garkuwan musulmi

Littafine da ya kunshi zikirai da addu’o’i da aka ruwaito ta matata ingantacciya.


Garkuwar Musulmi

< الهوسا >
        
Dr. Said bin Aliyu bn Wahaf Alkahtani





Salihu Abdullahi Abubakar
Aliyu Muhammad Sadisu

 

حصن المسلم

        

د. سعيد بن علي بن وهف القحطاني




ترجمة: صالح عبد الله أبو بكر
مراجعة: علي محمد سادس

 

حصن المسلم
د. سعيد بن علي بن وهف القحطاني

Garkuwar Musulmi
Na:
Dr. Said bin Aliyu bn Wahaf Alkahtani
Fassarar:
Salihu Abdullahi Abubakar.
Wanda ya duba:
Aliyu Muhammad Sadisu
Gabatarwar wanda ya duba.
   Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, dukkan godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah, Annabi Muhammad  da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya.
  Bayan haka; Wannan littafi na Hisnul Muslim, wato garkuwar musulmi littafi ne mai daraja kuma mai matukar muhimmanci wanda ya kunshi zikirai daga matata in gantacciya, yana da matukar muhimmanci a fassara shi zuwa harsuna da da ma, kuma cikin taimakon Allah an yi hakan, ciki harda harshen Hausa wanda malam Salihu Abdullahi Abubakar ya fassara. Kuma hakan ya zo ne a daidai lokacin da ake bukatarshi. Mu samman yadda zikiri yake abin so ne ga Allah madaukakin sarki wanda da shi zikin ne ma zuciya take samun natsuwa.
  Muna rokon Allah da ya saka da alheri ga wanda ya wallafa wannan littafin da kuma wadanda suka fassarashi zuwa harsuna daban-daban da wadanda suka yada shi ya saka musu da alheri, ya anfanar da mu. Shi kuma Allah mai iko ne akan hakan.
  Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzanshi Annabi Muhammad  da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya.
  Wanda ya duba,
Aliyu Muhammad Sadisu.  
email:[email protected]

 

 

 

 


Gabatarwar mawallafi.
    Lallai yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna godiya a gare shi kuma muna neman taimakwan sa, muna kuma neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu, da kuma munanan ayyukan mu.  Duk wanda Allah ya shiryar da shi to babu mai batar da shi, kuma duk wanda Allah ya batar da shi to kuma babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya da cancanta sai Allah, shi kadai yake kuma babu abokin tarayya a gare shi. Kuma Ina shaidawa cewa lalle Annabi Muhammad bawansa ne kumar Manznasa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da dak wanda ya bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako, da amincin mai yawa.
 Bayan haka;
   Wannan littafi na takaito shi ne daga littafina mai suna (Ambaton Allah da Addu’a da magani ta hanyar waraka daga Addu’o’in littafin Allah da Sannah. Na takaita a kan bangaren da ya shafi ambaton Allah (wato zikiri) don a sami saukin daukarsa a halin tafiya. Na takaita kuma kundarin lafazin zikirin, da kuma sunan littafin da aka ruwato zikrin daga cikin wadanda na kawo su a cikin littattafan na asalin wanda yake daya ne ko biyu, wanda kuma yake bukatar sanin sahabin da ya ruwato hadisin ko karin bayani akan wadanda suka ruwaito hadisin to sai ya koma ga asalin littafin.
      Ina rokon Allah mabuwayi kuma mai girama da daukaka, saboda albarkar sunayensa kyawawa da kuma siffofin sa madaukaka, ya sanya shi wannan littafin domin neman yardarsa mai daraja, kuma ya anfanar da shi a rayuwata da kuma bayan mutuwa ta, ya kuma anfanar da wanda ya rubuta, ko ya buga shi ko ya zama sababi wajan yada shi, lalle shi Allah mai tsarki majibancin wannan ne kuma mai iko ne a kansa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad da kuma iyalansa da sahabbansa da dukkan wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
  Mawallafi:
Sa’idu dan Aliyu dan Wahaf, Alkahtani.
A rubata a watan Satar, 1409. Hijira.
(Satumba, 1988).                         

 


فضل الذكر
Falalar Anbaton Allah (Zikirin) Ubangiji mai girma da daukaka.
Allah madaukakin sarki yana cewa:
ﭽ ﯩ   ﯪ  ﯫ  ﯬ  ﯭ    ﯮ  ﯯ  ﭼ البقرة: ١٥٢
Ma'ana: ''To ku anbaceni, zan anbaceku, kuma ku gode mini kada ku butulce mini (kada ku bar ni'imata)''. Suratul Bakarah, aya ta: 152.
Allah madaukain sarki yana cewa:
ﭽ ﯺ  ﯻ  ﯼ  ﯽ  ﯾ  ﯿ  ﰀ        ﰁ  ﭼ الأحزاب: ٤١
Ma'ana: ''Yaku wadanda su ka yi Imani, to ku ambaci Allah Ambato mai yawa''. Suratul Ahzab, aya ta: 41.
Allah madaukakin sarki yana cewa:
ﭽ ﯗ  ﯘ  ﯙ                ﯚ  ﯛ  ﯜ  ﯝ  ﯞ  ﯟ  ﯠ  ﯡ   ﭼ الأحزاب: ٣٥
Ma'ana: Da maza ma su anbaton Allah da yawa da mata masu anbaton, Allah ya yi musu tanadin gafara (ta musamman) dauma lada mai girma''. Suratul Ahzab, aya ta: 35.
Kuma Allah mai girma da daukaka yana cewa:
ﭽ ﯢ  ﯣ   ﯤ  ﯥ  ﯦ  ﯧ  ﯨ  ﯩ    ﯪ  ﯫ  ﯬ   ﯭ  ﯮ    ﯯ  ﯰ  ﯱ  ﯲ  ﭼ الأعراف: ٢٠٥
Ma'ana: ''Ka anbaci Ubangijinka a cikin ranka (zuciyarka) kana mai Kankan da kai kuma kana mai tsoro ba tare da ka bayyana ba (ya kasance tsakanin sirrantawa da bayyanawa) na maganar (zikirin), da safiya da marece, kuma kada ka kasance daga cikin rafkanannu”. Suratul A’araf, aya ta:205
Kuma ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi) ya ce:
(( مثل الي يذكر ربه والذي لا يذكر ربه مثل الحي والميت)).
رواه البخاري ومسلم.
Ma'ana: ''Misalin wanda ke anbaton Ubangijinsa da wanda baya anbaton Ubangijinsa misalign rayayyene da matacce''. Bukhari ya ruwaito.
Muslim ma ya ruwaito shi da wannan lafazin:
(( مثل البيت الذي يذكر الله فيه والبيت الذي لا يذكر الله فيه مثل الحي والميت)).
Ma'ana: "Misalin gidan da ake anbaton Allah a cikinsa da wanda ba'a anbaton Allah a cikinsa kamar rayayyene da matacce."
(Rayayye anan shi ne mai anbaton Allah, ko kuma gidan da ake anbaton Allah a cikinsa, matacce kuma da ake nufi shi ne gafalalle wanda baya anbaton Allah).
((ألا أنبئكم بخير أعمالكم، وأزكاها عند مليككم، وأرفعها فى درجاتكم. وخير لكم من إنفاق الذهب والورق، وخير لكم من أن تلقوا عدوكم فتضربوا أعناقهم ويضربوا أعناقكم؟ قالوا بلى. ذكرالله تعالى)). رواه الترمذي.
Ma'ana: "Shin ba na baku labari akan mafi alherin ayyukan ku ba, kuma mafi tsarkinsu a wurin mallakin ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojin ku, kuma mafi alheiri gareku da ciyar da zinariya da azurfa, kuma mafi alheri da ku hadu da abonkan gabarku ku doki wuyoyinn su,  su ma su doki wuyoyin ku"? Sai suka ce na'am sai yace: "Ambaton Allah madaukaikn sarki". Tirmizi ne ya ruwaito.
يقول الله تعالى: "أنا عند ظن عبدي بى، وأنا معه إذا دعانى، فإن ذكرنى فى نفسه ذكرته فى نفسى، وإن ذكرنى فى ملأ ذكته فى ملأ خير منهم، وإن تقرب إلي ذراعا تقربت إليه باعا، وإن أتاني يمشي أتيته هرولة" ((رواه البخاري ومسلم)).
Ma'ana: Allah mai girma da daukaka yana cewa: Ni inanan ainda bawa na ke zaton na, kuma ina tare da shi idan ya ambaceni, to idan ya ambaceni acikin ransa zan ambace shi acinki raina, kuma idan ya ambacewani a wuri mafi daukaka zan amnace shi a wuri mafi alkhairin na shi, idan kuma ya nemi kusanci a gare ni da taki guda zan kusace shin da zira'i guda, kuma idan ya kusance ni da kamu da zira'i, zan kusance shi tsawon gaba guda idan yazo gareni yana mai tafiya zan zo gare shi ina mai gaggawa". Bukhari da Musulim suka ruwaito.
 (( يا رسول الله إن شرائع الاسلام قد كثرت علي فأخبرنى بشئ أتشبث به. قال: لا يزال لسانك رطبا من ذكرالله )). رواه الترمذي.
Ma'ana: "Ya Manzan Allah shari'oin musulunci sun yi yawa a gare ni, sabo da haka ka bani labarin wani abu da zan yi riko da shi, sai ya ce: Kada ka bari harshenka ya gushe face yana danye ga ambanton Allah". Tirmizi ya ruwaito.
وقال صالى الله عليه وسلم: "من قرأ حرفا من كتاب الله فله به حسنة، والحسنة بعشر أمثالها، لا أقول: (الـــــــم) حرف، ولكن: ألف حرف، ولام حرف، وميم حرف". (رواه الترمذي).
Ma'ana: Manzon Allah tsira da amicin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Duk wanda ya karanta harafi guda daga cikin littafin Allah (madaukakin sarki) to yana da kyakkyawa (ma'ana lada) kuma kyakkyawan nan irinsa goma (10), ban ce ألم harafi bane? Abin sani shi ne ألف harafi daya kenan لام, harafi daya kenan ميم, harafi daya ke nan”. (Tiramallayy).
   وعن عقبة بن عامر رضى الله عنه، قال: خرج رسول الله صلى الله عليه وسلم ونحن فى الصفة فقال: "أيكم يحب أن يغدو كل يوم إلى بطحان أو إلى العقيق فيأتى منه بناقتين كوماوين فى غير إثم ولا قطيعة رحم؟. فقلنا: يا رسول الله نحب ذلك". قال "أفلا يغدو أحدكم إلى المسجد فيعلم، أو يقرأ آيتين من كتاب الله عز وجل خير له من ناقتين، وثلاث خير له من ثلاث، وأربع خير له من أربع، ومن أعدادهن من الإبل)). رواه مسلم.
Ma'ana: Daga Ukbah bn Amir, Allah ya yarda da shi yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya fito alhali muna Suffa, sai ya ce:"Wanene acinkin ku zai so a kallun ya yi asubanci zuwa Buthan ko zuwa Akik, ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna, ba tare da yin wani laifi ba, ko yanke zumunta? Sai muka ce muna son haka sai yace "A she dayan ku da wayewar gari ya tafi masallaci don neman sani, ko ya karanta ayoyi biyu daga littafin Allah mabuwayi da daukaka ya fi masa taguwa biyu, ayoyi hudu sun fin masa taguwa hudu da kwatankwacin adadinsa na rakuma”. ( Muslkim ya ruwaito).
وقال صلي الله عليه وسلم : ((من قعد مقعد لم يذكر الله فيه كانت عليه من الله ترة  ومن اصطجع مضجعا لم يذكر الله فيه كانت عليه من الله ترة)).  رواه  أبو داود
 Ma'ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Duk wanda ya zauna a wani wuri/waje bai ambaci Allah a wajen ba  to wannan zai zamo masa abin bibiya a wajen Allah, kuma wanda ya kwanta a makwancin sa bai anbaci Allah a wajen ba shi ma zai zame masa abin bibiya a wajan Allah”. (Abu Dawud ya ruwaito).
    وقال صلى الله عليه وسلم : ((ما جلس قوم مجسا لم يذكروا الله فيه. ولم يصلوا على نبيهم إلا كان عليهم ترة، إن شاء عذبهم وإن شاء غفرلهم)). رواه الترمذي.
Ma'ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ''Babu wasu mutane da suke zama a wani majalisi (mazauni) da basu an baci Allah acikinsa ba, kuma ba su yi salati ga Annabin su ba face ya zamo musu abin bibiya, in Allah ya so ya yi musu azaba, in kuma ya so ya gafarta musu)). (Tirmizi ya ruwaito).
    وقال صلى الله عليه وسلم: ((ما من قوم يقومون من مجلس لا يذ كرون الله فيه إلا قاموا عن مثل جيفة حمار وكان لهم حسرة)).  رواه أبو داود.
Ma’ana: Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “Babu wasu mutane da zasu tashi daga wani majlisi da basu ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan mushen jaki, kuma su zamanto masu abin da nasani''. ( Abu Daud ).
1-    أذكار الاستيقاظ من النوم
1-    Ambaton Allah yayin farkawa daga bacci .
((الحمد لله الذي أحيانا بعد ما أماتنا وإليه النشور))
Ma’ana: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya dauke ranmu (nufashi), kuma gare shi ne makoma take .
لا إله إلا الله وحده لا شريك له ، له الملك وله الحمد وهو على كل شىء قددير، سجان الله، والحمد لله ، ولا إله إلا الله ، والله أكبر ، ولا حول ولا قوة إلا الله العلي العظيم رب اغفرلي.
Ma’ana: Babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, mulki da godiya na sane, kuma shi akan dukkan komai mai iko ne, tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, kuma babu wanda ya cancan abauta masa sai Allah, Allah mai girma, babu wata dabara kuma babu karfi sai ga Allah madaukaki mai girma, Ubangi ka gafarta mini.
الحمد لله الذي عافاني في جسدي ورد علي روحي، وأذن لي بذكره
Dukkan godiya ta tabbata ga wanda ya bani lafiya a jikina, kuma ya dawo mini da raina kuma ya bani izinin ambaton sa .
Ayoyin guma 11 na karshe suratul Al imrana. (wato fadin Allah mai girma da daukaka):
ﭽ ﮉ  ﮊ      ﮋ  ﮌ  ﮍ  ﮎ  ﮏ  ﮐ  ﮑ     ﮒ  ﮓ  ﮔ  ﮕ  ﮖ  ﮗ  ﮘ  ﮙ      ﮚ  ﮛ  ﮜ  ﮝ   ﮞ  ﮟ  ﮠ     ﮡ  ﮢ  ﮣ  ﮤ  ﮥ  ﮦ  ﮧ  ﮨ  ﮩ       ﮪ   ﮫ  ﮬ   ﮭ  ﮮ  ﮯ  ﮰ  ﮱﯓ  ﯔ  ﯕ  ﯖ    ﯗ  ﯘ  ﯙ  ﯚ  ﯛ  ﯜ  ﯝ  ﯞ  ﯟ    ﯠ  ﯡ  ﯢﯣ  ﯤ  ﯥ  ﯦ  ﯧ  ﯨ  ﯩ    ﯪ  ﯫ  ﯬ  ﯭ  ﯮ  ﯯ  ﯰ  ﯱ  ﯲ   ﯳ  ﯴ  ﯵ   ﯶ  ﯷ  ﯸﯹ  ﯺ  ﯻ  ﯼ  ﯽ  ﯾ   ﭑ  ﭒ  ﭓ  ﭔ  ﭕ  ﭖ  ﭗ  ﭘ  ﭙ  ﭚ   ﭛ  ﭜ  ﭝﭞ  ﭟ  ﭠ  ﭡﭢ  ﭣ  ﭤ  ﭥ   ﭦ  ﭧ  ﭨ  ﭩ  ﭪ  ﭫ  ﭬ  ﭭ     ﭮ  ﭯ  ﭰ  ﭱ  ﭲ  ﭳ  ﭴ   ﭵ     ﭶ  ﭷ  ﭸ  ﭹﭺ  ﭻ  ﭼ  ﭽ  ﭾ  ﭿ   ﮀ  ﮁ  ﮂ  ﮃ  ﮄ      ﮅ  ﮆ  ﮇ  ﮈ  ﮉ     ﮊ  ﮋ  ﮌﮍ  ﮎ  ﮏ  ﮐ  ﮑ  ﮒ  ﮓ     ﮔ  ﮕ  ﮖ  ﮗ  ﮘ  ﮙ  ﮚ   ﮛ  ﮜ      ﮝ  ﮞ  ﮟ  ﮠﮡ  ﮢ  ﮣ  ﮤ  ﮥ  ﮦ  ﮧ  ﮨ  ﮩ   ﮪ  ﮫ  ﮬ  ﮭ  ﮮ  ﮯ  ﮰ  ﮱ  ﯓ    ﯔ  ﯕ  ﯖ  ﯗ  ﯘ  ﯙ  ﯚ  ﯛ  ﯜ   ﯝﯞ  ﯟ  ﯠ  ﯡ  ﯢ  ﯣﯤ  ﯥ  ﯦ   ﯧ  ﯨ  ﯩ  ﯪ  ﯫ  ﯬ  ﯭ   ﯮ  ﯯ  ﯰ  ﯱ  ﯲ  ﯳ  ﯴ   ﭼ آل عمران: ١٩٠ - ٢٠٠  
Ma’ana: Lalle a cikin halittar sammai da kasa, da kuma jujjuyawar dare da yini to akwai abubuwan la’akari ga ma’aboda hankula. Su ne wadanda suke anbaton Allah a tsaye da kuma zaune da kuma gefan jukkunansu, kuma suna tunani a halittar sammai da kasa, (suna cewa Ya) Ubangijin mu ba ka halicci wannan don wasa ba, tsarki ya tabbata a gareka to ka tsare mu azabar wuta. (Ya) Ubangijn mu! Lalle ne kai duk wanda ka shigar da shi wuta to hakika ka tozartar da shi, kuma kafirai ba su da mataimaka.
 (Ya) Ubangijin mu! Lalle ne mu mun ji maishela yana kira akan ku yi imani da Ubangijinku to mun yi imani, (Ya) Ubangijin mu ka gafarta mana zunuban mu, kuma ka kankare mana laifukan mu kuma ka dauki rayukan mu tare da mutanan kwarai. (Ya) Ubangijin mu! Kuma ka ba mu abinda ka yi mana alkawarinsa akan (har sunan) Manzanninka, kuma kada ka kunyata mu ranar alkiyama, lalle ne kai ba ka saba alkawari.
    Sai Ubangijin su ya amsa musu (cewa) lalle ni ba na tozartar da aikin mai aiki daga cikinku daga namiji ko mace, sashinku daga sashi, to dukkan wadanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajansu aka kuma cutar da su akan hanya ta, kuma suka yi yaki kuma aka kashe su hakika zan kankare musu laifukansu kuma hakika zan shigar da su gidaje na aljanna da koramu suke gudana daga karkashinsu (wannan) ladane daga wurin Allah, kuma Allah a wurinsa ne kyakkyawan lada yake.
 Kada jujjuyawar da kafirai suke yi a garuruwa ya rudar da kai. Jin dadine kadan, sannan makomarsu jahannama, kuma ta yi muni ta zama shinfida. Saidai dukkanin wadanda suka ji tsoron Ubangijinsu suna da gidaje na aljanna da koramu suke gudana daga karkashin su masu dawwamane a cikinta, garace daga wurin  Allah, kuma abinda yake a wurin Allah shi ne ya fi ga mutanan kwarai.
  Kuma hakika akwai daga cikin wadanda aka baiwa littafi wadanda tabbas suna yin imani da Allah da kuma abinda aka saukar  zuwa gareku da kuma abinda aka saukar zuwa garesu suna masu kankan-da-kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da kudi kadan, wadannan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, lalle Allah mai saurin hisabi ne.
  Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri ku cije kuma ku yi dako ku ji tsoron Allah domin ku rabauta. (Suratu Ali Imran, aya ta:190-200).    
2-    دعاء لبس الثوب
2- Addu’ar sanya tufafi
الحمد لله الذى كسانى هذا ((الثوب)) ورزقنيه من غير حول مني  ولا قوة.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wannan da ya sututar da ni wannan tufa, kuma ya arzurtani shi ba tare da wata dabara ba, kuma ba tare da karfi na ba.
3-    دعاء لبس الثوب الجديد
Addu’ar Sanya sabon kaya
اللهم لك الحمد أنت كسوتنيه ، أسلك من خيره وخير ما صنع له ، وأعوذ بك من شره وشر ما صنع له .
Ma’ana: Allah yabo da godiya naka ne, kai kadai ka tufatar da ni shi (wannan tufafin), ina neman tsarinka daga sharrinsa da sharrin abinda aka hallice shi da shi .
4-    الدعاء لمن لبس الثوب جديدا.
4- Addu’a ga wanda ya sanya sabon abu ko wanin sa
تبلى ويخلفا الله تعالى.
Ma’ana: Allah ya sa ka mayar da ita tsomin, kuma Allah madaukaki ya mayar maka da wata tufa.
البس جديدا ، وعش حميدا، ومت شهيدا .
Ma’ana: Allah nake roko ya sa albarka, ka sanya sabo kuma ka rayu kana abin yabo, kuma ka mutu kana shahidi .

 


5-    ما يقول إذا وضع ثوبه.
5- Abinda zai fada yayin cire tufa
بسم الله            Ma’ana: Da sunan Allah
6-    دعاء دخول الخلاء
6- Addu’ar shiga ban daki
( بسم الله ) اللهم إنى أعوذ بك من الخبث والخبائث
Ma’ana: (Da sunan Allah) ya Allah lalle ne ina neman tsarinka daga sharrin aljanu maza da aljanu mata “.
7-    دعاء الخروج من الخلاء
7- Addu’ar fita daga bandaki
غفرانك         Ya Allah gafararka nake neman
8-    الذكر قبل الوضوء
8- Ambaton Allah gabanin Alwala
بسم الله  Ma’anan:  Da sunan Allah,          
9-    الذكر بعد الفراغ من الوضوء
9- Bayana kamala alwala.
أشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له وأشهد أن محمد عبده  ورسوله .
Ma’ana : Ina shedawa babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah . kuma ina shaidawa da cewa lalle Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne .
اللهم اجعلنى من التوابين واجعلنى من المتطهرين
Ma’ana: Ya Allah ka sanya ni daga cikin masu tuba kuma ka sanya ni cikin masu sarki.
10-    الذكر عند الخروج من المنزل
10- Ambaton (Allah) yayin fita daga gida
بسم الله توكلت على الله ولا حول ولا قوة إلا بالله
Ma’ana: Da sunan Allah, ga Allah kadai na dogara, kuma babu wata dabara ko karfi sai ga Allah.
اللهم أعوذ بك أنْ أَضِلَّ، أَوْ أُضَلَّ، أو أَزِلَّ، أوْ أُزَلَّ أو أَظْلَمَ، أَوْ أُظْلَمَ أَوْ أَجْهَلَ أَوْ يُجْهَلَ عَلَيَّ.
Maana: Ya Allah ina neman tsarinka daga bata ko a batar da ni, ko na zame ko a zamar da ni, ko na yi zalunci ko azalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta.
11-    الدعاء عند دخول  المنزل.
11- Addu’ar  shiga gida.
بسم الله ولجنا، وبسم الله خرجنا، وعلى الله ربنا توكلنا.  ثم ليسلم على أهله
Ma’ana: Da sunan Allah ne muka fita, kuma da sunan Allah ne muke shiga, kuma da ga Allah Ubangijin mu kadai muka dogara. Sannan ya yi sallama ga iyalansa.
12-    دعاء الذهاب إلى المسجد
12- Addu’a yayin tafiya masallaci.
اللهم اجعل في قلبي نورا، وفى لسانى نورا، وفى سمعى نورا، وفى بصرى نورا، ومن فوقي نورا ومن تحتى نورا، وعن يمينى نورا وعن شمالي نورا، ومن أمامى نورا ومن خلفي نورا، واجعل فى نفسي نورا، وأعظم لى نورا وعظّم نورا، واجعل لى نورا واجعلنى نورا. اللهم أعطنى نورا واجعل فى عصبى نورا، وفى لحمى نورا، وفى دمي نورا وفى شعرى نورا، وفى بشَرى نورا، اللهم اجعل نورا في قبري، ونورا في عظامي، وزدني نورا، وزادني نورا، وهب لي نورا على نور.
Ma’ana: Ya Allah ka sanya haske acikin zuciya ta, da haske ga harshe na, da haske ga ji na, da haske a gani na, da haske a karkashi na da haske a sama na, da haske  a dama ta da haske a hagu na da haske a gaba na da haske a baya na, ka sanya haske a cikin raai na, ka girmama mini haske na, ka girmama haske, ka sanya ni na zama haske, ka sanya haske a cikin jijiyoyi na da haske acikin nama na, da haske a cikin jini na, da haske a cikin gashina, da haske a cikin fata ta. Ya Allah! Ka sanya mini haske a cikin kabarin na, da haske a cikin kasusuwa na, ka kara mini haske, ka kara mini haske, ka kara mini haske ka bani haske akan haske.

 

13-    دعاء دخول المسجد.
13- Addau'ar shiga masallaci.
 Zai fara gabatar da kafarsa ta dama ne a lokacin shiga, sannan ya ce:
"أعوذ بالله العظيم، وبوجهه الكريم، وسلطانه القديم، من الشيطان الرجيم"
Ma'ana: ina neman tsarin Allah mai girma, da fuskarsa mai alfarma, da na mulkin sa dadadde daga shaitan la'ananne.
بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله عليه، اللهم افتح لي أبواب رحمتك .
Ma’ana: Da sunan Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah. Ya Allah ka bude mini kofofin rahmarka.

 

14-    دعاء الخروج من المسجد
14- Addu’ar fita daga masallaci.
Zai fara gabatar da kafarsa ta hagune a lokacin fita, sannan kuma ya ce:
بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله. اللهم إني أسألك من فضلك، أعصمنى من الشيطان الرجيم .
Ma’ana: Da sunan Allah tsira da amincin Allah su tabbata ga mazon Allah ina rokonka daga cikin falalarka, ya Allah ka tsareni daga shaidan la’annane.
15-    أذكار الأذان
15- Ambaton Allah a lokacin kiran sallah.
يقول مثل ما يقول المؤذن إلا في: حي على الصلاة وحي على الفلاح  فيقول : لا حول ولا قوة إلا بالله.
Ma'ana: Musulmi zai fadi dukkan abinda mai kiran sallah ya ce, saidai idan mai kiran sallar ya ce:
"حى على الصلاة وحى على الفلاح".
Sai shi kuma ya ce:
"لاحول ولا قوة إلا بالله".
Bayan ladan ya yi Kalmar shahada sai shi mai sauraronsa ya kammala da cewa:
وأنا أشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له، وأن محمدا عبده ورسوله، رضيت بالله ربا وبمحمد رسولا، وبالإسلام دينا.
Ni ma ina shaidawa da cewa babu abin bautawa da gaskiyya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a agare shi, kuma Annabi Muhammad bawansa ne, kuma manzon sa ne. Na yarda da Allah shi ne Ubangiji, kuma (Annabi) Mahammad shi ne manzo, kuma musuluci shi ne addini.
ويقول ذلك عقب تشهد المؤذن.
Zai fadi haka ne a karshen kowacce shahadar da ladan ya yi.
يصلى على النبى صلى الله عليه وسلم بعد فراغه من إجابة المؤذن.
Zai yi salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bayan ya kammala amsawarsa ga ladan.
يقول: اللهم رب هذه الدعوة التامة والصلاة القائمة، آت محمد الوسية والفضيلة، وابعثه مقاما محمودا الذي وعدته (إنك لا تخلف الميعاد).
Ma'ana: sai ya ce ya Allah: Ubangiji wannan ita ce kira cikakka, da wannan sallar da za'a tsayar da ita, ka ba Annabi Muhammad wasila da falala, kuma ka ta she shi a matsayin abin yabo, wannan da ka alkawarta masa. (lalle kai baka saba alkawari).
يدعو لنفسه بين الأذان والإقامة فإن الدعاء حينئذ لا يرد.
  Sai ya yi wa kansa addu'a a tsakanin kiran sallah da tada ikama, domin addu'a a wannan lokaci ba'a kin karbar ta.
16-    دعاء الاستفتاح.
Addu'ar bude sallah.
Bayan kabbara kafin karafun faliha.
اللهم باعد بينى وبينى خطاياي كما باعدت بين المشرق والمغرب، اللهم نقِّني من خطايا، كما يُنقى الثوب الأبيض من الدنس، اللهم اغسلنى من خطاياى، بالثلج والماء والبرد".
Ma'ana: Ya Allah! ka nisanta tsakani na da laifuffukana kamar yadda ka nisanta tsakanin gabas da yamma, ya Allah! Ka tsarkake ni daga laifuffaka na kamar yadda ake tsakake farar tufa daga dauda, ya Allah! Ka wanke ni daga laifuffuka na da kankara da ruwa da raba.
   سبحانك اللهم وبحمدك وتبارك اسمك وتعالى جدك ولا إله غيرك.
Ma'ana: Tsarki ya tabbata gareka ya Allah, tare da yabo gareka; albarkatun sunanka sun yawaita, mulkinka da girmanka sun daukaka, babu abin bautawa da gaskiya da cancanata sa kai.
17-    دعاء الركوع
                       17- Addu’ar Ruku’i.
سبحان ربي العظيم ( ثلاث مرات ) .
Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga Ubangiji na mafi girma.

18-    دعاء الرفع من الركوع
18- Addu’ar dagowa daga Ruku’i
سمع الله لمن حمده .
Ma’ana: Allah ya ji dukkan wanda ya gode masa.
ربنا ولك الحمد حمدا كثيرا طيبا.
Ma’ana: Ya Ubangijin mu, dukkan yabo ya tabbata a gare ka, yabo mai yawa kyakkyawa, kuma abinsa wa albarka a cikinsa.
ملء السموات وملء الأرض وما بينهما، وملء ما شئت من شيء بعد، أهل الثناء والمجد، أحق ما قال العبد، وكلنا لك عبد، اللهم لا مانع لما أعطيت، و لا معطي لما منعت، و لا ينفع ذا الجد منك الجد.
 Ma’ana: Ya Ubangijin mu, dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai cika sammai da kasa da abinda ke tsakani su, kuma cika duk wani abu da ka so bayan haka, ya wanda ya cancanci yabo da daukaka, gaskiya ne abinda bawa ya fadi, kuma dukkanin mu bayi ne gare ka. Ya Allah babu mai hana abin da ka bayar, kuma babu mai bayar da abinda ka hana, kuma wadata ba ta tsirar da mai wadata daga gare ka.
19-    دعاء السجود
19- Addu’a a lokacin da aka yi sujuda.
سبحان ربي الأعلى (ثلاث مرات).
Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga Ubangiji na madaukaki .
سبحانك اللهم ربنا وبحمدك، اللهم اغفر لي.
Ma’ana: Tsarki ya tabbata gare ka ya kai Allah, ya Ubagijin mu godiya ta tabbata a gareka, ya Allah ka gafatar mini.
سبوح، قدوس، رب الملائكة والروح.
Ma’ana: Ubangiji abin tsarkakewa, mai kubuta daga dukkan abin da bai kamace da shi ba, Ubangijin mala’iku da jibirilu.
اللهم لك سجدت ، وبك أمنت ، ولك أسلمت ، سجد وجهى للذى خلقه ، وصوره ، وشق سمعه وبصره ، تبارك الله أحسن الخالقين.
Ma’ana: Ya Allah gareka na yi sujjada kuma da kai na yi imani, kuma gareka na mika wuya, fuskata ta yi sujjada ga wanda ya halicce ta, kuma ya suranta ta, kuma ya tsaga mata ji da gani, Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa sun yawaita.
سبحان ذى الجبروت ، والملكوت والكبرياء ، والعظمة.
Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga (Allah) mai dole da mulki, da kasaitar daukaka da girma.
اللهم اغفرلي  ذنبي كله ، دقه وجله ، وأوله ، وآخره ، وعلانيته وسره ".
Ma’ana: Ya Allah ka gafarta mini zunubina gabaki dayan su kananansu, da mayansu, na farkonsu da na karshansu bayanannansu da boyayyasu.
اللهم إني أعوذ برضاك من سخطك ، وبمعافاتك من عقوبتك وأعوذبك منك ، لا أحصي ثناء عليك ، أنت كما أثنيت على نفسك.
Ma’ana: Ya Allah ina neman tsari da yardarka daga fushinka da kuma rangwamanka daga ukubarka, kuma ina neman tsari da kai daga gareka, ban isa na tuke ga yabo mai cancanta gareka ba, kai dai kamar yadda ka yabi  kankane.
20- دعاء الجلسة بين السجدتين.
20- Addu’a a tsakanin sujjadu biyu.
           رب اغفرلي رب اغفرلي.                                                             Ma’ana: Ya Ubangijina ka gafarta mini, ya Ubangijina kagafarta min.
اللهم اغفرلي ، وارحمنى ، واهدني ، واجبرني ، وعافني ، وارذقني وارفعني.
Ma’ana: Ya Allah ka gafarta mini, ka ji kai na, ka shiryar da ni, ka bani lafiya da tsira daga musifu, ka wadata ni, ka azurta ni, ka daukaka ni .
21- دعاء سجود التلاوة.
21- Addu’ar sujjadar karatun Alkur’ani.
سجد وجهى الذى خلقه ، وشق سمعه وبصره بحوله وقوته ، ( فتبارك الله أحسن الخلقين ).
Ma’ana; Fuska ta ta yi sujjada ga wanda ya hallicce ta, kuma ya tsaga mata ji da gani, iyawarsa da kuma karfinsa (Allah mafi gwaninta masu halitta, ya girmama, kuma alherinsa ya yawaita) .
اللهم اكتب لي بها عندك أجرا وضع عنى بها وزرا ، واجعلها لي عندك ذخرا ، وتقبلها منى كما تقبلها من عندك داود.
Ma'ana: Ya Allah! Ka rubuta mini lada a wurinka sabaoda (wannan) sujjada, ka kankare mini zunibi saboda ita, ka sanyata ta zamo taskar arziki gare ni a wajen ka, kuma ka karbe ta daga gareni, kamar yadda ka karbe ta daga bawanka Daud.
22- التشهد.
22- Tahiyya
التحيات لله ، والصلوات ، والطيبات ، السلام عليك أيها النبي ورحمة الله وبركاته، السلام علينا وعلى عباد الله الصالحين . أشهد أن لا إله إلا الله وأشهد أن محمد عبده ورسوله.
Ma’ana: Dukkan gaisuwa ta bbata ga Allah, da kuma salloli da kyawawan kalmomi, amincin Allah ya tabbata gareka ya kai wannan Annabi, da rahmara da albarkarsa. Amincin Allah ya tabbata a gare mu da dukkan bayin Allah salihai. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma lalle Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzowa ne.
23- الصلاة على النبى صلى الله عليه وسلم بعد التشهد
23- Salati ga Ma’aikin Allah bayan Tahiyya.
اللهم صل على محمد وعلى آل محمد كما صليت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم،  إنك حميد مجيد. اللهم بارك على محمد وعلى آل محمد كما باركت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم، إنك حميد مجيد.
Ma’ana: Ya Allah ka dada tsira ga Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gaire shi), da iyalan Annabi Muhammad, kamar yadda ka dada tsira ga Annabi Ibrahim. Lalle kai abin godewa ne mai girma. Ya Allah ka yi albarka ga Annabi Muhammad, kamar yadda ka yi albarkar ga Annabi Ibrahim da iyalan Annabi Ibrahim. Lallai kai abin godewa ne mai girma .
اللهم صل على محمد وأزواجه وذريته كما صليت على آل إبراهيم، وبارك على محمد وعلى أزواجه وذريته  كما باركت على آل  إبراهيم إنك حميد مجيد.
Ma’ana: Ya Allah ka dada tsira ga Annabi Muhammad, kuma da matan sa da zuriyarsa, kamar yadda ka yi tsira ga Annabi Ibrahim, kuma ka yi albarka ga Annabi Muhammad da matan sa dazuriyar sa, kamar yadda ka yi albarka ga Annabi Ibrahim, lalle kai abin godewa ne mai girma.
24- الدعاء بعد التشهد الأخير قبل السلام.
24- Addu’a bayan Tahiyyar karshe kafin sallemewa.
اللهم إنى أعوذ بك من عذاب القبر، ومن عذاب جهنم،  ومن فتنة المحيا والممات، ومن شر فتنة المسيح الدجال.
Ma’ana: Ya Allah ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar jahannama, da fitinar rayuwa da mutuwa da sharrin fitinar dujal.
اللهم إنى إعوذ بك من عذاب القبر، ومن عذاب القبر، وأعوذ بك من فتنة المسيح الدجال، وأعوذ بك  من فتنة المحيا والممات، اللهم إنى إعوذ بك  فتنة من المأثم والمغرم.
Ma’ana: Ya Allah ina neman tsarinka daga azabar kabari, da kuma azabar fitinar Dujal, kuma ina neman tsarinkka daga azabar fitinar rayuwa da mutuwa, ya Allah ina neman tsarin ka daga kuma sharrin laifi da bashi.
اللهم إنى ظلمت نفسي ظلما كثيرا، ولا يغفر الذنوب إلا أنت، فاغفرلى مغفرة من عندك، وارحمنى، إنك أنت الغفور الرحيم.
Ma’ana: Ya Allah lalle ne ni na zalunci kai na zalunci mai yawa, kuma babu mai gafarta zunubai sai kai, saboda haka ka gafarta mini gafara daga gareka, kuma ka ka yi mini rahama, lalle kai ne mai yawan gafara mai yawan jinkai.
اللهم اغفرلى ما قدمت وما أخرت، وما أسررت وما أعلنت، وما أسرفت وما أنت أعلم به منى، أنت المقدم  وأنت المؤخر، لا إله إلا أنت.       
Ma’ana: Ya Allah ka gafarta mini abinda na gabatar da abinda na jinkirta, da abinda da na boye da abinda na bayyana, da abinda na yi da kuma abinda kai ne kafini sanin sa, kai ne na farko kuma kai ne na karshe, babu abin bauta da cancanta sai kai.
اللهم أعنى على ذكرك وشكرك وحسن عبادتك.
Ma’ana: Ya Allah ka taimake ni akan zikirinka da yin godiya a gare ka, da kyautata ibada gare ka.
اللهم إنى أعوذبك  من البخل وأعوذ بك من الجبن، وأعوذبك من أن أدر إلى أرذل العمر، وأعوذ بك من فتنة الدنيا وأعوذبك من عذاب القبر.
Ma’ana: Ya Allah lalle ne ni ina neman tsarinka daga rowa, ina kuma neman tsarinka daga tsoro, kuma ina neman tsarinka da a mai da ni wulakantacciyar rayuwa, kuma ina neman tsarinka daga fitinar duniya da kuma fitinar kabari.
اللهم إنى أسألك الجنة، وأعوذ بك من النار.
Ma’ana: Ya Allah lalle ne ni ina rokon ka aljanna, kuma ina neman tsarinka daga wuta.
اللهم بعلمك الغيب، وقدرتك على الخلق، أحينى ما علمت الحياة خيرا لى، وتوفنى إذا علمت الوفاة خيرا لى، اللهم إنى أسألك خشيتك فى الغيب والشهادة، وأسألك  كلمة الحق فى الرضا والغضب، وأسألك قصد فى الغنى والفقر، وأسألك نعيما لا ينفد، وأسألك قرة عين لا تنقطع، وأسألك الرضا بعد القضاء، وأسألك برد العيش بعد الموت، وأسألك لذة النظر إلى وجهك والشوق إلى لقائك فى غير ضراء مضرة، ولا فتنة مضلة، اللهم رينا برينة الإيمان واجعلنا هداة مهتدين.
Ma’ana: Ya Allah saboda saninka da abinda yake boye, da kuma ikonka akan hallita, ka rayar da ni idan ka san rayuwar tafi alheri a gare ni, kuma ka dauki raina idan ka san mutuwar tafi alheri a gare ni, Ya Allah lalle ne ina rokonka jin tsoronka a boye da kuma a sarari, kuma ina rokonka fadar gaskiya a halin dadin rai da halin fushi, kuma ina rokonka tsakaituwa a cikin wadata da kuma talauci, kuma ina rokonka ni’ima da bata karewa, kuma ina rokonka farin cikin da baya yankewa, kuma ina rokonka yarda da kaddara bayan aukuwarta, kuma ina rokonka rayuwa ta ni’ima bayan mutuwa, kuma ina rokonka dadin kallon fuskarka da kuma shaukin saduwa da kai, batare da cutar mai cutarwa ba ko fitinar mai batarwa ba, Ya Allah kayi mana ado da adon Imani, kuma ka sanya mu masu shiryarwa kuma shiryayyu.
اللهم إنى أسألك يالله بأنت الواحد الأحد الصمد الذي لم يلد ولم يولد ولم يكن له كفوا أحد أن تغفرلى ذنوبنى، إنك أنت الغفور الرحيم.
Ma’ana: Ya Allah lalle ne ni ina rokonka ya Allah saboda kai kadai ne tal wanda ake nufinsa da dukkan bukatu, wanda bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba, kuma babu wanitanka (irinsa) agare shi, ka gafarta mini zunubaina, kai ne mai yawan jinkai.
اللهم إنى أسألك بأن لك الحمد لا إله إلا أنت وحدك لاشريك لك، المنان يا بديع السموات والأرض يا ذا الجلال والإكرم، ياحي يا قيوم، إنى أسألك الجنة وأعوذبك من النار.
Ma’ana: Ya Allah lalle ne ni ina rokonka saboda dukkan yabo ya tabbata a gareka babu abin bautawa da cacanta sai kai kadai, babu abukin tarayya agareka, mai yawan baiwa ya makagin halittar sammai da kasa, Ya ma’abocin girma da alherai (karamci), Ya rayayye Ya mai tsayuwa (da kansa kuma kowa ya tsayu da shi), ina rokonka aljanna, kuma ina neman tsarinka daga wuta.
اللهم إنى أسألك بأنى أشهد أنك أنت الله لا إله إلا أنت الأحد الصمد الذى لم يلد ولم يلد ولم يكن له كفوا أحد.
Ma’ana: Ya Allah lalle ne ni ina rokonka saboda ni ina shaidawa da cewa kai ne Allah babu abin bautawa da cancanta sai kai, kai kadai tal wanda ake nufatarsa da dukkanin bukatu, wanda bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba, kuma babu wani tamka a gareshi.
25- الأذكار بعد السلام من الصلاة.
25- Zikiran bayan sallamewa daga sallah.
أستغفر الله (ثلات).
Ma'ana: Ina neman gafarar Allah. (San uku)
اللهم أنت السلام ومنك السلام تباركت يا ذا الجلال والإكرام.
Ma'ana: Ya Allah kai ne aminci, kuma daga gareka aminci yake, alherin ka ya yawaita ya ma'abocin girma da alheri (karanci).
"لا إله إلا الله وحده لاشريك له، له الملك وله الحمد، وهو على كل شىء قدير، (ثلاثا). اللهم لا مانع لما أعطيت ومعطي لما منعت، ولا ينفع ذا الجد منك الجد.
Ma'ana: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai yake bas hi da abokin tarayya, mulki na sane, kuma yabo ma na sane, kuma shi ne mai iko akan komai.(kafa uku). Ya Allah! Babu mai hana abinda ka bayar, kuma babu mai bayar da abinda ka hana, kuma wadata bata tsirar da mai wadata daga dare ka.
"لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شىء قدير، لاحول ولاقوة إلا بالله، لا إله إلا الله، ولا نعبد إلا إياه، له النعمة وله الفضل وله الثناء الحسن، لا  إله إلا الله مخلصين له الدين ولو كره الكافرون.
Ma'ana: Babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai ne tal ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, kuma yabo nasa ne, kuma shi ne mai’iko akan komai, kuma babu dabara kuma babu karfi sai ga Allah, babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah, ba za mu bautawa kowa ba sai shi (Allah), ni'ima tasa ce, kuma falala ma tasace, kyakkawan yabo nasa ne babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsarkake bauta a gare shi, (tsarkakewa daga shirka) koda kafirai sunki.
سبحان الله، والحمد لله، والله أكبر. (ثلاثا وثلاثين)
Ma'ana: Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma Allah shine mafi girma. (sau talati da uku:33).
لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شىء قدير.
Ma'ana: Babu wani abun bautawa da cancanta sai Allah, shi-shi kadai tal yake, ba shi da abon kin tarayyah, koma shi mai ika ne akan komai.
ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﭑ  ﭒ  ﭓ  ﭔ  ﭕ  ﭖ  ﭗ  ﭘ  ﭙ  ﭚ   ﭛ  ﭜ  ﭝ  ﭞ  ﭟ  ﭠ  ﭡ  ﭢ  ﭣ   ﭼ الإخلاص: ١ - ٤
Ma’ana: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin kai.
1. Ka ce; Shi ne Allah shi kadai.
2. Allah wanda ake nufata da dukkanin bukatu.
3. Bai haifa ba kuma ba’a haifeshi ba.
4. Kuma wani bai kasance kini a gare shi ba.
(Suratul Ikhlas, aya ta: 1-4).  

 
سورة الفلق
ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﭤ  ﭥ  ﭦ  ﭧ  ﭨ  ﭩ  ﭪ   ﭫ  ﭬ  ﭭ  ﭮ   ﭯ  ﭰ  ﭱ  ﭲ  ﭳ  ﭴ  ﭵ  ﭶ  ﭷ   ﭸ  ﭹ  ﭺ  ﭻ     ﭼ  ﭽ  ﭾ  ﭿ   ﭼ الفلق: ١ - ٥

Ma’ana: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin kai.
1. Ka ce; Ina neman tsari daga Ubangijin safiya.
2. (Ya tsare ni) daga sharrin abinda ya halitta.
3. Da kuma sharrin dare idan ya yi duhu.
4. Da kuma sharrin masu tofi akuduri (a kulli).
5. Da kuma sharrin mai hasada idan ya yi hasada.
        (Suratul Falak, aya ta: 1-5).

سورة الناس
ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﮀ  ﮁ   ﮂ  ﮃ  ﮄ  ﮅ  ﮆ  ﮇ  ﮈ   ﮉ  ﮊ  ﮋ  ﮌ  ﮍ  ﮎ  ﮏ  ﮐ   ﮑ  ﮒ  ﮓ  ﮔ  ﮕ   ﮖ  ﮗ  ﮘ  ﮙ   ﭼ الناس: ١ - ٦
Ma’ana: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin kai.
1. Ka ce; Ina neman tsari daga Ubangijin mutane.
2. Mamallakin mutane.
3. Abin bautar mutane.
4. (Ya tsare ni) daga sharrin maiwaswasi alkhannas.
5. Wanda yake waswasi a zukatan mutane.
6. Daga cikin aljanu yake da kuma mutane.
  (Suratun Nas, aya ta: 1-6).
ءاية الكرسي
Ayatul kursiyyi
ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﮣ  ﮤ  ﮥ  ﮦ   ﮧ   ﮨ  ﮩﮪ  ﮫ  ﮬ  ﮭ  ﮮ  ﮯﮰ  ﮱ  ﯓ  ﯔ  ﯕ  ﯖ     ﯗ  ﯘﯙ  ﯚ  ﯛ  ﯜ  ﯝ  ﯞ  ﯟ   ﯠﯡ  ﯢ  ﯣ  ﯤ   ﯥ  ﯦ  ﯧﯨ  ﯩ  ﯪ  ﯫ  ﯬ  ﯭ  ﯮ    ﯯ    ﯰﯱ  ﯲ  ﯳ           ﯴ  ﯵﯶ  ﯷ     ﯸ     ﯹﯺ   ﯻ  ﯼ   ﯽ  ﯾ  ﭼ البقرة: ٢٥٥

Ma’ana: “Allah, babu wani abin bautawa da cancanta sai shi, Rayayye, mai tsayuwa da komai, gyangyadi ba ya kamashi kuma macci baya kamashi, shi ke da abinda ya ke cikin sammai da abinda ke cikin kassai, wanene yake yin ceto awurinsa sai dai da izininsa? Yana sane da abinda yake gaban su da abinda ke bayan su, kuma ba su kewayewa da komai daga ilimi sa, saidai da abinda ya so, Kursiyin sa ya yalwaci sammai da kassai, Kuma shi ne madaukaki mai girma”. Suratul Bakara, aya ta: 255.
عقب كل صلاة      .    Bayyan kowa ce sallah.                                            
لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شىء قدير.(عشر مرات)
Ma'ana: Babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai tal yake ba shi da abokin tarayya, kuma mulki na sane, kuma yabo nasa ne, kuma shi mai’iko ne akan komai. (sau goma 10, bayan sallar magriba da asuba.)
اللهم إنى أسألك علما نافعا ورزقا طيبا، وعملا متقبلا. (بعد السلام من صلاة الفجر).
Ma'ana: Ya Allah! lalle ne ni ina rokon ka ilimi mai anfani, da arziki kyakkyawa wato nahalal, da aiki karbabbe. (bayan sallamewa daga sallar asuba).
دعاء صلاة الاستخارة.
Addu’ar sallar Istihara.
 Da ake yi dan gane da neman zabi a wurin Allah.
قال جابر بن عبد الله رضى الله عنهما: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يعلمنا الاستخارة فى الأمور كلها كما يعلمنا السورة من القرآن يقول: إذا هم أحدكم بالأمر فليركع ركعتين من غير الفريضة ثم ليقل: اللهم إنى أستخيرك بعلمك، وأستقدرك بقدرك، وأسألك من فضلك ، فإنك تقدر ولا أقدر، وتعلم ولا أعلم، أعلم، وأنت علام الغيوب، اللهم إن كنت تعلم أن هذا االأمر  (  ) ويسمى حاجته – خير لى فى دينى ومعاشي وعاقبة أمري – أو قال : عاجله وآجله – فاقدره لى ويسره لي ثم بارك لى فيه، وإن كنت تعلم أن هذا الأمر شر لى فى دينى ومعاشي وعاقبة أمري – أو قال : عاجله وآجله – فاصرفه عنى واصرفنى عنه واقدر لى الخير حيث كان ثم أرضىني به ).
Ma’ana: Jabir bin Abdullah (Allah ya yarda da shi da mahaifin sa) ya ce: Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) acikin dukkan al’amura baki-daya kamar yadda yake koya mana sura daga cikin Alkur’ani, ya kance idan dayanku ya yi niyyar yin wani al’amari to sai ya yi sallah raka’a biyu ba ta farilla ba, sannan sa ya ce: -
    “Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman ka bani iko domin ikonka, kuma ina rokonka daga falalar ka mai girma domin kai ne mai ikon ni kuwa bani da iko, kuma kai ne masani, ni kuwa ban sani ba, kuma kai ne masanin abubuwan boye. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al’amari (      ) sai ya ambaci bukatar tasa – alheri ne gare ni acikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al’amarina yanzunnan ko nangaba –ka kaddara mini shi, kuma ka saukake mini shi, sannan ka albarkace ni a cikinsa, kuma idan ka san wannan al’amari sharri ne a gare ni acikin addinina da rayuwata, da karshen al’amarina – awata ruwayar  kuma  yanzunnan ko nangana – ka kawar da shi daga gare ni, kuma ka kawar da ni daga gare shi, kuma ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma ka sanya ni in yarda da shi.
وما ندم من استخارة، وشاور المخلوقين المؤمنين وتثبت فى أمره، فقد قال سبحانه : ( وشاورهم فى الأمر فإذا عزمت فتوكل على الله).
Duk wanda ya nemi zabin mahalliccin, kuma yayi shiwara da talikai muminai, kuma ya yi ya himmatu a al’amarinsa to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki ya ce:- “Kuma ka shawarce su cikin al’amari, idan kuma ka kudurta niyya  to ka dogara ga Allah.
أذكار الصباح والمساء .    
Ambaton Allah na safiya da kuma maraice.
                                    ءاية الكرسي
ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ
ﭽ ﮣ  ﮤ  ﮥ  ﮦ   ﮧ   ﮨ  ﮩﮪ  ﮫ  ﮬ  ﮭ  ﮮ  ﮯﮰ  ﮱ  ﯓ  ﯔ  ﯕ  ﯖ     ﯗ  ﯘﯙ  ﯚ  ﯛ  ﯜ  ﯝ  ﯞ  ﯟ   ﯠﯡ  ﯢ  ﯣ  ﯤ   ﯥ  ﯦ  ﯧﯨ  ﯩ  ﯪ  ﯫ  ﯬ  ﯭ  ﯮ    ﯯ    ﯰﯱ  ﯲ  ﯳ           ﯴ  ﯵﯶ  ﯷ     ﯸ     ﯹﯺ   ﯻ  ﯼ   ﯽ  ﯾ  ﭼ البقرة: ٢٥٥
Ma’ana: “Allah, babu wani abin bautawa da cancanta sai shi, Rayayye, mai tsayuwa da komai, gyangyadi ba ya kamashi kuma macci baya kamashi, shi ke da abinda ya ke cikin sammai da abinda ke cikin kassai, wanene yake yin ceto awurinsa sai dai da izininsa? Yana sane da abinda yake gaban su da abinda ke bayan su, kuma ba su kewayewa da komai daga ilimi sa, saidai da abinda ya so, Kursiyin sa ya yalwaci sammai da kassai, Kuma shi ne madaukaki mai girma”. Suratul Bakara, aya ta: 255.

سورة الإخلاص
ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﭑ  ﭒ  ﭓ  ﭔ  ﭕ  ﭖ  ﭗ  ﭘ  ﭙ  ﭚ   ﭛ  ﭜ  ﭝ  ﭞ  ﭟ  ﭠ  ﭡ  ﭢ  ﭣ   ﭼ الإخلاص: ١ - ٤

Ma’ana: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin kai.
1. Ka ce; Shi ne Allah shi kadai.
2. Allah wanda ake nufata da dukkanin bukatu.
3. Bai haifa ba kuma ba’a haifeshi ba.
4. Kuma wani bai kasance kini a gare shi ba.

 

 


سورة الفلق
ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﭤ  ﭥ  ﭦ  ﭧ  ﭨ  ﭩ  ﭪ   ﭫ  ﭬ  ﭭ  ﭮ   ﭯ  ﭰ  ﭱ  ﭲ  ﭳ  ﭴ  ﭵ  ﭶ  ﭷ   ﭸ  ﭹ  ﭺ  ﭻ     ﭼ  ﭽ  ﭾ  ﭿ   ﭼ الفلق: ١ – ٥
Ma’ana: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin kai.
1. Ka ce; Ina neman tsari daga Ubangijin safiya.
2. (Ya tsare ni) daga sharrin abinda ya halitta.
3. Da kuma sharrin dare idan ya yi duhu.
4. Da kuma sharrin masu tofi akuduri (a kulli).
5. Da kuma sharrin mai hasada idan ya yi hasada.
        (Suratul Falak, aya ta: 1-5).

 

سورة الناس
ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﮀ  ﮁ   ﮂ  ﮃ  ﮄ  ﮅ  ﮆ  ﮇ  ﮈ   ﮉ  ﮊ  ﮋ  ﮌ  ﮍ  ﮎ  ﮏ  ﮐ   ﮑ  ﮒ  ﮓ  ﮔ  ﮕ   ﮖ  ﮗ  ﮘ  ﮙ   ﭼ الناس: ١ – ٦
Ma’ana: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin kai.
1. Ka ce; Ina neman tsari daga Ubangijin mutane.
2. Mamallakin mutane.
3. Abin bautar mutane.
4. (Ya tsare ni) daga sharrin maiwaswasi alkhannas.
5. Wanda yake waswasi a zukatan mutane.
6. Daga cikin aljanu yake da kuma mutane.
  (Suratun Nas, aya ta: 1-6).
 أصبحنا وأصبح الملك لله و الحمد لله، لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير، رب أسألك خير ما في هذا اليوم وخير ما بعده، وأعوذ بك من شر ما في هذا اليوم وشر مابعده، رب أعوذ بك من الكسل، وسوء الكبر، رب أعوذ بك من عذاب في النار وعذاب في القبر".
Ma’ana: Mun wayi gari, kuma mulki ya wayi gari yana mai tabbata ga Allah, dukkan yabo ya tabbata ga Allah babu abin bauta da cancanta sai shi, shi kadai ba shi da abokin tarayya agare shi, mulki na sane kuma yabo na sane kuma shi akan komai mai iko ne. Ya Ubangiji ina rokonka alherin da ke cikin wannan ranar, kuma da alherin dake bayan ta, kuma ina neman tsarinka daga sharrin dake cikin wannan ranar da sharrin dake bayan ta. Ubangiji ina neman tsarinka da ka kareni daga kasala da kuma mumunan tsufa.Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga azabar wuta da kuma azabar kabari.
  Idan kuma da maraice ne sai ya ce:
أمسينا وأمسى الملك لله والحمد لله، لا إله الا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير، رب أسألك خير ما في هذه الليلة وخير ما بعدها، وأعوذ بك من شر ما في هذه الليلة وشر ما بعدها، رب أعوذ بك من الكسل، وسوء الكبر، رب أعوذ بك من عذاب في القبر وعذاب في النار.
Ma’ana: Mun kai yammaci, kuma mulki ma ya kai yammaci ya na tabbata ga Allah, babu abin bautawa da cancanta sai shi kadai ba shi da abokin tarayya agare shi, mulki na sane kuma yabo ma nasa ne, kuma shi akan dukkan komai mai iko ne,Ya Ubangiji ina rokonka alherin dake cikin wannan dare da kuma alherin da ke bayan shi,Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga sharrin dake cikin wannan dare da abin da ke bayanta, Ya Ubangiji ina neman tsarinka da ka kareni daga kasala da kuma mumunan tsufa.Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga azabar wuta da azabar kabari.   
Idan kuma da maraice ne sai yace
اللهم بك أصبحنا وبك أمسنا، وبك نحيا وبك نموت وإليك النشور.
Ma’ana: Ya Allah, da ikonka ne muka wayi gari kuma da ikonka ne muke shiga maraice, kuma da ikonka ne muke mutuwa kuma gare ka ne taruwa.  Wanna idan aka wayi gari kenen.
اللهم بك أمسينا وبك أصبحنا، وبك نحيا وبك نموت وإليك المصير.
Ma’ana: Ya Allah, da ikonka ne muka kai yamma, kuma da ikonka ne, kuma da ikon ka ne muka wayi gari, kuma da ikonka ne muke muke mutuwa kuma gare ka makoma take.  Wanna idan yamma ta yi kenen.
اللهم أنت ربى لا إله إلا أنت، خلقتني وأنا عبدك وأنا على عهدك ووعدك ما استطعت، أعوذ بك من شر ما صنعت، أبو لك بنعمتك علي، وأبوء بذنبى فاغفرلى فإنه لا يغفر الذنوب إلا أنت .
Ma’ana: Ya Allah kai ne Ubangiji na, babu abin bautawa da cancanta sai kai, ka hallice ni kuma ni bawanka ne, kuma ina kan alkawarin da na yi maka da kuma alkawarin ka gwargwadon iko na, ina neman tsarin ka daga sharrin abin da na aikata ina tabbatar da ni’imarka gare ni, kuma ina tabbatar da zunubi na, ka gafarta mini domin ba wanda yake gafarta zunubi sai kai.
اللهم إنى أصبحت أشهدك وأشهد حملة عرشك وملائكتك وجميع خلقك، أنك أنت الله لا إله إلا أنت وحدك لا شريك لك وأن محمدا عبدك ورسولك. (أربع مرات).                                     Ma'ana: Ya Allah! Ni na wayi gari ina shaida maka, kuma ina shaida wa mala'uku masu dauke da al'afshinka da mala’ikunka, da dukkan halitarka cewa: Kai ne Allah babu abin bautawa da cancanta sai kai, kai kadai kake baaka da abonkin tarayya, kuma hakika (Annabi Muhammad) bawanka ne kuma manzonka ne. (Sau hudu:4).        
"اللهم ما أصبح بى من نعمة أو بأحد من خلقك فمنك وحدك لا شريك لك، فلك الحمد ولك الشكر".
Ma'ana: Allah! Dukkan abin da ya wayi gari nawa na daga ni’ima, ko ga wani daga cikin halattar ka, to daga gare ka ne, kai kadai babu abokin tarayya a gareka, kuma yabo ya tabbata a gareka, kuma godiya ta tabbata a gare ka.   
"اللهم عافني في بدنى، اللهم عافنى فى سمعى، اللهم عافني في بصري، اللهم إني أعوذ بك من الكفر والفقر، وأعوذ بك من عذاب القبر، لا إله إلا أنت". (ثلاث مرات).                 
Ma’ana: Ya Allah! Ka bani lafiya a jiki na, Ya Allah! ka bani lafiya a ji na, Ya Allah! Ka bani lafiya a gani na. Ya Allah Ubangiji lalle ni ina neman ka tsare ni daga kafirci da kuma talauci. Kuma ina neman tsarinka daga azabar kabari, babu abin bautawa da cancanta sai kai, (San uku::3).
حسبي الله لا إله إلا هو، عليه توكلت وهو رب العرش العظيم". (سبع مرات).
Ma'ana: Allah ya ishe ni, babu abin bautawa da cancanta sai shi, gare shi kadai na dogara, shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma. (Sau bakwai:7).
اللهم إنى أسألك العفو والعافية فى الدنيا والآخرة، اللهم إني أسألك العفو والعافية: في ديني ودنياي وأهلى ومالى، اللهم استر عوراتى، وآمن روعاتى، اللهم احفظنى من بين يدي، ومن خلفي، وعن يمينى وعن شمالى، ومن فوقي، وأعوذ بعظمتك أن أغتال من تحتي.
Ma’ana: Ya Allah ina rokonka afuwa da aminci a duniya da lahira, Ya Allah ina rokonka afuwa da aminci daga dukkan mummuna a addinina da duniya ta da iyal ina da dukiya ta. Ya Allah ka kiyaye ni ta gaba na da kuma ta bayana, da ta damana da kuma ta haguna, da kuma ta sama na. Ya Allah ina neman tsarinka da girmanka da a kisfe ni kasa da ni.
اللهم عالم الغيب والشهادة فاطر السموات والأرض، رب كل شىء ومليكه، أشهد أن لا إله إلا أنت، أعوذ بك من شر نفسي، ومن شر الشطاني وشركه، وأن أقترف على نفسى سوءا، أو أجره إلى مسلم.
Ma’ana: Ya Allah masanin abunda ke boye da na bayyane, mai kaga halittar sammai da kasa Ubangijin komai kuma mamallakinsa, ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai kai, kai kadai ina neman tsarinka daga sharrin rai na da kuma sharrin shaidan da shirkansa, da in daukar wa kai ne wani abu mummuna, ko in jawo shi ga wari musulmi.
    بسم الله الذى لا يضر مع اسمه شيء في الأرض ولا فى السماء وهو السميع العليم. (ثلاث مرات).
Ma’ana: Da sunan Allah wanda da sunansa wani abu ba zai cutar da wani ba a sama ko a kasa, kuma shi mai jine masani. (Sau Uku:3 ).
رضيت بالله ربا وبالإسلام دينا وبحمد صلى الله عليه وسلم نييا.      ( ثلاث م).
Ma’ana: Na yarda da Allah shi ne Ubangiji, da kuma musulunci shi ne addini, da kuma Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Annabi ne. (Sau Uku:3 ).
يا حي يا قيوم برحمتك أستغيث، أصلح لي شأني كله، ولا تكلنى إلى نفسى طرفة عين .
Ma’ana: Ya (Allah) rayayye, mai tsayuwa da (kansa, wanda komai ya tsayu da shi) da rahamarka na ke neman agaji, ka kyautata mini sha’ani na dukkaninsa, kada ka kyale ni ko da daidai da kyaffawar ido ne .
أصبحنا وأصبح الملك لله رب العالمين، اللهم إنى أسألك خير هذا اليوم، فتحه، ونصره، ونوره، وبركته، وهداه، وأعوذبك من شر ما فيه وشر ما بعده.
Ma’ana: Mun wayi gari kuma mulki ya wayi gari yana mai tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Ya Allah ina rokonka alherin wannan rana, budinta da nasanar ta da haskenta da albarkarta, da kuma shiryarta, kuma ina neman tsarinka daga sharrin abin da ke cikinta, da abin da ke bayanta.
 Da yamma kuma sai ya ce:
أمسينا وأمسى الملك لله رب العالمين، اللهم إنى أسألك خير هذه الليلة، فتحها، ونصرها، ونورها، وبركتها، وهداها، وأعوذبك من شر ما فيها وشر ما بعدها.
Ma’ana: Mun kai yammaci kuma mulki ya kai yammaci yana mai tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Ya Allah ina rokonka alherin wannan dare, budin shi da nasanar shi da hasken shi da albarkar shi, da kuma shiryar shi, kuma ina neman tsarinka daga sharrin abin da ke cikin shi, da abin da ke bayan shi.
أصبحنا على فطرة الإسلام وعلى كلمة الإخلاص، وعلى دين نبينا محمد صلى الله عليه وسلم، وعلى مله أبينا إبراهيم حنيفا مسلما وما كان من المشركين .            
Ma’ana: Mun wayi gari akan halittar da Allah ya yi mana ta musulunci, kuma akan kalmar tauhidi, kuma a kan addinin Annabin mu Muhammad – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma akan addinin baban mu Ibrahim mai kaucewa dukkan shirka zuwa ga addinin gaskiya mikakken kuma musulmi, bait aba kasancewa daga cikin mushrikai ba.
"سبحان الله وبحمده". (مائة مرة).
Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga Allah da kuma goliyar sa. (Sau dari: 100).
"لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد، وهو على كل شئ قدير".  
(عشر مرات: 10). أو (مرة واحدة عند السكل).
Ma'ana: Babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai yake babu da abokin tarayya a gare shi, mulki nasa ne shi kadai, yabo ma nasa ne shi kadai, kuma shi mai ikone akan komai. (San dari:100, ko sau daya, idan akwai kasala).
سبحان الله وبحمده عدد خلقه، ورضا نفسه، وزنة عرشه، ومداد كلمته". (ثلاث مرات إذ أصبح).
Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da yabo a gare shi iya adadin halittar sa, da gwargwadon yardar kansa, da iya nauyin al'arshinsa, da iya yawan tawadar da zata rubuta kalmominsa.  (Sau Uku :3 da Safe).
اللهم إني أسألك علما نافعا، ورزقا طيبا، وعملا متقبلا.
Ma'ana: Ya Allah! Ina rokonka ilimi mai amfani, da arziki na halal, da aiki karbabbe. (Da safe).
"أستغفر الله وأتوب إليه" (مائه مرة في اليوم).
Ma’ana: Ina neman gafarar Allah kuma ina tuba zuwa gareshi. (Sau dari: 100, a rana).
"أعوذ بكلمات الله التامات من شرما خلق. (ثلاث مرات إذا أمسى).
Ma'ana: ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin dukkan abin da ya halitta. (Sau uku: 3, da yamma).
"اللهم صل وسلم على نبينا محمد".     (عشر مرات).
Ma’ana: Ya Allah ka yi dadin tsira da aminci ga Annabin mu Muhammad. (Sau goma: 10).
أذكار النوم
Ambaton Allah yayin kwanciya bacci.
Idan mutun ya yi nufin kwanciya sai ya hada hannuwansa (biyu) ya karanta wadannan surorin masu zuwa:-

ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﭑ  ﭒ  ﭓ  ﭔ  ﭕ  ﭖ  ﭗ  ﭘ  ﭙ  ﭚ   ﭛ  ﭜ  ﭝ  ﭞ  ﭟ  ﭠ  ﭡ  ﭢ  ﭣ   ﭼ الإخلاص: ١ - ٤.

Ma’ana: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin kai.
1. Ka ce; Shi ne Allah shi kadai.
2. Allah wanda ake nufata da dukkanin bukatu.
3. Bai haifa ba kuma ba’a haifeshi ba.
4. Kuma wani bai kasance kini a gare shi ba.

 

سورة الفلق
ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﭤ  ﭥ  ﭦ  ﭧ  ﭨ  ﭩ  ﭪ   ﭫ  ﭬ  ﭭ  ﭮ   ﭯ  ﭰ  ﭱ  ﭲ  ﭳ  ﭴ  ﭵ  ﭶ  ﭷ   ﭸ  ﭹ  ﭺ  ﭻ     ﭼ  ﭽ  ﭾ  ﭿ   ﭼ الفلق: ١ – ٥
Ma’ana: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin kai.
1. Ka ce; Ina neman tsari daga Ubangijin safiya.
2. (Ya tsare ni) daga sharrin abinda ya halitta.
3. Da kuma sharrin dare idan ya yi duhu.
4. Da kuma sharrin masu tofi akuduri (a kulli).
5. Da kuma sharrin mai hasada idan ya yi hasada.
        (Suratul Falak, aya ta: 1-5).


سورة الناس
ﭑ ﭒ ﭓ
ﭽ ﮀ  ﮁ   ﮂ  ﮃ  ﮄ  ﮅ  ﮆ  ﮇ  ﮈ   ﮉ  ﮊ  ﮋ  ﮌ  ﮍ  ﮎ  ﮏ  ﮐ   ﮑ  ﮒ  ﮓ  ﮔ  ﮕ   ﮖ  ﮗ  ﮘ  ﮙ   ﭼ الناس: ١ – ٦
Ma’ana: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin kai.
1. Ka ce; Ina neman tsari daga Ubangijin mutane.
2. Mamallakin mutane.
3. Abin bautar mutane.
4. (Ya tsare ni) daga sharrin maiwaswasi alkhannas.
5. Wanda yake waswasi a zukatan mutane.
6. Daga cikin aljanu yake da kuma mutane.
  (Suratun Nas, aya ta: 1-6).
      Sannan ya shafa su iya inda zai iya na jikinsa, yana farawa da kansa, da fuskarsa da kuma gaban jikin sa yayi haka har sau uku.
ءاية الكرسي. Ayatul kursiyy.
ﭽ ﮣ  ﮤ  ﮥ  ﮦ   ﮧ   ﮨ  ﮩﮪ  ﮫ  ﮬ  ﮭ  ﮮ  ﮯﮰ  ﮱ  ﯓ  ﯔ  ﯕ  ﯖ     ﯗ  ﯘﯙ  ﯚ  ﯛ  ﯜ  ﯝ  ﯞ  ﯟ   ﯠﯡ  ﯢ  ﯣ  ﯤ   ﯥ  ﯦ  ﯧﯨ  ﯩ  ﯪ  ﯫ  ﯬ  ﯭ  ﯮ    ﯯ    ﯰﯱ  ﯲ  ﯳ           ﯴ  ﯵﯶ  ﯷ     ﯸ     ﯹﯺ   ﯻ  ﯼ   ﯽ  ﯾ  ﭼ البقرة: ٢٥٥

Ma’ana: “Allah, babu wani abin bautawa da cancanta sai shi, Rayayye, mai tsayuwa da komai, gyangyadi ba ya kamashi kuma macci baya kamashi, shi ke da abinda ya ke cikin sammai da abinda ke cikin kassai, wanene yake yin ceto awurinsa sai dai da izininsa? Yana sane da abinda yake gaban su da abinda ke bayan su, kuma ba su kewayewa da komai daga ilimi sa, saidai da abinda ya so, Kursiyin sa ya yalwaci sammai da kassai, Kuma shi ne madaukaki mai girma”. Suratul Bakara, aya ta: 255.

آمن الرسول
ﭽ ﮗ  ﮘ  ﮙ  ﮚ   ﮛ   ﮜ  ﮝ  ﮞﮟ  ﮠ      ﮡ  ﮢ  ﮣ  ﮤ   ﮥ  ﮦ  ﮧ  ﮨ  ﮩ  ﮪ  ﮫﮬ  ﮭ  ﮮ   ﮯﮰ  ﮱ  ﯓ  ﯔ  ﯕ  ﯖ  ﯗ  ﯘ   ﯙ  ﯚ  ﯛ  ﯜﯝ  ﯞ  ﯟ  ﯠ  ﯡ  ﯢ  ﯣﯤ   ﯥ  ﯦ  ﯧ  ﯨ    ﯩ  ﯪ  ﯫﯬ  ﯭ  ﯮ  ﯯ   ﯰ   ﯱ  ﯲ    ﯳ    ﯴ  ﯵ  ﯶ  ﯷﯸ  ﯹ  ﯺ   ﯻ  ﯼ  ﯽ    ﯾ  ﯿ  ﰀﰁ  ﰂ  ﰃ  ﰄ   ﰅ  ﰆﰇ   ﰈ  ﰉ  ﰊ  ﰋ  ﰌ  ﰍ  ﰎ   ﭼ البقرة: ٢٨٥ – ٢٨٦
Ma’ana: Manzon ya yi Imani da abinda aka saukar zuwa gareshi daga wurin Ubangijinshi, duk sun yi Imani da Allah da mala’ikunsa da littattafansa da kuma Manzanninsa, ba ma rarrabewa da wani cikin Manzanninsa (ware wani), kuma suka ce; mun ji kuma mun bi, (neman) gafararka ( muke yi Ya) Ubangijin mu, kuma gareka makoma take. Allah bai dorawa wata rai sai abinda zata iya, kuma duk abinda ta yin a alheri na ta ne, kuma dai yana kanta duk abinda ta yin a laifi, (Ya) Allah Ubangijin mu kada ka kama mu idan muka yi mantuwa ko kuma muka yi kuskure, (Ya) Ubangijin mu kuma kada ka dora mana nauyi kamar yadda ka dorashi ga wadanda suka zo kafin mu. (Ya) Ubangijin mu kuma kada ka dora mana abinda ba za mu iyaba, ka yi mana afuwa kuma ga gafarta man aka yi mana rahama, kai ne majibincin mu, ka tai make mu akan dukkanin kafirai.
 "باسمك (الله) ربى وضعت جنبى، وبك أرفعه، فإن أمسكت نفسى فارحمها، وإن أرسلتها فاحفظها بما تحفظ به عبادك الصالحين".
Ma'ana: Da sunanka Ya (Allah) Ubangijina kwanta kuma da izinika ne nake tashi, in ka rike raina (da mutuwa) to kaji kanta, in ka sake ta kuwa to ka kiyaye ta da abin da kake kiyaye bayin ka na kwarai.
اللهم إنك خلقت نفسى وأنت توفاها، لك مماتها ومحياها، إن أحييتها فاحفظها، وإن أمتها فاغفر لها، اللهم إنى أسألك العافية.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Lalle kai ne ka halicci rai na, kuma kai ne kake karbarta, mutuwarta gareka take haka kuma rayuwarka, in ka rayar da ita to ka kiyayeta, idan kuma ka dauketa to ka gafarta mata. Ya Allah lalle ni ina rokonka lafiya.
اللهم قني عذابك يوم تبعث عبادك.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji ka tsareni azabarka ranar da kake tashin bayinka.
بسمك اللهم أموت وأحيا
Ma’ana: Da sunanka Ya Ubangiji nake mutuwa (bacci) kuma nake rayuwa (tashi daga bacci).
سبحان الله، (33). والحمد لله، (33). والله أكبر، (34).
Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga Allah, (33). Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, (33). Allah mai girma, (34).
اللهم رب السماوات السبع ورب الأرض، ورب العرش العظيم، ربنا ورب كل شيء، فالق الحب والنوى، ومنزل التوراة والإنجيل والفرقان، أعوذ بك من شر كل شيء أنت آخذ بناصيته. اللهم أنت الأول فليس قبلك شيء، وأنت الآخر فليس بعدك شيء، وأنت الظاهر فليس فوقك شيء، وأنت الباطن فليس دونك شيء، اقض عنا الدين وأغننا من الفقر.
Ma'ana: Ya Allah Ubangijin sammai da kassai bakwai, Ubangijin al'arshi mai girma, Ubangiljin mu kuma Ubangijin komai, mai tsaga kwayar komayya da kwallon dabino, mai saukar da Attaura da Injila da Al'furkan.! Ina neman tsarinka daga sharrin komai wanda kai ne mai rike da makwarkwadarsa. Ya Allah Ubangiji! Kai ne na farko babu wani abu kafin kai, kai ne na karshe kuma babu wani abu bayanka, kai ne bayayya nan ne haka kuma babu wani abu da yake sama da kai, kai ne fa buyayye wanda babu wani abu da yake boyuwa gareka, ka biya mana basussuka, kuma ka wadatar da mu daga talauci.
"الحمد لله الذى أطعمَنَا وَسقَانَا، وكفَانَا وآوَانَا، فَكَم ْمِمَّنْ لاَ كافىَ لَه ولاَ مُؤوي".
Ma'ana: Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ciyar da mu, ya shayar da mu ya kuma tsare mu, ya ba mu makwanci, da yawa wanda ba shi da mai tsareshi kuma ba shi da mai ba shi makwanci.
اللهم عالم الغيب والشهادة فاطر السموات والأرص، رب كل شيء ومليكه، أشهد أن لا إله إلا أنت، أعوذبك من شر نفسي، ومن شر الشيطان وشركه، وأن أقترف على نفسى سوء أو أجره إلى مسلم.
Ma'ana: Ya Allah! Masanin abin da ke fake da na sarari, mai kagen halittar sammai da kasai! Ubangijin komai kuma mamallakin sa!. Ina shaidawa da babu abin bautawa da cancanta sa kai, ina neman tsaraika daga sharrin kai na, da kuma sharrin shaidan da shirkansa da ya tsare ni daga wani abu mumuna, ko in jawo shi ga wani musulmi.
"يقرآ "الم" تنزيل السجدة، وتبارك الذى بيده الملك".
Ma’ana: Sai kuma ya karanta suratus Sajada, da kuma Tabarah.
اللهم أسلمت نفسى إليك، وفوضت أمرى إليك، ووجهت وجهى إليك، وألجأت ظهرى إليك رغبة ورهبة إليك، لا ملجأ ولا منجا منك إلا إليك، آمنت بكتابك الذى أنزلت وبنبيك الذى أرسلت.
Ma'ana: Ya Allah! Na sallama raina gare ka, na maida al'amarina a gareka, na fuskanfar da fuskata gare ka, na dogar da gadon baya na a gareka, sabonda kwadayin abun da ke gareka da tsoronka, kuma babu mafaka babu matsera daga gareka sai fa zuwa gare ka. Na yi imani da littafinka da ka saukar da kuma Annabin ka da ka aiko.


((الدعاء إذا تقلبتَ ليلا)).
Addu'a yayin da ka/ki juya a cikin kwanciyar bacci.
لا إله إلا الله الواحد القهار، رب السموات والأرض وما بينهما العزيز الغفار".
Ma'ana: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, makadaici, marinjayi, Ubangijin sammai da kasa da duk abin da ke tsakaninsu, mabuwayi mai yawan gafara.

دعاء الفزع فى النوم ومن بلي بالوحشة
Addu'ar wanda yake razana (firgici) a cikin bacci da wanda ya kasa bacci.
"أعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وعقابه وشر عباده، ومن همزات الشياطين وأن يحضرون".
Ma'ana: Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku dagaa fushinsa da azabar sa da sharrin bayinsa da kuma wasuwasin shaidanu, da kada su zo mini.
ما يفعل من رأى الرؤيا أو الحلم.
Abinda wanda ya yi mummuna mafarki zai fada ko ya aikata.
"ينفث عن يساره.   (ثلاث)."Sai ya yi tofi a gafen sa na hagu"                             
يستعيذ بالله من الشيطان ومن شر ما رأى".   (ثلاث مرات).
"Sai ya nemi tsarin Allah daga shanrin shaidan da kuma sharrin abunda ya gani.  ( zai yi hakan sau uku).
"لا يحدث بها أحدا""Kuma kada ya gaya wa kowa irin mafarkin da ya yi "        .
"يتحول عن جنبه الذى كان عليه".
Ya juya daga gefan da ya kasance yana kwance a kanse
"يقوم يصلى إن أراد ذلك".
Ya tashi ya yi sallah idan ya ga daman hakan.
دعاء القنوت Addu'ar kunutir witiri.    
اللهم هدانى فيمن هديت، وعافنى فيمن عافيت، وتولني فيمن توليت، وبارك لى فيما أعطيت، وقنى شر ما قضيت، وإنك تقضي ولا يقضى عليك، إنه لا يذل من والَيت، (ولا يعز عاديت)، تباركت ربنا وتعاليت. اللهم إنى أعوذ برضاك من سخطك، ومعافاتك من عقوبتك، وأعوذ بك منك، لا أحصى ثناء عليك أنت كما أثنيت على نفسك".
    اللهم إياك نعبد، ولك نصلى ونسجد، وإليك نسعى ونحفد، نرجو رحمتك، ونخشى عذابك إن عذابك بالكافرين ملحق. اللهم إنا نستعينك ونستغفرك ونثنى عليك الخير، ولا نكفرك ونؤمن بك، ونخضع لك، ونخلع من يكفرك.
Ma'ana: Ya Allah! Ka shiryarda ni cikin wadanda ka shiryar, ka amintar da ni daga mummuna ayyuka cikin wadanda ka yi wa aminci daga mummunan ayyuka, ka jibinci al’amarina cikin wadanda ka jibinci al'amarin su, ka sanya min albarka a cikin abun da ka bani, ka kare ni  daga sharrin abin da ka kaddara, domin kai ne kake hukunci babu wanda ya ke hukunci akanka. Tabbas wanda ka jibince shi to ba zai wulakanta ba, wanda kuma ka ki shi ba zai daukaka ba. Alherinka sun yawaita, ya Ubangijin mu! Ka kuma ka daukaka.
    Ya Allah! Ina neman tsarin ka da yardarka daga fushinka, da kuma ramgwamenka daga azabarka, kuma ina neman tsarinka da kai daga gareka, ban isa in tuke ga yabon da ya cancanta a gare ka ba, kamar yadda ka yabi kanka ba.
    Ya Allah! Kai kadai muke bautawa, kuma gare ka kadai muke sallah muke sujjadah, kuma gare ka kadai muke kokari muke gaugawa wajen aiki, muna kaunar rahmarka, kuma muna jin tsoron azabarka, lalle azabarka mai riskar kafirar ce.
    Ya Allah! Muna neman taimakonka kuma muna neman gafararka, kuma muna yabon alheri a gare ka, ba ma kafirce maka, kuma muna imani da kai, muna kankan da kai gare ka, kuma muna yarfe wanda yake kafir ce maka.
الذكر عقب السلام من الوتر.
Zikiri bayan sallamewa daga wutiri.
"سبحان الملك القدوس" (ثلاث مرات).
والثالثة يجهربها ويمدبها صوتة بقول : ((رب الملائكة والروح)).
Ma'ana: Tsarki ya tabbata ga mai cikken mulki, mai wanda ya tsarkaka (daga dukkan abin da bai dace da shi ba). Ya karanta sau uku, a na ukun sai ya daga muryarsa yana cewa Ubangijin mala'iku da ar-rah watoJibril.

دعاء الهم والحزن.
Addau'ar maganin damuwa da bakin ciki.
اللهم إنى عبدك ابن عبد ابن أمتك، ناصيتي بيدك، ماض في حكمك، عدل في قصاءك، أسألك بكل اسم هو لك، سميت به نفسك، أو أنزلته فى كتابك، أو علمته أحدا من خلقك، أو استأثرت به فى علم الغيب عندك، أن تجعل القرآن ربيع قلبى، ونور صدري، وجلاء حزنى، وذهاب همي، اللهم إنى أعوذ بك من الهم والحزن، والعجز والكسل، والبخل والجبن، وضلح الدين وغلبة الرجال.
Ma’ana: Ya Allah! Ni bawanka ne, kuma dan bawanka, kuma dan baiwarka, makwarkwada ta a hannuka take, hukuncinka zartacce ne a kai na, kuma kaddararka a gare ni adalci ce. Ina rokonka da kowanne suna da yake naka, wanda ka ambaci kanka da shi, ko ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka sanar da wani daga cikin halittarka, ko ka kebance kanka da shi a cikin ilimin gaibi da ke wurin ka da ka sanya Alkar’ani ya zama kaka ga zaciyata, da haske ga kirjina da kwaranyewar bakin ciki na, da kuma mai tafiyar da damuwata.
  Ya Allah lalle ni ina neman tsarinka daga damuwa da bakin ciki da gajiyawa da lalaci da rowa da ragwantaka da nauyin bashi da rinjayar makiya.
دعاء الكرب
Addu’ar tafiyar da kunci zuciya.
لا إله إلا الله العظيم الحليم،  لا إله إلا الله رب العرش العظيم،  لا إله إلا الله رب السموات ورب الأرض ورب العرش الكريم.
Ma’ana: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah mai girma mai hakuri, babu abin bautawa da cancanta sai Allah Ubangijin al’arshi mai girma, babu abin bautawa da cancanta sai Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kassai kuma Ubangijin a’larshi mai yawan baiwa.  
اللهم رحمتك أرجو فلا تكلنى إلى نفسى طرفة عين وأصلح لى شأنى كله لا إله إلا أنت.
Ma’ana: Ya Allah rahamarka nake kauna, saboda haka karka kyale ni da kaina ko da da kyaffawar ido ne, kuma ka kyautata mini sha’anina dukkansa, babu abin bautawa da cancanta sai kai.
لا إله إلا أنت سبحانك إنى كنت من الظالمين.
Ma’ana: Babu abin bautawa da cancanta sai kai tsarki ya tabbata a gareka lalle ni na kasance daga cikin azzalumai.
اللهُ اللهُ ربى لا أشرك به شيئا.
Ma’ana: Allah Allah ne Ubangijina bana yin tarayya da shi da wani abu acikin bauta.
دعاء لقاء العدو وذي السطان.
Addua'ar haduwa da abokan gaba ko wani mai mulki.
اللهم إنا نجعلك فى نحورهم ونعوذ بك من شررهم.
Ma'ana: Ya Allah mu muna sanyaka agabansu kuma muna neman tsarin ka daga sharrance- sharrancen su.
اللهم أنت عضدى، وأنت نصيرى، بك أعول وبك أصول، وبك أقاتل.
Ma'ana: Ya Allah kai ne mai karfafa ni, kuma kai ne mataimakina da karfinka ne na ke yin dabarun yaki, kuma da karfinka ne nake kai hari, kuma da karfinka ne nake yin yaki.
حسبنا الله ونعم الوكيل.
Ma'ana: Allah ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro.
دعاء من خاف ظلم السلطان.
Adda'ar wanda ya ji tsoron zalunci wani mai mulki.
اللهم رب السموات السبع، ورب العرش العظيم، كن لى جارا من فلان بن فلان، وأحزابه من خلائقك، أن يفرط على أحد منهم أو يطغى، عزَّ جارك، وجل ثناءك، لا إله إلا أنت.
Ma'ana: Ya Allah! Ubangiji sammai bakwai, kuma Ubangijin al'arshi mai girma, ka kasance mai tsare ni daga wane dan wane da dukkan rundunarsa daga cikin haluttanka kar wani daga cikin su ya yi gaggawar azaba a gare ni, ko ya ketare iyaka akaina, kariyarka ta buwaya, kuma yabonka ya girmama, kuma babu abin bautawa da cancanta sai kai.
الله أكبر، الله أعزُّ من خلقه جميعا، الله أعزُّ مما أخاف وأحذر، أعوذ بالله الذي لا إله الا هو، الممسك السموات السبع أن يقعْنَ على الأرض إلا بإذنه، من شر عبدك فلان، وجنوده وأتباعه وأشياعه، من الجن والإنس، اللهم كن لي جارا من شرهم، جل ثناءك وعز جارك، وتبارك اسمك ولا إله غيرك. (ثلاث مرات).
Ma'ana: Allah shi ne mafi girma, Allah shi ne mafi buwaya daga dukkanin halittarsa, Allah shi ne mafi buwaya daga abinda nake jin tsronsa, kuma ina neman tsarin Allah wanda babu abin bautawa da cancanta sai shi, mai rike da sammai bakwai don kada su fada a kasa sai da izininsa, daga sharrin (wane sai ya ambaci sunansa), da randunarsa da mabiyansa, da kungiyoyinsa na aljanu da mutane. Ya Allah! Ka zamo mai tsareni ni daga sharrinsu, yabonka ya girmama, kuma kariyarka ta buwaya, kuma alherin sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da cancanta sai kai. (Sau Uku: 3).

الدعاء على العدو.
Addu’aka akan makiya.
اللهم منزل الكتاب، سريع الحساب، اهزم الأحزاب، اللهم اهزمهم وزلزلهم.
Ma'ana: Ya Allah! Mai saukar da littafi, mai saurin sakamako! Ka rinjayi kungiyoyin abokan gaba. Ya Allah! Ka rinjayesu, ka kuma girgiza su.
ما يقول من خاف قوما.
Abinda zai fada alokacin da ya ke jin tsoron wasu mutane.
اللهم اكفنيهم بما شئت.
Ya Allah! Ka isar mini su da duk abinda kaso.
دعاء من أصابه شك فى الإيمان.
Addu'ar wanda ya sami shakka game da imanin sa.
يستعيذ باللهMa'ana: Ya nemi tsari da Allah.                                                .
ينتهى عما شك فيه.                  . Ma’ana:Ya bar abin da yake sa shi shakkar
آمنت بالله ورسله.
Ma’ana: Na yi imani da Allah da manzanninsa.                     
Sai kuma ya karanta:
ﭽ ﯴ    ﯵ  ﯶ  ﯷ  ﯸﯹ  ﯺ  ﯻ  ﯼ  ﯽ  ﯾ   ﭼ
 الحديد: ٣
 Ma'ana: Shi ne na fark, shi ne kuma na karshe, shi ne bayyananne, shi ne boyayye, kuma shi masani ne akan komai.
دعاء قضاء الدين.
Addu'ar biyan bashin wanda ake bi.
اللهم اكفني بحلالك عن حرامك، وأغنني بفضلك عمن سواك.
Ma'ana: YaAllah ka wadatar da ni da abin da ka halatta ga barin abin da ka haramta, kuma ka wadatar da ni da falalarka ga barin waninka.
اللهم إنى أعوذ بك من الهم والحزن، والعجر والكسل والبخل والجبن، وضلع الدين وغلبة الرجال.
Ma'ana: Ya Allah! Ina neman tsarinka daga kunci, da bakin ciki da kasawa, da lalaci da rowa da tsoro, da nauyin bashi, da rinjayen makiya.
دعاء الوسوسة فى الصلاة  والقراءة.
Addu'ar wanda ya fitinu da wasuwasi a cikin sallah da karatu.
أعوذ بالله من الشيطان الرجيم
Ma'ana: Ina neman tsarin Allah daga shaidan tsinan ne.
وتفل على يسارك ((ثلاثا)).Sai ya  tofa a genfensa na hagu. (Sau Uku:3).             
دعاء من اسصعت عليه أمر.
Addu'a ga mutumin al'amari ya yi masa tsauri.
اللهم لا سهل إلا ما جعلته سهلا وأنت تجعل الحزْنَ إذا شئت سهلا.
Ma'ana: Ya Allah! Babu wani abu wani sauki sai abinda ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma kai kana sauya tsanani idan ka so ya zama sauki.
ما يقول ويفعل من أذنب ذنبا.
Abinda wanda ya aikata zubi zai fada kuma ya aikata
Babu wani bawa (mutum) da zai aikata wani zunubi sannan ya kyautata alwalarsa, ya tashi ya yi sallah raka’a biyu sannan ya nemi gafarar Allah face sai Allah ya gafarta masa.
دعاء طرد الشيطان ووساوسه.
Neman tsarin Allah daga shedan din, wato fadin:
أعوذ بالله من الشيطان الرجيم
Ma’ana: Ina neman tsarin Allah daga shedan la’ananne.
Sai kuma kiran sallah, da zikirori da kuma karatun Alkur’ani.

الدعاء حينما يقع ما لا يرضاه أو غلب عليه.
Addu’a alkacin da abinda bai so ya faru ko aka yi nasara akansa.
قدَّر الله وما شاء فعل.
Ma’ana: Haka Allah ya kaddara, kuma abinda ya ga dama ya aikata.
تهنئة المولود له وجوابه.
Barka da bada amsa.
بارك الله لك في الموهوب لك، وشكرت الواهب، وبلغ أشده، ورزقت بره. ويرد عليه المهنأ فيقول: بارك الله لك، وبارك عليك، وجزاك الله خيرا، ورزقك الله مثله، وأجزل ثوابك.
Ma’ana: Allah ya sanya maka albarka a baiwar da ya yi maka, kuma ya sa ka gode wa mai kyautar, kuma Allah ya sa ya kai karfinsa, kuma ya azurtaka da biyayyarsa.
Sai shi kuma da aka yi wa barka ya ce:
Allah ya yi maka albarka, ya sanya maka albarka ya kuma saka maka da alheri, kuma Allah ya azurtaka da irinsa, Allah ya bada lada.
ما يعوذ به الأولاد.
Addu’ar da ake yi wa yara.
Ma’aikin Allah  ya kasance yana yi wa Alhasan da Alhusaini addu’ar neman tsari yana cewa:
أعيذكما بكلمات الله التامة من كل شيطان وهامة، ومن كل عين لامة.
Ma’ana: Ina nema muku tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkanin shaidani  da canfecanfe, haka kuma daga dukkanin ido memugun nufi.
الدعاء للمريض في عيادته.
Addu’ar da za’a yi wa mara lafiya.
لا بأس طهور إن شاء الله.
Ma’ana: Karka damu, kankarar zunubine in Allah ya so.
أسأل الله العظيم رب العرش العظيم أن يشفيك (سبع مرات).
Ma’ana: Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin al’arshi mai girma da ya warkar da kai.
فضل عيادة المرض.
Falalar gaida mara lafiya.
Ma’aikin Allah  ya ce:
Idan mutum ya gaida dan’uwansa musulmi da ba shi da lafiya, to ya tafi ne akan hanyar aljanna har ya zauna, idan ya zauna kuma rahama ta lullube shi. Idan da safe ne mala’iku dubu saba’in ne za su yi masa salati har yamma ta yi. Idan kuwa da yamma ne to mala’iku dubu saba’in za su yi masa salati har gari yaw aye.
دعاء المريض الذي يئس من حياته.
Addu’ar mara lafiya da ya fidda ran zai ta shi.
اللهم اغفر لي وارحمني، وألحقني بالرفيق الأعلى.
Ma’ana: Ya Allah ka gafarta mini ka kuma yi mini rahama, ka riskar da ni da tawaga madaukaka.
  Ma’aikin Allah  ya kasance alokacin da ajali ya zo masa yana sanya hannuwansa a ruwa ne sai ya shafe fuskarsa da su, yana cewa:
لا إله إلا الله
Ma’ana: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Lalle mutuwa tana da magagi.
لا إله إلا الله، والله أكبر، لا إله إلا الله وحده، لا إله إلا الله وحده لا شريك له، لا إله إلا الله، له الملك وله الحمد، لا إله إلا الله، ولا حول ولا قوة إلا بالله.
Ma’ana: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah shi ne mai girma, babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake, babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, gareshi kadai mulki yake kuma dukkan godiya ta tabbata a gareshi, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, babu karfi kuma babu dabara sai ga Allah.

تلقين المحتضر.
Yadda za’a cewa mai gargara
من كان آخر كلامه لا إله إلا الله دخل الجنة.
Ma’ana: Dukkan wanda karshen maganarsa ta zama fadina: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah to ya shiga aljanna.
دعاء من أصيب بمصيبة.
Addu’ar wanda masifa ta afka masa.
إنا لله وإنا إليه راجعون، اللهم أجرني في مصيبتي وأخلف لي خيرا منها.
Ma’ana: Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu gareshi za mu koma. Ya Allah Ubangiji! Ka sakanka mini a masifar nan ta wa, ka mayar min da mafi alherinta.

 


الدعاء عند إغماض الميت.
Addu’a alokacin rufe idanun mamaci.
اللهم اغفر لفلان (باسمه)، وارفع درجته في المهديين، واخلفه في عقبه في الغابرين، واغفر لنا وله يا رب العالمين، وافسح له في قبره ونوره له فيه.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka gafartawa wane (sai ka fadi sunan sa), ka daga darajarsa a cikin wadanda aka shiryar, ka maye masa azuriyarsa da ya bari, ka gafarta mana kuma ka gafarta masa Ya Ubangijin talikai, ka yalwata masa a kabarinsa ka haskaka masa shi acikinsa.
الدعاء للميت في الصلاة.
Karatun sallar gawa.
اللهم اغفر له وارحمه، وعافه، واعف عنه، وأكرم نزله، ووسع مدخله، واغسله بالماء والثلج والبرد، ونقه من الخطايا كما نقيت الثوب الأبيض من الدنس، وأبدله دارا خيرا من داره، وأهلا خيرا من أهله، وزوجا خيرا من زوجه، وأدخله الجنة، وأعذه من عذاب القبر عذاب النار.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka gafarta masa ka ji kansa ka yi masa afuwa ka yafe masa ka girmama mazauninsa ka yalwata makwancinsa, ka wanke shi da ruwa da kankara da sanyi, ka tsarkake shi daga kurakurai kamar yadda ka tsaftace tufafi da yake fari daga datti, ka janza masa gida wanda ya fi gidanshi (na nan duniya), da iyalai wadanda suka fi iyalansa, da mata wacce ta fi matarshi, ka shigar da shi aljanna kuma ka tsare shi daga azabar wuta da kuma azabar kabari.
اللهم اغفر لحينا، وميتنا، وشاهدنا، وغائبنا، وصغيرنا وكبيرنا، وذكرنا وأنثانا. اللهم من أحييته منا فأحيه على الإسلام، ومن توفيته منا فتوفه على الإيمان، اللهم لا تحرمنا أجره ولا تضلنا بعده.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka gafartawa rayayyun mu da matattun mu da mahalartan mu da wadanda ba sa nan da kananan mu da manyan mu, da mazan mu da matan mu. Ya Allah Ubangiji! Duk wand aka rayar da shi daga cikin mu to ka rayar da shi akan musulunci, duk kuma wanda ka dauki ranshi daga cikin mu to ka dauki ranshi akan imani. Ya Allah Ubangiji! Kada ka haramta mana ladansa kuma kada ka batar da mu a bayansa.  
اللهم إن فلان بن فلان في ذمتك، وحبل جوارك، فقه من فتنة القبر وعذاب النار، وأنت أهل الوفاء والحق. فاغفر له وارحمه إنك أنت الغفور الرحيم.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Lalle wane dan wane (sai ka fadi sunansa) yana wurinka, kuma yana neman kariyarka, to ka tsare shi daga azabar wuta, kuma kai ne ma’abocin cika alkawari, to ka gafarta masa kuma ka yi masa rahama, lalle kai ne mai yawan gafara mai yawan jinkai.
اللهم عبدك بن أمتك احتاج إلى رحمتك، وأنت غني عن عذابه، إن كان محسنا فزد في إحسانه، وإن كان مسيئا فتجاوز عنه.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Bawanka dan baiwarka ya bukaci rahamarka, kai kuma mawadacine daga barin yi masa azaba, har in ya kasance mai kyautatawa to ka kara masa a kyautatawar ta sa, idan kuma ya kasance mai laifi ne to ka yafe masa.

الدعاء للفرط في الصلاة.
Karatun sallar jana’iza ta karamin yaro.
اللهم أعذه من عذاب القبر.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka tsare shi daga azabar kabari.
وإن قال: idan kuma ya kara da cewa:                                                                   
اللهم اجعله فرطا وذخرا لوالديه، وشفيعا مجابا. اللهم ثقل به موازينهما وأعظم به أجورهما، وألحقه بصالح المؤمنين، واجعله في كفاله إبراهيم، وقه برحمتك عذاب الجحيم، وأبدل دارا خيرا من داره، وأهلا خيرا من أهله، اللهم اغفر لأسلافنا، وأفراطنا، ومن سبقنا بالإيمان.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka sanya shi wata ajiya ce ga mahaifansa, kuma mai ceto, wanda kuma ake amsa masa. Ya Allah Ubangiji ka nauyaya ma’auninsu (su iyayan na shi) sabo da shi, kuma ka girmama ladansu, ka kuma riskar da shi da salihan bayi muminai, ka sanya shi a kulawar (Annabi) Ibrahim, kuma ka tsare shi da rahamarka daga azabar wutar jahim, ka canza masa gida wanda ya fi gidan sa, da iyalai wadanda suka fi iyalansa. Ya Allah Ubangiji! Ka gafarwa magabatan mu da wadanda suka riga mu, da duk wanda ya riga mu imani.
فحسن. To ya yi.                                                        
اللهم اجعله لنا فرطا، وسلفا، وأجرا.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka sanya shi ya zama wata ajiyace a gare mu, kuma wani abu da aka gabatar kuma lada.
دعاء التعزية.
Addu’ar Ta’aziyyah.
إن لله ما أخذ، وله ما أعطى وكل شيء عنده بأجل مسمى... فلتصبر ولتحتسب.
Ma’ana: Lalle na Allah ne duk abinda ya karba, kuma na shi ne duk abinda ya bayar, kuma kowanne abu awurinsa yana da lokaci sananne… ka yi hakuri kuma ka sami lada.
وإن قال: ida kuma ya kara da fadin:                                                              
أعظم الله أجرك، وأحسن عزاءك وغفر لميتك.
Ma’ana: Allah ya girmama ladanka, kuma Allah kara maka hakuri, Allah kuma ya gafarwa mamacinka.
فحسن. To ya yi.                                                   
الدعاء عند إدخال الميت القبر.
Addu’a a lokacin shigar da mamaci kabari.
بسم الله وعلى سنة رسول الله.
Ma’ana: Da sunan Allah, kuma akan sunnar Ma’aikin Allah .
الدعاء بعد دفن الميت
Addu’a bayan binne mamaci.
اللهم اغفر له وثبته.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka gafarta masa, kuma ka tabbatar da shi.

دعاء زيارة القبور.
Addu’ar ziyarar makabarta.
السلام عليكم أهل الديار، من المؤمنين والمسلمين، وإنا إن شاء الله بكم لاحقون ويرحم الله المستقدمين منا والمستأخرين، أسأل الله لنا ولكم العافية.
Ma’ana: Amincin Allah ya tabbata a gareku ma’abotan wannan gida wadanda suke muminai da musulmai, kuma lalle mu in Allah ya so masu riskarku ne, Allah ya jikan wadanda suka gabata daga cikin mu da kuma wadanda suka saura, ina roka mana Allah ya yafe mana mu da ku.
دعاء الريح.
Addu’a idan iska ta taso.
اللهم إني أسألك خيرها، وأعوذ بك من شرها.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Lalle ni ina rokonka alherinta, kuma ina neman tsari daga sharrinta.
اللهم إني أسألك خيرها، وخير ما فيها، وخير ما ارسلت به، وأعوذ بك من شرها، وشر ما فيها، وشر ما أرسلت به.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Lalle ni ina rokonka alherinta da kuma alherin da ke cikinta da kuma alherin da aka aikota da shi. Kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da kuma sharrin da ke cikinta da kuma sharrin da aka aikota da shi.
دعاء الرعد.
Addu’ar tsawa.
سبحان الذي يسبح الرعد بحمده والملائكة من خيفته.
Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga wanda tsawa take masa tasbihi hadi da gode masa da kuma mala’iku saboda tsoronsa.

 


من أدعية الاستسقاء.
Addu’ar sallar rokon ruwa.
اللهم أسقنا غيثا مغيثا مريئا مريعا، نافعا غير ضار، عاجلا غير آجل.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da mu ruwa mawadaci mai dadi, mai kosarwa mai anfani ba mai cutarwaba yanzu ba sai anjima ba.
اللهم أغثنا، اللهم أغثنا، اللهم أغثنا.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da mu, Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da mu, Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da mu.
اللهم اسق عبادك، وبهائمك، وانشر رحمتك، وأحيي بلدك الميت.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da bayinka da dabbobinka, ka watsa rahamarka ka rayar da kasarka wacce ta mutu.

 

الدعاء إذا رأى المطر.
Addu’a idan ya ga ruwan sama.
مطرنا بفضل الله ورحمته.
Ma’ana: An yi mana ruwa da falalar Allah da kuma rahamarsa.
من أدعية الاستصحاء.
Daga cikin addu’o’in markamarka.
اللهم حوالينا ولا علينا. اللهم على الآكام والظراب، وبطون الأودية، ومنابت الشجر.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka juyar mana da shi, kada ya yi mana barna. Ya Allah Ubangiji! A zuba shi akan katangu da magudanu da rafika, da kuma jijiyoyin bishiyoyi.

 


دعاء رؤية الهلال.
Addu’a idan an ga jinjirin wata.
الله أكبر، اللهم أهله علينا بالأمن والإيمان، والسلامة والإسلام، والتوفيق لما تحب ربنا وترضى، ربنا وربك الله.
Ma’ana: Allah mai girma. Ya Allah Ubangiji! Ka nuna mana shi cikin kwanciyar hankali da imani da kuma aminci da musulunci da dacewa da duk abinda kake so kuma ka yarda da shi Ya Ubangijin mu, Ubangijin mu kuma Ubangijinka shi ne Allah.
الدعاء عند إفطار الصائم.
Addu’a idan aka yi buda baki.
ذهب الظمأ وابتلت العروق، وثبت الأجر إن شاء الله.
Ma’ana: Kishi ya tafi, kuma jijiyoyi sun bude, lada kuma ya tabbata da izinin Allah.
اللهم إني أسألك برحمتك التي وسعت كل شيء أن تغفر لي.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Lalle ni ina rokonka da rahamarka wacce ta yalwaci komai da ka gafarta mini.
الدعاء قبل الطعام.
Addu’a kafi a ci abin ci.
Idan dayanku zai ci abinci to ya ce: بسم الله  idan kuma ya manta bai fada ba afarkon cin abincin to ya ce:  بسم الله في أوله وآخره
Duk wanda Allah ya ciyar da shi abin ci to ya ce:
اللهم بارك لنا فيه وأطعمنا خيرا منه.
Duk wanda Allah ya shayar da shin ono to ya ce:
اللهم بارك لنا فيه وزدنا منه.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Ka sanya mana albarka a cikinsa kuma ka kara mana shi.
الدعاء عند الفراغ من الطعام.
Addu’a bayan kammala cin abin ci.
الحمد لله الذي أطعمني هذا، ورزقنيه، من غير حول مني ولا قوة.
Ma’ana: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da ni wannan kuma ya azurta ni shi ba tare da wata dabara ba, kuma ba da karfi ba.
الحمد لله حمدا كثيرا طيبا مباركا فيه، غير مكفي ولا مودع، ولا مستغنى عنه ربنا.
Ma’ana: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah godiya mai yawa tsarkakakka mecike da albarka a ciki ba ta da iyaka kuma ba yankewa, kuma ba mai barin Allah Ubangijin mu.

دعاء الضيف لصاحب الطعام.
Addu’ar bako ga mai abinci.
اللهم بارك لهم فيما رزقتهم، واغفر لهم وارحمهم.
Ma’ana: Ya Allah Ubangijin mu! Ka sanya musu albarka a cikin duk abinda ka azurta su da shi, kuma ka gafarta musu ka yi musu rahama.    
الدعاء لمن سقاه أو أراد ذلك.
Addu’a ga wanda ya shayar da mutum, ko ya nufi hak.
اللهم أطعم من أطعمني، واسق من سقاني.
Ma’ana: Ya Allah ka ciyar da wanda ya ciyar da ni, ka kuma shayar da wanda ya shayar da ni.
الدعاء إذا أفطر عند أهل بيت
Addu’a idan ya yi buda baki a gidan wasu.
أفطر عندكم الصائمون، وأكل طعامكم الأبرار، وصلت عليكم الملائكة.
Ma’ana:  Ya Allah ka azurta su da masu azumi awajen buda baki, kuma ka azurta su da nagargun bayi da su ci abincinsu, kuma Allah ya sa mala’iku su yi muku atddu’a.
دعاء الصائم إذا حضر الطعام ولم يفطر.
Addu’ar: Ga wanda ke azumi idan aka kawo abinci bai ciba.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Idan aka kira dayanku cin abinci to ya amsa kiran, idan kuma yana azumi to ya yi addu’a ga wanda ya gayyace shi, idan kuma baya azumi to ya ci abin cin.
ما يقول الصائم إذا سابه أحد.
Abin da mai azumi zai fada ida wani ya zage shi.
Ya ce: Lalle ni azumi nake yi, kuma ni azumi nake yi”.

الدعاء عند رؤية باكرة الثمرة.
Add’a yayin da aka ga tumu (Hurai- sabon amfanin gona).
اللهم بارك لنا في ثمرنا، وبارك لنا في مدينتنا وبارك لنا في صاعنا، وبارك لنا في مدنا.
Ma’ana: Ya Allah ka sanya mana albarka a cikin ‘ya’yan itatuwan mu, ka albarkace mu a garuruwan mu, ka albarkace mu a kwanan awon mu, ka albarkace mu a mudun awon mu.
دعاء العطاس. Addu’a ga wanda yayi atishawa.  
Idan dayan ku ya yi atishawa to ya ce:
الحمد لله، وليقل له أخوه أو صاحبه: يرحمك الله، فإذا قال له: يرحمك الله، فليقل: يهديكم الله، ويصلح بالكم.
Ma’ana: Annabi tisira da amnici Allah su tabbata agare shi ya ce: ldan dayan ku ya yi atishawa to ya ce: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, dan’uwan sa kuma ko wanda ke zaune kusa da shi sai ya ce ma sa Allah ya yi maka rahama. To idan kuma ya fada masa haka, shi kuma ya ce masa Allah ya shiryar da ku kuma ya kyautata halayenku.
ما يقال للكافر إذا عطس فحمد الله.
Abinda ake cewa kafiri idan ya yi atishawa kuma ya gado wa Allah.
يهديكم الله ويصلح بالكم.
Ma’ana: Allah ya shirye ku, kuma ya kyantata halayenku.
الدعاء للمتزج.
 Addu’a ga wanda ya yi saban aure  
بارك الله لك، وبارك عليك، وجمع بينكما في خير.
Ma’ana: Allah ya sanya albarka agare ka kuma yayi maka albarka kuma ya hada tsakansku da alhairi.

دعاء المتزوج وشراء الدابة.
Addu’a ga wanda ya yi sabon aure ko ya sayi abin hawa.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: Idan dayan ku ya yi auri mace, ko ya sayi mai yi mishi hidima (bawa) to ya ce:
اللهم إني أسلك خيرها وخير ما جبلتها عليه، وأعوذ بك من شرها وشر ما جبلتها عليه.
Ma’ana: Ya Allah lalle ni ina rokonka alherin ta da kuma alherin da ka halicceta akan sa, ina kuma neman tsarinka daga sharrinta da kuma sharrin daka halicceta akan sa.
Idan kuma ya sayi rakumi (wato dukkan abin hawa), to ya rike can samansa sai kuma ya karanta wannan addu’ar.
الدعاء قبل إتيان الزوجة.
 Addu’ar saduwa da iyali.
بسم الله، اللهم جنبني الشيطان وجنب الشيطان ما زرقتنا.
Ma’ana: Da sunan Allah, Ya Allah ka nisantar da ni daga shedan, kuma ka nisantar da shedan abinda ka azurta mu.
دعاء الغضب. Addu’ar fishi.
أعوذ بالله من الشيطان الرجيم.
Ma’ana: Ina neman tsarin Allah daga shedan la’ananne.
دعاء من رأى مبتلى.
Addu’ar wanda ya ga mai cuta.
الحمد لله الذي عافاني مما ابتلاك به وفضلني على كثير ممن خلق تفضيلا.
Ma’ana: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda yay aye mini abinda ya jarrabeka da shi, kuma ya fifita ni akan abubuwa masu yawa da ya halitta fifitawa.
ما يقال في المجلس. Abinda ake fada a majalisi.
عن ابن عمر قال: كان يعد لرسول الله  في المجلس الواحد مائة مرة من قبل أن يقوم: رب اغفر لي وتب علي إنك أنت التواب الغفور.
Ma’ana: Daga Abdullahi dan Umar, Allah ya kara musu yarda, ya kasance yana lissafa (zikirin da) Ma’aikin Allah  a zama guda kafin ya tashi, (yana cewa): Ya Ubangiji ka gafarta mini, ka yafe mini. Lalle kai ne mai karbar tuba kuma mai yawan gafara.
كفارة المجلس. Kaffarar majalisi.
سبحانك اللهم وبحمدك، أشهد أن لا إله أنت، أستغفرك وأتوب إليك.
Ma’ana: Tsarki ya tabbata a gareka ya Allah, hadi da godiya a gareka, ina shaidawa da babu abin bautawa da cancanta sai kai, ina neman gafararka kuma ina tuba zuwa gareka.
الدعاء لمن قال غفر الله لك.
Addu’a ga wanda yace Allah ya gafarta maka.
ولك.  Kai ma haka.

الدعاء لمن صنع إليك معروفا.
Addu’ar wanda ya yi maka kyakkyawan abu.
جزاك الله خيرا. Allah ya saka maka da alheri.
ما يعصم الله به من الدجال.
Abinda Allah yake kare mutum da shi daga jujal.
من حفظ عشر آيات من أول سورة الكهف عصم من الدجال.
Ma’ana: Duk wanda ya kiyaye ayoyi goma na farkon Suratul Kahf, to kan an tsare shi daga jujal.
والاستعاذة بالله من فتنته عقب التشهد الأخير من كل صلاة.
Ma’ana: Yawaita neman tsarin Allah daga fitinan jujal a bayan tahiyar karshe (kafin sallama) a kowacce sallah.
الدعاء لمن قال: إني أحبك في الله.
Addu’a ga dukkan wanda yace ina sonka domin Allah.
أحبك الذي أحببتني له.
Ma’ana: Wanda ka so ni domin shi to ya so ka
الدعاء لمن عرض عليك ماله.
 Addu’a ya bijiromaka da dukiyarsa.
بارك الله لك في أهلك ومالك.
Allah ya sanya maka albarka a iyalanka da kuma dukiyarka.
الدعاء لمن أقرض عند القضاء.
Addu’ar wanda ya dawo da bashi.
بارك الله لك في أهلك ومالك، إنما جزاء السلف الحمد والأداء.
Ma’ana: Allah ya sanya maka albarka a iyalanka da kuma dukiyar, ai sakamakon bashi shi ne godiya da kuma biya.
دعاء الخوف من الشرك. Addu’ar tsoron shirka.
اللهم إني أعوذ بك أن أشرك بك وأنا أعلم، وأستغفرك لما لا أعلم.
Ma’ana: Ya Allah Ubangiji! Lalle ne ni ina neman tsarinka da in yi shirka da kai ina sane, ina kuma neman gafararka ga duk abinda ban sani ba.
الدعاء لمن قال: بارك الله فيك.
Addu’a ga wanda ya ce; Allah ya yi maka albarka.
وفيك بارك الله. Kai ma Allah ya yi maka albarka.   
دعاء كراهية الطيرة. Addu’ar kyamar canfi.
اللهم لا طير إلا طيرك،، ولا خير إلا خيرك، ولا إله غيرك.
Ma’ana: Ya Allah! Babu wani canfi sai fatanka, kuma babu wani alheri sai alherinka, kuma babu wani abin bauta idan ba kai ba.
دعاء الركوب. Addu’ar hawa abinhawa.
بسم الله، الحمد لله، ﭽ ﭶ   ﭷ  ﭸ   ﭹ  ﭺ  ﭻ  ﭼ  ﭽ    ﭾ  ﭿ  ﮀ  ﮁ       ﮂ   ﮃ  ﮄ  ﭼ، الحمد لله، الحمد لله، الحمد لله، الله أكبر، الله أكبر، الله أكبر، سبحانك اللهم إني ظلمت نفسي فاغفر لي، فإنه لا يغفر الذنوب إلا أنت.
Ma’ana: Da sunan Allah dukkan godiya ta tabbata ga Alla. Tsarki ya tabbata ga wanda yah ore mana wannan, kuma ba mu tkasance masu iya rijaya gareshi ba. Kuma lalle mu ga Ubangijin mu hakika masu komawa ne. dukkan godiya ta tabbata ga Allah, dukkan godiya ta tabbata ga Allah,dukkan godiya ta tabbata ga Allah,Allah shi ne mai girma, Allah shi ne mai girma, Allah shi ne mai girma. Tsarki ya tabbata ga reka Ya Allah, lalle ni na zalinci kai na, to ka gafarta mini, lalle fa babu wanda yake gafarta zunubai sai kai.
دعاء السفر.Addu’ar tafiya.       
الله أكبر، الله أكبر، الله أكبر. ﭽ ﭶ   ﭷ  ﭸ   ﭹ  ﭺ  ﭻ  ﭼ  ﭽ    ﭾ  ﭿ  ﮀ  ﮁ       ﮂ   ﮃ  ﮄ  ﭼ اللهم إنا نسألك في سفرنا هذا البر والتقوى، ومن العمل ما ترضى، اللهم هون علينا سفرنا هذا، واطو عنا بعده، اللهم أنت الصاحب في السفر، والخليفة في الأهل، اللهم إني أعوذ بك من وعثاء السفر، وكآبة المنظر، وسوء المنقلب في المال والأهل.
Ma’ana: Allah shi ne mai girma, Allah shi ne mai girma, Allah shi ne mai girma, Tsarki ya tabbata ga wanda yah ore mana wannan, kuma ba mu tkasance masu iya rijaya gareshi ba. Kuma lalle mu ga Ubangijin mu hakika masu komawa ne. Ya Allah lalle mu muna rokonta kyawawan al’amura da tsoronka a wannan tafiya ta mu, kuma muna rokonta aiki wand aka yarda da shi. Ya Allah ka sawwake mana wannan tafiya ta mu, ka nade mana nisanta. Ya Allah kai ne ma’abocin mu a cikin wannan tafiya, kuma kai ne halifan mu a cikin iyalan mu. Ya Allah! Ina neman tsarinka daga wahalar tafiya, da abin gani mai sanya bacin rai, da kuma mumnunar makoma ga iyali da dukiya.
  Idan ya dawo daga tafiyar ta sa, sai kuma ya fadi wannan addu’ar, ya kuma kara da cewa:
((آيبون، تائبون، عابدون، لربنا حامدون)).
Ma’ana: Mu masu komawa ne, masu tuba masu bauta, kuma masu godiya ne ga Ubangijin mu.  
دعاء دخول القرية أو البلد.
Addu’ar shiga alkarya ko wani gari.
اللهد رب السماوات السبع وما أظللن، ورب الأرضين السبع وما أقللن، ورب الشياطين وما أضللن، ورب الرياح وما ذرين. أسألك خير هذه القرية وخير أهلها، وخير ما فيها، وأعوذ بك من شرها، وشر أهلها، وشر ما فيها.
Ma’ana: Ya Allah Ubangijin sammai bakwai da abin da ta rufe ta, kuma Ubangijin kasa bakwai da abin da suke dauke da ita, kuma Ubangijin shaidanu da wadanda suka batar, kuma Ubangijin iska da abin da ya yaye, ina rokon ka alherin wannan alkaya da alherin mutanen da ke cikinta, da alharin abin da ke cikinta. Kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin mutanen ta da sharrin abin da ke cikinta.

دعاء دخول السوق.
Addu’ar shiga kasuwa.
لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد، يحيي ويميت وهو حي لا يموت، بيده الخير، وهو على كل شيء قدير.
Ma’ana: Babu wannin abin bautawa da cancanta sai Allah, mulki da godiya na sane. Yana rayarwa kuma yama kashewa, shi kuma rayyayene ba ya mutuwa, dukkan alheri a hannunsa suke, kuma shi mai iko ne akan komai.
الدعاء إذا تعس المركوب.
Addu’a idan abin hawan mutum ya yi tuntube.
بسم الله Ma’ana: “Da sunan Allah”                                                                .

دعاء المسافر للمقيم.
Addu’ar matafiyi ga mazaunin gida
أستودعكم اللهَ الذي لا تضيعُ ودائعه.
Ma’ana: Ina sanya ku a cikin kiyayewar Allah, wanda abin da aka sa a cikin kiyayewarsa ba ya tozarta.
دعاء المقيم للمسافر.
Addu’ar mazaunin gida ga matafiyi
أستودع الله دينك، وأمانتك، وخواتيم عملك.
Ma’ana: Ina bai wa Allah ajiyar addinin ka da a manarka da kuma ayyukan da ka ke cikawa a kan su.
زودك الله التقوى، وغفر ذنبك، ويسر لك الخير حيث ما كنت.
Ma’ana: Allah ya yi maka guziri da takawa, ya gafarta maka zunubanka, ya saukake alhari a gare ka a duk in da kake.

التكبير والتسبيح في سير السفر.
Yin kabbara da tasbihi yayin da ake cikin tafiya
Jabir   ya ce: Mun kasance idan muka hau tudu a halin tafiya sai mu yi kabbara wato mu ce : الله أكبر  , ma’ana: Allah ne mafigirma. Idan kuma muka zo gangara sai mu yi tasbihi wato mu ce: سبحان الله, Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga Allah.
دعاء المسافر إذا أسحر.
Addu’ar matafiyi idan ya riski dare.
سَمّع سامع بحمد الله، وحسن بلائه علينا. ربنا صاحبنا، وأفضِلْ علينا، عائذا بالله من النار.
Ma’ana: Mai ji ya jiyar da godiyar mu ga Allah, da kyakkyawar ni’imarsa a gare mu. Ya Ubanyiji! Ka kasance tare da mu ka tabbatar da falalarka a gare mu. Muna masu neman tsarin Allah daga wuta.

الدعاء إذا نزل منزلا في سفر أو غيره.
Addu’a idan ya sauka a wani masauki a halin lafiya ko waninta.
أعوذ بكلمات الله التاماتات من شر ما خلق.
Ma’ana: Ina nenan tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da
Ya halita’’.
ذكر الرجوع من السفر.
Ambaton Allah yayin dawowa daga tafiya.
الله أكبر، الله أكبر، الله أكبر. لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك، وله الحمد، وهو على كل شيء قدير. آيبون، تائبون، عابدون، لربنا حامدون، صدق الله وعده، ونصر عبده، وهزم الأحزاب وحده.
Ma’ana: Abdullahi dan Umar, Allah ya kara masa yarda ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah, su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya kama hanyar dawowa daga wurin yaki, ko aikin Hajji, ko Umra, idan ya hau tudu sai ya yi kabbara sau uku sannan ya ce: “Babu abin bautawa da cancanta (da gaskiya) sai Allah, shi, shi kandai yake, ba shi da abokin tarayya, Mulki nasa ne shi kadai, kuma shi mai ikone a kan komai. Mu masu komawa ne, masu tuba ne, masu bauta, kuma masu godiya ne ga Ubangijin mu. Allah ya gaskata alkawarinsa, Ya taimaki bawansa Ya ruguza rundunomin kafirai shi kadai.
ما يقول من أتاه أمر يسره أو يكرهه.
Abin da mutum zai fada idan wani al’amari ya zo masa na farin ciki ko na bakin ciki.
الحمد لله الذي بنعمته تتم الصالحات.
Ma’ana: Daga Aisha Allah ya kara mata yarda ta ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ka sance idan wani al’amar ya zo masa na farin cikin sai yace “Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda saboda ni’imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika. Idan kuma wani al’amari ya zo masa wanda yake ki sai ya ce:
الحمد لله على كل حال.
 Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah a cikin kowanne hali.  
فضل الصلاة على النبي .
Falalar salati ga Annabi .
((من صلى علي صلاة صلى الله عليه بها عشرا)).
Ma’ana: Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:“Wanda ya yi salata daya agare ni, Allah zai yi salati goma a gare shi”.
 وقال: لا تجعلوا قبري عيدا وصلوا علي، فإن صلاتكم تبلغني حيث كنتم.
Ma’ana: Kuma Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gare ni ko ina kuke, domin salatinku yana isa zuwa gare ni ko ina kuka kasance:
وقال: البخيل من ذكرت عنده فلم يصل علي.
Ma’ana: Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini salati ba”.
وقال : إن لله ملائكة سباحين في الأرض يبلغوني من أمتي السلام.
Ma’ana: Kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: ‘Allah yana da wadan su mala’iku matafiya a bayan kasa, suna isar mini da sallama daga al’umma ta’.
وقال : من أحد يسلم علي إلا رد الله علي روحي حتى أرد عليه السلام.
Ma’ana: Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Babu wani wanda zai yi mini sallama face Allah ya dawo mini da raina na amsa masa sallamarsa”.

إفشاء السلام.
Yada sallama a cikin al umma.
قال رسول الله : لا تدخلوا الجنة حتى تؤمنوا، ولا تؤمنوا حتى تحابوا، أو لا أدلكم على شيء إذا فعلتموه تحاببتم، أفشوا السلام بينكم.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, ya ce: “Ba zaku shiga aljannah ba sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba har sai kun so junan ku. Shin, ba na nuna muku wani abu da in kun yi shi za ku so junanku ba? Ku yada sallama a tsakaninku?.
((ثلاث من جمعهن فقد جمع الإيمان: الإنصاف من نفسك، وبذل السلام للعالمَ، والإنفاق من الإقتار)).
M’ana: Daga Ammar, Allah ya kara masa yarda ya ce: Abubuwa uku duk wanda ya hada su hakika ya hada imani: Mutum ya yi adalci akan kansa, kuma ya yada gaisuwar sallama a cikin al’umma da yin kyauta a cikin rashin wadata.
وعن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما: أن رجلا سأل النبي  أي الإسلام خير، قال: تطعم الطعام، وتقرأ السلام على من عرفت ومن لم تعرف.
Ma’ana: Daga Abdullahi bin Umar Allah ya kara masu yarda: Lallai wani Mutum ya tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Wane abu ne a cikin musulunci yafi alherin?. Sai ya ce ‘Ka ciyar da abinci kuma ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba kasani ba”.    
كيف يرد السلام على الكافر إذا سلم.
Ya zai amsa wa kafiri sallama idan ya yi masa sallama.
إذا سلم عليكم أهل الكتاب فقولوا: وعليكم.
Ma’ana: Idan Ma’abota litafi (Yahudu da Nasara), suka yi muku sallama, to ku ce musu: “Kuma haka”.

دعاء صيام الديك ونهيق الحمار.
Addu’a idan aka ji carar zakara da kukan jaki.
إذا سمعتم صياح الديك فاسالوا الله من فضله، فإنها را ملكاً، وإذا سمعتم نهيق الحمار فتعوذوا بالله من الشيطان، فإنه رأى الشيطان.
Ma’ana: Idan kuka ji carar zakara, to ku roki Allah daga falalarsa domin ya ga mala’iku ne. Idan kuma kuka ji kukan jaki, to ku nemi tsarin Allah daga shaidan domin ya ga shaidan ne.
دعاء نباح سماع الكلاب بالليل.
Addu’a idan aka ji kukan karnuka da daddare.
إذا سمعتم نباح الكلاب ونهيق الحمير بالليل فتعوذوا بالله منهن فإنهن يرين ما لا ترون.
Ma’ana: Idan kuka ji kukan karnuka (haushin karnuka) da kukan jaki da daddare to ku nemi tsarin Allah daga garesu, domin su suna ganin abin da bakwa gani?  
الدعاء لمن سببته.
Addu’a ga wanda ka zage shi
اللهم فأيما مؤمن سببته فاجعل ذلك له قربة إليك يوم القيامة.
Ma’ana: Manzo Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:  Ya Allah! Duk wani mumini da na zage shi, to ka sanya wannan ya zamanto sababi gare shi na samun kusaci zuwa gar ka namar kiyama.
ما يقول المسلم إذا مدح المسلم.
Abinda Musulimi zai ce idan yazo yabon musulimi.
قال : إذا كان أحدكم مادحا صاحبه لا محالة فليقل: أحسب فلانا والله حسيبه ولا أزكي على الله أحدا أحسبه – إن كان يعلم ذلك – كذا وكذا.
Ma’ana. Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: idan har dayanku babu makawa sai ya yabi abokinsa to ya ce. Ina yi wa wane kyakkyawan zato - Allah dai shi ne makiyayinsa, mai yi masa hisabi, kuma ni ba na tsarkake kowa ga Allaha – Ina zaton shi kaza – da – kaza ne – idan dai ya san hakan game dashi.
ما يقول المسلم إذا زكي.
Abin da musumi zai ce idan aka ya beshi.
اللهم لا تؤاخذني بما يقولون، واغفر لي ما لا يعلمون واجعلني خيرا مما يظنون.
Ma’ana: Ya Allah! Karka rike ni da abinda suke fada, ka gafarta mini abinda ba su sani ba, ka sanya ni fiye da yadda suke zato.
كيف يلبي المحرم في الحج أو العمرة.
Yadda mai harami akin Hajji ko Umrah zai yi.
لبيك اللهم لبيك، لبيك لا شريك لك لبيك، إن الحمد، والنعمة، لك والملك، لا شريك لك.
Ma’ana: Amsawarka Ya Allah na amsa kiranka, Ya Allah ba ka da abokin tarayya, na amsa kiranka ya Allah. Hakika dukkanin yabo da ni’ima da mulki na ka ne kaikadai, babu abokin taryya a gare ka.
التكبير إذا أتى الركن الأسود.
Kabbara yayin da aka zo daidai da rukunun Hajaral aswad.
طاف النبي  بالبيت على بعير، كلما أتى الركن أشار إليه بشء عنده وكبر.
Ma’ana: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi dawafin dakin Allah (Ka’abah) a kan rakumi, ko yaushe ya zo daidai da kusurwar Hajaral Aswad sai ya yi nuni gare shi da wani abu da yake hannusa, ya yi kabbara.
الدعاء بين الركن اليماني والحجر الأسود.
Addu’a Tsakanin Rukunul Yamani da Hajaral Aswad.
ﭽ ﯜ  ﯝ  ﯞ  ﯟ   ﯠ  ﯡ  ﯢ  ﯣ  ﯤ  ﯥ  ﯦ  ﭼ
Ma’ana: Ya Ubangijin mu ka ba mu kyakkyawa a nan duinya, da kuma kyakkyawa a lahira, kuma Ka kiyaye mu daga azabar wuta.
دعاء الوقوف على الصفا والمروة.
Addu’ar Tsayuwa Akan Dutsen Sata da Marwa.
لما دنا  من الصفا قرأ: ﭽ ﮄ  ﮅ   ﮆ  ﮇ  ﮈ  ﮉ  ﮊ ﭼ أبدأ بما بدأ الله به)) فبدأ بالصفا فرقي عليه حتى رأى البيت فاستقبل القبلة، فوحد الله وكبره وقال: لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير، لا إله إلا الله وحده، أنجز وعده، ونصر عبده، وهزم الأحزاب وحده. ثم دعا بين ذلك. وفيه: ففعل على المروة كما فعل على الصفا.
Ma’ana: Jabir dan Abduallah Allah ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amiacin Allah su tabbata a gare shi yanyin da ya kusanto dutsen Safa da sai ya karanta: “Lallai Dutsen Safa da Marwa suna daga cikin alamomin da Allah ya sanya na addinsa’’. Ina farawa da abinda Allah ya fara da shi, sannan ya fara da dutsen Safa, ya hau shi har saida ya hango dakin Allah, sai ya fuskaci alkibila, ya kadaita Allah kuma girmama shi sai ya ce: Allah ne mai girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma. Bayan haka sai ya kara da hailala ya ce: Babu wani abin bauta da cancanta sai shi, shi kadai yake ba shi da abokin tarraya mai iko ne a kan komai, babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake. Allah ya gaskata alkwarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza randunonin kafirai shi kadai.  
    Sannan ya karanta hakan yana mai addu’a a tsakanin haka: sai kuma ya fadi wannan addu’a misali sau uku.
Da ya hau Dutsen Marwa ma ya yi kamar yadda ya yi a kan dutsen Safa.
الدعاء يوم عرفة.
Addu’ar kuma Arfah.
خير الدعاء دعاء يوم عرؤفة، وخير ما قلت أنا والنبييون من قبلي: لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير.
Ma’ana: Daga Abdullahi dan Amru dan As, Allah ya kara musu yarda su biyu Mazon Allah tsira da amicin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Mafi alherin addu’a ita ce addu’a ranar arafah, kuma mafi alherin abin da na fada ni da Annabawa da suka gabace ni shi ne. “Babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, Mulki ya tabbata a gare shi, yabo ya tabbata a agare shi, kuma shi mai ikon ne akan komai.
الذكر عند المشعر الحرام.
Ambanton Allah A Mash’aril Haram (Muzdalifa).
ركب النبي  القصواء حتى أتى المشعر الحرام فاستقبل القبلة (فدعاه، وكبره، وهلله، ووحده) فلم يزل واقفا حتى أسفر جداًّا فدفع قبل أن تطلع الشمس.
Ma’ana: Daga Jabir dan Abdullahi, Allah ya kara musu yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi Ya hau taguwarsa mai suna Alkaswa’a har ya zo Mash’aril Haram (Muzdalifa), sai ya fuskanci alkibla ya yi addu’a ga Allah,ya yi kabbara ya yi hailala, ya kadaita Allah, bai gushe ba a tsaye yana addu’a har sai da gari ya waye sosai, sannan ya dauki hanya kafir rana ta fito.

التكبير عند رمي الجمار مع كل حصاة.
Kabba Yayin Jifan shedan tare da kowacce tsakuwa.
يكبر كلما رمى بحصاة عند الجمار الثلاث، ثم يتقدم، ويقف يدعو مستقبل القبلة رافعا يديه بعد الجمرة الأولى والثانية. أما الجمرة العقبة فيرميها ويكبر عند كل حصاة وينصرف ولا يقف عنده.
Ma’ana: Daga Abdullahi dan Umar Allah ya amicin Allah su tabbata a gareshi. Ya kasance yana yin kabbara tare da kowace tsakuwa idan yana jifan jamrori uku. Sannan sai ya yi gaba kadan ya yi addu’a yana mai fuskantar alkibla ya daga hamayensa biyu yayin addu’a. Yana yin haka ne bayan jifan jamra ta farko da ta biyu, amma bayan jamratul Akabah jamra ta karshe sai ya yi jifan kawai ya yi tabbara a kowacce tsakuwa, sannan ya tafi ba ya tsayawa ya yi addu’a a wajenta.

دعاء التعجب والأمر السار.
Addu’ar ban mamaki ko na farin ciki.
Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga Alla  .. سبحان الله
Ma’ana: Allah ne mafi girma.     الله أكبر.
ما يقول من أتاه أمر يسره.
Abinda mutum zai fada idan wani abu na farin ciki y azo masa.
كان النبي  إذا أتاه أمر يسره أو يسر به خر ساجدا شكرا لله تبارك وتعالى.
Ma’ana: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan wani al’amari da yake faranta masa rai, ko ake murna da shi yazo masa, sai ya fadi yana mai sujjada domin godiya ga Allah mai tsarki da daukaka.

ما يقول من أحس وجعاً في جسده.
Abinda wanda ya ji ciwo a jinkinsa zai fadi.
بسم الله. ثلاثا. أعوذ بالله وقدرته من شر ما أجد وأحاذر.
Ma’ana: Ka sanya hannuwan ka a wajen da yake maka ciwo a jikinka, ka ce: “Da sunan Allah”. Sau uku, sai kuma ka ce: “Ina neman tsarin Allah da kuma ikonsa daga sharrin abin da na ke ji na ciwo kuma nake jin tsoronsa.
دعاء من خشي أن يصيب شيئا بعينه.
Addu’ar wanda ya ji tsoron faruwar wani na kambunbaka.
إذا رأى أحدكم من أخيه، أو من نفسه، أو من ماله ما يعجبه فليدع له بالبركة فإن العين حق.
Ma’ana: Idan dayanku ya ga wani abu da ya kayatar da shi ga dan’uwansa, ko ga kansa, ko ga dukiyarsa, to ya roki Allah ya sanya albarka a gare shi, domin kambun baka gaskiya ne”.

ما يقال عند الفزع.
Abinda ake fada idan aka firgita.
لا إله إلا الله.
Ma’ana: “Babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah.
ما يقول عند الذبح أو النحر.
Abinda ake fada idan za’a yanka dabba ko za’a soke ta.
بسم الله والله أكبر. (اللهم منك ولك) اللهم تقبل مني.
Ma’ana: Da sunan Allah, kuma Allah ne mafi girma, Ya Allah wannan dabba daga gare ka take, kuma mallakaraka ce. Ya Allah! Ka karba daga gare ni.
ما يقول لرد كيد مردة الشياطين.
Abin da ake fada don kawar da kaidin shaidanu masu taurin kai.
أعوذ بكلمات الله التامات التي لا يجاوزهن بر ولا فاجر من شر ما خلق، وبرا وذرأ، ومن شر ما ينزل من السماء، ومن شر ما يعرج فيها، ومن شر ما ذرأ في الأرض، ومن شر ما يخرج منها، ومن شر فتن الليل والنهار، ومن شر كل طار إلا طارقا يطرق بخير يا رحمن.
Ma’ana: Ina neman tsari da Kalmomin Allah cikakku, waddanda wani bawa na gari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da Allah ya halitta, Ya Samar da shi daga babu Ya fari haliltarsa, haka kuma daga sharrin abin da yake saukowa daga samaa da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gareta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da Alheri Ya Allah mai yawan rahama.

الاستغفار والتوبة.
Neman gafara da tuba zuwa ga Allah.
قال رسول الله : والله إني لأستغفر الله وأتوب إليه في اليوم أكثر من سبعين مرة.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ina rantsuwa da Allah, lalle ni ina neman gafarar Allah kuma ina tuba gare shi a kowacce rana sama da sau saba’in.
وقال : يا أيها الناس توبوا إلى الله، فإني أتوب في اليوم إليه مائة مرة.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku tuba zuwa ga Allah domin ni ina tuba a kowace rana zuwa gare shi sau dari.
وقال : من قال أستغفر الله العظيم الذي إله إلا هو الحي القيوم وأتوب إليه، غفر الله له وإن كان فر من الزحف.
Ma’ana: Ina neman gafarar Allah, wanda babu abin bautawa da cancanta sai shi, Rayayye, Tsayayye (wanda kowa ya tsayu da shi), kuma ina tuba zuwa gare shi. Allah zai gafarta masa zunuban sa ko da ya gudu daga fagen fama ne.
وقال : أقرب ما يكون الرب من العبد في جوف الليل الآخر، فإن استطعت أن تكون ممن يذكر الله في تلك الساعة فكن.
Ma’ana: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Mafi kusanci da Allah yake kasancewa da bawansa shi ne a tsakiyar karshen darene. Don haka Idan kana da ikon kasancewa cikin masu ambaton Allah a wannan lokacin to ka kasance.
وقال : أقرب ما يكون العبد من ربه وهو ساجد، فأكثروا الدعاء.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Mafi kusancin da bawa zai kasance da Allah Ubangijinsa shi ne lokacin da bawansa yake sujada, don haka ku ya waita addu’a. (A cikin sujada)
وقال : إنه ليغان على قلبي وإني لأستغفر الله في اليوم مائة مرة.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce. “Hakika a kan lullube zuciyata, kuma ni ina neman gafarar Allaha sau dari a rana.
فضل التسبيح والتحميد والتهليل والتكبير.
Falalar tasbihi da godiya ga Allah da hailala da kuma kabbara.
قال : سبحان الله وبحمده في يوم مائة مرة حطت خطاياه ولو كانت مثل زبد البحر.
Ma’ana: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Duk wanda ya ce; Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyarsa, sau dari a rana, za a kankare masa zunuban sa ko da sun kasance kamar kumfar kogi ne.
وقال : من قال لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك، وله الحمد، وهو على كل شيء قدير. (عشر مرار). كان كمن أعتق أربعة أنفس من ولد إسماعيل.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; “Duk wanda ya ce: Babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah shi, Shi kadi, ba shi da abokin tarayya, dukkan mulki na sane kuma dukkanin yabo da godiya na sane, kuma shi mai iko ne akan komai. (Sai goma), to kamar wanda ya ‘yanta bayi hudu ne daga cikin ‘ya’yan Annabi Isma’il.
وقال : كلمتان خفيفتان على اللسان، ثقيلتان في الميزان، حبيبتان إلى الرحمن: سبحان الله وبحمده، سبحان الله العظيم.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Akwan wasu kalmomi guda biyu masu saukin fada a harshe, kuma masu nauyi a kan mizani (na ayyukan ranar kiyama) masu soyuwa zuwa ga Allah Mai yawan jinkai, sune; “Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyarsa, kuma tsarki ya tabbata ga Allah mai girma”.
وقال : لأن سبحان الله، والحمد لله، ولا إله إلا الله، والله أكبر، أحب إلي مما طلعت عليه الشمس.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Da zan fadi Tarki ya tabbata ga Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Allah ne mafi girma shi ya fi soyuwa a gare ni daga dukkan abin da rana ta hudo a kansa.
وقال :أيعجز أحدكم أن يكسب كل يوم ألف حسنة)) فسأله سائل من جلسائه كيف يكسب أحدنا ألف حسنة؟ قال: ((يسبح مائة تسبيحة، فيكتب له ألف حسنة أو يحط عنه ألف خطيئة)).
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin su tabbata a gare shi ya ce; “A yanzu dayan ku yana kasa aikata kyawawan ayyuka dubu a kowacce rana?, Sai wani mutum cikin wadanda suke zaune tare da shi ya ce; Ta yaya dayan mu zai aikata ayyuka dubu?. Sai Ma’aikin Allah  ya ce: Ya yi Tasbihi dari, (yace: سُبْحَانَ اَللهِ) Tsarki ya tabbata ga Allah! Sau dari, sai a rubuta masa kyawawan ayyuka dubu ko a kankare masa zanubai dubu.
((من قال: سبحان الله العظيم وبحمده، غرست له نخلة في الجنة)).
Ma’ana: “Duk wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah mai girma, tare da godiya gareshi. Za’a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna:
وقال : يا عبد الله بن قيس ألا أدلك على كنز من كنوز الجنة، فقلت: بلى يا رسول الله، قال: ((قل: لا حول ولا قوة إلا بالله)).
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ya Abdullah dan Kais! Ba na shiyar da kai ba ga wata taska daga cikin taskokin aljanna ba? Sai na ce. Shiryar da ni. “Sai ya ce: Ka ce:
 ((: لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ)). “Babu dabara babu karfi sai da Allah.
وقال : أحب الكلام إلى الله أربع: سبحان الله، والحمد لله، ولا إله إلا الله، والله أكبر، لا يضرك بأيهن بدأت.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; Mafi soyuwar zance a wajan Allah su ne abubuwa hudu: Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Allah ne mafi girma. Babu komai a gareka da wanne daga cikin su ka fara.
جاء أعرابي إلى رسول الله  فقال: علمني كلاما أقوله: قال: قل: لا إله إلا الله وحده لا شريك له، الله أكبر كبيرا، والحمد لله كثيرا، سبحان الله رب العالمين، لا حول ولا قوة إلا بالله العزيز الحكيم)). قال هؤلاء لربنا فما لي؟ قال: ((قل: اللهم اغفر لي، وارحمنى، واهدني، وارزقني)).
Ma’ana: Wani balaraben karkara ya zo wajen Manzon Allah, tsira da a mincin Allah su tabbata a gareshi, sai ya ce: Koya mini wadansu kalmomi da zan rika fada. Sai ya ce: “Ka ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, Allah ne mafi girma, ina girmama shi girmamawa, kuma godiya ta tabbata ga Allah da yawa, tsarki ya tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Babu dabara kuma babu karfi sai ga Allah mabuwayi mai hikima. Sai mutumin ya ce: Wadannan na Ubangijina ne, ni kuma nawa fa? Sai ya ce: Ka ce: Ya Allah Ka yi mini gafara, ka ji kai na ka shiryar da ni, ka azurtani.
كان الرجل إذا أسلم علمه النبي  الصلاة ثم أمره أن يدعو بهؤلاء الكلمات: اللهم اغفر لي، وارحمني، واهدني، وعاني، وارزقني)).
Ma’ana: ldan mutum ya musulunta sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya koya masa sallah, sannan ya umurce shi ya rika addu‘a da wadannan kalmomi: “Ya Allah ka gafarta mini, ka ji kai na, ka shiryar da ni, ka amintar da ni daga bala’i ka azurtani.
إن أفضل الدعاء: الحمد لله، وأفضل الذكر: لا إله إلا الله.
Ma’ana: Lalle mafificiyar addu’a ita ce fadin: “Dukkan godiya ta tabbata ga Allah”. Kuma mafificin zikiri shi ne fadin: “Babu abin bautawa da cancanta sai Allah”.
الباقيات الصالحات: سبحان الله، والحمد لله، ولا إله إلا الله، والله أكبر، ولا حول ولا قوة إلا بالله.
Ma’ana: Ayyuka nagartattu masu wanzuwa su ne fadin: “Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Allah ne mafi girma, kuma babu dabara babu karfi sai ga Allah.
كيف كان النبي  يسبح؟.
Ya Annabi  Ya ke lissafa tasbini ?.
عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما، قال: ((رأيت النبي  يعقد التسبيح بيمينه)).
“Daga Abdullahi bin Amr, Allah ya kara masa yarda, ya ce: Na ga manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana kidaya (lissafa) tasbihi da yatsun hannunsa na da mansa.
من أنواع الخير والآداب الجامعة.
Daga cikin ayyukan alheri da kyawan halaye.
إذا كان جنح الليل – أو أمسيتم – فكفوا صبيانكم، فإن الشياطين تنتشر حينئذ، فإذا ذهب ساعة من الليل فخلوهم، وأغلقوا الأبواب واذكروا اسم الله، فإن الشيطان لا يفتح باباً مغلقا، وأوكوا قربكم واذكروا اسم الله، وخمروا آنيتكم واذكروا اسم الله، ولو أن تعرضوا عليها شيئا، وأطفئوا مصابيحكم.
Ma’ana: “Idan duhun da ce ya gabato – ko kuma almuru ya yi – to ku hana “ya’yanku fita, domin shaidanu suna bazuwa a wannan lokacin. Idan sa’a ta gota a cikin dare, to sai ku bar su. Ku refe kofofi kuma ku ambaci sunan Allah yayin da ku refewa domin shaidan baya bude rufaffiyar kofa. Ku zuge salkar ruwanku (randa da ake zuba ruwa), kuma ku ambaci sunan Allah a yayi da kuke zugewa, kuma ku rufe kwanukan abin cin ku ku ambaci sunan Allah yayin da kuke rufewa, ko da ku dora wani abu ne a kan kwanukan, kuma ku kashe fitilunku na a cibalbal.
وصلى الله وسلم وبارك على نبينا محمد وعلى آله وأصحابه أجمعين.
   Allah Ya yi dadin tsira da aminci da albarka ga Annabin mu Muhammadu da alayansa da sahabbansa baki daya.
******           ******              ******

 

 

Abubuwan Dake ciki.
Gabatarwar wanda ya duba ………………………….. 3
Gabatarwar mawallafi ……………………………….. 5
Falalar zikiri …………………………………………. 8
1. Zikirin tashi daga bacci ………………………….. 15
2. Addu’ar sanya tufafi …………………………....... 20
3. Addu’ar sanya sabon tufafi ………………………..20
4. Addu’a ga wanda ya sanya sabon tufafi ………...… 21
5. Abinda zai fada idan ya sanya sabon tufafi …..….... 21
6. Addu’ar shiga bandaki …………………….…..… 22
7. Addu’ar fitowa daga bandaki …………….………. 22
8. Zikiri kafi alwala ………………………………… 22
9. Zikiri bayan kammala alwala ………………….….22
10. Zikiri yayin fita daga gida ……………….……… 23
11. Zikiri yayin shiga gida ………………….…..……24
12. Addu’ar tafiya masallaci…………………………. 24
13. Addu’ar shiga masallaci ……………….…………25
14. Addu’ar fita daga masallaci ……………………....25
15. Zikiran kiran sallah …………………………..….26
16. Addu’ar fara sallah ……………………………….29
17. Addu’ar ruku’i…………………………………...30
18. Addu’ar tasowa daga ruku’i………………………30
19. Addu’ar Sujjada ………………………………….31
20. Addu’a tsakanin sujjadu biyu ……………….……33
21. Addu’ar sujjadar karatun Alkur’ani ……………...34
22. Tahiya ……………………………………….….35
23. Salati ga Manzon Allah  bayan tahiya ………….36
24. Addu’a bayan tahiyar karshe……………….…….37
25. Zikirai bayan sallamewa daga sallah ……………..42
26. Addu’ar Sallar Istahara ……………………..……48
27. Zikiran safe da yamma ………………………..…50
28. Zikiran Bacci …………………………………....63
29. Addu’a idan ya juya cikin dare …………………..71
30. Addu’ar firgici cikin dare ……………….……….72
31. Abinda zai yi wanda ya yi mafarki ……………….73
32. Addu’ar Alkanut …………………………...……76
33. Zikiri bayan sallamewa daga wuturi ………….….77
34. Addu’ar bain-ciki da damuwa …………………..78
35. Addu’ar kunci ……………………………….…..79
36. Addu’ar haduwa da makiyi da mai mulki…….….81
37. Addu’ar wanda ya ji tsoron mai mulki ………..…81
38. Addu’a akan makiyi ……………………………..81
39. Abinda zai fada wanda ya ji tsoron wasu mutane…82
40. Addu’ar wanda aka jarrabeshi da shakka a Imani...83
41. Addu’ar biyan bashi ………………………….….83
42. Addu’ar mai wasuwasi a sallah da karatu ………...84
43. Addu’ar wanda al’amari ya yi mishi tsauri …….…84
44. Abinda zai fada ya kuma aikata wanda ya aikata zunbi………………………………………………...85
45. Addu’ar koran shaidani da kuma wasuwasinsa…...85
46. Addu’a alokacin da wani abu ya faru wanda ba ya so ko kuma aka rinjayeshi …………….………………..86
47. Barka ga wanda aka yi wa haihuwa da amsarsa…..86
48. Abinda ake karantawa yara domin neman tsari…..86
49. Addu’ar da ake yi wa maralafiya idan an je gaidashi………………………………………………87
50. Falalar gaida maralafiya ……………………….…87
51. Addu’ar maralafi da ya fidda rai da tashinsa……....89
52. Lakkanawa maralafiya “Kalmar Shahada”………..89
53. Addu’ar wanda aka jarraba da wata masifa ……….89
54. Addu’a yayin rufewa mamaci ido……………..…90
55. Karatun sallar jana’iza ……………………………93
56. Karatun sallar jana’iza ta karamin yaro ………..…94
57. Addu’ar ta’aziyyah ………………………………95
58. Addu’a yayin sanya mamaci a kabari ……….……96
59. Addu’a bayan binne mamaci …………………....96
60. Addu’a yayin ziyartar makabarta ………………...97
61. Addu’a yayin tasowar iska ……………………….97
62. Addu’a yayin tsawa …………………………..….98
63. Daga cikin addu’o’in sallar rokon ruwa …….……98
64. Addu’a idan aka ga ruwan sama …………………99
65. Zikiri bayan saukar ruwan sama ……………..….99
66. Daga cikin addu’o’in mark-marka ……….…….100
67. Addu’ar ganin jinjirin wata ……………….……100
68. Addu’a yayin bude baki ……………………..... 101
69. Addu’a kafin a fara cin abin ci……………..……102
70. Addu’a yayin kamala cin abin ci ………………..102
71. Addu’ar da bako zai yi wa mai abinci …………..103
72. Addu’a ga wanda ya shayar ko yake son ya shayar……………………………………………….103
73. Addu’ar da zai yi idan ya yi bude baki a gidan wani………………………………………………..104
74. Addu’ar da mai azumi zai yi idan aka kawo abin ci kuma shi bai sha ruwa ba ……………..……………104
75. Abinda mai azumi zai fada idan wani ya zage shi.105
76. Addu’a a lokacin da aka ga sabon amfanin godana……………………………………………...105
77. Addu’ar atishawa …………………….…………106
78. Abinda za’a cewa kafiri idan ya yi atishawa sa ya ce”Alhamdulillah”……………………………….…106
79. Addu’ar da za’a yi wa ango ………………….... 105
80. Addu’ar da ango zai yi wa kansa da kuma addu’ar sayan abin hawa …………………………………... 106
81. Addu’a kafin saduwar aure ……………………..106
82. Addu’a a lokacin fushi …………………….……107
83. Addu’ar wanda ya ga wanda aka jarraba ………..107
84. Abinda ake cewa a majalisi ……………………..107
85. Kaffarar majalisi ……………………………….. 108
86. Addu’a ga wanda ya ce: “Allah ya gafarta maka”……………………………………………....108
87. Addu’a ga wanda ya kyautata maka ………….…109
88. Zirin da Allah ya ke kare mutum daga jujal …....109
89. Addu;a ga wanda ya ce: “Ina sonka don Allah”…110
90. Addu’a ga wanda ya bijiro maka da dukiyarsa…..110
91. Addu’ar wanda ya dawo da bashi ………………111
92. Addu’ar tsoron shirka …………………………..111
93. Addu’a ga wanda ya ce: Allah ya yi maka albarka………………………………………………111
94. Addu’ar kyamar camfi ………………………....112
95. Addu’ar hawa dabba ko abin hawa …………….114
96. Addu’ar tafiya ……………………………….…115
97. Addu’ar shiga birni ko gari ……………………..115
98. Addu’ar shiga kasuwa …………………….….…116
99. Addu’a idan abin hawa ya gaza ……………..….116
100. Addu’ar matafiyi ga mazauni ………….………117
101. Addu’ar mazauni ga matafiyi ………………….117
102. Kabbara da tasbihi a lokacin tafiya …………....118
103. Addu’ar matafiyi idan dare ya same shi …….…118
104. Addu’a idan ya isa masauki a halin tafiya ……..119
105. Addu’ar dawowa daga tafiya ………………….120
106. Abinda zai ce wanda abin farin-ciki/damuwa ya zo mishi ………………………………………………122
107. Falalar salati ga Annabi …………...…………123
108. Yada sallama…………………..………………124
109. Yadda zai mayarwa kafiri sallama ida ya yi mishi………………………………………………..125
110. Addu’a yayin carar zakar da kukan jaki ……….125
111. Addu’a yayin jin kukan kare da daddare …..….126
112. Addu’a ga wand aka zage shi …………….……126
113. Abinda musulmi zai fada idan ya yabi musulmi..127
114. Abinda musulmi zai fada ida aka yabe shi….…..127
115. Yadda mai ihrami da hajji ko umara zai yi talbiya………………………………………………128
116. Kabbara idan ya zo rukunul aswad ……………129
117. Addu’a a tsakanin rukunul yamani da hajarul aswad……………………………………………….130
118. Addu’ar tsayuwa a safa da marwa …………..…131
119. Addu’a a Arafah ………………………………132
120. Zikiri a Muzdalifa …………………………….132
121. Kabbara a lokacin jifan shaidan a kowanne jifa………………………………………………..…133
122. Abinda zai ce alokacin mamaki da farin ciki ….133
123. Abinda zai yi wanda abin farin ciki ya zo masa..132
124. Abinda zai fada ya aikata wanda ya ji ciwo .......133
125. Abinda zai fada wanda ya ji tsoron kada a kamu da kanbun bakin sa …………………………………....133
126. Abinda zai fada alokacin firgici ………………..134
127. Abinda zai fada a lokacin yanka da suka ……....134
128. Abinda zai fada domin maida sharrin miyagun shaidanu ……………………………………………136
129. Istigfari da tuba ……………………………….138
130. Daga cikin falalar tasbihi da tahmidi …………..145
131. Ya Annabi  ya kasance yana tasbihi …………145
132. Daga cikin nau’ukan alherai da gunkulallun ladubba ……………………………………….……145
133. Abubuwan dake ciki ……………...…………..148
 
Contents

الصفحة    العنوان    م
3    مقدمة المراجع    1
5    مقدمة المؤلف    2
8    فضل الذكر    3
15    أذكار الاستيقاظ من النوم    4
20    دعاء لبس الثوب    5
20    دعاء لبس الثوب الجديد    6
21    الدعاء لمن لبس ثوبا جديدا    7
21    ما يقول إذا وضع ثوبه    8
22    دعاء دخول الخلاء    9
22    دعاء الخروج من الخلاء    10
22    الذكر قبل الوضوء    11
22    الذكر بعد الفراغ من الوضوء    12
23    الذكر عند الخروج من المنزل.    13
24    الذكر عند دخول المنزل.    14
24    دعاء الذهاب إلى المسجد.    15
25    دعاء دخول المسجد    16
26    أذكار الآذان    17
29    دعاء الاستفتاح    18
30    دعاء الركوع.    19
30    دعاء الرفع من الركوع    20
31    دعاء السجود    21
33    من أدعية الجلسة بين السجدتين    22
34    دعاء سجود التلاوة    23
35    التشهد    24
36    الصلاة على النبي  بعد التشهد     25
37    الدعاء بعد التشهد الأخير قبل السلام    26
42    الأذكار بعد السلام من الصلاة    27
48    دعاء صلاة الاستخارة    28
50    أذكار الصباح والمساء    29
63    أذكار النوم    30
71    الدعاء إذا تقلب ليلا    31
72    دعاء الفزع في النوم ومن بلي بالوحشة    32
72    ما يقول من رأى الرؤيا أو الحلم    33
73    دعاء قنوت الوتر    34
76    دعاء الهم والحزن    35
77    دعاء الكرب    36
78    دعاء لقاء العدو وذي السلطان    37
79    دعاء من خاف ظلم السلطان    38
81    الدعاء على العدو    39
81    ما يقول من خاف قوما    40
81    دعاء من أصابه شك في الإيمان    41
82    دعاء قضاء الدين.    42
83    دعاء الوسوسة في الصلاة والقراءة    43
83    دعاء من استصعب عليه أمر    44
84    ما يقول ويفعل من أذنب ذنبا    45
84    دعاء طرد الشيطان ووساوسه    46
85    الدعاء حينما يقع ما لا يرضاه أو غلب على أمره    47
85    تهنئة الملود له وجوابه    48
86    ما يعوذ به الأولاد    49
86    الدعاء للمريض في عيادته    50
86    فضل عيداة المريض    51
87    دعاء المريض الذي بئس من حياته    52
87    تلقين المحتضر: لا إله إلا الله    53
89    دعاء من أصيب بمصية    54
89    الدعاء عند إغماض الميت    55
89    الدعاء للميت في الصلاة عليه    56
90    الدعاء للفرط في الصلاة عليه    57
93    دعاء التعزية    58
94    الدعاء عند إدخال الميت القبر    59
95    الدعاء بعد دفن الميت    60
96    دعاء زيارة القبور    61
96    دعاء الريح    62
97    دعاء الرعد    63
97    من أدعية الاستسقاء    64
98    الدعاء إذا رأى المطر    65
98    من أدعية الاستصحاء    66
99    دعاء رؤية الهلال    67
99    الدعاء عند إفطار الصائم    68
100    الدعاء قبل الطعام    69
100    دعاء عند الفراغ من الطعام    70
101    دعاء الضيف لصاحب الطعام    71
102    الدعاء لمن سقاه أو أراد ذلك    72
102    الدعاء إذا أفطر عند أهل بيت    73
103    دعاء الصائم إذا حضر الطعام ولم يفطر    74
103    ما يقول الصائم إذا سابه أحد    75
104    الدعاء عند رؤية باكورة الثمر    76
104    دعاء العطاس    77
105    ما يقال للكافر إذا عطس فحمد الله    78
105    الدعاء للمتزوج    79
106    دعاء المتزوج لنفسه ودعء شراء الدابة    80
106    الدعاء قبل إتيان الأهل    81
107    دعاء الغضب    82
107    دعاء من رأى مبتلى    83
107    ما يقال في المجلس    84
108    كفارة المجلس    85
108    الدعاء لمن قال: غفر الله لك    86
109    الدعاء لمن صنع إليك معروفا.    87
109    الذكر الذي يعصم الله به من الدجال    88
109    الدعاء لمن قال: إني أحبك في الله     89
110    الدعاء لمن عرض عليك ماله    90
110    الدعاء لمن أقرض عند القضاء    91
110    دعاء الخوف من الشرك    92
111    الدعاء لمن قال: بارك الله فيك    93
111    دعاء كراهية الطيرة    94
111    دعاء ركوب الدابة أو ما يقوم مقامها    95
112    دعاء السفر    96
114    دعاء دخول القرية أو البلدة    97
115    دعاء دخول السوق    98
115    الدعاء إذا تعس المركوب    99
116    دعاء المسافر للمقيم    100
116    دعاء المقيم للمسافر    101
117    التكبير والتسبيح في سير السفر    102
117    دعاء المسافر إذا أسحر    103
118    الدعاء إذا نزل منزلا في سفر أو غيره    104
118    ذكر الرجوع من السفر    104
119    ما يقول من أتاه أمر يسره أو يكرهه    105
120    فضل الصلا على النبي     106
122    إفشاء السلام    107
123    كيف يرد السلام على الكافر إذا سلم    108
124    الدعاء عند صياح ونهيق الحمار    109
124    الدعاء عند سماع نباح الكلاب بالليل    110
125    الدعاء لمن سببته    111
125    ما يقول المسلم إذا مدح المسلم    112
126    ما يقول المسلم إذا زكي     113
126    كيف يلبي المحرم في الحج أو العمرة    114
127    التكبير إذا أتى الركن الأسود    115
127    الدعاء بين الركن اليمان والحجر الأسود    116
128    دعاء الوقوف على الصفا والمروة    117
129    الدعاء يوم عرفة    118
130    الذكر عند المشعر الحرام    119
131    التكبير عند رمي الجمار مع كل حصاة    120
132    ما يقول عند التعجب والأمر السار    121
132    ما يفعل من أتاه أمر يسره    122
133    ما يقول ويفعل من أحس وجعا في جسده    123
133    ما يقول من خشي أن يصيب شيئا بعينه    124
134    ما يقال عند الفزع     125
134    ما يقول عند الذبح أو النحر    126
136    ما يقول لرد كيد مردة الشياطين    127
138    الاستغفار والتوبة    128
145    من فضل التسبيح، والتحميد، والتهليل، والتكبير    129
145    كيف كان النبي  يسبح     130
145    من أنواع الخير والآداب الجامعة    131
148    الفهر    132