Shari‘a a addinin musulunci da kiristanci da yahudanci

Shari‘a a addinin musulunci da kiristanci da yahudanci

Sharia a addinin musulunci da kiristanci da yahudanci

 الشريعة في الإسلام والنصرانية واليهودية بلغة الهوسا

 

Wanda ya wallafa:

SHEIKH\ AHMAD AL-AMIR

أحمد الأمير

 

Lauya a koton daukaka kara

Wanda ya bibiye littafi da gyara shi da gabatar dashi:

DAKTA ABD ΑR-RAHMAN DAN ABD ΑL-KARIM AL-SHEHA

د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة

 

Fassara:

European Islamic Research Center (EIRC)

المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية

& Hashim Muhammad Sani

Wanda ya bibiyi fassara

& Faiz Shuaib Adam

 

WWW.ISLAMLAND.COM

 

 

 

GABATARWA

DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA MEJIN KAI

 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad da iyalan sa da sahabban sa baki daya.

Mutum halitta cikin halittun Allah madaukaki a cikin wannan duniya me fadi, bangare ne wanda baza'a iya rabashi ba daga gareshi, sunada amfani da aiki wanda iyakantacce ta yadda da zasu fita daga cikin wannan aiki wanda aka iyakance masu cikin littafai wanda aka saukar daga sama domin su da wani matsala ta faru wanda hakan zaiyi tasiri ga duniya, wannan abun lura ne da kuma gani da ido alokacin da mutum ya aikata abunda aka hane shi kuma suka kawar dakai daga abunda aka masu umurni dashi suka bi son zuciyoyin suda sha'awar su sai fasadi wanda zai mamaye duniya ya bayyana a doron kasa da sama, sai cututtuka su yadu wanda mutanen da suka gabata basu san su ba, kuma yaki ya yawaita wanda yake daidaita gonaki da zuriya, kuma matsaloli na yanani ya bayyana kamar yadda ake gani na dumama yanayi da kuma karuwan zafi – wanda da al'amarin zai ci gaba da kasance wa a hakan da duniya ta kowa wuri wanda mutum bazai iya rayuwa a cikinta ba – dukkanin haka sakamakon was an mutum ne na gwajin nukiliya da daukan abunda yafi karfuin sa da kuma kamfanoni wanda suke samar da sama da bukata na mutum dukkanin haka na faruwa ne domin samun abun duniya da kuma tabbatar da bukatu da biyan sha'awa koda kuwa ya kasance ta hanyar wulakanta yan uwan sa ne cikin mutane da yancin dan adam, suna son su koshi koda kuma a cikin asusun yunwan wanin su ne, kuma su sanya tufafi koda kuwa a cikin tsiraicin wasun su ne, da jin dadi koda kuma ta hanyar kashe wasun su ne, lallai Allah yayi gaskiya da yake fadi cewa:

“fasadi ya yadu a doron kasa da cikin ruwa sakamaon abubuwan da mutane ke aikatawa domin a ya dandana masu wasu daga cikin abunda suka aikata koda zasu dawo.” (30:41)

Sai Allah madaukaki ya bayyanawa mutum cewa ba'a halicce su ba da samar dasu cikin wannan duniya domin wasa ba, kuma ba'a kyale su haka ba kara zube, Allah madaukaki yace:

“shin kuna tsammani mun halicce ku ne kawai domin wasa kuma ku ba masu dawowa bane zuwa gare mu (115) tsarki da daukaka ya tabbata ga Allah sarki na gaskiya; babu abun bauta da gaskiya sai shi; ubangijin al'arshi me girma (116) (23:115-116)

Ya kuma bayyana cewa hikimar halitta da samar da mutane cikin wannan duniya al'umma bayan al'umma shine domin su bauta ma Allah shi kadai kuma kada su hada wani dashi cikin bauta, shi mawadaci daga bautan su tsarki ya tabbata a gareshi sai dai domin ya masu jarabawa ya gani wanenen zai kyautata aiki, Allah madaukaki yace:

“kuma ban halicci mutum da aljani ba face domin su bauta mani (56) bana bukatar arziki daga garesu kuma bana bukatar su ciyar dani (57) lallai Allah shine me yawan azurtawa ma'abocin karfi me cikakken karfi (58)(51:56-58)

Kamar kuma yadda madaukaki ya bayyana cajin na gwargwado su wanda gangan jikin bazai iya rayuwa ba sai dashi da fadin sa cewa:

“yaku wanda sukayi imani kuci daga abubuwa masu dadin da muka azurta ku dasu kuma ku godema Allah idan kun kasance shi kadai kuke bautatamawa (172)(2:172)

Ya bayyana caji na daidai gwargwado wanda bazasu iya rayuwa ba face dashi, bazasu samu sukuni ba batare da imani ba kuma bazasu samu hutu b aba tare da bautan mahaliccin ta ba, kuma bazasu tabbata ba batare da aiwatar da shari'ar sa ba, Allah madaukaki yace:

“wanda sukayi imani kuma zukatansu suka samu natsuwa da ambaton Allah; hakika da ambaton Allah ne zukata suke samun natsuwa (28)(13:28)

Domin mutum ya tabbatar da bauta ga Allah shi kadai an aiko masa da manzanni domin yayi koyi dasu kuma aka saukar masu da littattafai (shari'a) domin su shiryu da ita ya kuma kasance masu fitila me haskaka masu hanyar su, sai ta shiryar dasu zuwa ga alheri da kuma tsawatar dasu daga sharri da tsara masu al'amuran rayuwan su, ta yadda zasuyi amfani da gangan jiin su da rayukan su domin abunda aka halicce su domin sa, Allah madaukaki yace:

“mutane sun kasance al'umma daya; sai Allah ya aiko da manzanni masu bishara da gargadi ya kuma saukar masu da littattafai domin suyi hukunci tsakanin mutane cikin abunda suka samu sabani a cikin sa; kuma basu samu sabani ba game dashi sai ga wanda aka basu bayan hujjoji bayyanannu sunzo musu, sai Allah ya shiryar da wadanda sukai imani acikin abinda sukayi sabani da izininshi, lallai Allah yana shiryar da wanda yaso zuwa ga hanya madaidaiciya. (2:213)

Ya kasance na karshen su shine Muhammad s.a.w wanda Allah ya cika manzannin sa dashi ha kuma cika addinin sa dashi, ya kuma zo da addini wanda ya kunshi da tattara shari'a (dokoki) na Allah ga duniya baki daya wacce ta dace da ko wani zamani da lokaci, tana tsara rayuwan mutum da kuma basu farin ciki duniya da lahira, duk wanda yayi riko dashi ya samu farin ciki wanda kuma ya barta ya tabe, Allah madaukaki yace:

“lallai wannan alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga hanya me karko kuma yana yima muminai bishara wanda suka aikata ayyuka na kwarai cewa suna da lada me girma (9) wanda kuma basuyi imani ba da lahira mun tanadar masu da azaba me radadi (10) kuma mutum yana yima kansa addu'a na sharri kamar irin addu'ar da yakeyi ma kansa na alheri; kuma hakika mutum ya kasance me yawan gaggawa (11)(17:9-11)

(wannan kenan a fuskar game gari ga wanda yake shiryar dasu da kuma abunda da yake shiryar dasu zuwa gashi, sai shiryarwan ya kunshi mutane da al'ummomi marasa adadi na zamani ko kuma wuri kuma ya kunshi abunda da yake shiryar dasu zuwa gareshi dukkanin manhaji da hanya, da dukkanin alheri wanda suke mutum ke shiryuwa gareshi cikin dukkanin zamani da wuri.[1] Yana shiryar wa zuwa ga hanya me karko cikin duniyan me duhu da burace burace, da akida bayyananne me fadi wanda babu duhu a cikin sa, wanda take yantar da zukata daga nauyi na dimuwa da kararyaki, da kuma inganta batirin mutum na kwarai domin aiki da gini, da kuma kulla alaka tsakanin dokoki na duniya na dabi'a da fidirar mutum ta hanya me tsari da kamala.

Kuma yana shiryarwa zuwa ga hanya me karko cikin kulla alaka tsakanin zahirin mutum da badinin sa, da kuma burin sa da dabi'un sa, da akidar sa da aikin sa, kenan dukknain su suna hukunci ne zuwa ga kololuwan igiya wanda bata katsewa da kuma kai mutum zuwa ga kololuwan wuri tabbatacce akan doron kasa, kenan aiki ibada ne a duk lokacin da mutum ya nufi Allah dashi, koda kuwa aikin na jin dadi ne na rayuwa.

Kuma yana shiryar wa zuwa ga hanya ne karko cikin duniyar bauta ta hanyar kwatantawa tsakanin ayyuka da kuma iko, bata daurama rai aikin da bazata iyaba har ta kosa wurin sauke wannan nauyi. Kuma bata yin sakaci da rangwame har reai ta sangarce. Kuma bata wuce buri da daidaito da iyaka na abunda zai yiwu.

Kuma yan ashiryarwa zuwa ga hanya me karko cikin alakar mutane a tsakanin su: daidaikun su da kungiyoyin su, hukumomi da mutane, da kasashe da jinsuna, sannan kuma yana gina wannan alakar ne akan ginshiki me karfi kuma tabbatacce wanda baya tasirantuwa da ra'ayi ko kuma son rai kuma baya karkata tare da soyayya da kiyayya kuma maslaha bata canzata ko kuma buri. Ginshiki wanda masani kuma me bada labari akan halittansa ya gina, shine mafi snai ga abunda ya halitta, kuma mafi sani ga abunda ya dace dasu cikin dukkanin kasa da al'umma, sai ya shiryar dasu zuwa ga hanya me karko cikin tsari na mulki da tsari na dukiya da tsari na zamantakewa da kuma tsari na mu'ama tsakanin kasa da kasa na zamani cikin duniyan mutum.

Kuma yana shiryarwa zuwa ga hanya me karko wurin bayyanar da akida me kyau, sai ta sanar da mutane mahaliccin su abun bauta na gaskiya, kuma ta sanar da mutane addini na asali, kuma alkur'ani me girma yana yima muminai bishara da lada me girma wanda shine aljanna sakamakon imanin su, da kuma yima kafirai gargadi game da azabar Allah madaukaki.

“lallai wannan alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga hanya me karko kuma yana yima muminai bishara wanda suka aikata ayyuka na kwarai cewa suna da lada me girma (9) wanda kuma basuyi imani ba da lahira mun tanadar masu da azaba me radadi (10)(17:9-10)

Wannan ayar itace ka'idar sa ta asali cikin aiki da sakamako. Akan imani da kuma aiki na kwarai ne aka ginata. Babu imani ba tare da aiki ba, kuma babu aiki ba tare da imani ba. na farkon yankakke ne be samu kamala ba, na biyun kuma bashi da ginshi da asali. Dasu biyun ne rayuwa tane tafiya akan hanya me karko.. da kuma su biyun ne tare shiriya yake tabbatuwa da wannan alkur'ani.

Wanda kuma basu shiryu ba da wannan alkur'ani, suna masu masu bin son zuciya da sha'awar mutum. Mutum me gaggawa jahili da abunda zai amfane shi da cutar dashi, wanda baya tsara ayyukan sa koda kuwa sharri ne a bayan su a gareshi:

“kuma mutum yana yima kansa addu'a na sharri kamar irin addu'ar da yake yima kansa na alheri; kuma mutum ya kasance me gaggawa.” (17:11)

hakan ya faru ne saboda besan menene karshen abubuwa ba da sakamakon su. Kuma zai iya aikata aiki wanda sharri ne, kuma yayi gaggawa dashi akansa alhali be sani ba sai dai bazai iya yima kansa hukunci ba da iko da kansa.. to ina wannan yake ga shiriyan alkur'ani tabbatacce me shiryarwa a tsanake?)

Wannan itace shari'a ta musulunci wacce ta tabbatar da kunsanta ga komai da zamanta ta duniya baki daya da dacewan ta da kum aikon ta akan warware dukkanin wani matsala na mutum masu adalci wanda suke adalci wanda cikin wanda ba musulmai ba marasa addini, gaskiya itace abunda makiya suka tabbatar dashi yadda suka fadi da bakunan su gaskiyar da bazasu iya boye ta ba, zamu ambaci maganar su domin ya zama hujja akan mutanen su watakila zukatansu ya rabu da makauniyar biyayya sais u gane gaskiya wacce ta boye masu game da wannan shari'a me sauki yadda zukatan su zai samu natsuwa, (William Montogmery Watt) yace[2]:

“lallai izina na alkur'ani wanda yake hade da larabawa bazai yiwu a kore cewa ba ma'aboci ne na dabi'ar duniya, kuma wannan sako na musulunci wanda farkon say a tunkari mutanen makkaci cikin birni wacce ta kasance tana daukan iri ga duniya, ko kuma ta jasance tun farkon ta ko kuma abunda ta kunsa a farkon al'amari me nisa ne na duniya.”

Kuma yana cewa: lallai alkur'ani ya rabauto da samun karbuwa me fadi ba tare da duba zuwa ga yaren sa; domin yan akunshe ne al'amuran mutum.

Ya kuma kara cewa: hakika musulunci da kansa ya jadda da aiki cewa addini ne me cin gashin kansa daga sauran addininai tsofaffi (yahudanci da kiristanci), muna fadi akan gaskiya: lallai ya kasance ya samu rinjaye akansu ko kuma ya samu nasara akansu, ko kuma yafi su daukaka!

Shari'ar musulunta ta banbanta da banbanci a bayyane akan sauran nau'uka na dokoki; dokoki ne me cin gashin kansa, lallai shari'ar musulunci zance ne wanda ya kunshi umurnin na Allah wanda suke tsara rayuwan ko wani musulmi ta dukkanin bangarorinta.

Wannan shine addinin mu, kuma wannan itace shari'ar mu wanda muke fatan mutune baki daya su zabeta domin ba'a saukar masu da it aba face don rahama a garesu, zamuce ga dukkanin wanda ya karanta wannan littafi daga cikin wand aba musulmi ba fadin Allah madaukaki:

“idan kuma kuka juya baya zai canza wasu mutane wanda baku ba sa'annan kuma bazasu zama irin ku ba” (47:38)

 

DAKTA ABD ΑR-RAHMAN DAN ABD ΑL-KARIM AL-SHEHA

 

 

 

BABI NA FARKO

Ma'anar Kalmar shari'a cikin yaren larabci.

 

  • Yaudaran yan jarida na canza Kalmar shari'a.
  • Manufa na yin dokoki.
  • Doka na dindin din da kuma kirkiro dokoki.
  1. Gazawa na dokokin da mutane suka kirkira game da hukuncin akan ayyukan barna masu girma.
  2. Muhimmancin samun shari'ar Allah.
  3. Doka na mutane da doka ta daji.
  • Dimuwa na dokokin mutane da kuma rashin dawwamanta.
  1. Kisa na jin kai.
  2. Siyar da kayan miyagun kayan maye.
  3. Azabar kisa.
  • Shiririta na ukubar cikin doka na mutane.
  1. Akidar mika wuyan mutum cikin shari'u na mutane.
  • Laifukan da aka wallafa su daga cikin dokokin dan Adam

 

 

BABI NA FARKO

MA'ANAR KALMAR SHARI'A CIKIN YAREN LARABCI

 

Kalmar shari'a cikin harshen larabci tana nufin doka ko hanya ko manhaji, shari'a ta dagi itace doka na wanzuwan me karfi, dokoki kuma na coci dokoki ne wanda aka tsara su domin coci da yanayin ta, shari'a ta Humurabi shari'a ce wacce sarkin Humurabi na daular Babila tsohuwa ya kafa, shari'a na fir'auna itace shari'ar da misirawa tsofaffi suka kafa domin tsara al'amuran kasar su, amma aka jingina Kalmar shari'a da addinin yahudanci ko kuma kiristanci ko muslunci anan ana nufi da ita cewa abunda Allah ya shar'anta ya kuma wajabtama mutane na akidu da hukunce hukunce da dokoki wanda suke tsara al'amuran duniyan su da kuma nuna masu hanyar alheri da rabauta a lahiran su, tare da sanin cewa anan wurin abunda muke nufi da Kalmar shari'a na yahudanci ko kiristanci shine shari'a na asali wanda Allah madaukaki ya saukar ga annabin sa Musa da annabi Isa amincin Allah ya kara tabbata agare su gabanin mutanensu su canza su, shari'a ce wacce aka shafeta da shari'ar musulunci wacce Allah ya kiyaye ta daga dukkanin wani canzawa ko kuma gyara, Allah madaukaki yace:

“kuma mun saukar maka da littafi da gaskiya me gasgatawa ga abunda ke gabanin sa na littafi kuma me rinjaye ne akansa to kayi hukunci a tsakanin su da abunda Allah ya saukar kuma kada kabi son zuciyar su game da abunda yazo maka na gaskiya; ko wanne a cikin ku mun sanya masa shari'a da manhaji; kuma da Allah yaso da ya sanya ku kun zama al'umma daya sai dai domin ya jarabaku cikin abunda ya baku; to kuyi rigegeniya ga alheri; ga Allah makomar ku take baki daya sai ya baku labari game da abunda kuke samun sabani akai (48)” (5:48)

 

YAUDARA DA CANZA MA'ANAR KALMAR SHARI'A WANDA YAN JARIDA SUKEYI

 

Kalmar”shari'a”idan aka fassara su zuwa ga wasu yaruka za'a fassara ta ne da ma'anar”doka”wannan shine asali kuma gaskiya, sai dai wasu kafafen yada labarai na kasashen yamma masu manufa suna amfani da dukkanin damar su wurin nema daga musulunci da shari'ar sa me sauki kokarin bata shi da batar da hankulan mutane da nisantar dasu daga gareshi ta hanyar bata manufa na shari'ar daga Kalmar shari'ar musulunci, a duk lokacin da sukaci karo da wani wuri wanda yake da alaka da shari'ar musulunci basa fassara shi kamar yadda yake a harshen larabci”shari'a”da ma'anar sa na dai-dai a yaren su wanda yake nufin”doka", suna fassara shi ne kamar yadda ake furtashi da yaren larabci”shari'a", kuma suna rubuta shi ta hanyar”rubuta na sauti”sais u rubuta shi da haruffa na turanci kuma su furta shi da yare na daban kamar yadda ake furtashi da yaren larabci”shari'a"!!

SHARI'A = LAW

SHARI'A LAW = LAW LAW

Dalilin haka kuwa na rashin fassara shi da doka na musulunci domin kasancewar Kalmar doka tana nufin abu ne me tsari wanda yake tsara halayen mutane, sai kafafen yada labarai batattu suyi kokarin rabawa tsakanin Kalmar doka da kuma Kalmar shari'a da kuma rabe dukkanin wani mahada a tsakanin su, domin kokarin sun a haifar da wani taswiri a kwakwalwar me sauraro game da Kalmar shari'a da cewa al'adace na me muni da rashin imani bawai me tsara rayuwan mutum bace, amma ta dayan bangaren kuma idan zasu fassara shari'ar Musa sais u fassara ta da dokan Musa, haka idan zasu fassara shari'u na coci sais u fassara ta da dokoki na coci haka dai!! Kamar yadda a lokacin aikin ta na aikin jarida na yin shiri ko kuma bahasi akan shari'ar musulunci sai ta kashe kamaranta akan dukkanin musulman da suke cikin kasashe na duniya wanda adadin su yakai kusan biliyan biyu na musulmai sai gta tafi da dukkanin kamaranta zuwa ga tafiya me nisa tana tsallake tashoshi da garuruwa har sai ta isa zuwa ga dutsen Kandahar wanda wata matalauciyan kabila take rayuwa wanda yawan su be wuce wani adadi takaidacce ba, bata da abunda zataci sannan kuma basu samu dama ba na karatu kai hatta ruwan da zasu sha me kyau basu samu daman samun hakan ba balantana a suranta wahalhalun rayuwan su kuma duniya sun zaburar akan taimaka masu, tana tashi ne domin zaburar da duniya game da taimakon su da kuma sawwara su a matsayin sune wakilai na musulunci sannan kuma dukkanin ayyukan su musulunci ne a karon kansa!! Duk a wannan lokaci dai kuma take sawwara kiristoci da cewa su al'umma ce wayayyu masu ilimi kololuwa da ci gaba na ilimi cikin kokarinta na kirkiran sura cikin hankulan duniya na koma bayan musulunci, sannan babban abunda ya kawo masu wannan koma bayan shine dalilin binsu da sukeyi na karantarwan addinin musulunci, sannan kuma dalilin ci gaban kiristoci da wayewar su yana komawa ne dalilin binsu da sukeyi ma karantarwan addinin kiristanci!! Hakika kafafen yada labarai sun manta da wani abu cewa wannan fa wacce take aiki na kwatantawa tsakanin kabilun musulunci wanda suke rayuwa akan tsaunin Kandahar da kuma ko wace kungiya me kabilanci na kiristanci cewa ya wajaba a kwatanta da kabilar Gajar na kiristanci wacce ta cika dukkanin kasashe na turawa!!! Yadda dayawa cikin kasashen turawa suke wahala domin tsugunar da wannan kabila ta gajar cikin mahalli na natsuwa saboda cewa wannan kabilar taki zama a wuri daya domin sun zabi rayuwa na zango zango daga nan wuri zuwa wani wuri na daban.

Hakika wannan kabila na gajar tayi fama kiyayya na bangaranci me tsanani da kuma toye masu dayawa cikin hakkokin su cikin kasashen su, dukkan haka fa sun manta dashi sannan kuma sun kashe hasken kamaransu akan sa domin boye hakan ga duniya wanda da ace wannan kabilar ta gajar tana bin addinin musulunci ne da kamaransu ta dauke su da sawwara su da cewa hakan shine musulunci a karon kansa kuma karantarwan shari'ar musulunci itace ta sanya rayuwan su ya zama na yada zango daga wannan wuri zuwa wani wuri!!! Kamar kuma yadda kafafen yada labarai suka manta har wayau ta hasko mana malamaun musulunci wanda suke rayuwa a yau a kasashen turai ne ko kuma amerika ko austireliya ko asiya ko kuma afirka, wanda suke jagorantan duniya cikin dayawa na bangarorin ilimi ko tattalin arziki ko siyasa ballantana ace maluman musulmai na zamanin can wanda suka haskaka duniya da ilimin su a zamanin da ba'asan turai ba watan zamanin tsakiya ko kuma kuma zamanin duhu, a lokacin da turai ta kasance koma baya cikin dukkanin bangarorin ilimi da wayewa tun shekara 400 miladiyya har zuwa kusan shekara na 1400 miladiyya a lokacin da coci ta kasance tana fada da dukkanin abunda yake da alaka da ilimi ko kuma maluma, har wani cikin maluman tarihi na turawa me suna Edward Jeebon yafadi wata maganar sa shahararriya game da wannan zamani:

“shekara dubi na cin nasarar hamajiyya da kuma addini. [3]

 

MANUFA NAYIN DOKOKI

 

Lallai manufa daya dilo nayin dokoki da kuma rubuta kundun tsarin mulki shine tsara halin mutane shin ta bangaren zamantakewa ne ko kuma tattalin arziki ne ko kuma siyasa..., bayan nassi akan hakkokin da wajibobi na kowani mutum cikin al'umma na akaron kansa da kuma kasancewar sa daya cikin al'umma, da kuma nassi akan yanci mutum da kuma iyakokin sa, yancin ko wani mutum ba kai tsaye take ba babu iyaka a'a tana tsayawa ne akan yancin sauran mutane, watan ma'ana kada yake ta yancin wasu da yancin sa ko kuma ya zama ya ketara iyaka da barna, da haka ne ya zama dukkanin doka yana nassanta bangarori na ladabtarwa da kuma azabtarwa ga dukkanin wanda yak eta hakkin wasu.

Akan wannan abunda ya gabata lallai banbancin na tsira ko kuma rashin nasara na ko wani doka yana ginuwa ne akan ikonsa na tabbatar da burin da aka ambata abaya, da kuma samar da ukuba wacce ta kunshi tabbatar dashi da kuma yin ukuba ga duk wanda ya saba mashi, da kuma lura da cewa ukuba baya wajaba ace ta wuce iyaka inda zata cucar da me kuskure a'a ya wajaba ya zama tana da hadafi ne na tabbatar da abubuwa masu zuwa Kaman haka:

  1. GYARAN KUSKURE: kamar yadda yake cikin ukubar biyan kayan da aka lalata ta hanyar biyan kudi na gwargwadon abunda aka lalata ko kuma tara na kudi ga mutumin da aka cutar.
  2. GINA ME LAIFI: gina shi da kuma hurar dashi ta yadda zai zama mutum tsayayye wanda al'umma zasuyi marhaba dashi.
  3. TSAWATARWA ga mai laifi: da kuma hana aikata irin wannan laifi nan gaba.
  4. TSAWATAR WA GA MUTANE: saboda kada suyi koyi da mai laifi cikin aikata laifin irin nashi suma, bayan sunga irin ukubar da aka masa.

 

DOKA NA DINDIN DIN DA KUMA KIRKIRO DOKOKI

 

GAZAWA NA DOKOKIN DA MUTANE SUKA KIRKIRA GAME DA HUKUNCIN AKAN AYYUKAN BARNA MASU GIRMA:

A cikin wannan duniya tamu tayau muna ganin dayawa daga cikin kungiyoyi na dokoki da masana'antu na shari'u da kwalejoji na hakkoki da masalisun dokoki na kasashe na ciki da waje, bugu da kari kuma ga rundunoni na yan mutanen dokoki wanda ya kunshi lauyoyi da alkalai da masana kundin tsarin mulki da shuwagabanni na kasashe da sauran su, bugu da kari kuma da rundunoni wanda suka kunshi yan sanda da kuma miliyoyi na fursinoni da wanda ake tsare dasu, kmar yadda kuma muke ganin dayawa na kokarin kirkiran doka wanda zai tabbatar da manufar da muka fadi a baya, shin sun iya kirkiro wannan doka wanda wanda yake basu daman tabbatar da ganin cewa an tsawatar da mutane daga keta hakkokin wasu?!! Ko kuma dai har yanzu bamu gushe ba muna rayuwa cikin wannan duniya namu cikin manyan laifuka cikin kasashe da dama?!! Ko kuma ta wani fuskar muce shin wannan dokoki sunyi nasara wurin samar da tsaro ga duniya kuma shin yayi nasara hukunci na alkalanci akan manyan laifuka da matsaloli wand muke ganin su ayau kuma suna karuwa a kullum?!!! Idan haka ne ashe duniya tana da bukata na kawo wani doka wanda zai tabbatar da da hakan sai dai kuma ta yaya?

 

MUHIMMANCIN SAMUN SHARI'A NA ALLAH MADAUKAKI:

A cikin zamunan baya can da dadewa shin akwai kungiyoyi na dokoki ko kuma alkalanci ko kuma me sa ido wurin samar da doka da kuma aiki dashi wanda zai tsarama mutane al'amuran su?!! Saboda haka kodai Allah madaukaki ya saukar da doka daga gareshi me tsararriya da kuma tsara al'amuran mutum wanda baya mukatar wasu masu kirkiro doka su kawatashi ko kuma yi masa gyara, ko kuma doka na dawa yayi aiki me karfi yaci mara karfi!!

Ya kasance daga cikin adalcin sa da rahamar sag a bayin sa ya saukar masu da shari'a (dokoki), wacce bata canzawa, dawwamanta da adalcinta baya canzawa da shudewan zamani ko kuma wuri, babban laifi a cikinta babban laifi ne wanda babu yadda za'ayi har Abadan ya koma abu me kyau, sannan gaskiya a cikinta gaskiya ne bazai taba canzawa ba zuwa barna, dukkanin su daya suke a gaban adalcinta, amma hukunce hukuncen ta suna sabunta lokaci bayan lokaci ta hanyar manzanni wanda Allah yake aiko su domin su shiryar da mutane su kuma kawo masu shari'a wacce take tsara masu al'amuran su na rayuwa, bayan yahudawa sun manta da canza hukunce hukuncen na shari'ar su, sai Allah ya aiko da annabi Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi domin ya sabunta hukunce hukunce na shari'ar Allah, baya kiristoci sun manta da kuma canza hukunce hukunce na shari'ar su, sai Allah ya rufe shari'ar sa da manzancin Muhammad s.a.w, sai ya aiko shi da shari'a da hukunce hukunce masu kyau wanda suka dace da dukkanin zamani da wuri basa canzawa ko jujjuyawa da shudewan zamani, shari'a ce wacce take cikamako na shari'u, Allah madaukaki yace:

“sa'annan kuma muka sanya ka akan shari'a na umurni saboda haka ka bita kuma kada kabi son zuciya na wanda basa sani” (45:18)

Wannan zai bayyana maka a bayyane cikin kwatantawa ukuba na cikin shari'a da abunta take gadarwa, ya sanya tsanani na ukuba gwargwadon girman laifi da kuma hatsarinta ga al'umma, shari'a bata karkata ko kuma yin hidima ga son zuciya da daga kafa ko munafunci, tana daidaito tsakanin wanda suka cancanci ukuba kuma bata dauke ukuba akan wani babban mutum me alfarma domin matsayin sa cikin mutane ko kuma alfarman sa ko kuma mulkin sa, sannan kuma bata dauke ukuba akan me kudi domin yawan kudin sa, wannan a bayyane yake cikin fadin manzon Allah s.a.w:

“lallai yana daga cikin abunda ya halakar da mutane da suke gabanin ku shine, sun kasance idan wani babban mutum a cikin su yayi sata sais u kyale shi, amma idan kuma me raunin cikin su yayi sata sai su yanke masa hukunci, ina rantsuwa da Allah da ace Fatima diyar Muhammad [manzon Allah] zatayi sata da sai na yanke mata hannu” (buhari ne ya rawaito shi)

 

DOKOKIN DA MUTANE SUKA KIRKIRA DA DOKOKI NA DAWA:

A hakikanin gaskiya dayawa daga cikin dokoki na dan Adam a wannan zamani namu wani irin fuska ne na dokokin dawa saboda wasu zababbu na cikin majalisar dokoki ko kuma wasu daga cikin masu kirkiran doka mutane ba gurbatattu masu buri dason shugabanci ko kum aduniya sais u kirkiri doka wanda a zahirinta gyara ce amma kuma a badininta kawai tana tabbatar masu da maslahar su ce da kuma yin hidima ga burin su ta hanyar yin amfani da arzikin talakawa!! Saboda haka ne kuma Allah madaukaki me ni'ima a garemu ya saukar mana da doka me adalci da hikima wanda baya banbancewa tsakanin me mulki da wanda ake mulka ko kuma me kudi da talaka ko farin fata da bakin fata ko kuma wani aji akan wasu aji, doka ne me adalci wanda ya nisanta daga son zuciya ko zalumci ko buri!! Allah madaukaki yace:

“yanzu shin hukunci na jahilci suke so da kauna; kuma wanene yafi Allah kyawu na hukunci ga mutane masu sakankancewa” (5:50)

 

RASHIN DACEWAR MUTUM WURIN KIRKIRAN DOKOKI KANANA BA TARE DA KOMAWA ZUWA GA DOKAN ALLAH:

Lallai mutum tun fil azal sun banbanta, daga cikin su akwai me kabilanci sannan akwai jarumi sannan akwai mara hankali sannan akwai mujirimi sannan akwai dan fashi kuma akwai me tausayi kuma akwai mugu, daga cikin su akwai balarabe da dan china da dan indiya sannan akwai baki kuma akwai farin fata, kuma daga cikin su akwai dan jari hujja sannan kuma akwai dan mazan jiya da dai sauran su. Saboda wannan banbancin ne ya zama dalili babba na samun rashin tabbatar ra'ayi na dan Adam da kuma iyakanci hakkoki da wajibobi da kuma iyakance abubuwa masu kyau daga aikin barna, a zamanin Hitila misali an kawo dokoki wanda yake banbance tsakani gwargwadon dangantakan mutum ko kuma banbancin kalan fata, yadda suke daukan cewa jinsin da ake kira da suna Ariyawa su sukafi cancantar zama masu mulkin duniya baki dayan sa, sannan kuma shi mutum dan jinsin Ariyawa misali a ganin Hilta shine fari me idanu biyu masu kalan fatsi fatsi kuma dogo, wanda hakan yaba mutanen almaniyawa a farkon shekaran 1933 miladi daman yin aiki na mugunta akan mutane dayawa wanda ba jinsun ba na Ariyawa, kamar bakyaken mutane yan gudun hijira wanda yawan su yakai dubu 30 a almaniya a wannan lokaci, da nakasassu na almaniya ko kuma wanda aka Haifa kurma ko makaho ko mahaukaci dukda cewa suma yan almaniya ne, sai dai wanann nakasa nasu ko kuma rashin lafiyar su ya haramta masu a dauke su a matsayin jinsin ariyawa masu tsarki.

A kasar Amerika kuma misali anyi kisan kare dangi ga yan indiya da kuma kwace gonakin su, yadda aka kashe mutum miliyan dari na indiyawa, kuma hakika Hilta ya dauki darasi daga wannan kisa na kare dangi wurin yima yahudawa kisan kare dangi shima wanda kuma hakika an fadi hakan cikin bugun farko na littafi me suna”KAFAHI”[4].

Kuma sama da jihohi 30 na amerika sun hana auren wasu wanda ba asalin turawa ba na mutanen bakin fata ko china ko kuma almaniya ko indiya ko malayo ko magul. Sannan an kirkiro daywa daga dokoki na masu nuna banbanci wanda suke fifita da bayar da dama ga wasu bangare na mutune wanda sune farare na Anjilo Saskon daga protastanant. Sannan kuma abun Ambato ne cewa dukkanin shuwagabannin amerika sun fito ne daga cikin wannan bangare banda John kenedy da Barak ubama.  

Su kuma bakin fata anyi dokoki na kabilanci akan su wanda akafi sani da suna dokoki na Jim Crow[5].

 

TAFKA DA WARWARA NA DOKOKIN DA MUTANE SUKA KIRKIRA DA KUMA RASHIN DAWWAMAR TA

 

Lallai duk me duba cikin tarihi na dokoki da kuma rubutun kundun tsarin mulki zaiga cewa dokoki ne wanda mutane suka kirkira wacce take canzawa kullum yadda zakaga cewa doka baya tabbata zuwa wani dogon lokaci na zamani, abunda yake babban laifi ne a wannan lokaci ya zama cikin ayyuka masu kyau ko kuma hakki cikin wnai zamani na daban ko kuma akasin haka, misali kayan nunkaya na mace a amerika a shekarar 1850 miladi da kum shekarar 1920 ya kasance mayafi dogo wanda zai rufe dukkanin jikinta baki daya, kuma da mace zata ki juya baya irin yadda matan amerika masu nunkaya na wannan zamani namu suke juyawa akan haka da ankamata kuma an ladabtar da ita, haka kuma kamar yadda koda yake canzawa da canzawar zamani haka kuma yake canzawa da canzawan wuri, kamar misali a cikin kasashen hadin kan turawa dokar ko wace kasa ta banbanta da na wata kasar a cikin kasashen kawancen, kai hatta a cikin kasa daya misali kasar amerika dokan wata jiha tana banbanta data wata jihar, kenan tana aiki ne ga son zuciya da burin yan siyasa wanda suke wajabta akan mutane, daga cikin misali akan haka:-

 

KISAN MARA LAFIYA DOMIN SAUKAKA MASA[6]:

Shine kisa ta hanyar taimakon wani mutum na daman, kuma ya kasu zuwa gida uku:-

  1. KISAN MARA LAFIYA WANDA CIWO YA CINYE DOMIN A SAUKAKA MASA: anayin hakan ne da yardan mara lafiyan, al'amari na doka a wasu kasashe na turawa da kuma wasu hijohi cikin amerika.
  2. KISAN MARA LAFIYA WANDA CIWO YA CINYE DOMIN SAUKAKA MASA: wannan anayin shi ne ba tare da yardan mara lafiyar ba, misalin irin wannan kisa ga yara cikin wani yanayi na musamman a kasar Holand karkashin tsari na Jironijin[7].
  3. KISA NA TILAS: wannan anayin sa ne ba tare da son mara lafiya ba.

A takaicen al'amari samun wanda suke goyon baya da wanda basa goyon bayan haka wanda ko wannan ne yana da hujjojin sa da kuma dalilan sa wanda yake ganin ingancin su, wasu kasashen kuwa tana sanya hakan ya zama doka sabanin wasu kasashen da suke ganin hakan yana cikin manyan laifuka.

Kuma an rubuta irin wannan yanayi na kisa tare da niyya kamar misalin halin Dakta Nigal Cox[8] wanda yayi amfani dayin allura ga mara lafiyar sa Lailayan Buwis da allurer chloride potassium na guba domin ya tsayar da zuciyarta daga aiki, kuma ya kafa hujja ne a lokacin kare kansa da cewa yana son saukakawa ne a gareta na azabar radadin da take fama dashi, kuma kotun tayi masa hukunci da kulleshi a gidan yari na shekara da kuma hanashi aiki, bayan shekara daya sai ya samu lasisi na ci gaba da aikin likitancin sa kamar wani abu be taba faruwa ba.

 

SIYAR DA MIYAGUN KAYA NA MAYE:

Akwai wasu kasashe cikin kasashen turawa wanda sukayi doka na siyarwa da kuma yin mu'amala da miyagun kayan maye da sharadi da kuma adadi na abunda aka yarda asha ko asiyar, sannan kuma a daya bangaren kuma wasu daga cikin kasashen turawa sun haramta siyarwa ko kuma mu'amala da miyagun kaya maye, abun mamaki shine daya daga cikin kasashe kuma ta yi dokan sayar da miyagun kayan maye amma gay an kasanta kawai, yadda suka haramta hakan ga matafiya wanda sukazo bude ido da makamantan su yin mu'amala da miyagun kayan maye domin hana yawon kayan maye a cikin kasarta, wanda doka ne wanda dayawa na mutanen da suke siyar da kayan mayen sukayi fatali da ita suna masu fadin cewa hakan zai karya masu kasauwancin su da hanyan samun kudin su.

 

UKUBA TA KISA:

Akwai daga cikin kasashen turawa da wasu jihohi na kasar amerika wanda suka haramta ukuba na kisa, wanda a dayan bangaren kuma wasu kasashe na turawa da suwa jihohi na kasar maerika suke halasta hakan cikin dokokin su kuma suna aiki dashi!!

Kenan: ina illa dawwamamme wanda zamu iya yin kiyasi akan sa da kuma sani daga gareshi cewa menene babban laifi sannan kuma menene makaruhi?! Sannan kuma menene daidai kuma menene barna?!

Atakaice: abunda akayi ittifaki akansa a wurin masu hankali shine ita gaskiya day ace kuma dawwamammiya ce bata canzawa da canzawan zamani ko kuma wuri, haka kuma halaye na gari na kwarai da kuma hayalen banza da laifuka suma tabbatattu ne basa canzawa da canzawan zamani ko kuma wuri, kuma baya halatta har abadan ace aiki aikin nagari na koma aikin banza ko kuma aikin banza ya koma aiki na gari!!.

 

SHIRIRITAN UKUBA CIKIN DOKOKIN DA MUTANE SUKA KIRKIRE SU:

 

Cikin dubi zuwa ga wasu shari'u da ukuba wanda aka kirkire su a tsawon zamani kamar a lokacin mulkin fir'auna ko kuma china ko indiya ko almaniya ko romaniya tsofaffi ko kuma shari'u na kabilun afirka da bakake zamuga cewa shari'u ne ko kuma ukuba na shiririta, hakika wannan ukubar sun kasance masu azabtarwa ne ga me laifi na rashin tsari, kamar ukuba na kisa akan karamin abu da kuma hanyar da akebi wurin yin azabar wanda aka masa hukunci da kisa, wani lokaci a kashe shi ta hanyar yanke masa kai da abun yanke kai kamar misali abunda ya faru a lokacin mulkin firnasa louis na shida[9] a shekara ta 1793 miladi, wani lokaci kuma a yanke masa kai da adda sa'annan kuma a datsa gangan jikin su zuwa gida hudu kamar misalin abunda ya faru ga Thomas Armstrong[10] a shekara ta 1684 a kasar amerika, wani lokaci kuma a cire masa hanjin cikin sa da kuma yanke gabbansa da ransa sai kuma a cire zuciyar sa daga kirjin sa sai a yanke masa kai makar misali abunda ya faru ga Balthasar Gerard[11] a shekara ta 1584 a kasar holand, wani lokaci kuma a yankashi da wuka, wani lokaci kuma a gicciyeshi akan bishiya sai a kona shi da ransa kammar yadda yake a cikin kotuna na bincikie na kasar spaniya da Portugal da romaniya karkashin sa idon kasawasa, wani lokaci kuma a jefa shi ga zaki me jin yunwa a cikin filin wasan romaniya, wani lokaci kuma a sanya shi akan injin daka kai da ransa, wani lokaci kuma a sanya shi akan kujeran wutan lantarki kamar yadda akayima Lynda Lyon Block[12] a shekara ta 2002 a kasar amerika, a wani lokaci kuma a jefa shi cikin ruwa kamar yadda akayima masu taimakon juyin juya hali na faransa[13] a shekara ta 1793 a faransa, wani lokaci kuma a daura masa karfi me zafi akai ko kuma dutse me nauyi akan kirjin sa kamar yadda akayima Giles Corey[14] a shekara ta 1692 a amerika, wani lokaci kuma a jefa shi cikin mai me zafi kamar yadda akayima Richard Rice[15] a shekara ta 1531 a kasar amerika, wani lokaci kuma a sanya shi cikin dakin iska na guba, wani lokaci kuma a birne shi da ransa kamar yadda ya faru ga mazuna birni yan kasar china daga rundunan almaniyawa a wani mayanka me suna Nanakij a tsakiyan yakin duniya na biyu, wani lokaci kuma sassake jikin sa daga sama zuwa kasa da zarto na karfe[16], wani lokaci kuma a daureshi da igiya sannan a yankashi da dates kansa da wuka kamar yadda ya faru da Germier Branrich a shekara na 1817, wani lokaci kuma a daureshi akan turaku guda hudu ta yadda zai rabashi gida hudu kamar yadda ya faru ga Tobak Amaro ashekara na 1781 a beru a hannun masu mulkin mallaka na spaniya[17], wani lokaci kuma a fasa cikin mutum da ransa kamar yadda ya faru ga Juzeaf Marchand[18] a shekara na 1835 a garin pantanamo, wani lokaci kuma a tsoke shi, wani lokaci kuma a harbeshi da harsashi, wani lokaci kuma a tilasta masa kwanciya rubda ciki ya bude bakinsa sai yasa kan kaifin takobi abakin sa sai yani mutum da taka kansa yadda takobin nan zai yanke masa baki da kansa sai yam utu wannan itace hanya wacce tafi a wurin mutanen Naziyya na kasar amerika wurin kashe bakake[19], da sauransu na hanyoyin daban na rashin imani da shiririta wanda yasha banban wurin azabtarwa mabiya da hukuncin kisa a lokacin zartar da wannan hukunci a garesu kamar yadda dokokin su ya tanada!!! Saboda haka lallai shari'ar Allah rahama ce, wanda baya fadi wani ukuba mara amfani, kuma bai bar mana wata kafa ba kara bita domin son zuciya ko kuma wasan masu kirkiran dokoki na shiririta. Hatta tare da dabbobi hakika shari'ar musulunci ya fadi cewa a rika yin rahama da tausayi ga dabbobi hatta a lokacin yanka su domin cinsu, hakika manzon Allah s.a.w yace:

“lallai Allah ya wajabta kyautata akan komai, idan zakuyi kisa to ku kyautata kisan, sannan idan kuma zaku yanka dabbobi ku kyautata yankan, dayanku ya wasa wukarsa domin ya hutar da dabbar sa” (muslim ne ya rawaito shi)

 

AQIDAR YANKA DAN ADAM CIKIN SHARI'UN DAN ADAM

 

Mutanen amerika ta tsakiya sunyi aqidar yankan mutum[20] a masarauta ta Ibriradhuriyya Aztik[21] wanda mulkinsa ya dauretun daga karni na sha hudu na miladiyya har zuwa karni na sha shida miladi, sunyi mulki a jihar da ake kira ayau kasar Mexico, yadda bokaye suke halartar yankan mutane sais u sanya su akan dutse babbasai boka ya tashi ya tsaka cikin wannan mutumin da za'a yanka da ransa ya fito da zuciyar sa shi kuma yananan kwance yana kallon rana domin neman yardan allan Rana wanda ake kira huitzilopochtli[22]- Allah yayi mana tsari-, ko kuma dan neman yardan allan Ruwa wanda ake kira Tlaloc[23], ko kuma neman yardan allan Rana wanda ake kira Huehueteotl[24] ta hanyar hada wani biki na addini domin wannan alheri wanda zasu jefa mutanen da ransu cikin wuta kafin su mutu sai a fito dasu daga wutan a tsaga cikin su a cire zuciyar.

Daga cikin kayaryakin wannan masarauta na Imbiradhuriyya xewa lallai allar Xipe Totec[25] ya yanka fatansa domin ya baima dan adam abunda yakeso na zirra, saboda haka ne ya nema daga dan adam daya ya rika bashi fatar jikin sa a madadin wannan fata nashi, a dalilin haka ne bokaye suke tashi domin karrama wannan allan ta hanyar yanka fatar wanda za'a yanka cikin mutane sa'annan su sanya wannan fatar ta mutanen da suka yanka a jikin sun a tsawon kwanaki ashirin bayan wannan kwanaki sai su jefa fatar a wuta!!

A Afirka kuma misali akan irin wannan abu suna da yawa, kamar misali a bukin shekara na masarautan Dahumi[26] wanda aya ake kiranta da suna jamhuriyya ta Benin[27] a yanmacin Afrika, sun kasance suna zuwa fursinoni da bayan da aka kama agun yaki sais u yanka su amatsayin bangare dokokin wannan buki na shekara, kamar yadda a lokacin mutuwar sarki suke yanka dubbannin fursinoni, an yanka a cikin shekara ta 1727 miladiyya mutum 4000 a rana daya kawai!!.

A cikin al'adun china tsohuwa ya kasance suna birne bayi da ransu a lokacin da wani shugaba yam utu, a shekara ta 621 gabanin haihuwar annabi Isa sarki Moo[28] ya mutu wanda shine sarki na bangaren Keen[29], sai aka birne bayi (177) tare dashi da rayukan su.

A cikin mutanen Assalaafiyya, a cikin karni na goma sha biyu an yanka bayin da aka samo a wurin yaki da kuma gabatar dasu adomin neman kusanci ga allar mutanen aslaf[30] berun[31].

A kasar fabacin Asia a inda addinin Buzanci ya yadu munga hotuna a wannan zamani a kafar yanan gizo na matukar rashin imani, a ranar farko ta shekarar siniyya wasu daga cikin Buzawa suna zuwa da yan mata bayan sun nemi izini daga iyayen su, sais u wanke su da masu kwalliya da daure hannayen su daga baya sai suke su da wuka a wuyan su kamar yadda ake suke alade sai su sanya kwarya a karkashin wuyan nasu domin su tara jinin a ciki daka ya zube a kasa, daganan kuma sai su yayyanka gangan jikin su gunduwa gunduwa su raba naman su ga talakawa!!.

A cikin littafi me tsarki na kiristoci da yahudawa mungani a cikin littafin (safar) alkalai (11/29): (29 sai ra hin ubangiji ya koma zuwa ga Yaftah, sai ya wuce kasar Jil'ada da Manasaya da misfada jil'ada, daga cikinta sun gabata kamar yaran Ammun. 30 sai Yaftah yayi bakance ga ubangiji yace: << idan ka taimake ni akan yaran Ammun, 31 to idan na dawo lafiya daga wannan yaki na yaran Ammun, zan koma zuwa ga ubangiji konanne: farkon wanda ya fita daga cikin kofofin tsakanina da haduwa dasu>>. 32 sa'annan ya fita zuwa yakin yaran Ammaun, sai Allah bashi nasara akansu, 33 yayi kaca kaca dasu tun daga Aru'ir har zuwa Minnita kusan birane ashirin zuwa Abalil kurumi. Haka dai bani isra'ila suka mika wuya ga Ammunawa. 34 sa'annan ya Yaftahu ya koma gidan sa cikin Misfatim sai yarinyar sa dayake dashi guda daya ta fito, domin tarbansa da kida da guda. 35 a lokacin daya ganta sai ya yamutsa kayan sa da walwala yana cewa: << ya diyata, hakika kin batamun rai da tayarmun da hankali, domin kuwa nayima ubangiji bakance kuma babu hanyar yanje wannan bakance nawa>>. 36 sai yarinyar ta amsa mashi: << hakika kayi bakance ga ubangijin, saboda haka ka aiwatar da bakancenka kamar yadda kayi alkawari, kuma musamman ma ubangiji ya taimakeka akan makiyanka na yaran Ammun>>. 37 sai tace ga mahaifinta: << amma ka tabbatar mun da wannan abu nawa da nake nema: ka sauraramun na wata biyu nayi yawo a cikin su a tsakanin duwatsu naci budurci na tare da kawata >>. 38 sai yace mata << to jeki>>. Ya saurara mata na wata biyu ta kwashe wannan watanni biyu ita da kawarta a cikin duwatsu taci budurcinta. 39 sa'annan ta dawo a karshen watanni biyun zuwa ga mahaifinta sai ya konata ya mikata domin cika wannan bakance nashi, sai ta mutu tana budurwa.)

Munga cewa littafi me tsarki cikin labarin daya gabata ya rawaito kisan Yaftahu ga diyarsa ta hanyar konata da rant aba tare da wani laifi ba, kawai domin yayi bakance ga Allah cewa idan ya bashi nasara akan makiyar sa zai kona farkon wanda ya fito domin tarban sa daga cikin mutanen gidan sa bayan ya dawo, kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: (babu cika bakance na sabon Allah) muslim ne ya rawaito shi.

Wannan labari misali ne na wannan shari'u da akidu na shiririta wanda hankali me lafiya yake korewa, kuma babu wata kasa wacce ta tsira daga cikin irin wannan akidu na barna kamar akida na yanka mutane domin neman yardan allan da jinin mutum, duk wanda yakeson Karin bayani sai ya duba cikin tarihi na akidar yankan mutum cikin duniya zai gani da kansa yadda ta yadu a amerika da turai da Austireliya da afirka da asiya!!.

Hakika duniya yaga wannan zamani na al'ada ta'addanci me muni sannan kuma ya yaketa domin munin ta ya kuma sanya hukuncin sa mutuwa ta hanyar jifa yadda al'adar kan'aniyawa shine su bayar da yaran su domin a yanka su ga alla Mulik, yazo cikin littafin (safar) allawiyyin (1-2/20):

(1 sai ubangiji yayima musa magana da cewa: 2 kacema bani isra'il: ko wani mutum cikin bani isra'ila da baki masu sauka a cikin bani isra'ila ya bada jaririn sa ga Mulik to za'a kashe shi. Mutanen kasar zasu jefe shi da duwatsu).

Yadda wannan al'ada na kan'aniyyun na bayar da garirin su domin a yankasu ga alla Mulik – Allah yayi mana tsari -.

Saboda haka yana daga cikin rahamar Allah maduakaki ga halittun say a saukar masu da shari'a daga sama domin ya tunkari wannan shari'u na shiririta wanda aka gina su akan wulakanta mutum da yanka su wanda ya yadu a tsakanin zamuna cikin duniya!!. Allah madaukaki yace:

“kace masu [ya Muhammad] kuzo zan karanta maku abunda ubangijin ku ya haranta a gareku cewa kada ku hadashi da wani cikin bauta kuma ku kyautatawa iyaye; kuma kada ku kashe yaranku domin tsoron talauci; mune masu azurtaku dasu; kuma kada ku kusanci alfasha na bayyane da na boye; kuma kada ku kashe ran da Allah ya haramta kashewa sai bisa cancanta; da wannan ne yake maku wasiyya dashi koda zaku hankalta” (6:151)

Kuma Allah me girma yayi gaskiya a lokacin daya fadi akan Muhammad s.a.w wanda ya aiko shi da addinin gaskiya wanda ya kunshi dukkanin maslaha na al'amuran mutum a duniyar su da lahiran su, me farin ciki shine wanda yayi imani da shari'ar sa:

“kuma bamu aikeka ba face domin rahama ga talikai” (21:107)

Ibn Abbas yana cewa masanin fassarar alkur'ani:

lallai Allah ya aiko da annabin sa Muhammad s.a.w domin rahama ga dukkanin talikai, muminan su da kafiran su. Su muminan su lallai Allah ya shiryar dasu dashi, ya kuma shigar dasu aljanna dayin imani dashi da yin aiki da abunda yazo dashi daga wurin Allah, wanda kuma suka kafurta lallai ya kawar masu da bala'i dashi anan duniya wand ayake sauka akan mutanen da suka karyata manzannin su gabanin su.”

Allah ya aiko shi ga duniya baki daya domin su bautawa Allah shi kadai ba tare da hada shi da wani ba cikin bauta da kuma shafe karya na cikin al'amuran zamanin jahiliyya da al'adu na shirka da kuma ibadunsu na shiririta wanda aka sansu dashi.

 

LAIFUKA WANDA AKA RUBUTA SU CIKIN DOKOKI NA DAN ADAM:

 

Akwai laifuka dayawa ko kuma ayyuka wanda sunkai matsayin manyan laifuka wanda aka halastasu aka kuma mayar dasu doka a cikin wasu dokoki na dan Adam, misali irin su zubar da ciki da kisan jarirai!! Duk wanda besan yadda ake kashe garirai ba zai iya ganin haka cikin kafa ta yanan gizo cikin aikin zubar da ciki, wanda manyan likitoci kwararru sukeyi kuma kananan likitoci suke taimaka musu wanda ana anason su da siffa ta rahama a tattare dasu!! Abun mamaki itace wannan laifi mummuna wanda yake faruwa bayan mahaifiya dakanta ko kuma mahaifiya da mahaifi tare sun gabatar da bukatar su ga likita na kashe yaron su jariri, domin wasu dalilai wanda basu taka kara sun karya ba wand ayake nuna matakin dibmuwa na mutum wanda suke kai gareshi kasancewar basu shirya karban sa ba domin sunason jin dadi na tafiya da yanci gabanin a daura masu nauyi na kula da renon yaro, ko kuma domin dalilin matsi na talauci ko kuma wani matsala ta daban na rayuwa!!!.

Wannan aikin ya yadu cikin kasashe dayawa wanda sukaci gaba, da kuma wasu kasashe talakawa a asiya da afirka, musamman ma idan jaririn ya kasance macece domin suna daukanta akan cewa nauyi ce kawai akansu ta hanyar tattalin arziki akan iyalai sabanin yaro wanda suke daukan sa a matsayi jari da kuma ginshiki na gina iyali, suna dauke nauyin iyaye maza da taimakon su wurin samar da kudade ga iyalai. Hakika mun gani hotuna na wasu iyaye cikin wasu kasashe matalauta a gabashin asiya suna kashe yaransu mata da ransu kamar yadda kafirai na makka gabanin zuwan musulunci suke aikatawa, wanda Allah madaukaki ya fadi akan su yana me hakaituwa akana ayyukan su me muni da ta'addanci babba:

“idan kuma akayima dayan su bushara da diya mace sai fuskarsa tayi baka yana cikin kunci da bacin rai (58) yana boyewa mutane saboda mummunan abunda ya sameshi na busharar da aka masa; kodai ya riketa cikin wulakanci ko kuma ya birneta cikin kasa [da ranta] ku saurara kuji hukuncin su ya munana” (suratun nahli ayata 58-59)

Hakika wannan laifi ya kasance doka cikin wasu dokoki tsofaffi kamar dokar rumaniya wanda aka nassanta cikin sakin layi na hudu daga cikin sa cewa “akashe dukwani jariri me ciwon alaji”[32]. Kamar yadda wannan laifi ya kasance ya yadu cikin rayuwan almaniyawa tsoho yadda mahaifiya bayan ta haihu zata kai abunda ta haifa ga mahaifi idan ya yarda dashi sai ya rene shi idan kuma be yarda dashi ba sai a kashe shi kamar yadda daya daga cikin tsari da dokoki na romaniyawa ta kunsa wand aka kago shi a birnin Bahnasa (wanda a baya ake kiransa da sunan birni ko kuma uksirankhus) a cikin karamar hukumar almina a kasar misra kuma ya yaduwan wannan al'ada ya bayyana a tsakanin rumaniya wanda ya kunshi wannan dokoki a rubuce daga miji zuwa ga matarsa yana cewa a cikinsa: “idan abunda aka Haifa ya kasance namiji ki barshi ya rayu, idan kuma ya kasance mace ki kasheta”[33].

Amma shari'ar musulunci shari'a ce ta tausayi da rahama, hakika ta haranta wannan laifi mummuna, manzon Allah s.a.w yace:

(lallai Allah ya haramta maku cutar da mata, da kashe yara mata da hana hakkoki da kuma tambayan abunda bahakkin mutum ba, ya kuma karhanta maku ance kace) (buhari da muslim ne suka rawaito shi)

Kuma ya ambaci hakkoki na jarirai alhali yana cikin mahaifiyar sa wanda babban wannan hakkoki shin hakkin rayuwa!! Allah madaukaki yace:

“kuma kada ku kashe yaranku domin tsoron talauci; lallai mune muke azutra ku dasu [baki dayanku](suratul an'am ayata 151)

Ya kuma kore dukkanin abiunda zai kawo banbance banbance cikin mu'amala tsakanin yara mazan su da matan su, manzon Allah s.a.w yace:

“kuyi adalci a tsakanin yaran ku a cikin kyauta” (buhari ne ya rawaito shi)

 

 

 

BABI NA BIYU

SHARI'AR MUSULUNCI DA HADDOJI DA KUMA MANUFA NA SHARI'AR MUSULUNCI

 

  • Shari'ar musulunci
  • Manufa na shari'ar musulunci
  1. Kiyaye addini.
  2. Kiyaye rai.
  3. Kiyaye hankali.
  4. Kiyaye dukiya.
  5. Kiyaye dangankata.
  • Haddoji a cikin shari'ar musulunci.
  • Neman yin aiki da shari'ar musulunci a cikin kasashen da ba musulmai ba.
  1. Kutuna na shari'a a cikin kasashen da bana musulunci ba
  2. Shin yana wajaba neman kasashen da ba musulmai ba yin aiki da shari'ar musulunci.

 

 

 

BABI NA BIYU

SHARI'AR MUSULUNCI DA HADDOJI DA KUMA MANUFA NA SHARI'AR MUSULUNCI

SHARI'AR MUSULUNCI:

 

Kamar yadda ya gabata muka fadi cewa abunda Allah ya shar'anta ya kuma wajabtama mutane na dokoki masu tsara alakar su da Allah madaukaki da kuma alakar su da mutanen da suke rayuwa tare da dabbobi da mahalli, daga cikin wannnan dokoki akwai wanda yake tsara al'amuran ibada, daga cikin su kuma akwai wanda suke tsara mu'amala na tattalin arziki da kasuwanci da zamantakewa da kuma harkokin mutum da kuma dokoki wanda suke tsara ginshikai wanda kasa ke kafuwa akai da kuma tsara ayyuka na bangaren dokoki da kuma bangaren alkalanci da kuma bangaren zartarwa.

 

MANUFA NA SHARI'AR

MUSULUNCI:

 

Manufa na shari'a itace kololuwan manufa wanda shari'a tazo domin tabbatarwa, wanda sune ma'anoni wanda shari'a ta nufe su wanda kuma saboda haka ne aka shar'anta hukunce hukunce da haddoji, daga cikin manufa game gari na shari'ar musulunci akwai:

  1. KIYAYE ADDINI: lallai kiyaye addini shine babban manufa na shari'ar musulunci, Allah madaukaki yace:

“kuma ubangijin ka ya hukunta cewa kada ka bautawa kowa sais hi sannnan kuma ka kyautatawa iyaye” (suratul isra'i ayata 23)

Sannan kuma shari'a ta nassanta lada me girma ga wanda ya taimakawa mutane wurin kiyaye addinin su shin ta hanyar karantar dasu addini ne hakika manzon Allah s.a.w yace:

“mafi alherin ku shine wanda ya karanta alkur'ani kuma ya karantar” (buhari ne ya rawaito shi)

Ko kuma ta hanyar gina wurin da zasu taru ko kuma shiryr shirye domin karntar da mutane al'amuran addinin su da kuma sanar dasu hakan kamar gina masallatai domin bautan Allah da kuma karatu, hakika manzon Allah s.a.w yace:

“duk wanda ya ginawa Allah masallaci koda kwatankwacin wurin kwanciyan kaza ne, Allah zai gina masa gida cikin aljanna” (sahihu Ibn Hibban)

Kiyaye addini yana daga cikin manyan wajibobi cikin shari'ar musulunci saboda haka ne aka kiyaye shi karkashin wannan abubuwa masu zuwa:

  • Nassi akan wajabcin kare dukkanin wnai makiyi wanda zai shigo domin bata addini.
  • Yaki da kuma haramta dukkanin wani yunkurin bata addini na cikin kasa, kamar wanda yake son izgilanci da addini ta hanyar zana wani almara wanda zai bata musulunci ko kuma karamar manzon Allah s.a.w, da ikirarin yancin fadin albarkacin baki da makamantan haka, yancin fadin albarkacin baki ba tana nufin yancin zagi bane har Abadan ko kuma tozartawa da muzantawa da nuna banbanci na kabilanci.
  • Yaki da kuma hana dukkanin kirkiran wani abu cikin addini domin kasancewar sa addini ne cikakke, Allah madaukaki yace: “ayau ne nake cika maku addinin ku kuma yake cika maku ni'imomina agareku kuma na yardan maku da musulunci a matsayin addini” (suratul ma'ida ayata 3)

Duk wanda ya kirkiri wani abu cikin addini to hakika yayi kari a cikin say a kuma shigar da abunda baya cikin sa, shi kuma kirkiran wani abun hanya ne na rusa addini, daboda haka ne Allah madaukkai yace: “wanene yafi zalumci sama ga mutumin da ya kirkiri karya akan Allah domin ya batar da mutane ba tare da ilimi ba; lallai Allah baya shiryar da mutane azzalumai” (suratul an'am ayata 144)

 

  1. KIYAYE RAI: Allah madaukaki ya halicci ran dan adam ya kuma haramta da'addanci akanta shin wannan ta'addinji daga mutum din ne a karon kansa ta hanyar halakar da ita, domin fadin sa madaukaki:

“kada ku jefa kawunan ku zuwa ga halaka; lallai Allah ya kasance me rahama a gareku” (suratun nisa'i ayata 29)

Ko kuma ta hanyar ta'addanci ne akan rai daga wani mutum na daban shin wannan mutumin mumini ne ko kuma kafiri, Allah madaukaki yace:

“kada ku kashe ran da Allah ya haramta face bisa cancanta” (suratul isra'i ayata 33)

Duk wanda ya kashe da gangan za'ayi masa kisasi da hkuncin alkali kuma kofar yafiya a bude take daga wurin yan uwan wanda aka kashe na yafewa akan wannan kisasi, domin fadin Allah madaukaki:

“yaku wanda sukayi imani an wajabta maku kisasi agareku a cikin kisa; [ran] me yanci da [ran] me yanci; bawa da bawa; mace da mace; duk wanda kuma ya yafe masa daga dan uwansa wani abu to yabi haka da kyakyawa da kuma biya da kyautatawa; wannan rangwame ne daga ubangijinku da rahama; duk ya ketare gona da iri bayan haka to yana da azaba me radadi” (suratul bakara ayata 178)

 

  1. KIYAYE HANKALI: Allah ya zaba da kuma daukaka mutum akan sauran dabbobi da ni'imar hankali ya kuma wajabta dokoki wanda zai kiyaye wannan ni'ima ya hamanta dukkanin abunda zai cutar da ita ko kuma kawar da ita kamar giya da makamantan su na miyagun kwayoyin maye wanda suke tafiyar da hankali da kuma lalatashi, domin fadin sa madaukaki:

“yaku wanda sukayi imani lallai gina da caca da dara da rantsuwa da gumaka datti ne cikin ayyukan shedan saboda haka ku nuisance su koda zaku samu rabauta” (suratul ma'ida ayata 90)

Hakika an kirata cikin musulunci da sunan Ummul kaba'isa domin girman hatsarinta shin akan mutum ne ko kuma a al'umma itace uwar dukkanin sharri da kuma dalilin laifuka miyagu.

 

  1. KIYAYE DUKIYA: dukiya dan uwan rayuwa Allah ya sanya shi ginshiki na kiyaye ta ta dalilin sa ne maslahohi suke faruwa da kuma jawo arziki sai abinci ya yalwatu da kayayyaki da kartu da wurin zama… da sauransu, kuma hakika Allah madaukaki ya bayyana hanyoyi na shari'a na samun dukiya da kuma hanyoyi na habaka ta da kuma kashe su, saboda haka ne aka haramta dukkanin aikin wanda yake jawo halakar dukiya da kuma batashi ba tare da wani amfani ba me kyau, ya kuma haramta amfani da mutane da kuma cin dukiyar su da barna ta hanyar riba ko kuma rashawa da sata da caca da malumta, domin fadin Allah madaukaki:

“yaku wanda sukayi imani kada kuci dokiyoyin ku a tsakanin ku da barna” (suratun nisa'i ayata 29)

Ko kasheta ta hanyar da zutar da mutum ko kuma wanin sa ko kuma almubarzanci da barna wurin kasheta ba tare da bukatar hakan ba, ya kuma wajabta hakkoki a cikinta shin gay an uwa ne na jini ko kuma mabukata ne gama gari da sadaka da kuma kyautatawa domin fadin Allah madukaki:

“kuma kuba makusanta hakkin su da miskinai da matafiya kuma kada kuyi almubazaranci da; lallai masu almubazanci sun kasance yan uwan shedan; shi kuma shedan ya kasance kangararre ga ubangijin sa” (suratul isra'i ayata 26-27)

 

  1. KIYAYE DANGANTAKWA: shari'ar musulunci ta haramta dukkanin abunda zai zama sababi na caddanyan dangantaka misali kamar laifin zina, Allah madaukaki yace:

“kuma kada ku kasanci zina domin kuwa ta kaance alfasha kuma mummunan hanya” (suratul isra'i ayata 32)

Kamar yadda ya haramta har wayau dukkanin abunda zai sama sababi na karar da dangantaka ko kuma dates ta kamar luwadi da madigo, Allah madaukaki yace:

“kuma daga cikin mutane akwai wanda maganar sa zai baka mamaki a rayuwan duniya kuma Allah yana sheda abunda ke cikin zuciyar sa kuma a kasance me yawan musu idan ya kuma ya tafi sai ya shiga kasa yana me barna a cikinta ya kuma lalata gonaki da dangantaka; Allah kuma bayason masu fasadi” (suratul bakara ayata 204-205)

 

HADDOJI

 

An wajabta haddoji a cikin shari'ar musulunci domin kiyaye wannan dokoki da Allah ya saukar domin tsara rayuwan mutum, da kuma lamuni na aiki da ita kuma mutane su girmamata ya zama wajibi na samun doka wanda zai tsara hanyoyin kadabtarwa da ukuba ga duk wanda ya saba wannan doka saboda haka ne Allah ya shari;anta haddoji wanda (doka ne na ukuba) shari'a ta musulunci bata nassanta akan wani haddi ba face domin kiyaye hakki, kuma dayawa na abunda yake hadewa wand aba musulmai ba tsakanin ma'anar haddoji da shari'ar musulunci kanta suna masu sawwara cewa shari'ar musulunci haddi ne kawai da kuma hukunce hukunce na ladabtarwa da ukuba na yanke hannun me sata (tafin hannun sa) da kuma kashe wanda yayi kisa da dai sauransu, wannan sawwaran kuwa ba daidai bane, shi haddi ukuba ne wanda akw aiwatar dashi akan wanda ya tsabawa shari'ar musulunci domin kariya agareta da kuma lamuni akan rashin saba mata, a cikin aiwatar da haddoji (doka na ukaba) akwai rayuwa da kuma kiyaye rayuka da dukiyoyi na abunda suka mallaka da mutuncin su da hankulan su, lallai ita lamuni ne akan kiyaye zatin mutum ita kamar canji ne kan sura na waje wanda yake kiyaye birni wanda shine (shari'ar musulunci) daga yan fashi wanda suke neman fermata da kuma ta'andacci akan mutanen ta wanda suka aminta acikinta, Allah madaukaki yayi gaskiya:

“kuma kunada rayuwa a cikin kisasi yaku ma'abota hankula koda zaku samu takawa” (suratul bakara ayata 179)

Musani cewa haddoji bawai sabon al'amari bane cikin shari'ar musulunci, a'a Allah yayi umurni da ita cikin dukkanin shari'u na sama, hakika Allah yayi umurni dayin haddi cikin attaura wanda aka saukar ma Musa amincin Allah ya tabbata a gareshi, Allah madaukaki yace:

“lallai mun saukar da Attaura akwai shiriya da haske a cikinta, annabawan da suka mika wuya suna hukunci da ita ga wanda yahudawa da malamun su da fadoji daga abunda suka haddace daga littafin Allah kuma sun kasance masu sheka kansa, kada kuji tsoron mutane kuji tsoro na kuma kada ku siyar da ayoyin Allah akan lada dan kadan duk kuma wanda baya hukunci da abunda Allah ya saukar to wannan sune kafira. Kuma mun wajabta agare su a cikinta cewa rai da dai, ido da ido, hanci da hanci, kunne da kunne, hakori da hakori, raunuka kuma kisasi, duk wanda yayi yafiya dayain sadaka dashi to hakan kaffara ce a gareshi; duk wanda baya hukunci da abunda Allah ya saukar to wannan sune azzalumai” (suratul ma'ida ayata 44-45)

Kuma haka Allah yayi umurni da aiwatar da haddoji cikin Injila wanda aka saukar ga Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi, Allah madaukaki yace:

“sai muka biyo bayan su da Isa dan Maryam yan ame gasgatawa da abunda ke gaba gareshi na attaura kuma muka bashi Injla acikin sa akwai shiriya da haske kuma me gasgatawa ne ga abunda yake gaba gareshi na attaura da kuma shiriya da wa'azi ga masu takawa.* mutanen Injila suyi hukunci da abunda aka saukar masu acikin sa; kuma duk wanda baya hukunci da abunda Allah ya saukar to wannan sune fasikai” (suratul ma'ida ayata 46-47)

 

WANENE ZAI JAGORANCI TSAYAR DA HADDAI:

 

Lallai al'amarin zartar da haddoji akan wanda ya sabawa shari'ar sa (dokan musulunci) yayi laifin da yake jawo haddi wannan aiki ne na shugaba musulmi ko kuma mataimakin sa babu wani mutum cikin dai-daikon munanen al'umma da yake da hakkin zartar dashi, musulunci addini ne me tsari da oda da bi daki bayan daki bawai addini bane mara tari da oda, ba'a taba zai da haddi ba akan wani a azamanin manzon Allah s.a.w face da izinin sa domin shine aka wajabtawa zartar da hukunce hukunce idan kuma ya kasance shine wanda aka wajabtawa zairtar da hukunci domin kasancewar sa shugaba to lallai hakan ya zama hakki ne na shugaba wanda yake shugabancin musulmai cikin mutanen da zasu zo a bayan sa, Allah madaukaki yana cewa:

“kuma kayi masu hukunci a tsakanin su da abunda Allah ya saukar kuma kada kabi son zuciyan su kuma ka guji su jarabeka akan wasu daga abunda aka saukar maka; idan kuma suka juya baya to kasani lallai Allah yana son ya dandana masu wani azaba sakamakon wasu zunuban su; kuma dayawa daga cikin mutane fasikai ne” (suratul ma'ida ayata 49)

 

ABUNDA YAKE KAWAR DA ZARTAR DA HADDI:

 

  1. JANYEWA DAGA IKIRARI: mafi yawan muluman fiqhu na musulunci (abu hanifa da shafi'I da Ahmad) sun tafi akan cewa ana karban janyewar mutumin da yayi ikirari idan ya janye daga haka kuma haddi yana fadi akansa, kuma ana kyaleshi idan ya gudu koda zai janye[34], ma'iz dan Malik Allah ya kara masa yarda wanda ya kasance maraya cikin wasiyyar Hazal al-aslami Allah ya kara masa yarda, ya fada cikin zina tare da wata mata a cikin unguwa, sai Huzal ya nuna masa cewa yaje gun manzon Allah s.a.w ya tabbatar da laifinsa ga manzon Allah s.a.w, bayan yayi ikirari kansa har sau hudu sai manzon Allah s.a.w yayi umurni da a zartar da haddi akansa, sai dai a lokacin da ake zaitar da haddin akan sa sai ya tsorata ya gudu sai Abdulahi dan Anis ya bishi ya zartar masa da haddin, bayan ya dawo ya fadama manzon Allah abunda ya faru sai yace: (kash me yasa baku kyale shi, me yiwa zai tuba, Allah ya amshi tubar sa, yakai Huzal daka suturtashi da tufafinka yafi maka alheri akan hakan da ka aikata) Ahmad ne ya rawaito shi, da Abu Dawud, da Hakim, kuma albani ya inganta shi, Huzal shine wanda ya kwadaitar da ma'iz cewa yaje ya fadama manzon Allah domin ya tabbatar da zunuban sa, fadin sa manzon Allah s.a.w cewa: “daka suturta shi da tufafinka” yana nufin daya hanashi zuwa tabbatar da laifin sa wanda ya wajabta masa haddin, Baji yace: “suturtashi ya kasance ya umurceshi dayin tuba da boye laifin sa, an fadi mayafi ne domin girmama abun”[35]
  2. SHUBUHA: wata kila a tsayar da haddi da zata, shi haddi ana koreshi da shubuha Umar dan Khaddab Allah ya kara masa yarda kahlifa na biyu na manzon Allah s.a.w yace: “ya kawar da haddi da shubaha yafi soyuwa a gareni da na zartar dashi da shubuha” (Ibn Abi shaiba ne ya rawaito shi)

Saboda haka ne duk wanda ya saci kudi yana tunanin yanada hakki a cikin sa to haddi ya fadi akansa.

  1. TUBA: idan me laifi ya tuba gabanin a kama shi to lallai haddi ya fadi akansa, amma idan tuban ya faru ne bayan an kamashi to hakan baya kawar da wannan haddin akansa saboda fadin Allah madaukaki:

sai dai wanda suka tuba gabanin a kama su; ku sani lallai Allah me gafara ne da rahama (suratul ma'aida ayata 34)

Ita tuba makasudin ta anan shine wacce take kawar da haddi gabanin a kama me laifi itace tuban da take da alaka da haddin tare hanya (haddin masu yaki) da haddin Ridda, wannan da ijma'in malaman fiqihu baki dayan su. Amma sauran haddojin kuwa kamar misalin zina da sata anan wurin akwai magana biyu na ra'ayin malamai akansa: ra'ayi na farko sun tafi akan cewa tana kawar da wannan haddin da tuba gabanin a kama me laifi, ita kuma ra'ayi na biyu sun tafi akan cewa ita tuba a cikin wannan haddi gabanin akama me laifi bata kawar da haddi. Amma tuban da take da alaka da haddin kazafi malamai sunyi ittifaki akan sa cewa bata kawar da haddi gabanin akama me laifi ne ko kuma bayan an kama shi. A cikin wannan matsalar akwai bayani me fadi ga wanda yake neman Karin bayani akan haka sai ya koma littattafan fiqihu na musulunci a kan wannan matsala.

  1. JANYEWA DAGA SHEDA: janyewar shedu daga shedarsu bayan hukunci gabanin zartar dashi yana kawar da haddi akan wanda akayi sheda akansa me laifi.
  2. YAWAITAN HADDI IRI DAYA AKAN MUTUM: idan haddi iri daya suka maimaitu akan mutum gabanin zartar da haddin shikenan haddi daya ya wadatar.

 

SHARUDDA WAJABAN HADDI[36]:

 

  1. ATTAKLIF (HANKALI DA BALAGA) baya zartar da haddi akan yaro ko kuma mahaukaci ko mara dolo ko kuma me maye sai bayan ya warke, saboda fadin manzon Allah s.a.w:

“an dauke alkalamin rubutu akan mutum uku: akan mahaukaci har sai ya warke, dame bacci har sai ya farka, da kuma yaro har sai yayi mafarki” (Ahmad da Abu Dawud da Hakim ne suka rawaito shi) (sahihul jami'u- na albani)

  1. ZABI DA KUMA RASHIN TILASTAWA: Allah madaukaki yace:

“duk wanda ya kafurta da Allah bayan imanin sa sai dai wanda aka tilastamawa alhali zuciyar sa na cike da imani amma wanda zuciyar sa ya yalwatu da kafurci to wannan fushin Allah ya tabbata akansu kuma suna da azaba me girma” (suratun nahli ayata 106)

  1. LAFIYA da kuma iko ba'a zartar da haddi akan mara lafiya ko me rauni na juhha da jiki sai bayan warakan sa.
  2. ILIMI AKAN HARAMCIN HAKA. 

 

MUSTAHABBANCIN SUTURTAWA AKAN MUSULMI[37]: wanda yaga wani musulmi yana aikata laifi, yana da zabi tsakanin bayar da sheda domin kira zuwa ga Allah da kare dokokin sa, ko kuma suturta dan uwan sa musulmi, wanda wannan shi yafi (kuma akwai fifiko akan sag a duk wanda yake son Karin bayani akan say a koma uwa ga littattafin fiqihu na musulunci), hakika manzon Allah s.a.w yace:

“duk wanda ya suturta musulmi Allah zai suturtashi duniya da lahira” (muslim ne ya rawaito shi)

 

SHUBUHOHI AKAN TSAURIN HADDOJI:

 

Yana yawo a cikin kafafen yada labarai na turawa cewa haddojin da shari'ar musulunci ya sanya akan wasu laifuka (kisa da yanke hannu da jifa) ukuba ne me tsauri mara tausayi wanda bata dace ba da wannan zamani namu?!!

 

Amsa akan wannan shubuhar:

Lallai kowa ya yarda cewa wannan laifuka sunada cucarwa wanda suke a bayyane ga al'umma, sannan kuma dole ne a yake su da tushe su ta hanyar sanya masu ukuba, sai dai sabanin shine cikin nau'in ukubar! Kowa ya tanbayi kansa: shin ukubar da musulunci ya sanya su sunfi dace da samu nasara wurin toshe wannan laifuka ko rage su ko kuma ukubar da dokokin mutane suka tsara wanda bazat karama laifi komai face yaduwa!? Shi gaba gurbatacce dole ne a yanke shi domin lafiyar sauran gangan jiki!

  • Abune sananne a hankalce cewa dukkanin ukuba dole ne akwai tsauri a cikinta domin ta zama tana tsawatarwa da kuma hana masu laifi aikata laifi idan kuma bah aka ba to hakika ta rasa dacewar ta.
  • Rashin zartar da haddi domin tsaurinta zalumci ne ga al'umma taya mutum zai samu aminci akan ransa da dukiyar sa da mutuncin sa, lallai zartar da haddi rahama ne ga al'umma da kuma wand aka zartar da haddin akan sa, misali likitan da yake tiyata domin ya yanke ko kuma cire wani bangare a jikin mara lafiya da niyyar masa magani a zahirin aikin sa rashin tausayi ne cikin yanke wannan gaba sai dai kuma rahama ce ga sauran gangan jikin domin su tsira. Kaman haka ne haddi na kisa ko kuma kawar da gurbatacce cikin al'umma domin sauran al'umma su tsira.

 

ALAKAR SHARI'AR MUSULUNCI DA DOKOKI WANDA DAN ADAM YA KIRKIRE SU:

 

Asali cikin abubuwa cikin shari'ar musulunci shine halalci da halal saboda fadin Allah madaukaki:

“shin baka gani b acewa lallai Allah ya hore maka abunda yake cikin sammai da kasa kuma ya cika maka ni'imar sa agareku ya bayyanen su dana boyen su” (suratu Lukman ayata 20)

Sai dai abunda dalili cikin madogara na shari'a yazo da haramcin sa, saboda fadin amnzon Allah s.a.w:

“duk abunda Allah ya halasta cikin littafin sa to halal ne kuma abunda ya haramta haram ne, abun kuma da yayi shiru akan su sauki ne, ku amshi sauki daga Allah domin lallai Allah baya manta bane sa'anna ya karanta wannan ayara: kuma baungijin ka be kasance me mantuwa ba (suratu Maryam ayata 64)(Hakim da Baihaki ne suka rawiato shi kuma albani ya inganta shi cikin littafin silsitul sahuha numba ta 2256)

Kenan shari;ar musulunci bata haramta dokoki wanda dan adam suka kirkira ba wanda suke tsara rayuwan mutum hasalima ta halasta ne matukar basuci karo da uta ba kamar dokar ruwa ko kuma dokar aiki… da dai suaran su, kawai ta haramta wannan dokokin ne wanda suke halasta laifuka ko kuma abunda aka haramta wanda suke da sakamako mummuna ga mutum ta fuskar hankalin sa ne ko kuma dukiyar sa ko kuma zamantakewar sa ko kuma halayen sa ko lafiyan sa, haramcin yana zama maslaha ga mutum karon karon kansa domin Allah a cikin dokokin sa ya wadatu daga bayin sa zububan su baya taba cutar dashi haka kuma biyayyar su baya amfanar dashi da komai, Allah madaukaki yace:

“kace kawai abunda ubangiji nay a haramta shine alfasha abunda ya bayyana daga gareshi da abunda buya; da zunubi da dagawa ba tare da gaskiya ba da kuma ku hada Allah da wani cikin bauta abunda ba'a saukar da hujja ba akan sa da kuma ku fadi abaunda baku sani ba akan Allah” (suratul a'araf ayata 33)

 

NEMAN YIN AIKI

DA SHARI'AR MUSULUNCI

A CIKIN KASASHEN DA

 

KOTUNAN SHARI'AR MUSULUNCI A CIKIN KASASHEN DA BA MUSULMAI BA:

Akwai wasu kafafe da kuma bahasi nay an jaridu wanda suke inkarin samuwan malisu ko kuma kutuna na shari'ar musulunci a wasu kasashen yamma wanda ba musulmai ba wanda suka bada dama budesu da kuma sanya su cikin doka wanda baza'a ce masu kutuna ba kai tsaye masu sunan kotu wanda aka sani a dokance kawai majalisu ne wanda suke taimakawa musulmai cikin matsalolin su na aure da saki da gado da sauran su, misali da wani zai kashe wani wannan majalisan bazasu zartar masa da hukuncin kisa ba sai dai su kais hi zuwa gay an sanda domin gabatar dashi ga kotuna na al'ada na kasar. Amma dai wannan kafafe na sadarwa da bahasi na jaridu suna son tsoratarwa ne ga mutanen wanna kasashe daga wannan majalisun sais u rika sawwarata da cewa yakine ga kasashen su wanda wannan magana ne ta shirirrita wanda ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinta an ginata ne akan jahilci ko kuma tsantsan kiyayya ga musulunci da mutanen sa, yadda zasu sa mutane su rika shakka shine za'a zartar masu da hukunce ne da shari'ar musulunci wanda cikinta yayi nesa ga idanun yan sanda!! A cikin hakikanin al'amari kuma shine wannan majalisu an gina su ne akan tafarkin al'amuran mutane wand aba musulmai ba wanda ake aiki da ita a kasashen musulunci, daga cikin saukin shari'ar musulunci shine ta yarda da ayaima wanda ba musulmi ba wanda yake zaune cikin kasar musulunci hukunci da shari'ar su cikin dayawa na matsalolin su kamar aure da saki da makamantan su, ba'a wajabta masu dokoki ba na musulunci wanda aka aiki dasu akan musulmai cikin wannan matsalolin sai idan sun yarda da hakan da suje kotun musulunci domin ayi masu hukunci. Kuma hatta acikin wasu ayyuka wanda shari'ar musulunci ta nassanta akan haramcin su da kuma laifin su bata haramta ba akan wanda ba musulmai ba, kamar shan giya da cin naman alade domin kuwa shan giya da cin naman alade basa ganin haramcin sa dukda cewa a hakikanin akidar su shine haramcin su kuma akwai dalilai dayawa akan hakan.

Daga cikin misali akan munin wannan kafafen yada labarai da bahasi na jaridu wanda aka kafasu domin siyasa shine daya daga cikin me gabatar da shiri cikin irin wannan tuzartattun kafafe yana tambayan musulman da suke zaune cikin kasar sa: wanene yafi a wurinka tsakanin dokokin musulunci ko kuma kuma dokan wannan kasa?!! Sai musulmai suka amsa cikin yardan zuciya cewa”dokokin musulunci sune suka fi.” Wannan bayar da amsa ne na dabi'a matuka domin tambayar a karon kanta anyita ne ba a wurinta kuma baya nuni kan komai face tsantsan kiyayya da kabilanci daga wannan me gabatar da shiri. Saboda musulmi yana nufi ne cikin amsan shi cewa maganar Allah tana gaba da maganar mutum, bawai yana nufin baya girmama dokan kasa bane!! Saboda iata doka ta musulunci yana umurni da hana sata da kisa da yima mutane fince wanda shine dai abunda ke cikin dokoki na mutane saboda haka babu cin karo anan, abunda musulmin yake nufid a wannan amsa nashi cewa idan dokan da mutum ya kirkira cikin wannan kasa wacce ba musulma ba yana lahasta alfasha ko shan giya ko zubar da ciki ko cin naman alade shikenan baza'a bi wannan sauki ba hukuncin Allah za'a bi a cikinta bazai sha giya ba ko yin akfasha ba ko kuma kisan jariri ta hanyar zubar da ciki, kuma bawai yana nufi bane da amsan shin= cewa zai keta dokokin kasa ba, amma dangane da sauran ukuban kamar ukubar sata ko kisa ba'a zartarwa akan musulmi ba wanda yake dan gudun hijira ukubar da aka nassanta a cikin shari'ar musulunci saboda rashin cikan sharuddan sa, al'amarin haddi na shugaban musulmi ne sannan kuma kasancewar say a shiga wannan kasa karkashin tsari da dokanta shi kuma musulmi an umurce shi da cika alkawari na cika akawuran sa daya dauka, mu muna magana ne anan akan musulmi wanda yake rayuwa cikin kasar kirista bawai kasar musulunci ba.

Ya wajaba akan musulmi dan gudun hijira wanda yake rayuwa a cikin kasar da ba ta musulunci ba ya mutunta da kuma kiyaye dokoki na wannan kasa mutukar basa umurtan sa da sabon Allah madaukaki, idan suka umurce sa da sabon Allah madaukaki ya wajaba yayi hijira daga wannan kasa wacce bata mutunta yancin na addini da hakkoki na mutum, kamar misali da ace wannan dokan zasu umurci mace musulma da cire hijabi, to anan ya wajaba a gareta da tayi hijira daga wannan kasa da gaggawa domin ta tsaritar da kanta daga wannan dokoki na shiririta, baya halatta agareta fada ta hanyar da be dace ba ko kuma makamanta hada da wannan dokoki, amma idan an samu cin karo tsakanin dokoki na wannan kasashe tare da hakkin musulmin da yake zaune a ciki amma ba tare da tayi masa umurni ba da aikata sabon Allah to anan wurin ya halatta ga wannan musulmi yayi mu'amala da wannan dokoki ta hanyar daya dace domin bayyana rashin yardan sa akan wannan doka!! Misasali idan ya kasance doka be yarda da gina masallaci ba ta yadda musulmai zasu samu yin sallolin su a ciki, ko kuma yana hana ma musulmi Karin aure amma kuma ta halasta mashi yin kawaye mata kari akan matar sa, to anan ya wajaba akan wannan musulmin zuwa ga kotu ko kuwa majalisu na shari'a kamar majalisar dokoki ko kuma gidan jarida domin samun damar kwato hakkin sa na addini wanda Allah ya wajabta masa kamar salla ko kuma ya halasta masa kamar Karin aure.

 

SHIN YA HALASTA NEMAN DASASHEN DA BA MUSULMAI BA AIWATAR DA SHARI'AR MUSULUNCI:

Akwai wasu daga cikin muslmai yan gudun hijira ko kuma sababbi a cikin wasu kasashe na yamma wanda suke rike tuka bakyake suna rubuce akan su Kalmar shahada kyallaye wanda aka rubuta akansu shari'a a England a misali, shin wannan aikin yana da kyau ko kuma kuskusre ne?

Domin samun sani akan wannan amsar ya wajaba sauraran wannan kalmomi masu zuwa:

  • Wannan mutane basu tashi ba akaron farko da karantar da mazauna wannan kasa ba menene shari'ar musulunci na gaskiya, kawai sais u fara neman aiwatar da ita kai tsaye, bayan sunada sanin cewa dukkanin abunda tunanin su game da shari'ar musulunci itace wannan ukubar da aka nasssanta a cikin shari'ar musulunci kamar yanke hannun me sata da sauran su, to taya kake tunanin zasu yarda su karbi tunanin aiwatar da shari'a akan su?!! Da wannan aiki nasu bazasu karantar dasu ba shari'ar mususlunci face kawai tsoratar dasu sukeyi daga gareta!!.
  • Lallai wa'innan mutane a cikin mafi yawan halaye ya shige masu duhu tsakanin ma'anar shari'a da kuma addinin musulunci ma'ana da wannan ilimin nasu suna nufin kiransu zuwa ga shiga musulunci amma da wannan hanyar da suka bi sun nuna ma mutane cewa suna son aiwatar da shari'a ne akan su, kena acikin fahimtar mutanen itace suna son aiwatar da wannan ukuba ne wanda aka nassanta cikin shari'ar musulunci akan su.
  • Shari'ar musulunci shari'a ce ta kasashen musulunci baya wajaba neman aiwatar da ita akan kasashen da ba musulmai ba aiwatar yin aiki da ita, kamar yadda ba'a taba gani ba cikin tarihi a zamanin manzon Allah s.a.w da khalifofin sa cewa daya daga cikin su ya nemi wkasashen da ba musulmai ba aiwatar da shari'ar musulunci!! Saboda ta yaya zai yiwu kasar da yarda da addinin musulunci ba kum amafiya yawan yan kasan addinin kiristanci sukeyi ko yahudanci kuma me shugabantan su kirista ne ko bayahude da cewa su aiwatar da shari'ar da ba nasu ba?!!!.
  • Neman aiwatar da shari'ar musulunci a matsayin doka ya wajaba ya zama ta hanyar haddoji na dokoki misali wannan neman ya zama ta hanyar majalisa domin itace bangaren daya tilo wacce ta kebanta da tabbatar da dokoki, domin kuwa da zai samu ta hanyar daga kyallaye a hanya to lallai hakan zai haifar da fushin mutanen kasa sannan sakamakon hakan zai haifar da akasin abun da ake nema da kuma jawo cutarwa ga kokarin masu da'awa.

 

 

BABI NA UKU

Dokan musulunci da dokan da dan Adam ya kirkira da kuma tabbatar da manufa.

 

  • Ukubar barawo tsakanin yanke hannu da rufewa a gidan kurkuku.
  • Ukubar barawoa cikin littafai masu tsarki.
  • Kare kai cikin shari'ar musulunci.
  • Kare kai cikin dokan da dan Adam ya kirkira.

 

 

Babi na uku

Dokan musulunci da dokan da dan Adam ya kirkira da kuma tabbatar da manufa

 

Lallai dukkanin dokoki na ukuba ba'a sanya sub a face domin tabbatar da manufa na asali guda biyu wanda sune:-

  • TSAWATARWA: domin tsawatar da me laifi kada ya sake maimaitawa da kuma tsawatar da mutane kada suyi koyi dahi wurin aikata irin wannan laifi.
  • RAHAMA GA MUTUM DA MUTANE: rahama ga mutum na hanashi aikata aikin keta hakkokin wasu, da haka rahama zata tabbata akan wannan mutum da cewa bazai kusanci aikin laifi ba ta yadda ukuba bazai hau kansa ba, da kuma tabbatar da rahama ga mutane da hanyar kiyaye masu hakkokin su kada wani ya farmasu!! Anan wurin tambaya zaizo fadoma zauciya cewa wanne a tsakanin su yafi hanawa da kuma rahama a lokaci guda ga mutane, dokan musulunci ko kuma dokan da dan adam ya kirkira?! Bari mu kawo wasu misalai kamar misali laifin sata da kuma ukubar barawo a tsakanin dokan musulunci da dokan da dan adam ya kirkira mu gani wanne ne yafi nasara wurin tabbatar da manufar da muka fadi abaya!!

 

Ukubar barawo tsakanin yanke hannu (tafin hannun sa) da kuma ukubar dauri a kurkuku na tsawon shekaru:

 

Farko dai ya wagaba mu sani cewa ukuba baa bun so ban eko abu me kyau, idan da ta kasance haka kuwa da ba'a kirata da suna ukuba ba kuma da ta rasa rukunin ta na farko na asali watan tsawatarwa, haka kuma idan muna son kwatantawa akan ukubar barawo tsakanin yanke hannu da kuma ukubar dauri a kurkuku to zamu kwatanta ne tsakanin abu guda biyu saboda ko wannen su a zahiri ukuba ne amma dai zamu zabi abunda yafi dama dama acikin su wanda kuma cutarwan sa yafi zama da sauki.

Ta fuskan hankali da kuma masu bincike cikin al'amura wanda basu da son zuciya zai bayyanan mana cewa ukubar yanke hannu tafi zama tsawatarwa da hana sata sama ga ukubar kullewa a kurkuku da kuma zama misali mafi kyau ga hana laifin sata, saboda barawo a lokacin da yasan cewa zafa a yanke masa hannu a hankalce bazaije bari naje nayi satan ba sai wannan hannun nashi ya tsiri kuma dukiya mutane ya tsira shima, amma ita ukubar dauri a kurkuku dukda kasancewar ta ukuba sai dai bata hana barawo kara aikata wannan lafi na sata ukubata ce na wani takaitaccen lokaci kawai daganan sai a sakeshi to maganar gaskiya itace zaifa koma karayin wani laifin wanda ba ita ba saboda rena wannan ukubar da yayi!! Allah madaukaki yace:

“barawo da barauniya ku yanke masu hannuwa sakamakon abunda suka aikata daga Allah; kuma Allah ya kasance mabuwayi me hikima” (suratul ma'ida ayata 38)

Sai Allah madaukaki yace: “sakamakon abunda suka aikata daga Allah” watan ukuba daga Allah, domin hanasu wannan laifi dashi ukubace daga Allah bawai daga mutum ba, ya wajaba akan mutane suyi koyi da ita, domin shine mafi sanin ga halayen mutane da abunda ya dace dasu na al'amuran su da duniya, dukda kasancewar ukubar yanke hannun barawo tafi zama tsawatarwa da kuma hanashi aikata wannan laifi sama da ukubar daurewa a kurkuku har wayau kuma tafi zama mafi tausayi ga barawo da kuma mutane baki daya!! Kasancewar tana hana barawo aikata laifi wanda tsaro zai yadu tsakanin mutane suyi rayuwa cikin natsuwa suna masu aminci basa tsoron wani akan dukiyoyin su da abunda suka mallaka, haka yake kuma mafi rahama ga barawo kansa domin zata tsiratar dashi daga cutarwa na kurkuku, abu ne sananne cewa al'ummar kurkuku al'umma ce wacce ta tara masu laifuka iri daban daban wannan cutarwan tana halakar da me laifi kansa sannan kuma ta halaka al'umma baki dayan su, daga cikin wannan cutarwa kuwa akwai abubuwa masu zuwa kamar haka:

 

Illolin kurkuku:

 

  1. SANYA ME LAIFI YA KARA ZAMA HATSABIBI: daga cikin cutarwan kurkuku shine daure me laifi koya kankantan laifin sa a cikin al'umma mujirimai wanda zai koya a cikinta dayawa na laifuka daban daban mabanbanta kamar jami'a ce wacce mujirimai suke musayar fasaha na laifi a cikinta, me karamin laifi zai hadu da masu manyan laifuka ta yadda zai koya daga garesu salo na aikata laifuka na daban wanda sukafi nashi laifin hatsari, daganan sai wannan me karamin laifi na dawo cikin al'umma bayan an sake shi daga kurkuku a matsayin babban me laifi wanda yafi zama hatsari ga al'umma, yadda wannan mujirimai suke kulla abota atsakanin su wacce zata dore har zuwa fitan su daga cikin kurkuku, wannan zata hada kungiya na mujirimai sabuwa wacce zata kunshi me kisa da me safaran miyagun kwayoyi da masanin magunguna da me yin manhaja na na'ura me kwakwalwa tare da masanin makamashin nukiliya,babu abunda ya hadasu face shigansu kurkuku domin zartar masu da ukuba akan laifukan su mabanbanta a wurin girman su da yanayin su!!! Wannan al'amari me hatsari ne cikin ukubar kullewa a kurkuku wanda yake janyo hankula dayawa na masu kirkiran doka kara duba domin raba alaka tsakanin yan cikin kurkuku a lokacin da suke ciki, wanda wannan nazari ya tabbatar da gazawanta tun ba'aje ko ina ba saboda gagaran haka wurin aiki aiwatarwa a aikace, domin kuwa idan aka rarraba tsakanin yan kurkuku zai samar da matsaloli na hankali da kuma kabilanci a tsakanin su, da kuma bangaren kudin da za'a kashe masu wanda hakan zaija kashe kudi masu tarin yawa cikin dukiyar mutane wanda ake tattarawa ta hanyar harajin da suke biya domin gina kurkuku masu yawa manya da kuma na'urori wanda za'a iya rarraba wannan yan cikin kurkuku dashi!!!.
  2. KISAR MUMUKE GA MAI LAIFI NA ZUCI DANA HANKALI: lallai ukubar kurkuku tana lalata halin tunanin mutum da kuma gamawa da rayuwan sa a hankalce ga yan kurkuku baki daya a cikin mafiya wayan lokuta daga shigansa kurkuku, an tsare shi a cikin keji kamar dabbobi masu cutarwa da kuma nesanta shi daga al'ummar sa, kuma idan ya fito bayan y agama cinye lokacin da aka deba masa na zama a wannan kurkuku zai dawo cikin al'umma yana me yawan nesanta daga garesu da kuma zama hatsari yadda rayuwa tare da al'umma a karo na biyu zai masa wahala, kamar yadda zai dawo da matsaloli masu tarin yawa na zuciya da kabilanci wanda cucarwan su baya boyuwa.
  3. KISAR MUMUKE GA MAI LAIFI TA BANGAREN TATTALIN ARZIKI: lallai ukubar kurkuku tana lallata rayuwan tattalin arziki ga wanda aka kulle da kuma kasheshi baki daya daga lokacin da aka kulleshi, idan ya kasance ma'aikaci ce to za'a koreshi kai tsaye daga wannan aiki nashi, idan kuma dan kasuwa ne to kasuwancin sa zai mutu kuma aikin say a lallace abunda yakan yake jawo lallacewar rayuwan iyalansa ta bangaren tattalin arziki da kuma dukkanin mutanen da suke karkashin kasuwancin sa, ma'aikacin da yake aiki a a karkashin sa zasu rasa ayyukan su wanda cucarwan hakan zai koma ga iyalan su batare da sunyi laifin komai ba!!.
  4. KISAR MUMUKE GA MAI LAIFI TA BANGAREN ZAMANTAKEWA: lallai ukubar kurkuku tana gamawa ga rayuwan wanda aka kulle ta bangaren zamantakewa, to ma wai wani rayuwa ne ta zaman takewa zai kasance ga mutumin da aka kulle a kurkuku da kuma nesanta shi daga iyalin sa da rayansa da yan uwan sa da abokan sa?!!
  5. UKUBA NA ZAMAN TAKEWA GA DUKKANIN WANI IYALIN ME LAIFI: lallai iyalin me laifi wanda aka kulle azaba da zuciya da zamanta kewa zai samesu saboda kulle shi da akayi aka nesanta shi dasu, wannan matar da aka dauke mijinta, wannan uwa wanda aka nesanta yaronta daga gareta, ga yara kanana wanda aka haramta masu mahaifin sub a tare da sunyi wani laifi ba!! to ta yaya wanda aka rufe zai iya kula da bukatun matar san a zuciya dana tattalin arziki dana sha'awa dana zamantakewa, kuma ta yaya zai iya tarbiyyan yaran sa da nuna masu tausayi da kula dasu, kuma ta yaya zai iya kula da mahaifiyar sa idan sun kasance mara sa lafiya ko kuma tsofaffi?! A cikin hakikan alma'ari lallai kulleshi da akayi kamar an kulle su ne suma tare!! Wannan shine yanayin idan ya kasance wand aka kulle na miji ne amma idan ya kasance macece aka kulle kuma tana da yara kanana wanda take shayar dasu basu da wanda zai rene su da kuma kula dasu, wannan wani irin zuciya ce mara tausayi wanda take raba tsakanin yara kanana da mahaifiyar su ta kuma barsu cikin wasu kungiyoyi na rainon yara cikin kasa!! Wace irin reno ne wannan kungiya zatayi ga wannan yara wanda aka nesantar dasu daga mahaifiyar su, gaskiya ne zasu basu abinci abunsha da tufafi sai dai bazasu iya nuna masu masu tausayi ba da rahama ta mahaifiya da kuma tarbiyya na gari ba!! babu shakka cewa hakan zai haifar da al'umma masu ciwon zuciya da karancin halaye nagari wanda illar hakan zai bayyana a gaba yanayin al'umma bazaiyi daidai dasu ba!!.
  6. KISAR MUMUKE GA MAI LAIFI TA BANGAREN SIYASA: lallai ukubar kurkuku mutuwa ce na mumuke sannan kuma me sauri ga mai laifi wanda hakan zai iya zama a hakika wankakke daga zargin abunda aka jingina masa na tuhuma, a cikin wata kasa na kasashen da suka ci gaba an kirkiri wata tuhuma wacce bata da tushen gaskiya na satan kudin kasa ga wasu manyan manyan yan siyasan kasar, kuma hakika kasashe dayawa na kasashen da sukaci gaba sun wasafata wannan tuhuma a matsayin ta karya kuma anyita ne domin wata manufa na siyasa domin a lallata wannan mutumi suna a cikin mutanen sa cikin harkokin san a siyasa, ya kuma kasance zabi ne biyu a gaban hukumar sa, kodai kodai ta tsareshi ko kuma tayi masa takunkumi a harkokin san a siyasa ta hanyar tsareshi da kuma nesanta shi daga al'ummar sa da mutanen sa!!!.
  7. LALATA TATTALIN ARZIKIN KASA DA KUMA DUKIYAN YAN KASA TA HANYAR DA BE DACE BA: lallai kudin da za'a kashe wurin gina kurkuku da gyaran sa da kuma kudin tsaron sa da sauran ayyuka akan sa kamar me gadi da soja makaman da za'a siyan masu da kuma kudin motar da zai rika zirga zirga da yan kurkuku zuwa kotu da kuma kudin zirga zirgan masu tsaron su daga gidajen su zuwa wurin aikin su da kudin abincin su da zaunar da yan kurkukun acikin sa, wannan dukkanin su nauyi ne na kashe kudi wanda mutane masu daraja zasu dauka wanda aka sata daga garesu gabanin haka, hakan kuwa saboda kasa tana kara haraji ne akan kudaden yan kasa masu dajara domin samun kudin da zata kula da wannan yan kurkuku, ta wani ma'anar kuma na daban hakan yana nufi dan fashi ya masu sata gabanin a kama shi sai kuma gashi yana masu sata yana cikin kurkuku amma ba bayan gida ba kai shaye ba!! da wannan hanya ne dan kasa me daraja zai iya zama dan fashi shima na daban sabida wannan tsanani na haraji wanda yake kansa, maimakon ya rika kashe kudin sa domin karantar da yaran sa da kuma kyautata bukatun su na rayuwa sai aka sanya shi yana ciyar da yan fashi wanda yamai sata!! Wanda da ace wannan kudi kasa zata ciyar dasu domin kyautata yanayin samun wuraren samun kudi da ba'a samu dan fashi ba cikin al'umma!! Kara ahan wannan dokoki wanda mutane suka kirkira a karkashin ukubar dauri a kurkuku ta haifar da runduna nay an kurkuku da kuma runduna masu tsare su na sojoji da masu kula dasu ta kuma sanya ko wani runduna a acikin su yana da kaso akan al'umma maimakon ta sanya hanyoyi na kara tattalin arzikin su da habaka cikin al'umma!!

Wannan wusu ne daga cikin cutarwa na ukubar kurkuku akan mutane na al'umma, da haka da za'a cema barawo ya zaba tsakanin ukubar yake hannu (tafin hannu) da kuma kulle shi a kurkuku na tsawon shekaru da ya zabi yanke hannun sa daya maimakon a lallata masa rayuwa baki dayanta ta fuskan zamanta kewa da tattalin arziki da zuciya da hankali harda siyasa! Kuma da za'a za'aba wannan dan siya zabi akan haka da ya zabi yanke hannun shi daya (tafin hannu) da ana daure shi a kurkuku, da haka ne ukubar yanke hannu zata zama rahama a gareshi da azaba akan wanda aka jingina masu tuhuma na karya, domin kuwa maganar gaskiya shiya hakan bazai boye masa harkokin san a siyasa ba sannan zai kare kansa daga zagin kudin jama'a da halaye!!.

Ni kuma akan wannan wannan abu a matsayi na lauya da ma'aikaci a bangaren hakkokin dan Adam, ina kira ga kungiyoyi na kare hakkin dan Adam da majalisar dinkin duniya da ta dauki mataki na hana wannan ukuba mummuna me lallatawa da daidaitawa, ukubar daur barawo a kurkuku!!

 

 

 

Aiwatar da ukubar yanke hannu (tafin hannu) a aikace: malam Salihu Alfauzan Allah ya kiyaye shi ya fadi cikin daya daga cikin karatukan sa cewa a cikin shekaru goma da suka shude yaji labarin yanke hannun barawo mutum biyu kawai ko uku kacal a kasar Saudiyya. Kuma hakika da zama kwatanta wannan adadi da adadin dubunnai na wanda aka kulle su a kurkuku na shekaru da daya cikin kasashe dayawa wanda suka ci gaba da munga madarar rahama ta ukubar yanke hannu ga barawo da kuma al'umma baki daya, domin kuwa lallai zata iya kiyaye tsaro na al'umma da kuma tsaro ga barawo ta hanyar hanashi yin sata da wannan ne babu wani ukuba da zai same shi.

 

SHARUDDA NA YANKE HANNU (TAFIN HANNU):

 

Al'amarin ba kamar yadda wasu ke tunani bane cewa da zaran barawa yayi sata za'a yanke masu hannu ba kai tsaye a'a makasudin zartar da haddin yanke hannu ga barawo bawai domin cucar dashi bane domin yayi sata, manufa it ace hanashi yin wasa da tsaron mutane da kuma fada masu gidaje domin sata, kamar yadda ukuba ba'a aiwatar da ita akan ko wani barawo sai a wasu hali kebantacce yan kadan, domin a aiwatar da ukubar yanke hannu ga barawo dole ne a ciki wannan sharudda kamar haka:

  1. Ya saci abu a cikin Hirzi (wurin da aka boye), Hirzi shine wurin da mutane ke boye kudin su kamar asusu ko kuma makamancin haka. Surar sata ba'a daukan ta sata wacce take sanya yanke hannu a wurin dayawa daga cikin maluman fiqihu sai dai idan yayi sata daga cikin wannan asusu, kamar barawo ya bude kwadon gida ya shiga ko kuma ya karya kofa ko taga, ko kuma ya fasa rufin gida ko Katanga,ko kuma ya shigar da hannun sa aljihun wani domin satan abunda ke ciki da makamantan haka.
  2. Ya fitar da wannan abu daga asusu, idan aka kama barawo gabanin ya fitar da abunda ya sata daga cikin wannan gidan ko kuma asusu, baza'a yanke masa hannu ba, za'a ladabtar dashi ne kawai da wata ukuba na daban gwargwadon abunda alkali ya gani. A cikin wannan akwai rahama da kuma kawar da shubuha, domin kuma me wannan asusu zai iya zaton cewa daga lokacin dayaga mutum ya shiga cikin gidan sa ko kuma wurin ajiyan sa da wata manufa da badan wacce ba sat aba.
  3. Wanda akama satan ya nemi kudin sa, idan be nemi kudin nasa ba baya wajaba yanke hannu. Hakika manzon Allah s.a.w yace:

“ku rika yafiya akan haddi a tsakanin ku, duk abunda yazo wuri nan a haddi hakika ya wajaba” (Sahihu Abu Dawud)

A lokacin da Safwan dan Umayya ya kama barawo a cikin masallaci bayan ya kaishi gun manzon Allah s.a.w yanason kuma ya yafe masa, sai manzon Allah s.a.w yace masa:

da ace hakan ya kasance ne gabanin kazoo mun dashi (sahihu Abu Dawud)

  1. Abunda aka sata yakai nisabi (wani yawa na kudi wand aka gindaya), idan ya gawa daga hakan baza'a yanke hannu ba.
  2. A tabbatar da satan da shedu biyu maza adilai ko kuma da ikirarin barawon akan kan sa sau biyu.
  3. Ya kasance barawo ya dauki abune a boye, idan ba'a boye bane baza'a yanke hannu ba, kamar da zai kwaci kudi da ta fuskar galaba da fin karfi a idon mutane ko kuma ta hanyan karfin tuwo, saboda wannan me kudin zai iya neman taimako na amsan kudin a hannun wannan mutumi, ko kuma da ace zai dauka ta fuskar ha'inci kamar yanda za'a bashi ajiyan wani abu ta hanyar aro ko ajiya sai ya dauki wannan abu ya kuma yi ikirarin cewa ya bace, dalili kuwa akan haka shine kudin ya kasanci a karkashin kulawan sa kuma an masa izini na shigan sa wannan gida ko ma'aji, hakika manzon Allah s.a.w yace:

“babu yanke hannu akan wanda yayi ha'inci ko kuma wanda yayi kwace ko wanda yayi firze ya ruga a guje da gangan” (tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi)

Kuma an tanbayi manzon Allah s.a.w akan: dabinon da yake rataye? Sai yace: “duk wanda ya dauka domin yaci saboda yunwa ko kuma bukata, be dauka bay a zuba a rigan sa, to babu komai akansa, duk wanda ya fita da wani abu daga cikin sa to akwai tara nunkin sa akansa da kuma ukuba, wanda kuma ya saci wani abu daga cikin sa an killace shi a wurin da ake ajiyan dabino kuma kimar wannan dabino yakai daya bisa takwas na rigan da akae sanyawa a lokacin yaki to za'a yanke masa hannu” (sahihu abu dawud)

Daga cikin wannan hadisi zamuga cewa ukubar yanke nhannu shine kololuwan ukuba ga barawo, wanda gabanin haka akwai wasu ukuba na tara na kudi da makamantan sa.

  1. Barawon ya kasance balagagge me hankali babu yanke hannu akan yaro ko kuma barawo, domin dauke masu nauyi na ibada akan su.
  2. Ya kasance barawon da zabin sa yayi satan, babu yanke hannu ga wanda aka tilasta mawa ko kuma me uzuri.
  3. Ya kasance yasan haramcin hakan, babu yanke yannu akan jahili ga haramcin sata kuma hakan sha banban da dokoki ba wanda mutane suka kirkira wanda ya nassanta cewa”babu uzuri ga jahili", da ace mutum zai aikata laifi bisa jahilcin cewa hakan laifi ne babba dokoki wanda mutane suka kirkira zata zartar masa da ukuba sannan kuma bazata amshi uzirin sa ba da jahilcin sa cewa wannan aiki fa laifi ne babba, a cikin wannan tarko ne matafiya dayawa masu zuwa kasashe baki domin bude ido ko kuma neman magani ko karatu ko kuma makamancin haka suke fadawa saboda jahilcin su da dokokin wannan kasa.
  4. Ya kasance wannan barawo bashi da wata shubuha cikin wannan kudi daya sata, domin haddi ana kawar dashi da shubaha, misali mutum ya saci abunda yake da hakki acikin sa, da ace uba zai saci kudin yaron sa babu yanke hannu, haka kuma kakanni maza da mata babu yanke hannu akan su cikin abunda suka sata na dukiyar jikokin su, idan yaro ya saci kudin ubansa babu yanke hannu saboda yaro ana masa mu'amala cikin rangwame da sauki cikin dukiyar mahaifin sa a al'adance, idan daya daga cikin ma'aurata ya saci kudin dayan babu yanke hannu. Idan musulmi ya saci kudi daga cikin baitul mali shima babu yanke hannu saboda ko wani musulmi yana da hakki cikin baitul mali. Idan wanda yake bin bashi ya saci kudi daga cikin kudin wanda yakebi bashi da sharadin cewa wannan wanda yaba da bashin yana inkarin wannan bashi ko kuma wanda basa son biyan bashin su da ya saci gwargwadon hakkin sa kada ya kara komai akan haka to shima babu yanke hannu akan sa. idan mutum yayi sata domin lalura dan kare ransa daga halaka kamar mutum yayi sata domin toshe yunwa ko kishi me kisa babu ukuba akan sa kuma babu yanke hannu da sharadin ya kasance abunda ya sata gwargwadon abunda zai kare kansa daga halaka ne na yunwa ko kishi.
  5. Ya kasance barawon be janye ba daga ikirarin sa nayin tasa, idan dalili akan wannan sata nashi ikirari ne wanda yayi dakan sa gabanin a yanke hannu sai ya yanje daga wannan ikirari, to wannan yanke hannu ya fadi akan sa, domin janyewa daga ikirari yana haifar da shubuha.

SHUBUHA: mutum zai iya tambaya cewa me yasa ake yanke hannu ga wanda ya saci wani adadi na kudi wanda ya wuce nisabi, amma kuma ba'a yanke hannun wanda yayi kwace ya ruga a guje wanda zai iya yuwa abunda ya kwata kudi ne me yawan gaske?

Ibn Kayyim - Allah yayi mashi rahama yace - yace cikin bada amsa akan haka:

“wanna yana daga cikin cikar hikimar Allah, domin lallai barawo bazai yiwu a shamakance shi ba, domin kuwa yana fasa rufi da fasa asusu da balla kwado, kuma me wannan kudi bazaiyiwu yin shamaki ba ko kuma kariya ga kudin sa da sama da wannan abubuwa, da ace ba'a shar'anta yanke hannun ba da mutane sun ika yima juna sata, kuma da cucarwan ya girmama, da kuma aikin satay a girmama, sabanin wanda yayi kwace ko kuma ya fisge ya gudu, wanda yayi kwace da karfi a idon mutane, zai iya yuwa su amshi wannan abu daya kwata, ya rabu daga hakkin zalumci, ko kuma suyi masa shed agaban alkali. Shi kuma wanda ya fisge ya gudu lallai kodai ya kwaci kudin ne a lokacin da me shi ya gafala da makantan sa, baya wuce kodai sakaci ne wanda yaba wannan wanda ya fisga dama fisga, idan kuma bah aka idan dai ya kiyaye kudin say a basu kariya yadda ya kamata babu yadda za'ayi ya fisga ya gudu.”

 

Yadda ake yanke hannu:

Babau sabani a tsakanin maluman fiqihu cewa ya wajaba lura da kyautataw awurin tsayar da haddin sata, sai akai barawo zuwa ga wurin yanke hannu cikin tausasawa, ba tare da muzgunawa ba ko to zartawa ko zagi saboda fadin manzon Allah s.a.w:

“kada ku zama mataimaka ga shedan akan dan uwan ku” (silsilatul sahiha 1638, kuma sheikh Shu'aibu Al arnud yace: hadisi ne hasan)

Kamar yadda ya wajaba akan shugaba daya zabi lokacin daya dace da yanke hannu ta yadda zai nisanci lokacin zafi da sanyi me tsanani, kada ya zartar da haddi akan barawo a lokacin rashin lafiyar sa wanda ake fatan warakan sa, kuma kada ya zartar da haddi akan me ciki ko me jinin haihuwa ko kuma akan ko wani mutum wanda zartar da wannan haddi zai iyayin sanadiyyar mutuwar sa. idan yaje wurin yanke hannu sai ya zauna, ya kuma daure wurin dakyau domin kada yayi motsi sannan kuma a yi amfani da wuka me kaifi wacce zata yanke a lokaci daya, idan kuma yasan hanyar da tafi sauri wurin haka sai yayi amfani ita.

SHUBUHA: mutum zai iya fadi cewa: hakika naga yadda aka yanke hannun barawo daga wasu mutane musulmai cikin kasar larabawa wanda yak eke kewaye da ita, wanda wannan abu daya gani be dace ba, sun yanke hannun sa da wuka mara kaifi adadi dayawa har saida suka yanke hannun, kuma suna murna da wannan aiki nasu suna masu fadin Allah Akbar!!.

AMASA AKAN HAKA HAKA: lallai wannan aiki aiki ne na mutumin daya sabawa karantarwan shari'ar musulunci a wannan bangare baya halatta yanke hannun barawo a shari'ar musulunci ta irin wannan hanya tasu da sukayi, kuma aikin nan nasu yana nuna jahilcin su ne da karantarwan shari'ar ta hanya me kyau, hasalima wannan aiki nasu sun bata surar shari'ar musulunci ne me tsarki dashi! Fuskan sabawan su kuwa da karantarwan shari'ar musulunci ta fuskoki ne daga cikin akwai:-

  1. Lallai haddi ba'a zartar dashi a cikin kasar yaki: hakika manzon Allah s.a.w yace: “kada ku yanke hannu a cikin yaki” (Tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi cikin sahihul jami'u: 7397, da almishkat: 3601)

Kuma Ibn kayyim yace: “wannan haddi ne cikin haddin Allah kuma ya hana a zartar dashi cikin yaki, domin tsoron abunda zai haifar wanda Allah yafi kyaman sa sama da koreshi ko kuma ajinkirtashi, na abunda zai shafi mushrikai kabilanci da kiyayya kamar yadda Umar da Abuddarda'i da Huzaifa da sauran su suka fadi.” 

  1. Rashin murna domin zartar da haddi akan masu lafi: manzon Allah s.a.w be kasance ba yana murna da hakan hasalima ya kasance yana kin haka kuma yana hana hakan sai dai kawai zartar da haddi wajibi ne da kuma da'a ga Allah madaukaki da kuma rko da umurnin Allah, Abdulahi dan Mas'ud yace: lallai ina tuna mutumin farkon da manzon Allah s.a.w ya yanke ma hannu, anzo da barawo sai yayi umurni da ayanke masa hannu, sai gashi fuskar manzon Allah s.a.w ta baci, sai sukace: ya manzon Allah, kamar bakaso hakan ba? sai yace: “me kuwa zai hanani?! Kada ku zama yan uwan shedan akan dan uwanku, baya halatta ga shugaba idan aka kawo masa haddi yaki zartar dashi, lallai Allah me yafiya ne kuma yana son masu yafiya (kuma yayi yafiya da hakuri ko bakyason Allah ya gafarta maku ne, kuma Allah me gafara ne da rahama).” (Silsilatul sihiha: 1638, kuma Sheikh Shu'aibu al arnud yace: hadisi ne hasan)

Wannan itace ukubar barawo cikin shari'ar musulunci wanda muke gani ta fuskan hankali da tunani da kuma nan gaba cewa tafi zama daidai da amfani domin gyaran al'umma da kiyaye su, yanzu zamu ga ukubar hakan acikin wasu addininan  

 

UKUBAR SATA A CIKIN LITTAFI ME TSARKI:

 

  1. JIFA DA KUMA KONA BARAWO DA IYALAN SA: SAFAR YUSHA'U (1/7): (1 sai bani isra'ila sukayi ha'inci cikin haramun, sai Akhan dan Karami dan Zabdi dan Zarah daga jikokin Yahuza ya dauka daga cikin haramun, sai fushin Ubangiji ya lullube bani isra'ila… 10 sai ubangijin Yusha'u yace: “tashi! Me yasa ka bata ranka? 11 hakika bani isra'ila sunyi laifu, kai sunyi ketara alkawari na wanda na umurce su dashi, sun dauka daga haramun, kai sunyi sata, sunyi inkari, sun sanya cikin kayayyakin su. 12 bani isra'ila basusamu daman tabbata ba agaban makiyan su. Suna juya keyar su a gabann makiyan su domin sun kasance haramtattu, kuma bazan kasance tare daku ba idan kuna boye haramun a tsakanin ku….”19 sai Yusha'u yacema Akhan: “yaku bani isra'ila yanzu ku bada tabbata ga ubangijin bani isra'il, sai ya tabbatar masu ya kuma bani labari yanzu abunda zan aikata. Kada kaji tsoro na.” 20 sai ya akhan ya amsama Yusha'u da cewa: “gaskiya ne lallai nayi kuskure ga ubangijin bani isra'il kuma na aikata kaza da kaza. 21 naga wani mayafi na shan'ariyya me tsada a cikin kayan ganima, da kuma azurfa me nayin shakil guda dari biyu, da harshen a zinari wanda nauyin sa yakai shakil hamsin, sai nayi sha'awar sun a dauka. Ga wurin dana birne su cikin kasa a tsakin schemata, da kuma zinari a karkashinta.” 22 sai yusha'u ya aika dan sako sai yayi gudu zuwa ga wannan shema sai gashi ya birne su a cikin shema da azurfa a karkashinta. 23 sai ya dauko su ya kawo ma yusha'u da kuma sauran bani isra'ila, sai suka shinfide su a gaban ubangiji. 24 sai yusha'u ya dauki wannan mayafi da zinari da harshen a zinari tare dashi akhan da bani isra'ila da yaransa maza da mata da shanayen sa da jakunan sa da dabbobin da da shemar sa da dukkanin abunda ya mallaka, yah aura dashi zuwa ga koramo na akhur. 25 sai yusha'u yace: “yadda ka hufantar damu haka ubangiji zai hufantar dakai a cikin wannan rana!!. Sai bani isra'ila suka mike suka jefe shi suka kuma jefe iyalansa sannan suka kona su dukkanin su da wuta, 26 sai suka dauka dutse babba akan akhan har zuwa wannan rana tamu tayau. Sai ubangiji ya daina wannan fushi da yakeyi dasu).
  2. GICCIYEWA HAR SAI MUTUM YAM UTU: INJILA NA MATA (27/37): (37 sai suka sanya a samar kansa dalilin sa a rubuce: “wannan shine gicciyayyen sarkin yahudawa.” 38 a lokacin da aka gicciye lisan a tare dashi, daya a damar sa daya kuma a hagun sa).
  3. MUTUWA: SAFAR AL TASNIYA (24/7): (7 idan aka samu mutum ya saci rai daga dan uwan sa bani isra'il ya sace shi ya siyar dashi, wannan barawo zai mutu, sai ya cire sharri daga tsakiyar ka).
  4. BAUTA DA MAYAR DASHI BAWA: SAFAR AL KHURUJ (22/1-3): (ya wajaba akan barawo ya biya awanda yayima sata abunda ya sata, idan kuma bashi da kudi wanda zai isa biyan abunda ya sata, to anan lokacin za'a siyar dashi kamar bawa, sai a bayar da kudin shi ga wanda yayima sata).

Amma a cikin musulunci kowa yana daukan ukuba da laifin abunda ya aikata ne na laifi baya ketarewa zuwa ga wanin sa, Allah madaukaki yace:

“kuma rai bata daukan wani lafi sai akanta; kuma wani rai baya daukan zunubin wani rain a daban; sa'annan zuwa ga ubangijin ku zaku koma sai ya baku labari akan abunda kuka samu sabani” (suratul an'am ayata 164)

 

HANA AZZALUMI ZALUMCI CIKIN SHARI'AR MUSULUNCI DA KUMA KARE KAI

KARE KAI A CIKIN SHARI'AR MUSULUNCI:

 

Idan wani yayi ta'addanci akan wani a cikin dukiyar sa ko ran sa ko mutuncin sa, ko kuma ya fado masa yana neman kwace masa kudi ko ran sa a bisa zalumci, ya halatta ga mutum ya kare kansa ko kuma hana wannan zalumci gwargwadon idon sa, za fara da na kasa haka dai, idan ya smau nasarar mayar da wannan dan ta'addan da magana to bazayyi amfani da duka ba, idan ya iya kare shi da hannu to bazayyi amfani da sand aba, idan kuma ya iya mayar dashi ta hanyar yanke masa wani gaba ya haramta ya kashe shi, idan kuma bazai iya kare shi ba sai ta kisa to ya halatta ya kashe shi kuma babu wani lamuni akansa. idan kare kan nashi zai yiwu ne da guduwa to ya wajaba ya gudu, domin wanda akayima ta'addanci an mashi umurni ne da kare kansa da Karamin mataki[38], Allah madaukaki yace:

“duk wanda yayi ta'addanci akan ku to kuma ku rama kwatan kwacin irin ta'addancin dayayi maku; kuma kuji tsoron Allah kusani cewa lallai Allah yana tare da masu takawa” (suratul bakara ayata 194)

 

KARE KAI DAGA AZZALUMI YANA DA SHARUDDA DAGA CIKIN SU AKWAI:

  1. YA KASANCE AKWAI TA'ADDANCI: watan ma'ana ayi ta'addanci akan mutum ba tare da wani hakki ba.
  2. YA KASANCE TA'ADDANCIN A YANZU NE: da ace ta'addanci zai kasance ne ta hanyar sanya mutum aikata wani aiki anan gaba baya halatta kare kai saboda babu kare kai gabanin ta'addanci. Sai dai da ace ya shahara dayin haka ya kuma nunashi da abunda yana kisa cikin mafiya yawa kamar makami to yana daga cikin hakkin sa kare kai.
  3. GABATAR DA HUJJA DA DALILI wanda zai tabbatar da ta'addancin da aka masa daga wurin wannan azzalumi, amma ba'a amsa magana kawai; wanda da zai zubar da jini gabanin shi da hujjar kare kai daga ta'addanci.
  4. BI MATAKI MATAKI WURIN KARE KAI: abunda yake nuni akan bin mataki mataki wurin kare kai shine fadin manzon Allah s.a.w ga mutumin da ya tambaye shi:

“ya manzon Allah shin me kake gani da ta'addanci akan dukiya na? sai yace: ta hadashi da Allah ka kuma nuna mashi griman Allah sai yace: idan yaki fa sai yace: ka hadashi da Allah sai yace: idan yaki fa? Sai yace: ka hadashi da Allah sai yace: idan yaki fa sai yace: to ka yake shi, idan ya kashe ka to kana aljanna, idan kuma ka kakashe shi to yana wuta” (musnad na Ahmad kuma albani ya ingantashi kuma shu'aibu al arnud yace: hadisi ne ingantacce)

 

KARE KAI ACIKIN LITTAFI ME TSARKI:

 

Safar al khuruj (22/2): (2 idan ka samu barawo yana kokarin hana rami sai ka dukeshi yam utu, bashi da jini).

Amma abun fadi shine shine fassarar yunaniyya wanda aka yarda dashi na nassin da muka Ambato, an rubuta shi ne da wani yanayi wanda ya banbanta da fassarar larabci, sai yace: safar al khuruj (22/2): (2 idan kuka kama dan fashi yana sata sai aka kashe shi a wannan wuri, babu komai akan wannan wanda ya kasheshi din).

(Αν ο κλέφτης συλληφθεί επαυτοφόρω να κλέβει, θα εκτελείται επί τόπου, κι εκείνος που θα τον σκοτώσει δεν θα φέρει ευθύνη για το φόνο του.)

 

KARE KAI CIKIN DOKOKIN DA DAN ADAM YA KIRKIRA:

 

Kamar yadda ya gabata kuma muka gani cewa makura cikin tabka da warwaran dake cikin dokoki na dan adam wurin kayyade menene laifi kuma menene hakki, haka dai wannan tafka da warwara yake wurin kayyade ukuba wacce ta dace ta bai daya wurin zartarwa cikin mabanbanta kasashe wanda daga cikin aikinta ne kiyaye tsaro da kuma tsawatarwa da hana masu laifi, lallai wannan tafka da warwara da nakasu muna ganin sa har wayau cikin bangaren kare kai daga azzalumi, ta wani fuskan kuma akwai wasu dokoki wanda suka tsaya tsaya a bayan mujirima daga kisa sannan kuma akwai wasu dokoki da suka tsaya a bayan hukuncin basa bayan mujirimi, misali a kasar amerika ba'a zartar da dokar “tsayuka akan kasar ka”[39] ba wanda zataba masu gida damar amfani da karfin su me kisa daga lokacin da sukaci cea suna karkashin hatsari acikin gidan su, kuma wannan doka ya jawo cece kuce da sabani na siyasa da doka me tsanani, kuma an fita yin zanga zanga masu fada da wannan doka, a cikin jihar Connecticut na amerika wani malami ya shiga gida sai ya tarar da wani mutum a zaune yana dauke da wuka a hannun shi, sai kawai ya budema wannan mutum wuta cikin gaggawa ya kashe shi, sai ya bayyana bayan haka cewa wannan mutumi fa yaron shi ne saurayi. Amma a amerika kofar kare kai yaga kece kuce na siyasa da doka me yawa, a daidai lokacin da da shugabannin biyu David Cemarom da ministan shari'a Chris Gerlynge[40] suke kokarin wutar da doka wanda zayyi fada da dokan masu fadowa gida, sai dai majalisar dokoki na yancin birane sukaki yarda da wannan doka suna masu cewa wannan siyasa siyasa wacce za'a sakankanc mata.kuma ya kamata anan muyi hujja da maganar minister shari'a Christ gerlynge: “babu wani a cikin mu wanda yake da hakkin sanin yadda zayyi idan wani ya fada masa gida, babu wani a cikin mu wanda yake da hakkin sanin yadda al'amarin zai zama me fadi idan mukaga mutum a zaune a gidan mu a tsakiyan dare, ko kuma nawa ne fadin sa a lokacin da muke sani cewa iyakan mu suna cikin hatsari, kuma zaka iya sanya zafin wurin yadda bazakayi tunanin komai ba sai kiyaye masoyan ka, Sai dai har yanzu baka da yakinin cewa lallai doka zai baka goyon baya, kuma ni ina ganin cewa masu gidaje suna abunsu ne dai dai da fidira, kuma maganar gaskiya itace ya wajaba ai masu mu’amala a matsayin sune aka kawoma hari ba a matsayin mujirimai ba. Muna kokarin kate wani abu na daban me matukar muhimmanci, wanda ake kira da suna”duka biyu kuma zai kasance ne a waje”, da zaka aikata wani aikin na rashin imani ko kuma kayi kwace sau biyu zaka samu hukuncin dauri a kurkuku na karshen rayuwan ka!! Bayan zaben daya wuce munyi alkawarin cewa zamu dau gudanar da dabara na ci gaban hakkokin dan adam wanda yafi karfin sa, lallai wasu bangare na mahaukata ne wanda dage damtse domin yakar al'ummar mu, sunada ikon dawo da kotuna zuwa karkashin ikon su anan gaba, kuma za'ayi kira da cewa hakan toye hakkin dan adam ne idan mun tashi tsaye domin korar su zuwa kasashen da suka fito. Mun sani cewa bazamuyi iya mu'amala da wannan abu ba ta hanyar da muke so, sai dai zamu iya ci gaba da hanyar da muke kai ayanzu.” Ya wajaba ka sanya kanka a wurin namiji ko mace na mu'amalar da zakayi idan barawo dan ta'adda ya shigo maka, kuma ya kasance kare kansa yana hade da fushi da damuwa da kuma tsoro, kuma babu wani lokaci na kare kai na tsoro.”

Anan wurin zance ma firaminista David Cemaron: “kaza iya yin aikata komai matukar bawai bata dace bane ta hanya bararo, kamar misali bazai yiwu maka b aka soki dan fashi koda kuma da aiki ne wanda babu lura a cikin sa. sai dai gaskiya itace ya wajaba a sanya dokoki me karfi domin yin adalci ga masu gida, muce masu: a lokacin da dan fashi ya ketara maka gida ya shiga ciki a matsayin me kalubalantar iyalanka to hakika ya rasa dukkanin hakkokin sa.”

Wata daga cikin gidan jarida ta birtaniya masu karfafa yin doka me tsauri akan yan fashi tace: “ina tsammanin alkalai sunyi sakaci akan laifi me hatsari, kuma ina ganin cewa mutane sun samu matsala wurin taimakawa na ganin an dauki ukuba me tsanani game da dan fashi. Domin kuwa zaka iya fuskanta ukuba me tsauri akan aiki dan karami kamar laifin gudu a lokacin tuki da makamantan su, wanda kuma gashinan akwai wasu laifuka masu hatsari wanda ba'a masu ukuba ba me tsauri wanda zai dace da girman wannan laifuka"[41].

 

 

BABI NA HUDU

KARIN AURE A SHARI'AR MUSULUNCI DA KUMA KARIN AURE A DOKOKIN DAN ADAM.

 

  • Karin aure da kuma yin abokai mata dayawa da kuma canza mata.
  • Karin aure da kuma yin abokai mata dayawa cikin dokokin dan Adam.
  • Banbanci tsakanin mace ta biyu da kawa ta biyu.
  • Canza mata a cikin dokokin dan Adam.
  • Karin aure a cikin yahudanci da kiristanci.
  • Karin aure a musulunci.

 

 

 

BABI NA HUDU

Karin aure a shari'ar musulunci da kuma Karin aure a dokokin dan Adam.

Karin aure da kuma yin abokai mata dayawa da kuma canza mata.

 

Shari'ar musulunci ta halasta ma namiji Karin aure domin kiyaye dawwamar al'umma da iyalai, shi kuma dokoki na dan adam sun halasta yin kawaye a domin lallata al'umma da iyalai, zamu kawo maku da yardan Allah kwatanceceniya tsakanin Karin aure a shari'ar musulunci da dokan dan adam domin mugani wani shari'a ne ya dace da fidira da kuma kare hakkin mace da martabanta.

Lallai musulunci shine addini daya tilo wanda ya nassanta baro-baro akan Karin aure , Allah madaukaki yace:

“idan kuma kinji tsoron cewa bazakuyi adalci ba ga marayu to ku aure abunda ranku keso daga cikin mata biyu ko uku ko hudu; idan kuma kunji tsoron cewa baza kuyi adalci ba to ku auri daya ko kuma abunda kuka mallaka na bayi; wannann shi yafi dacewa domin kada kuyi zalumci” (suratun nisa'i ayata 3)

Amma kuma sauran addininan sun yarda da Karin aure babu adadi ga namiji. Gabanin mu kawo bayani akan matsayar addinai game da Karin aure zamu kawo matsayar doka na dan Adam akan haka.

 

KARIN AURE DA KUMA YIN ABOKAI MATA DAYAWA CIKIN DOKOKIN DAN ADAM.

 

Lallai Karin aure ko kuma yin kawaye yana da mana'ana daya ne a dunkule, shine cewa namiji zai iya bukatar cewa yanada mace sama da daya domin wasu dalilai nashi wanda zamu iya kawo wasu daga cikin su anan gaba, sai dai sakamakon ta karshe iri daya ne, itace cewa namiji yanada mata da kuma wata mace daban wand aba it aba, ko kuma mata da kawa ta daban wacce ba itaba!! A fuskar doka kuma wasu dokokin na dan Adam suna hana Karin aure suna cewa abu ne wanda yake kore halaye na masu kyau, amma adaidai lokacin da suna yin doka na halasta yin kawaye da kuma yin doka domin yin alfasha da karuwanci!! Watan da ace namiji zai auri wata mace ta daban sai hukuma ta sanin hakan to zai fiskanci shari'a a kotu saboda aikata wannan laifi na sha'awa da kuma lallata halaye a nasu ganin sannan kuma za'a masa ukuba da kullewa a kurkuku, amma idan yayi kawa bayan matar sa, kai koda zasu haifi yara ne da ita wanda bana halal ba, babu laifi da hakan, hakan ba laifi bane kuma babu ukuba akansa, saboda hakan a nasu ganin ba laifi bane ko kuma sha'awa ko lallata halaye a'a hakan yanci ne na mutum da kuma bude halaye!! Tare da sanin cewa banbanci tsakanin Karin aure da kuma yin kawaye shine samun takardan aure wacce take matsayin kwalla yarjejeniya wanda zai kiyaye hakkin macen ta biyu a lokacin aure, rashin samun wannan takarda yana nuna cewa wannan mace ta biyun kawa ce kawai wacce bata da wani hakkoki a dokance!! Shin dagaske ne hukuma tana fada ne da hana namiji yin mace ta biyu koda kuwa kawa ce, ko kuma kuma tana fada ne da wannan takarda watan wannan yarjejeniya daya kulla da macen ta biyu wanda ya lamunce mata hakkokinta akan sa da kuma wajabta mashi biyan wannan hakkoki?!! Da kuma wani ma'anar da daban shin laifin shine yin wata mace ta daban wacce ba matar shi ba koda kuwa aurenta yayi ko kuma kawa ce ko kuma laifin shine wannan sa hannun da yayi akan wannan takarda?!! Idan haramcin Karin aure ya kasance ne saboda cewa na miji kada yayi mata sama da daya kawai to ya zama wajibi yin kawaye ya zama laifi shima!! Hasalima maza dayawa a yanzu a kasar turawa basayin aure sun gwammace suyi rayuwan sub a tare da mace daya ba, domin ya samu daman canza kawaye dayawa cikin ko wani wata yayi zaman aure da it aba tare da wani alakada. To shin dokan dan adam ta magance wannan al'amari da mayar dashi laifi?!! Ko kuma hakan yana cikin yancin mutum ne namiji daya yayi rayuwan aure da mata dayawa wanda babu adadi?!! Abunda yafi muni akan wannan shine dokoki na dan Adam ta yarda da sana'ar karuwanci, yadda ake samun wasu wurare wanda aka masu rijista a hukumance, wacce take bautar da wasu mata da bayar dasu haya na awa-awa ga namiji wanda yakeson ha'intan matar shi. Kuma ko wace mace cikin wannan mata tanada rijista a hukumance nayin wannan aiki na karuwanci sannan tanada fiyel na biyan haraji wanda zata rika biyan haraji a duk karshen shekara ga hukuma matsayinta kamar sauran yan kasane nakwarai!! Hakika wannan al'amari ya yadu cikin kasashe masu yawa wanda suke hana Karin aure, hanya baya rabuwa da gidan karuwai!! Anan wurin muna cewa shima Karin aure sai a mayar dashi yanci cikin yancin mutum idan turawa sunason aiwatar dashi, musamman ma idan mun san cewa hakan baya yiwuwa sai da yardan namijin da macen, kamar yadda yin kawa da karuwanci baya kasancewa saida yardan namijin da macen, sai dai kawai kiyayyace da duk abunda yake na musulunci ne, Allah me girma yayi gaskiya: “kuma yahudawa ko kiristoci bazasu taba yarda ba dakai har sai kabi tafarkin su; kace masu shiriyar Allah itace shiriya; kuma idan kabi son zuciyan su bayan abunda yazo maka na ilimi to baka da wani majinbinci ko kuma mataimaki a wurin Allah” suratul bakara ayata 120.

 

BANBANCI TSAKANIN MACE TA BIYU DA KAWA TA BIYU:

 

Lallai namiji gabanin ya yanke yin mace ta biyu yana tunanin nauyin da hakan zai jawo akan wannan aure babba na wajibobin dake kan haka na hakkokin matar ta biyu shin na kudi ne ko kuma na shari'a, amma a cikin halin yin kawa abun yafi masa sauki saboda sanin cewa kawai nauyi da hakkokin wannan kawar ko yaranta yana kanshi ne a lokacin da take da ciki!! Wanda hakan yana bude kofar sharri da fasadi a cikin al'umma domin kuwa yana sanya namiji tsalle daga wannan kawa zuwa wancan kawa da burin silalewa dajin dadi, duk lokacin daya biya bukatar san a sha'awa da wanann kawa tashi sai ya nemi wata kawar kuma ta daban wacce zayyi wasa da ita da kuma lallata mata makoma!! Kuma mafiya yawan lokuwa wannan namijin bazayyi taka tsantsan ba wurin yin karya ga kawar tasa nason auren ta da kuma cewa abunda zai hana aurenta kawai shine hukuma bata yardan masa ba da karin aure kuma zai rabu da matar sa domin ya aure ta, duk wanda yayima matarshi karya da ha'intarta to me zai hana yayima kawar sa karya da ha'inci?!!

Dukda cewa wannan aiki (na yin kawa) yanada cutarwa akan namijin kansa, rayuwar sa zata kasance cikin asara da kunci kamar yadda me laifi yake rayuwa cikin buya domin bayason matar sa taganshi tare da kawar sa ko kuma taji yana labari akanta, wannan dabi'a kuwa dalili ne na karfi na nuna kuskuren wannan aiki wanda yake yi, domin kuwa da ace aiki ne me kyau da baya buya!! Haka kuma yanada cucarwa akan matar domin macen da tayarda ta zama kawa ga namiji me aure bazata taba zama ba daidai da wannan mata tashi ta farko har abadan zata rika daukan kanta a matsayin mace ce me daraja ta biyu tana sane cewa tana rayuwa da namijin da ba mijinta bane mijin wata matace ta daban, bazat iya rayuwa ba me kyau tare dashi na ciki ne ko kuma na waje bazata iya jin dadin ba a lokacin da take tare dashi domin tsoron kada wani yagansu, sannan kuma har wayau ga rashin tabbacin rai da tausayi domin kuwa zai iya barinta a duk loakcin da ya gaji da ita.

          Wani abu na daban kuma shine abunda da dokan dan adam ta gafala dashi ko kuma take kokarin mantawa dashi shine Karin aure yana jawo maslaha ga mace daga namiji, yawan matan duniya sun nun-nunka maza saboda dalilai dayawa daga cikin su akwai:-

  1. HAIHUWA: kididdiga na kasa da kasa ya nuna cewa yawan matan da ake haihuwa yafi na maza.
  2. YAWAN MUTUWA: yawan mutuwan maza yafi yawa saboda yaki wanda akeyi kamar yakin duniya na farko dana biyu da yakuna wanda yake tsakanin kasa da kasa a wani lokaci, haka kuma yawan hatsura na hanya wanda yafi ritsawa da maza ko kuma saboda mutuwan na wuri wanda yafi faruwa da maza akan mata.
  3. GAURANTAKA: saboda rashin bukatar daukan nauyi na mata da iyalai ko kuma saboda fita zakka wanda yake fuskanta wasu dayawa daga maza cikin wasu kasashe masu yawa wanda sukaci gaba ko kuma saboda maluntaka wanda yake kasancewa cikin al'ummar kiristoci na rashin yin aure.
  4. KURKUKU: yadda yawan yan kurkuku mafi yawa maza ne ba mat aba.

Dukkan wannan dalilai ne wanda yake zama da wahala mace ta samu miji ita kadai a rayuwanta. Kuma hakika dokoki na dan adam sun sanya mata dayawa yarda da zama kawaye na maza koda kuwa wannan namiji yanada mata domin samun namiji!! Wanda yafi dacewa ga dokoki na dan adam dasu yi doka akan Karin aure da kuma kawar dakai ga yancin mace, aure baya yiwuwa sai da yardan ma'aurata, sannan kuma hama Karin aure yana cin karo da yancin mutum wanda wannan kasashe suke kira dashi dakansu.

Da ace mutum zai cema wata daga cikin wannan mata wanda basu samu mazaje ba kuma sunason auren namiji koda bayahudiya ce ko kirista ko musulma ko buziyya cewa Karin aure be dace ba da halaye kuma yafi dacewa da ta zauna haka babu aure wanda za'a haramta mata hakkinta na rayuwa na dabi'a kamar sauran mata masu aure, ko kuma abunda yafi shine tayi rayuwa a matsayin kawa ga namiji me mata sannan daga baya ya barta, sai kuma ta kara neman wani abokin na daban wanda hakan rayuwanta zai kare, da sannu zata amsa maka da cewa: “kai ina ruwanka? Idan bakason Karin aure ko kuma kana ganin cewa be dace ba to wannan ra'ayinka ne kuma kada ka tilastama wani ra'ayin ka wand aba irin naka ba, duk wanda yaga dama yayi Karin aure wanda kuma yaga dama ya tsaya ga mace daya!!”

 

MUSAYAN MATA A CIKIN DOKOKI NA DAN ADAM:

 

Ya yadu yanzu cikin kasashe masu yawa wanda suka ci gaba a fili canjin mata[42], yadda mutum biyu zasu yi musayan matan su sai kowa ya kwanta da matar dayan, ko kuma mutum ya kwanta da matar shi da matar dayan a lokaci daya sannan bayan haka shima dayan sai ya kwanta dasu su biyun a lokaci daya. Dalili kuma na hakan kamar yadda dayawa daga cikin ma'aurata suka ambata shine kwadayin sun a canji da kuma banabantan yanayi na sha'awa da kuma daukan hakan a matsayin hanya ta abota da kuma kara dankon alaka a tsakanin su. Wani marubuci curtex berjistarland ya ambata cikin littafin sa”musayan mata a amerika”cewa wannan al'ada ta dauki yaduwa a amerika a tsakanin bangarori biyu masu yaki a lokacin yakin duniya na biyu, a lokacin da mutuwar mayakan ya karu, ya kasance mayakan sun hada al'ummar su ta musamman domin kulla alaka a tsakanin iyalansu ta hanyar da tafi, haka ya kasance mayakan suke kula da matan sauran mayakan idan sun mutu ko kuma sun bace, kuma wannan kulawar ya kasance yana wanzuwa zuwa kulawa ta tausayi da alaka sha'awa har wayau, daga cikin masalai na musayan mata wanda ya fara yaduwa a tsakanin ma'aurata a tsakanin al'ummar birane na amerika, abunda aka sani kungiyoyi na mabudai, yadda mutum zai jefa makullin gidan sa a kasa daganan sai wata mace ta dauka ko wani mabudi a ciki ta hanyar cinka, to hakan wannan mata zata zama rabon wannan mutum me wannan mabudin cikin wannan dare[43]. Kuma an yadashi cikin wata kafa ta labarai ta CNN a ranara 15 ga watan satumba na shekarar 2011 cewa adadin ma'auratan da suke yin musayar mata yakai kusan miliyan 15!! Kuma ana samun hakan yanzu dayawa kogigoyin duniya wanda suke kwadaitarwa akan musayar mata da kuma shirya tafiya da kuma kungiyoyi da biki na musamman domin aikata musayan mata, yadda ba'a barin mutane shiga wannan wurin bikin sai da matan su su kuma mata ana barin su shiga koda kuwa ba tare suke ba da maza, sannan zaka samu daki cikin wurin wannan biki wanda aka ware domin aikata hakan, kuma mutum zai iya bayan ya gama kwanciya da matar wani ya daya ya kara maimata wannan kacinci kacinci a cikin wannan daren, haka kuma itama macen zata iya yin wannan abu tare da maza dayawa ko wanne daban daban!! Kuma hakika musayan mat aba laifi bane cikin dokoki na dan adam yana daukan sa a matsayin yanci na mutum da sha'awa, kuma suna daukan sa cikin dabi'u wanda suka dace yadda mayaka zasu kula da matan mayakan da suka mutu ko kuma suka bace domin su biya masu bukatun sun a sha'awa da tausayi, shi kuma Karin aure suna daukan sa a matsayin laifi!!! Da ace wani mayaki ma aure zai kara auren matan wani mayaki wanda yam utu domin ya kula da ita hakan laifi ne kuma zasu kulle shi domin tuhumar sa da Karin aure!! Sai dai hakan yaci karo da fidira!!.

 

KARIN AURE A CIKIN YAHUDANCI DA KIRISTANCI:

 

Mafiya yawa ba'a ambatan wani annabi cikin littafi me tsarki face yanada mata dayawa, misali annabi Sulaiman da Dawud da Ibrahim da Ykubu da sauran su amincin Allah ya kara tabbata a garesu, hakika an Ambato cewa annabin Allah Sulaiman cikin littafin Safar al muluk na farko (11/3): (ya kasance yanada mata dari bakwai masu yanci da kuma bayi dari.) kuma an Ambato cikin safar al tasniya (21/15): (idan mutum ya kasance me aure da mata biyu, yanason daya daga cikin su kuma bayason dayar…).

Safar al khuruj (21/10): (amma idan ta burgeshi kuma ya aure ta, sa'annan ya dawo ya auri wata, to bazai rage mata komai ba daga cikin abincin ta da tufafinta da zamanta kewar ta.)

Kamar yadda babu wani nassi daya daya zo cikin littafi me tsarki tsohon lkawi ko kuma sabon alkawari wanda yake haramta karin aure ko kuma iyakance adadin matan da za'a aura!! Daga cikin nassoshi wanda suka tabbata a cikin sabon alkawari:

Sakon Bulus na farko zuwa ga Thimosawis (3/1): (1 gaskiya itace magana: idan daya yaso malumta, to yaso aikin kwarai. 2 ya wajaba yakasance mata: ba tare da zargi ba, mijin mace daya saliha, me hankali, kamulalle, me taran baki, wanda ya dace da karatu… 12 ya kasance ma'aikacin coki na musan man: mijin mace daya, me lura da yaran su da gidan su me kyau)

Acikin wannan nassi munga cewa Karin aure halal ne ga kowa ga duk wanda yakeson zama babban malami ko kuma ma'aikacin coci na musamman.

Kuma wata marubuciya Mathelyda juslyn ta ambata cikin littafin ta mace da coci da kasa abunda ke zuwa[44]: (shin wannan ba dalili bane a bayyane cikin maganganun Bulus akan siffofi na maluma - fadoji - cewa su kasance (mijin mace daya) cewa Karin aure halal ne a cikin coci shi yafi dacewa da manzanni almajiran shugaba Almasihu?!.. idan al'amarin haka yake me yasa yanzu aka kirkiro wasu siffofi wanda suka banbanta da wancan wanda manzanni suka tabbatar dashi da kansa?!)

Kuma wasu kiristoci sun kafa hujja da wasu nasooshi cikin sabon alkawari akan haramcin Karin aure, kamar misalin:

Injila ta markis (10/2): (2 sai firisiyyun suka gabato ya tambayesu: “shin ya halatta ga mutum ya saki matar sa?!!. domin su gwadashi. 3 sai ya amsa yace masu: “dame musa yayi maku wasiyya?.” 4 sai sukace: “Musa yayiizini da arubuta littafin saki, sai asaketa.” 5 sai Yusawwa'a ya amsa yace masu: “saboda bushewan zuciyar ku ya rubuta maku wannan wasiyyar, 6 sai dai a farkon halitta, miji da mace Allah ya halicce su. 7 saboda haka mutum yake barin ubansa da uwarsa ya hadu da matar sa, 8 sai su biyun su zama jiki daya. Idan basu kasance su biyun ba face gangan jiki daya. 9 wanda Allah ya hada su basa mutum baya rabasu.” 10 sa'annan kuma almajiran sa suka tambaye shi a gida har wayau akan haka, 11 sai yace masu: “duk wanda ya saki matar shi ya auri wata yana zina da matar farko. 12 idan kuma mace ta saki mijinta ta auri wani tana zina)

Injila na luka (16/14): (14 firisanawa sun kasance har wayau sunajin wannan dukkan sa, kuma suna son kudi, sai sukayi isgilanci dashi. 15 sai yace masu: “kune wanda kuke sanya kanku karkashin mutane! Amma Allah yana sane da zukatan ku. Lallai me girman kai agun mutane me datti ne na kafar allah. 16 namus da annabawa sun kasance zuwa ga Yuhana. Daga wannan lokaci ake masa bishara da madafun Allah, ko wannane fisgi kansa zuwa gareshi. 17 sai dai gushewar sama da kasa yafi sauki akan fadi dugo daga na namus. 18 duk wanda ya ski matar say a auri wata yana zina ne, kuma dukkan wanda ya auri wacce aka saka yana zina ne)

Injila ta Mathew "(5/31): (31 sai akace: duk wanda ya saki matar sa to ya bata littafin saki. 32 amma ni kuma ina ce maku: lallai duk wanda ya saki matar sa sai dai saboda tayi zina, duk wanda ya aure wacce aka saka to zina yakeyi).”

Kamar yadda muka gani cikin wannan nassuka guda uku wabda yake magana akan saki da Karin aure, a cikin jumlar (sai dai a farkon halitta namiji da mace Allah ya halicce su) wanda ake nufi anan Adam da Hauwa da aka koroshi cikin maganar da siffar kowa, amma bece Karin aure ba haramun tun farkon halitta, saboda hakan zaici karo da abunda aka sani a cikin littafi me tsarki na Karin auri musamman ga annabawa. Akan haka wannan nassuka basa dacewa da yin hujja dasu akan haramcin Karin aure sai dai ayi hujja dasu akan haramcin saki, shin koda kuwa mata day ace ga mutum ko kuma sama da haka. Kuma nassuka sun Ambato yanayi daya wanda aka amince yin saki a ciki shine idan mace tayi zina, anan wurin ya halatta miji ya sake ta, amma idan ya saketa domin zalumci ko kuma mugunta ba tare da tayi zina ba, sai kuma ya auri wata to yayi zina da ita (ai ya ha'ince ta kamar yayi mu'amala ne na aure da wata mace wacce bata halasta a gareshi ba), amma nassin bece duk wanda ya auri wata mata ba kari akan matar sa ba tare da ya sake ta ba cewa yayi zina ko ya ha'ince ta, wance yake cikin yanayi a jumla (idan mace ta saki mijinta ta auri wani mijin na daban to tayi zina) anan wurin ya alakanta siffar zina da sakin miji ba wai da Karin aure ba, da ace abunda ake nufi anan akrin aure ne ta yaya Karin aure zai kasance cikin halin matar da ta saki mijinta ta auri wani mijin na daban (shi kadai) ko kuma miji ya saki matar say a auri wata matan (ita kadai)?!! Watan da ace matslar itace Karin aure da sakin miji ga matar sa da kuma aure wata ya zama halal!! Sai dai abunda ake nufi shine rashin sakin miji ga matan sa koda kuwa yana da mata sama da daya. A cikin wani jumlar (duk wanda ya auri wacce aka saka to yana zina ne) anan wurin wannan jumlar yana nuna wa a bayyane cewa mijin daya auri macen da aka saki koda kuwa farkon auren sa da ita kenan, to hakan zina ne, bawai saboda Karin aure bane domin kuwa shi beyi karin ba, a'a dalili shine ya auri wacce aka saka.

Anan wurin zamuga tsantsan sabanin cikin nassi a tsakanin injila na Markis da Injila na Luka, maganar su ya Ambato labari daya ne sai dai da nassi mabanbanci matuka cikin abunda yake nuna rashin dacewar kafa hujja da dukkanin su da kuma daukan su a matsayin nassi me tsarki wanda akayi wahayi dashi daga wurin Allah ko kuma a jingina su ga shugaba almasihu amincin Allah ya tabbata a gareshi.

Sakon bulus na farko zuwa ga corinthians (7/1): (1 amma ta bangaren al'amurar da kuka rubutumin akan su: abunda yafi shi kada mutum ya taba mace. 2 amma saboda zina, kowa ya kasance yana da mata, kuma kowa ta kasance tana da miji…8 sai dai ina fadi ga wanda basu da aure da zaurawa, cewa yafi masu kyau su zauna kamar yadda nake. 9 amma idan bazasu iya kamewa ba to suyi aure. Domin aure yafi dacewa dasu dayin motsi.)

Anan wurin yana cewa (kowa ya kasance yana da mata) ma'anar wannan maganar bata da alaka da haramta Karin aure, tana nufin kada wani ya taba matar da ba nashi ba, watan kada yayi zina da ita, wannan shine cikin cewa: kowa a cikin mu ya kula da yaron shi, ko kuma kowa acikin mu yak are gidan sa ko dukiyan sa ko kasuwan cin sa, kuma kamar yadda aka fadi cikin Safar samuel na farko (15/3): (3 yanzu tafi sarakuna kuma ku haramta duk abunda suka mallaka, kada kuma ku masu afuwa, ku kashe miji da mata, yaro da wanda ake shayarwa, shanuwa da akuyoyi, rakumi da jaki) anan ba ana nufin ka kashe miji daya da mace daya da yaro daya da jaki daya, ana nufin dukkanin jinsin namiji da mace yara da jakuna zuwa karshe. A cikin fadin sa cewa (saboda aure yafi dacewa dasu akan motsi) babu nuni akan haramta Karin aure, cewa yayi yin aure ko kuma barin shi abude yake.

Akwai daya wa maluma – fadoji – da kiristoci na bangarori masu yawa wanda suke tabbatar da rashin samun haramci na Karin aure cikin kiristanci, kuma dayawa daga cikin su sun auri mace sama da daya, kamar sarkin sharlyman, Imbiradur faltiniyan na farko, Lusar da sauran su, kuma hakika marubuciya mathilanda juslyn ta ambaci haka tana cewa:

“lallai yana cikin abunda aka sani a cikin tarihi wanda babu jayayya a cikin sa, cewa ko wanne cikin coci na kiristanci da kasar kiristanci tsohon zamani mabanbanta da kuma kasan bukatu mabanbanta, wanda sukaba shuwagabannin su dacewa na Karin aure. Imbiradur faltiniyan na farko a karni na hudu na miladi yaba kiristoci hakkin auren mata biyu, a kuma karni na takwas sarki sharlyman wanda shine shugaban coci da kasar kiristanci, ya auri mata shida kuma wasu daga cikin masana tarihi sun Ambato cewa matan shi tara.. lusar dakansa me rike da littafi me tsarki na tsohon da sabon alkawari yana cewa: ina tabbatarwa daga gareni cewa idan mutum yanason auran mace biyu ko sama da haka, bazan iya haramta mashi hakan ba, kuma aikin sa be sabawa littafi me tsarki ba.”[45]

Augustine me tsarki yace: “yanzu a zamanin mu wannan, bayan munyi aiki da doka na romaniya, mutum bazai iya auren wata mata ba kari akan matar sa matukar matar sa tananan da rai.”[46]

Wannan yana nuni akan dalilin haramcin Karin aure shine dogaro da doka na romaniya bawai saboda nassuka ba na addini. Kuma ya kara cewa Augustine me tsarki:

“wani lokaci na daban, Yakubu dan Ishaq an tuhume shi da aikata laifi babba saboda ya auri mata hudu, sai dai ba'a samu asali ba na wannan tuhumar, saboda Karin aure ba lafi bane saboda ansan haka, sai dai yanzu ya zama laifi saboda ana daukan shi haka a al'adance… dalili daya tilo na daukan Karin aure a matsayin laifi shine saboda al'ada da doka sun haramta shi.”[47]

 

KARIN AURE A MUSULUNCI:

 

Domin fahimtar mahangan musulunci game da karin aure ya wajaba musan abubuwa masu zuwa hakan haka:

  1. Lallai musulunci bashi kaidai bane addinin daya shar'anta Karin aure, sai dais hi kadai ne addinin daya iyakan ce adadin matan da mutum zai iya aure wanda hakan halal ne a cikin sauran addinan baki daya, Haris dan Kais yace:

(na musulunta inada mata takwas, sai nafadama manzon Allah s.a.w hakan sai manzon Allah s.a.w yace: “zabi hudu acikin su”) (abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi)

  1. Lallai Karin aure a musulunci bawai yana cikin al'amura na wajibi bane akan ko wani musulmi wanda idan be aikata ba zayyi zunubi da kuma daukan sa a matsayi me nakasashen addini, a'a Karin aure yana cikin ayyuka ne na halal duk wanda yaso ya aikata wanda kuma beso ba bazai aikata ba, misalin sa kamar misalin sauran ababe halal ne a musulunci. Wanda ba'a kama musulmi da laifi idan be aikata su ba.
  2. Sanin dalilin saukar ayar Karin aure, gabanin karanta ayar alkur'ani me girma wacce ta halasta Karin aure da kuma iyakance shi da hudu ya kamata mu karanta ayoyin alkur'ani wanda ta gabace ta da kuma fahimtar su da fahimtar dalilin saukar ta domin musan cewa bata sauka ba face domin bada kariya ga mace da kuma kiyaye mata hakkokinta.

Allah madukaki yace:

 “yaku mutane kuji tsoron ubangijin ku wanda ya halicce ku daga rai daya ya kuma halitta masa mata daga gareshi sannan ya yada a tsakanin maza dayawa da mata; kuji tsoron Allah wanda kuke roko kuma kuke sada zumunta domin shi; lallai Allah ya kasance me sa ido akan ku (1) kuma kuba marayu dukiyoyin su kuma kada ku cudanya datti da me kyau kum akada kuci dokiyoyin su cikin dukiyoyin ku; lallai hakan ya kasance laifi me girma (2) idan kuma kunji tsoron cewa bazaku iya adalci bag a marayu to ku auri abunda ranku yaso cikin mata biyu ko uku ko hudu; idan kuma kunji tsoron cewa bazaku iya adalci ba to ku auri daya ko kuma abunda kuka mallaka na bayi; hakan shi yafi domin kada kuyi zalumci (3) kuma kuba mata sadakin su kyauta a garesu; idan sun tsammaku wani abu daga cikin sa to kuci halal ne agareku (4) kuma kada kuba wawaye dokiyoyin ku da Allah ya sanya ku tsayayyu akai kuma ku rika azurta su a cikin sa da tufatarwa kuma ku rika fada masu magana me dadi (5) kuyi ma marayu jarabawa har idan sun isa aure kuma kun ga shiriya a tare dasu to ku basu dukiyar su kuma kada kuci ta domin barna da gaggawa gabanin su girma; wanda ya kasance mawadaci acikin ku to ya kame wanda kuma ya kasance talakawa to yaci dai-dai misali; kuma idan kun basu dukiyar su ku samu shedu akan haka; kuma Allah ya isa zama me hisabi (6)” (suratun nisa'i 1-6)

Allah madaukaki a farkon ayoyin nan masu girma ya umurce mutane da jin tsoron sa da kiyayeshi kuma suba marayu wanda aka masu wasaici akan su dokiyoyin sui dan sun kai shekarun balaga kuma sunga ikon su akan iya kiyaye dukiyar, kuma kada su zalumce su ta hanyar cin dukiyoyin, larabawa sun kasance gabanin zuwan musulunci idan kawai wasaicin wani maraya karkashin wani daga cikin su na kudi, sais u cudanya dukiyar su dana shi sais u dauki me kyau aciki su bar mai lallataccen domin suyi masu dabara!! Imam Suddi ya ambata haka:

“ya kasance daya daga cikin su yana daukan akuya kusashiya cikin akuyoyin marayu, sai ya ajiye a maimakonta a kuya ramammiya, sai yace: “akuya da akuya", sai ya dauki dirhami me kyau ya ajiye mara kyau, sai yace: “dirhami da dirhami.”

Hakika Allah madaukaki ya hana wannan laifi na satan dukiyar marayu sai yace: (lallai hakan ya kasance laifi babba) watan zunubi me girma.

Salon yin wayau ga marayu haka yaci gaba da kuma cin kudin sui dan sun kasance mata ne, hakika Urwatu dan Zubair Allah ya kara masa yarda ya tambayi Aisha Allah ya kara mata yarda game da fadin Allah madaukaki (kuma idan kunji tsoron cewa bazaku iyayin adalci ba ga marayu) sai tace: (ya kai dan dan uwata wannan marainiyan zata kasance a dakin waliyyinta (watan karkashin kulawan sa) tana hadaka cikin kudin sa sai kudinta da kyauta ya birgeshi, sai waliyyanta yaso aurenta ba tare adalci ba wurin biyan sadakinta ya bata abunda waninshi zai bata, sai aka hanasu auren su sai dai idan zasu iyayi masu a dalci, su basu mafi kololuwa na sadakin su, sai aka masu izinin auren abunda ransu ke so cikin mata wanda basu ba). (buhari ne ya rawaito shi)

Haka abun yake lallai wannan aya me girma ta sauka ne akan mutumin da yakecin hakkin marainiya wacce take karkashin wasaicin sa da kulawan sa, idan yana son auren ta ne kuma bazai bata sadaki ba kamar yadda ake bas aura mata irinta, to Allah madaukaki ya hanashi wannan al'amari kuma ya umurce shi daya bata sadakinta wanda aka sani anaba sauran mata irinta a al'adance, ko kuma ya barta kada ya aureta yana da zabin ayren wata mace wacce ba itaba, ko mata biyu ko uku ko hudu daga cikin mata wanda hakan shine karshen. Sai dai dayawa daga cikin makiya musulunci suna zuwa ne da hadafin sun a rufa ido wacce suka saba, sai su yanke sauran ayoyin wanda suka gabata su kawo dai-dai fadin Allah madaukaki (ku auri abunda ranku keso cikin mata biyu ko uku ko hudu) kuma sais u yanke abunda ke bayan ayar wacce sharadi ne na Karin aure waton adalci tsakanin matan!!.

 

SHARADIN KARIN AURE A CIKIN ALKUR'ANI:

 

Lallai musulunci ba umurni yayi bag a mutum daya auri wata mata ta daban ba kari akan matar sa, a'a ya halalta masa hakan ne sannan kuma ya sanya masa sharudda wanda mutum zai kiyaye su gabanin auren mace ta biyu daga cikin wannan sharudda akwai tabbatar da yin adalci a tsakanin su cikin abinci da tufafi da abunsha da wurin kwana, Allah madaukaki yace:

(idan kunji tsoron cewa bazaku iya adalci ba to ku auri daya) (suratun nisa'i ayata 3)

Kuma ya hana yin zalumci da mugunta a tsakanin mataye da kuma karkata zuwa ga wata daga cikin su, Allah madaukaki yace:

(kuma bazaku taba iyayin adalci ba tsakanin matan koda kun so hakan amma kada ku karkata matuka sai ku barta kamar sagalalliyan riga; idan kukayi dai-daito da jin tsoron Allah to lallai Allah ya kasance me gafara me rahama) (suratun nisa'i ayata 129)

Kuma manzon Allah s.a.w yace:

“duk wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ga daya daga cikin su, zai zo ranan alkiyama me shafaffen rabin jiki” (hadisi ne ungantacce. Ahmada da abu dawud da nasa'i ne suka rawaito shi)

Ya wajaba gareka dan uwa makaranci me daraja sanin cewa musulunci addini ne da duniya baki daya an saukar dashi ga dukkanin mutane cikin dukkanin zamani da wuri bawai an saukar dashi bane ga wasu mutanen ko al'umma guda ba saboda haka ka'idojin sa da shari'un sa zuna zuwa ne domin dacewa da tunanin su da abunda suke su, saboda haka ne musulunci ya halalta ma maza auren mace sama da daya domin fahimtar waki'ina rayuwa da kuma uziri na rayuwan saboda haka abunda wani yake ganin be dace da wannan al'umma ba zai iya dacewa da wasu al'ummar wanda basu bah aka kuma abunda be dace ba da wannan zamani zai dace da wani zamanin bayan sa, kuma hakan rahama ne ga mata wanda zasu zauna gwagware idan akace kada a maza su auri mace sama da daya, duk wanda yakeson riko da wannan sauki sai yayi ya kuma kiyaye sharuddan sa wanda kuma baya so sai ya bari!!.

 

 

 

BABI NA BIYAR

DOKOKI MASU TSARA

AL'UMMOMI

 

  • Banbanci tsakanin shari'ar musulunci da dokoki – tsaruka - wanda dan adam ya kirkira.
  • Ra'ayin littafi me tsarki akan dimukradiyya.
  • Yancin da yin abunda mutum keso cikin shri'ar musulunci.

 

 

 

 

 

 

BABI NA BIYAR

DOKOKI MASU TSARA AL'UMMOMI.

BANBANCI TSAKANIN SHARI'AR MUSULUNCI DA DOKOKI – TSARUKA - WANDA DAN ADAM YA KIRKIRA:

 

Akwai dayawa na dokoki na tsarin al'umma amma wanda sukayi galaba sune guda biyu ne kacal acikin su wanda aka sani a cikin wannan al'umma tayau, tsarin dimukradiyya da kuma mulkin soja, kuma dukkanin su biyun tsari ne wanda aka tabbatar da gazawar su daga a lokacin amfani dasu a duniya tsawon karnin da suka gabata da kuma rashin tabbatar da da zaman lafiya da adalci na duniya wanda duniya ke ikirari ayau. Abun mamaki shine duniya suna neman tsari wanda zai tabbatar masu da amincin su da zaman lafiya, a lokacin da suke rayuwa da ganin shari'ar musulunci kusa dasu, sai dai wasu manyan yan siyasa masu shan jinin mutanen su sun san cewa yin amfani da ita zai sa su rasa dayawa na mulkin su da abubuwan su da suka kebanta dashi, saboda haka ne suke fadima masu rubuta dokoki abunda suke so na hukunce hukunce wanda zai basu daman riko da madafun ikon al'ummar su da basu rinjaye akan al'amarin su.

 

Ma'anar dimukradiyya:

Kalmar dimukradiyya kalma ce ta yunani wacce aka samota daga kalmomi biyu,”zimus”wacce take nufin”al'umma”da kuma”kiratus”wacce take nufin hukunci ko mulki, ma'ana mulkin al'ammu ga kanta, hakan ta hanyar tsayar da tsarin majilisar kasa wanda al'umma zasu zabi wanda zasu wakilce su cikin wannan majalisa, wanda acikin shi ne za'a tattauna dukkanin dokoki da kuma tabbatar da abunda ya dace acikin su da yardan mafiya yawan mutanen cikin majalisar, ma'ana idan mafiya yawan suka tafi akan ra'ayi to wannan shine ra'ayi wanda za'a zartar dashi dole koda kuwa akwai wani ra'ayin da yake karo dashi nay an cikin majalisar, saboda haka dokokin su da tsarin ba tabbatacce bane saboda yan majalisun da mambobin sa basa tabbata ana canza su. Allah yayi gaskiya wanda ya bayyana cikin alkur'ani cewa mutum besan abunda zai gyara masa hali ba face da hukuncin Allah yadda yace:

“da ace gaskiya zai bi son zuciyoyin su da sammai da kasa da abunda ke ciki su ya lallace; sai dai munzo masu da ambatin su kuma su masu kawar dakai ne daga ambaton su” (suratul muminun ayata 71)

 

Ma'anar dimukradiyya:

Tsarin mulkin soja akasin tsarin dimukradiyya ne baki daya, yadda ra'ayin shugaba ko zababbu ko kuma hukumar da take mulki shine ra'ayin da za'a zartar wajibi koda kuma ya sabama ra'ayin al'umma. Allah ya fadi game da fir'auna me mulki wanda yayi barna da zalumci a doron kasa ya kuma bautar da mutanen ta:

“Fir'auna yace ba'a ganin wani abu sai abunda kuka gani kuma bana shiyar daku face zuwa hanya ta shiriya” (suratul gafir ayata 29)

Lallai dayawa daga cikin mu a yayin jin wannan kalma na dimukradiyya abunda yake fara zuwa kwakwalwan su shine ma'ana me kyau kamar lamuni na yancin mutum da kuma martaba ra'ayin wasu da yancin fadin albarkacin baki da yancin tsayar da alamun addini ga kasashe da kuma martaba hakkokin su da maslahohin su da kuma rashin danne su, amma a agaskiyan al'amari tsarin dimukradiyya tsari ne mulkin soga ko kuma ace tsarin mulkin shugaba, hakan kuwa saboda mafiya yawan lokuta anayin dokoki ne wanda suke dacewa da abunda yake so a cikin kasa koda kuwa wannan dokoki sunci karo da maslaha ta asali ko kuma aqidun wannan kasa ko kuma zai yajo cucarwa a garesu. Akwai yanayi na wannan zamani wanda zai bayya mana wani fuskar ta daban na munin wannan tsari na dimukradiyya.

  • A shekara ta 2009 da sunan dimukradiyya an kirkiro doka da kuma aiwatar da ita wacce take hana gina wurarin kiran salla, kuma wannan doka anyita ne abisa ra'ayi na mafiya yawa wacce aka haramta wa musulmi marasa rinjaye gina wuraren kiran salla a masallatan su, wannan al'amari wanda ya sanya kungiyar lafiya na kasashe bayyana bacin ranta akan sakamakon wannna zabe wacce tace hakan yana kunshe da take hakkin na tilastawa swistzland yancin fadin albarkacin baki game da akida.
  • Da suna dimukradiyya a cikin wasu birane na turawa har zuwa yau ba'a yarda da gina masallatai ba ga musulmai marasa rinjaye, ko wnai lokaci musulmai marasa rinjaye sukayi kokarin samun izini na gina masallaci, sai yan majalisu masu rinjaye na wannan kasa su kada kuri'a wanda zai hana basu wannan izini na gina masallaci, idan kuma sun samu yarda na izinin ginawa to sai kaga tazo da wasu ka'idoji masu wahala wanda sun isa su hana gina wannan masallaci.
  • Da sunan dimukradiyya a cikin wasu kasashe na turawa akayi dokan hana mata musulmai sanya nikabi a cikin wurare na jama'a, suna masu nokewa da wasu hujjoji, daga cewa akwai cewa be dace ba a rufe fuska a wurin jama'a da makamantan su, dukda cewa wannan dalili zai iya karbuwa ga wasu mutane ta hanyar hankali, sai dai muna ganin ita dai wannan hukumar tana wajabtama masu tuka mashin rufe kansu da fuskar su akan tituna!! Shin wannan befi dacewa bag a masu tuka mashina su bude fuskokin su suma!! Kamar yadda akwai mutane dayawa cikin kasashe dayawa na turawa da kuma kasashen gabashin asiya kamar sin da tailand da makamantan su wanda suke ganin rufe fuska ga likita, saboda suna ganin zai kareshi daga kwayoyin cututtuka da rashin lafiya, amma babu wanda ya taba magana akan wannan al'amari har Abadan da cewa hakan be dace ba na rufe fuska a wuraren jama'a!! shin acikin hana mata sanya abunda suke so da zabin su ba rashin girmama zabin su bane da kuma iyakance masu yancin su na dan adam da kuma aqidun su na addini!! Bawai cewa idan baka yarda da aqidar wani bas hi kenan sai ka tilasta mashi sai ya barta, dayawa daga cikin uyan indiya suna sanya rawuna bakake akan kawuran su da kuma barin gashin su yayi yaw aba tare da rageshi ba, kuma suna harkoki cikin yancin a turai kuma ana basu ayyuka dayawa a cikin hukuma ba tare da ansanya su ba cire rawunan su, kuma babu wani wanda yake da hakki sanya shi cire wannan rawani ko kuma aske gashin saboda be natsu da wannan rawani ba ko kuma tsayin gashin.
  • Da sunan dimukradiyya a cikin wata kasar da sukaci gaba wani jam'iyya tayi nasara cikin zabuka a birane dayawa , sai ya kasance dokan sun a farko shine zasu hana kai abincin halal ga dalibai musulmai a makarantu wanda suke birane da sukaci nasara acikin su a zabuka, kuma haka aka wajabtama makarantu kai abinci wanda suka kunshi laman alade da kuma wasu namukan wanda ba'a yanka su ba abisa karantarwan shari'ar musulunci ga dalibai musulmi, wanda yafi dace dasu da kawo dokoki wanda zasu dakila barna da kuma lamuntan yanci.
  • Da sunan dimukradiyya a cikin wata kasa wanda suka ci gaba anyi doka wanda zai hana hanyar yankan halal a cikin kasar, abunda yake nufin hana musulmai samun naman da aka yandai dai dai da karantarwan musulunci, kuma hadafin haka shine kuntatawa musulmai domin su fice daga kasar zuwa wata kasar wacce zata martaba iqidunsu, dukkanin wata dabba wacce aka kashe da wutan lantarki ko kuma ta hanyar cire mata kai da wuka na karfe har ta mutu ko kuma aka shaketa ko kuma rufeta a inda babu iska ko nutsar da ita cikin ruwa musulmai bazasu iya cin namanta ba.

Wannan kadan ne daga cikin misalai nayin amfani da masu jinyaje a toye hakkin marasa rinjaye, hatta hakkinta na gudanar da addinin ta cikin yanci ba tare da tsangama ba ko kuma kuntatawa, ko kuma hakkinta na zabin irin kayan da zasu sa ko kuma kai hatta irin abincin da sukeson ci!! Daga cikin wannan misali da sauran su zai bayyanan maka cewa tsarin dimukradiyya ko kuma almaniyawa a zahirin magana bazai iya rayuwa ba sai ga karon kansa kadai, amma ga marasa rinjaye yana furta abubuwa dayawa na hujjoji domin ya danne su da kuma kuntata masu yana me zargin cewa bazasu iya rayuwa ba da wasu tsarin na daban!! Ita kuwa shari'ar musulunci sabanin haka ne, ya tattara dukkanin mutane bisa banbancin addinin su hakika ya nassanta hakkokin marasa rinjaye ya kuma sanya wannan hakkokin ya fita daga ikon masu rinjaye, kai ya kuma wajabta ma masu rinjaye lamuni na kiyaye wannan hakkoki da kuma rashin ketare su, koda kuwa ra'ayin masu rinjayen ya sabama hakan, anan wurin ba'ayi hujja ba da ra'ayin masu rinjaye matukar yaci karo da hakkokin wanda shari'a ta nassanta akan lamunin. Duk wanda yake neman Karin bayani akan wannan maudu'i akwai littattafai masu yawa wanda suke magana akan hakkoki na wand aba musulmai wanda suke cikin kasashen musulmai, zasu iya komawa zuwa garesu, kuma Allah yayi gaskiya:

“kuma idan kayi biyayya ga mafiya yawan mutanen duniya zasu batar dakai daga hanyar Allah; ba komai suke bi ba face zata kuma su din ba komai sukeyi ba face kiyastawa” (suratul an'am ayata 116)

          Babwa wata tsari na mutum duk yadda takai wacce zata iya tabbatar da rayuwa lafiyayye ga al'umma haka kuma rayuwa lafiyayye a cikin al'umma kanta kamar yadda shari'ar musulunci tayi kuma dalilin haka shine ita tsari ne da dokoki na Allah wanda ya saukar dasu ga mutane kuma shine mafi sanin abunda ya dace dasu, Allah madaukaki yace:

“shin wanda yayi halitta besan halittansa ba kuma shi me tausayi ne kuma masani” (suratul mulku ayata 14)

 

RA'AYIN LITTAFI ME TSARKI AKAN DIMUKRADIYYA

 

Amma shi littafi me girma yayi gifa da dimukradiyya baki dayan sa Bulus yana cewa cikin sakon sa zuwa ga mutanen Rumiyya (13/1): (1 kowa yayi biyyay ga shuwagabinni manya, saboda babu wani sarki sai daga Allah, kuma shuwagabanci martaba ne daga Allah 2 har wanda yake fito na fito ga shugaba yana fito na fito ne ga tsarin Allah, masu fito na fito za'a su kama kansu anan duniya. 3 lallai shuwagabanni basu da tsoro ga ayyukan su na kwarai sai ga na sharri. Shin kuna son sabama shugaba? Ka aikata abunda ya dace zai ya zaman maka yabo akan haka, 4 domin kuma me gyara kadimin Allah ne! amma idan ka aikata sharri kaji tsoro, domin wuka bata daukan wasa, saboda kadimin Allah ne, me hukunci ga wanda ya aikata sharri. 5 saboda haka ya wajaba kayi biyayya a gare shi, bawai saboda fushi ba kawai, a'a saboda wakilinsa. 6 lallai ku saboda haka zake bayar da jiziya, saboda kadimin Allah ne masu dagewa akan haka. 7 ku bayar da dukkanin hakkokin su: jiziya ga wanda yake da jiziya. Kariya ga wanda yake da kariya. Tsoro ga wanda yake da tsoro. Girmamawa ga wanda yake da girmamawa.) 

 

YANCIN DA YIN ABUNDA MUTUM KESO CIKIN SHRI'AR MUSULUNCI

 

Shari'ar musulunci ta nassanta akan yancin fadin albarkacin baki wanda yake aka iyakance da sharuddu na shari'a wanda zasu gyara al'umma kuma bazasu batata ba da kuma hada kai tsakanin mutane da kuma tabbatar da hadafin su wanda suke musaya a tsakanin su, bawai yanci bace wanda babu tsari me rusha gina da lalatawa da kuma haifar da gaba a tsakanin al'umma, yanci wacce bata ta'aji akan hakkokin mutane da kuma take su, Allah madaukaki yace:

“yaku wanda sukayi imani kada wasu mutane su rika yima wasu mutane isgilanci me yuwa sunfi su alheri; ko kuma mata su rika yima mata me yuwa sunfi su alheri, kada ku rika aibanta kawunan ku kuma kada ku rika jifan juna da sunayen banza, tur da sunan fasikanci bayan imani; duk kuma wanda be tubaba to wannan sune azzalumai” (suratul hujurat ayata 11)

A daidai lokacin da muke ganin shiri na kushewa na zolaya wanda suka cika kafafen yada labaru cikin kasashe dayawa a duniya wanda suke ikirarin ci gaba amma basu damu ba da halin wanda suke kushewa ba ta salon a wasa na wulakantacce, wannan izgilancin wanda dokan dan adam ke kira da sunan yanci na ra'ayi wanda ya kunshi yancinta! Kuma ya tabbata cewa wannan shiri a cikin wasu kasashe shiri ne kawai na misiltawa basu da wani alaka da yancin fadin albarkacin baki, inda suke samun gudun mawa na kudi gada wurin wasu yan siyasa domin raunata abokin hamayyar su da kuma janye masa mutane.

Amma shi yanci na ra'ayi a shari'ar musulunci an takaitashi da wasu sharudda wanda da mutum zai wuce su to zai zama wanda yayi ta'adi ga hakkokin mutane ko kuma al'umma, misali al'amarin izgilanci ga manzon Allah s.a.w menene sakamakon da zai biyo bayan sa, sannan kuma menene abunda za'a samu na alheri sakamakon haka? Shin acikin haka babu ingiza kiyayya a tsakanin zukatan mutane ko kuma a zuciyar musulmi da wanda baya yin musulunci a cikin al'umma, shin ta'adi akan mamata da kuma rashin mutunta su wani alama ne ci gaba gabanin ace addini ne? ina da yakinin cewa duk wanda ya aikata haka ko taimakawa akan haka da wani zai zagi mahaifan sa ko kuma yaran sa ko dan wani wasan sa dayake so ko dan film wanda yakeso bazai tsaya ya lankwashe hannu ba yana gani zayyi kokarin kare shi ta ko wani hanya, ka sani cewa wannan kasashe da aka muzanta annabi cikin annabawan Allah a cikin su suna karkashin inuwar fadin albarkacin baki, laifi ne a shari'ar su muzanta wani shugaban kasa ko kuma firaminista ko kuma rage masa mutunci ta ko wani irin yanayi ne!! shin bazai yiwu bane yin zanen shugaban kasa na shagube domin muzantawa duk a karkashin yancin fadin albarkacin baki?!!

Kuma hakika musulunci ya haramta zagin addinin wasu domin gudun jawo fitina da kisan wasu mutanen al'umma, saboda haka ya zama wajibi akan masu hankali su kama hannun wanda yake son kunna fitina da rura kiyayya tsakanin al'umma wanda sakamakon ta zai iya zama yaki wacce zataci kowa, Allah madaukaki yace:

“kada ku zagi abunda suke kira koma bayan Allah sai su zagi Allah suma domin kiyayya ba tare da ilimi ba; da kaman haka ne muka zayyanawa ko wace al'umma aikinta sa'annan zuwa ga ubangijinsu zasu koma sai ya basu labari akan abunda suke aikatawa” (suratul an'am ayata 108)

Ka sani cewa al'amarin isgilanci ga manzon Allah s.a.w bawai sabon abu bane wanda aka kirkira a wannan zamani, ya fara tun daga lokacin da aka aiko shi, hakika sun kira akan haka da suna makaryaci da boka da mawaki da mahaukaci, kuma alkur'ani ya mabato haka cikin fadin sa cewa:

“kuma hakika mun sani cewa zuciyan ka na kunci saboda abunda suke fadi; kayi tasbihi da godiya ga ubangijin kuma ka zama cikin masu sujjada; kuma ka bautawa ubangijin ka har sai yakini yazo maka” (suratul hijri ayata 97-99)

Iyakance yancin fadin albarkacin baki kuwa bawai sabon abu bane wanda ya takaita ga shari'ar musulunci kawai bane a'a, wasu al'ummomi ma sun takiata yancin fadin albarkacin baki ga mutanen ta dai-dai da addini da kuma maslahar mutanen ta, birtaniya misali ta hana yada fim akan Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi da hujjar cewa addinin kiristanci yana cikin tsari na kasa wanda ya zama wajibi a mutuntashi da kiyaye shi. Kuma kasashe dayawa suma sun takaita yancin fadin albarkacin baki akan mutanen ta idan wannan yancin zai taba yancin yahudawa ko kuma kawo cikas ga Holocaust yadda wannan kasashe suke himmatuwa da wannan ayyuka da kuma yin ukubar dauri a gidan kurkuka akan hakan.

Hakika shari'ar musulunci ya shirya ga yancin wacce take kira zuwa ga kyakyawan aiki da kuma hani ga mummunan aiki wuri me kyau wacce zata girma a ciki da tabbata taba ko wani mutum hakkin sa nayin goganya da fadin ra'ayi akan abunda ya shafe al'umma kuma fadakarwa na Allah be sauka akan hakan bay a sanya hakan wurin yin shawara a tsakanin su, Allah madaukaki yace:

“da rahamar Allah ne ka zama mai tausasawa garesu, amman da ace ka zama mai tsanani kuma mai fishi da sun waste daga gefenka, ka musu yafiya kuma ka nema musu gafara sannan ka zama mai shawartarsu cikin lamuranka, idan kuma ka yunkura yin wani abu saika dogara ga Allah, lallai Allah yana san masu tawakkali” (suratu ali Imran aya ta 159)

Kuma ya wajabta cewa yancin fadin ra'ayi nauyi ne akan kowa domin hakan ya zama me fayyacewa tsakanin gaskiya da karya, saboda fadin Abdullahi dan mas'ud Allah ya kara masa yarda:

“kada ku zama masu dogaru akan ra'ayin wsu kuce idan mutane sun kyauta sun kyauta idan sunyi zalumci munyi zalumci sai dai ku shirya kawunan ku idan mutane sun kyauta kuma ku kyauta idan kuma sunyi kuskure kada kuyi zalumci” (sunan al tirmizi, hadisi ne maukufi – wanda aka jingina shi ga sahabi)

Wannan yancin bata zama wacce ta takaitu ga ga wasu mutane kawai a'a ta kowa ce karkashin ka'idoji na shari'a, wacce wanda aka aiko rahama ga talikai ya zartar da ita a aikace domin al'ummar bayan sa suyi koyi dashi, Abu Sa'id al khudri yana cewa:

“wani mutum bakyauye yazo gun manzon Allah s.a.w wanda bashi yamai katutu akai sai al'amarin ya mashi kamari har yace mashi: bazan bark aba har sai ka biyamun bashi na, sai sahabban sa suka masa tsawa sukace: kaicon ka kasan wanda kake yima magana kuwa? Sai yace ni hakkina nake nema, sai manzon Allah s.a.w yace: lallai kuna tare da me hakki, sai yayi aike zuwa ga Kuwaila yar Kais yace mata: idan akwai dabini agunki ki ranta mani har akawo mana dabinon mu sai na biyaki, sai tace: eh ya manzon Allah nabada mahaifana fansa agareka, sai yace: sai ta ranta mashi ya biyama wannan bakyauye bashi kuma ya ciyar dashi, sai yace: ka cika kaima Allah ya cika maka, sai yace: wannan sune zababbun mutane, lallai al'umma bata samun tsarkaka matukar basa amsan ma me raunin cikin su hakkin sa ba tare da wahala ba” (albani ya ingantashi cikin sahihu sunan Ibn Majjah da kuma sahihul jami'u: 1857)

Sahabban sa da suka zo bayan sa sunyi koyi dashi a lokacin da akayima Abubakar Assiddiq Allah ya kara masa yarda mubaya'a da khalifanci yah au minbari yayima mutane huduba wacce ta kunshi ginshikai na shugabanci a musulunci na abubuwan da mutane basu tabbatar dashi ba a karkashin shari'u na dan adam wanda yake yima son rai hidima da burin a siyasa da tattalin arziki, sai yace: (yaku mutane, hakika na zama shugaba akanku bawai nafiku alheri bane, idan kunganni akan gaskiya to ku taimake ni, idan kuma kun ganni akan bata to ku mun gyara. Ku mun bayayya matukar nayima Allah biyayya a cikin ku, idan kuma na saba masa to kada kumun biyayya, ku saurara kuji me karfi acikin ku me rauni ne aguna har sai na amsa hakki a hannun sa, kuma me raunin cikin ku me karfi ne a guna har sai na amsan masa hakkin sa, ina fadin wannan magana nawa kuma ina rokon Allah gafara gareni da ku baki daya.)[48] (siratun nabawiyya na Ibn Hisham, da dabakat na Ibn sa'ad, da nihaya wal bidaya na Ibn kasir kuma yace isnadin shi ingantacce ne).

 

Yancin yi addini: shari'ar musulunci ta nassanta akan lamunin yanci na yin addini ga wand aba musulmai ba na yahudawa da kiristoci ba tare da tsangwame ba, ba'a tilastawa wani barin addinin say a koma musulunci, Allah madaukaki yace:

“babbu tilastawa cikin addini; hakika shiriya ya bayyana daga bata” (suratul bakara ayata 256), a lokacin da tarihi yake Ambato mana tsangwamen da kiristoci ke fama dashi a tsakanin su sakamakon banbancin aqida.

 

Yancin yin ilimi: shari'ar musulunci ta nassanta akan yancin yin ilimi da karatu da kuma daukaka martaban malamai zuwa kololuwa, a daidia loakcin da tarihi yake Ambato mana ciwon kai me tsanani tsakanin coci da ilimi da maluma wanda aka hana yancin yin ilimi.

Haalima shari'ar musulunci ta wajabta wa ko wnai musulmi neman ilimi, manzon Allah s.a.w yana cewa:

“neman ilimi wajibi ne akan ko wani musulmi” (abu dawud da Ibn majjah ne suka rawaito shi kuma yana cikin sahihul jami'u)

Kuma shari'ar musulunci ta daga darajar malamai zuwa kololuwa, Allah madaukaki yana cewa:

“Allah zai daga wanda sukayi imani acikin ku wanda kuma aka basu ilimi suna sama a daraja; kuma Allah masani ne game da abunda kuke aikatawa” (suratul mujadala ayata 11)

 

YANCIN YIN ABUNDA KAKESO A CIKIN LITTAFI EM TSARKI:

 

Kamar yadda muka gani cikin sakon Bukus zuwa ga mutanen Rumiyya (13/1), wannan sakon tayi watsi da dukkanin abunda yake da ma'anar dimukradiyya ko yancin yin abunda kakeso, hasalima ta assasa ka'idoji ne na mulkin soja da kuma sarauta da biyayya ga shugaba biyayya kai tsaye mara shamaki.

 

 

 

BABI NA SHIDA

Jihadi acikin shari'ar musulunci.

 

  • Halin duniya gabanin a rarraba iyakoki da kuma bayan bayyanar musulunci.
  • Mutane akan tafarkin addinin sarakunan su.
  • Wajabta addinin kiristanci da bakin takobi.
  • Jihadi da kuma lamuni na yancin yin addini.
  • Sakwannin manzon Allah s.a.w domin kariya ga kiristoci.
  • Jihadi a musulunci da kuma karka suwan sa
  1. Matakai na jihadi.
  2. Abubuwan da suke hana jihadi.
  3. Hadafi da manufa na yin jihadi.
  4. Suwa ake nufi da jihadi.
  5. Ka'idoji na jihadi.
  • Shin ko wani yaki ne na musulmi yake jihadi.
  • Yaki me tsarki.
  • Banbanci tsakanin yaki da jihadi.

 

 

 

BABI NA SHIDA

JIHADI A CIKIN SHARI'AR MUSULUNCI

 

Wannan babi bazai isa yin bayani ba game da ma'anar jihadi baki dayan sa da kuma dalilan sa da hadafin sa da ladubban sa, sai dai zamuyi magana akan sa da takaitawa domin muba me karatu fikira takaitacciya akan maudu'in jihadi domin daukaka Kalmar Allah wanda masu kiyayya ga shari'ar Allah suka samu kafa a cikin sa na suka da bata shari'ar musulunci da kuma tsoratarwa daga gareshi wanda zamu fahimta a cikin sa ta fuskar bayani cewa fa rahama ne ga mutane baki daya.

 

HALIN DUNIYA GABANIN A RARRABA IYAKOKI DA KUMA BAYAN BAYYANAR MUSULUNCI:

 

Duk wanda yake bincike da karatu cikin tarihi na al'umma da kuma ci gabanta baki dayanshi a tarihi zaiga cewa duniya ta kasance wuri ne na yaki kawai wanda turakunta shine dukiya da mazaje, garuruwa nawa aka lallata, kuma aka lallata tattalin arzikinta, aka mayar da matan su zaurawa, da mayar da yaran su marayu, aka kuma keta a dalilinta dukkanin hakkoki na miliyoyin mutane wanda ta rutsa dasu a cikin ko wani wuri, a yankin turawa kawai kasashe basu samu tabbata ba akan kafafuwan su ko kuma iyakokin su na wani dan lokaci takaitacce ba, sun kasance kullum cikin canza iyaka adalilin yaki daga bangaren yamma gabas ko yamma ko kudu da arewa, kuma ba'a kashe wutan yaki ba tsakanin kasashe a cikin kwana daya, kasashe sun kasance ko dai suna biyan haraji (ga wanda sukayi galaba akanta) ko kuma suna amsa (a matsayin wanda sukayi galaba), kuma hadafin wajabta wannan haraji shine sanin daurewan shugabanci ko kuma rashin sa, da ace kasa zata daina biyan haraji ga kasar da ta samu galaba akanta da sun shelanta yakan su.

 

AL'UMMA AKAN TAFARKIN ADDININ SARAKUNAN SU:

 

Wannan shine halin mutum gabanin bayyanan musulunci sun kasance sunabin addinin sarakunan su, yadda babu wanda ya isa ya fandare ga Imbiradhuriyya na albizindiyya cikin yan kasa a misali ko kuma me addinin bautan wuta yayi addinin Imbiradhuriyya na farisa, ko kuma ya zama me ha'inci ga Imbiradhur kuma za'a masa hukunci da kisa da kuma gicciyewa domin yayi addinin makiya, haka akasin haka. Abunda yafi haka muni shine yakin daya faru tsakanin kiristoci dalilin sabanin na aqida, misali akan haka daular rumaniyawa wacce ta abakawa misarawa da kamu domin sun kasance kiristoci a wannan lokacin da addini a hukumance shine bautan gumaka, bayan daular rumaniyawa sun koma addinin kiristanci kuma sai addinin kiristanci ya koma addini a hukumance wanda yaci gaba da da abakwa da kuma yanka misarawa kiristoci saboda banbancin na kungiya!!

 

WAJABTA ADDININ KIRISTANCI DA BAKIN TAKOBI:

 

Kiristoci sun kasance mutane ne yan kadan makaskanta a tsakanin Imbiradhuriyya na rumaniyawa, amma addinin Kisdindin na farko na kiristanci ya karfafasu kiristanci ya zama addini a hukumance ga Imbiradhuriyya na rumaniyawa, akan haka ne yanayi ya canza sai kaskanci ya kima ga dukkanin masu bautan gumaka da kuma rusa wuraren bautan su da mayar dashi coci, haka kuma kaskanci yake ga kiristoc wanda suke da banbanci na bangaranci kamar misali:-

  • A zamanin Theodusiwus na farko an sanar da cewa kiristanci itace addini daya tilo wacce za'a karbeta a Imbiradhuriyya na rumaniyawa, sai aka kona office din Iskanariyya da hujjar cewa ta kunshi littattafai na addinin gumaka, da kuma soke wasanni na olimbiyya na yunaniyawa da hujjar cewa al'ada ce na bautan gumaka.
  • A shekara ta 772 sarki Charlemagne[49] ya yaki Saxon[50] na tsawon shekaru 33 domin ya wajabta masu kiristanci da bakin takobi, ya kuma kasance daga cikin laifukan sa shine mayanka na Firdan[51] wanda aka yanka fursinonin yaki 4500 acikin sasaboda sunki amsan addinin kiristanci, bayan tafiyar rundunan Charlemagne daga wannan mayanka sai Saxon ya kona couka da yanka kasawisawa domin ramuwa ga abunda ya faru, sai Charlemagne yayi doka[52] wanda ya kunshi kashe duk wanda yaki yin addinin kiristanci cikin yan Saxon.
  • A tsakanin shekara ta 1929 zuwa 1945 anyi wani gangami na yan kuroshiya[53] domin yanka wanda suka saba masu yan addinin Arsuzik da kuma tilasta masu yin mazhabar katolika, wanda ya ritsa da dubban mutane.
  • Yaran da aka sace ko kuma al'umma wacce aka sace a tsakanin shekara ta 1909 zuwa 1970 hukumar austreliya da coci na austreliya sun kwace yara daga wurin iyayen su na mazauna kasar yan asalin abirjan da karfin tuwo da kuma nesantar dasu da mayar dasu kiristoci.
  • A shekara ta 2007 Baba Fatika ta gabatar da uzirin sag a mazauna yankin amerika farare akan yanka da kaskantarwan da wahalhalun da suka fuskanta daga wurin mutanen da suka tilasta masu kiristanci masu mulkin mallaka na spaniya[54].
  • A tsakanin karni na goma sha shida dana sha bakwai masu mulkin mallaka na kasar Portugal sun wulakanta da yanka duk wanda yaki yin kiristanci nikin mazauna garin Jawa na Indiya, kuma sun rusa sama da wuraren bauta 300 na indiyawa, bayan haramtawa kasawisawa yan indiya karatun littattafan buzanci masu tsarki a wurin su da kuma yin ukuba ta rashin imani ga duk wanda ya saba, da kuma tilastawa yara wanda suka haura shekara sha biyar jin dadi da bishara na kiristanci, da kuma tilasta masu yaren kasar Portugal ga mutanen kasar indiya da kuma haramta masu amfani da yaren su na asali.

Wannan kawai misali ne takaitacce na tilastawa mutane addinin kiristanci da bakin takobi da kuma wulakanta masu wasu addinai na daban, bayan yawan yakuna wanda aka rura tsakanin bangarori na kiristanci a tsakanin su na katulika protastenant da arsiziks dalilin banbancin sub a bangaranci da kuma wulakanta sashin su ga wasu shashi, daga cikin misalin da zai bayyana tsantsan kiyayya a tsakanin bangarori na kiristanci:

  • Mayanka ga duk wanda ya sabawa mazahabar Kasari na katulika a kasar lanjuwedud wanda suke kudu faransa a shekara ta 1209 zuwa 1229, yadda Baba Inusiyat na uku ya sanar da aikin gicciye duk wani dan Karisawa abunda yakai ga yanka mutane miliyan a cikin shekaru 20 na yaki dasu. Ya kasance farkon wannan mayanka itace mayankar birnin Biziyiyya a shekara ta 1209 yadda aka yanka dukkanin mazauna wannan birni da kuma kona birnin baki dayan sa bayan an masu kawanya me tsanani[55].
  • Mayankar birnin Mirandol, a saransa shekara ta 1545, yadda aka kashe dubban kiristoci na bangaren alwadinasiyana a hannun katulika[56].
  • Mayankar birnin tuluz, a faransa shekara ta 1562 yadda aka kashe mutum 5000 na birutastani a hannun katulika da kuma tayar da birutastani a birnin[57].
  • Mayankan fasi ko kuma wasi, a faransa shekara ta 1562 na katulika masu fada da birutustanant, kuma wannan mayanka ta hura wutan yaki na addini a faransa wanda suka kai yaki takwas ga birutustanant[58].
  • Mayanka na idin me tsarki Mika'ila a birnin Nim, a faransa shekara ta 1567 yadda yan Birutustanant suka zartar da yanka gay an katulika a cikin birnin kuma cikin wanda aka yanka akwai manyan malamai 24 na katulika domin fansa ga wulankancin da katulika tayi masu[59].
  • Mayankan Barsolumiyus, faransa shekarata 1572 yadda aka kashe mutum dubu talatin na birutustanant a hannun katulika[60].
  • Mayanka masu tarin yawa wanda akayi ga mabiyasa birutustanan daga katulika da kuma wanda akayi ma mutanen takulika daga birutustanan a lokacin yakin shekara goma sha daya tsakanin Arilandiyawa yan katulika da albarlimaniyawa turawa da kuma aliskutalandiyawa yan burutustanan, Ireland (1641-1652)[61].
  • Mayanka da wulakanta dubban mutane na sabuwar bangare na ma'amudiyya (Anababitisat) daga takulikawa da birutustaniyawa, a tsakanin shekara ta 1525 da 1660 wanda yakai ga hijira me girma ga mutanen wannan bangare zuwa ga kasar amerika ta arewa[62].
  • A shekara ta 1656 makariyu na uku ya rubuta ta hanyar Andhakiyya game da mayanka wanda yan bulandiyawa yan katulika suka keta sabanin kiristoci mabiya cocin arsuzikisiyya na yunaniya, yan ame nunawa cewa yanda aka kashe a wannan mayankan zasu kai tsakanin dubu sabanin zuwa tamanin[63].

Wannan alamace yar kadan na yawan yakuna da tashin hankula da mayanka da wulakanci wanda mabiya addinai sukayi fama dashi a tsakanin su, bayan haka kuma zamuyi magana akan jihadi a musulunci domin ya bayyana ga ma'abota hankula cewa fa jihadi rahama ne ga mutane bawai kamar yadda wasu suke tunani ba irin na jarirai da kuma kafafen yada labarai mayaudara da munafunci.

 

Jihadi da kuma lamuni ga yancin yin addini

 

Gabanin musan tunbin lamuni na musulunci na yancin yin addini ya wajaba musan manufofin yaki na hakika wanda suran abun zai bayyanan mana dayawa zamu fara mataki mataki wurin fayyace abunda Kalmar jihadi take nufi da kuma abunda jihadi na game gari da kuma kebantacce yake nufi.

1. Jihadi na game gari ya kasu gida biyu:

  • JIHADIN ZUCIYA: shine mutum ya yaki zuciyar sa akan sanin addini da kuma aiki dashi da kuma kira zuwa gareshi da kuma hakuri akan dukkanin cucarwa akan haka, haka kuma yakan ta akan barin ayyukan da aka haramta da kuma aikata ayyukan da aka wajabta gwargwadon iko da iyawa domin neman yardan Allah, manzon Allah s.a.w yana cewa:

“mujahidin shine wanda ya yaki zuciyar sa ga Allah madaukaki” (sahihu Ibn Hibban, da kuma sahigu Abu dawud 2258)

  • JIHADIN SHEDAN: shine yakin shedan da yakinin akan wasiwasi – kokwanto- da yake sanyama mutum na shubuhohi da kaya wanda suke yin illa ga imani. Da kuma yin hakuri akan wasiwasin san a shubuhohi da barna. Allah madaukaki yana cewa:

“idan kuma wani fuzga ya fisgeka daga shedan to ka nemi tsari ga Allah; lalla shi meji ne kuma masani” (suratul fussilat ayata 36)

Jihadi na game gari shine jihadi na hakika matukar mutum yana yakan kansa da shedan kasancewar sa yana lazumtar musulmi tsawon rayuwan sa baya rabuwa dashi, haka dukkanin ayyukan da'a wanda musulmi ke aikatawa domin Allah shi kadai shima Jihadi ne daga cikin su akwai:

  • Aikin hajji na dakin Allah me alfarma yana cikin jihadi saboda wahalhalun dake cikin sa da kuma yin hakuri na cutarwa da kashe kudi domin Allah, an karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace: (nace ya manzon Allah muna ganin jihadi shin mafi alherin aiki, shin bazamuyi jihadi ba muma? Sai yace: “sai dai mafi alherin jihadi shine yin aikin hajji mabrur – wanda babu sabon Allah aciki –“) (buhari ne ya rawaito shi)
  • Fadin gaskiya, manzon Allah s.a.w yace: (mafi alheri jihadi shine Kalmar gaskiya a gaban shugaba azzalumi) (sahihu Abu awud).
  • Isar da musulunci ga wand aba musulmi ba dayin kira zuwa gareshi ta hanyar masa bayani da hujja da alkur'ani da hakuri akan karyatawan ga wanda aka karyata shima yana cikin hijadi, Allah madaukaki yana cewa: “da mun so da mun aikama ko wani alkarya da me gargadi (51) kada kayi biyya ga kafirai kuma kayi masu jihadi dashi jihadi babba (52)” (suratul furkan 51-52)
  • Yin umurni da kyakyawan aiki da hani da mummunan aiki shine yana cikin Jihadi kuma shine tafarkin manzanni da mabiyan su wanda suka zo bayan su, manzon Allah s.a.w yace: babu wani annabi a cikin wani al'ummar da suka gabace ni face ya kasance yana da mataimaki cikin mutanen sa da sahabban sa wanda zasuyi kodi da riko da sunnar sa bayan sa sa'annan wasu al'umma zasu zo bayan su suna fadin abunda basa aikatawa da kuma aikata abunda ba'a umurce su dashi ba duk wanda ya yakesu da hannun sa mumini ne wanda kuma ya yake su da harshen sa shima mumini ne wanda kuma ya yakesu da zuciyar sa shima mumini ne kuma babu wani imani bayan wannan koda kwatankwacin kwayan zarri” (muslim ne ya rawaito shi)
  • Kyautatawa mutane da kuma rashin cucar dasu da kuma yin aiki domin shigar da farin ciki cikin zukatan su da yin hakuri akan cutarwan su duk yana cikin Jihadi, manzon Allah s.a.w yana cewa: “me aiki domin taimakon mara miji da miskinai kamar mujahidin ne fisabilillah ko kuma kamar me sallan dare ne da kuma azumi da rana” (buhari ne ya rawaito shi)
  • Tafiya domin neman ilimi shima yana cikin jihadi, manzon Allah s.a.w yana cewa: “duk wanda ya fita domin neman ilimi yana tafarkin Allah har sai ya dawo” (tirmizi ne ya rawaito shi kuma y ace hadisi ne hasan, albani kuma ya inganta shi cikin littafin sahihul targib wal tarhib: 88)
  • Neman ilimi yana cikin Jihadi, manzon Allah s.a.w yana cewa: (duk wanda yzo wannan masallaci nawa domin wani alherin da yake so ya kowa ko kuma ya karantar dashi to yana da martaban Mujahidi akan tafarkin Allah wanda kuma badan haka ba to kamar mutumin da yake neman kayan da ba nashi ba) (sahihu Ibn Hibban, sahihul Jami'u: 6184)
  • Biyayyar iyaye, hakika wani mutum yazo gun manzon Allah s.a.w yana nemna izinin san a zuwa Jihadi sai yace: “(iyayen ka suna raye?) sai yace: eh sunanan, sai yace: (kaje kayi jihadi akan su - na masu biyayya da hidima-)” (suhihul buhari)
  • Rikon amana da kuma rashin yin ha'inci da kuma kiyayewa ga duk wanda mutane suka daurashi kan amanar aiki ko kuma na al'umma shine yana cikin jihadi, manzon Allah s.a.w yana cewa: “me aiki idan an sanya shi aiki sai ya amshi gaskiya kuma ya bada gaskiya bazai gushe ba yanan jihadi a kan tafarkin Allah har sai ya dawo zuwa gidan sa” (Dabarani ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi cikin sahihul targb wal tarhib: 774)

2. Jihadi takaitacce (jihadin kare kai da jihadin nema):

Allah madaukaki yana cewa: “don me yasa bazakuyi yaki ba fisabilillah alhali masu rauni cikin maza da mata da yara suna cewa ya ubangijin mu ka fitar damu cikin wannan gari masu zalumtar mutanemn su, kuma kasanya mana majibinci daga gare ka kuma kasanya mana mataimaki daga gare ka” (suratun nisa'i ayata 75)

 

Jihadi kuma ya kasu zuw gida biyu:

Jihadin kare kai: ya kasu zuwa gida biyu:-

  1. JIHADI NA WAJE: yana kasancewa ne da kare zalumci da kuma kawar dashi da yakan duk wanda yayi ta'addanci akan gidajen musulmai ko kuma mutumcinsu ko dukiyan su ko addinin su wannan gaskiya ne an shar'anta shi ga mutane baki daya amma yaki domin wata maslaha na duniya kamar samun karfin iko ko kuma yaki domin ramuwa hakika musulunci ya hana su.
  2. JIHADI NA CIKI WANDA IRI BIYU:
  1.  Jihadi na daidai ku: yana kasancewa ne da kare kai ko kuma kare wasu daga wani dan ta'addan wanda yake son sata ko kuma kisa ko ta'adi, wannan jihadin yana kasancewa ne ko dai da hannu watan mayar da dan ta'adda da dakatar dashi, idan hakan ya gagara sai yayi da harshe watan magana, idan hakan ya gagara sai yaki abun a zuciya, wannan shine nau'i na karshe me matukan muhimmanci kuma muhimmancin san a raya zukata taki zalumci kuma bazata saba ba da ganin sa, manzon Allah s.a.w yana cewa: “duk wanda yaga wani mummunan abu acikin ku to ya canzashi da hannun sa idan kuma bazai iya ba to yayi da harshe idan kuma bazai iya ba to yaki abun da zuciyan sa. wannan shine mafi raunin imani. (Sahihu muslim)
  2.  Jihadi na jama'a: shine yaki mutanen da kuka kawo hari ga musulmai har sai sun koma zuwa ga gaskiya Allah madaukaki yace: “idan wasu mutane suna fada cikin muminai to kuyi sasanta sakanin sui dan daya ya afkawa dayan to ku yaki wanda ya afaka har sai ya koma zuwa ga al'amarin Allah; idan kuma ya koma to sai ku sasanta tsakanin su da adalci kuma kuyi adalci lallai Allah yana son masu adalci” (suratul hujurat ayata 9)

Wannan shine ma'anar fadin manzon Allah s.a.w: “ka taimaki dan uwanka wanda yayi zalumci ko kuma aka zalumta.” Sai muakce ya manzon Allah zamu taimake shi idan an zalumce shi amma taya zamu taimake shi idan shine yayi zalumcin? Sai yace: “ka hanashi zalumcin shine taimakon sa.” (Buhari da Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito shi)

 

  • JIHADI NA NEMA:

Domin mu fahimci menene jihadi na nema zamu kawo wani bangare daga cikin sakwanni na manzon Allah s.a.w wanda ya aika zuwa ga Hirakal Imbiradur bizanadhata da kuma almukuskus shugaban Iskandariyya domin muga abunda ke faruwa da basira bawai da ido ba kawai.

 

Sakwannin manzon Allah s.a.w domin kare kiristoci:

 

Manzon Allah s.a.w yayi ramuwa ga zalumcin dake faruwa a tsakanin kiristoci da kuma zalumtar kawunan su na yima Allah kishiya cikin wannan sako zuwa ga Hirakal sarkin Rum, ya kasance cikin sakon sa:

“da sunan Allah me rahama mejin kai, daga Muhammad manzon Allah s.a.w zuwa ga Hirakal sarkin Rum, amincin Allah ya tabbata ga wanda yabi shiriya, bayan haka: lallai ni ina kiranka zuwa ga kiran musulunci, ka musulunta zaka tsira, ka musulunta Allah zai baka ladanka nunki biyu, idan kuma ka juya baya to zunubin Arisinawa yana kanka, kuma (yaku ma'abota littafi ku zo zuwa ga wata kalma dai-dai a tsakanin mu daku cewa bazamu bautawa kowa ba sai Allah kuma bazamu hada Allah da komai ba cikin bauta kuma sashin mu bazasu riki wani sashi ba abun bauta koma bayan Allah; idan sun juya baya kuce ku shaida mu musulmai ne). (sahihu Muslim)

Kuma yayi magana har wayau ga makuskus[64] sarkin Kibdi shugaban Iskandariyya, ya kasance cikin sakon sa:

“da sunan Allah me rahama mejin kai, daga Muhammad bawan Allah kuma manzon sa zuwa ga makuskus sarkin kibdi amincin Allah ya tabbata ga wanda yabi shiriya, bayan haka: lallai ni ina kiranka zuwa ga kiran musulunci, ka musulunta zaka tsira, ka musulunta Allah zai baka ladanka nunki biyu, idan kuma ka juya baya to zunubin Kibdaniyawa yana kanka” (zadul ma'ad 3/603)

Hakika manzon Allah s.a.w yayi nuni cikin wasikun sa guda biyu kuma ya daura nauyin laifi na yankan mutanen Arisaniyawa[65] da Kibaniyawa a masar akan Hirkal da Makuskus.

Babban abun ambata shine Ariwusanawa basu bawai kawai mutanen sai dai turawa kusan sune mafiya rinjaye, kuma Kasisi Jirum ya ambaci haka yana cewa:

ka tashi duniya da haske domin ya samu kansa a ba'ariwusayawa!![66]

An wulakanta arisayawa ta hannun masarautan romawa ta hannun sarakunan su wanda arisayawa ne, sannan hakan ya yadu a arewaci, gabas, tsakiya da yamman turai a karkashin wulakantarwan arisayawa ta hannun sarakunan su ( visigoth da Ostrogoth), da sarkin Vandal, da sarkin Suebi. Hatta Sir Isaac Newton shimaba'arise ne.

Sai dai cin mutuncin da akayima arisaniyawa dayawa suna kokarin boyewa, kuma duk me son Karin sani game da hakan sai ya koma littattafai wanda aka ambaci wasu daga wannan cin mutuncin akansu.

Kuma kamar yadda muka fadi ne a baya cewa ka'idar da ake aiki da ita abaya cikin duniya baki daya itace”mutane suna kan addinin sarakunan su ne na dole, bawanda yake da zabin yin addini daya so a cikin su", saboda haka jihadin nema shine jihadi wanda rundunan musulmai ke fita a cikin sa domin isar wa da yada sakon musulunci ga mutane da kuma bayya Kalmar Allah da kuma kore shugabancin shuwagabanni na dole akan mutanen su akan yin addinin su da kuma hanasu yin addinin musulunci, sharhin haka zai zo a kasa. A cikin wannan nau'i na jihadi ya banbanta da jerin daya wuce, baya farawa da hannu sai harshe sai zuciya, a'a yana faraway ne da harshe sai hannu, kuma an sharudda cikin wannan nau'i na jihadi ya kasance da izinin shugaban musulmai.

 

Manyan Ka'idoji na yaki domin isar da sakon musulunci:

 

1. Samun izini daga shugaban Musulmai:

Sheikh Muhammad dan Usaimin Allah yayi mashi rahama yace: “baya halatta yakan runduna face da izinin shugaba duk yadda al'amarin ya kasance domin wanda aka umurce su dayin yaki da jihadi suna shuwagabanni bawai dai-daikon mutane ba, su dai-daikun mutane suna bin shugabannin shura'a ne, baya halatta ga wani yayi yaki ba tare da izinin shugaba ba sai dai idan yakin kare kai ne, idan makiyi ya mamaye shi kuma suna jin tsoron su to anan zasu kare kansu domin wajabcin yin jihadi. Hakan be halatta bane domin al'amarin yana kewaye ne da shugaba yaki ba tare da izinin shugaba ta'addanci ne kuma ketare iyakan sa ne, kuma saboda da ace ya halatta ga mutabe yin yaki ba tare da izinin shugaba ba da matsalar ta zama hayaniya. Duk wanda yaso kawai sai yahau dokin sa yayi yaki. Kuma saboda da anba mutane daman haka da barna me girma ta faru.”[67]

2. Iko da daman yin yaki Kuma sheikh usaimin ya kara fadin sharadin me matukan muhimmanci na jihadin nema wanda shine iko akan haka sai yace: “dole ne ya zama akwai sharadi a cikin sa, wanda shine ya zama musulmai suna da iko da karfi wanda zasu iya yin yakin dashi, idan basu da iko to lallai jefa kansu cikin yaki jefa kai ne cikin halaka, saboda haka ne Allah – madaukaki - be wajaba ba akan musulmai yin yaki a makka, domin basu da iko ga rauni, a lokacin da sukayi hijira zuwa madina suna kafa kasa ta musulunci suka zama suna da karfi sai aka umurce su da yaki, akan haka ya zama dole sai da wannan sharadi idan kuma bah aka ba to wannan wajabcin ya fadi akan mutane kamar sauran ayyukan wajibobi, domin ana shar'anta iko acikin su"[68].

 

MATAKAI NA JIHADIN NEMA:

 

Jihadin nema yana da matakai guda uku wanda sharadi ne a binsu a jere din su yadda suke wannan matakai kuma sune:-

  1. DA'AWA – KIRA -: yadda musulmai zasu fara aikawa da sakwannni na kira zuwa ga wani sarki suna kiranshi zuwa ga musulunci, kuma wannan sarkin yana da yanci kai tsaye na amasan wannan kira da shiga musulunci ko kuma tsayawa akan addinin sa.
  2. BIYAN JIZIYA: jiziya tsari ne na duniya wanda ake aiki dashi a duniya baki dayan sa tun a zamanin da har zuwa wannan zamani namu, alama ne na biyayya ko kuma sulhu da ittifaki da aminci, kuma dukkanin kasashe na duniya kodai kasa ta amsa jiziya (wani kudi sananne) ko kuma ta biya jiziya ga wata kasar ta daban, kuma ya kasance ma'anar kin biyan kasa ga wannan jiziya sunyi watsi da wannan biyayya kenan ko kuma sulhu dasu da kuma shirinta na tayar da yaki. Tsarin jiziya ana amfani dashi har yanzu duniya baki dayanta ta kasu cikin kawance masu yawa, yadda ko wace kasa cikin kasashe manya take shirya kawance na duniya tare da kasashe kanana domin basu taimako na siyaysa ko kuma na karfin soja… da sauran su, maimakon wannan taimako kuma manyan kasashe suna samun wasu abubuwa na amfani na kudi kamar wata kasa karama ta yardan mata yin amfani da hanyoyin ruwanta domin yin aikin soja a gareta, ko kuma manyan kasashe ta samu abubuwan da wasu kasashen ke fitar na kaya ko uranion ko karfe ko man fetur da farashi me saukin gaske, ko kuma da samu damar habaka tattalin arzikin ta, da makamantan su, dukkan wannan ana daukan sa a matsayin abokin hulda na sadaka da kuma taimako na siyasa da soja, da ace wata kasa zata kai hari ga kasar da suke da kawance da wata babbar kasa da wannan kasa ta shigan mata da karfin soja da kuma kare ta, wannan shine abunda aka sani na tsarin jiziya.

Kuma ya wajaba ga shugaba yin kira domin shiga musulunci ga wanda sukaki amsan kira da kuma kare shugabancin sa, bazai farma wani ba, sai dai ya nemi ya biya jiziya kuma wani yan kudi ne domin kariyan da ake bashi wanda yake rayuwa a cikinta a kasar musulunci, tunda cewa iyakan kasar sa yana da iyaka da kasar musulunci wannan yana matsayin kulla yarjejeniya ce ta aminci wanda ake aiki dashi cikin kasashe duniya baki dayan su kamar yadda muka fadi, lamuni ce na rashin farmasu daga kasar musulunci, kuma haka a halin da wasu runduna na daban suka farmasu ya wajaba akan musulmai su mayar da wannan ta'addancin akan su ta hanyar yakan dan ta'adda.

Kuma ya wajaba a fadakar akan cewa karban jiziya da shugaba keyi bawai ma'anar sa cewa yana da yancin aikata abunda yake so bane ga mutanen sa na bautar dasu ko azabtar dasu da wajabta masu bin addinin sa, a'a kuma ya wajaba a gareshi da cewa kada ya yaki muslunci da musulmai, kuma kada ya shiga tsakanin maluman musulmai da mutanen su, ya kyale su yin kira ga mutane domin shiga musulunci, duk wanda yaso acikin su bayahude ne ko kirista ya musulunta kuma baza'a wulakanta shi ba kuma wanda yaso ya tsaya a addinin sa, Allah madaukaki yace:

“kuma ka fadi gaskiya daga ubangijin ka; duk wanda yasu yayi imani wanda kuma yaso ya kafurta; lallai mun tanadar wa azzalumi wata irinn wuta wacce zata shanye gabban su” (suratul kahafi ayata 29)

3. YAKI: da sarki zai yin abunda muka lissafo na shiga musulunci ko kuma biyan jiziya ko rashin wulakanta mutanen sa, anan ne kawai aka yardan ma rundunan musulmai yin yaki da wannan sarki da rundunan dake tare dashi, amma kuma basu da alaka da mutanen sa, bazasu yaki wanda basa yaki ba kuma bazasu afkawa mata ba ko yara ko tsofaffi ko masu ibada ko kuma wanda suka barranta daga yakin.

 

Abubuwan da suke hana

yakin nema:

 

Yakin nema bawai kai tsaye yake ba a'a yana da abubuwan da suke hanashi daga ciki akwai:-

  1. Rashin iko ga musulmai akan yin yaki, domin rashin karfin su ko kuma karantan su.
  2. Rashin samun alkawari da kafiri domin kuwa baya halatta warware wannan alkawari, kuma wannan yana da misali a wannan zamani namu mafi yawancin kasashen duniya suna da alkawura a tsakanin su da hadaka na kasuwanci.
  3. Samun maslaha a fili na rashin yin yaki tare da iko akan haka, kamar yadda yake cikin sulhul hudaibiya.

 

MANUFA NA YIN JIHADI:

 

Abunda ake nanatawa dayawa cikin wasu kafafen yadan labarai wanda basu tabbata ba kuma bakomai bane face karya domin tabbatar da wani manufa na siyasa nasu shine magana cewa jihadi ga yaki ne ga duniya domin su kasance karkashin shugabanci daya wanda wannan magana ba gaskiya bane fadin Allah madaukaki yana karyata shi:

“da ubangijin ka yaso daya sanya mutane sun zama a'umma daya; kuma bazasu gushe ba suna samun sabani (118) sai dai wanda Allag yayima rahama; domin haka aka halicce su; kuma kalmar ubangijin ka ta gabata cewa sai na cika jahanna da aljanu da mutane baki daya (119)” (suratu Hudu 118-119)

Manufa na jihadi zai bayya ne na hakika cikin fadin Allah madaukai:

“anyi izini ga wanda suke yaki lallai fa an zalumce su kuma lallai Allah me iko ne akan taimakon su (39) wanda aka fitar dasu daga gidajen sub a tare da wani laifi ba sai dan sunce ubangijin mu shine Allah; kuma badan kariyan Allah baga mutane sashin su akan sashi da an rurusa wuraren ibadu da kasuwanci da wurin sallar kiristoci ko yahudawa da masallatai wanda ake ambaton Allah acikin su; kuma wallahi Allah zai taimaki wanda yake taimakon sa; lallai Allah me karfi ne kuma mabuwayi (40) wanda idan mun tabbatar dasu a doron kasa suna tsaida sallah kuma suna bada zakka kuma suna umurni da kyakyawan aiki da yin hani daga mummunan aiki; kuma ga Allah karshen abubuwa ke komawa” (suratul hajji ayata 39-41)

Allah madaukaki ya kara cewa:

“dan me yasa bazakuyi yaki ba domin Allah alhali masu rauni daga cikin maza da mata da yara wanda suke cewa ya Ubangijin mu ka fitar damu daga cikin wannan gari me zalumtar mutanen ta; kuma kasanya mana majibinci daga gare ka kuma ka sanya mana mataimaki daga gareka.” (An-Nisâ’ 4:75)

Kamar yadda muke gani cewa manufan Jihadi shine kare hakki da addini da kuma kare zalumci, yahudawa da kiristoci da musulunci suna amfana dashi, bawai kawai kariyan na amfanin musulmai bane kawai[69]. Badan abunda Allah ya shar'anta ba na kare zalumci da barna dayin yaki da an rusa gaskiya da lallata duniya kuma da an rusa wuraren ibadu na fadoji da cocuka na kiristoci, da wuraren bauta na yahudawa, da masallatan musulmai[70]. Mun gani kuma cikin ayar cewa sakamakon jihadi ko kuma abunda yake bayan yakin bayan mutanen gaskiya sunci nasara akan mutanen banza da zalumci da barna, yadda ayara tayi bayanin cewa mujahidai musu riko da hadafin jihadi wanda shin gyara bawai yada barna ba, sai su tsayar da salla basa mugunta a doron kasa, kuma suna fitar da zakkan dukiyoyin su ga masu shi cikin talakawa da mabukata kuma basa rubda ciki da dukiyoyin mutane da arzikin su na kasa, kuma suna umurni da kyakyawan aiki da hani daga mummunan aiki.

 

MUTANEN DA AKE NUFA DA YAKI:

 

Idan jihadi ya kasance domin kiyaye gaskiya da kuma daukaka Kalmar Allah da kiyaye masu rauni kenan suwa ake yaka?!! Allah madaukaki ya bayya wanda ake nufa da jihadi cikin fadin sa:

“kuma Allah be hanaku ba ga wanda basu yake ku ba kuma basu fitar daku daga gidanje da kuyi masu biyayya da kuma yin adalci a garesu; lallai Allah yanason masu yin adalci (8) lallai wanda Allah ya hanaku sune wanda suka yake ku cikin addinin ku kuma suka fitar daku daga cikin gidajen ku kuma sukayi yunkurin fitar daku da ku so su; duk kuma wanda yaso su to wannan sune azzalumai” (suratul mumtahana ayata 8-9)

Dan abbas yana cewa:

(mushrikai sun kasance cikin matsayi biyu agun manzon Allah s.a.w da muminai: sun kasance mushrikai masu yaki, suna yakansu suma suna yakan su, da mushrikai na amana da alkawari, wanda basa yakan su kuma suma basa yakansu) (buhari ne ya rawaito shi)

Kuma hakika manzon Allah s.a.w yace:

(duk wanda ya kashe wanda akayi alkawari dashi ko kuma wanda yake karkashin kariyan Allah da manzon sa, to bazai ji kamshin aljanna ba, kuma lallai kamshinta anajin sa ne tun daga nisan tafiyar shekara saba'in) (Ibn Majjah ne ya rawaito shi kuma ingantacce ne hadisin)

Ya kuma kara fadi har wayau s.a.w:

(ku saurara kuji duk wanda ya kasa dan amana wanda yake da kariyan Allah da manzon sa to hakika ya kunyata kariyan Allah kuma bazaiji kamshin aljanna ba, kuma kamshinta anajinsa ne tun daga nesan tafiyan kaka saba'in) (tirmizi ne ya rawaito shi – hadisi ne ingantacce)

Ya kuma kara fadi har wayau s.a.w:

“lallai zakuci kasar misra da yaki kuma kasace wacce akwai Kiradi acikinta – sunan kudin da suke amfani dashi ne a misra a lokacin – idan kun bude ta to ku kyautata ma mutanen garin domin sunada kariya da dangantaka.” Ko kumakariya da sirikanci” (muslim ne ya rawaito shi)

Mujahid ( Allah ya kara masa yarda) na rawaito cewa:

" Abdullahi dan Umar an yanka masa rago domin tarban sa daga tafiya, bayan yazo sai yace: ' shin kun tsamma makwabtar ku kuwa wani abu daga ciki, watan yahudawa? Shin kun tsamma makwabtar ku kuwa wani abu daga ciki, watan yahudawa? Naji manzon Allah s.a.w yana cewa: ' mala'ika Jibril be gushe ba yana mun wasiyya game da kyautatwa makwabci har saida nayi zaton cewa Allah zai bayar da umurnun a raba gadon ka dasu." (Tirmizi ne ya rawaito shi)

 

Menene littafin kiristoci ya rubuta game da Jihadi:

Bari muga abunda littattafan kirista na ambata da kansu akan irin girman lafiya da kuma rashin wulakanta su daga musulmai, sun ambata cikin littafin al sankasar[71] wanda yana cikin muhiman littattafan coci na Khabadiyyawan arsuziksiyya, kuma littafi ne wanda ya tattara tarihi na dukkanin annabawa da shahidai da masu girman cikin su, akan labarin Amru dan Aas Allah ya kara masa yarda da Baba Bunyamin na farko[72], wanda acikinta zamu iya ganin wanda ake nufa da jihadi da kuma yadda musulmai ke mu'amala da al'umma, kuma zamu gani cikin labarin gaskiyan suwace suke wulakanta al'umma:

“lallai saboda mayankan Imbiradhuriyya na Bizandhiyya da kuma wulakantawar su ga Khabidawa yan misra, ya sanya annabi bunyamin na farko Baba Iskandariyya guduwa shi da mutanen sa zuwa kan dutse na tsawon shekara 13, bayan musulunci yaci garin misra ta hannun Amru dan Aas – Allah ya kara masa yarda – sai Amru dan Aas ya tafi bude birnin Iskandariyya da yakan Rumawa nanan wurin domin yakore su, sai girgiza da tsoro na samu tsaro, sai wasu miyagu rumawa sukayi amfani da wannan dama suka kona coci da wuraren ibadu, ya kasance daga cikin su akwai coci me tsarki na Mirkas[73] kuma suka sace dukkan abunda ke cikin sa, sai wani mutum sojan ruwa ya shiga cikin cocin ya sanya hannun sa cikin lalita Mirkas me tsarki yana tunanin akwai kudi ne a ciki, sai be samu komai ba sai gangan jiki sai ya dauke kayan dake jikin sa, ya dauk kan Mirkas me tsarki tare dashi ya jega jikin jirgin ruwan sa. shi kuma Amru dan Aas a lokacin daya san buyan Baba Bunyamin, sai ya aika sako zuwa sauran biranen na misira yana cewa: “wurin da akwai Baba bunyamin a na kiristocin Khibdawa suna da alkawari da aminci,to su zo cikin kwanciyan hankali domin yaci gaba dajan ragamar mutanen su da cocin, sai annabi bunyamin yazo bayan ya shude shekaru goma sha uku na a inda ya gudu, sai Amru dan Aas ya karrama shi matuka ya kuma yi umurni da abashi cocin shi da sauran abubuwan daya mallaka.” A lokacin da rundunar Amru sukayi niyyar barin Iskandiriyya zuwa ga gashi biya na garuruwa, sai daya daga cikin jirgin ruwa ya tsaya baya motsawa daga wurin sa, sai rundunar Amru suka domin duba shi sai sukaga kan Mirkas me tsarki. Sai suka kira Baba bunyamin ya dauka ya tafi dashi tare dashi akwai bokaye da mutane suna waka na farinciki har suka kai cocin su.”

 

MATAKAI MATAKAN DA HUKUNCIN JIHADI YABI TUN DAGA HARAMTA SHI ZUWA WAJABTASHI:

 

  1. HARAMTA YAKI: jihadi na yaki ya kasance a farkon da'awar musulunci haramun ne ga musulmai, Allah madaukaki yace: “shin baka gani ba ga wanda aka ce masu ku kame hannayen ku daga yaki ku tsayar da sallah da bayar da zakkah” (suratun nisa'i ayata 77)
  2. IZININ YIN YAKI: daganan sai akayi ma musulami izinin yin jihadi bayan mushrikai sun faro kuntata masu ta hanyar rayuwan su da kuma tilasta su barin gidajen su, Allah madaukaki yace: “anyi izini ga masu yaki cewa fa an zalumce su kuma lallai Allah me iko ne game da taimakon su (39) wanda aka fitar dasu daga gidajen sub a tare da wani dalili ba sai dan sunce ubangijin mu shine Allah” (suratul hajj ayata 39-41)
  3. KARE KAI DAYIN YAKI IDAN AN FADO MAKU DA YAKI: daganan sai umurnin yin jihadi yazo idan mushrikai sun fadama musulmai suka kuma fara takulan su da yaki, Allah madaukaki yace: “ku yaki wanda suke yakan ku domin tafarkin Allah kuma kada kuyi ta'addanci, lallai Allah bayason masu yin ta'addanci” (suratul bakara ayata 190)
  4. UMURNI DAYIN YAKI: a lokacin musulunci ya bayyana ya kuma yadu mutane sun fara shiga cikin sa kungiya kungiya, kuma makiyan su sun karu na waje na kasashen dake gefen su wanda suke ganin akwai babban hatsari akan su a cikin haka, Allah madukaki ya umurci musulmai da yin yakin nema domin isar wa da kai sakon tauhidi ga mutane da kuma yada addinin musulunci da daukaka Kalmar Allah, da kuma neman sarakuna da shugabanni da kiransu zuwa ga musulunci, domin nufin daukaka Kalmar tauhidi da tabbatar da adalci da yada shi bawai domin yakin faidi da karfi da zartarwa da daukaka da girman kai ba a doron kasa ko kuma domin ramuwa wanda sakamakon sa shine barna da dirkakewa, Allah madaukaki yace: “kada ku zama kamar wanda suka fita daga gidajen su masu tunkawo da riya ga mutane kuma suna kangewa game da tafarkin Allahl kuma Allah ya karade dukkan abunda suke aikatawa” (suratul anfal ayata 47)

Hakika alkur'ani ya bayyana wulakancin daya samu wanda sukayi imani da Allah cikin kiristoci a hannun mutanen su gabanin bayyanar musulunci kuma Allah ya tabbatar da labarin wulakancin nasu cikin alkur'ani domin ya bayyana manufa na hakika shine dauke zalumci akan muminai sun kasance kiristoci ne ko kuma yahudawa ko musulmai: Allah madaukaki yace:

“An la’anci mutanen rami (4) wato wuta wadda aka hura (5) a lokacin da suke akan (gefen) ta a zazzaune (6) alhali su bisa ga abinda suke aikatawa ga muminai, suna halarce (7) kuma basu tuhumce su ba, face kawai domin sunyi imani da Allah Mabuwayi, Wanda ake godemawa (8).” (suratul buruj ayata 4-8)

Hakika wannan ayoyi sun sauka cikin alkur'ani domin ya tabbatar da labarin mumimai na kiristan kasar yamen har abadan wanda suka kasance gabanin zuwan manzon Allah Muhammad s.a.w, an azabtar dasu daga wurin mutanen kasarsu domin sunyi imani da Allah madaukaki, aka haka rami me zurfin gaske domin su aka kuma rurashi da wuta sai aka basu zabi ko dai su bar addinin su ko kuma ajefa a wannan wuta, haka dai aka jefa su ciki domin sunyi imani da Allah madaukaki suka kuma zauna a wurin wannan rami suna ganin azabar da kuma kona su din.

 

KA'IDOJI NA JIHADI A MUSULUNCI:

 

Jihadi a musulunci yana da ka;idoji da ladubba wanda ya banbanta dashi daga zalumci ko mugunta da kuma ta'addanci, ba'a kashewa cikin abokan gaba sai wanda yaye yaki ko kuma ya taimaka akan yakin. Kuma an haramta kashe tsofaffi da yara da mata da marasa lafiya da likitoci na marasa lafiya da masu rauni da firsinonin yaki haka kuma masu ibada wanda suka shagaltu da ibadar su!. Kuma ba'a karasa me rauni cikin mayaka, kuma ba'a gunduwa gunduwa da wanda aka kashe, kuma ba'abin wanda ya gudu daga yakin, kuma ba'a kashe dabbobi, kuma ba'a rusa gidaje, kuma ba'a rusa wurarern ibadu da barna, kuma ba'a lallata ruwa da rijiyoyi, kuma ba'a yanke bishiyoyi ko kuma kona su.. zuwa dai karshe.

Hakikan wannan ya kasance shine karantarwan manzon Allah me daraja s.a.w da khalifofin sa a bayan sa ga rundunar su wanda suke turawa yin yaki, ya kasance wasiyyar khalifar manzon Allah s.a.w Abubakar al siddiq Allah ya kara masa yarda ga shugabannin rundunar sa:

“ku tsaya zanyi maku wasaici da abubuwa goma ku kiyaye su daga gareni: kada kuyi ha'inci, kuma kada ku boye wani abu cikin kayan ganima, kuma kada kuyi yaudara, kuma kada kuyi gunuduwa gunduwa, kuma kada ku kashe yaro karami, kuma kada ku kashe tsoho ko mace, kuma kada ku yanke bishiyan dabino ko kuma konata, kuma kada ku yanke bishiya me yara, kuma kada ku yanka akuya ko sanuwa ko rakumi sai idan ci zakuyi. Kuma zaku wuce wasu mutane sun shagaltu cikin wuraren bauta ku kyale su da abunda suka shagaltu dashi.[74]

Su kuma firsinonin yaki a musulunci suna da hakkoki: baya halatta a zabtar dasu ko kuma kaskantar dasu ko kuma tsoratar dasu ko kuma hanasu abinci da abunsha har sum utu, a'a a mutunta su da muka kyautata masu mu'amala, saboda fadin Allah madaukaki:

“kuma suna ciyar da abincin a bisa son su ga miskinai da marayu da kuma firsinan yaki (8) hakika muna ciyar daku ne domin domin kuma bama neman sakanya ko kuma godiya daga gare ku.[75]

Daular musulunci tana da hakkin yin mu'amala da firsinonin yaki gwargwadon maslaha na jama'a da kuma ittifaki na kasashe kodai su sake firsinonin sub a tare da biyan fansa ba ko kuma kuma su fanshi kansu da kudi, ko kuma ayi musayan su da firsinoni musulmai.

Amma ga sauran gama garin mutane wand aba musulmai ba dake cikin wannan daula wacce musulmai suka shiga, hakika musulunci ya haramta yi masu ta'adi ko kuma cucat dasu ta ko wani irin yanayi, manzon Allah s.a.w yace:

“wanda ya kashe wanda akayi alkawari dashi yana da kariyan Allah da kariyan manzon sa, bazaici kamshin aljanna ba kuma kamashin ta anajin sa ne daga nisan tafiyar shekara saba'in” (Ibn Majjah ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi cikin littafin alsahiha: 2356)

Kuma ya haramta kutse cikin darajar su, ba'a kaskantar dasu ko kuma jizginawa, kuma ba'a zamumtar su ko kuma wulakanta su, hakika manzon Allah s.a.w yace:

“ku saurara kuji duk wanda ya zalumci wanda akayi alkawari dashi, ko kuma ya toye masa hakkin sa ko ya sanya shi aikin da yafi karfin sa, ko kuma ya amshi wani abu a hannun sa ba tare da yardan sa ba to lallai ni zanyi jayayya dashi ranan alkiyama” (abu dawud ne ya rawaito shi, alsilsilatul sahiha: 445)

Kuma manzon Allah s.a.w ya kasance yana yin wasiyya ga sahabban sa mujahidai da kyautatawa mutanen garin da sukaci da yaki dayi masu mu'amala me kyau yana cewa:

“lallai zaku bude misra kuma kasa ce wacce akwai Khiradi acikinta, idan kun bude ta to ku kyautata ga mutanen ta domin sunada kariya da dangantaka.” Ko kumakariya da sirikanci” (muslim ne ya rawaito shi)

Mafi alherin dalili akan zartar da wasiyyar manzon Allah s.a.w wshine wannan alkawarin da Umar dan Khaddab Allah ya kara masa yarda ya bayar ga mutanen baitul makdis lokacin daya shigeta bayan ya budeta sai yace:

da sunan Allah me rahma mejin kai. Wannan shine abunda bawan Allah Umar dan Khaddab shugaban muminai ya bayar ga mutanen baitul makdis na aminci: ya basu amana akan rayukan su da dukiyoyin su da cocunan su da wuraren ibadun su…. Kuma baza'a tilasta masu ba akan addinin su kuma baza'a cutar da wani ba a cikin su…. Zuwa karshe.

Shin tarihi ya taba ganun wannan tsantsan adalci da yafiya daga bangaren wanda yaci nasari wanda yayi galaba akan wanda y agama dasu?! Duk da cewa Umar Allah ya kara masa yarda yana da iko ya fada masu abunda ya so na sharudda! Sai dai kawai adalci ne da kuma burin yada addinin Allah, da son alheri ga mutane. Wannan yana nuna cewa jihadi a cikin musulunci bawai domin kwadayin abun duniya bane.

 

Shin ko wani yaki ne daga musulmai ya zama jihadi:

 

Ya wajaba mu lura cewa bafa ko wani yaki bane wanda kasar musulunci keyi yake jihadi, kuma ba duk wanda yayi yaki bane cikin musulmi yake mujahidin, jihadi yana da sharudda kuma mu musulmai muna banbancewa a kullum tsakanin Kalmar jihadi da Kalmar yaki, kafafen yada labarai dayawa na wannan zamani suna kokarin bata sunan musulunci ta hanyar jihadi ta ko wani kafa domin tabbatar da manufa ta siyasa wacce sune so, mu duba mugani cikin ko wace yaki da akeyi a duniya idan ya kasance ne a tsakanin kiristoci sai suce: “yaki ya kautre tsakanin kasa kaza da kasa kaza”, kuma bata hada wannan yaki da addinin masu yaki, amma idan dayan bangaren da suke yaki ya kasance musulmi sai kaji sunce: “musulmai musu tsananin ra'ani mujahidai suna shelanta yaki akan kasar kirista.”

Tambayar anan itace: me ya sasu kiran Kalmar jihadi akan wannan yaki ko kuma Kalmar mujahidai akan wannan masu yakin?!! Domin su sani ko wannan yakin jihadi ne kuma wannan masu yakin mujahidai ne ko a'a sai su sanya manufa na yaki da sharuddan sa a gaban su sais u duba su ganin shin sunyi daidai da wannan yaki ko a'a!! ya wajaba mu sani cewa akwai dayawa na abubuwan siyasa wacce take mulkin duniyan nan da kuma alaka tsakanin kasashen wandasunyi hannun riga da sunan jihadi yakuna ne kawai da akeyi domin maslaha, kamar misali:

  1. Yakin kirim[76] a shekara ta 1853 tsakanin Imbiradhuriyya na rusiya da daular usmaniya, birtaniya da faransa sun shiga cikin yaki suna yakar rusiya domin taimakon kawar su daular usmaniya, wannan ta mahamgan siyasa ne tabbas bawai dan addini bane, duka masu yakin na kasan rusiya da birtaniya da faransa kasa ce ta kiristanci a wannan lokacin kuma daular usmaniya daula ce musulma.
  2. A shekara ta 1854 yunan ta rura wutan yaki wacce take tarkashin mulkin usmani a wannan lokaci domin damar yakin kirim tsakanin rusiya da turkawa, sai suka fara zanga zanga na Ibirus[77] domin adawa da turkawa dan fitar dasu daga cikin yunan, ya kasance wanda ya hana wannan zanga zanga sune faransa da birtaniya, yadda suka yima shugaban yunani kawanya da kuma yana shigar masu da komai da kuma toshe masu yin wannan zangan zanga, har yunan ta koma karkashin mulkin usmaniya wacce ta musulunci ce.

 

YAKI ME TSARKI:

 

Shin jihadi a musulunci yaki ne me tsarki wanda ta hanyar sa za'a tilasta mutane barin addinin su da yin musulunci da kuma rushe cocin su da wuraren bautan su? Amsar itace a'a domin samun nassi a bayyane cikin alkur'ani me girma wanda yake hana tilastawa mutane akan barin addinin su da yin musulunci dole, Allah madaukaki yana cewa:

“babu tilastawa a addini hakika shiriya ta bayya daga bata” (suratul bakara ayata 256)

Jihadi domin isar da addinin Allah ga mutane bawai tilasta masu yin addinin ba, saboda fadin Allah madaukaki:

“idan sunyi imani to hakika sun shiryu idan kuma sun juya baya to naka kadai shine isarwa; kuma Allah me ganin bayin sa ne” (suratu al'imran ayata 20)

Dalili kuwa na rashin tilastawa akan shiriya zuwa ga addinin gaskiya da kuma sanin sa kyauta ce na Allah wanda Allah ya kebanta dashi ga wanda yaso cikin bayinsa hakab baya zuwa ta hanyar wajabtawa mutum ko kuwa tilastashi, saboda fadi Allah madaukaki:

“shiriyan su baya kanka sai dai Allah yana shiryar da wanda yaso” (suratul bakara ayata 272)

Baya halatta tilastawa wand aba musulmi ba cikin yahudawa ko kirista shiga musulunci idan kuma hakan ya faru to ba daidai bane, domin daga cikin sharadin shiga musulunci shine ya kasance da zabin mutum ne da kuma son sa bawai da tilastawa da yimai dole. Mutum zai iya cewa to me yasa muke ganin abubuwan masu tayar da hankali na labari akan ta'addanci akan coci a wata kasar da ake yaki, sai muce: labarin zai iya zama gaskiya ko kuma karya, da ace zamu dauka cewa gaskiya ne to masallatai nawa ne aka rusa da yin ta'addanci akan sa a cikin wannan kasa shima?!! Da za'ace akwai kiristoci da aka kashe sai muce musulmai nawa aka kashe suma anan?!! A lokacin da muke magana akan wata kasa wacce take yaki abunda yake a al'adance shine mu rika magana akan misalin irin wannan abubuwa wanda basu da alaka da musulunci da karantarwan sa, baza'a kira wannan ba da jihadi, dalili kuwa shine dayawa mutane sunyi kaura ko kuma ankashe su kuma wuraren bauta dayawa an rusa su wanda dukkanin wannan abubuwa jihadi yana yaki dasu kuma baya yarda dasu.

 

BANBANCI TSAKANIN YAKI DA JIHADI:

 

Zamu gane banbanci ne tsakanin yaki da jihadi a lokacin da muka kawo wasu daga cikin yakuna wanda akayi su a tarihi daga cikin su akwai:-

  • ISKANDAR BABBA: Iskandar babba yana samun girmamawa daga wurin mutanen sa da kasashen duniya baki dayan su a matsayin mutum me tasira a duniya, musamman yakuna masu yawa da akayi domin kara yawan fadin mulkin sa wanda har yakai ga iyakan Imbiradhuriyya na al igrikiyya zuwa indiya.
  • JINKIZ KHAN: ya kafa babban Imbiradhuriyya a duniya wacce bayan mutuwar sa takai har zuwa ga sin da gabashin turai kamar kasar porland da makamantan su, kuma yana da mabiya dayawa a kasashe daban daban sannan kuma mutane suna matukar girmama shi a duniya.
  • HITLA: ya darkake turai har saida ya hade iyakan Imbiradhuriyyar sa da kasashe da yawa ana turawa.
  • IMBIRADHURIYYA NA BIRTANIYA (Imbiradhuriyya wacce ta karade ko ina): mulkin mallakarta ya karede ko ina a duniya tun daga gabas zuwa yamma shi yasa ake mata kirani da Imbiradhuriyyar da rana yaba bace mata.
  • MUSU MULKIN MALLAKA NA FARANSA DA SPAIN DA PORTUGAL DA ITALY DA JAPAN: ya karade duniya gabas zuwa yamma domin fadada shugabancin ta da ikonta.

A takaicen magana: tarayya dukkanin wannan imbiradhuriyya da dukkanin yakunan wacce tayi wanda burinta shine mamayewa arziki da kasashen duniya na daban da kuma fadada karfin fadanta aji da sshugabanci a duniya, kuma tan atarayya har wayau cikin kasancewar sakamakon shine lallata wayewa, da yankawa da bautar da mutane wacce tabar miliyoyi da tabon haka, wannan shine abunda tarihi ya tabbatar mana, Jinkiz khan wanda yana cikin jaruman da ake irgawa a kasarsa ana kalloan sa da jikan sa Hulako cikin garin da ya daidaita a matsayin me laifin yaki, ya daidaita mutane da yada barna a doron kasa da lallatata, hakika Hulako ya lallata gidan hikma da abunda ke cikinta na littattafai da rubuce rubuce na ilimi wanda ba'a iya kimantawa. Akan haka kuma domin sanin banbanci tsakanin yaki da jihadi ya wajaba mu auna tsakanin manufafi na wannan yakuna da sakamakon su da dabi'un su da kuma manufofi na jihadi da sakamon ka sa dabi'un sa! Jihadi wanda ya tsayar da wannan zalumcin ya kuma kiyaye masu addinai musulmai da wand aba musulmai ba.

 

JIHADI CIKIN LITTAFI ME TSARKI:

 

Gabanin mu kawo wasu daga cikin nassoshi akan jihadi a cikin tsohon alkawari zamu kawo cikin sabon alkawari shima na maganganun Bulu wanda ya wanzar da jihadin da aka ambata cikin tsohon alkawari, kuma da yawa sun yaba akan dukkanin abunda ya aikata cikin wannan yakuna na kashe masu addini na Azli!!

BULUS YANA CEWA CIKIN SAKON SA ZUWA GA IBRANIYAWA (11/30): (30 da imani ne Aswar Ariha ya fadi bayan ya zauna cikin ta na tsawon kwanaki bakwai 31 da imani akayi maraba da zaniyawa ba'a taba hakaba tare da masu laigfi idan aka amshi amsu liken sirri da aminci 32 me kuma nake cewa har wayau domin lokaci bazai isheni ba dana bada labari akan Jada'un da Barak da shamsun da Yaftahu da Dawud da Samuel da annabawa 33 wanda suka samu galaba akan sarakuna da imani sun aikata biyya sun kuma samu alkawura sun rufe bakuna na zaki 34 sun kashe karfin wuta sun tsira daga kaifi takobi sunyi karfi daga rauni sun zama masu tsanani a yaki sun rusha rundunoni na baki)!!

Yanzu zamugani cikin tsohon alkawari abunda ya faru bayan Aswar Ariha ya fadi wanda aka ambata kuma dayawa ke yabon sa cikin sakon Bulus wanda ya gabata!!

 

SAFAR YUSHA'U (6/16): (16 ya kasanci a karo na bakwai a lokacin da bokaye suka duki kofuka lallai yusha'u yace ma mutane kuyi ihu domin kuma ubangiji ya baku birni. 17 birnin zai kasance da dukkanin abunda ke cikin ga harami ne ga ubangiji. Yayi maraba da zaniyata ne kawai don gaisuwa ita da dukkanin abunda ke cikinta a cikin gida domin ya boye manzannin da aka aiko su. 18 amma ku ku fitar da haramun domin a haramta kuma ku amshi haramun da sanyata a wurin bani isra'il haramun da lalatata. 19 dukkanin zinari da azurfa da kwano na copper da karfe zai kasance me tsarki ga ubangiji kuma zai shiga cikin ma'jiya na ubangiji. 20 sai mutane sukayi ihu suka duki kofuka kuma ya kasance a lokacin da mutane sukaji sautin Buka cewa mutane sunyi ihu ihu me kara sai bango ya fadi daga wurin sa sai mutane suka shiga cikin birni ko wani mutum tare da fuskar sa suka amshi wannan birni. 21 suka haramta dukkanin abunda ke cikinta na namiji da mace yaro da tsoho hatta shanaye da awakai da jakuna da da bakin takobi……24 suka kuma kona birnin da wuta da dukkanin abunda ke cikinta)

Basu tsaya ba kawai akan kisan duk wani abu me rai na maza da mata da yara hatta dabbobi a'a sai da suka kona birnin baki dayan sa da wuta!!!!!!!

 

SAFAR SAMUEL NA FARKO (15/3): (3 to yanzu ka tafi ka duki sarakuna kuma ka haramta dukkanin abunda suke dashi, kuma kada ka yafe masu, ka kashe namiji da mace, yaro da jariri, shanu da akuwa, rakumi da jaki)

SAFAR HUSHA'U AL ISHAH (13/16): (16 an yima samurata sakamako domin ya sabama allanta, da takobi suka fadi. Suna kashe yaran su da raba masu cikin su).

SAFAR ISHA'A AL ISHAH (13/15): (15 duk wanda ya sumu yana soke shi kuma duk wanda ya samu yana fadar dashi da takobi. 16 yan akuma kashe yaran su agaban idon su, da kona gidan =je da wulakanta matan su).

SAFAR SAMUEL NA BIYU (4/12): (12 sai dawud ya umurci gilmana sai suka kashe su da yanke hannuwan su da kafafun su da kuma sagaleta akan taguwa na Hibrun)

SAFAR N AKABARUN KWANAKI NA FARKO (20/3): (3 sai dawud ya fitar da mutanen da ke cikinta ya yankasu da zarto da gatari da adda haka dawud ya aikata ga dukkanin mutanen dani Umun)

 

 

BABI NA BAKWAI

WUCE GONA DA IRI DA TSANANI TSAKANIN SHARI'AR MUSULUNCI DA DOKOKIN DA MUTANE SUKA KIRKIRA.

 

  • Yaki da wuce gona da iri da kuma tsanani a cikin shari'ar musulunci.
  • Ruhbaniyyanci a cikin kiristanci:
  1. Gauranci yafi aure falala:
  2. Rashin yin saki:
  3. Yanke kawuna:
  • Yakin tsarin bautar da mutane a musulunci.
  • Tsarin bauta a cikin littafi me tsarki na yahudawa da kiristoci.
  • Yaki da kabilanci a cikin musulunci:
  • Halasta jin dadin duniya da kuma kwadaitarwa akan rayata a cikin musulunci.

 

 

 

BABI NA BAKWAI

WUCE GONA DA IRI DA TSANANI TSAKANIN SHARI'AR MUSULUNCI DA DOKOKIN DA MUTANE SUKA KIRKIRA.

YAKI DA WUCE GONA DA IRI DA KUMA TSANANI A CIKIN SHARI'AR MUSULUNCI:

 

Allah madaukaki ya aiko Muhammad manzon Allah s.a.w kuma ya saukar masa da shari'a wacce take rahama ga talikai, sai yace:

“kuma bamu aikeka ba face rahama ga talikai” (suratul anbiya'i ayata 107)

Rahama a agresu cikin dukkanin al'amuran su, rahama ga kawunan su da rayukan su wacce ta yanta su daga bautan gumakan da basa amfanar dasu kuma basa cjutar dasu suna bautama bayi irin su sai Allah ya shiryar dasu zuwa ga bautan sa shi kadai da kuma rashin yi masa shirka.

Rahama ga jikin su yadda ya haramta masu abinci da abunsha wanda zayyi sababin halakar dasu, Allah madaukaki yace:

“Kace bani samu, acikin abinda akayo wahayi zuwa gareni, abin haramtawa, akan wani maici wanda yake cin sa face idan ya kasance mushe, ko kuwa jini abin zubarwa, ko kuwa naman alade, to lallai ne shi kazanta ne, ko kuwa fasikanci wanda aka kururuta domin wanin Allah, dashi. Sa’annan wanda lalura ta kama shi, ba mai fita jama’a ba kuma ba mai ta’addi ba, to lallai Ubangijinka Mai gafara ne , mai jin kai.” (suratul an'am ayata 145)

Kuma rahama ne ga tattalin arzikin su yadda aka haramta masu dukiyan da aka amsa bada hakki ba ko kuma aka tara da algushi da kuma cin dukiyan mutane da barna, Allah madaukaki yana cewa:

“kuma kada kuci dukiyanku a tsakanin ku da barna kuna kaiwa zuwa ga mahukunta domin kuci dukiyan mutane da barna alhali suna sane” (suratul bakara ayata 188)

Ya kuma shar'anta masu tsara abubuwan al'amuran sun a rayuwa sazu gudanu da kuma ginuwa akai kuma yayi daidai da fidira ta mutane wanda babu wuce gona da iri a cikinsa ko kuma sakaci, Allah madaukaki yace:

“ya shar'anta maku cikin addini bunda yayi ma Nuhu wasiyya dashi da abunda mukayi maka wahayi dashi da abunda mukayi wasiyya dashi ga Ibrahim da Musa da Isa; cewa ku tsayar da addini kuma kada ku rarraba a cikin sa; abunda kake kiran mushrikai akai yayi masu girma; Allah yana zaban wanda yaso zuwa gareshi ya kuma shiryar da wanda ya jawo zuwa gare shi” (suratul shura ayata 13)

Allah ya aiko shi da shari'a ta rahama, Allah madaukaki yace:

“saboda rahamar Allah ne ka zama mai tausayi akansu, da ace ka kasance mai tsanani kuma mai fishi da sun tashi daga gefenka, ka zama mai yafiya garesu kuma ka roka musu gafara sannan ka nemi shawararsu, idan ka yunkura don aikata wani abu saika dogara ga Allah, lallai Allah yana son masu tawakkali.” (suratu al'imran ayata 159)

Ya aiko shi da shari'a me sauki da tausayi, Allah madaukaki yana cewa yana me gori ga mutum da aiko shi zuwa garesu:

“Lallai ne, hakika , manzon daga cikinku yaje muku. Abunda kuka wahala dashi me nauyi ne akansa. Mai kwadayi ne saboda ku. Ga muminai mai tausayi ne, mai jin kai.” (suratul taubah ayata 128)

Ya kasanci cikin siffifin wannan shari'a iatce sauki da rangwame babu tsanani a cikinta da kunci, Allah madaukaki yace:

“Allah baya daura ma rai face abunda da zata iya, tana da ladan abunda ta aikata kuma tana da zunubin abunda ta aikata” (suratul bakara ayata 286)

Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa:

“idan na haneku akan wani abu to ku nuisance shi, kuma idan ya umurce ku da wani abu to ku aikata shi gwargwadon iyawan ku” (sahihul buhari)

Aisha matarsa uwar muminai Allah ya kara mata yarda tana cewa:

“ba'a tab aba manzon Allah s.a.w zabi ba akan abu biyu, daya yafi sauki akan dayan, face ya zabi wanda yafi sauki a cikin su matukan be kasance zunubi ba. idan kuma ua kasance zunubi to yafi kowa nisanta daga gareshi” (sahihu muslim)

Allah y aiko shi da shari'a wacce ta yaki dukkanin dangin wuce gona da iri da tsanani cikin nassoshi na shari'a wanda suke a bayyane wanda suka tsawatar akan sakaci da rashin aikata abunda akayi umurni dashi cikin addini kamar yadda wanda suka gabace mu suka aikata, Allah madaukaki yace:

“kace yaku ma'abota littafi kada ku wuce gona da iri cikin addinin ku wand aba gaskiya ba kuma kada kubi son zuciyoyin mutanen da hakika sun bata tuntuni kuma sun batar da mutane dayawa kuma sun bace akan hanyar madai daiciya” (suratul ma'ida ayata 77)

  • Yayi hani akan tsanani da wuce gona da iri cikin addini, manzon Allah s.a.w ya tsawatar akan sa tsawatar wa me tsanani yace: “kashedinku da wuce gona da iri cikin addini, domin kuwa abunda ya halaka wanda suke gabace ku shine wuce gona da iri cikin addini” (Ahmad da Nasa'i da Ibn Majjah ne suka rawaito shi cikin silsilatul sahiha: 2144)
  • Kuma yayi hani game da tsanani da wuce gona da iri cikin ibadu, hakika Anas dan Malik Allah ya kara masa yarda ya rawaito daga gareshi cewa: “wasu mutane uku sun zo gidan matan manzon Allah s.a.w suna tambayan su game da ibadar manzon Allah s.a.w, baya sun fada masu sai suka ce: mu muna ina cikin wannan aiki na manzon Allah s.a.w? wanda an gafarta mashi abunda ya gabata na zunuban sa da abunda zai zo, sai dayan su yace: ni dai daga yau kullam sallah zantayi da daddare har Abadan, sai dayan kuma yace: ni kuma daga yau kullum azumi zantayi bazan hut aba, sai dayan yace: ni zan nisanci mata bazanyi aure ba har Abadan, sai manzon Allah s.a.w yazo yace: “kune kuka ce kaza da kaza ko? Lallai ni wallahi nafiku tsoron Allah da kiyaye shi, amma ni ina azumi kuma ina hutawa, ina kuma sallah ina barci, ina kuma auran mata, dan haka duk wanda ya kyamaci sunnata to baya tare dani.” (Sahihul buhari)
  • Kuma yayi hani game da tsanani da wuce gona da iri cikin mu'amala, hakika manzon Allah s.a.w yace: “lallai addini me sauki ne, kuma babu wanda zai tsananta wannan addini face ya rinjaye shi” (sahihul buhari)
  • Kuma yayi hani game da tsanani da wuce gona da iri cikin kira zuwa ga Allah, manzon Allah s.a.w yace: “kuyi bishara kada ku kore mutane kuma ku saukaka kada ku tsananta” (sahihu muslim)

 

RAHBANIYANCI CIKIN ADDININ KIRISTANCI:

 

Babu ruhbaniyanci cikin musulunci ko kuma malamin coci kamar yadda yake cikin sauran addinai, kuma hakika Allah ya zargi wannan aiki na mutanen addinan da suka gabata, Allah madaukaki yace:

“Sa’annan muka biyar a bayan su da manzanni mu; kuma muka biyar da Isa dan Maryam, kuma muka bashi Injila kuma muka sanya tausayi da rahama a cikin zukatan wadanda suka bishi, da ruhbananci wanda suka kaga shi bamu rubuta shi ba a kansu, face dai (mun rubuta musu) neman yardan Allah, sa’annan basu tsare shi hakikanin tsarewarsa ba, saboda haka baiwa wadanda sukayi imani daga cikin su sakamakonsu, kuma masu yawa daga cikin su fasikai ne” (suratul hadid ayata 27)

Kuma manzo Allah ya tsawatar akan haka tsawatarwa ne tsanani yace:

“kada ku tsanantawa kanku sai Allah ya tsananta muku domin kuwa wasu mutane sun tsanantawa kansu sai Allah ya tsananta masu ga kufai can na wuraren ibadun su da gidajen su (rahbaniyyan ci ne wanda suka kirkireta Allah be wajabta masu ba)(silsilatul sahiha: 3124)

Mu sani cewa Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi be kasance baruhbane ba kuma be shar'anta ma mutanen sa ruhbaniyanci ba, ya umurci Taliban sa ne da su tafi su isar da addinin Allah ga mutane da shiryar dasu zuwa ga addini na ingantacce.

Akwaai nauyi babba akan malamin addinin musulunci dole ne yayi cudanya da mutane yana umurtan su da kyaukyawan aiki da kuma hanasu mummunan aiki ya kuma nuna masu hanya ingantacciya, saboda fadin manzon Allah s.a.w:

“ku isar game dani koda da aya daya ce.” (Sahihul Bukhari)

Sannan kuma ya zama dan kasa nagari abun misali da koyi ga al'ummar sa. manzon Allah s.a.w yace:

 “mumini wanda yake cudanya da mutane da kuma yin hakuri abisa cutarwan su, yafi alheri akan muminin da baya cudanya da mutane kuma baya hakuri akan cutarwan su” (buhari ne ya rawaito shi cikin adabul mufrid kuma Albani ya inganta shi cikin sahihul jami'u)

Kuma kada ya zaman masu nauyi yana neman taimakon sun a abunda zaici annabawa sun kasance amincin Allah ya tabbata agaresu suna aiki da hannun su kuma suna kewon dabbobi domin neman abinci dashi da kame kawunan su da kula da iyalan su, hakika ancema manzon Allah s.a.w shin kayi kewon dabbobi? Sai yace:

“eh, akwai wani annabin da beyi kewon dabbobi bane” (sahihul buhari)

 

GAURANTAKA YAFI FALALA AKAN AURE:

 

Bulus yana cewa cikin sakon farko zuwa ga Kurinsus (7/1): (1 amma ta bangaren al'amura wanda kuka rubuto mun su: abinda yafi shine mutum kada ya taba mace…. 8 sai dai ina cewa ga marasa aure da zaurawa, lallai yafi kyau agare sui dan sun zauna kamar yadda nake) – watan gauro-.

Kuma lallai wannan shine karantarwan bulus da kansa bawai karantarwan shugabammu Isa almasihi bane amnincin Allah ya tabbata agareshi, domin ta sabawa fidira wacce Allah ya halicci mutane akanta hasalima aure sunna ce ta annabawa amincin Allah ya tabbata agaresu Allah madaukaki yace:

“kuma hakika mun aika da manzanni gabanin ka kuma mun sanya masu mataye da zuriya; kuma be kasance ga wani manzo ba daya zo da wata aya face da izinin Allah; ko wani aiki da Allah ya hukunta yana da lokaci sananne” (suratul ra'ad ayata 38)

Shin al'ummar yanxu sun taba nazari akan wannan magana da rashin yin aure da kuma hayaiyafa wanda sakamakon sa shine zai karar da jinsin mutum? Shin Allah yana son mu kare ne ko kuma yanason mu da mu raya kasa na da hayaiyafa? Wannan duka sabanin umurnin Allah ne madaukaki wanda yace:

“kuma shine wanda yasanya ku khalifofi abayan kasa ya kuma daukaka darajan wasu akan wasu a cikin ku domin ya jarabaku cikin abunda ya baku; lallai ubangijin ku me saurin ukuba ne kuma lallai shi me gafara ne me jin kai” (suratul an'am ayata 165)

Duk a lokacin da muke neman mutane da zama gaurantaka da rashin yin aure to fa muna cin karu ne da sha'awar da take tare dasu, sha'awa ce cikin mutum kamar sha'awar cin abinci da shan ruwa, sai dai shari'a ta sanya mashi hanyar biyan sa a shari'ance ta hanyar aure yadda soyayya da tausayi da natsuwar zuciyar ga ma'aurata zai samu da kuma raya kasa, Allah madaukaki yace:

“kuma daga cikin ayoyin shi ya halitta maku mataye daga jikin ku domin ku samu natsuwa zuwa gare su ya kuma sanya soyayya da rahama atsakanin ku; lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani” (suratul rum ayata 21)

Manzon Allah s.a.w ya kasance yanayin umurni dayin aure da kuma kwataidar wa dashi da kuma yin hani akan gaurantaka hani me tsanani yana cewa:

“ku aure mata masu haihuwa wanda kuke son su domin zanyi alfari daku ranan alkiyama” (sahihu Ibn Hibban, kuma albani ya ingantashi cikin “sahihu Abu Dawud”: 1789)

Ya kuma kwadaitar da samari musamman akan yin aure domin yawan sha'awa da suke da ita da kuma toshe hanyar alfasha, sai yace:

“yaku tarin samari! Duk wanda ya samu dama a cikin ku to yayi aure domin shi yafi rufe gani, da kiyaye farji, wanda kuma bai samu ba sai ya rika yin azumi, domin hakan kariya ce a gareshi” (buhari da muslim ne suka rawaito shi)

Kuma abunda yafi wananan shine ya sanya aure ya zama hanya ya neman kwayawan ayyuka da sadaka, sai yace:

“kuma acikin sduwar dayan ku akwai sadaka”, sai sukace ya manzon Allah! Yanzu wanin mu zai biya sha'awar sa kuma ya samu lada? Sai yace: “yaya kuke gani da ace yaje ya sanyata cikin haramun zai samu zunubi? To haka abun yake idan ya sanyata cikin halal zai samu lada da hakan” (sahihu Muslim)

 

RASHIN YIN SAKI:

 

INJILA NA MATA (5/31): (31 kuma ance: duk wanda ya saki matar sa to ya bata littafin saki. 32 amma kuma ni ina cewa maku: lallai duk wanda ya saki matar sa sai dai idan saboda zina ne zai sanyata yin zina, duk kuma wanda y auri wacce aka saka to yana zina)

Shin al'ummar wannan zamani wayayya sun yarda da rashin halascin yin sadi ko kuma dai mafi yawan kaso na saki ana samun sa dayawa cikin kasashen da sukaci gaba?!! Shin kiristoci sunci iyabin wannan karantarwan ko kuma sun dauke a matsayin wuce gona da iri ne da tsanantawa?! Abunda yake a bayyane na aiki yana cewa akwai akwai dayawa na auratayya wanda bazai yiwuba suci gaba da zama domin kuwa cikin ci gaba da zaman akwai cucarwa wanda baza'a iya kawar da hakan ba sai da saki, kai mun karanta cikin jaridu yanayin kisan mace ga mijinta kirista a matsayin hanya na rabuwa dashi da rayuwa dashi domin rashin ikon da take dashi na rabuwa dashi!! Amma shi musulunci hakika ya halasta saki domin saukakewa akan mutane a halin rashin iya ci gaban rayuwan aure, sai kowa ya rabu da abokin zaman sa ta hanya ta wayewa kuma ko wanne a cikin su ya auri abunda ya yarda shi na abokin zama agareshi, Allah madaukaki yace:

“ku rikeso da kyautatawa ko kuma ku rabu dasu da kyautatawa” (suratul dalak ayata 2)

Kuma hakika dukkanin kasashen da suka waye ayanzu sunbi shari'ar musulunci akan wannan al'amari kuma sun halasta da dokanta saki kuma sun mayar dashi ya kuma saki a hukumance wanda ya nesanta daga ikon coci wacce take kin aure baki dayan sa.

 

YANKA KAI:

 

Lallai yanke kan makiya da kuma gunduwa gunduwa da gawan wanda aka kashe abu ne wanda musulunci ya hana ya kuma tsawatar akan aikata shi, a lokacin da Amru dan Aas, da Shuraihu dan Hasanata dan Ukubata suka aika da sako zuwa ga Abubakar na kan Unaka ta hanyar sham, a lokacin da ya isa zuwa ga Abubakar sai yayi inkarin haka, sai Ukubata yace masa: ya khalifan manzon Allah muma fa haka suke mana; sai yace: koyi da farisa da rumawa, kada akawo mun kai. Kawai rubutu da sako ya magana ya ishe ni. (Ibn Hajar al askalani ne ya rawaito shi)

Lallai wasu masu gabatar da shiri a cikin kafafen yada labarai na yamma a wannan zamani namu suna jingina wa musulmai al'adar yanke kai, sai dai da masu gabatar da wannan shiri na shashanci zasu koma su karanta tarihi da sun ga sabanin haka shine ingantacce, kawuna nawa aka yanke a cikin garuruwan su hatta cikin shekura nan baya baya kadan da suka wuce. A misali ana samu a jikin bango na coci zanen Milano daga waje na Faris yana rike da kan wani mutum wanda ya yanke a dayan hannun nashi kuma ya rike wuka doguwa, shin mun munga irin wannan ajikin bangon masallatan musulmai?!! Amma abunda ake gani daga wasu musulmai suna yanka wasu mutane a fili da kuma yanke kawunan su wannan ayyuka ne na dai daikon mutane bashi da alaka da shari'a musulunci kuma ya barranta daga shi,

Babban burin wannan aikata wannan aiki shine domin samun wata manufa marakyau na siyasa da kuma bata sunan musulunci da korarn mutane daga gareshi. Wannan mutane ana samun su a matsayin yan ba ruwan mu domin yin fim da na'urar daukan hoton su me tsada kwararriya, suyi fim misali akan yadda aka kashe wanda babu ruwan su babu wani abunda sukayi kuma basu yake su ba. Irin wannan mutane barna suke yadawa a doron kasa da kuma rashin son zaman lafiya. Allah madaukaki yace:

" kuma idan suka juya baya sai su yadu cikin kasa domin yin barna a cikinta kuma su halaka gona da zuriya; kuma bayason barna." (suratul bakara ayata 205)

Wani zai iya cewa: ' to wannan tutar fa wanda wannan mutane ke dagawa wanda ya kunshi rubutu na musulunci a jikin sa, shin wannan baya karfafa da shedar cewa su musulmai ne?. zamu ba da amsa agaresu da cewa: idan mutum yana da mota karama me arha sai ya kawo alama na motar marcedi na makala mata, shin hakan zai sa motar sa ta koma marcedi?' hakika amsar itace A'a. ya kamata ka kwatanta aikin su da kuma karantarwan musulunci zakaga cewa sunyi hannun riga a tsakanin su.

Allah madaukaki yana cewa:

“kuma idan zakuyi ramuwa to ku rama da kwatnkwacin abunda daka maku, kuma da zakuyi hakuri shi yafi alheri ga masu hakuri” (suratun nahali ayata 126)

 

YAKI DA TSARIN BAUTAN MUTANE A MUSULUNCI:

 

Musulunci ya yaki tsarin bautan mutane ta ko wani hanya yayi umurni da yanta bawa ya kuma shar'anta yanta su da kuma yin alkawari na lada me yawa ga wanda ya yanta bawansa, ya kuma sanya shi cikin dalilai na shiga aljanna, manzon Allah s.a.w yana cewa:

“duk wanda ya yanta wani bawa Allah zai yanta daga wuta da ko wace daga cikin gabban sa hatta farjin sa” (muslim ne ya rawaito shi)

Sai dai musulunci be haramta tsarin bauta ba saboda kada yaci karo babba da abunda ke faruwa a duniya ya kasance tsari ne na duniya wanda kasashe ke aiki dashi baki dayan su yasancewar sa tsari ne na tattalin arziki da kudi wanda ake dogaru dashi cikin dukkanin al'umma, kuma a kan wannan hanya shugaban mu Isa almasihu be haramta tsarin bauta ba. sai dai musulunci ya hamate dukkanin hanyuka wanda zai kai ga bautar da mutum sai ta hanya daya kacal wacce itace hanyar fursinonin yaki da sharadin shugabanin musulmai ya zartar da zamr dasu bayi, kasancewar musulunci ta takaita hanyoyi na bayi sai hanya daya kawai, sai ya sanya a maimakon sa hanyoyi nay anta bayi ya sanya kaffara dayawa daga zunubai wanda musulmi ke aikatawa kamar misalin:

  • KISA A BISA KUSKURE, saboda fadin Allah madaukaki: “duk wanda ya kashe mumini da kuskure to ya yanta bawa mumini da kuma diyya da zai bayar ga iyalan sa sai dai idan sun yafe; idan kuma ya kasance daga cikin mutane ne makiyanku amma mumini to sai a yanta bawa mumini; idan kuma ya kasance cikin mutanen da akwai alkawari tsakanin ku dasu to a biya diyya zuwa ga iyalan sa da kuma yanta bawa mumini” (suratun nisa'i ayata 92)
  • KAFFARAR RANTSUWA, saboda fadin Allah madaukaki: “Allah baya kamaku abisa subutan baki na rantsuwan ku sai dai yana kamaku ne a bisa rantsuwar da kukayi shi da tabbaci; kuma kaffarar sa shine ciyar da miskinai goma na tsaka tsakanin abincin da kuke ciyar da iyalan ku ko kuma tufatar dasu ko kuma yanta bawa” (suratul ma'ida ayata 89)
  • ZIHARI, saboda fadin Allah madaukaki: “wanda suke zihari akan matansu sa'annan su janye daga abunda suka fadi to su yanta bawa gabanin su kusance su” (suratul mujadala ayata 3)
  • YIN JIMA'I A TSAKIYAN RANA DA WATAN RAMADAN, an karbo daga Abi huraira Allah ya kara masa yarda cewa wani mutum ya fadama matar sa cikin Ramadan sai ya tambayi manzon Allah fatawa akan haka, sai yace: “shin kanada bawa?”sai yace: a'a, sai yace: “shin zaka iya azumin wata biyu ajere: “sai yace: a'a, sai yace: “to ka ciyar da miskinai sittin.” (Muslim ne ya rawaito shi)
  • YA SANYA SHI KAFFARAN TA'ADI AKAN WANI BAWA, saboda fadin manzon Allah s.a.w: “duk wanda ya zalumci bawan sa ko kuma ya duke shi to kaffaran sa shine yay anta shi” (muslim ne ya rawaito shi)

Kuma daga cikin abunda zai tabbatar da kwadayin musulunci akan yanta bayi:

  1. Yayi umurni da rubuta yarjejeniya, shine kulla yarjejeniya tsakanin bawa da ubangidan sa wanda zai yanta shi akan wani kudi wanda sukayi ittifaki akai atsakanin su, kuma hakika wasu maluman fiqihun[78] Allah yayi masu rahama sun wajabta cewa idan bawa ya nemi ubangidan sa rubuta yarjejeniya suna masu kafa hujja da wannan fadin Allah madaukaki cewa: “wanda suke son rubuta yarjejenya cikin abunda kuka mallaka na bayi to ku rubuta masu idan kunsan alheri a tare dasu; kuma ku basu cikin dukiyar Allah daya baku” (suratun nur ayata 33)
  2. Ya sanya yanta bayi cikin abubuwan da ake basu kudin zakka, shine yanta bawa daga bauta, saboda fadin Allah madaukaki: “lallai zakka ana bayar da itace ga fukara'u da miskinai da masu aikin tattarata, da wanda ake lallashin zuciyar su, da bayi masu fansar kansu, da wanda ya raba fada ya daukan ma kansa biyan kudin, da majahidai fi sabilillah, da matafiyi; wajibi ne daga Allah; kuma Allah masani ne me hikima” (suratul tauba ayata 60)

 

TSARIN BAUTA CIKIN LITTAFI ME TSARKI NA YAHUDAWA DA KIRISTOCI:

 

YAZO CIKIN SAFAR NA TASNIYA (20/10): (10 a lokacin da ya kusanto birni domin yakanta ka kirata zuwa ga yin sulhu, 11 idan sun amsa yin sulhu suka bude maka, to dukkan mutanen da suke nan zasu zama karkashin ikon ka dayi maka bauta. Idan basuyi sulhu dakai sukayi yaki dakai, to kayi masu kawanya. 13 idan ubangiji allanka ya baka birnin a hannun ka to ka kashe dukkan mazajen su da takobi. 14 su kuma matan da yara da dabbobi da dukkan abunda ke cikin birnin ganima agareka, kaci ganimar makiyan ka wanda ubangijinka allanka ya baka. 15 haka zaka aikata da dukkanin birane masu nisa da kai wanda basa cikin biranen wannan mutanen na nan. 16 amma biranen wannan mutane wanda ubangijin ka allanka ya baka rabonka kada ka rika wani mutum daga ciki, ka haramta su haramtawa).

YAZO CIKIN SAFAR ALKHURUJ (21/7): (7 idan mutum ya siyar da yarinyar sa kamar baiwa, ba'a sakin me yanci kamar yadda bawa yake sakin mutane masu yanci bayan shekara shida na bauta. 8 acikin yanayin cewa shugabanta be burgeta ba wanda ya siye ta kamar abokiya agareshi, ya wajaba yaba mahaifinta damar fansar ta da kudi ya amshe ta daga gareshi).

YAZO CIKIN SAFAR ALKHURUJ (21/5): (5 amma idan bawa yace: inason shugabana da matata da yarana, bazan fita daga me yanci ba, 6 shugabanshi zai gabatar dashi ga allah, ya kuma kusantar dashi zuwa ga kofa ko itace sai ya bugi kunnuna sa da abun duka yayi masa hidima na har Abadan). – wa'ana bauta ta har Abadan-.

YAZO CIKIN SAFAR ALKHURUJ (22/1-3): (ya wajaba akan barawo da ya biya me wanann abunda ya sata, idan kuma bashi da kudi wanda zai isa biya wannan mutumi, to anan za'a siyar da wannan barawo kamar bawa, yabada kudin ga wannan mutumi dayama sata. Yanzu mu karanta abunda injila ya jingina zuwa ga shugabammu almasihu amincin Allah ya tabbata a gareshi.)

 

YAKI DA KABILANCI

A MUSULUNCI:

 

Musulunci yayi hurgi da dukkanin abunda yake jawo banbanci tsakanin mutane na shari'a wanda yake furta kabilanci ko kuma aiki dashi ko banbancin launin gfata tsakanin mutane ya kuma sanya banbanci tsakanin su yana ginuwa ne akan tsantsan kusanta da kuma nisantar aiwatar da shari'un Allah, Allah madaukaki yace:

“yaku mutane lallai mun halicce ku daga namiji da mace kuma mukasanya ku kuka zama mutane da kabilu domin ku samu sanayyi; lallai wanda yafi wani acikin ku shine wanda yafi tsoron Allah; lallai Allah masanin ne me bada labari” (suratul hujurat ayata 13)

Kuma manzon Allah s.a.w yace:

“yaku mutane! Lallai ubangijin ku daya ne, kuma babanku daya ne, ku saurara kuji babu falala ga balarabe akan wand aba balarabe ba ko kuma wanda ba balarabe ba akan balarabe, ko kuma fari akan baki, ko baki akan fari sai da tsoron Allah, lallai mafificin ku a gun Allah shine wanda yafi tsoron sa, ku saurara kuji shin na isar? Sai suka ce: eh ka isar ya manzon Allah sai yace: to wanda yaji ya isar zuwa ga wanda bayanan” (silsilatul sahiha)

 

A LOKACIN DA MUKA SAMU CIKIN LITTAFI ME TSARKI NA YAHUDAWA DA KIRISTOCI ABU MASU ZUWA:

YAZO CIKIN INJILA NA MATA (15/24): (24 sai ya amsa: << ba'a aiko nib a face zuwa ga Kirafa batattu, zuwa ga gidan isra'ila, 25 sai dai mace ta kusa gare shi, kuma tayi mashi sujjada, ta kuma ce: ta taimake ni ya shugabana! 26 sai ya amsa: ba daidai bane a dauki biredin yara maza a jefama karnuka! 27 sai tace: <28 sai yusha'u ya masa: << yake mace, imanin ki yana da girma! Ya kasance maki abunda kike nema!>> sai aka warkar da yaron ta a wannan lokaci).

A cikin wannan nassin akwai raddi a bayyane me karfi kuma ga duk wanda yake ikirarin cewa almasihu yazo ne domin tsarkake duniya da gicciyewa da kuma fansa da makamantan haka, yana cewa maka a fili cewa ba'a aiko ni ba zuwa gare ka kuma bansanka ba!! sai dai an aiko ni ne zuwa ga bani isra'ila su kadai!!

YAZO CIKIN SAFAR NA TASNIYA (23/19): (19 kada ya wajabtama dan uwanka da riba, riban azurfa, ko kuma riban abinci ko riban wani abu cikin abunda da ake riba dasu 20 ga wand aba bani isra'ila bane zaka wajabtawa riba, amma ga kada ka wajabta ga dan uwanka, domin ubangiji allahnka yayi albarka agareka).

 

HALASTA JIN DADIN DUNIYA CIKIN SHARI'AR MUSULUNCI:

SANYA TUFAFI DA TSABTA:

 

Shri'ar musulunc yana umurni ga musulmi daya zama me kyau cikin dukkanin yanajin sun a tufafi da ganin sa da kamshin sa da maganar sa, saboda fadin manzon Allah s.a.w:

“lallai Allah me kyau ne yana son masu kyau” (sahihu muslim)

Kuma Jabir dan Abdullah yace:

(manzon Allah s.a.w yazo mana sai yaga wani mutum buzu buzu gashinsa yayi bakyaun gani sai yace: “shin wannan be samu abunda zai gyara gashin sa bane.” Ya kuma ga wani mutumi shima sanye da tufafi me datti sai yace: “shin wannan bai samu ruwan da zai wanke tufafin shi bane”) (sunan abu dawud kuma albani ya ingantashi)

Kuma abu Ahwas ya rawaito daga babansa yace:

(nazo gun manzon Allah s.a.w cikin riga mara kima[79], sai yace: kana da kudi? Sai nace: eh, sai yace: wani irin kudi?[80] Sai yace: hakika Allah ya bani rakuma da dabbobi da doki da bawa, sai yace: idan Allah ya baka kudi to aga alamun ni'imar Allah da falalar sa a tattare da kai) (Abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi)

Kuma Jabir dan samurata yace:

(naga manzon Allah s.a.w cikin daren salla[81], yana sanye da riga ja, sai na rika kallon sa da wata, wallahi yafi watan nan kyau) (tirmizi ne ya rawaito shi- ingantacce ne)

Kuma Barra'u dan Azib yace:

(manzon Allah s.a.w ya kasance mutum ne matsakaici me fadin kafada[82], me yawan gashi[83] har zuwa kunnen sa, yana da tufafi ja[84] bantaba ganin wani abuba a rayuwa me wanda yafi shi kyau) (sahihu muslim)

Kuma Abu Zamil ya rawaito cewa Abdullahi dan Abbas yace:

(a lokacin da kharijawa suka bayyana sai nazo gun Aliyu allah ya kara masa yarda sai yace: ka zo da wannan mutane. Sai ya sanya tufafi me kyau wanda yafi huliyyi na yaman kyau sai Abu zamil yace: Ibn Abbas ya kasance mutum ne me kyau gani – sai dan Abbas yace: sai nazo wurin su sukace mun marhaba da zuwanka ya dan Abbas, wannan rigan fa?! Sai yace: kada ku aibanta mun riga hakika naga manzon Allah s.a.w ya sanya riga wacce tafi irinta kyau) (Abu dawud ne ya rawaito shi kuma shu'aibual arnud yace: isnadin shi me karfi ne)

Kuma shari'a ta dauka kashe dukkanin abunda zai cika rai mutum musulmi cikin dukkanin yanayi ba tare da barna ba da almubazaran ci da girman kai cikin abubuwan da ake bashi lada akai, saboda fadin Allah madaukaki:

“yaku yan Adam ku riki kawarku a ,okacin zuwa ko wani salla kuma kuci kusha kada kuyi barna; lallai shi bayason masu barna” (suratul a'araba ayata 31)

Shiga irin ta musulunci:

Kuma babu wani tufafi cikin shari'ar musulunci da ake kira da suna tufafin musulunci, kamar abunda wasu sufaye da yan shi'a suke sanyawa me launi daban kamar launin kore ko baki ko makamantan su, sai dai akwai siffofi na tufafin shari'ar musulunci, wanda ya wajaba musulmi ko kuma musulma su takaita akansu, daga cikinsu akwai:

  • Ya kasance cikin wannan tufafi babu koyi da wand aba musulmi ba kamar mutum yasa tufafin da buzawa ke sanyawa ko kiristoci ko yahudawa kawai kamar tufafin fadoji da fastoci a misali, saboda fadin manzon Allah s.a.w: “duk wanda yayi koyi da wasu mutane to shima yana daga cikin su” (Ibn Hibban ne ya rawaito shi -kuma ingantacc ne)
  • Ya rufe masa al'auran sa wanda shari'a ya hana bayyanar dashi, kada ya bayyana saboda gajartan sa ko kuma shara-sharansa.
  • Ya kasance tufafi ne me tsabta da kyaun gani, hakika manzon Allah s.a.w yaga wani mutum sanye da tufafi me datti sai yace: “shin wannan bashi da ruwan da zai wanke wannan tufafin ne nashi” (sunan abu dawud, silsilatul sahiha: 493)
  • Ya kasance tufafi me kamshi wanda baya koran mutane daga kusantan me shi, manzon Allah s.a.w ya hana cin tafarnuwa ko albasa a lokacin zuwa masallaci domin cucarwan dake cikin sa wanda zai samu na gefen sa dashi, saboda fadin sa manzon Allah s.a.w: “duk wanda yaci albasa ko tafarnuwa (wani wurin kuma yace duk wanda yaci albasa da tafarnuwa da lawashi kada ya kusanci masallacin mu. Domin mala'iku suna cutuwa daga abunda yake cucar da dan adam” (sahihu muslim)
  • Kada ya zama tufafin na alfahari ne ya kasance bako ne cikin al'umman da yake rayuwa a ciki, idan ya sanya shi mutane zasuyi mamaki domin kyaun sa sai ya karama me shi girman kai da dagawa, ko kuma ya kasance tufafi ne wand abe dace da yayin shi ba a al'adance da kuma kore masa mutuncin sa, sabod afadin manzon Allah s.a.w: “duk wanda ya sanya tufafin alfahari a duniya to Allah zai sanya masa tufafin kaskanci ranar alkiyama” (Ahmad nay a rawaito shi, kuma albani ya inganta shi cikin sahihu abu dawud)
  • ya zama babu koyi da maza a cikin sa ga mata, ko kuma koyi da mata ga maza “manzon Allah s.a.w ya tsinema namijin daya sanya tufafin mace ko kuma macen da ta sanya tufafin namiji” (sahihu Ibn Hibban)

Akwai kuma hadisai masu nuni akan muhimmancin musulmi ya rika kula da shigan sa duk wanda yakeson Karin bayani akan haka sai ya koma zuwa ga littattafan tufafi a musulunci, zamu takaita cikin abunda muka ambata a baya cewa shari'ar musulunci ya himmatu matuka da tsaftar musulmi da kuma kyawun ganin sa baya halatta ga musulmi ya kori mutane daga wurin sa domin munin shigan sa da kuma rashin tsabta.

A nan wurin akwai gaba me muhimanci wanda zai iya kawo shubuha game da shari'ar musulunci ga wanda ba musulmai ba a dalilin tufafi musamman a wasu kasashen yamma wanda muke ganin wasu daga cikin musulmai baki ko kuma wasu musulmai sababbin musulunta a wasu kasashe suna sanya tufafi wanda wanda yaganshi zaiyi makakin cewa anya wannan musulmi ne kuwa, kamar ya sanya (mayafi irin wanda muatanen misra suke sakawa musulman su da kristan su wanda beya sanin cewa shi musulmi ne kawai abunda ya sani shine shi mutumin misra ne) ko kuma ya sanya tufafi sabo ko kuma kayan sojoji kuma shi ba soja bane ko kuma ya kewaye kansa da wani bandeji ba ta hanyar da aka saba gani ba, wanda ya kamata ya sanya irin tufafin da mutane suka sani ne wanda bazai sanya mutane su guje shi ba ko kuma samun shakka akansa ba, hakika manzon Allah s.a.w ya kasance yafi kyauwun mutane a wurin shiga kuma wanda yafi su kamshi kuma duk wanda ya ganshi yanajin natsuwa da kwanciyan hankali.

Sai dai ya wajaba nu banbance tsakanin kayan da akasan wasu mutanen ne ke sanyawa da kuma kayan da wasu bangare ne ke sanyawa ko kuwa wasu bangare na mazhaba domin addini kamar misali abunda sufaye da shi'a keyi, amma kayan makaranta ko jami'u da kungiyoyi na kasa da kasa data cikin gida kaya domin a gane su wanda bawai an ginashi bane akan wani turba na mazhaba ko bangaranci a'a kawai domin a rika gane wannan ma'aikatan ne dashi ko kuma dalibai.

 

CI DA SHA:

 

Allah madaukaki yace:

“kace masu wanene ya haramta ado na Allah wanda ya fitar da ita domin bayin sa da dadadan abubuwa na arziki; kace anyi su ne domin wanda sukayi imani cikin rayuwan duniya kuma nasu ne su kadai a ranan alkiyama; Kaman haka ne muke bayyana ayoyi ga mutane masu sani” (suratul a'araf ayata 32)

Shari'ar musulunci ta halasta jin dadi da more dukkanin dayan ci da sha, sai abunda da dalili ya nassanta akan haramcin sa, Allah madaukaki yace:

“an haramta maku mushe da jini da naman alade da abunda aka yanka domin wanin Allah da kuma wanda aka shaketa ta mutu da wanda aka duka ko harba da dutse ta mutu da wacce ta fado daga tsauni ta mutu da wacce yar uwarta ta tunkura da kaho ta mutu da wanda dabban farauta ya kashe sai wanda kuka yanka da abunda aka yanka akan gunki (shima an haramta) kuma kada kuyi rabo da kibau na caca; wannan fasikanci ne.” (suratul ma'ida ayata 3)

Allah madaukaki yana cewa:

“suna tambayan ka game da giya da caca; kace suna da zunubi me girma da dan amfani ga mutane; kuma zunubin su yafi amfanin su girma; kuma suna tambayan ka me zasu ciyar kace masu abunda ya samu ya sawwaka ya ragu; kaman haka ne Allah yake bayyana maku ayoyin sa koda zakuyi tunani” (suratul bakara ayata 219)

Ya kuma sharada rashin yin barna, Allah madaukaki yace:

“kuma kuci kusha kada kuyi barna; lallai shi bayason mabarnata” (suratul a'araf ayata 31)

Ya kuma bayyana hanya ingantacciya na ci da sha wanda suka kunshi lafiya da izinin Allah ga jiki daga cutuka, manzon Allah s.a.w yana cewa:

“mutum be taba cika tunbi na sharri ba kamar ciki, ya ishi dan adam yaci wasu yan loma na abinci wanda zai karfafa kashin bayan sa dashi, idan ya kasance babu makawa to: ya raba daya biya uku na cikin sa yaci abinci, daya bisa uku na ruwa, daya bisa uku kuma nayin nunfashi” (Tirmizi ne ya rawaito shi – kuma ingantacce ne – cikin “al irawa'I”: 1983)

 

WASAN DAYA HALATTA:

Rayuwa a shari'ar musulunci bawai kamar yadda wasu ke tsammanin ta bane cewa babu wasa acikin ta wanda yake halal, Hanzalata yana cewa:

Abubakar ya hadu dani sai yace: ya kake ya Hanzalata? Sai nace: hanzalata yayi munafunci! Sai yace: subhanallah! Me kake cewa:? Sai nace: idan muna gun manzon Allah s.a.w yana tunatar damu akan wuta da aljanna sai kaga kamar muna ganin su da idanun mu, amma idan muka bar wurin manzon Allah s.a.w sai mu shagalta da matan mu da yara sai mu manta dayawa!. Sai Abubakar yace: wallahi nima ina fama da irin wannan abu. Sai suka tafi zuwa ga manzon allah s.a.w muka shiga wurin shi sai nace: Hanzalata yayi munafunci ya manzon Allah! Sai manzon Allah s.a.w yace: “me yayi haka”sai nace: ya manzon Allah! Idan muna wurin ka kana tunatar damu akan wuta da akjanna sai kaga kamar muna ganin su da idanun mu, amma da zaran mun bar wurin ka sai mu shagalta da matan mu da yara da kayan wasa sai mu manta dayawa! Sai manzon Allah s.a.w yace: “ina rantsuwa da wanda raina ke hannun sa! da zaku dawwama akan halin da kuke a wurina a ciki da kuma zikiri da mala'iku sun gaisa daku akan gadajen ku da hanyoyin ku, sai dai ya Hanzalat! Lokaci bayan lokaci ya maimata haka har sau uku.”[85]

Sai manzon Allah s.aw ya bayyana cikin wannann hadisi cewa wasa halal ne da kuma hutar da kai anason yin shi domin mutum ya samu nishadi da lafiyanta, kuma ya bayyana wa sahabban sa ladubba na wasa da zaulaya a lokacin da suka tamabaye shi sukace: ya manzon Allah kana mana wasa! Sai yace: “eh inayi amma bana fadi sai face gaskiya[86]

Kamar yadda wasa yana kasancewa da magana haka kuma yake kasancewa da aiki, Anas dan Malik Allah ya kara masa yarda yace:

“Wani mutum cikin mutanen kauye me suna Zahir, ya kasance yana kawo ma manzon Allah kyauta na kayan kyauye, sai manzon Allah s.a.w ya shiryashi idan zai tafi. Sai manzon Allah s.a.w yace: “lallai Zahid shine dan kyauyen mu mukuma yan birnin sa, sai manzon Allah s.a.w yaje masa wata rana yana siyar da kayan sa sai ya kamashi daga bayan sa baya ganin sa, sai yace: wanene wannan? Sakeni! Sai ya juya yaga manzon Allah s.a.w sai yaci gaba da hada bayansa da kirjin manzon Allah. Sai manzon Allah s.a.w yace: “wazai siya wannan bawan?”sai Zahid yace: ya manzon Allah ai arha zanyi bazanyi kudi ba, sai manzon Allah s.a.w yace: “amma dai zakayi kudi agun Allah! Ko kuma yace: kai me tsada ne agun Allah[87].

 

Yana da ladubba acikin shari'ar musulunci daga cikin su akwai:

  • ya kasance babu cutarwa cikin wasan ga musulmi ko kuma muzguna masa aciki, saboda fadin manzon Allah s.a.w: “baya halatta ga musulmi ya tsorata musulmi”[88]
  • Kada wasan ya fita daga cikin abota, yayi karya domin ya sanya mutane daria, saboda fadin manzon Allah s.a.w: “bani ya tabbata ga wanda yake bada labari sai yayi karya domin yasa mutane dariya! Bani ya tabbata a gareshi bani ya tabbata a gareshi![89]

Kamar yadda shari'ar musulunci ta halasta wasa da sharadin ya kasance halal kamar jifan kibiya ko kwari da baka da tseren doki, manzon Allah s.a.w yace: “dukkanin wani wasan da musulmi zayyi bashi da kyau sai dai jifa mashi ko koyon tseren doki ko kuma wasan sa da matar shi” (Tirmzi ne ya rawaito shi kuma albani ya igantashi), kuma dukkanin abunda yake gida jika da kuma kare lafiya na nau'ukan motsa jiki kamar nunkaya da gasa da kokawa, manzon Allah s.a.w yayi kokawa da wani mutum wanda ake kira – Rakanata- sai manzon Allah s.a.w ya kayar dashi kuma ya kasance me karfi sai yace: a sanya akuya da akuya sai manzon Allah ya kayar dashi sai yace: mu sake sai ya kayar dashi har sau uku sai mutumin yace: me zance ma iyalai na? karkace ya cinye akuya daya dayan kuma ta fado to dayan kuma me zance masu, sai manzon Allah s.a.w yace: “bazamu hada maka shan kayi ba da kuma cin tara dauki akuyoyin ka”albani ne ya rawaito shi- kuma hasan ne.

 

 

BABAI NA TAKWAS

FAYYACE GASKIYA

MISALI NA SHARI'AR KIRISTANCI DA YAHUDANCI DAGA CIKIN LITTAFI ME TSARKI

 

  1. Ukubar yanke hannu cikin littafi me tsarki.
  2. Ukubar zina cikin littafi me tsarki.
  3. Ukubar kisa cikin littafi me tsarki
  4. Yancin yin addini cikin littafi me tsarki (yin ridda)
  5. Shari'ar kishi cikin littafi me tsarki (li'ani – yin rantuwa tsakanin ma'aurata domin barranta dga tuhumar yin zina)

 

 

 

BABAI NA TAKWAS

FAYYACE GASKIYA

MISALI NA SHARI'AR KIRISTANCI DA YAHUDANCI DAGA CIKIN LITTAFI ME TSARKI

 

Mafiya yawan kasashen turawa suna tashi ta hanyar sanarwan su domin bata suna ga addinin musulunci ta hanyar tallata haddoji wanda ake zartarwa a musulunci da cewa hakan be dace da ci gaban zamani ba wanda duniya ke ciki yanzu da makamantan haka na manufar su na kare mutane game da wannan addini na Allah wanda da mutane zasu kalleshi ba tare da kabilanci ba ko kuma hukuncin da akayi mashi abaya ba da sunsan cewa lallai addini ne na gaskiya wanda ya wajaba abishi sai dai tsoro sautin gaskiya ya isa ga mutane dukda cewa sai fay a isan ko mutum yaki ko yaso domin tabbatar da alkawarin Allah da yake cewa: “suna son kashe hasken Allah da bakunan su sai dai Allah yaki hakan sai ya cika hasken sa koda kuwa kafirai sunki hakan” (suratul taubah ayata 32)

Zartar da haddoji cikin musulunci zartar da shari'ar Allah ne bawai daga wurin musulmai bane kuma mun gani cikin babukan da suka wuce cewa rahama ce ga mutum da al'umma baki daya kuma zamu gani cikin shafuka na littafi me tsarki na tsohon alkawari da sabon zartar da haddoji abunda suke aibantawa a wurin musulmai hasalima yafi tsanani ma, sai dai kafafen yada labaran turawa wanda suke makirci da kuma aiki da gabban su wurin ganin sun batama shari'ar musulunci suna wanda hakan baya karamai komai face yaduwa kasancewar sa sauti ne na gaskiya wanda baza'a iya kashe shi ba, kuma Allah yayi gaskiya: “kuma shine wanda ya aiko da manzon sa da shiriya da addinin gaskiya domin ya rinjayar dashi akan dukkanin addinai koda kuwa mushrikai sunki hakan”suratul taubah ayata 33.

SHIN TSOHON ALKAWARI LITTAFI NE ME TSARKI NA KIRISTOCI DA YAHUDAWA?!

Gabanin mu kutsa cikin koro wani hukunce hukunce (haddoji) daga shari'ar kiristoci da yahudawa, munason sanin idan tsohon alkawari littafi ne me tsarki a gun kiristoci da yahudawa ko a'a", karkashin tattaunawa ta da wasu daga cikin kiristoc na samu suna bayya cewa littafi me tsarki tsoho da sabon alkawarin duk Kalmar Allah ne na asali sauran kuma an cancanza wanda zabai bace ba ko kuma canzuwa, bayan karanta mashi wasu nassoshi daga cikin tsohon alkawari sai yayi gaggawan dawowa da janyewa yana cewa zaka iya tambayan malamin addini akan wannan nassoshi ni ba bayahude bane, kai al'amarin yakan kaisu cikin wasu lokuta na barranta daga tsohon alkawari baki daya yana cewa dukkan wannan ya kasance ne gabanin zuwan almasihu amma bayan yazo sai komai ya canza, kuma tabbas tafsirin sa ba'a sallama masa a hankalce ko ta fuskan rawaitowa. Dukkanin kirista bazai iya zama kirista ba sai dai idan yayi imani da littafi me tsarki tsoho da sabon alkawari baki daya, wannan abu a bayyane yake agun dukkan kirista, akan haka idan wani kirista beyi imani ba da tsohon alkawari ba dayin imani kawai da sabon alkawari to ya zama arne da addinin kiristanci! Duk wanda yake son tabbatarwa akan haka zai iya tambayan malamun su yaji dakan sa abunda zasu ce mashi!

Hakika an ambata cikin injila na mata (5/17) cewa Isa yace: “kada kuyi tsamanin cewa nazo ne domin na toye Namus ko kuma kuma annabawa. Banzo domin toyewa ba sai don cikawa. Lallai gaskiya ce nake fada maku: har zuwa karshen duniya babu wani harafi da zai gushe ko kuma wata kalma daya cikin Namus har yazama duka. Duk wanda ya toye daya daga cikin wasiyyoyi kanana kuma mutane suka sani a hakan, za'a kirashi makaskanci cikin sama.”

Zamu kawo wasu daga cikin nassoshin haddoji wanda suka zo cikin littafi me tsarki:-

 

UKUBAR YANKE HANNU CIKIN LITTAFI ME TSARKI:

 

Safar altasniya (25/11): (11 idan mutum biyu sukayi fada da juna, da mutum da dan uwan sa, sai matar daya daga ckin su tazo kwatan mijinta a hannun wanda ya duke shi, sai hannun ta ya zarce ya kama al'auran shi, 12 ku yanke hannun ta, kuma kada idonka yaji tausayi).

 

UKUBAR ZINA CIKIN LITTAFI ME TSARKI:

 

SAFAR AL LAWIYYIN (21/9): (9 idan wata diya tayi datti na aikata zina to hakika ya bata mahaifinta da datti. Da wuta za'a konata!!!!!!!!).

SAFAR AL TASNIYA (22/20): (20 sai dai idan wannan al'amari ya kasance ingantacce kuma ba'a samu kazanta ba ga budurwa, 21 za'a fitar da budurwa zuwa ga kofar mahaifinta mazajen birnin su jefe ta da duwatsu har sai ta mutu domin ta aikata mummunan abu cikin bani isra'ila da zinan da tayi cikin gidan mahaifinta sai a cije sharri daga tsakiyan ka).

SAFAR AL TASNIYA (22/22): (22 idan aka samu wani akan matan wani za'a kashe duka su biyun mutumin da matan).

SAFAR AL TASNIYA (22/23): (23 idan mace ta kasance budurwa wani ya nemi auren ta sai mutum ya same ta a cikin birni ya kwanta da ita, 24 to ku fito dasu zuwa ga kofar wannan birni sai ku jefe su da duwatsu har sai sun mutu).

AN AMBATA CIKIN INJILA NA MATA (5/27) CEWA ISA YACE: (27 hakika kunji cewa ancema tsofaffi: kada kayi zina. Amma ni inace maku: lallai duk wanda ya kalli matar wani domin sha'awa, hakika yayi zina da ita cikin zuciyar sa. idan ya kasance idonka na dama ya sanyaka hakan to ka cire shi ka huragar dashi domin hakan yafi maka alheri da wani gabbanka ya halaka kuma kar ya jefa jikin ka duka a cikin jahannama. Idan ya kasance hannun ka ne na dama yayi aikin to ka yanke shi ka hurgar dashi, hakan yafi zama maka alheri daya halaka daya daga cikin gabban ka ya kuma jefaka cikin jahannama.)

SAFAR AL LAWIYYIN (20/10): (10 idan wani yayi zina da mace, idan yayi zina da mace yar uwa, to za'a kashe shi da ita. 11 idan mutum ya kwanta da matar babanshi, hakika ya bayyana al'auran bababnshi. Za'a kashe su. Jinin su yana kansu. 12 idan mutum ya kwanta da yar uwar sa, za'a kashe su, hakika sun aikata alfasha. Kuma jinin su yana kansu. 13 idan mutum ya kwanta dana miji kwanciya irin na mace, hakika sun aikata datti. Za'a kashe su. Kuma jinin su yana kansu. 14 kuma idan mutum ya hada yarinya da mamanta wannan sabo ne. da wuta za'a kona shi dasu, domin kada sabo ya kasance a tsakanin ku. 15 idan kuma mutum ya kwanta da dabba, za'a kashe shi da dabbar….).

Haka dai al Ishah yaci gaba da Ambato ukubar mutuwa ga macen da ta kwanta da dabba ko kuma namiji wand ayaga al'auran yar uwansa tare da wata mata ko kuma yaga al'aurar kanwar mahaifiyar sa ko kanwar mahaifi ko ya kwanta da matan kawun sa ko bdan uwansa!! Mutum zai iya cewa ashe almasihu be share wannan ukubar ba na zina wacce take jifa har sai an mutu ya mayar da ita laifi wacce bata a ukuba? Shin baya fad aba cikin injila na yuhana (8/7): (7 duk wanda yakasance a cikin ku bashi da budurwa to ya jefata da dutse) sai muyi bada amsa agareshi da cewa: hakika maluman Lahuta cikin kiristoci sunyi ittifakin cewa wanann labari bata inganta ba an karata ne cikin injila a cikin karni na goma na miladiyya[90], akan haka ne baya halatta dogaro akai.

Ka kara akan haka da maganganun shugaban mu almasihu da kansa waccce take kore sabawa Namus ko kuma shari'ar Musa, injila na mata (5/17): (17 kada kuyi tsammanin nazo ne domin toye Namus ko kuma annabawa, banzo ba domin toyewa ba sai dan cikawa. 18 lallai ina fada maku gaskiya: har zuwa karshen duniya babu wani harafi daya da zai gushe ko kuma kalma daya cikin Namus har ya zama duka).

Watan ta wani ma'anar da taban da ace shugaban mu almasihu yana tare damu ayau daya jefe duk matan da tayi zina kamar yadda shari'ar Musa ya fada.

 

UKUBAR KISA CIKIN LITTAFI ME TSARKI:

 

BULUS YANA CEWA CIKIN SAKON SA ZUWA GA IBRANIYAWA (28/10): “duk wanda ya sabama Namus na Musa to a gaban shedu biyu ko uku zai mutu babu taisayi..”

SAFAR AL KHURUJ (21/12): (12 wanda ya duki mutum ya mutu za’a kashe shi….14 idan mutum ya zalumci dan uwan sa domin ya kashe shi da yaudara to a wurin mayanka na za’a kashe shi. 15 wanda ya duki babanshi ko mahaifiyarshi za’a kashe shi. 16 wanda ya saci mutum ya siyar dashi ko kuma aka same shi a hannun shi za’a kashe shi. 17 wanda ya zagi babanshi ko maman shi za’a kashe shi.. 22 idan mutum yayi fada ya bige mace me ciki sai yaron cikinta ya fado amma bata samu wata cutarwa ba, za’aci shi tara zai biya ta hannun alkali 23 idan kuma ta cutu za'a bata rai da rai, 24 ido da ido, hakori da hakori, hannu da hannu, kafa da kafa, 25 kuna da kuna, kwankwa tsawa da kwankwa tsawa).

SAFAR AL KHURUJ (21/18): (18 kada kabar boka ta rayu. 19 duk wanda ya kwanda da dabba akashe shi. 20 wanda yayi yanka ga wani ba ubangiji bas hi kadai zai halaka).

SAFAR AL TAKWIN (9/6): (6 wanda ya zubar da jinin mutum da mutum za'a zubar da jinin shi).

SAFAR AL ADAD: (35/31): (31 kada ku amshi fansa na kudi akan mutumin da yayi kisa me zunubin mutuwa, za'a kashe shi ne… 33 kada ku lalata kasar da kuke cikinta, domin jini yana lallata kasa, kuma akan kasa ba'a kankare zunubi domin jinin da aka zubar a cikinta sai da jinin wanda ya zubar dashi).

SAFAR ALKHURUJ (32/26): (26 musa ya tsaya a kofar wurin sa, sai yace: “duk wani na Allah yazo nan”sai suka hadu awurin sa baki daya yaran Lawi. 27 sai yace masu: “haka ubangiji allan bani isra'ila yace: kowa yasa wukan sa akan cinyan sa kuje ku dawo daga kofa zuwa kofa a muhalla, kowa ya kashe dan uwan sa kowa ya kashe abokin sa kowa ya kashe dan na kusa dashi.” 28 sai yaran Lawi suka aikata yadda musa ya umurce su. Aka kashe kusan mutum dubu uku a wannan rana).

SAFAR AL TASNIYA (21/18): (18 idan mutum yana da yaro marajin magana takadari bayajin maganar mahaifin shi da mahaifiyar sa, kuma suna ladabta shi amma baya ji. 19 mahaifin shi zai rike shi da mahaifiyar shi sai su zo dashi zuwa ga shugaban birnin su zuwa ga kofar wurin sa, 20 sai su ce mashi: wannan yaro namu takadari marajin maganan mu, kuma shi me barna ne da maye. 21 sai mutanen ganin dukan su sujefe shi da dutse har sai yam utu).

 

YANCIN YIN AQIDA CIKIN LITTAFI ME TSARKI (YIN RIDDA)

 

INJILA NA LUKA (19/27) ana jinginawa ga shugaba almasihu cewa yace: (27 amma makiyana wannan sune wanda basa so na mallake su ku zo dasu zuwa nan ku yanka su a gabana").

SAFAR AL TASNIYA (13/12): (12 idan kaji labari a cikin daya daga garuruwan ka wanda ubangijin ka allanka ya baka domin ka zauna a cikinta, 13 wasu mutanen yaran Lu'aim sun fita daga tsakiyar ka suka kara mutanen garin su suna ce masu: muje mu bautawa wani allan wanda basu sanshi ba. 14 ka bincika ka tabbar da yin tambaya dakyau idan al'amarin gaskiya ya tabbata, wani mjutum ya aikata haka a tsakiyar ka, 15 ku kashe mutanen wannan birni da takobi. 16 ka tara dukkan kayan ta a tsakiyan filinta, ka kona su da wutan garin kuma dukkan kayan ta baki dayan sun a ubangiji ne allanka, zai ka kasance kwafai ba'a ginata ba bayan ka).

SAFAR AL TASNIYA (7/1): (1 duk lokacin da ubangijin ka allanka yazo dakai cikin kasar da kake ciki domin ka mallaketa, aka kori mutane dayawa a gabanka…. 2 ubangijin allanka ya koro su gabanka, ka duke su, lallai kana haramta su. Kada ya yanka masu alkawari, kuma kada ka tausaya masu. 3 kuma kada ka aure su… sai dai haka zaka aikata dasu: da rusa mayankan su ka sassare wuraren bautan su, ya yayyanka rigunan yakin su, ka kona gumakan su da wuta).

SAFAR EZIKEL (9/4): (4 sai ubangiji yace mashi: “ka tekara tsakiyan birni, Ka sanya zane akan fuskan mutanen masu nadama da hucewa.” 5 sai wannan suka fadi acikin kunne na: “ku tsallaka cikin birni a bayan sa ku duka. Kada ku tausaya kuma kada kuyi yafiya. 6 tsoho da matashi mara lafiya da mace da yaro, ku kashe su domin halaka. Kuma kada ku kusanci mutumin da akwai zane akan sa, ka fara daga makdisi”sai suka fara da maza tsofafi wanda suke bakin gida. 7 sai yace masu: “sun lallata gidan da datti, sun cika wuraren bautan da gawa. Ku fito”sai suka fito cikin birnin). 

 

SHARI'AR KISHI CIKIN LITTAFI ME TSARKI (LI'ANI)

 

SAFAR AL ADAD (5/11): (11 sai ubangiji yace ma Musa: “kayima bani isra'ila wasiyya kace masu: idan matar mutum tayi sabo ta ha'ince shi 13 dayin zina da wani mutum na daban, kuma al'amarin ya buya ga mijinta, kuma babu wani dalili akan su kuma ba'a kama su ba suna yin zinan 14 idan mujinta yayi kishi ya dawo daga rakiyan matar sa kuma ta kasance najasa, ko kuma yayi kishi akan matar shi duk da cewa me tsarki ce 15 to mutumin yazo yakai matan zuwa ga boka, kuma yazo da garin masara na yawan ifata goma (kamar lita biyu da rabi). Kada ya zuba mashi mai, kuma kada ya zuba mashi madara, saboda gabatarwa ne na kishi, gabatarwa na tunatarwa yana tunatar da zunubi. 16 sai bokan ya sanya matar ta tsuguna agaban ubangiji, 17 sai ya amshi ruwa me tsarki a cikin kwarya na tire sai ya tsinci wasu tsakuwa na kasar gidan ya sanya cikin ruwan 18 ya bude kan matan, ya sanya a hannun ta gabatarwa na tunatarwa wanda shine gabatarwa na kishi, sai boka ya dauki ruwan la'ana da hannun sa me daci 19 yasa matan ta rantse da cewa: idan wani mutum daban be kwanta dake ba, kuma baki ha'inci mijinki ba, to ki barranta daga ruwan la'anta me daci wannan 20 amma idan kin ha'inci mijin ki kika kwanta da wani mutum wanda bashi ba 21 ubangiji ya sanya tsinuwar mutanen ki akanki, zai barranta daga gareki a lokacin da ubangiji ya sanya cinyan ki rube kuma cikinki ya kunbura. 22 kuwa wannan ruwa na la'ana ya shiga cikin hanjin ki domin yasa cikinki ya kunbura, da cinyarki ya rube.” Sai matan tace: Amin. Amin 23 sa'annan wannan boka ya rubuta wannan tsinuwa ajikin bango ya share shi da ruwa me daci; 24 ya shayar da matan wannan ruwan tsinuwa me daci sai ruwan rantsuwa ya shigeta domin ya sanya mata radadi. 25 sa'annan boka ya rike hannun matan ta gabatar da kishi, ya rinjayar da ita agaban ubangiji, sa'annan ya kaita zuwa wurin yanka. 26 kuma ya dibo gwargwadon kamdan hannun sa dayayi mata ya kona shi akan mayanka, bayan haka sai y aba matan ruwan tasha. 27 idan matar tayi zunubi ta ha'inci mijinta, to alokacin da take shan ruwna tana jawo tsinuwa ya sanya mata radadi sai ya kunbura mata ciki ya kuma rubar mata da cinya, sai matar ta zama tsinanniya a tsakiyan mutanen ta. 28 amma idan ta kasance barrantacciya me tsarki zata barranta tayi ciki).

 

 

KARSHEN LITTAFI

 

A karshe inason fadi cewa dukkanin abunda muka Ambato cikin littafi me tsarki, domin manufan warware kulli da dimuwan wannan wanda suke zargin musulunci da shari'ar musulunci da abubuwa masu yaw aba tare da wani fuskan gaskiya ba kuma ba tare da dubi ba a farko ciki abunda littafi su me tsarki ya fadi. Lallai shari'ar musulunci ita kadai ce a fadin duniya cikin shari'u wacce take yaki da dukkanin abunda yake kawo kabilanci da banbanci a tsakanin mutane da cin dunkiyoyin su da satan su da daidaita su da ta'adi akan mutuncin su da abunda suka mallaka.

A lokacin da muka karanta cikin littafi me tsarki cikin safar al TASNIYA (23/19): (19 kada ka wajabta ma dan uwanka riba, riban azurfa, ko kuma riban abinci, ko kuma riban duk abunda ake sa masa riba 20 kawia ga bako ne zaka wajabtama riba, amma dan uwanka kada ka wajabta masa riba, domin ubangijin ka allanka yayi maka albarka).

A CIKIN SAFAR ALKHURUJ (3/22): (22 ko wace mata ta nemi daga makwabciyar ta da kuma bakuwar gidan ta kayan azurfa da kayan zinari da tufafi kuma tasanya shi akan yaranku maza da mata. Sais u sanya misrawa).

A CIKIN SAFAR ZAKARIYYA (14/1): (1 wata ran ace ga ubangijin ka zaizo sai ya raba rabonka a tsakiyan ka. Kuma dukkanin mutane su hadu dominn yin yaki, sai ka amshi birnin, sai ka rusa gidaje,ka wukanta mata, ka fitar da rabin birni zuwa ga fursinonin yaki).

To ina kafafen yada labarai na turawa suke wanda suke tuhumar shari'ar musulunci dare da rana da karya, daga ina zasu warware abunda muka karanta yanzu ya take hakkokin mutane a fili!! Sai dai sanin su a ciki cewa addini ne na gaskiya da kuma makircin su akan sa shi yasanya su suke jifansa da wannnan sharri domin su kori mutane daga gareshi musamman ma bayan sunga karbuwar da yake samu yadda ake shiga musulunci. Sai dai kash sun zama kamar me sanya hannun sa a gaban rana domin yak are hasken sa a duniya, Allah madaukaki yace:

“a lokacin da littafi daga wurin Allah yazo masu me gasgatawa ga abunda yake a gaba gare su kuma sun kasance gabanin haka suna tambaya game da wanda suka kafurta; a lokacin da abunda suka sani yazo masu sai suka kafurta dashi; tsinuwar Allah ta tabbata akan kafirai (89) tir da abunda suka siya da kawunan su dasu kafurce da abunda Allah ya saukar saboda hassadan Allah ya saukar da falalar sa akan wanda yaso cikin bayin sa; sai suka dawo da fushi akan fushi; kuma kafirai sunada azaba ta wulakanci (90) idan akace masu kubi abunda Allah ya saukar masu sai suce munyi imani da abunda aka saukar mana kuma suna kafurta da duk abunda bashi ba kuma shi gaskiya ne me gasgatawa ga abunda ke tare dasu; kace to dan me yasa kuke kashe annabawan Allah a baya idan kun kasance muminai (91) kuma hakika Musa yazo maku da hujjoji sa'annan kuma kuka riki dan maraki a bayan sa kuma kuna azzalumai (92)” (Suratul bakara 89-92)

Ina fadi da yakini cewa babu abunda zai ceci al'ummar duniya cikin halin da suke cikin na dimuwar da ya same su cikin dukkanin bangarori na halaye da zamantakewa da tattalin arziki da siyasa saboda zalumcin dokoki na dan adam na jari hujja muguwa da da bangarenci na rashin addini da hadaka wacce take kaskantar da mutane me cin gumin su da kokarin su, da tsarin mulkin kama karya muguwa me kisa ga kirkiran mutum da abunda ytake gani na rayuwa na shugabancin rashin imani da banbanci na kabilanci saboda bangaranci da banbancin fata, haka kuma babu abunda zai tsiratar da rayukan mutane na tsoro da abunda ake gani na rayuwa na karewan rai da damuwa face da riko da musulunci da kuma rungumar sa da aiwatar da karantarwan sa, a lokacin aminci da adalci da tsaro da kwanciyar hankali na rahama zai samu cikin al'ummar mutane, kuma hankulan su zai kwanta da budewar zuciya wacce tayi kunci da tsoro da bakin ciki, Allah yayi gaskiya:

“da ace mutanen gari zasuyi imani da mun bude masu albarkoki daga sama da kasa sai dai sun karyata sai muka rike su da abunda suke aikatawa” (suratul a'araf ayata 96)

 Dayawa daga cikin masu falsafa turawa sun bayyana wanda suke tallar musulunci ya kasance me cecon mutane daga cikin dimuwar da suke na fasadi da fasikanci da kare hakkin dan adam, wani dan falsafa dan faransa (Deebckeeh) yana cewa:

“lallai turawa basusan musulunci ba har Abadan, tun daga lokacin da musulunci ya bayyana turawa suka riki adawa dashi, basu kame ba game da masa kage da muzantashi ba domin su samu daman yakar sa, hakika muzantashi da suke yi yayi tasiri wurin shiga kwakwalen turawa na kalamai zargin musulunci, babu babu shakka tabbas musulunci shine addinin da daya tilo wanda duniya ke bukata a yanzu domin fita daga cikin dimuwa da zamani wanda babu makawa ci gaba da zama acikinta zai daidaita mutum.”

Me falsafa bature (GeorgeBernaed Shaw) yana cewa cikin littafin sa me suna (Muhammad) wanda hukumar birtaniya suka konashi a wannan lokaci saboda abunda ya kunsa na bayyana ikirin sa ga sakon Muhammad s.a.w da kuma dacewar addinin sa:

“lallai duniya suna bukatar bukatar yin tunani game da Muhammad, wannan annabi wanda ya sanya addinin shi a koda yaushi a manzili na girmamawa da mutuntawa, lallai shine addini mafi karfi na shan kan masu addinai na har Abadan, kuma ni inaganin dayawa daga cikin mutane na wanda suka shige shi abisa basira, kuma da sannu wanna addini zai samu wuri me fadi cikin wannan yanki – watan turai – lallai maluman addini cikin karni na tsakiya, da kuma sakamakon jahilci ko kuma kabilanci zai iya zana addinin Muhammad a shura na zalumci hakika sun kasance suna kallon sa a matsayin me adawa da almasihu.”

Yana fadi a cikin wani wuri kuma na daban a cikin littafin dai:

“sai dai ni na duba wannan al'amarin wannan mutumi sai na same shi me matukan ban mamaki gagara badau, na kai ga cewa ba dan adawa bane da almasihu, ya wajaba a kirashi da suna me ceton dan adam, a ra'ayina da zai shugabanci al'amarin duniya da ya dace wurin waraware mushkilolin mu, saboda abunda mukayi imani dashi na aminci da murna wacce mutum ke bukatar ta.”

Wani malamin tarihi bature me suna Wales yana cewa:

“dukkan addinin wanda baya tafiya da birni cikin dukkanin ci gabanta kayi hurgi dashi, kuma lallai addainin gaskiya wand aka same shi yana tafiya da birni duk inda yake shine musulunci.. duk wanda yakeson dalili ya karanta alkur'ani da abunda ke cikinsa na dokoki da hangen nesan sa da manhaji na ilimi da tsari na zamantakewa, lallai littafi ne na addini da ilimi da zamantakewa da dabi'u da tarihi, kuma idan ka nemi na takaita maka ma'anar musulunci lallai zan takaita maka shine cikin wannan jumlar “musulunci shine addinin birni.”

Anan tambaya zai zo:

“me yasa basason musulunci kuma basason ku kusan shi ko kuma kusanshi cikin yadda suka batashi?”

Dalili: bazasu iya mamaye maku dukiyan ku ba a karkashin musulunci ta hanyar daura maku haraji da riba da sunan tattalin arziki na duniya wanda yake abude, kuma bazasu iya bautar da mutum ba ta hanyar wajabta maku dokoki nasu da suka kirkiro wanda baya kara wani abu face yi masu hidima da bauta, sai dai a karkashin shari'ar musulunci babu wanda ya isa ya amshi dukiyan ka kuma babu wanda zai iya ta'adi ga mutuncin ka kuma babu wanda zai iya bautar dakai, manzon Alah s.a.w yana cewa:

“lallai dukiyoyin da mutuncin ku da jinin ku haramun ne a gareku kamar haramcin wannan rana cikin wannan watan naku cikin wannan gari naku” (albani ya rawaito shi – kuma ingantacce ne)

A cikin wannan rayuwa namu ta yanzu a lokacin da ka bace hanya zaka samu wanda zai nuna maka hanyar da kake nema kamai godiya da mutunci, kenan ya kake gani akan wanda zai zuw aga hanyar da zai kai ka zuwa ga murna da ni'ima tsayayye cikin rayuwa har Abadan cikin aljanna ya kuma tsawatar dakai hanyar da zata kaika zuwa ga zabata tsayayye cikin rayuwa na har abdan cikin wuta shin bashi bane yafi cancanta da kamai godiya dayawa akan abunda yayi na tsamar da ranka da jikinka daga wuta maimakon ka rika masa yajayya kana tsoratar da mutane daga gareshi!!? Kaman haka ne manzon Allah Muhammad s.a.w wanda ba'a taba saninshi ba da karya da ha'inci gabanin musulunci da kuma bayan sa, ya kasance abun misali na cikakke na amana da kuma bayar da hakkoki zuwa ga masu ita, da gaskiya cikin labarin sa, ba'a taba ganin ha'inci ba ko karya agunsa ko sau daya, hakika ya shahara da amana tun yarintan sa har aka masa lakabi da amintacce, a lokacin da wasikar sa yakai ga Hirkal sarkin rumyana me kiran sa zuwa ga musulunci ya nemi wasu daga cikin mutanen sa yana tambayan su game dashi, sai aka zo da wasu mutane daga cikin su: Abu sufyan dan Harbi ya kasance cikin abunda ya tambaye shi: (shin kuna zargin sa da karya gabanin ya fadi abunda ya fadi?) sai yace: a'a, sai Hirkal yace: (bazai yiwu ba yabar yima mutane karya ya koma yana yima Allah karya!!) daga cikin amanar sa s.a.w a lokacin dayayi hijira zuwa madina a boye domin tsoron mutanen sa sai yabar dan babban saAliyu a makka domin ya mayar ma mutane da ajiyar su wanda yake wurin sa zuwa ga masu shi; saboda haka ne suka masa lakabi da me gaskiya amintacce, abunda ya wajaba afadi akansa shine irin abunda Hirkal sarkin rum ya fadi cewa bazayyiwu ba yabar yima mutane karya ya koma yana yima Allah karya!!.

Wanda yazo da shari'ar musulunci domin ta cece ka a duniya daga zaumcin da muguntan shuwagabanni da dokoki azzalumai ya kuma ceci ranka daga dimuwa da damuwa saboda abunda take gani na cin karo cikin addinai da shari'u wanda muke bautar da mutum da zama allansu kuma ya zama me ceton ka daga wuta bayan mutuwa, shari'ar musulunci itace gaskiya duk wanda yaga dama yayi imani wanda kuma yaga dama ya kafura, Allah madaukaki yana cewa:

“kace kuyima Allah biyayya kuma kuyima manzon sa biyayya; idan sun juya baya to lallai nauyin abunda aka daura masa yana kansa kuma nauyin abunda aka daura maku yana kanku, idan kunyi masa biyayya zaku shiryu; kuma babu komai akan manzon Allah face isarwa bayyananne” (suratun nur ayata 54)

 

 

WWW.ISLAMLAND.COM

 

 

 

[1] Sayyid Khudub Allah yayi mashi rahama cikin littafin sa me suna zilalul kur'an, mujalladi na 4, shafi na 2215

[2] William Montogmery Watt malamin tarihi ne na turawa, cikin littafin musulunci da kiristanci a wannan zamani namu, shafi na (33) (223-226)

[3] Edward Gibbon: cikin shinfidar wannan juzu'I na tarihi ' na kuma bayyana nasara na zamanin jahilci da addini'. Cikin littafin kafuwa da kuma faduwar masarautan Ruma' juzu'I na 3, ch. LXXI, shafi na 1068.

[4] Mein Kampf

[5] Jim Crow laws.

[6] Euthanasia da turanci.

[7] Groningen Protocol, 2004, Eduard Verhagen, Netherlands

[8] Nigel Cox.

[9] Louis XVI.

[10] Hanged, drawn and quarter, sir Thomas Armstrong.

[11] Disembowelment or evisceration, Balthasar Gerrard.

[12] Lynda Lyon Blok.

[13] Drownings at Nntes, Noyades de Nantes.

[14] Kisa ta hanyar rataya, Giles Corey.

[15] Richard Rice.

[16] Kisa ta hanyar yanka mutum da zarto.

[17] Dismemberment, Peru, Tupac Amaru II

[18] Slow slicing, Joseph Marchand.

[19] Bite the Curb, or Curb stomp.

[20] Yanka mutane.

[21] Aztec.

[22] Huitzilopochtli.

[23] Tlaloc.

[24] Huitzilopochtli.

[25] Xipe Totec

[26] Annual Customs of Dahomey

[27] Benin

[28] Mu

[29] Qin

[30] Slavs

[31] Perun

[32] Roman Law, Table IV. A dreadfully deformed child shall be quickly killed.

[33] Oxyrhynchus، Egypt، 1 B.C. (Oxyrhynchus papyrus 744. G).

[34] Sahihu fiqhus sunnah (4/8)

[35] Almuntaqa (7/135)

[36] Sahihu fiqhus sunnah (4/13)

[37] Sahihu fiqhus sunnah

[38] Duba cikin littafin mausu'atul fiqhul islami, na Muhammad dan Ibrahim dan Abdullahi At tuwaijiri.

[39]'stand your ground' law.

[40] Christopher Stephen Grayling، Lord Chancellor and Secretary of State for Justice. http://www.independent.co.uk/news/uk/politics/the-burglar-is-unarmed-you-have-a-knife-so-what-do-you-do-next-8203046.html  

[41] http://www.telegraph.co.uk/news/politics/conservative/9595589/David-Cameron-when-a-burglar-invades-your-home-they-give-up-their-rights.html

[42] Swinging، wife swapping، wife sharing، partner sharing، wife trading or wife lending.

[43] Swinging in America: Love، Sex، and Marriage in the 21st Century، By Curtis R. Bergstrand، Jennifer Blevins Sinski.

[44]  Matilda Joslyn Gage، ‘‘Women، Church and State’’، Chapter VII، Polygamy، page 404.

[45] Matilda Joslyn Gage، ‘‘Women، Church and State’’، Chapter VII، Polygamy، page 398.

[46] St. Augustine of Hippo، ‘‘Moral Treatises Of St. Augustine’’.  

[47] Philip Schaff، ‘‘Nicene and Post-Nicene Fathers’’: First Series، Volume IV St. Augustine: The Writings Against the Manichaeans، and Against the Donatists، Book XXII، Page 289.

[48] Littafin Asar na Ibn Badis

[49] Charlemagne.

[50] Saxons.

[51] Verden، 782.

[52] Capitulatio de partibus Saxoniae.

[53] Ustaša، Croatian Revolutionary Movement.

[55] Albigensian Crusade or Cathar Crusade (1209–1229)، Catharism، Pope Innocent III، Massacre at Béziers 1209.

[56] Massacre of Mérindol (1545)، Waldensians.

[57] Riots of Toulouse 1562.

[58] Massacre of Vassy 1562.

[59] Michelade، Saint Michael’s Day (1567)، Nîmes.

[60] St. Bartholomew's Day massacre 1572.

[61] Irish Confederate Wars 1641 – 1652.

[62]  Anabaptists 1525 – 1660.

 [63] Macarios III Zaim Patriarch of Antioch.

[64] Cyrus of Alexandria.

[65] Arianism – nontrinitarian، Arius.

[66] Look: ‘When Jesus became god’، page 191، Richard E. Rubenstein.

[67] Sharhul mumti'u (8/22).

[68] Sharhul mumti'u (8/7)

[69] Tafsir Ibn Ashur.

[70] Tafsirul muyassar.

[71] Coptic Synaxarium، Pope Benjamin I of Alexandria http://st-takla.org/Full-Free-Coptic-Books/Coptic-Synaxarium-or-Synaxarion_English/05-Topah/Coptic-Calendar_08-Toba.html#3.

[72] Pope Benjamin I of Alexandria. 

[73] Saint Mark's Coptic Orthodox Cathedral (Alexandria).

[74]  addabari mujalladi na 3, shafi na 226  

[75] Suratul insan ayata 8-9.

[76] Crimean War.

[77]  Epirus Revolt of 1854.

[78] A wurin imamu Ahamd.

[79] tufafin da be dace da masu kudi ba.

[80] Nauyi cikin jinsin kudi.

[81] Watan me haske

[82] Me fadin kafada

[83] Gasgin da yake sauka kafada

 [84] watan riga ja

[85] Sahihu muslim mujalladi na 4 shafi na 2104 lambar hadisi na 2750

[86] Sunan tirmizi mujalladi na 4 shafi na 357 lambar hadisi na 1990

[87]   Sahihu ibn hibban ,ujalladi na 13, shafi na 106, lambar hadisi na 5790 – kuma ingantacce ne.

[88]Musnad imamu Ahmad, mujalladi na 5, shafi na 362, lambar hadisi na 23114 – kuma ingantacce ne

[89]  Sunan abu dawud, mujalladi na 4, shafi na 297, lambar hadisi 4990 – hadisi ne hasan.

     [90] Bart D. Ehrman ‘‘Misquoting Jesus in the Bible’’ LECTURE minute 33:00. /see also، Bart D. Ehrman "Jesus and the Adulteress،" ‘‘New Testament Studies’’، xxxiv (1988) pp. 24-44./ See also، Bruce Metzger، A Textual Commentary on the Greek New Testament (Stuttgart، 1971)، pages 219-221.