Game da rubutattun maudu'ai

mawallafi :

www.eajaz.org

kwanan wata :

Thu, Jan 15 2015

Bangarori :

Buwayar Ilimi

Riga kafi kariya

Riga kafi kariya

 

Manzo (s.a.w) ya ce (idan kuka ji annoba awani gari kada ku shige shi,idean ya auku a wani gari kuna cikinsa kada ku fita daga ciki) Buhari da Muslim suka ruwaito.

Manzo (s.a.w) ya ce (idan kuka ji annoba awani gari kada ku shige shi,idean ya auku a wani gari kuna cikinsa kada ku fita daga ciki) Buhari da Muslim suka ruwaito.

Ma'aiki (s.a.w) ya kara cewa: "mai gudun annoba kaman mai gudu ne daga yaki, wanda yayi hakuri yana da ladan shahidi."Ahmad ya ruwaito.
 
Haqiqanin Ilimi:

Cigaban ilimi ya tabbatar da wasu halittu kanana. Kuma ya bayyana hanyoyin yaduwansu da hayayyafansu

A lokacon da cutuka ko annoba suka faru. Aka gano cewa masi lafiya wadanda ba su da alamar kamuwa da ciwon a wuraren annoba  su ne suke daukan makirob din ciwon , kuma sune babban hadari wurin daukan cutar zuwa  wasu wuraren idan suka tafi can. Saboda gano wannan hakikar ne aka kirkiro abinda ake kira " riga kafin kariya" wamda aka sani a duniya yanzu. Wato wanda yake hana dukkan mazauna garin da annoba ta sauka da su fita daga wannan garin sannan kuma a hana wasu shiga.

Annoba ta taba kwarara a turai a karni na goma sha biyar miladiyya inda ta kashe daya cikin hudun mazauna turai. Alokacin da ta zamo bata yaduwa a kasashen musulmi da yawa,a wancan lokaci  annoba da cutuka sun fi yaduwa akasashen turai fiye da kasashen musulmai..
 
Fuskacin mu'ujiza:

Mutane a zamanin ma'aiki (s.a.w) da kafin zamaninsa  sun kasance suna kudurta cewa- har lokacin da (baster) ya gano makrobat- wannan cuta aljannu ne  iskoki ko taurari suke kawo ta ba ta da wani alaka da tsafta ko kazanta ko wani yanayi, saboda haka ba sa yarda da cewa kwayoyin cutan zasu iya tashi daga mutun zuwa wani,sai suna neman mata magani ta hanyar tsibbu da bori tsafi.

awannan  yanayin ne ma'aiki (s.a.w) ya kawo wata ka'ida wacce ta zama asasin ilimin riga kafin kariya na zamani, bayan da aka gano dalilan da suke sanya cutukan da annobar, wato riga kafin kariya, don hana watsuwar annoba a wasu biranen ko gungun wasu mutanen. Ma;aiki (s.a.w) shi ya tabbatar da wannan hakikanin ilimin acikin hadisinsa" (idan kuka ji annoba awani gari kada ku shige shi,idean ya auku a wani gari kuna cikinsa kada ku fita daga ciki) Buhari da Muslim suka ruwaito.

Don a kara tabbatar da wannan wasiyar ta Ma'aiki (s.a.w) ya gina kango mai karfi a wurin annoba yayi wa wanda yayi hakuri ya zauna awurin annoban da ladan shahidai, kuma yayi wa wanda ya gudu daga wurin alkawarin narkon azaba da cewa: "mai gudun annoba kaman mai gudu ne daga yaki, wanda yayi hakuri yana da ladan shahidi."Ahmad ya ruwaito.

Idan akacewa mutum lafiyayye a shekaru xari biyu da suka gabata, alhalin yana ganin masu ciwo na mutuwa a gefensa, kuma yana cikin qoshin lafiyarsa  ace masa: ka zauna kada kabar inda kake . da sai yace wannan maganan hauka ne ko kuma ba a qaunarsa da rayuwa, zai zabura ya gudu zuwa wurinda babu wannan annoba , saboda haka mu musulmi ne kawai muke zama alaokacin da annoba ya faru muna aiwatar da maganan manzonmu (s.a.w). har sai lokacin da ilimi ya gano haka aka fara amfani da wannan sabon ilimin da aka gano alokacin da mu musulmi mun jima muna aiki da wannan koyarwar manzo(s.a.w)

Shin akwai wanda zai iya bada wannan bayani  aqarni goma sha huxu da suka gabata ? in dai ba wanda yake da wahayi na ubangiji ba!! Allah (s.w) na cewa " ka ce godiya ta tabbata ga Allah, zai nuna maku ayoyinsa kuma zaku sansu , Ubangijinku ba mai rafkana ba ne ga abinda kuke aikatawa)(an-namli  93).