Game da rubutattun maudu'ai

mawallafi :

www.eajaz.org

kwanan wata :

Thu, Jan 15 2015

Bangarori :

Buwayar Ilimi

SIFFOFIN TEKUNA MASU ZURFI

SIFFOFIN TEKUNA MASU ZURFI


Allah (s.w) na cewa:"ko kamar dufai acikin teku mai zurfi, wanda taguwar ruwa ta rufe shi, abisansa akwai wata taguwar,abisansa kuma akwai girgije, duffai sashinta akan sashi, har in ya fitar da hannunsa ba ya iya ganinsa , duk wanda Allah bai sanya masa haske ba ba zai tava samun haske ba." (An-nur 40).
Haqiqar ilimi:
Kundin ilimin insakwalfidiya ta Birtaniya ta bayyana cewa: da yawa daga cikin tekuna  masu zurfi suna rufe ne da wasu giragizai inda suke karai mafi yawan hasken rana, kamar yadda ake iya gani ta tauraron xan Adam.. wannan hazo da yake bayyana shi yake kare hasken rana, kuma duk lokacin da ruwan yayi zurfi da yawa duhun na qara yawa, tun daga mita dari biyu har ya zuwa mita dubu, inda za a rasa ganin komai baki xaya. Faifan sesshi shine wato(secchi disk) shine injin farko da aka fara amfani dashi wurin gane dushewar haske acikin zurfin teku. Masana sun iya hango kifaye acikin tsakiyar zurfin teku  mita(600-2700) ta hanyar amfani da wata fitila mai haske sai daga baya a cafke kifayen.
Ilimin tekuna na zamani a qarshen qarni na sha tara ya binciko hanyoyin amfani da wasu kamarorin xaukan hoto.daga baya aka qara bunqasa kamaran a tsakiyar qarni na ashirin don amfani da shi a irin wadannan tekuna masu zurfin gaske. Kundin Insakwalfidiyar ta qara bayyana cewa: ba asan cewa akwai irin wannan duhun ba acikin tekuna masu zurfi sai a kusan shekaru da suka wuce.ta yadda irin wannan taguwar ruwar take qara duhun ruwan da sanyinsa ko zafinsa gwargwadon zurfin ruwan da yawan ambaliyarsa da yadda iska yake kaxawa.
Wannan taguwar da take rarrabe tsakanin kamanin ruwar teku wurin zafi da sanyi  da zartsi da garxi, ba a iya gane irin wannan  bambamcin da ido. Amma akwai lokacin da zaka ga jiragen ruwa sukan kasa motsi a wani irin yanayi, akan kira wannan ruwa da sunan"kwantaccen ruwa"  wanda docta V.W Ekman shi ya fara binciken wannan aqarni na ashirin.
Fuskacin mu'ujiza:
Da can mutane suna da wani camfi da suke yiwa koguna da teku , kuma masana ruwa na wancan likacin basu da cikakken masani game da abin da ya shafi yanayin ruwa da sassayawarsa, mai zurfin gaske.
abinda yasa wasu suke yin camfi a irin waxannan ruwa marasa tafiya sukan ce akwai waxansu kifaye ne da muke riqe jirage a irin wannan wurare, kamar yadda romawa na da sukan ce.duk da cewa suna sane da cewa kaxawar iska na tasiri acikin harkokin taguwar ruwa, amma duk da haka zai masu wahalar fahimtar teku mai zurfin gaske, kamar yadda nazari ya tabbatar da cewa ba afara bincike mai zurfi gameda ruwa ba sai atsakiyar qarni na ashirin, yayinda aka gano irin zurfin ruwa da duhun da yake ciki da abubuwan da suke faruwa sakamakon duhun.amma wannan aya ta Alqur'ani mai girma tayi nuni ga waxannan abubuwa biyu.
Haqiqa ayar tayi nuni ga zurfin teku da duhunsa da kalmar"teku mai zurfi" masu tafsiri suka ce: abinda ake nufi da waxannan duffai sune: duhun girgije, da duhun taguwar ruwa, da duhun teku. Duk wanda ya kasance a xayan wuraran nan uku ba zai ga komai ba" amma giragizai masu yawa da suka kare wannan teku, ita kuma taguwar ruwa tana rufe sauran hasken ta haka duhun ya ke faruwa hatta kifaye da suke wannan yanayi Allah ya haliccesu da wani jiki mai haskaka masu hanyarsu:"  duk wanda Allah bai sanya masa haske ba ba zai tava samun haske ba"
Kuma Allah ya yi nuni ga yanayin motsin tekun da faxinsa" acikin teku mai zurfi, wanda taguwar ruwa ta rufe shi, abisansa akwai wata taguwar" ma'ana taguwar tana rufe tekun mai zurfi wannan shine haqiqanin abinda masana na zamani suka gano  na cewa ruwa mara zurfi yayi dabam da ruwa mai zurfi ,abinda ba a gano ba sai nan da shekaru xari da suka gabata kawai.
amma waxannan bayanai duka Alqur'ani yayi nuni garesu filla filla a qarni goma sha huxu da suka gabata. To wanene ya baiwa muhammad (s.a.w) wannan labari ? shine Allah (s.w).