HALITTAN JARIRI A MATAKAI

HALITTAN JARIRI A MATAKAI

  

  

 

Allah ta'ala yana cewa: "me yasa ba ku neman daraja  daga Allah *  lalle ya hallice ku a matakai" nuh 13-14.

Allah ta'ala yana cewa: "me yasa ba ku neman daraja  daga Allah *  lalle ya hallice ku a matakai" nuh 13-14.
 
Haqiqar ilimi:

Harvey shine farkon wanda ya fara nazari  akan  xan tsakon kaza ta hanyar amfani da gilashin a shekara ta 1651, sannan kuma ya yi nazari  akan  tayin barewa saboda wahalar da ya fuskanta  wurin sanin haqiqanin  yadda ciki yake a farkon kamuwarsa, sai ya tabbatar dacewa ciki wani yanayi ne na kumburin mahaifa. ashekara ta 1672 wani malami wai shi Graaf ya gano qwayaye a mahaifa waxanda ake kira da" Graafian Follieles", kamar yadda ya gano wasu kafafe acikin mahaifar zomo masu ciki, daga nan ya gano cewa ciki ba kumburin mahaifa bane . aa kwayayene da suke kyankyasuwa acikin mahaifa wato Blastoeysts. A shekara ta 1675 wani malami mai suna Malpighi ya gano ttayin tsako acikin kwan kaza amma yaga cewa  baya buqatan maxadin kyankyasa  daga namiji.ya gano cewa yana kara girma amma ba akan matakai ba. Ta hanyar amfani da madubin likita Leeuwenhock ya gano yadda kwayayen mutum ke ginuwa a matakin farko ashekara ta 1677,amma ba su gano yadda abin ke kaiwa har likacin haihuwa ba.,amma dai sun gano cewa tayi na hauhawa daga mataki zuwa mataki. A shekara ta 1759 Wolff yayi hasashen yadda jariri ke girma akan matakai .

ashekara ta1775 aka qarasa rikicin cewa jariri ba lokaci guda yake haxuwa ba sa ya bi wasu matakai  bayan gwajin da Spallanzani yayi  akan wasu kwayoyin halittu . a shekara ta 1827 bayan shekaru 150 kenan aka gano cewa  wani malami Von Baer ya gano kwayaye acikin wata karya mai ciki . sannan a shekara ta 1839 Schleiden da Schwann suka gano yadda hallittan bil adam ke hauhawa mai suna CELLS. Daga baya aka gano yadda haqiqanin lamarin yaketa hanyar haxuwar kwayayen mace da maniyin namiji,.
 
Fuskacin mu'ujizar:

ayoyi sun tabbatar da cewa mutum na hauhawa ne mataki bayan mataki savanin abin da aka sani abaya lokacin su Arastol na cewa a dunqule mutum yake faruwa sannan ya girma har haihuwa

yanzu il;imin likitancin zamani ya tabbar da yadda mutum yake hauhawa tun daga kwai har ya zuwa kyankyasa da ikon Allah. Wannan shine abinda Ubangiji ya bamu labarinsa acikin kur'ani mai girma na halittan mutum.