Haramcin dukan mata a musulunci

 Haramcin dukan mata a musuluncix 

Haramcin dukan mata a musulunci
تحريم ضرب النساء في الإسلام بلغة الهوسا

 


Mawallafi
Ahmed Al-Amir & Tsekoura Vivian

 

Fassara
European Islamic Research Center (EIRC)
المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية
& Muhammad Khamis
Wanda ya bibiyi fassara
Hashim Muhammad Sani
 

www.islamland.com

Haramcin dukan mata a musulunci
Gabatarwa
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya aiko Muhammad me bushara da gargadi da kuma kira zuwa ga Allah da izinin sa da fitila me haskakawa, ya kuma daukaka sahabban say a basu falala me girma, amincin Allah me tarin yawa a jere ya tabbata a kan Muhammad da iyalan sa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka na rubuta wannan littafi ne a matsayin raddi akan shubuhohi ga wanda shedan ya rude su ya kuma batar dasu bata me girma, hakika nayi magana akan matsalar dukan mace a musulunci a wurare da dama kuma muna gani a yanar gizo wanda suke bada fatawa ba tare da ilimi ba akan wannan al'amari sannan kuma makiya musulunci sun jibge akan wannan al'amari suna masu kirkiran karya da shedar zur daga cikin maganganu wanda basu da tushe balle makama, saboda haka ne na naga ya dace na rubuta wani littafi ga makaranci na bayyan matsayar musulunci game da dukan mace da kuma banbancin sa da sauran addinai banbanci bayyananne, lallai shi kadai ne addinin da ya nassanta akan haramcin duka mata yarinya ce ko kuma babba ce, ga bayanin gareku sannan bayan haka sai kuyi hukunci akan al'amarin bayan karantawa da kuma ilimi akan haka.

                        Mawallafi……
                            Ahmad Amir.


Babi na farko
Aikata ayyuka dai dai da shari'ar musulunci
Lallai dayawa daga cikin ayyukan mutane suna aikata su ne karkashin inuwar shari'a na musulunci karkashin hukunce hukunce masu zuwa a dunkule saboda hukuncin aikin ya bayyana a garemu tsakanin halasci ko kuma haramci:
1-    Farilla: wannan shine kololuwa wurin martaba na ayyukan bayi, shine duk wani abu da Allah ya nema aikata shi wanda yake dole da wani dalili kai tsaye wanda babu shubuha a cikin sa, kamar umurni da yin salla da azumi da karatun alkur'ani, hukuncin sa shine lazumtar aikata haka da kuma zuwa da abunda aka bukata daga bawa na wannan ayyuka tare da samun lada akan aikatashi ko kuma zunubi akan wanda yaki aikatashi.
2-    Mustahabbi: shine dukkanin abunda Allah yayi umurni dashi ba akan fuskar dole ba, ana bayar da lada ga wanda ya aikata shi sannan kuma babu zunubi ga wanda be aikatashi ba, kamar misalign asiwaki kafin fara salla.
3-    Halal: shine dukkanin abunda babu lada akan aikatashi ko kuma zunubi akan barin shi, kamar tafiya da hawan mota da makamantan su na dukkanin abunda aka yarda da aikatashi cikin ayyuka na al'ada na rayuwan mutum na yau da kullum.
4-    Makaruhi: shine dukkanin abunda Allah ya hana hana aikatashi ba akan dole ba, ana bada lada ga wanda yabar aikatashi domin biyayya ga Allah kuma babu zunubi ga wanda ya aikata shi, sai dai anason ya nesanta daga gareshi da kuma abunda ya kunsa sai dai baza'a rubuta zunubi bag a wanda ya aikata shi, sai dai yawan maimatashi da dogewa akan shi zai iya sa mutum ke tare iyakokin Allah da kuma fadawa zuwa ga abunda Allah mabuwayi da daukaka ya hana aikatawa, dalilin da yasa baza'a rubuta zunubi ba ga mutumin daya aikata makaruhi dukda cewa aiki ne wanda aka kyamace shi saboda zai iya yayi ne domin biyan wanin lalura me girma da yanayi na rayuwan mutum wanda zai sanya shi aikata wannan aiki da yake makaruhi, misali ubangiji madaukaki yana kin saki amma be haramta shi ba akan bayin sa domin fadada masu al'amuran su idan akwai laluran aikata hakan.
5-    Haramun: shine dukkanin wani aiki da Allah ya hana aikatashi a fuskar wajibi da wani dalili kai tsaye wanda babu wani shubuha a cikin sa, ana bayar da zunubi ga wanda ya aikata shi sannan kuma akwai lada ga wanda yabar aikata shi domin biyayya ga Allah, Kaman haramcin shan giya.

Banbanci tsakanin halal da haramun:
Lallai sanin halal da kuma banbanta shi daga haram shine ginshiki na musulunci da kuma dalili akan imani, yana hade ne da ayyukan zuciya kamar yadda kuma yake hade da ayyukan gabbai, hukuncin asali na aikata abubuwa shine halal babu haramun sai ga abunda dalili yazo ingantacce kuma a bayyane akan haramcin sa, haramtawa da halastawa hakki ne na Allah madaukaki, kasancewar sa shine mahalicci da reno da saukakewa da bada ni'ima yana halastawa bayin sa abunda yake so ya kuma haramta musu abunda yake so, sai dai saboda rahamar Allah madaukaki da falalar daga gareshi ya sanya halal da haram domin dalilai wanda ake iya hankalta wanda yake komawa ga maslahar mutum, akan wannan Allah madaukaki be halasta wani abu ba face me dadi kuma be haramta komai ba sai datti.
Canzawar aiki daga wannan gida na hukunci zuwa wani gida:
1.     canzawar aiki daga halal ya koma gidan haramci ko kuma akasin haka:
aiki na halal zai iya canzawa zuwa haramun idan aka samu dalilai wanda zasu say a canza maimakon aiki ya zama me kyau wanda rai ke sonsa zuwa aikin mummuna wanda yake cutar da jiki, misali akan haka shine hukuncin sharia na yawo akan hanya shine halal, sai dai zai iya canzawa zuwa haramun idan wani shugaba na musulunci na wani kasa ya karrara haramcin yawo daga karfe goma na dare misali akan wasu tutuka ko kuma cikin wasu bira ne saboda wasu dalilai na tsaro wanda zai iya kaiwa ga rasa ran mutum.
        Aiki na haramun zai iya canzawa zuwa halal idan aka samu dalilai wanda zai sanyashi haka na lalura domin kiyaye rai daga halaka, kamar shan giya, shan giya hukuncin sa haramun ne sai zai iya zama halal idan mutum ya bata hanya acikin sahara ya kusan mutuwa saboda kishi kuma bai samu ruwa ba sai giya, a wannan yanayi zai sha giyan nan gwargwadon yadda zai kiyaye ran sa daga halaka amma kuma bazai wuce wannan kima ba.
2.    Aiki ya canza daga wajabci zuwa haramci ko kuma akasin haka:
 Aikin zai iya canzawa daga wajabci zuwa haramci, kuma aikin na haramun zai iya canzawa zuwa na wajibi, saboda dalilai wanda zai kawo hakan kamar yadda mukayi bayani a baya, misali salla wajibi ne sai dai aikata salla zai iya zama haramun idan mutum yayi salla a cikin gidansa a tsakiyar girgizan kasa me tsanani wanda yana da tabbacin fa zai halaka idan dai be fita daga wannan gidan ba da sauri!! Ko kuma ta'addanci ga mutum na yanke masa kafa hakan haramun ne sai dai uziri na rashin lafiya zai iya a yankewa mutum kafar sa domin ceton rayuwan daga halaka to anan wurin yanke kafan wannan mara lafiya ya zama wajibi akan likita domin masa magani idan kuma be aikata hakan ba yana da laifi kuma Allah zai azabtar dashi akan rashin yanke wannan kafa ta mara lafiya.
3.    Canzawan aiki daga makaruhi zuwa zuwa mustahabbi, da kuma canzawan aiki daga mustahabbi ko kuma sunna suwa haramci:
Aiki na makaruhi zai iya canzawa zuwa mustahabbi ko kuma wajabci, misali saki aiki ne wanda yake makaruhi a shari'a Allah madaukaki yana kyamansa sai dai a wani lokutan rashin sakin matan zai iya kaiwa zuwa ga haramun wanda babu wani hanya da zai gusar da hakan sai sakinta, kamar idan mace ta kasance me karancin kamun kai kuma ya kasa gyarata anan wurin abunda yafi shine ya saketa, anan wurin aiki makaruhi ya zama mustahabbi.
Aiki mustahabbi zai iya komawa haramun, misali yin asuwaki aiki ne wanda yake mustahabbi amma zai iya zama makaruhiko kuma haramun idan hakoran mutum suna ciwo zasu fita ya kuma san cewa idan fa yayi asuwaki zasu fita, a cikin wannan hali yin asuwaki yaci karo da ka'ida ta shari'a cikin musulunci wacce tace (babu cuta kuma babu cutarwa).
 
A takaice:
A takaice da dunkule maganar da sharhin sa ya gabata shine muslunci ba addini bane makaho wanda baya gani kuma bay alula da uzirin mutane da ikon sun a rayuwa nay au da kullum, lallai makanci ya hakika yana cikin idanun makiyan sa ne wanda suke son yada shubuhohi da kararyaki akan musulunci domin su rufe hasken Allah kuma Allah sai ya cika hasken sa koda kuwa kafirai basaso.
        Me yuwa ne yakai me karatu me karamci kasan cewa musulunci ba addini ne ban a zalumci addini ne na adalci, shi kuma adalci suna cikin sunayen Allah kyawawa, saboda haka haramci da halastawa a cikin musulunci sun ginu ne akan adalci ba akan makanta ba, shi kuma zalumci baki dayan sa haramun ne a cikin shari'ar musulunci.


Babi na biyu
Mu'amalantar matan aure a karkashin hasken alkur'ani da sunnar me tsarki
 A cikin hasken nassoshi na alkur'ani me girma Allah madaukaki yayi umurni da kyautatawa ga mata da kuma karramata da rayuwa da ita me dadi hatta bayan karewan soyayya ta zuciya, Allah madaukaki yace: " kuyi zama dasu me kyau da dadi, idan kun kyamaci su to wata kila fa kuna kyamatan abu sai Allah yasa masa alheri me yawa"
(suratun nisa'i ayata 19)
Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " kada mumini ya kyamaci mumina idan ya kyamaci wani dabi'a daga gareta zai yarda da wasu". Muslim ne ya rawaito shi.
Allah madaukaki yayi bayanin hakkokin mata akan mijinta kamar yadda mijin shima yake da hakkoki akanta, sai Allah madaukaki yace: " suma sunada kwatankwacin abunda yake kansu na kyautatawa"
(suratul bakara ayata 228)
Wasiyyar manzon Allah s.a.w ta kasance gabanin rasuwar sa da kula da dama da karrama su da kuma rashin zalumtar su da danne masu hakkokin su, manzon Allah s.a.w yace: " ina maku wasiyya na alheri game da mata" muslim ne ya rawaito shi.
Ya kuma kara cewa s.a.w: " wanda yafi muminai cikan imani shine wanda yafisu kyawawan dabi'u kuma zababbun ku sune wanda suka kasance zababbu ga iyalan su" tirmizi da ibn hibban ne suka rawaito shi, tirmizi yace hadisi ne hasan sahih kuma yana cikin littafin sahihul jami'u lambar hadisi na: 1230.
An karbo hadisi kuma daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace: manzon Allah s.a.w yace: " mafi alherin ku shine wanda ya zama mafi alheri ga iyalan sa kuma ni nafiku zama mafi alheri ga iyalai na". Ibn hibban ne ya rawaito shi cikin littafin san a sahihi da tirmizi hadisi na 3314 cikin littafin sahihul jami'u.
Ya kuma yi umurni da hakuri akan kura kuran su da kuma raunin hankalinta da kuma kawar dakai daga kaskancinta yana me bayyana dabi'ar mace wanda Allah madaukaki ya halicce ta akai, sai manzon Allah s.a.w yace: " lallai mace fa an halicce ta ne daga kashin hakarkari, bazata taba mike maka ba, idan zakaji dadi da ita kaji dadi da ita a haka a karkacenta, idan kuma kace zata mikar da ita zaka karya ta ne kawai, karyata shine sakinta". Muslim ne ya rawaito shi.
Ya kuma kara fadi har wayau cewa: " ina maku wasiyya na alheri ga mata saboda an halicce su ne daga kashin hakarkari kuma mafi karkacewar kashin hakar kari shine na sama, idan kace zaka mikar dashi zaka karya shi idan kuma ka kyale shi hakan zaici gaba da zama a karkatanshi, sabo da haka ina maku wasiyya na alheri akansu". Buhari ne ya rawaito shi.

Shin manzon Allah s.a.w ya taba dukan wata daga cikin matan sa ko sau daya ne?
Maznon Allah s.a.w shine abun koyin musulmai wanda Allah ya wajabta masu bin sunnar sa, Allah madaukaki yace: " hakika kunada koyi na kwarai daga manzon Allah ga wanda yake kwadayin samun rahamar Allah da rana ta karshe ya kuma ambaci Allah dayawa".
(Suratul ahazab ayata 21)
Shine abun kuyi na kololuwa da kuwa dabi'a masu daraja Allah ya aiko shi da addini mikakke kuma ubangijin sa ya tarbiyyantar dashi ya kuma kyautata tarbiyyan sai ya kasance abun kuyi wurin kyawawan dabi'u da halaye na gari, Allah madaukaki yace: " lallai kana kan dabi'u masu girma".
(Suratul kalam ayata 4)
Yayi aiki da kyawawan dabi'un sa a aikace akan abubuwan da suka faru ya sanyata kuma suka zama milali na gani, cikin fadin sa s.a.w: " an aiko ni ne domin na cika kyawawun halaye". Malik ya kawo shi cikin muwadda da kuma buhari cikin adabul mufrad kuma yana cikin littafin sahihah lambar hadisi na (45).
Matar sa Aisha tana fadi game dashi wacce tasan bubuwan shi mu'amala saba da sahabban sa: " dabi'un sa ya kasance alkur'ani ne". ahmad ne ya rawaito shi cikin sahihul jami'a(4811), watan yana bin umurnin da yayi yana kuma barin dukkanin abunda da ya hana babu wata dabi'a ta kwarai wanda alkur'ani ya kwataidar akanta face manzon Allah s.a.w ya kasance wanda yafi kowa riko da ita, kuma babu wata dabi'a mara kyau wanda alkur'ani ya hana face manzon Allah s.a.w ya kasance wanda yafi kowa tsananin nisantar sa.

Shin ya zo cikin tarihin sa cewa ya taba dukan wata mace ko kuma yaro ko sau daya ne?!!!!
Hakika duk wanda yake bibiyan tarihin sa da lura cikin hadisan sa masu daraja zai gani a bayyane cewa manzon Allah s.a.w ya hana hakan kuma ya tsawatar akan haka matuka, matar sa Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa game dashi: " manzon Allah s.a.w be taba dukan komai ba da hannun sa ko mace ko wani bawan sa me masa hidima sai dai yayi jihadi fisabilillah. Kuma ba'a taba masa wani laifi ba ya rama sai dai idan an keta hurumin Allah shine yake ramako domin Allah madaukaki mabuwayi" msulim ne ya rawaito hadisin [ ma'anar hadisin shine ba'a taba cutar dashi bay ace zai dau fansa ko kuma ramuwa ba sai dai idan an keta iyakokin Allah sai ya taimaki hakan ya kuma ladabta wanda ya keta su].
Kai hatta makiyan sa wanda suke kokarin bata da'awar sa da kuma katange mutane daga gareta basu taba tabbatar da wani abu akan haka ba wanda yake sabama abunda muka ambata.
Bari muka abunda wanda yafi kusanci dashi cikin mutane ya kuma lazimce shi sosai wanda babu shakka dadewa da lazimtar mutum zai bayyana maka halayen sa baki daya, hadimin sa Anas dan malik yana cewa game dashi wanda yayi masa hidima na tsawon shekaru goma:
" na yima manzon Allah s.a.w hidima na tsawon shekaru goma amma be taba cemun ba kul ko sau daya, kuma be taba cemun ba game da wani abu dana aikata me yasa ka aikata ko kuma abunda ban aikata ba yacemun me yasa baka aikata shi ba? Manzon Allah s.a.w ya kasance yafi kowa kyawawun dabi'u cikin mutane" muslim da tirmizi ne suka rawaito shi.


Babi na uku
Hukuncin miji ya duki matar sa a musulunci?
Lallai inda ake samu dalilai a musulunci shine cikin nassosi na littafin Allah madaukaki da sunnar manzon sa in gantacce me daraja amincin Allah ya tabbata a gareshi da sahabban sa da iyalan sa, daga cikin wannan abubuwa biyun ne zamu kafa hujja dasu wanda a karkashin su ne zai bayyanar mana hukuncin dukar mace a cikin musulunci shin hakan wajibi ne ko kuma mustahabbi ko halal ko makaruhi ne ko kuma haramun daga cikin hadisin da Iyas dan Abdullahi ya rawaito inda yace: manzon Allah s.a.w yace: " kada ku rika dukan bayin Allah mata, sai umar yazo wurin manzon Allah s.a.w yace masa: mata suna bijirewa mazajen su, sai yayi ramgwame akan dukan su sai gidan manzon Allah s.a.w ya cika da mata suna kawo koken mazajen su, sai manzon Allah s.a.w yace: " hakika gidan Muhammad fay a cikia da mata suna kokawa akan mazajen su to wa'innan basu basa cikin zababbun su". Abu dawud da ibn majjah da darimi ne suka rawaito shi, albani yace hadisi ne ingantacce.
A karkashin sharhin wannan hadisin me dajara zai abubuwa Kaman haka zasu bayyanan mana:
Lallai hadisin nan na manzon Allah me girma be fade shi ba a lokaci gudu kuma a zamani daya, ya fadeshi ne s.a.w cikin zamani guda uku mabanbanta:
Zamani na farko: manzon Allah s.a.w yace a cikinta " kada ku rika dukan bayin Allah mata" wannan shine karshen zamani na farko da wuri na farko.
A bisa da haka duk wanda yaji wannan maganar daga manzon Allah s.a.w zai sani cewa lallai hukuncin dukan mata a muslunci haramun saboda manzon Allah s.a.w ya hana kuma duk wanda ya aikata hakan ya sabama Allah kuma za'a hukunta shi saboda ya sabama wannan umurni na manzon Allah s.a.w.
Zamani na biyu: zuwan Umar dan kaddab Allah ya kara masa yarda a lokacin da ya sabawa lokacin farko wanda manzon Allah s.a.w yace acikin sa: " kada ku rika dukan bayin Allah mata" domin kawo kuka akan mata da cewar sa: mata suna bijirewa mazajen su. Watan ma'ana basa bin umurnin su kuma suna kausasa masu da magana kuma sun galabe mazajen su, anan ne manzon Allajh s.a.w yayi rangwame da dukan mata saboda amfani da yayi da ra'anin sa na fiqhun zamani da lalura na rayuwa wanda rayuwa bazayyiwu ba sai dashi, sai dai kuma yaye yanayin wannan duka yake? Wannan shine abunda zamuyi magana akan sa nan bada jimawa ba.
Zamani na uku: bayan izinin manzon Allah s.a.w ga, mazaje da kudan matan su wanda suke saba masu da bijirewa akan mazajen su, sai mata dayawa sukazo gun manzon Allah s.a. yana kokawa akan mazajen su, sai manzon Allah s.a.w yace: " hakika gidan Muhammadu ya cika da mata suna kokawa akan mazajen su lallai wannan mazajen basa cikin zababbun cikin ku"
Wannan shine zamani na karshe wanda hukuncin haramcin dukan mata ya bayyana a cikin musulunci wanda hakan makaruhi ne da kuma haramun idan mijin ya ketare iyakokin Allah -wanda zamuyi bayanin haka nan bada jimawa ba- shin za'a fahimta cikin wannan nassin hadisin cewa manzon Allah s.a.w ya kwadaita akan dukan mata? Ko kuma yayi shagube ne ga dukkanin me dukan matar sa? Lallai cikin maganar sa s.a.w akwai rashin mugunta da kuma kore alheri ga mutumin dake dukan matar sa?!!!
Hakika sahabbai Allah ya kara masu yarda sun fahimci isharar wannan maganar ta manzon Allah s.a.w kuma sun gane cewa lallai duk wanda yake dukan matar sa bazai taba samn yardan da kyautatawa ba daga manzon Allah s.a.w, babu shakka kuma cewa duk abunda manzon Allah s.a.w be yarda dashi ba to yana cikin hukuncin makaruhanci me tsanani wanda hakan zai iya kaiwa zuwa ga haramun.
Hasali ma a lokacin da mijin Fadima ditar kais ya saketa wasu mutum biyu sun zo sun nemi aurenta wanda sune mu'awiya dan abu sufyan da Abu jahmin da usama dan zaid Allah ya kara masu yarda, a lokacin ne manzon Allah s.a.w yace mata: " shi mu'awiya mutum ne talaka, shi kuma abu jahmin mutum ne me yawan dukan mata amma shi usama dan zaid" sai ta fada da hannun cewa: usama! Usama!". Muslim ne ya rawaito shi.

Shin dukan mace zai iya canzawa daga makaruhanci zuwa haramci?
Hakika mun gani yadda yake cewa asali da hukuncin farko akan dukan mata haramun ne sa'annan ya canza ya zama halal saboda wasu dalili da magani na musamman wanda suka sanya hakan daga nan kuma ya canza zuwa makaruhanci babba, sai dai yaushe ne dukan mace yake zama haramun? Dukan mace yana zama haramun ne idan ya kasance najin ciwo maimakon wanda zai ladabtar kawai ba tare da jin ciwo ba lallai dukkanin ta'adi cikin musulunci haramun ne idan ya kasance zalumci ne ko kuma muganta, Allah madaukaki yace cikin littafin sa me hikima yana tsawatarwa gane da dukkanin nau'in zalumci: " duk wanda yayi zalumci daga cikin ku zamu dandana masa azaba me girma"
(suratul furkan ayata 19)
Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " kuji tsoron zalumci domin kuwa zalumci duhu ne ranar alkiyama" muslim ne ya rawaito shi.
An kuma karbo hadisi daga Anas Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: " kuji tsoron addu'ar wanda aka zalumta koda kuma kafiri ne saboda addu'ar sa bashi da wani shamaki tsakanin sa da Allah". Ahmad ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
Musulunci ya haramta cutarwa koya yake da dukkanin surorin sa da nau'ukan sa shin na magana saboda fadin Allah madaukaki cewa: " lalllai wanda suke jifan mata muminai kamammu wanda babu ruwan su an tsine masu duniya da lahira kuma suna da azaba me girma".
(Suratun nur ayata 23)
Ko kuma cutarwa na jiki da kuda da makamantan sa sai idan ya kasance a bisa hakki ne, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " wanda suke cutar da muminai maza da mat aba tare da wani laifi ba to haki sun daukan ma kansu nauyi da zunubi bayyananne"
(suratul ahazab ayata 58)
Wannan haramcin ya shafi kowa cikin mutane maza da mata kanana da manya musulmi da kafiri, an karbo hadisi daga abi huraira Allah ya kara masa yarda daga manzon Allah s.a.w yace: " musulumi shine wanda mutane suka kubuta daga sharrin harshen sa da hannun sa mumini kuma shine wanda mutane suka amince masa akan dukiyar su da jinin su". Sanunan al nisa'i, sheikh albani yace hadisi ne hasan sahih.
Duk wanda yace musulunci yana ta'addanci ko kuma mugunta ko dukan mace to hakika yayi kage ga addinin Allah karya me girma.

Hukuncin alkalanci na musulunci akan dukan mace:
Alkalanci ta musulunci yana daukan al'amarin dukan mace da cutar da ita daga wurin mijinta da matukar muuhimmanci sannan kuma beyi kasa a gwewa ba wurin hukunta ladabtarwa ga miji akan me ta'adi da zalumci da mugunta ba akanta kuma yana dabbaka shi a aikace da hukunci na shari'a a duk lokacin da aka kawo kara akan haka, misali wannan kararraki masu zuwa:
1-    Sharidar riyad ta yada akan shafinta na intanet a kwanan wata 12/12/2012 labari kamar haka:
Kotun koli akan laifuffuka na yankin jihar katif cikin kasar saudiyya tayi hukunci akan miji akan ta'addancin da yayi ma matar sa na duka da cewa za'ayi masa bulala 30 a idon mutane saboda haka ya zama izina ga masu ta'addanci akan matar su, sannan kuma tayi masa hukunci har wayau da zai karantar a daya daga cikin makaruntu na gaba da sakandire a fannin mu'amala tare da matan aure da kuma al'amarin iyali, sannan kuma zai gabatar da jarabawa na rubutu wanda zai sanya shi a cikin fayel din wannan shari'a.
Akan irin wannan matsala dukkanin kotuna cikin garuruwan musulmai baki daya suna hukunta miji wanda yayi ta'addanci ga matar sa da duka, ta dayan bangaren kuma matan da suke tsoratar da mazajen su da nuna su da makami ko kuma niyyar cutar dasu da makirci ga mazajen su ana masu hukuncin bulala ba dayawa ba daganan kuma akaisu wurin yan sanda domin wannan aiki nasu da sukayi ma mazajen su idan mijin ya barranta daga wannan tuhumar.
Abunda muke so a cikin wannan hukunci shine lallai musulmi me hankali wanda yake bin karantarwan musulunci baya yarda da zalumtar mace ko kuma yi mata ta'addanci, kamar yadda addinin mu ya be karantar damu ba ko kuma umurtan mu da hakan sai dai ya haramta mana hakan ya kuma sanya hakan cikin ayyukan zalumci na haramun, hasali ma ya umurce mu ne da hakuri da yafiya da kawar dakai da kuma sakayya akan laifi da kyakyawan aiki, dukda cewa musulunci be sanya dukan mace ya zama halal ba ya dai sanya shi ya zama a wasu lokutan kadai ya kamata ayi hakan idan ya rayuwan ma'aurata bazai gyaru ba sai dashikuma ya kayyade hakan da sharudda wanda zai sanya hakan ya zama yayi karanci sosai domin tabbatar da burin daya wanda shine kiyaye gida da kuma ladubban jama'a cikin al'umma baki daya.


Babi na hudu
Hukunce hukuncen musulunci a halin bijirewar mace
Mutum zai iya cewa shin baya fi dacewa ba da namiji ya rika yima matar sa wa'azi idan ta bijire maimakon dukanta, sai muce mas aba haka bane wannan shine hukuncin Allah madaukaki me buwaya wanda yace cikin littafin sa me hikima:
" Wanda kuma kuke tsoron bijirewar su kuyi masa wa'azi a farko sannan ku kaurace masu a wurin kwana sannan kuma ku duke su, idan kuma sunyi maku biyayya to kada kirkizo wani hanyar cutarwa a gare su, lallai Allah ya kasance madaukaki ne me girma".
(Suratun nisa'i ayata 34)
Manzon Allah s.a.w kuma yace cikin hajjin san a bankwana:
" ku saurara kuji ina maku wasiyya na alheri game da mata domin lallai suna rayuwa ne akarkashin ku amma baku mallaki komai ba da ya wuce haka game dasu, sai dai idan sunzo da alfasha bayyananne, idan suka aikata haka to ku kaurace masu a wurin kwana sannan kuma idan basu shiryu ba sai ku duke su duka bana jin rauni ba, idan kuma sukayi maku biyayya to kada ku kirkiro wata hanyar zalumci akan su. Ku saurara kuji lallai kuna da hakki akan matan ku haka suma suna da hakki akan ku" tirmizi ne ya rawaito shi, albani yace hadisi ne hasan.
Haka zamu rika ganin yadda Allah madaukaki me hikima yake bayyana mana cikin hikimar sa masani ga harkokin bayin sa da manzon sa me daraja hanya domin magance matsalolin mace wanda ta bijire a hankali har zuwa matakai uku:
1.    Mataki na farko:
Ya nuna ma miji hanyar wa'azi da nasiha a matsayin mafita na farko domin gyara macen da ta bijire kafen kaurace mata a wurin kwana wannan matakan wajibi ne binsu a jere a wurin mafiya yawan malaman fiqihu, ya wajaba akan namiji ya kusanci zuciyar matar sa da maganganu masu dadi da kuma jiyar da ita abunda zai lallashi zuciyar ta ya kuma nuna mata muhimmancin ta a wurinshi da cewa lallai yanasonta da alheri yana mata nasiha ya kuma aiwatar da ikon sa akan mata nasiha da wa'azi wurin ganin cewa ya gyara halinta, musani cewa fa wa'azi baya zuwa daga busashiyar zuciya ko kuma da usulubi mara kausasawasai dai yana samuwa ne da magana me dadi da kuma mu'amala kamar siyan kauta ga mace har ta amshi maganar mijinta da zuciya daya kuma cikin yarda,hakika ya wajaba akan mace me kwakwalwa da dabi'u kyawawa data wa'aztu daga maganar mijinta tana kallon makomar gidanta da yaranta, amma idan mace ta kasance me taurin kai me mummunan hali to nasiha baya amfanar da ita ko kuma wa'azi ko fadakarwa sai mijin ya aikata abunda zai iya cikin haka sai ya tafi zuwa mataki na biyu cikin jerin kamar yadda Allah madaukaki ya umurce mu dashi wanda shine kaurace mata a wurin kwana.
2.    Mataki na biyu:
Miji ya bi hanyar kwarace wa a wurin kwana watan ya juya mata baya kuma kada ya kusanceta har na tsawon kwana uku amma kuma kada ya wuce kwanaki uku saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " baya halatta ga musulmi daya kaurace ma dan uwansa sama da kwana uku". Muwadda da buhari da buslim duk sun rawaito shi.
Domin ya tsawatar mata akan aikinta wannan shine mataki na biyu kuma damace ga matan domin ta gyara cikin wannan lokaci na tsawon kwanaki uku, idan ta gyara halinta to ya wajaba a gareshi dana yanke wannan kaura nashi ya yafe masa da nasiha idan kuma taci gaba dayin girman kai da dagawa ya zama wannan kauracewan da yayi mata be amfanar da komai ba sai na tafi zuwa mataki na uku.
3.    Mataki na uku:
Idan miji yayi kokarin gayra wannan mata nashi ta hanyar nasiha da wa'azi da kyawawan magana da kauta duka amma babu amfani sannan ya kaurace mata a wurin kwana amma duka shiru ya kuma bayyana mata rashin yardanshi da aikinta shima be samu nasaraba, to anan wurin an yardan ma miji daya ladabtar da matan da duka wanda banajin ciwo ba ko kuma yi mata wani lahani, hakika malamai inyi ittifaki akan wajabcin bin wannan matakai a jere wurin warware matsalar mace wanda ta bijire wanda sune wa'azi a matakin farko sai kaurace mata sannan idan bata gyara ba sai duka, Ada'u yace nace ma ibn Abbas menene duka mara cutar wa? Sai yace mun shine duka da asiwaki da makamantan su!! Hasanul basari yace: ma'ana duka bame tasiri ba. Dan Allah dai ya kai makaranci me daraja shin duka da asuwaki yakai ace masa duka na mugunta da rashin tausayi abunda bai wuce tsayin pensir ban a rubutu?
Idan dai kana daukan duka da pensir a matsayin duka na mugunta da rashin tausayi to kazoo mugani baki dayan mu dakai sau nawa muke gani a cikin gidajen talabijin na holanda da sauransu suna sawwara mana labarin miji wanda yayi fishi da matar sa ko kuma tsakanin sa da abokin sa ko kuma wata mata ko shugaban kamfani da ma'aikacin sa wanda muke gani a cikin labarin wannan mutumi zai daura yatsantsa manuni akan kirjin sa yana masa kashedi ko kuma sanya pensir a kirjin sa wani loakci ma har abun yakai ga mari, hakan na faruwa cikin dayawa daga cikin finafinai idan miji yayi fushi da matar sa hakan na kaiwa ga mari me karfi a fuskanta sa'annan ya bar wurin, amma wannan dukkunin sa turawa basa daukan sa a matsayin mugunta kawai yanayi ne yakai mijin nan da marin matar sa, kuma kaga suna daukan wannan mutumi a matsayin mutum wayayye, duk da cewa mari a fuska haramun ne a musulunci sai dai suna fada ne da musulunci suna fadin karya akansa cewa yana koyar da rashin tausayi.
 Duk da cewa musulunci yaba namiji damar amfanin da ikon sa na ganin ya gyara wannan mata cikin matakin farko dana biyu sannan na uku lallai musulunce yaba wannan matar hakki na neman saki tun kafin akwai ga wannan mataki abunda yake kira da suna khul'i idan ta iatce ta nemi hakan daganan kuma sai ta yanke ma kanta hukunci inane zata gaba: wannan shine abunda zamuyi magana akansa nan gaba da yardan Allah madaukaki.
Masani fa cewa nasiha da kauracewa sannan duka bashi bane hanyar warware matsaloli nay au da kullum ba tsakanin ma'aurata, wannan hanya ce ta warware manyan matsaloli a tsakanin su, misali da ace miji zai cema matar sa ki girka mana shinkafa yau da kifi sai ta manta ta girka shinkafa da kaza shin wannan ayar zai tabbata akanta da yayi mata nasiha sannan ya kaurace mata sai kuma duka?!!!!
Amsar itace a'a, wannan al'amura ne kanana wanda ya wajaba a rika yafiya akai ba tare da ladabtarwa ba, amma kuma idan matan ta kasance bata da halaye na gari me girman kai sannan mijin ya fara ganin ta fara ayyuka na bijirewa da girman kai da saba masa!! Mu anan muna magana ne akan mace wanda ta bijire wacce take bukatan nasiha da shiryarwa da magani akan matsalolinta kamar mara lafiya ne wanda yake bukatan magani, muyi kaddar cewa wannan mata wanda ta bijire mijin yayi nasihar da kauracen wa da duka na tsawon lokaci taki gayruwa shin sakinta shine yafi ko kuma duka wanda bana cutarwa ba?!!!! Idan duka ya kasance harara gefe shi kuma saki makanta to lallai me harar gefe yafi makaho kuma da za'a bar wannan mata akan halinta zata tarwatsa iyalan nan da al'umma baki daki!!

Babi na biyar
Ma'ana da kuma abunda duka yake nufi a cikin musulunci.
Tun gabanin kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya ta gara yaki da mugunta tsakanin ma'aurata da yara hakika musulunci ya rigata da hakan yadda yayi yaki dashi ya kuma haramta shi da tanadar wa me aikata hakan da ukuba nan duniya dana lahira bawai haramta hakan ya tsaya bane akan aikin kawai a'a hatta magana wanda ya shafi hakan yana cikin wannan haramci wanda hakan yafi zama kamala akan dokokiwanda suke yin ukuba na duniya kawai tun gabanin shekaru 1400 da suka wuce manzon Allah s.a.w yace: " musulmi shine wanda musulmi ya kubuta daga sharrin harshen sa da hannun sa, mumini kuma shine wanda mutane suka aminta masa akan jinin su da dukiyan su" Ahmad da tirmizi ne suka rawaito hadisin, albani kuma ya ingantashi.
Ya kuma kara cewa har wayau: " ba mumini bane me yawan suka ko kuma tsinuwa ko alfasha ko kuma mara kama kai". Buhari ne ya rawaito shi cikin adabul kadi da tirmizi kuma albani ya inganta shi.
Me tambaya zai iya tambaya cewa ta yaya musunci ya hana mugunta amma kuma ya halatta miji ya duki matar sa?!!
Game da amsan wannan tambaya ya kamata muyi bayani a farko banbanci tsakanin abunda duka yake nufi a cikin rayuwan mu ta yau da ma'anarta a cikin shari'ar musulunci, a cikin rayuwan mu tayau idan mutum yaji cewa mutum ya duki matar sa abunda zai zo a tunanin sa shine wannan aiki na rashin tausayi ne da mugunta da zalumci na wannan miji wanda yakai sa da dukan matar sa sannan yanayin wannan mata da mijinta ya zalumta da duka shine ya jijji mata ciwuka dukkanin jikinta da karaya, wannan shine ma'anar duka a rayuwan mu ta yau wanda muka samo shi dilimin mu da rayuwan mu da cewa shine misalign daya duki matar sa, amma idan nace maka na duki karar rawan kowa shin zata fahimci cewa tana ta'addanci ga wannan kofa?!! Sannan idan nace maka zan duke misali shin zaka fahimci cewa zan maka ta'adi ne irin haka?!! Kenan Kalmar duka tana cancanzawa gwargwadon yadda akayi amfani da ita a harshen wannan mutane da kuma dabi'ar wannan mutumi dukkanin wannan zai zo cikin tunanin mu akan ma'anar duka, saboda haka ma'anar duka a musulunci yasha banban gabaki daya da ma'anar sa cikin rayuwan mu nay au wanda hakan haramun ne kuma ta'addanci ne a cikin musulunci sosai, wannan ma'anonin bazasu taba haduwa ba har Abadan idan munason yin adalci saboda haka ya wajaba muce babu dukan mata ga miji acikin musulunci kuma ba'a yardan masa da wulakantata ba ko kuma muzguna mata ko yi mata magana da kalamai marasa dadi, ma'anar duka a musulunci yana nufin duka dan kadan kamar misalign dukan karar rawa wanda ake nufin isharantar da matan dashi da cewa lallai tanayin kuskure cikin hakkin mijinta sannan kuma mijin yanada hakki na gyarata da daidaita ta, kuma hakika musulunci ya gindayawa miji matakai na warware matsalolin mace wanda ta bijire wanda matakai ne da suke gabanin duka ya sanya duka shine shine mataki na karshi ga duk macen da bata gyaru ba har zuwa wannan mataki, kuma musulunci ya zo da tsawatar wa da hukunce hukunce na shari'a ga mijin da ya wuce gona da iri yadda zai zama me sabo me ketare iyakokin Allah madaukaki wanda ya cancanci a azabtar dashi duniya da lahira wannan matakai kuwa sune:

Dokokin ladabtar wa da duka:
1-    Bi mataki bayan mataki wurin warware matsala ta hanyar yin kokarin sa wurin matakai na farko dana biyu wanda suke gabanin duka da yin wa'azi da fadakarwa sa'annan kaurace mata a wurin kwana.
2-    Dukan ya kasance da asiwaki ko kuma makamancin haka wanda dan kara ne da be wuce tsayin pensir din rubutu ba da fadin sa.
3-     Nisantar fuska wurin duka ko kuma gabban da ake ji dasu, saboda musulunci ya hana dukan fuskar na miji ne ko mace ko kuma dabbobi, saboda fuska tana da daraja sannan kuma taba shi yana cutar da ganin mutum kamar yadda aka haramta dukan gabbai wanda ake ji dasu na jiki kuma an tsananta akan hakan, wannan sune iyakokin Allah duk kuma wanda ya ketare su to yayi zunubi.
4-     Wurin dukan kada ya zama a idon mutane cikin ko wani hali, baya halatta miji ya duki matar sa a gababan mutane musamman yaransa, saboda hakan akwai wulakanta matar acikin sa a karon farko sannan kuma jawo lallacewar tarbiyyan yaran, wani irin tarbiyya ce wannan uba keyi da dukan mahaifiyar su a gaban su ko kuma a kunnan su?!!!
5-     Kada dukan ya zama me cutarwa wanda zayyi mata tabo a jiki ko kuma karaya ko ciwo, duk mijin daya jima matar sa ciwo ko tabo ko karaya yayi zunubi kuma wannan miji mugu ne me bushashen zuciya wanda bayason gyaruwan matar kawai hukuntata yake sonyi sannan kuma ya jawo kiyayya sannan kuma shari'ar musulunci me adalci ta wajaba a tuhume shi da kuma hukunta shi akan haka.

 

Babi na shida
Dukan mace cikin sauran addinai
 Lallai maganar dukan mace ba matsala ce wacce ta shafi wani lokaci ba ko zama daya kawai ba cikin al'umma guda daya, a'a wannan matsalatra kwaita cikin dukkanin al'ummomi na dukkanin zamani baka daya, kuma duk wanda yakeson sani darajar mace cikin al'ummonin da ana samun littattafai dayawa wanda sukayi magana akan hakan, game da darajar mace kuma cikin al'ummar girka da rumawa da china da hindiya na da can… zuwa dai karshen su, sannan kuma akan haka yaya addinin yahudanci da kiristanci suka mu'amalaci al'amarin dukan mace wacce ta zama matsala wanda aka saba kuma tana yaduwa cikin al'umma tsofaffi har zuwa al'ummar shugaban mu almasihi, shin shugaban mu almasihi amincin Allah ya tabbata a gareshi yayi magana akan haramcin dukan mace koda sau daya?!!! Kuma shin akwai nassoshi cikin littattafai masu tsarki ltsohon alkawari ne ko kuma sabon alkawari wanda ya haramta ko kuma kyamatan dukan mace?!! Bayan bincika zai bayyanan maka cewa babu wani abu wanda yake nuna haka.
Idan kirista ya duki matarsa shin yayi sabo sannan za'a hukunta ta fuskan addini wanda hakan itace ukubansa wanda nassi yazo dashi cikin littafi me tsarki? Hakika bayi sabo ba saboda babu wani nassi wanda yake nuna hakan cikin littafi masu tsarki shin tsohon alkawari ne ko kuma sabon alkawari!!
Kamar kuma yadda babu wani hukunci ta bangaren doka na ukuba akan mijin daya duki matar sa sai dai idan alamar ta'addanci ya bayyana a jikin matar kamar karaya ko kuma kunburi ko ciwo, amma idan babu wani alama wanda ya bayyana a jikinta to tayaya za'a tabbatar da dukan nan nashi dayayi mata!!! Ma'ana idan yayi mata duka wanda babu ciwo ko karaya acikin sa baza'a mai wani ukuba baa nan duniya ko kuma cikin dokakin su!!!
Mu duba mugani cikin yahudanci da buzanci shin akwai wani nassi wanda yake haramta dukan mace?!!!
Hakika babu wani nassi na addini cikin ko wani addini wanda yake haramta dukan mace sai cikin musulunci kadai!!!!!! Kafin ko bayan dukan mace ya tashi daga hukuncin haramci ne zuwa makaruhanci dukda haka dai musulunci shi kadai ne wani addini wanda ya nassanta akan kyamar dukan mace!! Amma sauran addinan babu furta ba kai tsaye haramci ko kuma kyaman haka a wurin su.
Kamar yadda babu wani addini wanda ya shinfida dokoki ya iayaka wurin dukan mace sai musulunci kawai, watan ma'ana idan miji kirista ya kasa mallakan zuciyar say a duki matan sa, to menene tsari ko kuma iyaka wanda baya halatta ya ketare su? Shin kiristanci ya nassa akan dokoki da iyaka ga miji na dukan matan sa kamar ace kada ya duki fuskanta ko kuma yayi mata rauni wanda zai bar mata tabo ajiki… da sauarn su? Hakika babu hakan.
Duk me lura da rayuwan mu nay au wanda muke ciki sai ga akwai wasu adadi na kiyasi game da dukan mata wanda mazan kiristoci sukeyi ko kuma yahudawa ko kuma sauran su wand aba musulmai ba, kaje ka bincika cikin hukunce hukunce da kararraki a gaban yan sanda ko kuma kotu a amerika da kasashen turawa zakaga adadi wanda aka kiyasta na dukan mata wanda mazaje marasa tausayi suke yima matan su da yaran su!!!
Hatta a cikin al'ummar jihiliyya gabanin zuwan musulunci zaka samu cewa larabawa suna zane matan su irin bulalan da sukeyi ma bayin su kuma hakan ya zama sananne ko al'ada wanda ba haramun bane ko kuma akwai hukunci akan haka na wani shari'a ko kuma wani doka, a lokacin da aka aiko Muhammad s.a.w ya hana wannan aiki hanawa me tsanani sai yace: " shin dayan ku zai duki matar sa da dara da gangan kamar yadda yake dukan zane bawan sa sa'annan kuma ya kwanta da ita a cikin daren", buhari da muslim ne suka rawaito shi amma lafazin na buhari ne, a cikin wannanhadisi manzon Allah yana raddi game dukan matar sa cd rana sannan kuma da daddare yana neman ya kwanta da ita!! Watan ma'ana taya zaka zama mugu me baki hali da ita da rana amma kana son ta manta hakan da daddare ka lallashe ta!!.

Abubuwan da aka kalato game da darajan mace cikin littattafai masu tsarki cikin tsohon alkawari da sabon alkawari:
Sau dayawa abunda mutanen addinin kiristanci suna sawwara mana shine shugabammu almasihi amincin Allah ya tabbata agareshi shine mutumi na farko wanda ya fara karewa mace hakkokinta kuma shine wanda ya bata hakkokinta wanda babu wani addinin da suka bata irin sa, kuma littafi me tsarki ya mata adalci sannan ya kuma daga darajarta!!! Sai dai kuma shin wannan maganar yana daidai da aikin mu na yanzu?!!!
Kowa ya sani cewa littafi me tsarki ya haramtawa mace shiga cikin tsarin shugaban cin coci wanda shine shugaban masu tsarki ko kuma meyin yankan me tsarki, shin wannan mace karama ce ko budurwa ko tsohuwa, al'amarin bashi da alaka da shekaru ko kuma jinsin mata, babu wani littafi cikin littattafai amsu tsarki na tsohon alkawari ko kuma sabon alkawari wanda yayi ishara da shigan mace cikin tsarin shugabancin coci, bare kuma a bata daman a zama cikin malaman addini, mace asali ma ba'a mata izinin magana ba a cikin coci ko kuma karantan wani abu cikin coci kuma ba'a bata izinin neman wani matsayi ban a manyan malaman coci kawai matsayin da aka yardan mata da nema shine mataimakan malamai wanda matsayi ne nayin hidima ga malamai!!!!! Hakika littafi me tsarki ya gabatar mana da nau'oka na malaman su dukkanin su mazaje ne shin manyan malaman ne na farko kamar Nuhu da Ayyub da Ibrahim da Ishaq da yakub, ko kuma kuma malaman haruniyya ne ko kuma malaman malikus sadik, ko kuma malaman manzanni da khalifofin su na kasa kasa, dukkanin su mazaje ne, sannan da ace za'a ba mace matsayin malanta da shugabarmu Maryam akaba itace tafi cancanta da wannan matsayi sai dai karkashin karantarwan addinin kiristanci an haramta ma mace haka!!!!!

Bari mu kawo wasu daga cikin nassoshi cikin littattafai masu tsarki domin muga matsayin mace a cikinta da darajar ta:

1.    Mace ana azabtar da ita da laifin namji:
Safar na Irmiya (23:34): " annabi ko kuma wani mahaluki ko mutanen da yake cewa: wahayin Allah, za'a azabtar dashi da iyalin sa"
2.     Kona mace mazinaciya da wuta:
Safar al lawiyyin (9:21): " idan wani mahaluki ya tayi sabo na zina to hakika tayi datti a kona ta da wuta"
3.     Yanke hannun mace da wasu dalila wanda hankali baya dauka:
Safar al tasniya (11:25): " idan mutane biyu sukayi fada da juna mutum da dan uwan sa sai matar daya daga cikin su tazo wurin domin ta kwaci mijinta sai hannunta yayi tazar ce ta kama al'aurar sa, za'a yanke mata hannu kuma za'a tsire idanun ta".
4.     Macen da aka saketa da ita da tsohuwa mara aure da mazinaciya duka daya ne:
Safar al lawiyyin (9:21): " duk wani mutum me girma ….., wannan yana auren mace ce tsarki. Ita kuma mace tsohuwa mara aure ko wanda aka saka ko me daddi ko mazinaciya to kada ya aure daya daga cikin su, sai dai ya aure masu tsarki daga mutanen sa, sannan kuma kada ya bata shukar sa a tsakanin kafafuwar sa saboda ni ne ubangiji me tsarki".
5.     Bautar macen da aka saka ga mijinta:
Sakon bulus zuwa ga mutanen afsis (5:22): "yaku mata kuyi bauta ga mazajenku kamar ubangiji, saboda namiji shine shugaban mace kamar yadda masihi shine shugaban coci kuma shine me tsarkakejiki. Sai dai kamar yadda coci take bauta ga masihi, haka mata zasu rika bautan mazan su cikin komai"
6.    Wajabtawa mace yin shiru cikin coci:
Sakon bulus na farko zuwa ga mutanen kurunsus (14:34): " matan ku su rika yin shiru a cikin coci, saboda ba'ayi mata izini ba da magana kawai bauta zasuyi kamar yadda namus yace. Sai dai idan suna son sanin wanin abu to su tambayi mazajen su a gida, saboda abun kyama ne ga mace tayi magana cikin coci".
7.    Mata sanadi ce ta bata:
Sakon bulus na farko zuwa ga timosayis (11:2): " mata su koyi shiru cikin bauta. Sai dai ba'ayima mace izini ba da neman ilima ko kuma ta shugabanci namiji, ta zauna shiru kawai, saboda adam aka fara halitta sannan sai hauwa. Kuma adam beyi laifi ba mace ce tayi laifi sai ta'addanci ya auku. Sai dai wannan zunubi nata zata tsakaka daga garesu da haihuwan yara matukar sun tabbata cikin imani da so da girmamawa tare da hankalta"
8.    Shugabantan namiji ga mace:
Sakon badris na farko (3:1): " gare ku yaku mata ku zama masu bauta ga mazajen ku… taka adon ku ya zama irin adon wace, na bude gari da sanya zinari da tufafi, sai dai mutumin zuciya na biye wurin tabbatar da farna, adon rai da bankwana na tsanake, wanda sune kafafuwan allah masu yawan nauyi.haka mata suka asance ada can masu tsarki da tawakkali ga allah suna gyara jikin su suna bauta ga mazajen su, kamar yadda saratu tayima Ibrahim biyayya tana me kiransa da "shugabana".
Safarul takwin (3:16): " sai mace tace: ina wahala dayawa wurin daukan maka ciki da Haifa maka yara kuma ga kafafunka nake biyayya"
9.     Jifar mace mazinaciya har sai ta mutu:
Safar al tasniya (22:13): " idan mutum ya aure mace lokacin da yayi amfani da ita sai yaji ya kita, ya kuma jingina mata dalilan magana, sannan yayi ishara da cewa sunanta mayafi, sai yace: wannan matar na rike ta kuma nayi zunubi da ita ban sameta da budurci ba, sai uba da uwa su dauki yarinyar su su fitar mata da alamar budurci zuwa ga malaman garin zuwa ga kofa,… sai malaman wannan gari su dauki wannan mutum su ladabtar dashi suci tarar sa na azurfa dari,… sai dai idan wannan al'amari ya kasance ingantacce ba'a sami budurci ba ajikin yarin yan. Sai a fitar da ita zuwa kofar gidan babanta mazajen wannan gari su jefe ta da duwasu har sai ta mutu".
Safar al tasniya (22:22): " idan aka samu wani mutum kwance da wata mace matar wani, to a kashe su biyun: namijin daya kwanta da matar, sai a cire sharri daga isr'il".
Safar al tasniya (22:23): " idan mace budurwa ta wani ya nemi aurenta sai wani mutum ya sameta na daban ya kwanta a ita a cikin gari, to ku fita dasu zuwa kofar wannan gari ku jefe su da dutse har sai sun mutu".
10.    Mace tana kasa da namiji a daraja:
Sakon bulus na farko zuwa ga mutanen kurnunsus (11:3): " inason ku sani cewa shugaban ko wani namiji shine masihi, shugaban mace kuma shine namiji, shugaban masihi kuma shine Allah. Ko wani mutum da yake salla ko ya zama annabi to akan sa akwai abu wnada wulakanta kansa, amma duk mace da take salla ko annabta kanta abude to ta wulakanta kanta saboda da ita da wanda aka aske abu daya ne. idan mace ta zama bata rufe kanta to a rake mata gashin kanta, idan kuma ya kasance abun kyama ga mace a rage mata gashi ko kuma aski to ta rufe shi. Baya halatta namiji ya rufe kansa saboda kasancewar sa surar allah da kokarin sa. Ita kuma mace kokarin namiji ce, saboda namiji ba daga mace yake ba ita macen ce take daga namiji. Kuma saboda na miji ba'a halicce sa ba domin mace, ita macece aka halitta domin namiji. Saboda haka ya wajaba ga mace ya zama akwai shugabanci akanta saboda da mala'ika."
11. karantar da mata littafin diskoliyya (littafe ne wanda ya kunshi karantar da ubangiji da manzanni):
Babi na biyu cikin littafin diskoliyya me maudu'in (ya wajaba akan mata su bautawa mazajensu kuma su rika tafiya ka hikima) yana cewa: " mace tayi ma mijinta bauta domin shine shugabanta,… kiri tsoron mijin ki ke mace, kuma ki rikajin kunyar sa da neman yardan sa shi kadai bayan Allah, kamar misalign abunda mukace, ki hutashe dashi wurin maki hidima domin ya jawo zuwa gareki,…. Idan kina son ki kasance mumina wanda Allah ya yarda da ita kada ku rika kwalli domin samarin mazaje su yarda, kuma kada ki rika sha'awar riga mara nauyi masu nauyi wanda basu dace da kowa ba sai mazinata domin wanda suke son ki kasance a haka su rika binki. Idan kun kasance bakwa aikata wannan ayyukan masu muni saboda zunubai to ki rika kwalliya ke kadai domin addini saboda da haka ne zaki tsagu ga wanda zai ganki yayi sha'awarki, to me yasa bazaku kiyaye ba domin kada ku fada cikin zunubi, kuma kada kusa wani yafada cikin shakka ko kuma kishi domin ki, idan kinyi kuskure na daurewanki akan wannan aiki to lallai zaki fadi, domin kina gina sababi ne na halakar da ran wannan mutumi. Sannan idan kayi kuskure ga wani akan wannan aiki lokaci daya shi kuma zai kasance sababi na kayi kuskure ga mutane dayawa, ke kuma kina cikin karanci kwadayi, kamar yadda littafi me tsarki yake cewa: (idan munafika ya fada cikin sharrukan mutane dayawa to lallai yana sani da kuma yawowa masa radadi da kunya), duk wacce take aikata haka zata halaka da zunubi sannan kuma zata farauto zuciyar maza ba tare da kayan farauta ba, ku karanci abunda littafi me tsarki yake cewa game da wanda yake kirkira akan wannan mutane kamar haka cikin fadin sa: ( kanakin mace me zunubi sama da mutuwa, wannan dinnan da ta zama abun farautan jahilai), ya kuma kara fada a wani wuri na daban: ( misalign tsutsan da yake cin katako, haka mace me zunubi take halaka mijinta) ya kuma kara fada cewa: ( abunda yafi shine zama a lungun saman gida sama da zama tare da mace me datti mara kama kai). Kada kuyi koyi da irin wannan mata, yaku matan misihi idan kuna son ku kasance muminai to lallai ku himmatu da mijinki domin samun yardan sa shi kadai. Kada kawata fuskar ki da Allah ya halicceta, babu abunda yake rage kwalliya, soboda dukkan abunda Allah ya halicce sa yana da kyau sosai, baya bukatar kwalliya, duk abunda ya karo akan kyau to lallai yana canza ni'imar mahalicci. Idan kina tafiya ya kasance kina kallon kasa bayan kin rufe jikinki baki daya, ka nisanci dukkanin wani aboki wanda be cancanci kasance wa abayi ba tare da mazaje, da yawa abokan fasikanci ne, kada mace mumina ta rika cudanya da maza. Sannan kuma idan zata rufe fuskarta ta rufeshi da tsoron kallon maza samari… abunda ya wajaba agareki idan kin kasanc emumina shine ki guji dukkanin nau'i na kari, da kuma kallon idanu dayawa… (lallai zama a daji yafi alheri da zama da mace me dogon harshe mara tarbiyya)".
 
Babi na bakwai
Dukan mace cikin al'ummar yamma na kiristoci
Makiya musulunci dayawa sunyi kokarin yada wasu shubuhohi game da musulunci daga cikin su akwai maganar dukan mace suna amfani da almakashin su na sirihi wanda suka saba yadda suke hakaito wa daga cikin ayoyin alkur'ani me girma da hadisan manzon Allah s.a.w dukkanin maganar da shubaha zai ina hawa kansa tare da tabbatar da abunda zai tabbatar da wannan shubuhar nasu, kamar duka a cikin musulunci misali sais u ambaci tsurar maganar kawai ba tare da Ambato maganar da yake gaban sa ba ko bayan sa suna kokarin kawo shibuhohi na karya akan musulunci da dabarar su mummuna wacce tayi nisa gabaki daya da gaskiya da maudu'i, baza su kawo maudu'in ba baki dayan sa sais u yanke sa wanda za'a masa mummunan fahimfa, musa yin wannan aiki suna kirkiran karya ga musulunci da ikirarin wayewar su da warkewan su wurin mu'amala da mace da matan sun a gida, sai dai a hakika sun rufe idon su akan wasu gaskiya da hakika masu zuwa:
Na farko: lallai musulunci shine addini daya tilo wanda yayi bayani akan alaka ta rahama da soyayya tsakanin ma'aurata, kuma shine addina daya tilo wanda yah aka ta'addanci da cuta na magana ne ko kuma aiki, Allah madaukaki yana cewa: " kuma daga cikin ayoyin say a halitta maku mata daga kawunan ku domin ku samu natsuwa zuwa gare su ya kuma sanya soyayya da rahama atsakanin ku"
(suratul rum ayata 21)
Amma fa musani cewa wannan soyayyar da rahama bata zuwa sai bayan daurin aure ingantacce wanda ya halatta a shari'a.

Na biyu: lallai musulunci shine addini daya tilo wanda ya magance duka da wulakantar da mace da kuma kallonta da idon nakasa tun shekaru dubu daya da dari hudu da suka wuce a baya ya kuma irga hakan daga cikin ayyukan nakasu ga maza.
Da ace zamu bincike na keke da keke cikin littattafai masu tsarki na kiristoci tsohon alkawari ne ko kuma sabon alkawari bazamu samu ishara ba akan haka na kusa ko kuma ta nesa wanda yake haramta dukan mace.

Na uku: lallai musulunci ya kwadaitar da yin mu'ama na karamci ga mata cikin dukkanin ayoyin alkur'ani da hadisai masu daraja wanda suke magana akan alaka tsakanin ma'aurata, Allah madaukaki yace: " suma sunada irin abunda kuke dashi akansu a wurin na kyautatawa"
(Suratul bakara ayata 228)

Na hudu: lallai musulunci ya sanya mu'ama ta mutane ta jin kai musamman tsakanin ma'aurata daga cikin ayyukan da suke jawo lada da sakamako, manzon Allah s.a.w yace: " babu wata ciyarwa da za'ayi ana neman yardan Allah da ita face Allah ya baka lada akanta hatta loman da zaka sanya a bakin matar ka" buhari da muslim ne suka rawaito shi.

Na biyar: lallai musulunci ya halalta dukar mace a wasu lokuta bawai ka'ida bace sannan kuma gindaya wasu sharudda ga miji wanda zai farayin su kafin duka wanda shine mafita na karshe sannan kuma dukan ya kasance kare barna ne babba, saboda kasancewar mata ba'a yanayi daya suke cikin dukkanin zamani da al'umomin da iyalai. Abunda zai iya daidai da wannan al'umma ba dole bane yayi daidai ga wasun su kila ma su ya cutar dasu ne, sannan abunda zayyi daidai na mu'amala da wani mace bazai zama yayi daidai ga waccen macen ba cikin wani al'umma ta daban ko kuma cikin zamani na daban duk yadda kayi kokarin sanya shi ya dace da ita kuwa, hakan yana cikin gamayyar muslumci da karade dukkanin al'amura.

Na shida: lallai zahirin mugunta na zamanta kewar iyali ya yandu cikin garuwan mutane da kasashe wanda sukaci gaba da wanda basuci gaba ba cikin wannan zamani namu, maza nawa ne na kiristoci turawa suke yin ta'addanci a fili ga matan su a gaban mutane a filin jirgi ko wurin cin abici ko wani wurin taruwa na daban kai hatta akan tituna manya a gaban wurin wucewar mutane ana samu hakan bawai a asirce akeyin su ba a'a takai ga har a gidajen yada labarai wanda ake gani da wanda akeji duk suna kawo wannan labari.
Kuma mata nawa ne na kiristoci cikin turawa cikin Amerika da kanada da austreliya wanda suka ware bangare nay an sanda domin fuskantar aikin ta'addanci akan mata na duka gada mazajen su, sannan wannan shari'ar bazata yiwu ba sai ansamu alamomi na fili kamar yadda mukayi bayani a abaya kamar karaya ko kuma kunburan kasan ido ko tabo a fuska saboda da wannan duka, duk wanda ya bincika cikin hasashe na gwamnati na bangaren yan sanda cikin amerika da kasashen turawa da austireliya hakan zai bayyanan masa.

Yaduwar alamar duki cikin a'umma yamma:
Abunda yake bayyana yaduwan mugunta na iyalai cikin kasashen yamma wanda suke ikiraren wayewa da ci gaba na hakkin dan adam bana arziki ba abubuwa ne Kaman haka:
1.    Yaduwar kungiyoyi na hukuma da wanda bana hukuma ba cikin kasashen turawa wanda suke kurmushe matsalar ta'addanci ga mata da muguntan iyalai wanda sashin shari'a ta kasa magance masu hakan na zalumcin mazaje akan matan su.
2.    Wannan sanarwan da ake nanatawa akoda yaushe cikin kafafen yada labarai wanda ake gani da naji wanda suke kwadaitar da isar da hukuma cikin gaggawa game da duk wani labari na ta'addancin daya daga cikin ma'aura ta ga abokin zaman sa.
3.    Tambayoyin da akeyima daidaikon al'umma a koda yaushe na kasashen yamma wanda daga cikin su akwai:
Shin ka taba dukan matar ka ko sau daya ne?
Shin ka taba gani ko ji a wata rana ko sau daya ne babanka ya duki mamarka?
Shin ka tabaji abaya cewa wani daga cikin yan uwanka ya duki matar sa?
Shin ka tabajin daya daga cikin makwabtar ka ya duki matar sa?

Abun nufi na yin wannan tambayoyi ga mutane shine anason tabbatar da afkuwar samun ta'addanci ga mata daga mazajen su kiristoci cikin dukkanin kasashen turawa da amerika da Canada da austireliya, kuma wannan shine zahirin abunda yake yaduwa a tsakanin su dayawa.
A karshe falalar musumci ga mace zai bayyana ga dukkanin mutum me adalci kasancewa shi kadai ne addini daya tilo wanda ya karrama mace ya kuma daga darajarta da sunanta daga dukkanin wanda yake toye mata karamarta yake kuma jarabtar kamewarta sannan kuma yayi tsoratarwa babba game da zalumtar mace, manzon Allah s.a.w yace: "lallai ina jiye maku hakkokin masu rauni marayu da mata a kanku" Ahmad ne ya rawaito shi da nasa'i da ibn majjah kuma yana cikin littafin sahihul jami'u 2447.

 
www.islamland.com