya tsawatar, kuma ba; a bauta wa Allah sa da abin da ya shar’anta, wajibcin kore dukkan qirqirqrren abu a addini zai bayyana a garemu, Allah madaukaki yace: [46].

 Kuma Annabi (SAW) yana cewa: .[47]

Huzaifa dan yaman Allah ya qara masa yadda yana cewa:[48]

 

An samo hadisi daga Abdullahi dan masa’udu Allah ya kara masa yadda yace: manzan Allah (SAW) yace: [49]

 

Kuma an samo hadisi daga anas dan malik Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah (SAW) yace: [50].

 

Haqiqa Annabi (SAW) ya baiyana cewa akwai fitintinu a bayan sa, ammam mafita daga garesu shi ne riqo da littafin Allah da sunnar manzan Allah (SAW), amma ba wai qirqire da qage ba a cikin addini, an samo hadisi daga Abu huraira Allah ya kara masa yadda yace: manzan Allah (SAW) yace: ". Bukhari da muslim ne suka ruwaito shi.

 

 

WASU BAYANAI NA MALAMAI DA MASANA TAFSIRI GAME DA ZARGIN BIDI’A:

 

  • Umar dan khaddabi Allah ya kara masa yarda yace: " kashedin ku da masu bin san rai a addini, domin su makiya sunnah ne, sun kasa haddan hadisai sai suka koma bin san rai, sai suka bace kuma suka batar".[51]

 

  • Abullahi dan Abbas Allah ya kara masa yarda yace: a qarqashin tafsirin fadar Allah madaukaki: " a ranar da wasu fuskoki zasu yi fari wasu fuskokin kuma zasu yi baki", sai yace: wadanda fuskokin su zasu yi fari (haske) su ne ahlussunnah da ma’abota ilimi, amma wadan da fuskokin su zasu yi baki (duhu) su ne iyan bidi’a da batattu”.[52]

 

  • Umar dan Abdul azeez Allah yayi masa rahama yace: Annabi (SAW) ya sunnanta sunnoni, riqo da su gaskata littafin Allah ne, kuma yin biyayya ne ga Allah, kuma ruqo da su karfi ne a addinin Allah, bai hallata ba wani ya canza su ko kuma sauya su, duk wanda ya nemi shiriya a cikin su to zai shiryu, kuma duk wanda ya nemi taimakon allah da su to zai samu taimako, duk kuma wanda ya saba musu ya bi wata hanya wacce ba ta muminai ba, sai Allah ya jibinta masa abin da ya janyo, kuma ya wurga shi cikin wutar jahannama, kuma makoma ta yi muni.[53]

 

  • Fudailu dan iyaad Allah yayi masa rahama y ace: idan ka hadu da dan bidi’a akan hanya to ka canza wata hanyar, kuma Allah baya daga aikin dan bidi’a zuwa sama, duk kuma wanda ya taimaki dan bidi’a to kamar yana taimako ne a rusa addinin musulinci.[54]

 

  • Sufan as saury Allah yayi masa rahama y ace: bidi’a ta fi soyuwa a wurin shaidan fiye da sabo, domin sabi akan iya tuba a bar yin sa, ita kuma bidi’a ba’a tuba daga gare ta, (ba’a barin ta)[55].

 

  • Ibnul qayyim Allah yayi masa rahama yan cewa: idan zukata suka shagaltu da bidi’a sai su bijire wa sunnah[56]

 

 

 

WASU SHUBUHOHI DA RADDI A KANSU GAME DA BIDI’A

Wasu wadan da basu san addini ba yadda ya kamata suna kafa hujja da wasu hadisai dan kare bidi’o’in su a addini, sukan kafa hujja da fadar Annabi (SAW): [57]

Amsa akan haka itace: lallai wanda yace: " duk wanda ya sunnanta wata sunna mai kyau a musulinci" shi ne wanda yace: " dukkan bidi’a a addini bata ce", bazai yiwu ba ace akwai cin karo a cikin maganar Annabi, bayanin hadisan guda biyu shi ne kamar haka: Annabi cewa yayi: " duk wanda ya sunnanta wata sunnah mai kyau a musulinci", to ai bidi’a ba musulinci bane…..haka kuma da yace " mai kyau" to ai ita bidi’a ba mai kyau bace (babu kyau yin ta)., kuma Annabi ya bambanta tsakanin bidi’a da kuma sunnah, dan ma’anar fadar sa " duk wanda ya sunnanta", ai wanda ya raya wata sunnah, wacce dama akwai ta, Annabi (SAW) yayi umarni da ita, ko dai zance ko kuma aiki ko kuma qudircewa, sai aka samo tsawon lokaci mutane sun manta wannan sunnar,. Abin da ke qarfafa hakan shi ne hadisin wannan mutanen da suka zo wurin Annabi (SAW) alhali suna cikin talauci mai tsanani, sai Annabi ya buqaci a taimaka musu, sai wani mutum cikin mutanen madinah ya kawo wata jaka ta cika fal da azurfa, har ma da qyar yak e daukan ta, sai ya ajiye ta a gaban Annabi (SAW), sai Annabi ya fara murnushi (fuskar sa tana walwala), sai Annabi yace: " duk wanda ya sunnan ta wata sunnah to yana da ladar ta da kuma ladar duk wanda yayi aiki da ita har zuwa ranar alkiyama" [ sahihu muslim][58]. A nan kunga ma’anar fadar Annabi " wan da ya sunnanta" ai wato wanda yayi gaba wurin aikin alheri, amma bai wai wanda ya qirqiro ba, domin haramun ne qirqiro sabon abu a addini, dan yin hakan bidi’a ne, ita kuma " dukkan bidi’a bat ace"[59]

 

Ash sheikh Abdul azeez ibn baz Allah yayi masa rahama yana cewa: maganganun Annabi (SAW) basa karo da juna, wannan ijima’i ne na malanai masana, wannan ke nuna cewa ma’anar hadisin shi ne: raya sunnah da kuma bayyanata ga al ummah, misalign hakan, kamar a ce a samu wani malami a wani gari wanda basu koyar da al qurani ko kuma sunnah sai yazo ya fara koya musu qur’ani da hadisi, ko kuma ya kqwo musu malaman da zasu dinga karantar da su, ko kuma ace kamar ya same su ne suna aske gemu, ko kuma suma ragewa, sai ya umarce su da cika gemun su, da hakan sai ya zamo ya raya sunnar Annabi (SAW) a cikin wannan garin, da haka sai yayi ta samun lada irin na su a duk lokacin da suka yi aiki da wannan sunnar, haqiqa Annabi (SAW) yace: " [60] Mutane yayin da suka ga wannan malamin ya cika gemun sa yayi kira zuwa ga haka sai suma su cika na su dan yin koyi da shi, sai da haka sunnah ta rayu,… ko kuma abin da yayi kama da haka na ibada da hukunce nukunce na addini wanda aka sani sai wasu kasa ko kabila su jahilce ta, to wanda ya raya wannan sunnar a tsakanin su ya yadata da bayyana ta sai ace " duk wanda ya sunnanta wata sunna me kyau cikin musulunci" watan ma'ana ya bayyana hukuncin musulunci sai ya zama da wannan aiki nashi cikin wanda suka sunnanta sunna mai kyau cikin musulunci, bawai ana nufin ya kirkiri wani sabon abu ba ne a cikin addini wanda Allah bai yi umarni da shi ba, domin dukkan bidi’a bat ace, saboda fadar Annabi (SAW) a cikin hadisi: [61]

Hakanan kuma iyan bidi’a na kafa hujja da maganar umar dan khaddabi Allah ya qara masa yadda, dan su tallata bidi’ar su su kuna yada ta, yayin da sayyidina unary a tattara mutane a qarqashin limami guda daya a sallar tarawihy, sai yace: (madalla da wannan bidi’ar), anan yana nufin bidi’a ne a yaren larabci ba a shari’ance ba, domin sallar tarawiyi tana da madogara a addini, ba umar bane ya qirqirota, domin Annabi ma ai yayi sallar tarawihi da sahabbansa har na tsawon darare uku, sai daga baya Annabi ya daina, sai yace: " ni ina jin tsoro ne kar a wajab ta muku sai ku gaza (baza ku jure ba)".[62]

Sahabbai sun cigaba da yin sallar tarawihy a rayuwar Annabi (SAW) haka nan ma bayan ya rasu, amma kowa nayin nashi ne daban-daban a cikin masallacin Annabi (SAW), da umar yaga haka sai ya tattara su ya saka musu limami guda da suna bin sa bayan rasuwar Annabi (SAW), da haka ne zamu gane ashe sallar tarawihy tana da asali a addini, ba wai umar ne ya qirqire ta ba, dan Annabi ya sallace ta sai ya bari dan gudun kar a wajabta ta a kan al ummar sa, dan haka abin da umar (RA) yake nufi shi ne bidi’a a yaren larabci ba a shari’ah ba.

 

 

MATSAYAR MU GAME DA BIDI’A

Allah madaukaki yace: " ku bi abin da aka saukar muku daga ubangijin ku kuma kada ku bi wani koma bayansa kadan ne kuke yin tunani (4)"[63]

Me yin bidi’a ko dai ya zamo yana yi ne ba da ilimi ba (bai sani ba), kuma bidi’ar sa bata yadu ba, to irin wannan za’a karantar da shi ne kuma a fada masa gaskiya, tare bashi hujjoji daga al qur’ani da hadisai akan bacin aikin sa da kuma sabawar saga addini, ko kuma ya zamo yana yin bidi’ar ne dan san rai, to irin wannan za’a tunasash she sa ne kuma a tsoratar da shi Allah, kuma ayi mai bayani da hujjoji akan cewa abin da yake yi barna ne, aja hankalin sa da hikima da kuma wa’azi ta hanya kyakkyawa, to in har ya bijire kuma yayi girman kai, kuma ya doge akan bidi’ar sa, to ya wajaba ayi bayani akan bidi’ar sa da hujjoji, kuma a ja kunnen mutane game da shi da kuma bidi’ar sa, dan mutane su guje shi kuma su guji bidi’ar ta sa, kuma ita bidi’a kodai ta kasance mai fitar da mutun daga musulinci ko kuma ba mai fitar da mutum daga musulinci ba, to in ta kasance mai fitarwa daga musulinci, to ya wajaba a qaurace wa mai yin ta, in har anyi mai nasiha shi kuma yaqi ji ya doge akan bidi’ar sa, in kuma bidi’ar ba mai fitarwa b ace daga musulinci, to in akwai maslaha a cikin qaurace masa sai a qaura ce masa, in kuma ba wata maslaha a cikin qaurace masa to baza a qaurace masa din ba domin kada a taimaki shaidan akan sa, wataqila in ta hanyar yi masa nasiha zai bae bidi’ar tasa, saboda fadar Annabi (SAW): " bai halatta ba ga musulmi ya kaurace wa dan uwansa fiye da kwana uku"[64]

Yin raddi akan dukkan bidi’a in ta bayyana, da al qur’ani da sunnah wannan shi ne abin da magabatan wannan al ummah suka tafi akan sa, kuma yin raddi ga iyan bidi’a ba wai ya taqaita ga malamai ne kawai ba, a’a duk wanda yaga wata bidi’a a addini to ya wajaba yayi inkari in zai iya, in kuma bazai iya ba to wajibin sa ne ya fadawa malamai na Allah dan suyi wa mutane bayanin wannan bidi’ar da aka qirqiro a cikin addini Allah.

 

 

 

DALILAN DA KE SA BIDI’A YADUWA A ADDINI

  • Rashin dabbaqa shari’ar Allah da nisa daga hakan, da kuma yadda da wani abu sabanin shari’ar, Allah madaukaki yace: " yak u wadan da sukayi imani, kuyi wa Allah biyayya da manzan sa da kuma shuwagabanni daga cikin ku, in kukayi sabani a kan wani abuto ku maida shi ga Allah da manzo in har kunyi imani da Allah da kum rana ta qarshe, dan wannan shi ne mafi alheri kuma mafi kyawon bayani (59)".[65]
  • Rashin dabbaqa sunnah da kuma guje mata, duk lokacin da bawa yayi nisa daga sunnah to bidi’a ce zata kusance sa, kuma alhalin acikin sunnah akwai maganganun Annabi da ayyukan sa da kuma ababen da ya tabbatar wadanda zasu wadaci musulmi ba sai ya qirqiro wani abu a aaddini ba, Annabi (SAW) yana cewa: " haqiqa na bar muku abubuwa guda biyu in kun riqe su baza ku bace ba, littafin Allah da kuma sunnah ta"[66]
  • Qaurace wa al qur’ani da kuma rashin tadabburin sa da kuma aje shi dan tabbaruki kawai, da kuma rashin ambatun Allah, da kuma gudun ilimin addini, Allah madaukaki yace: " duk wanda ya guje wa ambaton Allah to zamu hada shi da shaidani sai ya zame masa aboki amini (36)"[67]
  • Tunkude gaskiya da kuma rashin karbar ta, Allah madaukaki yace: " kuma idan aka ce masa kaji tsoron Allah sai jiji da kai ya rufi shi yayi ta sabo, to wannan wutar jahannama ta ishe shi, kuma makoma tayi muni (206)"[68]
  • Riqon wasu malamai jahilai ko kuma batattu, Annabi (SAW) yace: " lallai Allah baya zare ilimi daga zukatan bayi, sai dai yana dauke ilimi ne ta hanyar dauke malami, har idan ya zamo ba malamai sai mutane su riqi jahilai a matsayin malamai, sai suyi ta basu fatawa ba da ilimi ba, sais u bace kuma su batar"[69]
  • Rashin koyan ilimi a wurin malamai da taqaituwa ga littafi kawai, masu hikima na cewa (duk wanda littafi ne malamin sa to kusakuren shi sun fi dai dan shi yawa), hakanan kuma karanta littattafai wadanda akwai barna a cikin su, ko kuma mawallafan su mabannata ne, wata rana Umar dab khaddabi (RA) ya zo wurin Annabi (SAW) da wani littafi wanda ya karbo a hannun yahudawa, sai Annabi (SAW) ya karanta shi, sai yayi fushi, sai yace:”shin kuna shakka ne ya kai dan khaddabi?, na rantse da wanda raina ke hannun sa haqiqa na zo muku da wannan addini fari tas, kada kuje ku tambaye su wani wabu sais u fada muku gaskiya ku kuma ku qaryata su, ko kuma su fada muku qarya sai ku gaskata su, na rantse da wanda rain a ke hannun sa da ace Annabi musa na raye to da shima sai dai ya bi ni”[70]
  • Rashin yada ingantaccen ilimi, wannan kuma na faeuwa ne in har malamai suka yi shiru, kuma suka boye ilimi, Allah madaukaki yace: " lallai wadan da suke boye abun da muka saukar na bayani da kuma shiriya bayan munyi bayanin sag a mutane a littafi to wadannan Allah na tsine musu da kuma masu tsinuwa (159) sai dai fa wadanda suka tuba suka gyara kuma sukayi bayani to wadannan zan karbi tuban su, kuma ni ne mai yawan karbar tuba kuma mai jin kai (160)"[71]
  • Qetare iyaka a cikin addini (guluwwi), hakan na daga cikin dalilan da ke sa shirka da bidi’a yaduwa, Annabi (SAW) yace: " kashedin ku da qetare iyaka a addini (guluwwi), domin abin da ya halakar da wadan da suka gabace ku shi ne wuce gona da iri acikin addini (guluwwi)"[72]
  • dogaro akan hankali cikin al'amuran addini, Allah madaukaki yace: " bai dace bag a mumini ko kuma mumina mace idan Allah da manzon sa suka hukunta wani abu ya zama suna da zabin ran su akan wannan hukunci nasu, duk wanda yake sabama Allah da manzon sa to hakika ya bace bata bayyananne (36)"[73]
  • Bin san rai da kuma labewa a bayan sa, Allah madaukaki yace: " shin ko ka ga wanda ya riqi san ransa a matsayin abin bautar sa, sai Allah ya batar da shi akan sani, sai yayi rufi akan jin sa da zuciyar sa kuma ya sanya shamaki a ganin sa, to wa zai iya shiryar da shi in ba Allah ba, ashe baza kuyi tunani ba (23)"[74]
  • Makauniyar biyayya, da kuma qanqame al’ada a abin da ya shafi addini, ba tare da ilimi ba ko kuma shiriya, da kuma qin komawa ga littafin Allah da kuma sunnar manzan sa (SAW), Allah madaukaki yace: " kuma idan aka ce musu ku bi abin da Allah ya saukar sai su ce mu zamu bi abin da muka samu iyayen mu ne akan sa, kuma koda iyayen na su basu san komai ba kuma basu kan shiriya (170)"[75]
  • Zama da mabannata da masu sharri, Allah madaukaki yace: " kuma a ranar da azzalumi zai dinga cizon yatsan sa yana cewa kaico nan a riqi wata hanya tare da hanyar manzo (27) ya kaico na ina ma ban riqi wa ne aboki ba (28) hakika ya batar da ni daga ambatan Allah bayan ya zo min, kuma shaidan ya kasan ce ga mutum mai tabar wa ne (29)"[76]
  • Barin yin umarni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna, Allah madaukaki yace: " lallai a samu wasu mutane a cikin ku masu kira zuwa ga alkhairi, suna umurni da kyakkyawa kuma suna hani daga mummuna, to wadannan su ne masu rabauta (104)”[77]

 kuma Annabi (SAW) yana cewa: " babu wani annabin da Allah ya aiko kafin ni face yana da dalibai da sahabbai wadanda suke ruqo da sunnar sa kuma suna koyi da al’amuran sa, sannan sai a samu wasu suzo a bayan su , suna fadar abun da basa aikatawa, kuma suna aikata abun da basa umarni da shi, duk wanda ya yake su da hannun sa to shi mumini ne, haka kuma duk wanda ya yaqe su da harshen sa to shima mumini ne, haka nan duk wanda ya yaqe su da zuciyar sa to shima mumini ne, to babu ko kwayar zarra ta imani bayan haka"[78]

  • Bin abubuwa masu rikitarwa a addini, Allah madaukaki yace: " shi ne wanda ya saukar maka da littafi a cikin sa akwai a’yoyi muhkamai su ne tushen littafi da wasu kuma masu rikitarwa, to wadan da zukatan su akwai karkata sais u dinga bin abubuwan da ke rikitarwa dan san fitina da kuma san tawili, to babu wanda ya san tawilin su sai Allah, su kuma masu zurfi a cikin ilimi cewa suke yi munyi imani da shi, dukkan sa daga ubangijin mu yake, kuma babu masu tutuwa sai ma’abota hankula (7)"[79]
  • Yin sakaci da matsalar wala’a da bara’a (kauna da kiyayya), san maqiya addini na shiga qarqashin haka, domin san sun a kaiwa zuwa ga kwaikwayon su, da kuma Kamanceceniya da su, an ruwaito hadisi daga Abi waqidi al laisi Allah ya kara masa yadda yace: yayin da Annabi ya ci maka da yaki, sai ya fita da mu zuwa hawazin, sai muka wuce wata bishiyar magarya ta kafirai suna bauta a wurin ta (suna bauta mata), kuma suna kiran ta “zatu anwad”, sai muka ce ya manzan Allah: mum aka sanya mana zatu anwad, kamar yadda suke da zatu anwad, sai Annabi (SAW) yace: "Allahu akbar, lallai haka abin yake, kun fada kamar yadda banu isra’ila suka ce wa Musa, kasanya mana abun bauta kamar yadda suke da abun bauta, sai yace lallai ku mutane ma masu jahilci" sannan manzon Allah s.a.w yace: "lallai ku zaku dinga bin hanyoyin wadanda suka gabace ku. (yahudu da nasara ""[80]
  • Yin ijtihadi a cikin abin da ba’a ijtihadi, da kuma lanqwasa wuyan nassosi, daga cikin abin da ya kamata mu kula shi ne akwai hadisan da ake jingina su ga Annabi (SAW) na karya, to irin wadannan ya kamata ayi hattara da su, ayi gargadi game da su kuma aki yada su ko kuma kafa hujja da su, sai kuma hadisai masu rauni, duk da wasu malamai basa ganinmlaifin kafa hujja da su a wurin ayyuka masu falala amma da sharadin kada suci karo da ingantattun hadisai, amma abin da ya shafi ibada to ba’a kafa hujja da su, abun da ake dogara da shi shi ne abin da ya tabbata daga manzan Allah (SAW).

 

 

 

SHARUDDAN KARBAR AIKI

Lalli ayyuka basa karbuwa sai sun cika sharudda guda biyu:

  • Sharadi na farko shine yin aiki dan Allah (ikhlasi), Allah madaukaki yace: " kuma ba’a umurce sub a sai dais u bauta wa Allah suna masu tsarkake addini a gare shi suna masu karkata zuwa ga addinin gaskiya kuma su tsaida salla kuma su bada zakka, kuma wannan shi ne addini miqaqqe (5)"[81]

 kuma Allah yana fada a cikin hadisin qudusi: "[82]

  • Sharadi na biyu / koyi da Annabi, ta yadda aiki zai zamo yayi dai dai da abin da Annabi (SAW) yazo da shi, shi kuma koyi da Annabi bai inganta sai da sharudda gda shida, su ne kamar haka:
  1. Sababi, idan mutum ya bauta wa Allah da wata ibada mai hade da wani sababimwanda ba shar’antacce ba to wannan ibadar bidi’a ce, za’a dawo da ita ga ma’abocin ta, misali akan haka: wasu mutane kan raya daren 27 na watan rajab, wai saboda wai shi ne daren da aka yi tafiya da Annabi (SAW) zuwa sama, sallar dare dai ibada ce amma yayin da ya zamo wannan ne sababin ta sai hakan ya zamo bidi’ah, domin an gina ta akan wani sababi wanda bai tabbata ba a shari’a, wannan al’amari ne mai mahimman ci mutum yasan sa, dan guje wa fadawa a wasu abubuwa da yawa wadanda ake zaton sunnah ne alhali ba unnah bane.
  2. Nau’I, dole ne ibada ta zamo ta dace da shari’ah a wurin nauin ta, da mutum zai bauta wa Allah da wata ibada wacce babu irin ta a shari’ah, to baza’a karba ba, misali akan haka: da mutum zaiyi layya da doki da layyar sa batayi ba, domin ya sabawa shari’ah a wurin nau’i, saboda ba’a layya sai da dabbobin ni’ima, (raquma da shanu da awaki).
  3. Adadi, da ace wani mutum zai zo ya qaro adadin sallolin farilla (su wuce biyar), sai muce masa wannan bidi’a ce kuma baza a karba ba, domin ta saba wa shari’ah a wurin adadi, to hakanan da mutum zaiyi sallar azahar raka’a biyar, sallar sa bata inganta ba, (saboda yayi qari a cikin adadi).
  4. Yanayi, da ace wani mutum zai yi alwala sai ya fara daga qafa, sannan ya zo shafar kai sannan ya wanke hannaye sannan fuska, sai muce alwalar sa batayi ba, saboda ya sabawa shari’a wurin yanayin alwala.
  5. Lokaci, da ace mutum zai yi yanka a matsayin layya tun ranar farko a watan zul hijjah, da layyayr sa batayi ba, domin ya saba wa shari’a a lokacin da ta sa.
  6. Wuri, da ace mutum zai yi itikafi a cikin daki (ba a masallaci ba), da itikafin sa bai yi ba, saboda itikafi ba’a yin sa sai a masallaci …[83]

 

 

 

 

HATSARIN BIDI’A

Lallai bidi’a sharrin ta mai yawa ne kuma hatsarin ta mai girma ne, saboda wata kofa ce wadda maqiya musulinci ke amfani da ita dan rushi addini, saboda haka ko wane a cikin mu ya kiyaye dan kar ya zama wanda ake amfani da shi wurin rusa wannan addinin namu, hakanan kuma kar mu taimaka da da dukiyar mu ko matsayin mu wurin goyon bayan bidi’a, kuma ta hanyar bidi’a maqiya musulinci sun samu damar rarrabe kan musulmai, da kuma ware kawunan su, a duk lokacin da bidi’a ta yadu to za’a kasha sunnar Annabi ne, daga nan kuma kada kayi mamkin abun da zai faru na mantawa da kuma tozartawa da kuma ruqon sakainar kasha da za’a dinga yi wa addini, wanda a qarshe zasu iya sa’a a bar addinin ma baki daya, (Allah yayi mana kariya),.

Annabi (SAW) yana cewa: " .[84]

Dan haka ya kamata duk wanda zaiyi wani aiki wanda ya shafi ibada to ya dora ibadar a ma’auni na littafin Allah da sunnar manzan Allah (SAW) da kuma aikin magabata na qwarai (halifofi shiryayyu), duk abin da ya dace da shari’ah sai ya karba kuma ya aikata, saboda fadar Annabi (SAW): [85]

 duk kuma abin da ya saba wa shari’ah to zaman lafiya shi ne a bar sa, kuma kada a yada shi, Annabi (SAW) yana cewa: [86]

Laali musulinci shari’ar Allah ne, kuma Aannabi (SAW) ya baiyana shi, to duk abun da Annabi bai baiyana ba kuma bai yi kira zuwa gare shi ba to wannan abun ba addinin Allah bane, duk wanda ke qaunar tsira da rabo a lahira da kuma samun yaddar Allah to Annabi ya zamo shi ne abun koyin sa, domin koyi da shi da kuma bin tafarkin sashi ne zai kai bawa zuwa ga samun yaddar Allah da kuma qaunar sa, Aallah madaukaki yace: "[87]

 duk mai san ya samu yaddar Allah da kuma gafarar sa to ya saki duk wanda ba Annabi ba, domin babu ma’asumi (wanda baya sabo) sai shi kadai, sauran mutane kuma sukan yi dai dai, amma sau da yawa san rai da kuma bin san zuciya da bin sha’awa na samun su.

 

 

 

FADAKARWA DA KUMA JAN HANKALI

Abdullahi ibn addailami yace: lallai farkon rushewar addini shi ne barin sunnah, addini na rushewa kadan-kadan kamar yadda igiya take tsinkewa sili-sili.[88]

Saboda haka ya wajaba kowannen mu yayi riqo da sunnar Annabi (SAW) ingantacciya da kuma yin kira na gaskiya dan yin aiki da ita, domin dukkan alheri na cikin koyi da shi da kuma riko da sunnar sa, ta aiki ko zance da kuma barin dukkan wani abu koma bayan hakan wanda aka qirqiro a cikin addinin Allah, hakanan kuma yana wajaba aan kowa daga cikin mu idan yaga ko kuma ya ji wani abu wanda ke sabawa shari’ah ko kuma wanda baya cikin ta yayi nasiha kuma ya bayyana gaskiya, dan ya samu lada na masu kariya ga addinin Allah da kuma daga tutar sa, Annabi (SAW) yana cewa: [89]

tunkude bidi’a da kuma qoqarin janza ta babu wand aba wajibin sa bane, kowa gwargwadon ikon sa da kuma iyawar sa, Annabi (SAW) yana cewa: [90].

 ya zamo lokacin da yake kokarin yin nasiha da kuma baiyana gaskiya yana qoqarin dacewa da fadar Allah madaukaki: "[91]

Lallai al'amuran addini ba kowa ba ne da zarar yayi da’awar ilimi da fahimta sai a karba daga gare shi, a’a yana wajaba ne a karbo al'amuran addini a wurin amintacce a cikin addinin sa ilimin sa tsoron Allahn sa da kuma gudun duniyar sa sannan kuma da amanar sa, Annabi (SAW) yana cewa: " l[92]

Kuma koda yaushe mu dinga tina fadar manzan Allah (SAW): [93]

Ita bidi’a tana cikin bata.

haka nan kuma duk wanda ya nuna wa mutane kofar sharri -bidi’a sharri ce- to zunubi na kan sa da kuma zunuban duk wanda ya bi shi, Annabi (SAW) yana cewa: [94].

Da wannan ne girman hatsarin yin bidi’a a addini zai baiyana, dan haka wajibi ne ga dukkan wandake so ya aikata wani aiki ko kuma yayi umarni da shi to ya duba shin ya dace da shari’ar Allah koko bai dace ba, in har ya dace da shari’ar Allah sai ya aikata shi kuma yayi kira zuwa gare shi kuma ya kwadaitar akannaikata shi, in kuma ya saba wa shari’a ko kuma Annabi (SAW) bai aikata ba hakanan ma sahabban sa basu aikata ba, sai ya bar shi kuma ya gargadi mutane game da shi, dan kada zunubi ya hau kansa hakanan da zunubin wanda suka aikata har zuwa ranar qiyama, dan haka wannan al’amari ne mai hadarin gaske, ya wajaba a fadaka daga gare shi kuma a riqe kariya game da shi.

 

www.islamland.com

 

 

 

[1] - suratul Hashri aya ta 7

[2] - suratu Aaliimran aya ta 31

[3] - sahihul bukhari mujalladi na 2 shafi na 959 lamba ta 2550

[4] - suratul furqan aya ta 43

[5] - suratul ambiya, aya ta 7

[6] - suratu luqman, aya ta 21

[7] - suratu nuh, aya ta 23

[8] - sahihul bukhari, mujalladi na 4, shafi na 1873, lamba ta 4636

[9] - madarijussalikeen, shsfi na 24-256

[10] - musnadul imam ahmad, mujalladi na 5, lambar hadisi 22860

[11] - sahihul bukhari, mujalladi na 1, shafi na 434, lamba ta 1229

[12] - al ma’ida, aya ta 7

[13] - an nahl, aya ta 89

[14] - an nisa, aya ta 113

[15] - an nahl, aya ta 44

[16] - sahihu muslim, mujalladi na 3, shafi na 1472, lamba ta 1844.

[17] - al mustadrah ala as sahihain, mujalladi na 1, shafi na 175, lamba ta 331.

[18] - al baqara, aya ta 112.

[19] - yayi bauta ta hanyar koyi da alqur’ani da hadisi.

[20] - taisiru al karim al rahman, ash sheikh/ abd arrahman as sa’ady

[21] - al an’a’m, aya ta153. Da kuma sahihu ibn hibban, mujalladi na 1, shafi na 180, lamba ta 6.

[22] - sahihu ibn khuzaimah, mujalladi na 3, shafi na 143, lamba ta 1785.

[23] - al a’araf, aya ta 33

[24] - al isra’I, aya ta 36

[25] - ash shura, aya ta 71.

[26] - at tauba, aya ta 31.

[27] - sunan altirmizi, mujalladi na5, shafi na278, lambar hadisi na 3095

[28] - taisiru al karim ar rahman, shafi na 295.

[29] - jami’ul ulum wal hikam, 1/120.

[30] - al ahzab, aya ta 21.

[31] - sahihu ibn hibban, mujalladi na 1, shafi na 178, lamba ta 5.

[32] - yunus, aya ta 62-63.

[33] - al hujurat, aya ta 13.

[34] - al magazy al kubra, shafi na 178-179.

[35] - al baqara, aya ta 118.

[36] - taisirul karim ar rahman, aya ta 16.

[37] - al ahqaf, aya ta 9.

[38] - taisirul karim ar rahman, shafi na 725.

[39] - an nisa’, aya ta 115

[40] - sahihul bukhari, mujalladi na 6, shafi na 2655, lamba ta 6851.

[41] - al fatawa al kubra, shafi na 194.

[42] - al an a’m, aya ta 162.

[43] - sunsn abu daud, mujalladi na 7, shafi na 718, lamba ta 2042.

[44] - sahihul bukhari, mujalladi na 5, shafi na 1949, lamba ta 4776.

[45] - sahihu ibn hibban, mujalladi na 1, shafi na 178, lamba ta 5.

[46] - an nur, aya ta 63.

[47] - sahihul bukhari, mujalladi na 2, shafi na 1319, lamba ta 2550.

[48] - sahihul bukhari, mujalladi na 3, shafi na 1319, lamba ta 3411.

[49] - sahihul bukhari, mujalladi na 5, shafi na 2404, lamba ta 6705.

[50] - ibn majah ne ya ruwaito shi a cikin shu’abul iman, da dabarany a cikin awsad, al bany ya inganta shi a sahiha 1670.

[51] - al fathul bari, 13/307.

[52] Usulul I’itiqad, 1/72.

[53] - igathat al lahfaan 1/159.

[54] - talbees iblees, shafi na 14.

[55] - talbees iblees, shafi na 13.

[56] - igasat al lahfan, 1/213.

[57] - sahihu muslim, mujalladi na 7, shafi na 704, lamba ta 1017.

[58] - muslim ne ya ruwaito shi.

[59] - ash sheikh ibn uthaimeen, a cikin littafin sa “ al ibda;a fi kamali ash shar’i………..

[60] - majmu’u fatawa wa maqalaat mutanawwi’a, na sheikh Abdul azeez ibn baz.

[61] - sahihul bukhari. Mujalladi na 7, shafi na 708, lamba ta 1908.

[62] - sahihul bukhari, mujalladi na 2, shafi na 708, lamba ta 1908.

[63] - al a’raf aya ta 3.

[64] - sahihul bukhari, mujalladi na 5, shafi na 7753, lamba ta 5718.

[65] - an nisa’, aya ta 59.

[66] - al mustadrak ala as sahihain, mujalladi na 1, shafi na 172, lamba ta 319.

[67] - azzukhruf, aya ta 36.

[68] - al baqara, aya ta 206.

[69] - sahihul bukhari, mujalladi na 1, shafi na 50, lamba ta 100.

[70] - musnadul imam ahmad, mujalladi na 3, shafi na 387, lamba ta 15195,

[71] - al baqara, ayata 159 – 160.

[72] - sahihu ibn hibban, mujalladi na9, shafi na 182, lamba ta 3871.

[73] - suratul ahazab ayata 36

[74] - al jathiya, aya ta 23.

[75] - al baqara, aya ta 170.

[76] - al furqan, aya ta 27 – 29.

[77] - aali Imran, aya ta 104.

[78] - sahihu muslim, mujalladi na 1, shafi na 69, lamba ta 50.

[79] - aali Imran, aya ta 7.

[80] - sahihu ibn hibban, mujalladi na 15, shafi na 94, lamba ta 6702.

[81] - al baiyinah, aya ta 5.

[82] Sahihu muslim, mujalladi na 1, shafi na 2289, lamba ta 2985.

[83] - saihu muslim, mujalladi na 4, shafi na 2289, lamba ta 2985.

[84] - daga littafin al ibda’a fi kamli ash shar’e, na ash sheikh Muhammad ibn uthaimeen.

[85] - al mustadrak ala as sahihaini, mujalladi na 4, shafi na 477, lamba ta8325.

[86] - al mustadrak ala as sahihaini, mujalladi na 1, shafi na 172, lamba ta 319.

[87] - aali Imran, aya ta 31.

[88] - sunan addarimi, mujalladi na 1, shafi na 58, lamba ta 97.

[89] - sahihul bukhari, mujalladi na 3, shafi na 1275, lamba ta 3274.

[90] - sahihu muslim, mujalladi na 1, shafi na 69, lamba ta 49.

[91] - an nahl, aya ta 125.

[92] - sahihu ibn hibban, mujalladi na 1, shafi na 289, lamba ta 88.

[93] - sahihu muslim, mujalladi na 4, shafi na 2060, lamba ta 2674.

[94] - sahihu ibn kuzaymah, mujalladi na 3, shafi na 143, lamba ta 1785.