Makwararar qoramai

Makwararar qoramai

 

Makwararar qoramai
Allah ta;ala yana cewa: shi ne wanda ya tafiyar da qoramai biyu wannan mai daxi qorama, wannan kuma mao zartsi mara daxi ya kuma sanya shamaki mai shingewa tsakaninsu " Al- furqan 53)
Haqiqar ilimi:
Littafin farko da da ya bayyana a kan ilimin koguna  da tekuna a qarni na sha takwas babu bayanai masu gamsarwa na ilimi a ciki daga baya ilimin tekuna ya qara samun bunqasa lokacin da jirgin ruwan Ingila ta farko calengar ta fara kewaya duniya daga shekara ta 1872 har zuwa 1876, sanna kuma aka cigaba ta tafiye tafiyen ilimi don bincike ruwa. a qarshen  qarni na ashirin aka qara samun masaniya kain da nain game da tekuna ta hanyar amfani da tauraron  xan Adam da xaukan hoto daga nesa, bayan anyi waxan nan gwaje gwajen da dama aka gano cewa: makwararan ruwan teku da na koguna da koramai ko wanne yana da yana yinsa dabam da kuma irin halittun da suke rayuwa a cikinsa duk da cewa akwai cuxuwar ruwa tsakaninsu da shigan juna, gwargwadon kwararan ko wanne daga cikinsu da kai komon su, amma duk da haka akwai shamaki tsakanin makwararan ko wanne da ga cikinsu basa haxewa da juna . kamar yadda aka gano cewa akwai wasu halittu da basa rayuwa awasu nahiyoyin makwaran ruwa akwai inda ma ba a samun wani abu mai rai a ciki, duk da ambaliyar da ruwa ke yi atsakaninsu.saboda kowanne yanke bvantuwa da irin suffofinsa.
Fuskacin mu;ujiza:
Ko wane taruwan ruwa za a iya kiranra kogi, amma ruwan daxi mai garxi sosai shine kogi, ruwan zartsi mai gishiri sosai shi ne teku, ta haka zamu fidda makwararan ruwa wato mahaxa ta yadda ba za mu iya kiransa da ruwan garxi ba ba kuma zamu iya ce masa ruwan zartsi ba, don haka muna da kashin ruwa har uku kenan ruwan garxi da na zartsi da na tsaka tsaki.wanda aka sifata a cikin Qur'ani cewa akwai shamaki a tsakaninsu basa haxuwa , wato ruwan garxi ba zai rinjayi ruwan zartsi ba, wannan shi ne abin da ke rabe magudana ruwa. Uku ko wanne da siffofinsa da yanayinsa da kuma irin halittun da suke rayuwa ciki.
Tarihi ya tabbatar da cewa babu wani ilimi da ya shafi ruwa mai zurfi a cikin shekaru 1400 da suka gabata, amma duk da haka Alqur'ani ya  bayyana mana wannan abu cikin cikakken bayani mai gamsarwa ta hanyar cakuxuwar ruwa da koramai da koguna da teku, kuma ko wane na da siffofinsa.
Ta ina aka smi wannan bayanai b tare da tauraron dan ADAM ba, ba kuma wasu kayan gwaje gwaje na takanolaji, indai wannan bayani ba daga wurin Allah da yasan komai da komai ba.